A d u n i y a ta complt by huguma - Chapter 12
A d u n i y a ta complt by huguma Chapter 12: A d u n i y a ta complt by huguma Chapter 12. Tun daga tashar da suka samu mafaka sukasan lallai an baza…
4,491 words
Tun daga tashar da suka samu mafaka sukasan lallai an baza nemarsu,a daren suka haye motocin kaya dake lodin arewa suka wuto gida.......wanda sai daga bisani abba yasan komai.
Yayi fada yayi fada kaman zai ari baki......ya kuma yi musu fadan da bai taba musu shi ba,musamman me babban suna da yake girmama sunansa yake kuma qaunar yaron har cikin ransa. ANNI ce ta sanya baki aka samu ya lafa sannan aka fara tunanin yadda zaa yi da abinda ya haqo din,tunda ya riga ya shigo hannu ba batun ace za'a maida musu.
Bisa dukkan dokoki da tsare tsare kan tsaftatacciyar hanya aka tsara komai ya zama dukiyar da a yanzun suke juyata shida farouq dinsa. Abban kuma ya zame musu jagora madubi.....ma'adanin kuma ya zama shine kasuwancinsu.....babbar masana'antar karbar haqaqqun ma'adanai su tace su gyarashi su fiddashi xuwa manyan qasashe,irinsu china,south Korea japan UK da manyan qasashen dake hulda da cinikayyar ma'adanan qasa masu tsada da daraja.
A nahiyar africa JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES ya zama kamfani na daya da qasashen ke rububin karbar kaya a hannunsu bayan doke Coregeo mining company din da yayi. Kamfanin daya jima yana murza zarensa da kyau,sai gashi rana tsaka JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES yazo yasha gabansa ta ba zata,al'amarin daya haifar da takun saqa me girma a zuciyar kamfanin. Duk da fu'ad yasan da wannan......amma ya dauka normal competition da kishi ne da kan iya faruwa tsakanin kowanne kasuwanci,saidai ga mamallakin kamfanin JOE abun ba haka bane.
*_D A W O W A_*
Dubansa abba yayi bayan ya aje mug din hannunsa
"Kwanaki nawa ya rage mu tafi ne me babban suna?" Zama yayi sosai yana goge gumin fuskarsa da dan qaramin towel din da magaji(hadiminsa) ya miqo masa.
"Ba zamu wuce sati daya ko kwana biyar ba abba,hankalina yana kan anni......jikintan nan ya fiya matsawa da yawa" Yayi maganar alamun abun yana tabashi ya bayyana har saman fuskarsa. Idanu abban yadan zuba masa,har a ransa yana cike da zallar mamaki na yadda me babban suna ke damuwa da anni da rayuwarta fiye da dukkansu su ukun. Annin da abban yake ganin ba itace halitta ta farko data cancanci samun wannan qauna da kulawa daga gareshi shi din ba......annin da yake ganin kulawar da yake bata baifi ya bata kaso hamsin cikin dari ba.......ita kanta wasu lokuta tana sanya damuwa a ranta game da inda yafi karkatar da kulawar tasa sama da daya bigiren da shine dolensa,.....kuma akafi buqatar hakan daga gareshi.
"Yanzun haka ma nan da awa daya zan fita,zamu gana da ceo na Labrilliante company,zan miqa musu iya abinda zasu samu.....don abba wannan karon tunanina ya fara sauyawa" Maganar fu'ad cikin tatacciyar nutsuwar nan tasa da wani irin jan aji kamar mace ya dawo da Alhaji hamza daga tunaninsa
"Wanne tunani ne fu'ad?" Zamansa ya gyara sosai yana bawa abba dukkan kallo da hankalinsa
"Abba......a yadda mutanen nan daga kowacce qasa suke rububin siyan resources namu da muke fiddowa daga qarqashin qasar da Allah ya shimfida mana kadai ya isa ka fahimci suna amfani damu ne suna kuma amfani da damarsu......yanzu haka a daren jiya kafin na kwanta sai dana karba kira daga wani company dake japan bayan ainihin kamfanin da muke kaiwa kaya......suna taya kayanmu akan farashin da wancan kamfanin basa bamu......wannan shi yasa nayi wani nazari......abba ya kamata qasarmu ta amfana da wadannan ma'adanai masu tsada da daraja,wanda mu Allah ya mallakawa su.....abba inda a qasarsu wadannan ma'adanai suke,babu wani baqar fata daya isa ya sameshi.....it's hardly ka iya isa wajen......nayi tunanin bude babban company da zai dinga sarrafa wadannan ababen zuwa kayan qyale qyale na mata.....don dama company daya muke da na alhaji rayyan(dangantakar zuciya),shi kuma duwatsu masu daraja suke sarrafawa ba gold ko diamond ba".
Shuru abba yayi yana girgiza kai. Tabbas fu'ad din yazo da tunani me kyau daya kamata ace tuntuni sun yishi
"Na yarda da wannan tunanin naka.....to amma fu'ad qarqashin haka akwai tarin matsaloli da qalubale......"
"Na sani abba......insecurity na qasarmu ma kawai qalubale ne......amma a hakan.....ya zama dole mu raya qasarmu da kowanne qaramin chance da muka samu a rayuwarmu......tsoro da tunanin asara ko faduwa shine abinda zaici gaba da kasheta kowacce rana......bayan tsoron dauko shi akayi aka dasa mana shi a zukatanmu......kuma ake da buri da fatan ganin ci gaba da wanzuwarsa har zuwa rayuwar na bayanmu"
"Best son ever" Abban ya furta yana sakin wani irin murmushi tare da jin qarin alfahari da fu'ad din,gefe guda kuma yana taya ainihin mahaifinsa murnar samun nagartaccen yaro mara tsoro irin muhammad fu'ad din.
Qas yayi da kansa cikin girmama abban
"A tayamu da addu'a abba"
"Kullum cikinta muke"
"Allah yaja kwana,ya qara lafiya me amfani" Ya masa addu'ar da yake jinta har cikin zuciyarsa.
Agogon dake manne a bango ya kalla,sai ya miqe a nutse yana cewa
"Zan qarasa ciki abba na shirya kada na sabawa lokaci"
"Hakan yayi kyau" Abba ya fada fu'ad din yana sake burgeshi saboda yadda ya dauki alqawari da matuqar muhimmanci kaman yadda yake girmama lokaci.
A nutse ya tura qofar dakin da sallama a bakinsa,duk kuwa da yasan ba wanda zai taras a ciki. Dakine da duka duka basufi sati guda a cikinsa ba......amma har ya kama ya kuma rine da sassanyan qamshin nan nasa dake iya bawa zuciya nutsuwa da kwanciyar hankali koda cikin radadi da qunci take.
Towel din hannunsa ya rataye,ya kuma matsa gaba kadan ya ajjiye takalmin motsa jikinsa wanda daga ranar da suka tasamma barin Korea sunansa shara. Baya yawo da kaya,kowacce qasa zaije,koda kwana nawa zaiyi single yake tafiya abinsa,saidai yana sauka a qasar komai da zai buqata na amfani zai sanya a tanadar masa,yana gama amfani dashi kuma a nan zai barshi ya qara gaba.
Matsawa gaba kadan yayi gaban wata mini dispenser da tafi kama da tulun zamani wadda ke zaune saman wani kyakkyawan table kusa da mirror,ya dauki disposable cup ya matsi ruwan dake da madaidaicin yanayi ya fara sha a hankali bayan yayi tsaye gaban madubin idanunshi a kai kamar me karantar yadda yake zuqar ruwan zuwa cikinsa.
Ya gama ya ajiye saman madubin yana fidda siririyar iska yana ci gaba da kallon fuskarsa a madubin. Kyakkyawar sumar kansa data wadatu da tsafta ya taba sannan ya gangaro zuwa madaidaiciyar qasumbarsa data hade da gemunsa wadda ta zamawa fuskarsa wani lafiyayyen ado daya qara fidda zahirin kyawun fuskarsa,ta kuma qara masa wani mahaukacin kwarjini. Gemun da qasumbar daya zama topic of discussion a wajen 'yammatan da suka marmace a kansa. Kusan kowacce tana gayawa kanta namiji babu gashi a fuska ai mace ne,bata taba ganin qasumba da gemu da yakai kyan nasa ba......tsabar macewa a soyayya ne.....ko kuma zallar tsagwaron gaskiya suka fadi?.
Rigar jikinsa ya yaye zuwa sama sannan ya zareta ya ajjiyeta saman gadon,wannan ya bawa Ginannun muscles din jikinsa bayyana muraran. Muradden jikin da zai gaya maka adadin lokutan da aka bata ana bashi kulawa ta fannin lafiya da cin lafiyayyen abinci me gina jiki. Yayi taku daya don dauko bath set nashi zai wuce toilet sai ya fasa,ya dawo da baya ya dauki wata farar samsung dake ajjiye saman mirror din.
Yaga miscal amma sai ya fara maida hankalinsa ga dalilin daukar wayar,ya latsa ya fara lalubar magaji. Umarni ya bashi na abincin da zai hada masa kafin ya fito,saiya maida wayar yana shirin ajeta kira ya shigo wayar.
Cak ya tsaya yana kallon sunan dake tsalle saman wayar. MOM kaman yadda farouq ya dauka da hannunsa yayi masa saving. Kafe sunan yayi da idanuwa,wayar tana kadawa hade da zuciyarsa. Sunan yake tuna ma'anarsa da kyau cikin kwanyarsa.....wadda aka maqalawa sunan ta cancanci wannan sunan kuwa anya?......ta dace data karbi sunan?,nata ne sunan da gaske?.
Kamar bashi da idea akan yadda ake daga waya,haka yaci gaba da kallon wayar har ta qaraci ringing ta katse. Ya sake daga qafarsa zai wucs kiran ya sake shigowa. Kamar dai dazu a yanzunma haka ta gama kadawa ta katse,kira na uku kuma ya sake shigowa immediately,saidai akasin dazu,yanzu sunan daya fito akai ya banbanta dana dazu.
Lovy dovy shine sunan daya bayyana,sai ya saki qaramin murmushi yana dawowa baya kadan. Kafin ya daga sai daya kalli lokaci,tabbas ya tsaya saurarenta ya tabbatar saita kwakwashe masa duka mintunan daya tsara zaiyi a gidan ya fice zuwa Labrilliante amma hakan bai sanya ya fasa dagawa ba,ya sanya wayar a kunnensa.
Da siririyar baby voice dinnan nata tayi masa sallama. A nutse fuskarsa a sake ya amsa
"I will call you back habibty.....nan da one hour haka?"
"Yes habibee.....byeee" Ta fada cikin rashin damuwa da kuma fahimtarsa a duk sanda ya sako mata uzurinsa. Wayar ya mayar ya ajjiye yana murmushi,daidai sanda a daya BANGAREN.........
Ta daga kai ta kalleta sanda take zaune a gabanta
"Waya yake amsawa hajiya" Ta fadi tana sauke wayar daga kunnenta bayan computer ta gaya masa ana amfani da layin ta hanyar amsa wani kiran
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:@Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
PAGE 32 ___________________________
"Waya kuma ake amsawa?" Ta tambaya cikin wata irin isa sa ginshiri tana qanqance idanunta,qwayar idanun nata suna kan wadda tayi maganar. Kai ta jinjina mata cikin bata tabbaci
"Eh haka ne". Juyawa tayi ta zauna sosai tana fesar da iska me zafi daga bakinta. Ta qanqance idanu sosai tare da zubawa guri daya idanu,abinda zai baka tabbacin akwai wani radadi me yawa da take ji daga cikin zuciyartata
"Alamu kenan suna nuna yaga kiran,nice dai…….nice dai da bazai amsa wayata ba,nice dai da bazai saurareni ba sai a sanda yaga dama ko kuma aka bashi umarni?" Ta qarashe maganar ta hanyar yiwa kanta da kanta tambayar. Tambayar da bata haifar mata da komai ba sai qarin qunci da bacin ran da ya sanyata miqewa tsaye.
Hannunta ta dunqule ciki juna,ta fara kai kawo tana naushin tafin hannunta da daya hannun data dunqule waje guda. Ba shakka tayi sake ba dan qarami ba,ba shakka kuma hajiya mariya tana son jefa kanta tsakiyar shingen da ba nata ba. A baya tayi tarin ayyuka game da hakan,amma idan har tace taga nasara tattare da hakan to tayi qarya me yawa ma,zata iya kiran ayyukanta na baya da JIYA I YAU,tana tsaye a waje daya babu sauyi ko qanqani,zata zuba idanu ne abubuwa mafiya daraja da kima a rayuwarta…..kuma mallakinta amma ace suna ci gaba da subuce mata?,suna ci gaba da zama haramiya a gareta?,shin zata yarda da zamowa 'YAR RAKIYA ko kuma taci gaba da wanzuwa a mazaunin 'yar kallo?.
"Ba zata sabu ba!" Ta furta a zabure sannan ta juya da sassarfa tana daukan mayafinta dake yashe saman kujera
"Tashi samira muje" ta bawa hadimar tata umarni,wadda ke zaune tun dazu guri daya tana duban kai komo da maganganun da takeyi ita daya
"Ina hajiya?" Ta tambayeta murya a lanqwashe. Tayi imanin tunda har ta buqaci fita irin wannan afujajan ba shakka ba alkhairi a cikinta sam
"Gidan alhaji hamza!" Ta bata amsa a tsawace da salon abun nan da ake cewa haushin kaza huce kan dami. Tsam ta miqe tana gyara daurin zaninta sannan ta wuce da sassarfa zuwa shiyyar dakunansu don dauko hijabi.
Cikin jerin amintattu kuma lafiyayyun dakunan da mansion house din na alhaji hamza kibiya ya mallaka. Zaune take tsakiyar wani lallausan rug dake a gefe daya na dakin wanda aka masa rukuni da lausasan sofas qwaya uku da suka zamewa wajen tamkar wani dan qwarya qwaryar falo ne na cikin bedroom. Wani irin lafiyayyen daki ne da ba zai barka kasan safiya ko dare ba,zafi ko sanyi,damuna ballanta rani ba muddin ka kasance wanzajje a dakin.
Daga saman rug din take zaune saman abun salla da zai baka tabbacin bata jima da kammala sallar walaha ba. Salla ceda bata taba wuceta a rayuwa muddin ba wani qaqqarfan dalili ya gifta ba,tun zamanin quruciyarta har kawo yanzu da girma da shekaru suka hau kanta. Shine kuma ya same mata sila da tsani na dawowa rayuwa hamza a shekarun baya,a sanda ta yanke zato da tsammani daga sake rayuwa dashi da kuma yaranta da suka zame mata sanyin idaniyarta.
Wataqila nutsuwa da kamalar da fuskarta ta wadatu dashi yana da alaqa da wannan din,yawan ibada,yawan bautar Allah,yawan azumin tadawwu'i da babu wanda yayo gadonta a wannan fannin qafa da qafa irin muhammad fu'ad.
Akwai haske sosai saman fuskarta,tana saye da atamfar chiganvy gold mekauri kyau da asalin tsada. Jikinta lullube da mayafi me kauri,yayin da yatsarta ke maqale da qaramin carbi irin na ma tsawa.
Daga gefanta saitin kafadarta shine a kashingide,kana kallonsu zakasan magana sukeyi,magana kuma irin ta da da uwa,hira cikin nutsuwa qauna da kuma kulawa
"Nikam saddiq……sake kiramin wayata mana,jakata tun ranar da akayi asibiti dani ban sake ganin gilmawarta ba,akwai muhimman abubuwa a ciki,harda kudaden Amna data bani ajiya" idanu ya zaro sannan ya miqe yana zama sosai
"What?,anni?,dollars fa?"
"Wallahi sadiq" ta fada a nutse.
"To Allah ya tsananta rabo,don auta ta saka buri akan wannan ajiyar,naji tana lissafin abinda zatayi dasu idan ta dawo" ya fada yana cusa hannunsa a aljihu yana laluben wayarsa. Fuskarta anni ta shafa tana fadin
"Idan har ba'a gansu haka zata haqura ai,tsautsayi da qaddara tana wuyan kowane bawa".
Shuru sukayi dukkansu suna saurareb sautin din…..din,sautin dake gaya musu lallai kiran ya isa ga wayar anni dake tare da documents dinta da kuma sauran kudade masu kauri cikin jakar.
Kamar cikin mafarkinta ta dinga jin wani sauti mara qarfi yana ratsa kunnuwa zuwa kwanyarta.
Shuru tayi ba tare data motsa ba,daddan ring tone din mara hayaniya yana tasowa can qasa qasa,da alama akwai abinda ya sake rage kaifin sautin.
Sai data fahimci ba cikin bacci bane sannan ta qarasa bude fararen idanunta da suka qara girma saboda bacci. A hankali ta yamutsa fuskar tata sannan ta sanya hannunta ta maida lallausar sumarta me tsaho data rufe rabin fuskarta baya,ta juya daga rub da cikin da tayi zuwa rigingine sannan ta miqe ta zauna sosai tana wuwwurga idanunta zuwa kowanne sashe na dakin don gano ainihin ta inda sautin yake fita.
Ba kowa a dakin,don tuntuni su huda sun gama shiryawa sunyi abincin safe kaman yadda suka saba sun wuce makaranta,don ko idanunta bata iya budewa tace dai kawai su buda jakarta su dauki kudin makaranta su kuma ja mata qofan idan sun fita.
Fes dakin yake kamar kullum kamar kuma ko yaushe,sai ta saka hannunta ta tattare gashinta ta qulleshi tsakiyar kanta idanunta ta tsaiwa kan medium luggage din dake cike da tsarabar da aka kawo mata,wadda ko samun damar budeta batayi ba.
Tayi matuqar gajiya a jiyan,tana fita kusan kowacce rana.....amma bata yin awanni masu yawa kaman haka a wajen. Komai nata yana da lokaci tsari da kuma iyaka. Ta zube fararen qafafunta saman qaramin carfet data sanya musu daga gaban gadajen nasu saboda sanyin tile,ta jawo dankwali me santsi ta daura sannan ta miqe tana isa gaban luggage din.
Sai a sannan ta kuma gasgatawa daga cikin qaramar handbag dinta sautin ke fita,jakar ma da gaba daya ta mance da ita tun ranar data je musu siyayya ta dawo,ko tarkacen ciki bata kwashe ba. Hannu ta zura tana laluben meye yaketa qara din haka cikin jakar,sai kawai ta wuce gaban gadon ta zazzage jakar gaba daya saman gadon.
Kyakkyawar purse baquwa ta gani cikin jerin tarkacen dake cikin jakar wanda ta tabbatar duka nata ne. Onion color me ratsin maroon a jiki. Hannu ta miqa ta jawota,ta dagata a hannunta tana jujjuyata cikin mamakin a ina ta samo ta?,kuma ta waye?,tun yaushe take cikin kayan nata?. Kamar anason sanar mata da amsar duka tambayoyinta ne sai wannan siririn sautin da ya tasheta a bacci ya sake kadawa daga cikin jakar.
Kai tsaye ta zuge jakar,ba wani ba wata ta sani waya ce. Wayace qila da take da alaqa da mamallaki ko mamallakiyar jakar.
Wata siririyar Samsung ta gani,ta sanya hannu don cirota da gaggawa gudun kada kiran yanke,take sabbin dollar din dake maqale a zip na daban na jakar suka biyota suka fada saman cinyarta hade da qananun hotunan passport. Ba wannan bane a gabanta,don haka batabi ta kai ba ta fara duba sunan dake yawo saman screen din wayar
MUSADDIQU NA....shine full name din dake jikin number. Tadan tsaya tana sake duba sunan da kyau tare da bitar karantashi,sai kuma tadan tabe baki kadan sannan ta daga kiran ta Kara wayar a kunnenta
"Alhamdulillah.....an daga anni" Musaddiq ya fada yana sanya wayar a kunnensa.
Shuru tayi tana sauraren motsin dake fita daga daya bangaren,kafin daga bisani sallamarsa ta maye gurbin shurun. Muryarsa a nutse dake dauke da kamala yayi cikakkiyar sallama data sanyata motsa bakinta da tata siriryar muryar tana amsa sallamar.
"Barka da warhaka" Ya fada a nutse.
"Yauwa.....barka" Itama ta amsa masa a taqaice
"Don Allah idan ba zaki damu ba zan iya tambayarki wayar nan ta waye?" Banbarakwai taji tambayar tazo mata,har sai data sake duba sunan dake jikin wayar,amma yanayin yadda muryarsa ke nuna kamalarsa da nutsuwarsa ya sanya tayi gyaran murya daban
"Kaman sunan me kiran dana gani akan wayar yana da alaqa me qarfi ko kuma mafi kusanci dame wayar ko?". Murmushi ya saki,yadda tayi maganar cikin fasahar harshe da tsari sai yaji ya burgeshi,hakanan kuma a karon farko ya gano muryar,yakuma dago ko wacece
"Hakane ranki ya dade.....idan na canka dai dai.....kamar mutuniyar kirkin nan kuma baiwar Allahn nan data ceci rayuwar mahaifiyarmu ko?" Dan jim tayi tana son gano ma'anar zancansa,don tuni rayuwarta taci gaba daga inda ta tsaya,tuni ta shiga wani babin kuma na daban,ta manta abinda ya faru dazu jiya bare shekaran jiya.
Haka policy na rayuwarta yake. Ba kasafai take bawa komai gurbi cikin rayuwarta ba bare ta hadu da traffic akan dukka plans nata da kuma tunaninta ba.
"Dattijuwa me asthma a masallacin HGMS store?"
"Oops....." Ta furta a hankali,yanayin daya sanya musaddiq sakin murmushi don ya fahimci abun ya kwanta mata
"Kayi haquri don Allah,ka kuma nawa mama haquri,na hada da purse dinta ne a cikin kayana bisa rashin sani,bansan ma da ita din ba sai yau da aka kira"
"No....karki damu......mune ma muke fata Allah yasa bamu takuraki ba....."
"Zaku iya karbanta a jambulo third gate.....link 5" Abinda ta furta kenan ta yanke wayar,daidai sanda anni ta miqa hannu da zummar karbar wayar su gaisa.
"Ya ka katse wayarwayar inaso mu gaisa nayi mata godiya da ban gajiya"
"Daga canne anni ta yanke......" Ya bawa anni amsa yana duban wayar tare da mamakin yadda take magana da bada amsa haka cikin taqaice komai
"Babu matsala.....amma zanso sake ganinta ko magana da ita......zanso nayi mata godiya sosai,dukan wanda yayi saving rayuwarka ai baka da sama dashi.....mutum ne me matuqar kima da martaba cikin rayuwarka.....har yanzu ina iya jin sanda ta rungumeni sosai a jikinta kamar ta sanni......sai na dinga jin kamar amna ke riqr dani......ta damu sosai kamar mahaifiyarta ce a cikin halin" Ta qarasa maganar tana duban fuskar musaddiq,fuskarta kuma na nuna abubuwa da dama da zuciyartata taji. Zamanshi sosai ya gyara yana murmushi.
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*Arewabooks:@Huguma*
PAGE 33
"Ni kaina anni ina iya hango sanda taketa masifa da fada da gaske wai mun banzatar da rayuwarki,bamusan illa da kaifin ciwon ba......amma fa anni kaman ina zaton.....anya bata da ciwon itama ko wani nata?" Yayi tambayar yana duban anni kamar annin tasan zahirin maganar.
Cikin isa izza da jin cewa takai kowanne qololuwar mataki na rayuwa ta ratsa babban falo kuma na farko na gidan,ta ratse dukkan wasu hadimai da kuma masu aiki na farkon gidan,falon farko har ta dangane da falo na biyu.
Kowanne taku idan tayi idanunta suna sauke zazzafan kallo ne akan kowanne alatu da kuma jayan jin dadi na rayuwa dake kowanne muhalli na falon. Kowanne abu da idanunta zaya sauka akai tana debe kallonta ne daga kanshi cikin jin wani irin zafi da quna gami da radadi idan ta tuna cewa MUHAMMAD FU'AD ne ya yishi tare da gumin dan uwansa MUSADDIQ.
Da wannan tunanin ta tsaya tsakiyar falo na biyu hannayenta riqe da qugunta tamkar qaramar yarinyar da take ganiyar fitsara da kuma jin cewa tana daidai da kowa.
Ko ita dinma a yanzun kusan hakan take. Tsaiwarta a falon qiris ya rage dukkan wani ganuwar haquri nata kawaici da yakana da takeyi su qare,haquri da kawaicin da take ganin tunda tazo duniya bata taba yiwa wata halitta irinta ba
"Amina nakeson nayi magana da ita" Ta fadi kanta tsaye sanda daya daga cikin hadiman dake da alhakin kula da wannan sashen ta qaraso.
"Eyeee?" Me aikin ta tambaya cike da mamakin yadda ta kirayi sunan dattijuwar data zame musu baya goya marayi haka gatsal,babu sayawa ko qanqani,duk kuwa da cewa zasuyi sa'annin juna,amma a garesu kiran ainihin sunanta wani baqon abune da yake jimawa bai faru ba
"Nace AMINA nake buqatar gani.....uwar farouqu da saddiqu" Ta maimaita a wannan karon da madaukakiyar muryar data sanya hadimar maida hankalinta ta hanyar dubanta da kyau,sai kuma taja baya kadan tana cewa
"Inji wa zaa ce mata?" Ta tambayeta tana sake kallonta sosai
"Kice mata uwar Muhammadu da musaddiqu" Sunayen data furta din ya saka hadimar sake dubanta da kyau,saidai bata ce komai ba don bata da hurumin cewa komai din,ta taka a hankali ta kama stairs tana hawa a hankali don isar da saqonta ga anni.
Kafin anni ta furta nata hasashen knocking dinta ya dakatar da firar tasu. Firace da yawancin lokuta musaddiq din yakan qaraso har quryar bedroom din anni ya tayata don debe mata kewa lokaci lokaci da hanata zaman kadaici. Duk da cewa gidan cike yake da hadimai wadanda suka aiki qarqashinta ta kowanne fanni da take da buqata na rayuwa. Hatta hirar akwai masu tayata cikin masu aikin,wadanda aikinsu kenan,gwanaye ne wajen iya hira da mutum,debe masa kewa da sanyashi nishadi......musamman FU'AD ya daukesu aiki saboda haka kawai,amma ko kusa ko alama hira dasu bai kama qafan hira da yaranta ababen soyuwarta ba.
"Waye?" Musaddiq ya riga anni tambaya
"Badawiyya ce"
"Bismillah qaraso" Anni ta bata umarni tana gyara zamanta saman lallausan abun sallarta.
A nutse kuma cikin girmamawa ta qaraso cikin dakin. Ta tako a hankali zuwa gaban annin ta tsugunna
"Baquwa kikayi anni" Ta fadi kanta a qasa
"Baquwa kuma?,daga ina?" Tayi tambayar cikin dan mamaki,saboda yau din ba ranar ganin baqi bane,tana cikin ranakun hutunta,sannan tun bayan dawowarta ma daga asibiti fu'ad ya hana kowa ganinta,yace saita murmure ta huta tukunna.
"Ban dai kai ga gane fuskarta ba.....tadai ambaci asalin sunanki,tace kuma a gaya miki babar fu'ad da musaddiq.......kuma...." Tadan fadi tana daga kai kadan ta dubi fuskar musaddiq da ya tattara dukka hankalinsa akan waya,har sai da yaji sunansa ya fito cikin zancan
".....suna dan yanayi da yallabai musaddiq kadan". Dukkaninsu daga ita har musaddiq din kowannensu ya fahimci wace......kowannensu ya gane wace take nemanta.
Fuska annin tadan saka kadan tana murmushi
" Banda abun badawiyya,ai ba baquwa bace 'yar gida ce itama.....ki gaya mata ta hauro.....ta qaraso zuwa falon sama".
"To anni" Ta amsawa anni din a ladabce tana miqewa don isar da umarninta,saidai kuma a can qasan tata zuciyar mamaki ne kwance. Mamakin yadda annin ta bada umarnin qarasowar matar zuwa falonta na qarshe wanda daga shi sai dakunan baccinta.....matar da sam bataga ruwa ko alamun kirki a tattare da ita ba,tun daga yanayin kallonta har zuwa lafuzzan bakinta,to amma menene ALAQARSU DA YALLABAI FU'AD DA KUMA MUSADDIQU?,tambayar da bata da amsarta kenan daidai sanda ra qaraso falon.
Tana nan a tsaye inda ta barta,kamar dazun ba abinda ya sauya daga yanayin tsaiwarta a cikin falon,zuwaira na daga gefanta bayan tayi amfani da sakannin hawan badawiyya sama da saukowarta ta sake yiwa zuciya da ruhinta wani karatu da sake dorata akan wani bigiren.
"Tace ki qaraso saman" Badawiyya ta furta a ladabce kaman yadda tsarin aikinsu yake cikin gidan girmamawa ga duk wani baqo da zai sanya qafafunsa cikin gidan alhaji hamza kibiya,walau me dogon zangon zama,ko kuma me gajeriyar baquntar da bata wuce awanni zuwa mintuna
Kai ta jinjina,eh yana da kyau hakan,ko ba komai a karon farko idanunta zasu ganeta komai da kyau......idanunta zasu gane mata yadda akayi amfani da kudi da jini da kuma quruciyar d'iyanta don shimfida kyakkyawan rayuwa ga wasu.
Cikin jin isa taqama gami da izza take taka kowanne step na stairs din,idanunta na sake qididdige mata adadin dukiyar da aka narkar wajen ginin gidan tare da qawatashi da kayan alatu dana alfarma na kecewa sa'a. Irin alatun da ita shine nata mafarkin,irin qawar da shine burinta DUNIYARTA. Yau ga komai a kusa......komai a dab da ita da sunan mallakinta.....amma wani taqi da kuma taku kadan sun hanata isa ga wannan bigiren. Iya lallausan carpet din da aka mamaye ilahirin stairs din dashi aka lullube tsadajje marbles din dake shimfide don kada anni taji sanyi cikin jiki da qashinta......duba daya zakayi masa kasan asalin tsadar da yake dashi. Wani abu ya dinga taruwar mata yana tsaya mata a wuya,wutar bacin rai taba taso mata kamar ta hallakata.