A d u n i y a ta complt by huguma - Chapter 15
A d u n i y a ta complt by huguma Chapter 15: A d u n i y a ta complt by huguma Chapter 15. "Wayata bata da guarantee adress kuma bani da" Ta bashi amsa ta…
4,459 words
"Wayata bata da guarantee adress kuma bani da" Ta bashi amsa ta kai tsaye daidai sanda yake tsaida motor din a inda ta nuna masa.
"Waya ba guarantee adress aishi zai zama babban guarantee ko?....me yasa kikace baki da adress?"
"Saboda bamu da gida" Ta sake bashi amsa kai tsaye sanda take dubansa da fararen idanunta masu sheqi da hasken rana ya qara musu qyalli,abinda ya sake daukan hankalinsa kenan. Murmushi ya saki yana jin tana sake burgeshi
"Alright.....nasan dai ba dan adam din dake rayuwa a titi.....amma bazan takurawa zabinki ba......zaki iya bani dama ta uku?,damar yin magana dake a nan?" Numfashi ta sauke a hankali tana jin ya takurata da yawa,ta daga hannunta dake daure da agogo ta kalla sannan ta sauke tana juya idonta daya sashen alamun qosawa
"Mintuna biyar kawai"
"Na gode" Ya fada yana gyara zamansa sosai.
"Bari na tafi kai tsaye kada na cinye mintunana ko?" Ya furta yana sake sakin murmushi. Batace masa komai ba still,saidai ta kafe idanunta ne saman qofar gidan dake gabansu kadan. Tunaninta yafi karkata akan gidan,tana tunanin me zataje ta taras?,wanne abu zata samu cikin gidan.
"Tunda na ganki sawwama naji zuciyata ta kwanta dake.....ta kuma kamu da sonki......naji kuma a raina na samu matar aure.....ina fatan zaki bani dama....." Statement dinsa na qarshe data samu fahimta kenan.
Waiwayawa tayi ta dubeshi,shima idanunsa yana kanta,da alama ya gama dukkanin bayanansa ita yake da buqatar jin ta bakinta. Dauke duban nata tayi,sannan ta saka hannu ta bude murfin motar ta zura qafafunta ta fito. Da mamaki yake binta da kallo har zuwa sanda ta maida masa murfin motar ta rufe,tadan rage tsaho kadan tana dubansa da shiny eyes dinta
"Na gode da karamcinka......amma kayi haquri.....babu aure a rubuce cikin rayuwata.....na barka lafiya" Ta motsa labbanta a hankali sannan ta janye jikinta daga motar.
Soma takawa tayi a hankali tana barin wajen,AURE na daya daga cikin abinda take mantawa dashi a rayuwarta. Aure yana cikin abinda yake a lissafin qarshe cikin abubuwan da suke ba dole ba a rayuwarta. Aure yana daya daga cikin abinda take masa wani irin kallon da batasan ajin data zubashi ba.....babu shi ko kadan a dictionary dinta,idanma anyi zancensa,tana masa kallon wani baqon abu wanda batasan ranar da zata saba da ji ko ganinsa ba,bare azo da batun wanzuwarsa akan kanta.
Ko kadan bata damu da tsaiwarsa a wajen ba,abu daya ta sani.....kaman sauran mazan,yadda basu da masaniyar daga inda ta fito......hakanan bata basu qofa ko qanqani game da sanin inda zata ko inda zata shiga. Don haka bata kutsa kanta cikin gidan ba sai data kadar masa da hankali,ta kuma tabbatar ya bar layin.
Da sallama a bakinta ta shiga madaidaicin tsakar gidan dake shimfide da sabon simintin da bata jima da sanyawa ayi musi shi ba saboda jin dadinsu.
Yara ne aqalla kusan guda biyar wadanda shekarunsu bazai haura goma zuwa sha uku ba. Biyu daga cikinsu wanki sukeyi,daya kuma tana wanke wanke,yayin da guda dayar take jawo ruwa a rijiya tana zubawa a babban mazubin ruwan da suke amfani dashi a gidan.
Sallamarta ya sanya kowacce ta watsar da abinda takeyi,suka kuma rugo da gudu suna rige rigen isa inda take. Kyakkyawar fuskarta ta fadada da fara'a itama ta buda hannunta tana tarbarsu,daidai sanda muryar matar ta iskesu
"Ku da waye haka?" Ta bayyana tare da qarashen tambayarta tana qoqarin daura dankwali saman kanta.
Murmushi ne ya wadaci fuskarta itama,kakkaurar matar ma'abociyar tsaho da qiba,saidai alamu sun nuna yanayi na rayuwa ya sanya qibar zubewa sai saura data zama halittarta ce ba zata iya rabuwa da ita ba. Baqace wannan ya sanya dukka kamanninta sukafi karkata ga kamannin babarbariya.
"To ku barta ta qaraso mana" Ta fadi tana juyawa cikin dakin da ta fito,dukansu sai suka bi bayanta harda sabreen daketa jefawa yaran tambayoyi.
Tare suka zauna da yaran saman shimfidaddiyar dardumar da matar ta shimfida saboda sabreen din,daya daga cikin yaran ta miqe ta fice sai gata da ruwa adan qaramin jug da cup,yayin da sauran sukaci gaba da zama a kewayenta.
"Ina Ayshatu?" Tambayar farko da sabreen tayi mata bayan sun gama gaisawa,tambayar data sanya yaran suka miqe daya bayan daya suna fita a dakin.
Bata ce komai ba matar saita miqe tana dosar wata qofa dake maqale a falon,itama batace komai din ba ta miqe ta biyo bayanta.
Yalwataccen daki ne dake wadace da tsafts,ba komai a qasan sai wata lamusashiyar katifa guda daya yashe a qasa. Daga samanta idan ka duba da kyau mutum ce a kwance data lulluba duka jikinta. A sanyaye sabreen ta qarasa gaban katifar,ta saka hannu ta yaye rufar bakinta yana rawa ta kira sunanta
"Aishatu?" A hankali ta ware idanunta akan sabreen din,sai kuma wani busashen murmushi ya subucewa kyakkyawar fuskar yarinyar
"Aunty....kece kika zo?" Ta tambayeta da siririyar muryarta. Kasa riqe kanta tayi,sai kawai tayi qasa da kanta hawaye yana diga daga idanunta. Tana jin tausayin yarinyar kamar zai fasa zuciyarta,tana jin kamar zata narke a wajen,tana jin inama ace tana da ikon fidda ciwo ta farat daya daga jikin mutum a yanzu yanzu basai anjima ta cisgeshi daga jikin ayshatu
"Ko baki da ikon cire mata shi yanzu yanzu.....kina iya sama muku dama ke da ita na samo mata lafiya a duk inda lafiyar take a fadin duniya" Wani sashe na zuciyarta ya bata amsar data motsa mata wani qwarin gwiwa daga can qasan zuciyarta. Wannan ya sanya ta sake daga idanunta tana kallon aysha. Allah ne kadai yasan bila'adadin mata da yaran da suka shiga irin yanayin da ayshatu ke ciki duka sanadin TAIMAKO. Lalacewar al'ummarmu abune me matuqar ban mamaki da daure kai. FYADE ba'a daukeshi da wani muhimmancin da me aikatashi zai fuskanci hukunci mafi tsananu ba a tsarin doka. Tana iya tuna yawan kudaden data kashe,shige da ficenta da kai kawo data dinga yi kafin ta samu ayiwa azzalumin hukuncin da doka ta tanada. A abinda ya yiwa aisha,ba hukuncin daurin shekaru take da buqata ba......lahira yafi kamata ya baqunta yaje ya hadu da hukuncin mafi iya hukuncin masu hukunci.
Sosai ta bawa zuciya da gangar jikinta qwarin gwiwa,ta zauna sosai ta yiwa yarinyar komai. Ta bata abinci ta kuma dinga hilatarta,har suka dinga hira tana saurarensu murmushi yana subuce mata. Hakan ya sanyaya ranta kafin su kebe da ummaa ta sake mata bayanin data yi mata a waya.
"Waje nakeson a fita da ayshatu,inason ta warke sumul taci gaba da rayuwarta,duka duka shekarunta sha uku,ya kamata ta rayu kamar kowa" Ta fada zuciyarta tana mata zafi. Allah ya dora mata tausayin yaran da matar kanta da batasan asalinsu ba,amma dukka dawainiyarsu kusan kaso tamanin cikin dari tana a wuyanta,hatta da hayar gidan da suke zaune a ciki kuwa,banda abinci da ma karantarsu rayuka shida.
Da idanu ummaa take bin sabreen. Tasan cewa dukkaninsu babu wanda suka hada dangantaka a tsakaninsu,amma suna jin juna kamar 'yan uwa,suna kuma ci gaba da tsananin shaquwa da juna.....kuma a yanzun sune 'yan uwan kawunansu.
"Sabreen......kiyi iya abinda zaki iya mu barwa Allah sauran.....samun maganin ayshatu a gida Nigeria ma miliyan nawa ya kama bare ayi batun fita da ita waje?,kinsan miliyoyin kudin da za'a cajemu?,daga visa passport masauki abinci da zaman asibiti zuwa kudin magani?" Shuru sabreen tayi tana saurarenta,tana jin zuciyarta na wani irin ciwo,irin ciwon da mutum kanji a duk sanda yake tsananin son abu amma babu ikon samuwar wannan abun gareshi. Numfashi taja sosai ta aje tana duban maama
"Allah zaiyi cikin iko da isarsa......na tabbatar Allah bazai taba wofantar da bayin da aka zalunta ba" Kai ummaa ke jinjinawa tare da yaba tauhidi da yaqinin sabreen.
Ta jima dasu saidai hankalinta yana kan asibiti,don haka lokaci kadan ta qara akai tayi musu sallama bayan ta aje musu kudi kaman yadda ta saba da basa wuce cefane da zirga zirgar makarantar yaran.
Tana hanya zuciyarta kamar ta fashe,hakanan ta sake jinta a rikice bayan fitowarta daga asibitin bayan taji bayani daki daki na yadda zata fita da ayshatu waje ayi mata aiki.
Kudade ne masu kaurin da a yanzun bata dasu bata kuma bawa wani ajiya ba. Batasan tayi farautar kudi don ta ajiye ta tara abun duniya ba......tana farautarta ne don ta raba a tsakanin mabuqata marasa galihu irinta,yanzun ka buqata ta taso mata wadda take da girma da muhimmanci a rayuwarta. Sai taja numfashi mai nauyi,tabbas a yanzun zatayi FARAUTA ta ainihi,tsakanin MIKA'IL YA'AQOUB da kuma MASHKUR waye zaiyi aman wadannan maqudan?.
_tofa zamuji waye,komarta zatayi kamu ko kuma wannan karon ita zata shiga komar?_
*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*_Arewabooks:@Huguma_* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 __________________________
PAGE 41
Kusan a tare wayoyi uku suka dauki ruri dake nuna alamun ana kiranta.
Mashkur mikail da ya'aqoub,abubuwan farautarta da batasan waye a ciki zai fada komarta ba. Ta dinga bin sunayen da wayoyin da kallo cikin canki cankin wanda zata fara daga wayarsa a ciki har sai da suka katse,sai ta barwa ranta wanda ya soma sake kira. Saidai kuma cikin rashin sa'a sai ga mashkur da mikail suna kiranta lokaci guda. Plate din hannunta ta ajiye,ta sanya hannu tana daukan kiran mikail. A lissafinta shine mutum na farko da takeson saukewa daga layinta. Dukka wani binciken halayya nasa suna gwada mata tsantsar dacewar ya karbi sakamako da horo yadda ya dace. Ita kanta batasan adadin abinda zata diba daga gareshi ba,saidai ko banza ta sanya zata sanyasu a muhalli da guraben da suka dace.
A jirkice yayi mata sallama da muryar data sanya ta saka masa ayar tambaya. Ta daga wayar daga kunnuwanta ta duba fuskar wayar tana mamaki
"Bayan neman mata harda caca da harqallolinsa harda shaye shaye?" Ta tambayi kanta cikin mamaki,sai ta maida wayar kunnenta kawai tana saurarensa.
"Sai yaushe zaki bani dama ne?......ina tsananin kewarki......ina son kasancewa dake" Abinda ya fada kenan yana jin kamar ana fusgarshi zuwa gareta. Katse wayar tayi tana jan dogon tsaki. Baci kawai takeji ranta yana yi kota ina tare da azalzala mata akan mikail. Sai ta jawo wata qaramar waya daga gefanta wadda bata hasken komai ba ta turawa JIB qaramin saqo. Tana jin ya kamata aikinta ya fara ta kansa.
Yadda mashkur yaketa kiranta ba daga qafa ya sanya ta share kiran ya'aqoub ta daga nashi. Kiran ya'aqoub din ma bata mata rai yakeyi,ta tabbatar dukkan wani magidanci me mata irinsa a yanzun yana cikin gidansa ne koda a dakinsa ko a sassan yake. Taga maza da yawa da halayensu,daya daga cikin halayyar tasu kuma da tafi baqanta mata rai take tunzurata shine wannan. Wai ta yaya ma zatayi Aure?,bayan bataga komai ba a tattare da mazan sai munanan dabi'u dake girgiza zukatan matan su haifar musu da muguwar illar hawan jini ko ciwon zuciya?,ko mummunan zawarcin da har ki mutu bazai fita a tarihinki ba?. Har abada tana kallon zaman 'ya mace me cikakken 'yanci a yayin da ya kasance babu igiyar wani a kanta.
"Saura kadan ki kashemin raina muhseena......hala bakisan girman soyayyar da nake miki ba har yanzu?......kinsan Allah?,banqi a daren nan ace an daura aurena dake ba?"
"Aure?" Ta furta a hankali tana jin kalmar tayi mata girma da yawa.
"Yes aure muhseena....." Ya maimaita fada yana gyara zamansa cikin tattausar sofa din da yake kai. Yana fatan samun gamsashen amsa tare da mamakin kansa yadda yarinyar ta sauya masa tsari gaba daya.
"Gaskiya ne" Ta amsa masa a taqaice tana aje numfashi.
Hira ya dinga qoqarin janta dashi,duk da ita din bame doguwar hira bace amma ta dan sake masa,don itace hanya guda daya da take dashi da zata haska mata hanyar gano gurbin da zata dasa bomb dinta.
"Kiyimin alfarma daya mana......ki gaya min credit dinki na yimin rakiya dubai for just one week......ni kuma nayi alqawari zan biya ko nawa ne" Ya fada yana sake jin kowacce gaba tasa tana narkewa da sha'awarta da sonta. Yanajin koda bata shirya aurensa ba......zai kashe mata ko nawa ne suyi irin rayuwar da yake muradi......idan da yiwuwar ta zama tashin a gaba sai ta zama.....idan ma hakan bata samu ba yana ganin duk inda ta kwana sha ne muddin ya tsira da abinda yake qulafucin samu.
"Zan baki dama kiyi tunani......sannan ki yanke ko nawa kikeso muhseena.....ko nawa ne muddin raina zaikai ga muradinsa".
Maganarsa t qarshe kenan data sake sanyawa sabreen mummunan zato ga maza......maganarsa ta qarshe data sanyata ta kusa raba dare tana kuka......ta kuma dinga godewa Allah ta wasu fannin.
Mashkur din data tura masa mabanbantan mabuqata da buqatar neman tallafin da duka duka baikai ko digo cikin abinda ya mallaka ba yasa aka koresu?......yace bashi dashi?.....yace bazaya bada ba?......wannan mashkur din yau shike bada damar a nemi ko nawa ne zai iya mallaka mata bisa rashin sanin WACECE ITA?.
Hakan tamkar wata dama ce a gareta kenan da zata samu dukka kudaden da takeso......amma bisa sharadin sadaukar da abinda yafi komai mutunci a tare da ita?.
Koda ta saba ko tana da damar accepting masa abinda yazo dashi.......tabbas ba zata lamunce ba......tanaso ta debi kudadensa ta hanyar data saba azabtar da sauran.......tanaso ta debesu ta hanyar da zaiji ciwon da bazai kankaru ba a zuciyarsa.......tanaso ta debi kudin da zai tsaye masa a rai......yayi masa ciwo fiye da yadda rayuwa da zukatan matan da ya fadawa mutuncinsu sukayi musu ciwo......tanason bashi darasi me girma a rayuwa.......tanason shima ya girgiza girgizar da zata tsaida masa komai na rayuwarsa cakkkkk koda ba tsaiwa bace ta har abada......to amma kuma ta sani.......babban plan da yake buqatar nutsuwa da tsare tsare masu yawa. Don haka da safiyar washegari ta tura JIB wani saqon da sunan mutum biyu.
Tana tsaye tana shan ruwan dumin da takesha duk safiya kafin shigarta wanka saqo ya shigo wayarta. Sanda ta duba sai ta samu alert na kudi daga wajen ya'aqoub. Five hundred thousand ce,sai ta gyada kai a hankali tana sakin murmushin takaici. Don kyauta yana da kyauta ya'aqoub ba daga baya ba......abinda bata da yaqini shine haka yake a cikin gidansa?,ko shima fankan fayau ne?.
Saqon godiya ta tura masa a gajarce,ta aje wayar tana shirin wucewa wanka wani saqon ya sake shigowa
"Patiently waiting for you" Share saqon tayi hade da sauran. Tasan me saqonsa ke nufi a gajarce. Kowacce safiya izina ce a gareta,kowacce rana kowanne sati da kuma kowanne wata cikin rayuwarta yana bude mata babi na abubuwa da yawa cikin rayuwarta. Waishin akwai ragowar NAGARTATTUN MAZA kuwa?,tambayar da kullum idan ta yiwa kanta ita take bawa kanta da kanta amsa da BABU.
Kanta tsaye take takawa cikin tsakar gidan nasu ba tare data daga kai ba bare ta lura da waye a hagunta ko damanta?. Ba tare data damu da kallon nan nasu data tabbatar a safiyar yau zai ninka ko ma ya canza salo saboda abinda ya faru a jiya.
Dab da zata sanya qafarta a qofar toilet din nasu dake da sassa biyu bathroom da toilet ta jiyo muryarsa yana koda sallama. Sallamar da muddin ya yita duk wani dake da hadin kai dashi take masa dadi......duk wani wanda yake da qulli dashi Kuma yake neman yin ta kansa,mutane kuma kamar ita sukejin kamar su turashi ya koma muhallin da ya fito.
Koda taso tayi shigewarta toilet din ta tabbatar sai ya ganta don ya iso dab da wajen. Don haka ta tsaya a nutse tana bude toilet din ta hanyar murza handle,abinda ya bashi damar qarasa shigowa farfajiyar tsakar gidan.
Da ita ya fara hada idanu kamar yadda nata idanun suka zube a fuskarsa. Kamanni dai da mahaifinta har kullum sune,bata kuma fasa ganinsu shimfide a fuskarsa,saidai nisan tazarar halayya da dabi'un sun kai girman tazarar dake tsakanin sama da qasa.
"Yauwa alhamdulillah......ai gwara dana sameki cikin gidan.....zuwan dama naki ne" Kallonsa kawai tayi ba tare da wani mamaki ba,dama wanne zuwa ne zaiyi gidan ba nata ba?,koda yayi zuwan daba nata ba to lallai daga qarshe sai ya zama nata ko kuma ya hado da ita a abinda bai zama damuwarta bama bare y shafeta. Amma tun a jiya tasan tabbas dama zayazo,shi yasa taso su fice kitso da wuri yazo ya taras da sararinsu kawai.
"Ina kwana kawu?" Ta fada cikin girman nan da bata fasa bashi shi kaman yadda kowa cikin gidan ke bashi duk kuwa da farin sanin da tayi na waye shi?,sanin da kaf gidan tayi yaqinin ba wanda ya masa shi......sanin da a qa'ida ya cancanci ta rainashi......amma sai kuma batayi hakan ba.......sanin da ko yaushe ta tunashi dashi take jin kaico da bacin rai da rashin sanin son ganin gilmawarsa.
"Lafiya qalau......idan kin baro bandakin ki sameni a dakin bibo" Ya fada yana saba babbar rigarsa yana wucewa ciki tare da jaddada sallamarsa.
Da kallon takaici ta bishi,tasan dama zaa rina,ba wani abu da zai fari cikin gidan ya kwana ya hhantse baije kunnuwansa ba.......yana kuma zuwa kunnuwan nasa ne ta hanya guda daya rak wato BIBO. Idanma akwai ta biyunta to bata bayyana ba tukunna. Cikin rashin damuwa da lamuransu gaba dayansu ta kada kanta ta wuce bandakin.
Babu wani abu da zai sanyata gaggawa a zuwa kiran data tabbatar babu alkhairi sam sam a tare dashi. Wannan ya sanya ta kammala wankanta a nutse,takuma tsaya gaban madubi ta shirya tsaf kamar yadda ta saba. Tun bata kammala ba ya aiko kiranta ya kusa sau biyar. Ana shidan ta tsaida nadra da taji tana gaya musu cewan kaya take sanyawa
"Kace gani nan zuwa" Ta fadima usman daya aiko. Rigar lace tayi niyyar sakawa,don haka ta fara sanya 'yar cikin rigar ta yane kanta da mayafi ta zura slippers dinta tana cewa
"Ku kammala shiryawa ina dawowa zamu wuce" Ta qarasa fada tana sanya qafafunta a waje,huda kuma ta bita da kallo. Sam bataso ace sabreen din taje da kanta kamar yadda kawu ya buqata ba,ta tabbatar da cewa ba wai wani abun arziqi zai aiwatar ba face tsantsar son zuciya da son rai kamar yadda suka saba. Ba wani lokaci da abu irin haka zai taso cikin gidan ya zamana anyi hukunci cikin adalci da sanin ya kamata.
Hankali kwance ta daga labulen dakin bibo gami da sallama. Su uku ne cikin falon,kawu bibo sai hadiyya dake zaune saman daya daga cikin kujerun. Qafarta daya saman daya tana kadata a hankali. Tako ina tana jin kishin wanzuwar komai dake tattare da sabreen din. Kowanne abu tana yinsa ne don kawai ta samu daqile sabreen din. Ba haka takeso ta bude idanuwa ta ganta ba. Wani qaqqarfan abu ya dasu a ranta game da sabreen din.
A haka mutane ke raina matakin da take kai.....suke mata kallon wadda ke tafiya bisa baragurbin bigire......amma ita a nata idanun ta sani cewa sabreen din tayi mata wani irin nisan tazara me tarin yawa. Bataso ta ganta a haka.....ba'a haka take da muradin ganinta ba,tana son ta sauya daga matsayin da take kai a yanzun,shine abu daya da zai gamsar da ita.....
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*
*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*
*ZAFAFA BIYAR*
*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*
*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA DA SU*
_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_
_K'ALBIM Mamuhghee_
_AJIYA A DUHU Billynabdul_
_DUNIYATA Huguma_
_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*
*uku 1500*
*Biyu 1k*
*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_
*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA* *09033181070*
*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*
*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪
89825722 Nousaiba lawali maradi 1000cf
*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*
*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰 *D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*
*_Arewabooks:@Huguma_* https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997 ________________________
PAGE 42
Janye dubanta tayi daga kan hadiyya,sai ta nemi hannun kujerar dake daga bakin qofa ta zauna akai,wayarta a hannunta tana qoqarin sakata a silent. Ta manta yaushe ne lokaci na qarshe data shigo wannan dakin,bama shi ba,dukkan wani daki dake cikin gidan ba muhallin shigarta bane.
"To da kika shigo kikayi mana derere saman kujera ai sai ki sauko ko?" Muryar bibo ta rasa kunnenta. Dauke dubanta tayi daga saman wayar ta aza a fuskarta. Abubuwanta sun fara mata nauyi akai,tanason ta fara shige huruminta. Tana ganin kima da martabarta a matsayinta na macen data taba kasancewa mata a wajen mahaifinta,amma ta lura da sam sam bata kula da wannan.
Dauke idanunta tayi daga kan bibo din,tana ji a ranta lokaci ya kusa da zata sassauta wannan girma da martabar da take bata,tunda har ita din ta gaza riqo dasu yadda ya kamata
"Gani" Ta fadi kai tsaye tana duban kawun. Zamansa ya gyara yana wani hakimcewa. Jira yake su kammala da maganar da aka tattagoshi a kanta ya gabatar da nasa batun wanda shine yafi damunsa
"Yanzu ke......wani irin baqin hali gareki ne?.....kin fita ZAKKA ke kadai?,kin addabi kowa kin damu kowa?,a gidan nan kaf babu wanda yake da matsala sai ke?" Duk da tasan qarshen zancan,ta kuma san abinda ya sanyashi debo dogon zance har haka amma sai maganganun nasa suka bata mamaki. Banda tsabar rashin son zaman lafiya na mutanen gidan......a yanayin yadda ta tsara rayuwarta dana 'yan uwanta,ya kamata ace tana cikin sahun jerin mutanen da za'a mance da wanzuwarsu cikin gidan. Zaka jima baka ga gilmawarta ba,zaka jima baka ganta zaune a farfajiya ko filin tsakar gidansu ba.....zaka jima baka ganta a tsaye tana magana da kowa ba,to wai shin me ta tsarewa bibo da ire irenta cikin gidan?.
"Wani abu akace maka ya faru?" Tayi tambayar tana tsareshi da idanu. Fada yakeso rufeta dashi kamar yadda bibo ke buqata.....amma kuma yana duba da tunanin kada hakan ya sarayar da samuwar tashi buqatar.
"Yo har sai ance miki ma wani abu ya faru cikin gidan nan banda raini?.....me ya kaiku shiga hurumin yarinyar nan banda neman tada zaune tsaye?,yarinyar da babu abinda ta sanya a gaba banda karatunta?,inajin kaf cikin yaran marigayi babu kamarta ko akwai?" Ya qarashe tambayar yana maida dubansa kan bibo da taketa cika tana batsewa. Dukka salon fadan daya dauko babu wanda yayi mata
"Ina fa?.....mu irin karatu ne,kuma karatu shine a gabanmu" Ta fada tana gyara daurin dankwalinta.
Da idanu kawai take binsu tamkar bata fahimtar koda kalma daya daga cikin maganganunsa,har zuwa sanda yakai qarshe ya kuma jona da tambayar bayyana fifiko me yawa tsakaninsu da hadiyya.
Tsam ta miqe tana duban kawun
"An gama?,inaso na fita ne" Ta fadi kai tsaye ba tare da tayi duba ga sashen da bibo ke zaune ba. Dukkaninsu idanu suka zuba mata su ukun,yayin data juya a hankali tana nufar qofa ganin kawun bai iya cewa komai da ita ba.
Cikin tsananin jin zafi gami da yunqurowar wani boyayyen zazzafan kishinta a kanta ta sauke qafafunta tana aje wayar hannunta gefe
"Kin gani ko bibo?,ai dama na gaya miki......wallahi bata kunya ko shakkar kowa......ni nasan kawu ba matakin da zai iya dauka a kai....."
"Ke!.....yimin shuru,rashin kunya zakiyimin?" Ya fada cikin fadan nan nasa yana rarraba idanu. A duniya idan akwai abinda ya tsana itace kalmar YA KASA KO YA GAZA
"Aah dakata sule......" Bibo ta fada tana daga masa hannunta daidai sanda kunnuwan sabreen sukayi nisa daga jin cecekucensu.
"rashin kunya har takai wadda waccen figaggiyar gantalalliyar yarinyar tayi maka.....tambadaddiya da ka kasa saitota cikin yaran dan uwanka......kaf dinsu yara mata goma sha tara amma ita daya ta fita ZAKKA?,to kada kazo kace zaka zaqemin akan yarinya......me laifi daban wanda za'a huce a kansa daban?". Ransa ya baci sosai,don shi din irin mutanen nan ne da basa son raini ko wargi ko qanqani. Banda ma bibo din da taga wallensa......kaf yaran gidan tsoro da shakkarsa suke idan ka cire SABREEN din
"Ke hajara......dakata,hawainiyarki ta kiyayi ramata......kibar ganin ina daka ta taki.....wallahi ina nan yadda kika sanni......kawai ina duba wasu abubuwa ne nake rama miki halacci da halacci......amma tunda iskancin naki a kaina zai sauka a gaban qaramar yarinya irin wannan......to shikenan......ni na zare hannuna daga sha'aninki cikin gidan nan......" Ya fada yana miqewa cikin hargagi gami da kakkabe babbar rigarsa.
"Haba sule.....zauna mana kaji......ba haka nake nufi ba.....ni dadina dakai wannan masifar taka da jarabar". Tsaiwa yayi yana hade rai gami da dubanta
"Ba haka kike nufi ba hajara gayamin abinda kike nufi". Sai kuma ya waiwaya sashen da hadiyya ke zaune
"Tashi ki bawa mutane guri kin zauna kina raba idanu a gabansu" Ya fadi mata cikin tsawa kamar zaibi ta kanta. Wayarta ta dauka sumi sumi tana yin hanyar shigewa bedroom din bibo din,qasan ranta cunkushe fal da baqinciki. Baiyi mata yadda takeso ba,ba kuma haka takeso ya yiwa SABREEN ba. Batasan dame sabreen din ta fisu ba da har tauraruwarta tafi tasu haske cikin gidan,duk da tayi yaqinin ko meye sabreen din zata juya ta kuma nunawa duniya shi to ba shakka ya samu ne daga dattin ZINA da kuma dattin BARIKI. Ba abu mafi daure kai irin mazan dake karakaina a kanta tamkar su sadaukar mata da rayukansu......amma ta gaza cafke koda guda daya ta maisheshi mijin aure?.
"Mazan bariki dama suna auren macen da suka hadu da ita a bariki?,ai saidai su tsotseta tas.....su musaya wannan zaqin da gardin da suka samu daga gareta da 'yan kudaden da zasuyita mata barinsa......daga sanda buqata kuma ta biya su tattarata su watsar su qara gaba zu zabi wata". Sai ta tuna maganar da sukayi taba yi da bibo wadda ke kamaceceniya da kalmomin maleeka roommate dinta. Juyi tayi kadan saman gadon,tana da burika masu tarin yawa akan karatunta,wannan ya sanya ta sadaukar da rayuwarka akanshi. Tana so ta ganta tana fantamawa,tanason ta ganta tana haskawa tamkar sabreen da dukkan wani alatu da jin dadi......tanaso taga maza suna mutuwa a kanta sama da sabreen......amma dukka ta hanyar karatunta da kyawun sura da Allah ya bata. Tana cikin sahun jerin farko farko da 'ya'ya masu kyau a gidan......ta tabbata ko wannan ya isheta jari wajen zaben kalar mijin da take buri da muradi idan aka qara da karatunta da takesa ran kammalashi ta kuma riqi kyakkyawan certificate mafi girman daraja a idanun mutane.
Ta samesu a zaune sun gama shiryawa sanda ta koma dakin. Kai tsaye ta wuce can ciki ta jawo rigarta ta sama ta zura,ta hada igiyoyin ta daureta ta zauna dai dai jikinta,abinda ya bawa rigar daman fidda kyakkyawan shape din nan nata da ba kasafai ya fiya bayyana ba saboda ita din ba ma'abociyar sanya damammun kaya bace. Sai data sake goge jikinta da sassanyan oil perfume dinta sannan ta fara rolling dan kwalinta saman kanta idanunta akan fuskarta data bayyana tarwai ta cikin madubin.