Kenza eBookz

A gidana complete novel - Chapter 22

A gidana complete novel - Chapter 22

A gidana complete novel Chapter 22: A gidana complete novel Chapter 22. Murmushi Dady yai yace “sannan na fahimceka taya zakai aiki a kasan matarka? Bayan…

846 words

Murmushi Dady yai yace “sannan na fahimceka taya zakai aiki a kasan matarka? Bayan ita tayi zurfi a aikin? Sannan kai ba abinda ka karanta ba kenan, ta fika sanin komai a fanni, duk wanda yazo kallan wanda ke kasan matarsa zai maka.”

Khalid yai murmushi yace “nagode da fahimta.”

Dady ne yace “maganar lefe dan Allah karkayi”

Khalid yace “dady ayi hakuri abarni nayi, ni nake san yi.”

Shiru dady yai yana kara san yaran a ransa, yace “shikenan tunda kai kake san hakan, in yaso in ta tare sai ka bata, angode sosai.”

Khalid yace “nine da godiya nagode sosai.”

“Ka turo min takardun ka ta email zan turo ma yanzu, inkaje gidan mayi waya da mahaifin naka.”

Khalid yace to angode cikin girmamawa.

Dady yace “sai na jika, in ba damuwa ka kirata.”

Nan sukai sallama, kallan wayar yai maimakon ya kirata kawai sai yai text yace “na dade da isowa lafiya.”

Tana zaune tana cin abinci tai karo da sakon, cikin takaici tace “banaji na tambaya.”

“Au tunda baki tambaya ba na goge maganar.”

Takaici ne ya kara makureta ta kira wayarsa, yana kokarin sauka daga mota ya daga.

Yana dagawa tace “na cikin wayata fa?”

“Sai ki danna delete”

“Cikin takaici tace “banda hannu.”

“Wanda kika kira dashi fa?”

Haushi ne ya tiketa ta kashe wayar, cila ta tai kan gado ta cije lebanta cikin takaici.

Zuciyarta ce tace “kinsan halinsa ai meyasa zuciyarki ta zabe shi?”

Shiru tai tana tunani kafin tace “saboda ni dashi akama laifi? Saboda shikadai nasan bazai cuceni ba? Ya akai nasan hakan?”

Ganin ta rasa amsa kawai ta jigina kanta da gado cikin takaici abubuwan da take kunsa na Khalid.

******

Tundaga wannan rana basu sake ko waya ba itakam fa dukufa sosai gun shirya abubuwan aikin da zata fara, shi kuma yana ta famar neman kudi, har Kawo Idris da yan uwan Abba suka zo garin Abuja, Abba kam ba halin zuwa, duk da yaso zuwa sai dai Dady ne ya hanashi saboda kafarsa.

Su Kawo Idris kam an koma da gulma a baki ganin zabgegen gida da irin uban hidimar da aka shirya musu, Matansu kam sunsha xance kai kace mata ne. Wani kanin kawo ma cewa yai auren Jari su Khalid kesan yi.

Ansa rana wata biyu saboda Dady yace jan abin bashi da wani amfani tunda dai sun aminta da juna to ai abinda za’ai.

Khalid kam yai kokari dan Dady har fada sai dayamai na bada kudin gaisuwa dubu dari dayai. Wanda a zahiri yasha wahala matuka kafin ya hada wannan kudi, tun asuba in ya fita aiki sai dare yake dawowa, sannan da weekend ma daina zama yai aiki yake fita, wani sa’in har sai goma yake dawowa gida.

Zainab kam takaici ya gama isarta na ko sako balle waya ba abinda yake shiga tsakaninsu ga gidansu sai wani shirin biki ake tun balle Dady, sai dai in ta tuna aikinta sai taji komai ya mata daidai dan dama saboda shi take san aure, tunda ta samu ba abinda take nema.

Dady ya sanarwa Abokinsa anyi dace dan takardunsa ya birge Mutumin, cikin jin dadi ya kira abokinsa a Zenith bank ya sanar mai, sannan ya fadawa Dady sai dai ya faro daga kasa dan baisan harkar zallunci.

Dady ya nuna shima hakan yake so.

**********

Kayansu yake cillowa waje, Goggo sai hakuri take bashi, Malam Salau kam ya rufe ido yace “wlh yau sai kum bar gidan nan ko za’a mutu ko kanin ubana bazan barshi har yai wata kusa biyu bai bani ficika ba.”

Goggo tace “kayi hakuri munyi magana da wata tace “zata samomai aiki.”

Wannan damuwarku ce ba tawa ba ni tawa daya ce ku hada kwamutsenku ku barmin gida, banda tsiya ma me kuke dashi daga katifa sai tv, na rasa uban me ake da tv gida ba komai, koma tv din yanzu zan tafi da ita ma rage zafin kudina.”

Adam ne yace “Malam ka shiga hankalinka da ci mana zarafi bafa matsiyata ka samu ba.”

“Yo ai ku da matsiyatan fakirai bakuda maraba.”

Yaja kofar dakin ya garkame da kwado ya fida daga gidan.

Kallan juna sukai tace “Adam ya zamuyi? Haryanzu bata kiraka ba?”

Bata nan ne sunyi tafiya da mahaifinta suna Ko Paris?

“Faras? Ni meya damen da wani Faras? Tazo ta taimakemu mudai dan Allah.

Nikam yau munshiga uku ina zamu nufa.”

Adam yai ajiyar zuciya na takaici.

*******

Dady ne ya kalli Zainab ya mika mata kudin, kallansa tai tace “ duk na meye?”

Gashi nan dai ya kawo, nima sai dana mai fada yayi yawa.

Kallan kudin tai, jikinta ne duk yai sanyi ta amsa. Dady yace “kinga ana gobe biki su Nabila da Nusaiba zasu dawo.”

Kai kawai ta daga ta mike ta dawo daki.

A hankali ta bude ledar da aka nade kudin dashi, kallan yan dubu daidai din tai mai dasu tai ta rufe ta bude drawer ta ajiye sannan tai shiru, kafin ta jawo laptop dinta ya cigaba da shirye shiryen aikinta da take tayi a kwanakin nan..........

Eheeeeeem🤸🏻‍♂🤸🏻‍♂🤸🏻‍♂ An fa.................

******* Ayusher🏌🏻‍♀

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull