Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 105

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 105

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 105: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 105. ****** ********* ****** Amira na fita wasu hayen bakin ciki…

2,117 words

****** ********* ****** Amira na fita wasu hayen bakin ciki suka zubo mata nace yanzu ni may laifina kuma? Idan naki Nafisa kuma zagina za,ayi ace bani son dangin mijina balle ni Nafisa tsakani na da ita yanzu sai hamdala kawai. Duk da ta girmay ni amma idan nai mata magana takan daina abinda takeyi a lokacin. Amma may zai sa Amira tace wai kila harkan mu daya dasu bayan ta san koni wacece takuma san halina din. Yayan ta ma ya ganni dasu bai ce komai ba don shine ta jawota gare ni . Allah sarki yaya sadauki mutumin kirki mutum mai adalci wanda ta san ya kamata . Muryan su naji suna fadin sister indai don muna hurda dake zamu jawo maki matsala zamu daina zuwa gurin ki gaskiya. Nace akan may anty wanda ya ajeni baiyi bakin ciki da zamana da ku ba sai don anty tazo da wani zancen ta can na daban. Nace ba inda zaku idan dai ba maigidan da kanshi yace min bai son hurdana da ku ba. Wayan shi ne ya shigo a lokacin jin ina kuka yasa shi cewa Amira tazo ta bata maki rai ko? Yace ina Nafisa take nace mai gata nan yaya yace bata waya na mika mata wayan nace yaya yana magana da ke anty. Ta karbi wayan daga hannu na yan uwan suka tsura mata ido don son jin may zai fada mata a lokacin. Mun dai ga tana cewa ai ba komai yaya duk abinda tai min yar uwata ce ita tace ba komai komai ya wuce ai don badon ta muke zuwa ba ai dama. Sukai sallama ta miko min wayan ya tambayi jikina nace naji sauki ni so ma nake a sallamay ni na koma dakina wallahi. Yace sallama Fatima likita yace min sai kin haihu zasu sallamayki fa don bazasu bari ki fita asibitin nan ba hakana. Banji dadin wanan zancen ba ina cikin asibiti har tsawon wani lokaci ni wani irin ciki ne dani haka wai ? Gashi muna batun fara exam haka nake karatu a asibiti sai idan lokaci yayi zasi yarda na tafi na zana koshi tare da wata nurse zamu tafi suka ce. Yadda suka fada ko hakane haka zan shirya da safe yaya bashar yazo ya dauke mu zuwa school dani da,wata nurse da aka dauka haya don dubani ba dama nayi wani dogon motsi dana gama zamu juyo zuwa asibiti tare da ita a sauke mu. Bai tafiya gida sai yaga anbani magani na kwanta zai bar asibitin har na kare exam dina da mukayi. Gaskiya yaya bashar mutum ne don yana bani duk wani kulawan da ya dace wanda zai sa banji kewan mijina ba gurin kula. Haka zai kawo min maryam mu wuni da ita muna hira sai dare sanan yazo ya dauke ta. Mama ma takanzo sosai kuma abinci dare da rana yana saman hanya ana kawo muna duk abinda muke so. Ba laifi don yanzu da cikina yake wata shidda da yan kai saura kiris ya cika wata bakwai ina dan iya cin abinci kadan. Sai dai ba mai yawa ba don idan har naci mai yawa ranan sai na fadawa aya zaki gurin wahala. Haka dai nake zaune Iyya tayi min halarci matuka a rayuwan na don komai itace ke min shi iyakana naiwa kaina wanka kawai. Bayan shi duk wani abin bukata na itace mai aiwatar dashi da kan ta zatai min komai. Yan uwa sai faman zarraiya suke zuwa gurina duba ni zuwan Baba na biyu yana duba lafiya na a,asibitin. Haka ma a bangaren mamana saida sukayi mota daya ita da abokan arzikin ta da yan uwa sukazo duba ni. Don haka ban da wani damuwa a tare dani sai na kadaicin mijina a kusa dani kawai zance yana damuna. Acan ma Germany ya wuce gurin buga wani wasa da akayi mai zafi inda kuma team din su na basilona da yai ma,wasa yai nasaran lashe wasan da suka buga. Ba karamin kudi ya kwaso ba sai dai bai dawo gida ba ya koma gurin su baba asibiti. Baba yanzu ya dan samu lafiya don likita yace zasu iya dawowa dashi nan da sati biyu masu zuwa idan an tantance lafiyan jikin nashi da kyau. Sai kuma ga,wasa ya taso mai zai tafi arabian kingdom ya bufa,wasa wanda ake tsanmanin zasu samu makuddan kudi idan har sunyi nasara ga wasan da zasu buga. Jirgi ya samu ya kammala komai akan tafiyan su Mummy da baba sai yaya sagir da zasu dawo gida. Ya basu kudi kowa ya sawo tsaraban da zai zo gida dashi inda,zasu dawo tare suka fita dashi ya kaisu sukai sayayya inda yaya sagir ya kwaso laptop da kudin shi zaizo dasu ya,sayar itako mummy kayan yaranta da,wasu abubuwan anfanin ta ne ta sayo acan kasan. Ranan da zasu dawo kowa yana cikin farinciki da dawowan su gida anshirya ma dawiwan baba din sosai yanzu. Muna asibiti labarin dawowan shi ya riske mu sai dai ance bari dayan baba bai aiki gaba na ne ta yanke yafadi ras. Amma Rukaiyya tace min sai dai gaskiya idan kin ganshi ya samu lafiya sosai wallahi. Tun bayan fitanta nake jin marana yana dan yanka min kamar zanyi period nake ji. Sai ban damu ba don nasan tunda ina da lalura mai zai tayarwa kaina da hankali dashi. Wasa wasa ban daina ji ba har cikin dare sai barci ya gagare ni ina kallon iyya da ta samu barci tana barcin ta hankalinta a kwance abinta. Jin mara din ya matsa min ne na mike zaune aiko zama yace bai sanni ba can da naji wani iein ciwo na sauko na kama karfe gadon na dan nisa tare da murde bakina don dan zafin danaji a lokacin.

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YA SAKA MUNA,,,

Kukan dan jarin da ya fado ne ya saka Iyya dake kwance dan bude idon ta a hankali. A lokacin da nake fadin Iyya Iyya tashi ki gani abin cikin cikina ya fito Iyyah ko na haihu ne ? Tamike tana fadin subbahanallahi ikon Allah uwar dakina kin sauka ne ? Sai kuka yaron dan karami dashi sosai yake tsalawa duk Iyya tabi ta rude taje inda ake kunna wutan dakin ta kunna tana cewa. Kinko haihu wallahi uwar dakina amma sai dai killa bakwaini ne kika haifa don yaron yai kankanta da yawa. Ta dan taba yaron yakara tsala ihu tace namiji ne sai dai bakwaini ne da sauri tafita daga dakin zuwa inda nurses suke kwana ta kira su. Sai gasu da saurin su sun shigo tare da ita taimakon gagawa suka fara ba yaron nan suka rabashi da uwar tafiya Allah yasa akwai reza da na anty Raiha ta sayo min sai ta sayo parked din shi gaba daya. Dayar nurse din taje dakin doctors takira likita mace wacce tai adimin dina a,asibitin ranan ita ce akan duty. Tana zuwa ta danyi dube duben da zatayi ta tambaye ni banjin komai na fada mata komai bana ji. A cikin daren akaiwa yaron wanka nima nai wanka Iyya tace a kira gida ne a fada masu nace tabari harda safe sai a kira gida don yanzu kowa yayi barci hankalin su zai tashi tunda ina lafiya. Sosai likitan taita gwada yaron tace min lafiya yake sai dai premature baby ne idan da rabo zai rayu insha Allahu. Nace daga inda nake zaune a bakin gado anty zai rayu kuwa ? Tace insha Allahu zai rayu ai seven months ne yanzu kike da kwana biyu. Sai dai da,safe zan so muyi shawara muji idan zai yuyu sai a dan saka shi a kwaba yadan kara tasawa tukun. Bamuyi barci ba sai da,asuba muka dan runtsa kadan shigowan nurse din dakin ya,samu falkawa Iyya ta tafi sallah ni kuma ina kwance ina kallon yadda sukewa baby din. Bakwai da yan mintina Iyya tashigo dakin nace ta bani wayana , numban mama na fara kira har ya kusa tsunkewa ta daga da,sauri ba ko gaisuwa hankalinta ya daga don ta ga ban kiran ta da farar safiya irin haka. Tace Fatima lafiya dai ko ? Nace a hankali mama na haihu ne. Cikin wani murya tace kinyi may fatima nace na haihu ne mama. Sai naji ta kashe wayan maryam na nema tana barci wayana ya tayar da ita na fada mata na haihu sai Nafisa. Koda na kira nafisa ina jin muryan mutanen gida a na yaya nasan zancen ne mama ta fada masu a lokacin. Kafin wani lokaci naji kiran sadauki ya shigo yace batare da gaisuwa ba Fatima is that true o you are joking yanzu bashar ya kirani. Kafin na bashi amsa yaron da nurse din ta daga ya dan yi kuka na kara mashi a waya yaji. Yace it means yaron yana da rai har yanzu ke nan nace mai eh kawai sai aka turo kofa su mama ne da mummy da mama Asiya suka shigo dakin a rude. Idon su akan nurse din dake shirya yaron za,a kaishi pediatric asaka a kwalba. Gurin nurse din suka nufa suna kallon yaron dan karami dashi a cikin zani na da aka nade shi. Muna kallo suka fita da yaron mummy da,su sagir suka bi bayan su harda mama Asiya. Sai lokacin mama ta karaso inda nake zaune a bakin gado take cewa Fatima lafiya dai kike ko ? Na kakaro murmushi don hankalina a tashe yake nake cewa lafiya kalau nake mama. Tace to ki kwantar da hankalin ki idan yaron Allah yayi shi rayayye insha Allahu zai rayu. Nakoma a hankali saman gado na kwanta na lumshe idanuwa na shigowan su maryam ne yasa na bude idanuwana a lokacin. Maryam tana fadin tare da,waige waige ina yaron yake maji ? Tace sun tafi dashi nan tafada masu komai basu tsaya ko a gaisa ba suma suka bi bayan su da sauri. An saka shi a cikin wani dan karamin gado mai naurori tare da saka mai wani dan rigan sayi a ciki. Kafin likita ya shigo dakin sun fada min zan tashi daga wanan dakin da muke na gany room zuwa maternity room. Sai da,aka gyara komai suka mayar damu dakin lokacin yan uwa da,abokan arziki sun cika a dakin ko. Sai hira ake yayin da niko zuciya na duk a cunkushe yake min ban majin farin ciki ko kadan ni. Duk da kowa yazo fadin yake ai anyi arziki wata bakwaine insha Allahu zai iya rayuwa da yardan Allah. Barci ne ya dauke ni a lokacin mai nauyi sai mama Asiya ne naji tana tayar dani wai na tashi na sha tea da aka hada min. Na mike zaune ta miko min tea din yana wani irin tururi tace na kafa kai nasha shi hakanan. Har na daure na kafa kai zafi ya konani nai saurin cire bakina daga cup din ga tea din gudan mai yawa dashi. Lokaci daya suke ce min a,a a Fatima anya kuwa kafa kaifa zakiyi ki shanye shi duka yanzu. Nace a dan marairaice mama duka fa wallahi akwai zafi mummy tace kin manta cikin ki akwai miki a cikin shi maza shanye shi don Allah kinji. Haka na shanye tea din ina zufa take naji bakina ya dauki zafin kuna sai dai tea din yana shiga cikina naji wani irin dadi a jikina da nake jina yau kamar banawa ba. Ban dade ba na koma barci mama Asiya da mummy sukace a dan rage a dakin don na samu barci. Barci nayi sosai sai zuwa sha biyu da rabi na rana wata nurse tashigo dakin wai na tashi naje naba yaron nono. Tare muka tafi da maryam da Nafisa da mummy a ka dauko shi na zauna na fara bashi nono sai dai bai iya kamawa. Mummy ce ta gyara shi da dan kyau ya dan tsosa kadan ya koma barci don ba komai a nonon ma lokacin. Likita ya shigo yana cewa sannu madam ashe haka abin yazo muna kuma dai. Allah ya raya muna,shi ga baban shi yace yau yana da ball da mungashi yazo. Haka muka wuni yan uwa da abokan arziki sai zuwa suke gaishe ni allura akai min sai magani da,suke bani kawai. Bayan shi ni banda wani matsala a tare danj gaskiya mama ta bugawa iyayyena waya ta sheda masu yadda haihuwan yazo min haka. Sai dare aka rage a gurin mu inda aka barmu da Iyya sai mama Asiya da tace itama zata tsaya wai. Nafisa bata bar gurin mu ba sai zuwa sha dayan dare wani yazo ya dauke ta tafi.

Readers Also Read