Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 44

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 44

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 44: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 44. Lokacin da,labarin cin mutuncin da matar shi tazo har gida tai…

2,985 words

Lokacin da,labarin cin mutuncin da matar shi tazo har gida tai min hankalin Kabir yai matukar tashi sosai tunda safe sai gashi kofan gidan mu. Da Baba na yafara ganawa, kafin daga baya asa a kira ni nafito ina daure da fuskana tamau, Tun fitowa na,Kabir ya kura,min ido yana kallon yanayin da,na,fito dashi don yana son fahinta da sauki ko akwai magana. A mutunce na durkusa na gaishe su sannan na koma gefe nace Baba gani, Mutanen da Kabir yazo dasu suna zaune saman tabarman da aka,shimfida masu idanuwan su a,kaina karrr, Baba yace Bintu Kabir ne ya samu labarin abinda matar shi tazo hannan gida tai maki shine yazo ya,bada hakkuri akan sabanin da aka samu da ita. Kaina na sadda kasa nace cikin yar murya Baba gaskiya ayi hakkuri da wanan zancen don tun ba,a shiga ba an fara irin hakan Ina ga in an shiga gidan baki daya sai ai marus ke nan lokaci daya sukace ,a,a wanan ma,ai baiyuyuwa sam. Duk da sun fahinci kan zance na ina nufin nafasa ke nan sai suka shiga ba da baki da gyaran zance . Shiko kabir yana zaune yai shiru kawai abin duniya ya,kai mai ko ina abinda matar shi tazo tayi ta bashi kunya. Baba dai da yaji irin yadda suke bada hakkuri ni kuma na kafe akan sai dai a,rabu. Sai baba yace Bintu tashi jeki ciki kawai ma,karasa,maganan dasu. Namike nashige ina jin yadda Kabir yake sauke ajiyan zuciya daga inda nazo wucewa ta gaban shi. Ban kara jin zancen ya tashi ba sai bayan kwana hudu sai gashi yazo har lokacin bai sake jikin shi ba dani. Na fito saye da zani da rigar atamfa mai ruwan jan kalla, dinkin shi yai matukar karban jikina da kyau. Son in mashi kwalelenka, ranan gyale na yafa ajikina sabanin hijjab din da ko yaushe nake rufe jikina dashi. Na durkusa na gaida shi a cikin ladabi da biyayya tare da,tambayan shi gajiyan buki. A,sanyayw yace Fatima kinga yadda kika,wahal dani da,kalman ki dakike fadin wai kin fasa aurena. Don Allah Fatima koda nine nai, maki laifi, kada kice kin fasa aurena, don baki san irin wahalar da na,sha ba na ganin za,a raba ni da wanan kyakyawan halittan mai suran larabawa a hannu na. Don Allah Fatima koma may ye kada ki kara cewa zaki rabu dani akan wata, wacce dama ita bukatan ta ke nan nayin haka. Wallahi ranan da,muka,bar nan nayi tunane dubu a raina don sai na kasa banbance so na yasa kika ce hakan ko kina. Nan yadan zubo min ido yanaxmai kare min kallon kurullah , akunyace na dan rufe fuskana da hannayena . Yai ajiyan zuciya yace nagode Fatima don ko hakan ma,sheda ce ta kin sauko zaki yarda dani. Mun jima muna hira dashi yana bani labarin irin fitin matar tashi saratu yadda sukw kwasan masifa da uwargidan shi a kan lalai ita ala,dole abar mata miji ita kadai ko da ya zo tafiya sai yace kin hana ni shakat wallahi Fatima gashi haka nazo ban riko maki komai ba. A hankali nace mai babu,komai, ko haka,na gode ai, Ya ce sure ? Nace, mashi insha Allahu. Haka yatafi ba don ya,so ba yana ta,faman bani hakkuri ya,wuce abinshi. Anyi wanqn rikicin da Sati biyu ina gidan mu gaban iyayyena hankali a kwance abina na fitar da komai a raina, Ina zaune ina gyaran ganyen da mama,tabawa tasayo lanbu zamuyi miyan dare dashi. Ina cikin gyaran ganyen ne sai naji karan diran mota ta tsaya a kofan gidan mu. Dan dakatawa nayi da aikin nawa ina sauraren ko anyi bakine gidan daga bisani dai naci gaba da aiki na. Gwago na ce ta shigo gidan da sallaman ta saura kiris na zubar da ganyen da nake gyarawa don murnan ganin ta danayi. Fuskanta dauke da yalwatacen fara,a take ce min dana karaso gurin ta cikin daukin ganin ta. Bintu baki da kirki banzaci zaki zo ki share ki zaman ki haka a kauye kin bar uwar dakin ki sai damuna take tunda na koma. Ledan dake hannun ta na karba daidai lokacin da mama tabawa takw dawowa da makwabtan su. Mama tabawa tace a,a yau gwagon yara ce a garin kwana biyu kin shige birni abinki. Nan dai suka dan taba wasa tsakanin su sai kuma gwago take tambaya yayanta yana gona ke nan ko bai dawo ba har yanzu kuma tana son ganin shi. Ba ,a jima,ba Baba na ya dawo daga daji, sun jima suna hira da babana wanda akasarin hiran akan yar uwar suce da gwago tai jinya takare. Can tun ina jin hiran su sai na bar jin tashin muryan su, ma,ana dai za ai magana ta,siri a tsakanin su ke nan. Zuwa can Baba na ya daga murya ya kira ni nazo, na,samu guri dan nesa dasu kadan na,tsugun na. Baba na yace Bintu gwagon ki tazo tafiya dake ne akan umurnin mijin uwar dakin ki, na can. Don haka,sai ki harama ki shirya ku kama hanya don kinga mota,sukutun ya bayar azo a tafi dake don ba,ayi zaki zo ki zauna haka,ba harki dade. A take na bata rai na,tare da,dukar da kaina a kasa, baba na yace ko baki ji may nace bane Bintu. Cikin yar karamar murya nace naji Baba yace tau yau din nan ki hada kayan ki ku tafi tunda sunyi mutunci haka nima idan na samu lokaci wuri yasha iska zan shigo naga inda kuke. Na dago kai din nai magana gwago ta watsa min harara dole na noke kai bance uffan ba. Namike jiki ba karfi idanuwa na,sun ciko da,hawaye amma,ba,wanda ya kula da damuwa na nafara ashirya kayana. Kafin sallah magariba haka gwago tace sai muyi hara man tafiya kada muyi dare sosai a hanya. Nan na,dauko yan abubuwa nabawa Farida yarinyar da zantafi na bari cikin uku ban mama tabawa, Komai da muke boyewa,nabar mata,ban dauka,ba, sai kudin dana,bata ta boye ta tafi garin su dashi idan taga wuya,zai kashe ta a gidan. A sanyaye na gama hada kayana raina a bace don kwata kwata ban son komawa gidan su maji don bani bukatan zama cikin wanan babban gida mai cike da tarin rikici a cikin shi. Saboda wancan karon ma banji dadi ba don a tauye nake cikin su sai dai na kulla a raina wanan karon kan zasuga canji sosai a gare ni don su barni na,dawo kauyen mu. Munyi sallama da kowa mun kama hanya sai dai kallo daya ya ishi mutun sanya alaman tambaya a kaina din yadda nai kicin kicin da raina. Sai ranan naga mama tabawa ta,tausaya,mun tana fadin haba baban binta in bata son zuwa abarta mana. Daga Baba har gwago na ba wanda yabita kanta sai kyaleta sukayi kawai. Mun hau titi da kyau mun saki hanyar dajin mu gwago ta kalle tana cewa Bintu kin bani mamaki sai kace wace za,a kai mugun guri. Acikin wata raunaniyar murya da take gap da,narushe da kuka nace gwago bawai mugun wuri bane. Amma zama gidan da,baka,da,alaka da kowa,sai zaman girma,da,arziki kawai, shine nake jiyewa. Tace da kika zauna wancan karon anyi wani abin ne sai da na nisa kadan nafara fada,mata,duk yadda aka,kwashe da,bata,garin. Tace ni na sani ai ba yau ba Hajiya kubura munafukace ta,karshe wallahi ko. Tsayin lokaci muna,tafiya muna hira har muka fara hango cikin garin sokoto. Unguwan sama road muka dosa inda muka tsaya a kofan gidan Alhaji habu. Lokacin dare yayi ko don har anyi sallah isha,i don haka cikin gidan muka shiga kai tsaye. Na zaci gidan mu zamu shiga amma,sai naga sabanin hakan kawai mun shiga gidan masu hali. A dan tafiyan da,nayi na,samu canji na sauyin launin gidan sosai an canza abubuwa da dama a gidan. A kofan da aka,sake wanda ban zaci na,maji bane muka tsaya tana sallama daga kofan shiga. Muryan maryam ce naji tana a,a mai masa,oyoyo harkin dawo ashe? Sai tafara leken bayan gwago tagani ko ita kadaice tazohangini tayi ina,saye da lace din da Kabir ya dinka min da matan shi cotton lace ne mai laushi sosai da duwatsu caaa a jikin shi. A razane tace maji yau kan ga yarki ta dawo gare ki gwago ta cika alkawari kowa ya huta dada. Da sauri ta karaso gareni ta rugumay ni cikin jin dadin ganina a lokacin. Jin abinda ta,fadi yasa Amira fitowa daga dakin ta cikin sauri tana min sannu da zuwa cikin murna da jin dadi itama. Maji tafito a hankali daga daki ganin yanayinta yasani saurin fahintar bata da,lafiya a jikin ta. Inda,take na nufa da,sauri na,fada jikin ta sai ta rungumayni cikin jin dadi. Ta,dago kai ta kalli gwagona tace mai masa nagode da,wanan karamcin da kikai min dawo min da Fatima,a kusa dani. Kai amma dai Bintu badai a kauye kike ba dai ko gaba daya kin canza kin koma wata big girl dake haka. Nan aka faea hiran yaushe rabo bayan nadan huta anmin tayin abinci nace na koshi. Sai Maji tace naje na gaida Baba kafin ya,shige da sauran mutanen gidan gaba daya. Ido na,runtse gami da,cewa ya Arhamanin Rahimin, ahankali na mike nafita,duk kallo suka,bini dashi. Ina fita maryam tace maji gaba,daya, fa diyar ki ta,sake ta canza kyaunta ya,dada,fitowa a fili, jita kamar wata wace take zaune a abuja ba kauye ba. A falon Baba na samu hjy kubura na shiga da sallama na itace tafara cewa wa nake gani haka kamar Bintun hajiya maijidda. Na karasa inda suke gefe kadan na tsugunna ina gaishe su Baba ya nuna j8n dadin gani sosai tare da min ba,a naje gida na lake na manta da karatu a gabana. Na dan kai lokaci a gurin Baba yana dan min tambayoyi a kan noman mutanen kauyen mu nai masu sallama nafita daga dakin. Dakin Umma da nake jin haya niyar su na fara shiga duk sunyi mamakin gani na a wanan lokacin da kuma yanayin da suka ganni ba,wani fita hayacin da nayi banda kara kyau. Nan dai duk na zagaya nagaida su na,dawo dakin mu nan aka zauna a ta hira inda maji da gwago suna can gefe suna,maganan su ta mayan wanda bamu san akan may sukeyin shi ba. Sai dai yanayin Maji ya nuna min cewa tana a cikin damuwa sosai ko ba,a fadi ba. Ban dade dasu ba na mike ina fadin zanyi sallah dake kaina. Nan dai bayan na idar na mika,kukana ga Allah akan ya,kareni daga duk wani rintsi ko matsalar da zan fuskanta agidan mutane. Ban fito ba na koma na kwanta amma kuma na kasa barci sai sunayen Allah maigirma nake kira ina neman agaji a gurin shi. Tun dawowana kula,da lafiyan maji ya koma kaina ko yaushe ina daki tare da ita. Banga Sadauki ba kuma,ban tambaya ko ina yake ba nasan dai kila baya garin ne. A hankali natsuwa yazo min da zamana dasu don suna nuna min kulawa sam mutum bai gane cewa ba Maji ce ra haifeni ba a gidan. Satina biyu a,sokoto nagane yanzu yanayin gidan ya kara canzawa sosai ba ruwan wani da wani a gidan har yanzu. Amma,akwai ci gaban rayuwa,sosai da,suka,samu don yanzu budi ya kara sanuw masu sosai. Hankalina yafara kwanciya sai dai kullun ina kewan iyayyena da yan uwana adan zaman da mukayi da,mamatabawa da sauko da,akidar nuna min tsana,a fili datakeyi. Kuma wani abinda ya,tsaya min a,rai shine tunanen Kabir yadda zaiji idan yazo ya,samu banan nan nabar gari bada sanin shu ba. A haka takardan makarantana ya fito wanda ban san baba yai min process ba saida yazo a hannuna. Ranan nai murna da farinciki garda kuna don murna,saboda ban taba zaton zan samu ci gaba da karatuna ba. Na fara zuwa makaranta tare da Anty maryam muke tafiya don makarantar daya da ita state university muke.

Wata rana mun taso daga makaranta ga hadari ta gauraye garin da kyat muka samu Napep din da zai kawo mu gida. Ganin iska da kura ya,taso a lokaci guda nace wa mai Napep malam don Allah ka,samu dan guri ka Parker har iskan nan ya dan rage yawa don tafiyan mu a haka hatsari ne. Guri ya samu kamar tadda nace ya dan tsaya a gefen titi kamar ance na daga kai na hango Nafisa a cikin motan wani matashi. Yanayin dana ganau yasa gabana faduwa da,sauri na juta gurin da Maryann take zaune sai naga hankalinta a,waya yake ita, don haka naja bakina nai shiru ban fada mata ba. Can naji mai Napep na cewa bari mu lalaba don ga alamar ruwa nan tafe da sauri yake tuki sai gamu a unguwar mu har kofan gida yakaimu daidai ruwa yana fadowa da karfin Allah. Take ruwa ya zubu ga iska sai kamshi yanayin garin ya canza launi alaman sabon damana yazo ke nan. Haka muka sauka shiga gida ruwa,na kada mu yana daga muna mayafin jikin mu. Yaya Imirana na hango can tsaye daga kofan part din shi tawani kura muna ido kamar tsohon maye. Da,sauri muka nufi hanya shiga cikin gida duk habar kafan mu iska na dagawa yana fita a fili. Daga inda yake naji muryan shi yana fadin kai ashe cikan nan tadawo ne tubarkallah dai kan komai tsab wallahi akwai kayan dadi a gurin nan. Banzaci maryam taji shi ba saiji nayi tace dan iska a haka dai zaka kare gindin mata. Mukan da,sauri muka karasa ciki muna kankamay kayan mu daya jike sharkaf da,ruwan da,akeyi. Da karfi maryam ta rura kofan falon maji muka fada ciki a guje saukar da ajiyan zuciya nayi yain da naji ruwan bai dukan mu. Ashe maji na,falon cikin damuwan rashin ganin mundawo kafin ruwa ya fado din sai ce muna take sannuku ku shiga ku cire wa yan nan kayan kafin sanyi yakara hawan ku. Sam ban lura da mutum a zaune ba a lokacin sai ji da nayi Anty maryam ta,saji kara da karfi. Da sauri na juya zan kona,waje da gudu sai naji tana fadin oyoyo yaya sadauki. Najuya da sauri inda naga ta nufa yana zaune fuskan shi dauke da murmushi. Yace jeki cire kayan sanyin nan kafin yai maki illa, Cikin shagwaba tace yaya ni har na manta dasu ina murnan ganin ka ai. Nikan ban tsaya ta kan su ba na,shige daki nafara rage kayan jikina tare da zuwa faban mirror dakinmu nayi wata futu, futu dani don jikewan danayi. Na fada ban daki nawatsa ruwa tare da,dauro alwala nazo nai sallah. Saida na,gama komai nafito falon ina,saye da,wata doguwar riga dark blue doguwa ce rigar har kasa hannun ta shara shara nazo na zauna falon har lokacin yana zaune suna hira da kannen shi. Zamana yai daidai da kiran wayana da akayi na dauka ina mamakin wanda ya kirani a wanan lokacin haka. Sai na,dan basar ban dauki wayan ba don ban san mai kiranaba alokacin. Sai kuma ga,kiran ya kara shigowa again na dauka da,sallama ban damu da cewa wai na daga daga falon ba. Don nasan daga inda suke babu wanda zai iya jin abinda nake fadi don tsabar kwantar da muryana da keyi. Bayan na gaisa da may shi na nuna bangane mai magana ba. Yace haba Fatima na zaci ko a mafarki kikaji muryana zaki sheda ai tau Kabir dinki ne wanda aka gudo akabari a kauye. Maganan shi ce ta dab sani dariya sai duk suka juyo gareni hardashi suna min kallon mamaki. Nan na,fara bashi hakkuri ina,fada mashi yadda tafiyan yazo min a bazata nadawo sokoto. Amma yayi hakkuri dan banda nomba shine yasa ban fada mashi ba yakara complain kan cewa ban damu dashi badaine tasa hakan. A hankali nace na tuba sake ba insha Allahu, abin mamaki sai naji ya kwashe da,dariya tana is alright hakan ma yafi min don yanzu zan dinga samun ki available, Uhhm kawai nace cikin murmushi. Ina dago ido mukai arba da yaya sadauki da ya maka min wata uban harara na kawar da kaina tare da ci gaba da waya na. Kabir yace min yanzu yana hanya zai tafi wani gurin aiki ne amma idan ya,dawo zai kirani. Nace tau Allah yakaika lafiya Allah ya,tsare min kai. Ina kara dago ido muka kara arba dashi dole nace mashi cikin yar murya sannu da zuwa yaya ya hanya. A daure ya amsa min kamar wanda akasa shi amsawa dole. Nikan namike zuwa daki sai Maji take cewa ina kuma zaki ba,aci abinci ba nace sai anjima zanci mama. Kai Fatima kina dai wasa da cin abinci har yanzu mutum haka bai damu da cin abinci ba. Nikan na shige abina daki ban tsaya ta kansuba don wanan mai mugun halin dake zaune a falon. Ban dade da shiga ba naji ruwa yakara tsinkewa kamar da bakin kwarya. A hankali na mike don na rufe window din dakin mu dake bude don feshin ruwan dake shigowa. Karan mota naji za,a fita daga gidan mamaki ya kamani wake da karfin halin fita daga gida a,wanan lokacin da ake tsula ruwa haka masu yawa. Mantawa nayi ina,son nasha ruwa sai na koma falin na dauka nan nasamu Maji na magana cikin takaici. Tana cewa yanzu fita yayi cikin wanan ruwan haka ba ko ina zai tafi ba sai gurin shegen shaye shayen su. A duke nake gaban fridge ban san lokacin da na dago ba nace mama yaya ya koma shane kuma ? Cikin takaici tace min Fatima bari ke dai, Allah dai ya kawo min saukin wanan al,amarin kawai. Abu sai yayi kamar ya sauki sai kiga yaron nan ya kuma koma ma halinshi lokaci guda. Nace anya mama wanan abin ba ci gaba ake da tufka ana,wal,wala ba kuwa? Amirah tace nima dai hakanace daki na koma hankalina a tashe da zancen danaji mara dadi. Sai yanzu nagane abinda ya jawa maji ciwon zuciyan da akace yana barazanan kama ta.

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,

A LOKANCIN MU KE,,,,,

Readers Also Read