Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 47

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 47

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 47: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 47. ****** ********* ****** Dakin kudi muka koma mu kadai ne a…

1,923 words

****** ********* ****** Dakin kudi muka koma mu kadai ne a dakin yana da tsari sosai harda dan fridge da kayan kallo a cikin sa. Maji har lokacin magani bai sake ta ba na kafe ta da idanu sai barci take gashi duk ta wani ramay sosai da ita. Ban san lokacin da tausayin ta ya kamani ba sai jin hawaye nayi sun zubo a idanuwana sai sauka suke a kumatuna. Ban san ya shigo ba yana tsaye yana kallo na may kikewa kuka haka duk suka juto gareni kuka kuma Bintu sai maryam itama ta fara kuka. Tace Tun safe Bintu ke kukan nan idan ta kalli maji nai mata magana taki bari. Likitane yashigo dakin saye da corth din shi baka duk muka gaishe shi yake cewa tare dan taba jikin ta har idanun ta. Zata dan samu sauki idan ta farka amma yaya akayi kuna gari kuka bari har ciwo yaci ta haka a gida. Gaskiya data kara awa a lokacin bata samu taimako ba da zamu iya rasata wallahi. Ya juyo inda nake yana fadin idan ta farka sai ki hada mata tea mai zafi tasha sai ki bata wanan maganin da aka sayo amma don Allah kada kiyi mata wasa da maganin don ba abin wasa bane. Yana fita dakin na mike tare da daukan cup na fita na dauraye shi na,dawo na,saka acikin wani leda baki. Yace Amira waya zo daga gida cikin su Umma eh to Bintu tace ina barci wai mommy ta shigo bayan ita ba,wanda yazo kuma. Muna zaune dakin kowa yai shiru a cikin mu duk kowa da abinda yakeyi sai ga hjy Kubura itace a gaba yaranta na bin ta a bayanta. Suna dauke da kwandon da kuloli a cikin sa da flask din ruwan zafi sai ledojin da yaran suka riko na kayan fruit. Tana ganin sadauki take cewa ,a,a sadauki ashe har ka iso yace cikin dagawa daga saman kujeran da yake zaune kusa da maji don ya bata guri na iso mummy. Da sauri na mike na karbi kwandon dake hannun ta, nakao saman durowan dakin na asibiti na aje. Tace ai natafi wancan dakin na farko sukace min kuna nan ancan guri. Yace eh mummy gurin can bai min ba mutane sunyi tawa baza,a bar mara lafiya yayi barci ba da dadi. Hakane gaskiya amma nan din kaga is ok zata samu hutawa sosai anan din. Likitan ya shigo ko may yace kafin wata tai magana nace zazzabine wai typhod yai mata yawa suka ce ta ce wai da sauki ai nazaci suce ciwon zuciyan tane ke batin tashi. Nace yama ce bata da ciwon zuciya wancan daya fadi haka bai san aikin shiba. To Allah ya sauwaka muka amsa mata da Ameen mummy tace zamu koma don dare yayi sosai gani da yara bandawo da wuri ba shiyasa ban yi girki cikin lokaci ba. Anwar yana lake jikin yayan shi tun shigowan su dakin yagan shi ya lake mashi sai hira suke dashi. Tamike tare da muna sallama tabar dakin muka dan rakata zuwa kofa tace ku koma abinku zanga wata kawana dake duty acan ward din. Tana wuce muka dawo ni da maryam nace yaya a zuba ma abincin kaci ne? Yace No barshi banjin cin abinci yanzu Amira tace yayana bari a zuba maka kaci ko kadan ne don Allah. Hakana jawo plate na,soma zuba mai abincin wanda dafa duka ne da kayan lanbu a cikin shi sai kifi da tai amfani dashi. Sai dan ferfesun kifi danye da tayi daban ta zuba shi a wani dan kula karami. Shina zuba mai don nasan bai shiri da dafa duka shi sai dai da miya ko tuwo. Na koma gefe na zauna maryam tace zuba muna abincin muci mana kin kima zauna. Nace sai dai na zuba maki ni ba yanzu zanci ba Amira tace kinbsan bafillatace sai kafa ya dauke taci. Hmm aini Bintu tabani mamaki jifa yadda tai saurin boye ciwon maji wa mummy harda cewa ance wanda yace tana dashi bai san aikin shi ba. Nace eh mana yanzu da anfadi gaskiya sun samu na fadi kena a unguwa cewa bakinciki ne zai kasheta ai likita yace kaza yace kaza. Maryam tace wallahi kamar kina zaune kuwa don tana komawa zakiga muna fukancan sun tambayeta may ke damun ta kamar da gaske da an fada masu shike nan an samu na fafi ana canza magana. Sadauki wanda yake zaune yana shan ferfesun shi hankali kwance bai ce muna kala ba. Suna cin abincin duk kamshi ya bude dakin sai hira suke kasa kasa kan mummy a gidan su . Yana gama wa yadago kai muka hada ido na daure fuska na yace kwashe kayan nan anan . Sai da ya sha ruwa yace ke may yasa bazakici abincin ba ke nace sai anjima zanci yaya nadan sha lemo dazun. Ya dan kalleni kamar mai nazari can yace su waye zasu kwana anan don dare ya soma sai nakai sauran gida. Maryam tace sai dai abar anty Amira tunda itace babba ko da sauri tace a,a wallahi ban iya tsayawa ni kadai don tsoro nake ji. Baki da hankali ne idan baki zauna ba wazai zauna dama ke dakike babba wallahi yayana ban iya zama ni kadai anan gaskiya. Nace dama ka barsu yaya dama ni anan zan kwana ai tare da mama su tafi gida su huta su. Yace don may za,a barki ke kadai dole dayan su ta tsaya tare dake a nan ya wuce da maryam mukuma muka zauna dakin nan zamu kwana da mama. Azaton mu ya tafi ke nan can sai gashi ya dawo dauke da ledoji ya sayo muna su kayan shayi da kwalayen drinks sai naman kaza mai zafi ya kawo muna. Yamika muna yana cewa kuci naman kubar wa maji idan ta farka kila ta danci Amira ta jawo ledan gamu tana fadin oya muci Bintu nace fara ci ke, nan tafara yagan naman tana kaiwa bakin ta. Zaune yake a saitina yana amfani da wayan shi data dauke mai hankali. Yace wai may yasa ke bazakici komai bane wai, na dan tsuke fuskana san nan na ce haka kawai . Yace amma badon kin ci wani abuba ko kin koshi ba ko? Nace ban karya ba yaya ban dai iyacin komai ne saboda hankalina daya tashi. Yaya na fada maka bar Bintu haka take ita bata damu da cin abinci ba fa ita. Ya dubi Amira yace kina nufin zata iya kwana a haka bata ci komai ba? Haka take ko agida sai maji tai mata fada take cin abu ita. Yace tura mata naman da kwalin drink din tasha ban musa musuba na dauki yaka gudanakai abakina da kyat nake iya taunawa na dauki drinks din nakai abikina sai naji sanyin shi yai min yawa sosai. Haka dai na danci naman nasha drinks din kamar wace za,a kama a lokacin Wayana yai ruri da sauri na nufi side drower dana aje wayan akai. Ina kokarin duba maikirana a wanan lokacin don dai nasan ba Kabir bane don a lokacin yana cikin iyalinshi. Sadauki ya kafe ni da ido don jin waya kirani a wanan lokacin kuma ko zanyi fitsaran dana saba na waya agaban mutane dayace inayi. Na daga tare da sallama sai naji muryan gwagona tana tambayana jikin maji nace gamunan ma asibiti da ita an bata gado. Nan take ce min insha Allahu gobe tun da safe zata shigo gari don yanzu tafi gane ma ta dinga kai kaya gari gari. Ina kashe wayan maji tana,farkawa duk mukayi kanta gaba dayan mu muna mata sannu da jikin ta.

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA,BA KA DA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,

A LOKACIN MU KE,,,,,,,

Kudi yabashi har dubu daya,yace yaje yasaya duk abinda yake so dashi yaron bai san girman kudin ba yadai san ko nawane don yaka,yaje ya fara sayen abinda ke ran shi. Kayan zaki sai kayan sanyi su ya,kwasa ya sha har yafara kyautawa,abokan shi. Ya dawo dauke da roban shi dakin sisko nan suka zauna ya sa masu wasan turawa suna kallo daga,shi sai shi a daki. Can sai ya sauya tasha inda ake wani wasan shedana zallah. Yaron sai ya,fara kawar da kan shi gefe sisko ya ja mai kafa yana fadi ji dan nema kaida wata rana zaka zama boss da wanan harkan kake kawar da fuska ai gara ka fara koyo tun yanzu. Nan dai har yaron Aliyu yadan fara tsayawa yana kallo ta gefen idon shi ajima kadan yake cewa zai tafi gida sisko yace kai tun yanzu yace lokacin zuwan shi makaranta yayi ne. Jawo shi yayi kamar wandaya,samu budurwa yana dan wani wasani dashi sai da yaji dai,dai ya sake shi da zai tafi sai da ya,kara mai dan kudi saboda jan ra,ayi gobe. Ruwan sai makaranta,wasu, almajirai yakai yace inji wani mutum yace na bayar sadaka anan. Shi kuma ya kama hanyan gida yana murna da farinciki ya isa gida ya mika wa uwar shi kudin ta,saura ya samu guri ya boye. Kamshi turare taji a jikin shi tace kai kai kai ina,kasamu wanan turaren haka mai kamshi. Nan ya shafto karya yana fadi wani yaro ya ysunci kwallaban turare shine muka dan sawa jikin mu. Tace yaci abinci yace sai ya dawo ba yanzu don haka tace yai niya yafita koshi da kyat tasamu ya fita don ya kwata jikin shi yana mai ciwo ga kuna kayan sanyin da ya cika cikin shi dashi fam. Amma ita da yake son kudi ya rufe mata idon ta sam bata hango illa ga rashin cin abincin da yaron baiyi a kwanakin nan ba. Yaro idan ya,fara talla ko yarinya komai zama kamilin yaro kwana kadan da,fara tallan yaro idon shi zai bushe. Idan sau daya kakewa yaro tsawa ya bar abu yanzu sai kayi uku masu karfi kfin ya bat abinda ka hanne shi. Yaro idan ya fara talla baijin naiyi ko kunya fada wa babba magana yadda yaso sai dai kai babba kaji kunya. Yanzu duk irin haka ke faruwa,da,Aliyu amma uwar bata da fahinta ita bukatar ta kawai ya kawo mata kudi a rayuwan ta. Mahaifin yaron ya ga matukar canji akan dan shi sai dai ya danganta halin yaron sai ya dangata shi da girma yasa shi canzawa a baki daya. Tun wanan ranan kullun sai Aliyu ya,tafi gurin sisko saboda dan kudin da yake samu gare shi. Gashi uwar ba ido take sakawa akan yaron ba ita gurinta kawai shine, taga ya kawo mata kudin da yawa.

****** ********* ****** Tun wanan ranan da suka hadu suka zama abokai tsakanin su da Nafisa. Ance abokin barawo barawo ne don Nafisa bata san ya akayi tafara shan abubuwan dasu Raiha ke shaba saidai kawai ta tsunci kanta a cikin shaye shaye dumu dumu da ita. Ga uwar ta,Umma a kullun zancen ta sai zagin sadauki da yiwa uwarshi dariya bata san na dakin ta yafi illa,ba ma. Sai dai tana kokarin ganin kowa a gidan su kada ya,san zancen har a,kyamce ta ita da uwarta kamar yadda akewa Maji da diyan ta gaba daya da abin bai shafa bama. Yanzun takai har fitan da,su Raiha keyi zuwa wani gari tare da Nafisa suke yin shi, don sai ta,shirya karya cewa za su wani gurin yan uwan su ko gidan kawarta sai kawai su fita garin suyi kwanakin da zasuyi ba ta gidan. Gashi ir8n na fitsara ba komai bane a gurin ta don wayewan ta tana ganin yakai haka ita.

Readers Also Read