Kenza eBookz

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 65

A lokacin muke by zainab i makawa - Chapter 65

A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 65: A lokacin muke by zainab i makawa Chapter 65. Suna zaune sai hayaniya suke a tsakanin maryam da Amira suna…

1,435 words

Suna zaune sai hayaniya suke a tsakanin maryam da Amira suna hiran wai sun kalli wani film din biri jiya da,dare shine suke hira a tsakanin su. Ina zaune a kan kujera na jingine jikina saman makarin kujeran nai shiru ina sauraren hiran su. Sai dai anihi na sha jinin jikina sosai daga irin kallon tsana da yaya sadauki yake min daga gefen da yake zaune. Na fahinci wayan da nayi ne yanzu ya jawo min wanan tsanar haka to amma ai saboda shine ,aka gaisa dani din. Hannun shi saman goshin shi ya dan dafe kai yakai bayan shi a makarin kujera yai kwanciyar balance saman kujera ta hanyar mike kafafuwan shi. Ganin haka nima na murde nawa fuska babu wallawala acikin sa ko kadan. Ganin yaki ya bar falon yasani mikewa ina tafiya cikin dan dan gyasawa na nufi kofan shiga daga ciki. Yabi bayana da kallo a hankali yana duban yadda nake taka kafana still a cikin wahala. Yace ke zo nan kawo kafan nan nan na kara ganin yadda yayi sai a shafa magani . Kamar na wuce don yadda yake magana cikin nuna isa, da gadara kamar dan wani sarki shi mutum ne muskilin karshe kilama shiya sa yake cin kwallo don in ya kama sai ya kai gola kamar abin tsafi sai yaci kwallo. Shigowan Maji falon ne, shi ya katse min zancen zucin da nakayi tsaye . Sai maryam ke fadi lah Bintu ba dai wai tsoro kike ji ba haka tun dazun yaya yace ki kai kafan ya duba ya gani, ko sai an koma asibitin ne ? Nace cikin daurewa ni kafata normal take don banjin komai yanzu, Yadda nai magnan tare da dan murguda baki kadan yasashi cewa cikin takaici wanan yariyar typical yar kauye ce wallahi. Shigowan mama yasa take kallon mamaki da son tambayan ko lafiya yace cikin rashin nuna tsoro ko damuwa. Wanan local yarinyace ance tazo a duba kafan takewa mutane maganan nosenses, wai da kafan ma baka,barta ba sadauki? Yanzun kuma may ne mata, maji, kawai don za,a duba lafiyan kafan a shafa mata magani shine abin magana kuma. Maji zatai magana sukaji muryan mata kaman da dan yawa suna kwada sallama a kofan dakin maryam dake tsaye tafito don taga ko waye? Suna gaisawa daya daga cikin matar tace ance a nuna muna dakin hajiya Atika da hannu Bintu tai masu kwatance su tafi can. Su na dauke da akwatina sa sauran kayan tarkace irin wanda ake kai kayan lefen mace kayan aure. Maryam na fadawa Maji ta ce kayan lefe kuwa a gidan nan kaya waye ke nan kuma. Amirah tace kila Nafisa ce ta samu miji ko Rukaiyya, shine aka kawo kayan su. Can muka ji suna fadin bamu ba aura wa yar mu mazinaci mai abin kunya abin fadi irin haka. Nan dai suke ta sake bakaken, magan ganu iri iri suna aibanta Imirah dashi haka yasa duk muka fahinci cewa ashe kayan lefen da akakai na auren Imiran shine gidan matan suka dawo dashi, wai sun fasa saboda labarin da suka samu na abin kunyan da yayai wa yar mutane a gari. Daga inda nake zaune nace Allahu akbar yanzu a take Allah ke gwadawa mutun laofin shi tun a duniyan nan. Gashi dai Umma da kafatan suka je gidan su Rahama suka aibanta yaya uwar ta tace am fasa auren yaya da yar su. Ranan kun, manta babu irin maganan da su mama basu fadi ba, a gidan nan su ke cewa aure sai da muga anayin shi shiyan nan. Yau ga shi Allah ya mayar masu da martani abinda suka shuka tun ba,a je ko inaba sun fara girban abin su. Masha yin da suke fadi abin kyama gashi sai a zauna dashi ayi koma hankali a kwance sabanin dan ta katon mazinaci da ko maza yan uwan shi tsoron shi suke ji balle mata. Muna ta hiran mu hankali kwance ban san cewa yaya Sadauki ya dawo falon ba duk abinda nake fadi a kunnuwan shi. Ganin Amira tana kallon kofan shigowa falon yasani juyawa naga may take kallo ne wai. Ganin shi nayi tsaye kinkam ya harde hannayen shi a saman kirjin shi, Ya zura min ido fuskan shi babu walwala ko kadan a cikin shi ya sha mur sosai dashi. Ina ganin shi tsoro ya shi ya dan kamani indai har baiji abinda nace gamay da tsohuwar budurwan shi ba. Sai kawai nai shiru tare da dukar da kaina kasa dariya maryam takeyi tace kai Bintu yanzun fa kike ta masifa kan anwa yayan ki wullakanci yau gashi Allah ya rama mashi. Maimakon nayi magana sai ma dan kai kaina saman kujera nai shiru tare da lumshe idanuwa na kawai. Fuska a murtuke ya karasa takowa zuwa tsakiyan falon yana cewa wani gulman takeyi wa mutane ne wai? Nace ai bani kadai bace magulmaciya kowa ma anan gulman yakeyi akan abinda ya faru. Yace see your mouth muna fuka ta iya maida magana kamar wata tsohuwa can da ita . Yarinyar ta iya babban magana da gulma kamar bayerabiya. Haushin abin da ya fadi naji nace kai nifa wallahi in mutum bai daina kirana da mugun suna ba wallahi zan ramane wata rana. Ni natsani wanan kalman na munafuka da kake kiramin in hakane ai kaima mugune na karshe. Cafka guda yai min akaina na yanka ihu da dan karfi ido suka sako muna gaba dayan su da mamakin yadda halaiyan yayan su ya canza yanzu da irin mugunta da yake min. Bai sake min kai ba nikuma sai fadi nake wallahi zan fadawa mama don Allah yaya ka bari wallahi akwai zafi sosai. Ba kince ke baki da kunya ba bari na gwada maki mugu nake naja shegen kan nan mai tsawon banza ba gyara. Ji kan ta kamar ba mace ba kullun a yamutse ko gyara bata iya ba irin na mata, sai shegen gulman tsiya karama dake. Wai Sadauki may yake damunka ne ban san wanan irin iskancin ba da kake wa yarinyar nan a gidan nan Tace karya take ba mugun kake ba dubi yadda ka rike mata gashin kai kaman wani mayanki. Ya dago kai don jin muryan mama a bayan mu ya koma ya dubi gashin da tace ya rike min bai sake ba har lokacin. Yace wallahi maji Fatima ta raina ni gulmana nasamu tayi da su Amirah shine nake koya mata hankali. Koyon hankalin ne a haka? Yace maji wallahi duk kin bari ta raina ni Allah ko. Tace rufe min baki mara kunya kawai ina maka kashe di akan wanan yarinyar amma bakaji da Baban ku zan hada ka tunda ni ka raina ni. Jin abinda maji tafadi yasa shi sake min kai tare da kutawa yace sai na balballa ki wata rana. Ya juya yana gyara hannun rigan shi da yai dan squeezing. Maji ta girgiza kai tace sai nayi maganin ka wallahi akan Fatima. Yana fita daga falon ta juyo gare ni tace Fatima ki kiyayi sadauki don ba hankali gare shi ba kada ya halaka ki a banza. Wallahi mama ban mashi komai ba kawai ya samu muna hirane shine ni ya sauke haushi a kaina. Tace na dai fada maki ki iya kanki dashi mugun yaro ne bai dariya sai bakin ketan tsiya kawai. Amirah tace kai maji yayane kuma mugu yau ? Ba mugun yake ba may yake? Maji wallahi in kina shiga tsakanin yaya da Bintu watarana fa zakiyi kunyane barsu kawai inda kika gansu a dunkule. Maganan da Maryam tayi yasa maji kallo na nace ni wallahi mama karya take min ba,wani abin dukule dana sani. Shiru tayi tare da shigewa daki tabar munan falo maryam na fadi muna ganin wani sabon sallo a gidan nan. Na ce don Allah anty bari kada ya balballani kinji dai ya fadi ni yanzun ma,in yashigo gudu zan dinga yi yafi min wallahi. Hummm kamar da gaske nifa nasan komai wallahi. Tare muka hada baki da Amira muna cewa kin san komai kamar yaya fa? Tace ni wallahi tun a asibiti ranan na kara gane komai. Jifa yadda yaya ya rugumay ki yana lalashin ki. Nace kai anty maryam wallahi kada ki kulla min sheri don Allah rufa min asiri kada kisa yai ball dani a gidan nan. Shidai kawai ya tsanine yasa yake min haka wallahi in gaskiyane yai maku haka mana. Sai naga ta sa dariya tace ji min wanan fa yai muna haka mu kannen sa. O ni ba kanwarsa bane ke nan ko ? Koma dai may kike ai zamu sani watarana Allah dai ya nuna muna lokacin kawai zakuce na fadi ai.

Readers Also Read