A tausayawa juna complete novel - Chapter 2
A tausayawa juna complete novel Chapter 2: A tausayawa juna complete novel Chapter 2. Cikin sanyi Innah ta zauna gefen su tare da cewa. "Hak'ik'a Aysha kin…
1,255 words
Cikin sanyi Innah ta zauna gefen su tare da cewa. "Hak'ik'a Aysha kin cika k'awa ta gari mai tunatar wa tabbas ke abin son kiyi k'awance ga duk mai hali irin na Rukayyat dan zaki tunasar da ita hak'ik'a naji dad'in kasan cewarki tare da y'ata da surkata". Sai ta kuma juyawa gun Maryam da tayi k'asa da kanta cikin kula da k'aunar matar d'an nata tace. " Maryama Allah ya miki albarka rabbi ya baki ladan hakurin da kikeyi, kuma Insha Allah Umar kam zai sauya miki insha Allah zanmi shi nasiha zan kuma nusarda dashi zan fahimtar dashi illar rashin tausayawarsa gareki". Cikin sanyi tace. "Innah kar ayi mai fad'a zai d'auka k'ararsa na kawo". Murmushi tayi tare da juyawa gun Rukayyat cikin had'e fuska tace. " kinga mata nagari sune masu hakuri da mazan su a cikin ko wanne yanayin matukar bai sama addininmu ba, kinga duk yadda yake mata tana gudun bacin ransa".
Cikin sanyi tace "Innah Insha Allah nima zan kula zan nemi gafarar Abban Salim hak'ik'a nasan yayi hakuri dani da halina".
Innah ce taci gaba da cewa . " Hak'ik'a ya zama wajibi a garemu mata mu tausayawa mazanmu domin suna buk'atar tausayawar mu garesu sabida rayuwa ta juya komai ya canza Allah ya kawomu lkcin da tsada tai mana kaka gida sai dai muyi ta Addu'a Allah ya kawo mana d'auki dan wannan tsad'a ba mutun d'aya ta shafaba ta shafi kowa, Kuma wannan tsada ba laifin kowa bane muk'addari ne jarrabawa ce mu dage mu samu muci wannan jarabawah, sannan mu godewa Allah da ya bamu zaman lfy a kasar dan zama lfy yafi zama d'an sarki, Mata musa hakuri a ranmu muke godewa mazanmu da duk abinda sukayi mana komai k'ank'antar sa, zanin sallah ba wajibi bane sai Super was ba kuma ba sai Holland ba dan super tafi k'arfin mai k'aramin k'arfi abin dubu 25 ya koma dubu 42 yayin da duk sauran zannuwan suka ninka kud'insu, shin maza suji da ciyar damu ko da burukan rayuwar mu abincin kanshi sai hamdala ba batun araha kam daga kan maggin da da d'ari 200 zuwa yanzu yaje har d'ari 400 sauran kayan masaru finma komai yayi wuta bare aje ga kayan yaran da sai dai hamdala babban gatan da Allah ya mana dai mun samu zaman lfy, dako da arahar Amman baka da konciyar hankali da zaka samu nitsuwa ana rayuwa ne cikin tsoron da firgici ga dukiyar da abin more rayuwar amman ba nitsuwar da konciyar hankalin da za'a mori arahar haka ko wanne shekara da yadda zai zoma bani 'Adam mu godewa Allah mu daina jingina tsadae da muke ciki akan wani abokin halitta kamar mu wanda bai da damar sau k'ak'awa ko tsanan tawa mukoma ga Allah mu dena al'k'anta tsadar damuke ciki akan shugaban mu Baba Buhara ba Allah bane ba kuma ba manzon Allah baneba kuma ba kumfa yakun neba shima Bawane kamar kowa baida ikon sauk'ak'awa ko tsanan tawa".
Sosai tai tamusu nasiha mai rasa jiki daga bisani tajuya gun Aysha tai ta mata Addu'a sannan ta baiwa Maryam hakuri ta kuma tasa Rukayyat a gaba tai ta mata nasiha. sannan suka fito parlon suna fita Aysha tace ita kam zata tafi aikin yamma najiran ta suna cikin haka Bashir yazo d'au kar Rukayyat ganin Aysha zata fita sai suka tafi tare ya sauk'eta a k'ofar gidan ta sannan ya juya da Rukayyat kuma ya nufi gida da ita, tun an cikin mota Bashir ido ya zuba mata ganin duk jikinta a mace ga fuskarta data nuna alamar tayi kuka gaba d'aya sai abin ya dameshi cikin kula yace. "Baby meke damun ki? ko azumin ne ke wahal dake?". jiki a mace ta tsura mai ido tana mmkin yadda Bashir ke tausaya mata Amman ita ta kasa mai uzuri a rayuwar su, shiko ganin tayi shiru yasa d'aya sauk'eta ma bai fitaba sai bin bayan ta yayi suna shiga parlon ya kalleta cikin sanyi yace. " Baki da lfy ko?" kai ta girgiza alamar a,a Ayijar zuciya ya sauk'e tare da cewa . "OK ki konta ki huta toh bari na shiga kitchen na fara mana aikin kafin su Salima su taso islamiya na d'auko su". yana kaiwa nan ya nufi kitchen ita kam sai binshi da ido tayi cikin mutuwar jiki tana son mishi mgn da Bashir hakuri da nemar yafiyar sa sai kunya ta hanata a haka har zuwa dare.
Bayan sun gama komai har Bashir ya konta itako tana gefen shi tana zaune mik'ewa yayi cikin sanyi yace. " Na manta abu a moto bari na d'auko". Har ya mik'e sai ya kuma zama jin ta rik'o hannushi cikin sanyi da kunya murya a raunane tace. "Abban Salim ka gafar ceni kamin afuwa hak'ik'a nasan na kasance mai b'atama da kalamai na masu zafi da d'aci, Hamma Bashir ina tsoron me zancewa maliccina in namutu da hak'k'in ka, ka yafe min hak'ik'a na gane kuskure na na kasa tawausaya ma bare nama uzuri".
Sai ta kuma fad'a jikinshi tare da sakin kukan nadama, cikin sanyi da jin dad'i ya tsura mata ido tare da sauk'e ajiyar zuciya yace. " Share hawayen ki matata ni dama ban rik'eki ba na yafe miki duniya da lahira Allah ya miki albarka Baby na".
Haka suka rink'a farin ciki da samun nishad'i cikin sauri Bashir ya fice yana "bari kiga wani abu"
Bayan ya dawo ne ya dire kayan hannushi kayan yaran masu kyau da tsada kala uku-uku na mata da maza sai turame 2da leshi 1 sai shadda mai kyau kala 3 sai sauran tarka cen yara su takal ma yan kunne gyale da dai sauran su cikin mmk Rukayyat ta bishi da ido, Shi kuma fuska a sake ganin ya samu lfy a gun matar tasa yace. "Ga kayan yaranki Hajia kema ga naji nima ga nawa sannan naki zaki d'inka da Salima niko zan d'inka da salim kinga d'en sun samu kala shida -shida ko?".
Kai ta sunkuyar cikin jin kunya da nadama ta fad'a gareshi gashi da batayi mgn bama da ba taji kunya a banza ba.
Haka rayuwa ta koma musu cikin wadatar zuciya da tausayawa juna da yiwa juna uzuri shi kam Bashir Allah ya Bashir ladan hakurin shi.....
Maryam ce konce tana baccin ta cikin sanyi taji Umar na Jan yatsun k'afar ta a hankali ta bud'e ido tana kallonshi shiko murmushi yayi cikin sanyi yace. " Baby tashi muyi sahur kada mu makara". ido ta lumshe tare da cewa. "Ni bacci nake ji Ya Umar kuma nagaji". da sauri ya mik'e tare da cewa bari na kawo miki abin cin nasan kin gaji kina k'ok'ari ga Ramadan ga aiyuka sun k'aru".
Abin cin ya kawo har gaban ta sannan ya had'a mata tea da kanshi ya bata. Ita kam Maryam Allah take godewa d'aya canza mata halin mijin ta.
Yusuf da Aysha ko rayuwa ta kara musu dad'i cikin fahim tar juna..
*Alhamdulillah* *Alhamdulillah* *Alhamdulillah ala kulli halin*
~Abin da nai dai-dai Allah ya had'amu kan ladan abinda nai kuskure Allahu ya gafar tamin~
Wannan d'an guntun lbrin k'agene banyi dan wasu ba duk Wanda na batawa ta/ya gafar ceni.
Ngd wannan lbrin bawai na soyeyya bane rayuwa mu ta yau na d'an duba.
Sai mun had'e a littafi na na gaba.
*masoya na ina k'aunarku a duk inda kuke Garkuwa takuce* 😍😘
By Garkuwar Fulani
Copied By YAYA HAYAT (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion Cool novel, makeup and kitchen1⃣ AND Cool novel, makeup and kitchen2⃣)
WHATSAPP NO: +2347039625239