Kenza eBookz

Abadan complete hausa novel - Chapter 12

Abadan complete hausa novel - Chapter 12

Abadan complete hausa novel Chapter 12: Abadan complete hausa novel Chapter 12. *_ubangiji madaukakin sarki yakanyi duba izuwa filin arfa,sai yace da…

3,316 words

*_ubangiji madaukakin sarki yakanyi duba izuwa filin arfa,sai yace da mala'ika jibrilu,me bayin nan nawa suke nema haka(duk da cewa shine mafi sani),sun fito cikin tsananin zafin rana da qasqantar da kai?,sai mala'ika jibrilu yace''rahamarka da gafararka,sai ubangiji yace na gafarta musu''_* *_haka ubangiji s.w.a yake rabon irin wanna garabasar a filin idi,annabi muhammad s.a.w yana cewa''kada ku hana bayin Allah mata zuwa masallaci''_* *_sannan yayi umarni da a fita sallar idi maza da mata yara da tsofaffi_* *_yake 'yar uwa,kada ki bari wanann garabasa ta wuceki wadda baki da tabbas din ganin wata kamarta,Allah yasa mu dace,ya yafe mana kurakuranmu,yasa mu cikin bayinsa da za'a gafatarwa Allahumma ameen_*

*_wannan shafin sadaukarwa ne ga dukkanin al'ummar musulmi,Allah ya karbi ibadunmu_*

ci gaba yayi da lallonta kamar yadda take kallonshi,tuni oily eyes dinta suka qara sheqi da sakamakon tsoro da qwalla da ta tarar mata,zuciyarta na raya mata mummunan abu abdallah ya yiwa abida,cikin hanzadi ta juya da nufin komawa dakinta ta banke saidai taku daya biyu ana ukun ya cafkota ya maidota baya,take jikinta ya soma bari,bakinta na rawa ta soma fadin ''don.....d....don Allah kayi haquri,ka fufamin asiri''

galala yake binta da kallo,tuni ya gano manufarta,ganin taqi nutsuwa ya sanyashi daka mata tsawa ''me zayi dake da har kike tsammanin wani abu zan miki?,koyin ma zanyi kin min kadan 'yar tsakuwa,abinda nakeso dake kada ki kuskura wani yaji abinsa kika gani?,ina fatan kin fajimceni?'' kai kawai take gyadawa babu qaqqautawa,burinta kawai ya saketa ta samu ta tsere,yana sakin nata kuwa ta shige dakin jiki na rawa ta murza key

binta yayi da kallo cikin mamkin mummunar fassarar da tayi masa tashi guda,koda ya koma daki sai yaji abun ya tsaye masa a rai,ta tuhumeshi da laifin da bai taba sha'awar aikatawa ba,hasalima ya tsani mai aikata shi,gefe guda kuma tsanar abida ce fal cikin zuciyarshi,yaci alwashin koda zata rasa rayuwarta bazai iya aurenta ba,yana da tsananin kishi ya tabbatar koa ya aureta din bazaya samu kwanciyar hankali ba

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

kusan dukkaninsu kwanan zaune sukayi babu wanda ya runtsa,kowa da abunda ke yawo cikin rai da zuciyarshi,duk da hakan maryam bata kasa tashi yadda ta saba ba ta hada breakfast,saidai babu wanda yaci,bata san da hakan ba sai da mami ta dawo ta hau sama ta kintsa kana ta sake dawowa qasa don yin karin safe,abida qunar zuciya ta hanata fitowa,abdallah yayi sammakon zuwa ofgice saboda wani taron gaggawa da zasuyo wanda shi kansa bai san da shi ba sai da asubahin ranar his excellency mr presdent ya sanar mishi,saboda haka kiegin qarfe shida yabi zuwa abuja

maryama kuwa tsoro da fargabar haduwa da abdallan ne ya hanata fitowa bayan ta samu ta kammala aikin ba tare da sun hadu ba ''shi kam abdallah ai ya jima yanzun a abuja,jeki kiramin abidar dai ta karya,ya zatayita zama bata ci komai ba'' kamar tace da mami ba zata iya zuwa ba don tana fargabar halin da zata je ta taradda abidar,bata da amsar tambayar da mami zata yi mata game da abunda zata ga ya samu abidan

ba zata iya qin zuwan ba don haka ta miqe jiki a sanyaye ta nufi dakin,sai da tayi knocking sau biyar kafin a bada izinin shiga cikin qaqqarfa kuma kausa sashiyar muryar abidar ga mamakinta sai ta tadda abidar ta fito daga wanka ras da ita,babu wasu alamu dake nuna wani mummunan abu ya faru da ita ''meye kika tsaya kikatsaya kika zuba min idanun kin nan masu zubi da na mage?'' sai a lokacin ta ankara da tsayawa tayi kallon abidar ''mami ke kiranki''tana jinta tana tambayarya ta dawo ne tayi mata banza ta wuce

da daren ranar ta sake shiga wani rudanin,a hanyarta ta dawowa daga sashen baba uwani zahariyya ta sha gabanta ,tace taje nene na kiranta

zaune take gaban nenen cikin falonta na can sama,daga ita sai nenen sai zahariyyar ''maryamu kike ko?,nasan zakiyi mamakin irin wannan kira na bazata,ba komai bane yasa na kira ki wata buqace da ni wadda nake neman taimakonki gurin cikarta,ina fata kuma zan samu hadin kanki gun cikar buri na'' ''zan iya taimaka mikin indai bai kauce addini na na ba'' wata dariya nenen ta kece da ita ''idan banda quruciya irin taki ai yanzu kowa ma ba bin qa'idar addinin yake ba,biyan buqata kawai ake nema''nene ta sake qasa da murya kana ta kuma matsowa kusa da maryam ''ba wani abu nake nema agunki illa poising da nake buqata kawai ki diga a abincin abdullahi'' a firgice ta miqe har jiri na shirin kayar da ita lokacin da nenen ta gama zayyana mata buqatarta,bari kawai jikinta yake,addu'a duk wadda tazo bakinta yi take

halin da ta shiga kawai ya ishi nene amsa ''kinga zauna ki nutsu,sai kace wadda aka ce ta diga a abincin ubanta,aikin nan fa ba a kyauta zakimin ba,biyanki zanyi kudi masu yawa da nauyi,zan dauke miki dukkan wani quncin talauci da kike ciki,zan wadata ki zan yalwataki''

hawaye ne ya shiga bin kuncinta,girgiza kai kawai take cikin takaici takaicin ha'intar managarciyar mace kamar mami takaicin cin aman ada yaudara da sukewa mamin takaicin son dasa baqincikin da qunci na har abada da mutanen keson dasawa a zuciyar mamin wannan cin amana da me tayi kama?,haka mutanen duniya suke

''bazan iya ba,bazan iya cin amanar mami ba ko duniua da abunda yake cikinta zaki bani''abunda ta iya fada kenan ta juya a guje zata bar sashen ''ke,dakata''mamin ta tsaidata,har ta iso gabanta ta kasa motsawa,cikin huci take dubanta ''rashin karbar tayi na yarinya daidai yake da tangal tangal da rayuwarki,arziqi na binki tsiya ta hanaki ki ganewa,kije....ko babu ke sai na cika burina,hanyoyin nada yawa,amma ki tabbata rayuwarki na cikin hadari,kuma wallahil azeem kika bari maganar nan ta fita sai na batar dake''

a sukwane ta bar sashen,da qyar ta kai kanta dakinta cikin mawuyacin hali,fadar irin halin data tsinci kanta bata baki ne tabbas ta kuma gasgata cewa nene na iya aiwatar da duk abinda ta fada din,ta gani,cikin qwayar idonta mafita daya take hangowa a gareta shine ta nemi miji tayi aure,ba zata iya kallon qwayar idanun mami ba tace tabar aiki,wata fuskar tafi gaban mari,aure shine zai rabasu salin alin

*_dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki_*

*_ina taya daukacin al'ummar annabi murnar zagayowar babbar sallah da fatan za'a gudanar da bukukuwan sallah lafiya_*

*_insha Allahu daga yau zamu je hutun sallah,littafin abadan zaici gaba da izinin Allah bayan qare hidindimun sallah_*

*_subhanakallahumma wabi hamdika,ashhadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa'a tubu ilaika_*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻 [17/09, 12:47] Frd Group Yareema: 💖💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺🌺 🌺💖🌺💖🌺 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 🌺💖 💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 *WRITTEN BY* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖 💖🌺💖🌺 🌺💖🌺 🌺💖 🌺 ▶2⃣8⃣

*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*💡

*_wannan page din naku ne,wato mata iyayen gida,ku huce gajiyar sallah,Allah ya qara mana himma da lafiya,ya bamu ladan kula da iyali_*

material ne a jikinta mai baqi da fari,skert din baqine sol babu digon komai,rigar kuma fara ce mai adon baqaqen fulawoyi,irin dinkin nan ne da muke kira three quater iya gwiwa,skert din simple ne mai tsaga a baya,baqin mayafi ne tayi rolling da shi sai farin plate shoes mai igiya data sanya

a kasalance take nunawa ma'aikatan irin kayan da suke so su kuma suna cirowa suna sanyawa cikin keken tura kayan,qarfin hali kawai take,batason nunawa mami wani abun na damunta,duk da tana jin kamar zazzabi na shirin kamata

sannu a hankali suka qurewa bangarwn electronics dake cikin makeken shagon zamanin nan na shoprite dake ado bayero mall,suka juya bangaren warmers da plates cups da sauransu,daya bayan daya take bi tana zaban sababbin design

''subhanallah''suka fadi a kusan tare suka kuma ja da baya,tuni cups din da ta dauko sukayi nasu guri a qasa sakamakon karon da sukayi,a tare suka duqa suka soma kwashewa

''kiyi haquri madam don Allah ban kula bane''ya fada yana miqa mata guda ukun da yayi nasarar kwashewa,sai a lokacin ta dubeshi,baqi ne ba can ba zaka iya kiranshi da chaculet,dogo ne maras qiba,ya mata kama sosai da mutanen qasar habasha ko kuma baqaqen fulani ''ba komai'' ta fada tana amsar kofunan,kana ta rabeshi ta wuce

''ko am min izini na taya madam din zabar kayan duk da ba bangare na bane?''taji an fada daga bayanta,da sauri ta waigo mutumin dazun ne,tamkar tace a'a sai kuma taga babu buqatar ta fadi hakan ''bismillah''tace da shi cikin hikima da dabara yake bayyana mata ko shi waye

''ni sunana abdur rahim tasi'u alhasan,ina zaune a unguwar qoqi dake tsakiyan birnin,ni dan kasuwa ne kamar yadda mahaifina yake,ina fata kin gamsu da dan taqaitaccen bayanin da na miki''ya qarashe magana lokacin da yake tura kwandon yana kuma kallon fuskarta dan qaramin murmushi ne ya subuce mata ''to ni kuma meye nawa da sanin kai waye,daga taya ni siyayya?''

murmushin shima yayi bayan ya tsaida basket din ''ke kuwa kike da ruwa,saboda ina sa ran zamowarki uwar gida na,bazan boye miki ba tunda na ganki naji kin kwanta min,da gaske nake sonki *maryam*aurenki kuma nake so inyi anan kusa'' a mamakance take kallonshi,to ko addu'ar da ta kwana yi jiya ne Allah ya amshi roqonta?,babu shakka Alkah maji roqon bayinshi a kurkusa ko a nesa ''yaya akayi kasan sunana,bayan a iya sanina ban gaya maka ba baka kuma ji wani ya ambata ba?'' murmushi ya sakeyi ''maso dan tsuntsu shike binsq da jifa,sonki nake bada wasa ba hakan yasa nasan komai game dake kafin na iso gareki''

cikin wani mamakin ta kuma dubanshi ''kana nufin ba yau ka fara sani na ba?'' ya dage girarsa sama ''eh,kusan haka dinne''cike da mamakin shigowar abdur rahim cikin rayuwarta lokaci guda suka kammala dukkan siyayyrsu ita da abokan tafiyar tata,har lokacin abdur rahim din na biye da su hqr suka kammala,a bakin motarsu ya dubeta ''yaushe zanzo mu tattuna a nutse''ya tambayeta yana murmushi,dan jim tayi tana tunani a lokacin taji wayarta na ringin,da sauri ta cirota,ta duba,atsammaninta hindatu ce don tace zasuyi waya sai kuma taga baquwar number ''ga number dina nan kiyi serving zan kiraki naji lokacin da zanzo din''

da mamakin karona uku ta sake dubanshi,mamakin ina ya samu num dinta,kamar yasan me take tunani yace ''nasan mamkin inda na sami number dinki nake ko,kada ki manta na gaya miki dazu,na shigo sonki ne bada wasa ba hakan ya sanyani sanin komai game da ke tun kafin na iso gareki''murmushi ta sakar masa,sai taji abdur rahim din ya burgeta karo na farko,wannan wane irin so ne haka?

ko cikin motarma tunani abdur rahim din ta fada,tana gaya wa kanta ta samu mijin aure tabbas,tana kuma qarfafawa kanta gwiwar wannan karon zata shiga dakin aure kamar kowacce mace

bayan mami ta gama ganin kayan ta yaba sosai,don tace basu taba siyan kaya new fashioned and durable haka ba kamar wannan shekarar,kai tsaye dakinta ta wuce don tayi sallar la'asar su fara rage koda gyaran kitchen ne tunda taga da time,biyu daga cikin daki hudun dake rufe ta sake gani a bude,bata ce komai ba don ga tsammaninta baqi mamin ta sakeyi

da taimakon ma'aikatan harda baaba uwani cikin qanqanin lokaci suka fidda tsoffin kayan kitchen din suka fara shirya sababbi,aiki na yiwa maryam dadi sakamakon yadda yake tqfiya cikin tsari,sunayi kuna suna hiransu abinsu,kada ma baaba uwani taji labari,akwai abun dariya ''lamarinku na yaran zamani na bani mamaki''baba uwani ke fadawa maryam qasa qasa ''me mukayi baaba uwani?''maryam ta tambayeta tana fiddo da wani foodflask daga cikin kwalinshi ''mata su dinga biyo maza gida suna neman aurensu?'' ''kamar yaya baaba?'' ''hmmm,yaran nan mana dake son yaron gurin hajiya abdullahi,dazu daya yarinyar nan itama tazo da kayanta na satittika,ummm.......salamatu,mu a da ba sai an kaiki daki ba ma kike sanin waye mijin?,idan ma kuwa har kinsan waye shi din kafin a daura aurenku to ko hanyar da yabi baki iya bi saboda kunya,idan kuwa tsautsayi ysda kuka hada hanya to sai kinkusa qamewa a tsaye vaki iya motsi har sai ya wuce''

dariya ce ta kubcewa maryam ''baaba kin iya bata suna,salma ake cewa ba salamatu ba'' ''kome me take ne barta,abun nasu sai addu'a,ko kunyar hajiya basa ji,ko fada ne ya kama yi suke a gabanta,abunda mu ko abinci baka iya ci gaban suruka,wannan zamani wannan zamani yazo qarshe,fatan Allah yasa mu gama lafiya'' ''ameen''maryam din ta amsa mata da shi,daga haka bata ce komai ba,ita kanta mamaki take,saidai babu ruwanta don bata shiga shirgin da ba nata ba

ana kiran sallar magariba suka kammala aikin duk girman kitchen din yayi kyau ya sake haske,lallai sabon abu akwai kyau inji baaba uwani,ita kanta mamin ba qaramin mamaki tayi ba,ta sallami sauran ma'aikatan tana yabawa qoqarinsu

dakinta ta kuma komawa sanda tafito daga kitchen din abida ce zaune gaban makekiyar t.v plasma tana kallo sanye da matsattsun riga da wando,kusan duka shigarta kenan ta fidda tiraici ko doguwar riga zata sanya sai ta samu mai tighting jiki,wanka tayi ta sauya kayan jikinta,ta daura alwala tayi sallah,tana saman dadsuma tana lazumi ta tuna zata kira fa hindatu,ta laluba wayar bata jita ba hakan ya bata tabbacin ta manto ta a kitchen,ta gyara zaman ijabin jikinta ta fice ta nufi kitchen

su uku ta tadda yanzu a falon abida salma da abdallah da suka saka atsakiya,kallo daya zaka musu ka tabbatar daga abidan har salman ba jin dadin zaman suke ba,shi kuwa hakimin na tsakiya zaune yana ta aikin amsa waya,bisa dukan alamu wani aiki yake shiryawa don taji bada order din yayi yawa cikin fada da fushi

ilai kuwa cikin sabuwan kitchen wear din ta ganta,missed call goma ta taras,hudu na hindatu hudu na abdur rahim daya na raliya,murmushi tayi don dama ta sani bata da masu kiran nata sai su,sai ta rasa wanda zata soma kira a cikinsun,cikin haka kiran mami ya shigo ''kina ina ne maryamu,na shiga dakinki ban tadda ki ba'' ''mami ina kitchen'' ''baki gajiya ne maryam aiki sai kace inji,already baaba uwani tayi abinci ki huta haka nan don Allah'' tana jin dadin qaunar da mami ke nuna mata qwarai da gaske ''wayata na manta ma nazo in dauka'' ''ok,ki sameni a parlour na'' ''to''ta amsa mata ta cire wayar daga kunnenta ta fita daga kitchin din

''ke mero''taji an fada lokacin da take qoqarin hawa matattakalar benan kamar kada ta juyo sai kuma ta waiwayo din don ganin mai mata kiran,abida ce ''meye kika tsatstsareni da idanuwankin nan kamar na?,shawarma nake sonci,ki shiga kitchen yanzun kimin idan kin iya'' rausayar da kai maryam tayi ''batun iyawa na dade da wuce babinshi,saidai lokacin aiki ya qare,zaki iya barwa gobw idan Allah ya kaimu,tunda majority utensils din duka sabbi ne bamu bude su ba''

cikin izza isa da gadara tace ''ke,wai mai kike taqama da shi ne,ki fadi nawa ne albashinki duka a nunka miki bama iya kudin aikin yau ba,ban mance ba rannan haka kika mana wani abu tuwo sunanshi ko me?nace kimin wani kalar girkin kika ban banzan answear irin wannan,kinsan wace ni kuwa?''

sakin makarin silver din da maryam din ta riqe tayi ta juyo ga abidan sosai ''ni ba kowa bace kuma bana taqama da kowa face Allah,kudi kuma ba zaki bani yanke talauci ba har abada,matsayin da Allah ya ajjiyeni ya gamsar da ni sosai na kuma gode masa,gaskiyata na fada tsarin siki na kenan cikin gidan nan,baquwa ce ke ina zato shi yssa kike mantawa,sannan ke din ma ba kowa bace face baiwar ubangiji kamar yadda nike kowa kuma yake''

a hankali abdallah ya dago kanshi daga kallon wrestling a tashar mbc action da yake ya dubeta,sai yaji amsarta ta burgeshi,babu hayaniya cikin raddinta,cikin calmnesses and cool voice,sai ya dan tsaida abunda yake yaga yadda za'a qare tuni fuskar abida ta canza,cikin bacin rai ta dubi abdallah ''mu sugar kana gani da jin abunda yarinyar nan ke gaya min ko''ta fadatana nuna maryam wadda tuni har ta kusa kaiwa qarshen benan

murmushi ya saki mai hade da yar dariya ''duk bakery din dake garin kano kin raina,kin rasa inda zaki ci shawarma ne?'' ''zaka iya kaini ne?' ''a lissafin lukuta na babu wannan,idan kina so akwai direbobi sai wani daga ciki ya kaiki ya dauko''sai ta sake tunzura,ya yrfata gaban salma kenan?,abunda madyam din ta mata ya hadu da wanda abdallah ya mata ya zamar mata zafi biyu a zafafe ta miqe tana cewa ''tunda kai bazaka iya daukan matakin komai ba to ni zan daukarwa kaina,bazan zauna talaka 'yar talaka wulaqantacciya ta dinga taba mutuncina ba''

wani murmushin ya kuma saki ya kima kashingida ''eh kuma fa,gaskiyarki nima na goyi bayanki,kamarki diyar ambassador guda bai kamata a dinga samun iein haka ba,jeki dauki mataki'' sai ya kuma tunzurata don ta fuskanci kamar gatse yake mata ko kuma jirwaye mai kamar wanka,a haukace ta haye saman

kujera ta samu ta zauna tana fadin ''gani mami'' ''yauwa maryam....cewa nayi''maganar mamin ta katse sakamon kiran da ya shigo wayar maryam din,screen din ta duba,sunan abdur rahim ya bayyana,sai ta maidata silent taqi dagawa ''ki daga mana maryamu''inji mami murmushi tayi ta dan sadda kanta ''um um mami,ina jinki'' cikin murmushin da salon zolaya tace ''kodai suruki na ne maryam?''

sai kunya duk ta kamata tayi qasa da kanta tana murmushi ,ganin tayi shiru yasa mami cewa ''Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa,shawarata gareki ki riqe mutuncinki,ka kame kanki,mutuncin mace kunya da kamun kai,duk da nasan duka halayenki ne,idan na samu lokaci zan miki magana yazo inganshi mu gaisa''cikin jin dadi da gamsuwa da maganganun mamin take gyada kai,sai ta kuma tsokanarta ''bari nayi sauri na sallameki kada surukin nawa ya qosa da jirankin ko''sai ta sake bawa maryam din kunya

''kaya ne wadanda aka fitar da kayan firniture da za'a fitar gobe nake son ki zazzabi dukka abunda kike so ki kaiwa mamnki ko zatayi amfani da wasu wadanda bata so ta bada'' tayi mamakin yadda mamin ta bada kayqn,don kaya ne da babu abunda aukayi tamkar yau aka zuba su espicially kayan furniture din,ta wani fannin kuma ba abun mamaki bane saboda halayen mamin ne *karamci* da *kyauta* sabanin wasu masu hannu da shunin da sun gwammace su saida kayan maimakon 'yan uwanau su amfana furniture ne ko kayan sawa,ko me zasuyi da kudin oho,bayan Allah ya wadata su ya basu arziqin amma suna maida kansu baya

''na gode mami qwarai,Allah ya qara girma'' murmushi mamin tayi ''bakin maryamu ya saba da godiya,nasha fadi miki ba haka tsakani na da ke'' kafin tace wani abu an banko qofar an shigo,abida ce kanta tsaye ta tafi gurin mami ''mami,ki shiga tsakanina da house girl din nan,hala bata san koni wace ba,ta raina ni matuqa,wallahi idan bata kama kanta ba zanyi sanadiyyar qulle danginta kaf babu wanda ya isa ya fito da su,batasan ba'a raina ni ba,bana daukar raini?'' kama kai mami tayi tana kallon abida ''qara kika kawomin ko mataki kika zo dauka?''cikin rashin iya magana tace ''duka mami'' ta riga da tasan abida rainon tabara ce,ta san ita har zuciyarta magana ta fada mai kyau,ta bar ta tata ta juya ga maryam ta tambayeta mai ya faru,a nutse ta gaya mata ''tashi kije maryam,sai da safe Allah ya bamu alkahairi'' ''ameen mami''ta fada tana ficewa,yunqurowa abida tayi gurin maryam mami ta dakatar da ita

mamaki ne ya ishi maryam,tana shiga daki kiran abdur rahim ya shigo wayarta,murmushi ta saki ta isa gefan gadonta ta zauna sannan ta daga

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻 [17/09, 12:48] Frd Group Yareema: 💖💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺🌺 🌺💖🌺💖🌺 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 🌺💖 💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 *WRITTEN BY* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖 💖🌺💖🌺 🌺💖🌺 🌺💖 🌺 ▶2⃣9⃣

*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*💡 *_home of expert and perfect writers_*

Kimanin awanni biyu suka shafe kan layi ita da abdur rahim din,ta fuskanci ya dan san wasu abubuwa game da ita wanda hakan ke qara mata amanna da qaunar da yake iqirarin yana mata din,tuni ta yanke ma ranta abdur rahim na daya daga cikin batutuwan da zasu tattauna a gobe ita da mamanta,bai barta ba har sai da ya fuskanci ta soma jin bacci tukunna ya mata sallama cike da qauna da bege mai yawa

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

Readers Also Read

More by Ayshacool 1