Abadan complete hausa novel - Chapter 29
Abadan complete hausa novel Chapter 29: Abadan complete hausa novel Chapter 29. kan mero ta bude idonta har maryam ta taashi ta kama wheelchair din tayi…
3,372 words
kan mero ta bude idonta har maryam ta taashi ta kama wheelchair din tayi hanyar fita da shi,sai data bude idon nata raga dakin wayam har sun fice,jiki ba qwari jtama ta fice a dakin inna wuro bata a tsakar gidan don haka tayi maza ta tura suka shige bayan gidan ''take it easy mana madam,kada ki fadar da bawan Allah''inji abdallah cike da dariyar mugunta da yake qunsheta tana tsaye ya soma cire kayanshi ta dauke kanta qirjinta na lugude,saura gajeran wandon daya rage wanda yake bari a jikinsa idan zaiyi wanka,gaba daya ta rude don bata yarda taga jikinshi har kamar haka,hatta da cinyoyinshi dake cike da gargasa sun fito,ganin yana niyyar fidda shi shima yasa ta qarasa rudewar gaba daya,batasan ta dafe hannunshi ba ''ayya mana abdallah ba kyau fa don Allah''ta fada cikin son fashewa da kuka dariya sosai ta kamshi amma ya hade rai yayi kicin kicin ''to me naki,dazun fa adaki kika gayan babu ruwan wani da wani,kema me ruwanki da ni ko na cire din,ba wanka zaki tayani ba?,kimin wankanki kawai ki maida ni daki,wai haka ma ake jinyar mutum?,oh ni abdallah sam baki iya jinya ba''ba bakin maida amsa girgiza kai tayi yaci gaba da kiciniyarshi,a guje ta kwasa ta fice a bayin dariyar da yake boyewa tilas ta fito,mamaki take bashi tamkar cikin qauyen aka haifeta ko kuma shi din ba mijinta bane,kunyarta ta mata yawa ta maida shi kamar wani dodo,Allah yasa komai na wanka na gabanshi don haka ya qyaleta yayi abunshi tunda hannunshi na kaiwa.
sai da ya kammala ya bubbuga qofan bandakin tazo ta fidda shi,tana ta rarraba ido kamar wadda ta yiwa sarki qarya ta shigo idanunta a qasa taqi yarda su hada idanu,itakam rashin kunyar shi ta fara isarta,daga warkewarsa jiya zuwa yau ya addabeta gaba daya ya hanata sukuni,ina dalili,yana abu kamar su biyu ne kadai cikin gidan.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
[5:23pm, 9/26/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺 💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖🌺💖🌺 💖🌺💖 🌺💖 💖
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 🌺💖🌺💖🌺💖 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 💖🌺 💖 © *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *_home of expert and perfect writers_*
4⃣8⃣
*_cikin kudubobin annabi Muhammad S A W yana cewa:yaku taron mata ku yi saddaqa saboda naga yawancinku cikin wuta''sai suka tambayi annabi saboda me?,sai Manzon Allag S A W yace ''domin kuna yawaita yin zagi da kafurcewa/butulcewa zaman tare(rashin godiya ga miji)anas dan maalik R A sai yace take sai suka dinga ciro dan kunnayensu da abun hannunsu suna jefawa sadaka_*
Cikin motar suka,zauna duka su ukun suna jiran tsammanin dawowar dan aiken nasu,kowannansu cike yake da fata da buri,minti takwas dan tsamurmurin saurayin busashshe wanda wiwi da sholi ta tsotseshi ya dawo cikin motar ya zauna kusa da adnan da yake zaune a mazaunin driver,cikin ciccijewa da magana irin ta 'yan daba yace ''wallahi hajjaju gidan nan fa babu kowa,na tambayi mai gadin maqotansu yace tun jiya da rana suka kulle gidan sunyi tafiya'' ''na shiga uku ni nene,Allah ya isa tsakanin na da hisham ka shiga tsakani na da cikar burina''ta fada cikin tashin hankali don tunaninta kawai yadda zata biya kudaden aikin data saka ayi mata,millin biyu ina zata sameta,kusan duka kudden hannun nata ba zaau haura million biyun ba don rabi sun tafi gun malam na hayi,bata damu ba don tana ganin da zarar aiki yayi kyau sun kashe abdallah zata maida ninkin duk wani abu data rasa ''hmmmm''zahariyya ta fada tana dauke kanta gefe zuciyarta cike da baqinciki da takaici,abu qwaya daya yaqi ci yaqi cinyewa sai kace cin qwan makauniya,adnan kuwa sitiyarin motar ya daka yana fada ''oh my godness''.
shiru ne ya ratsa motar,saurayin ya dubo ya kalli nene ''hajiya sallameni kawai ni daga nan akwai inda zanyi tunda aikin abi yiwu ba''ta dubeshi kamar ta qunduma masa ashar sai kima ta tina uadda sukayi da jama'arta na baya kada shima wannan ya shemesu ga adnan ba wani qarfin arziqi gareshi ba ballantana tace zai cecesu,duk da sirantakar saurayin ta tqbbatar daba ta ratsa shi zai iya illatasu yayi nasa guri,wato su ba ruwansu duk lokacin da ka daukesu hayar aiki aikin ya yiwu bai yiwu ba duk matsalarka ce sai ka biya haka nan tana ji tana gani ta fidda dubu dari uku ta danqa masa ya fice a motar babu ko sallama,ta bishi da harara idonta kamar zai gado sai da taga ya gusa daga inda yake ta samu bakin yin magana ''shege tsinannen yaro...'' ''kada ki tsine masa aiki kkka daukoshi kuma dole a biyashi,koma mene ai duk ke kika jawowa mutane,sai azabar cika baki amma har yau gaahi nan wankin hula na shirin kaimu dare.....kai ya riga ma da ya kaimu din,nayi mamakinki wlh kamar ba nene ba duk cika bakinki da iya kutungwila.......''.
Bata kai ga qarashe zancen ba nenen ta kawowa bakinta bugu,saidai tuni ta riqe hannun ''akan me zaki huce a kaina,ba gaskiya na fada ba,idan zaki iya ki aikata mana mu gani,mun gaji da gafara sa bamu ga qaho ba,dukiya nake buqata mai tarin uawa da zanji dadin rayuwata,dukka qawayena babu wanda ya kaini talauci,mtswee''ta ja tsaki kana ta saki hannun nenen tana shirin,bude murfin motar ta fice,riqeta nenen tayi da sauri tana fadin ''ina zaki zahariyya kuma''juyowa tayi ta harari nenen tana fadin ''cikani naje na samawa kaina mafita'' ''kiyi haquri ka tsaya mana zahariyya,in sha Allahu burinmu sai ya cika dukkanmu''ta fada cikin kwantar da murya.
Dan jim tayi kamar bazata dawo din ba,kana daga bisani ta ja qwafa ta dawo cikin motar ta rufe,wayarta nenen ta ciro ta nemo lambar malam na hayi,cikin sakanni ya daga,ba wata gaisawa suka yi ba ta fara masa batun abdallah tiryan tiryan bai katse ta ba har ta qare sannan ya saki dariya ''ai na gaya miki habiba,koda aikinku zaiyi yasiri kan yaron nan ma tasirin ba mai yawa bane dalilin yarinyar da suke tare,bata wasa da addu'a ta bata muhimmanci a rayuwarta,haka abun a jininsu yake tun kakannin kakanni suna da dafa'i a ajikinsu,sabida haka ni bansan me zan muku ba don duk cikin ma'aikatanmu babu mai iya kisan yaron balle yarinyar'' ta marairaice murya kamar zata duqa masa duk da baya ganinta ''dob Allah malam ka taimaka mana,ko me kakeso wallahi zan maka zan baka shi,aikinka ne nasan zaka iya don Allah malam''yayi ahiru cikin zuciyarshi yana dariyar jin dadi,domin hanyar cikar burinshi tazo masa a sauqaqe kenan,ya riga ya sani sam babu nasararsu kansu abdallah amma zai iya damfararsu ai yaci kudinsu ya kuma qaru da su.
Ya sake dake muryarsa kamar gaske harda hadawa da gyaran murya ''shikenan,yanzu abinda za'ayi,akwai wani babba cikinaljanunmu yaga yarinyar gurinki zahariyya yana so,to kasancewar babu aure tsakanin jinsinmu da nasu ya sa na gaya masa ya haqura kawai,kuma ikin da kuke so a yi muku yanzu babu wanda zai iya shi sai shi,sabida haka indai za'a aura masa ita na tabbatar zai muku aikin kyauta ma ba sai kun biya ba a matsayin shine sadakinta''ba zahariyya da ake maganarta ba hatta da hajiya nene sai data girgirza,bakinta na rawa tace ''mal....malam....ta yaya za'ayi zahariyya ta auri aljani malam ina aka taba haka?'' dakiya ya sake sawa cikin muryarshi don kada su kawo masa wargi ''kada ki damu habiba anayi sosai ma,ko cikin masu zuwa gurinmu mutum nawa aka yiwa,yadda abun yake shine aljanin yana zama ajikina ne yana amfani da ni amma a badini shine bani bane kin fahimta?''.
ajiyar zuciya suka saki su duka biyun suna jin abun yazo da sauqi,don ua qara kwantar musu da hankali game da lamarib sai ya karkace yana gyara wasansa ''hajiya ina zaton da kunsan irin dumbin dukiyar da zaku mallaka bayan kun kashe yaron nan ina zato ko tsirara ma nace ku dinga yawo ba zaku musa ba,na buga qasa qasa ta gayamin cewa kuna daf da zama miloniyoyin da za'a dinga kwatancansu cikin fadin duniya,mugayen kudade ne suke dab da zama mallakinku idan har kuka yi biyayya kan duka umarnin da zan ahimfida muku,musamman ita zahariyyar ba qaramin qaahin arziqi ne da ita ba,da buqata ta biya aljanin zai saketa tunda shima tasa buqatar ta biya taje ragi rayuwarta yadda take so bayan ya mallaka mata wasu dunqulallun zinare da yayi alqwarin zai bata duk randa zasu rabu din don shi dama auri saki ne da shi''.
Hatta adnan dake gaban mota yaba zuqar sigari saboda bacin rai sai da ya wurgar da ita kana ya waiwayo jin albishir din 'yan neho da malam na hayi ya musu,hatta shi kansa da yake namiji ya gasgata zancan dari bisa dari,nene ta zaro ido kana tace ''amma malam da kasan da wannan hanyar ka barmu muna ta shan wuya'' ''eh to,kinsan ku bamu da tukarawa ko azarbabi kan coatumer dinmu,don wani lokacin kana son taimaka musu suna ganin kamar cutarsu kake yi shi ya sanya'' nan suka taqarqare suna ta zabgawa malam godiya tare da tambayarsa lokacin da za'a gudanar da aikin,yace su bari sai nan da sati guda zai sanar da aljanin zaiyi wasu shirye da gyare gyare don cikin gidan malam din zai tare.
cike da murna da farinciki suka rabu a wayar,sgewa suke tati harda tafawa,adnan ya dubi nene ''amma nene akwai maysala qwaya daya fa,mutumin nan gizago da mutanensa,miliyon biyinsu fa jibi zaizo,wallahi nene bashi da mutunci baiqi ya kashemu ba baki dayanmu ya taqaita mana jin dadin da muke sa ran samuwarahi,nan da lokaci qanqani'',cikin ko in kula tace ''rabu da tsinanne,malam zansa ya masa aikin da zai mance ma da batun baki daya,yanzun ma mantawa nayi ban gaya masa ba,amma babu damuwa gove yace zai kira ni da kansa sai na gaya masa'' da haka adnan ya ja motar suka bar layin zuciyar kowa fes cike kuma da qiyasi da kasafta me zai gudanar da kudadensa idan suka ahigo hannunsa,kowa kallon kansa yake a matsayin miloniya kada ma zahariyyan taji labari,don har ta fara lissafin wadanda zata ci uwarsu ciki harda dangin mahaifibta da nene ta cusa musu tsanarsu.
🍃🍂🍃🍂🍃🍂
Kamar kowanne yammaci yau ma tafe suke zuwa bakin qoramar malam dogo dake bayan garin na ni'ima,maryam ke tura keken mero na gefansu tana bawa abdallah labaran qauyan na su dama maqwaftansu,maryam jin zuciyarta take kamar ana gobara,qoqarin qaryata kanta take game da lamarin saidai ta kasa,so take ta cire damuwa game da mero da abdallah amma ta gaza,ci kanka bata ce muau cikin hirarsu,yau kam kusan tafi ko yaushe quluwa ganin yadda abdallah ke bada hankalinsa kan hirar meron harda hada mata da tambayoyi.
sannu a hankali suka isa inda suka saba zama,ta tsaida kemen kana ta gangara bakin qoramar kamar yadda ta saba ta zauna kana ta zira qafafunta ciki,yauma tana jiyo hirarsu da meron sama sama,idanunta na kan shanun dake tsallaken kogin wadanda duk zuwa anan suke tadda su,haka kawai taji tana sha'awar zuwa gurin su bata madarar shanun ta sha sakamakon amfaninta da ta gani jiya cikin research din da tayi kan wayarta,a nutse ta miqe ta gyara rufin mayafin abayar dake jikinta,ta janyo baqaqen takalmanta dake gefe ta zura cikin nutsuwa ta kewaye ruwan ta,nufi inda sganun suke ta kiwonsu.
da ido abdallah ya bita,yadda take kebewa ita kadai gaban ruwan haka kullum hankalinshi,na kanta har su dawo gidan,yau din ma hakqne,kunnensa na jin mairo dake ta zuba labari yayin da idonsa zuciyarsa dama tunaninshi baki daya na ga maryam.
sallama tayi bayan ta isa inda dabbobin da masu kiwonau suke,daga baya baya ta tsaya sabida taoron shiga cikin shanun da takeyi,daya daga cikin fulanin wanda yaro ne baifi shekaru goma sha biyar ba ya amsa mata yana kallonta ''sannunka'' ''yauwa shannunka kado''ua amsa mata cikin gurbatacciyar hausarshi,kafin ta sake cewa komai wani ya sake qarasowa saidai yafi wancan shekaru,don a qalla wannan din zai kai shekqaru arba'in da takwas,a mutunce ta gaidaahi shima cikin sakin fuska ya amsa mata yana fadin ta qarso ciki mana,girgiza kai tayi tana murmushi tace tsoro takeji,dukkansu dadiya suka yi mata suna fadin babu abin tsoro ai basa komai.
mutanen suna da kirki tamkar sun saba suka dan dinga hira tana tambayarsu wasu abubuwan game da shanun suna amsa mata cikin mutunci da karamci,ganin shanun nada yawa yasa ta tambayesu ''ku biyu kuke kula da shanun nan ne gaba daya baffa?'' ''a'ah yaro ai bamu iyawa,akwai wasu su uku suna cikin rumfarshan suna magana da maigidanmu wanda duka shanun nasa ne'' ''ayyah Allah ya taimaka...baffa ku zaku sanmin nonon shanun insha''dariya ya danyi ''me zaya hana yaro,amma zamu tambaya miki maigida tukunna kafin mu baki tunda yau yazo ko?,kai jauro kula da su kada suyi wani guri,haa in shiga in tamabaya mata''ya fada yana kada 'yar sandarsa,tabi,baffan da ido tana yaba karamcinsu har ya shige wani daki,na bukka da akayi wa roofing na bunu.
babu dadewa ya fito ''yace mu bayar,bori na tatso miki,Allah yasa dai zaka iya sha naga kaima kamar mutumin maraya ne ko''ya fada yana ciro wata yar abq dagq damararsa mai kama da qaramin akushi harda murfinsa saidai murfin maqale yake a jiki,murmushi tayi ''zan iya sha mana baffa,tana da amfani fa ajikinmu'' ''sosai kuwa yaro,naga kuna rainata ne shi ya sonya''ya fada yana tatso madarar jikin wata saniya mai shayarwa ta dinga kallinsa cike da sha'awar yadda ya gwanance gun iya tatsar sai da ya kammala kana ya juyo da abun ya nufota yana fadin ''to gashi'' hannu tasa ta karba taba fadin ''to na gode baffa'' ''mai gida zaka godewa don tace idan aka zo karba mu daina hanawa,gatacan ma ta hito,sai kayi mata godiya''.
Da murmushi ta waiga,ga zatonta zata ga mace a yadda baffa keta bashi lafazin mace sai taga ashe namiji ne,matashi ne wanda a qalla zaiyi kusan sa'an abdallah,sanye yake da yadin kufta blue black a jikinshi da aka yiwa dinkin hannu,fari ne shima wanda kallo daya zaka yi masa ka tabbatar bafulatani ne,idanu suka hada bayan ya iso gurin yana fadin ''babu dai wata matsala baffa zan wuce cikin gari'' ''babu mai gida ahmadu,saidai mairama da zata maka godiya wadda aka bawa madarar sanu'' ya waigo ya kalleta sannan ya sakar mata murmushi itama nurmushin tayi kana tace ''na gode fa,Allah ya qarq arziqi'' ''a'a babu damuwa ai''ya sake kallin baffa ''zan tafi baffa,ina zaton sai jibi zan sake shigowa mu qarasa duba dabbobin ko?'' ''to hai mun tawo'' juyawa yayi ya sake kallon maryam ''cikin gari zaki shiga ne mu fita tare?''kai ta girgiza tana diban ysallaken kogin ko zata ga su abdallah,bata samu damar ganin nasu ba saboda yana zaune kuma yawan dabbobin ya raba tsakaninsu ''eh ciki zan shiga'' ''to muje na saukeki hanya tunda amota nake''dariya ma ya bata tace ''nan da cikin garin ne sai mutum ya shiga mota,a'a na gode,baya ga haka ma bani kadai bace,ni da yaya na ne'' murmushin shima ya sake yi ''bazaki shiga bane kawai ba sai kince min ke da yayanki bane,any way shikenan,ni sunan na ahmad,nan garin iyayena ne duk da,basu zaune ciki ina zuwa lokaci lokaci ina duba dabbobinmu da gidab gonarmu dake nan garin,ina sauka ne gidan kakanni na gidan malam labaran mai kanwa wanda shi ya haifi mahaifiya ta''kai ta jinjina tamkar taso taji sunan bakin inna wuro.
''ke kuma maryam ko naji baffa yace mairamu?,ina kika zo ke kuma?'' a qagauce tace masa ''ni ma gidan kakanni na ne,zan wuce yamma tayi sosai sai anjima'' ''ok,ki,gaida gida''ya fada yana binta da kallo daga bisani shima ya shige motarshi yana waiwayenta har suka bacewa juna.
Sabanin dazun yanzu shiru ta taddasu ahi da mero din,kallo ya bita da shi,har ta iso inda suke,hakanan yake jin bacin rai na mamaye zuciyarsa,bata cewa kowa komai ba ta kama habdle din wheelchair din ta fara tura abdallahn.
ganin sauyawar yanayin abdallah yasa nero haqura da tarin hirarrakinta,ita kam ba qaramin dadi takeji ba idan suna tare tana masa hira irin haka,tamkar kurame haka suka qarasa gida,har inna wuro na tambayar lafiyau yau bata ji karadinsu ba sai shigowarsu,dauke kai maryam tayi tana daukar buta ''nima ban san musu ba inna,nima haka na taddasu,saidai ki tambayi ita gwanar ko?''banbwarakwai meron taji ita kanta bata lura da yadda take zaqewa abdallahn gaban matarshi,tana mamakin ma yadda maryam din ke rabuwa da su tamkar bata damu ba,duk da tana ganin sauyi qarara kan fuskarta,amma batayi zatoba bun da sauqi haka ba,don tana ganin yadda mata da 'yan matan garinsu ke gwabza kishi da ruguntsumin fada kan saurayi balle uwa uba miji.
Alwala ta yima abdallah ba tare da ta ko dubeshi ba duk da tana jin idanunshi a akanta yake,tana qoqarin sake zuba wani ruwan tayi alwala taji shi qasa qasa yana fadin ''bani butar''da mamaki ta kalleshi sai kuma ta dauke kai ba tare da tace komai ba ta qarasa kusa da shi ta miqa masa butar,yasa hannu ya karba yana kallonta qasa qasa yace ''tun shekaran jiya kiba daura min alwala tana karyewa,bazan juri ki dinga min alwala ba maryam karyewa take,zan dinga yin abata da kaina'' kunya tsoro da miskilanci suka hade mata,tun jiyan take ganin sauyi cikin idanunshi,shi yasa ko katifarsu ta daina kwanciya kai,tunda yana da baki yanzun zai iya tada ta idan yana da buqatar wani abub.
Kallonta yayi tana tsaye tana jira ya kammala ya bata ta daura don dayar mero ta shiga bandaki da ita tun dazun bata fito ba da alama toilet take ''anyi ba'ayi ba,ko nayi da kaina din ma kina tsaye gaba na dubebi ba hijabi ai zan koma gidan jiya ko?''kamar qasa ta tsage ta fada ciki ganin isowar inna wuro da tukunyar miya zata wanke don tun kafin su fita maryam ta tuqe mata tuwon,kuma ta tabbata da taji abunda yace din duk da cewa babu wasu alamu da suka nuna hakan din dauke kanta ma ta sake yi,sai kawai ta waske da amshe tukunyar hanjun inna wuron tana mata sannu,bar mata tayi ta koma,madafi tana tattare gurin.
Tana duqe tana wanke tukunyar shi kuma yana alwalar idanunshi na kanta,har ta gama bai kammala ba,sau biyu yan sakewa wata,butar ta miqa mata yana fadin ''zubomin wani ruwan ki matsa a gun don Allah''bata tanka masa ba ta zuba masa din ta koma can baya tana jiran ya gama mero ta fito tana daura zaninta,suna hada ido da abdallan ta fara washe haqora,warin kashin nata ya buso masa,zuciyarsgi ta soma tashi,cikin sauri ya kammala alwalar,ganin haka maryam ta taho don kaishi gun sallar,saidai kafin ta qaraso har mero ta fara turoshin,shi da ita din duka fuskarsu a sake,shi yana murmushi ita tana dariya kome ya saka su dariyar oho,bai dubeta ba zasu wuce ta gabanta.
a nutse ta qarasa ta cite hannun mero daga handle din tana fadin ''ke baki damu da wucewar lokacin salla ba?''ta qarasa turashin ranta a bace dan tsaki taja bayan ta ajjiyeshi tana shirin juyawa ta bar gurin,haushin kanta take ji na yadda take sawa kanta damuwar abdallah da mero,hannunta ya riqo yana fadin ''ni kike wa tsaki maryamu'' sai a kunnen inna wuro tana fitowa daga daki ''tsaki mairamu kike wa mijinki?'',inna wuron ta fada tana kallonta,murmushi yayi ''inna wuro kin ganta nan,ki tambayar mana ita me muka mata,fushi take da mu'' idonta yayi qwalqwal da hawaye ganin abdallah na son hada ta da inna wuron,a hankali ta zame hannunta daga nashi don yaqi sakin nata.
''yo me kuwa aka mata,banda shashanci irin na yaran yau,ahir kada na kuma jin tsaki daga bakinki kan mijinki maza bashi haquri'' ta juya qwalla na shirin zubo mata ''kayi haquri''dariya taso kamashi ganin yadda taqi kallonshi kuma a haka haquri take bashi,madubi kawai ya kamata ta kalla idan ma bata gane feelings dinta ba ta fuskanci halin da zuciyarta ke ciki,sai da yasan yadda yayi suka hada ido,ya wani basar kana yace ''na haqura'',da sauri ta juya zata bar rumfar yace ''ki sake kawomin ruwan alwala'' ruwan ta ajjiye masa zata juya,ya janyota ta fada jikinsa,hannunsa yasa yana dauje hawayen da ya soma gangaro mata ''sarkin kuka,bakisan hawayenki masu tsada bane?,ki tausayawa zuciyarki hakanan mana diyana ta''tayi qoqarin qwace jikinta ganin tahowar mero don sam bata fuskanci me yake nufi ba ma saidai sam ko a jikinsa yaqi sakinta balle ta tashi,sai da ya gama goge mata hawayen tas da tafin hannunshi kana ya saketa,kan mero a qasa ta,shige dakin inna wuro a can ta tada sallarta kamar ta saki kuka saboda abinda ta gani din ya motsa mata kishinta kan maryam.
*mrs muhammad ce*👑
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽