Kenza eBookz

Abadan complete hausa novel - Chapter 31

Abadan complete hausa novel - Chapter 31

Abadan complete hausa novel Chapter 31: Abadan complete hausa novel Chapter 31. Gaba daya ilahirin jikinta ya kama rawa har ta gaza ci gaba da rura…

3,294 words

Gaba daya ilahirin jikinta ya kama rawa har ta gaza ci gaba da rura wheelchair din,wanne tonin silili abdallah ke son yi mata,saidai sam na zata bashi dama ya riga zare mata duk wata laka da qwarin gwiwa dake jikinta ba yadda yaga dama,don haka ta ttara sauran dukkan wani karsashi nata ''idanunka da zuciyarka sun maka qarya abdallah,ban taba sonka ban taba sha'awar na qaunaceka ba ko ka manta da bakinka kasha fadan ba kowacce mace ta dace da kaiba?bako wacce mace ta cancanci ka sota ba,nasan naso abdur rahim amma ba kai ba kuma bana sonka,bana sonka bana......'' idanunshi a rufe suke yana jin saukar maganarta,sukan zuciyarshi take da wani abu mai kaifi ba tare data sani ba,duk da zuciyarshi na qaryata duk wata magana dake fitowa daga bakinta saidai bai son jin furucin sam,sannu kuma kishin abdur rahim mai qarfi ya fara shigarsa,sanadiyyan katsewar maganarta shine fincikota da yayi ta dire a gabanshi,rashin qwarin jikinta ya sanyata zubewa a gaban nashi.

Murmushi ne kan fuskarsa wanda ko yaushe ke fidda sigar kyawunshi ''banyarda baki son abdallah ba sabida na jima da ci miki alwashin sai kin soni,alhmdlh ban zama looser ba ni nayi nasara,but now ina mai qara tabbatar miki sai son abdallah ya ninku cikin zuciyarki fiye da da,i promise''ya fada yana miqa mata qaramin yatsanshi alamar su qulla,ba tare da jinkiri ba ta miqa masa suka qulle kamar yadda yara keyi,shi ya dagata da kanshi ya kade mata jikinta kana suka ci gaba da tafiya.

suna tafe yana murmushi,raguwar kuzarin jikinta kawai ya isheshi amsar tambayarsa,sai da suka qara mintinan da suke yi akan nada kafin su isa ta ajjiyeshi inda ta saba,qur'aninsa ya ciro gaban aljihunsa don kwana biyu da suke tahowa su kadai da alqur'ani yake tahowa,yana yin tilawa kuwa mai yawa kafin su koma,wucewa tayi gurin da ta saba zama kamar ko yaushe ta zauna.

ta daga idonta take ta hango shanun su baffa da kwana biyu bata ganinsu,murmushi ta saki don sun kwana biyin basu gaisa ba,ciro qafafunta tayi ta karkade jikinta bayan ta miqe ta maida takalmanta ta fara tafiya,daga idonshi yayi a hankali ya bita da kallo,yana lura da yadda ko yaushe idan sunzo idonta na tsallaken rafin bai san meke burgeta ba a gun.

kamar ko wanne lokaci daga baya ta tsaya bata shiga cikin shanun ba sai baffa ne ya isketa,tamkar wadanda suka ahekara tare haka suka dinga hirarsu,ta tambaya kwana biyu bata ganin fitowarsu yace eh mai gida ke fidda zaka cikin dabbobin nasa to sai jiya ya kammala shi yasa sai yau suka fito ba tare dafa tambaya ba ya ciro wani mazubi mai kyau ya fara tatsar mata madara ''mai gida yace duk sanda ka zo a baka,yana ta tambayarka ma''tayi murmushi tana fadin ''Allah sarki na gode kuwa baffa''ta miqa hannu ta karbi mazubin tayi bismillah ta fara sha ''kisha ahankali idan bai isa ba ma sai a qara miki''taji muryar daga gefanta na gada,ta daga kanta ahankali,mahmud ne yauma cikin shigar kufta,murmushi ta danyi kana ta ja baya tana fadin ''ina wuni''ya amsa mata da ''lafiya lau,tun rannan kuma sai kika bace abunki ban sake ganinki ba'' '?eh wlh ta amsa masa a taqaice tana rufe mazubin ta miqawa baffa ''baffa gashi na gode ni zan wuce'' ''a'ah,jeki da shi meramu,duk lokacib da kike so kizo da shi sai a dinga zuba miki ciki''godiya ta masa don abun ya mata kyau,dan mazubi ne maikyau irin na fulani ''zaki gudu kenan kam irin na rannan?''ya tambayeta yana dan dada sauri don su jera tare ''a'ah,bani kadaice bace na fada maka,da yayana kuma mijina muke tare''ta fada cikin rashin sakin jiki dariya ya saka ''wai ni zaki yiwa wayo,don kin fuskanci na yaba ko?'' kai ta girgiza idanunta a qasa ''da gaake ni matar aure ce'' ''nima mijin aure ne''ya maida mata amsa cikin maida maganar wasa wasa,ganin da gaske yaqi yarda din ya sata tsayawa da tafiyar da takeyi don sun,kusa da inda abdallah yake bayan ta rage fara'ar fuskarta sosai ''idan baka amince ba muje ka ganshi da idonka,amma ka fara yin gaba tukun yana nan zaune akan kujera idan yaso sai na biyo bayanka''.

kafada ya daga kana yace ''is ok,bari nayi gaban,amma da sharadin idan qarya kike zaki amshi soyayyata'' kada kai tayi kawai ba tare da tace komai ba idanunta suka sauka kan abdallah zaune kan kujerarsa a gabansu,mamakin yadda ya iya kawo kanshi tayi,sai ta dubi kujerar wasu abubuwa guda biyu ta gani gefe da gefe bata taba kula da su ba wanda bisa alamu da su ya tuqa kanshi.

Kallo daya ta yiwa idonshi bata sake marmarun kuma kallonsu ba,ya kalleta ya kalki mahmud sai taga ya danna wani abu,rivearse kujerar tayi da kanta kana ta saita hanya ya soma tafiya sannu a hankali ''ko baki fada ba nasan shine mijinkin,kiyi haquri don Allah,wlh harga Allah ban dauka da gaske kike ba''mahmud ya fada cike da damuwa a gagguce ta gyada kai bata samu cewa komai ba ta biyo bayan abdallah.

*mrs muhammd ce*👑

📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽

[2:00pm, 9/29/2017] Huguma👑: [11:46am, 9/29/2017] Huguma👑: 💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺 💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖🌺💖🌺 💖🌺💖 🌺💖 💖

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 🌺💖🌺💖🌺💖 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 💖🌺 💖 © *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *_home of expert and perfect writers_*

5⃣0⃣

👁👁👁👁👁👂🏾👅

*_shin ka/kina lura kuwa 'yar uwa?,kin fuskanci kuwa yadda kwanaki keta zura gudu abinsu?,kinsan me hakan yake nufi a gareka/ki?,tamkar gaya miki suke kifa shirya kina kusantar kabari ne,ki shirya kina kisantar ajalinki,ki shirya kwanakin ki na duniya da aka diba miki na qarewa_*

*_daure ki aikata mai kyau don ki tarar da me kyau,babu yadda za'ayi ki shuka qaya kice inibi kikeson cira,duk fitar numfashinki daya daidai yake da kusantowar ajalinki,yadda idan second guda ta kubuce miki har abda bazata dawo ba haka ajalinki idan yazo daidai da qiftawar ido Allah bazai barki cikin duniya ba,to don me zaki batawa kanki lokaci kan cutar da wani?,don me zaki damu kanki da ababan duniya,duniyar da take wulaqantacciya?,duniyar da Allah yace bata kai qima da darajar da girma daidai da na fukafukin sauro a gurinsa ba,saboda me zaki shagala kin manta ki daina tuna mutuwa,bayan kina da yaqinin tabbas/lallai/babu makawa sai kin muyu kamar yadda kika ga wasu sun mace kema wataran haka ne,komai qararre ne banda zatin Allah,ya ubangijin kowa da komai ya mai rahama da tausayin bayinsa kasa muyi kyakkyawan qarshe,mu mutu muna kan tafarkinka na gaskiya_* *ALHAMDULILLAHI ALA NI'IMATUL ISLAM*

*_kafin na fara shafin nan ya zama dole na gaisar na kuma miqa godiya ta ga masu aiko da saqonninsu gareni,saqonninku sun ishemin,ina muku fatan alkhairi naji dadi qwarai da addu'o'inku,abinda kuketa roqamin na alkhairi ina fatan Allah ya sanyaku ciki kuma_*

*ummi jos* *mrs tafida* *haulat m badamasi* *Aisha kanyah* *ummu zainab* *sis rabi'a* *jammy jammy zbi group* *zahra hari zbi group* *na gode Allah ya bar zumunci da qauna*🙏🏽

Cikin kwana goma sha hudu da zahariyya tayi cikin gidan ba qaramar dandana kudarta tayi ba,sauqinta daya malam na hayi ya tsawatarwa iyalin nasa bayan bore da tayi ta samu sauqin abubuwa,saidai babu mai kulata ci kanki babu mai ce mata,ita din ma bata damu ba domin ta dade da raina ajawalinsu,tana ganin babu wadda tayi isar da zqtq rabe ta balle mu'amala ta hadasu,banda neman biyan buqata daya tilasta ta zama cikinsu ba su isa ta zauna da su ba har wata guda,ba don suna waya da nene ba tana tausarta ta tabbatar da tuni ta jima da cika bujenta da iska,wuyar ta isheta,kullum dare kwana ake ana abu daya ita da aljani zul anfaini,ga masifaffen wari da take ji jikin aljanin wanda kullum yake sata tashi da amai da ciwon kai

Dadin bakin neme da lussafin da tayi na saura sati biyu ta bar wanann zaman shahadar,saura sati biyu ta zama mai arziqi irin aezuqin nan na kwatance na gayawa sa'a yasa ta danne taci gaba da lissafin

********

Misalin sha biyu ne na rana wanda ko ba'a fada maka ba kasan lokaci ne da rana ke kan ganiyar zafinta,bare rana irin ta qauye da take budewa sosai saboda wadatar fili da suke da shi,tana cikin dakin amma ji take kamar tayi hauka,ta riga da ta saba zama cikin a.c ko yaushe,rufin dakin na langa langa kawai ya taimaka wajan qaro dumamar zafin ranar zuwa cikin dakin tsaki ta ja tana goge gumi ''kai,Allah ka tsinewa talauci,me za'ayi da talauci don Allah,Allah ka nuna cikar sati biyun nan nayi na gama wannan aikin na san inda dare ya yimin,ai wlh ko a hanya bazan bari mu hadu da talauci ba,zamana nan gidan kawai ya qara fito min da illarsa qarara wadda a baya ban sani ba,haba wannan azaba dole ne ma fa kasona cikin dukiyar abdallah tafi yawa idan mun karbe wallahi''ita kadai take sumbatu cikin dakin,vest,ce kawaia a jikinta doguwa har zuwa gwiwa amma ji take kamar tayi tsirara

kallo daya zaka mata kaga yadda fatarta tayo baqi ta kuma rame a hakan ma wai aljanin mujinta na dauke mata abinci irin wanda ta saba ci yake kawo mata,ta kuma jan tsaki ta gyara kwanciyarta kan katifar ta don dama ikin kenan,idan ta kwanta irin haka ko sallah saidai ta yi maja ta hadeta baki daya

Karo na farko taji ana qoqarin dago jibgegen labulen dakin da ya qara sawa dakin duhu,kanta ta dago don ganin waye,domin bata taba ganin wani ya rqbo bakin qofar dakin nata ba idan ka dauke malam na hayi siriryar macace wadda a kallon farko zaka gane sanda duniya na damawa da ita fara ce,wuya da yunwa suka maidata baqa baqa duk da akwai sauran haskenta,tsugunnawa tayi gefan zahariyya da ta zuba mata ido tana kallonta bayab tayi kicin kicin da rai,murmushi matar ta saki wanda ya bayyana jerarrun haqoranta da suka dafe ''sannu amarya,dama zuwa nayi na gaya miki ki fito yau zaki amshi girki''

Ba shiri ta miqe zaune daga kwanciyar da take a dazu,ckkin sake hade girar dama data qasa tace ''ke malama,bana son hauka,wa ya gaya miki ni matar gidan nan ce?,akwai abunda ya kawo ni zama nan kuma nan da sati biyi zan bar muku wanann dajin naku'' murmushi ta gani matar ta yi har da dan darawa kadan ''Allah sarki,ina zaton azal din data hau kaina kema ita ta hau kanki''cikin raahin fahimta take dubanta,daga bisani ganin matar bata da niyyar cewa komai ta kafe zahariyyan da ido yasa ta tambayeta ''kamar yaya?''ajiuar numfashi tayi,wannan karon zama tayi dirshan kan ledar dakin ''malam ga aureki ba tare da sanin cewa shi kika aura ba ko'' ''inji uban wa?,ni ba malam na aura ba,aljani zul'anfaini na aura,kuma ina sane,kada ki zomin da maganar banza,malam din da sai da safe yake leqoni mu gaisa ko ya kawomin saqon aljani'' dariya ta subucewa matar sai da tayi iya yinya kana ta tsagaita,zahariyya bata samu faragar tsaidata ba don kanta a qulle yake tamau

qasa qasa tayi da muryata kana tayi yan dube dube don tabbatar da babu wanda yake jinsu ''akwai wani aljani ne bayan malam na hayi?,ai malam shine aljani,zul'anfaini yana biyo dare yana turmusheki da sunan aljani,dalili,kenan da ya kafa miki sharadin zama cikin duhu daga magariba har gari ya waye'' tsawa zahariyya ta daka mata jikinta ya soma bari ''ke malama,banasom hauka don na fuskqnci duka jama'ar cikin gidan nan kamar daga gidan mahaukata aka debo ku'' murmushi fa kuma yi ''kema din kwana nawa ne kinbi sahu,badai kin gama kwana goma sha hudunki ba,ki fara duban hanya to''daga haka matar ta miqe tana niyyar ficewa,ganin indai ta fice din kuma babu lallai zahariyya ta sake samun wasu bayanai ba tunda babu da wanda take magana hakanan babu wanda ke magana da ita ya sanya ta riqo gefan daddaudan zaninta ''ya zaki sakani a duhu kuma ki tafi,don Allah zauna kimin bayani mana''sai data qarewa zahariyyan kallo na kusan minti biyar har taji ta tsargu sannan ta koma ta zauna inda ta tashin

''suna na habiba,ni nan da kika ganni ada yadda kike haka nake koma nace na fiki''cike da mamaki zahariyya ke kallin habiban wadda babu mugumin da zai kalleta baice mahaukaciya bace ''mamaki kike,to ki daina mamaki don kema lokaci kadan ya rage ki koma kamar mu,ba kanki malam ya fara haka ba,'yar gata ce ni gaba da baya,don gaba daya a buja muke zaune ni da iyaye na,haka da na tashi aure ma acan nayi aure na,na auri mijina mai kudin gaske saidai na taddashi da matarsa da yaransa uku,matarsa fatima sam bata da fitina,duk yadda taso mu zauna lafiya fur naqi,burina kawai shine na koreta daga gidan na mallake enginer abubakar,iya adalci yana nina shi tsakaninmu babu zalunci tattare da shi,wani abun ma haqqinta ne fatima amma zata ce ta barmin sabida haqurinta da kawaici,duk inda nasan zan samu malami da zai mini aiki na kutsa kai na sai dai babu nasara,sabida fatima irin matan nan ne masu yawan azumi duk litinin da alhamis bai wuceta,haka tana da yawan salla musamman ta dare,don nasha tashi aiwata da mugun nufina a kanta sai na taddata tana sallah,haka karatun alqur'ani,kafin ka samu fatima kan wata tasha ba saudi qur'an ba kai da wuya,amma hakan bai isheni iahara ba,da yake bata da haqqina Allah na tare da kta kuma yayi nufin kareta sai muka samu labarin malam na hayi

Babu bata lokaci muka shirya ni da mahaifiyata wadda ita ke taya bera bari na yiwa enginer qaryan zamu kano ziyarar yan uwan mama duk da salinmu ba kanawan bane yan katsina ne ya sani amma baice komai ba ya amince ya barni,har da bani kudi nayi tsaraba,har bakin mota fatima ta rakoni tasa yaranta na min a dawo lafiya amma ko kallo basu isheni ba muka taho,tun zuwan mu na farko yaci ace idan da ni mai rabo ce na gane inda malam na hayi ya dosa saboda kalamai da hanyoyin da riqa bi da ni neman biyab buqatarsa amma na kauce na qiya,qarshe ya harhada min duk wani abu da zan aiwatar cikin gidan muka taho bayan iyayen kudi da muka zube masa,amma wani abu da ya bani mamaki tsakanin fatima ko 'ya'yanta babu wanda yayi ciwon kai bare na sa tsammanin wani mummunan abu zai faru da su,ta tsaya tsayin daka wajen yiwa yaranta addu'ar tsari,hakanan lokuta da dama zaka ga ta cika botiki da ruwa ta musu tofin ayoyin tsari ta sa musu a frigde shine ruwan shansu duk da ruwan roba da mahaifinsu ke cika mana firizai da shi

ko cikin dare udan ta farka duk da ba dakinsu daya da yarqn ba sai ta leqa dakinsu ta tofa musu addu'o'i take komawa nata dakin nasha ganinhakan da idona,to duk abuna musulma ce ni kuma masan addu'a takobin mumini ce nice dai nasa qafa na shure,na tabbatar bazan nasar a kan fatima ba don,haka hankalina ya tashi ba bata lokaci muka sake dawowa,ashe zuwan tsautsayi da qaddara mukayi cemin yayi kada na damu akwai wani abban aljaninsa da zai bawa kwangilar aikinsu fatima amma shifa ba biyansa ake da kudi ba,ana biyansa ne ta hanyar auransa na wasu satitika ko watanni,da fari tuburewa nayi ganin da akwai auren enginer a kaina,amma da dadin baki malam ya ciyo kaina yace sati biyu kacal zanyi zaman auren ina komawa gida na zan taras buqata ta biya,nace ta yaya za'ayi mikina ya barni nayi tafiya har ta tsawon sati uku,wani garin magani da wasu layoyi ya,bani yace na samu dutse cikin gidan mu qato na daga qasanshi na saka na danne,yadda na danne layoyin nan haka engineer zai kasa min musu duk sanda na tambayeshi,haka kuwa akayi baice komai ba face Allah ya kiyaye hanya sai na dawo

satina daya cikin gidan ina wahala don ban saba ba sam,cikin daula na tashi haka cikin gidan mijina ma,amma da yake son zuciya da son duniya ya rufemin ido na daure a haka har nayi kwana goma sha biyu,kamar irin wannan lokacin da na zo miki haka daya daga cikin matansa tazo min da irin maganar da nazo miki uadda kika yimin haka nayi mata nima,yadda na zauna na baki labarina haka ta bani labarinta ita din ma duk kusan hakane,saidai ita maganin mallaka tazo ta karba,mallakar ma ra saurayi,saidai ita tasan malam ne zai aureta don yace wani rubutu zai dinga yi a alqalaminsa yana wanke mata acikinta,ta gayan har yau ta kasa kubuta daga gunsa,na fiki shiga tashin hankali sabida tuno mijina da gidana da iyayena da nayi da yarona qwaya daya da na haifa yana gida hannun fatima tace zqta riqe minshi har na dawo

Na fita da niyyar guduwa daga gidan saidai kinsan me?,wuni nayi ina shawagi cikin duhun masada da na dawa,an qullemin kaina tamau na rasa hanya,duk inda na kewaya ina tsammanin zai fita sai inga na dawo gidan nan,daga qarshe da duhun dare yamin babu wanda ya neme ni haka na dawo,kwana na bakwai ina wannan wahalar cikin gidan babu wanda yace min ci kanki hatta da shi malam din haka zan gama walagigi na na dawo,daga qarshe na tabbatar bazan iya kubuta ba haka na dawo naci gaba da zama na fawwalawa Allah lamura na,ina zaune cikin uqubqar malam din,matansa mu goma sha hudu ne kowacce tana da rana daya a matsayin ranar girkinta,yaransa guda hamsin ne,wasu suna nan tare da mu wasu sun watsu duniya,nima haihuwata uku da shi suna mutuwa yanzu haka yaronmu daya da shi shine wanda kika mara rannan kaltime ta janyeshi,mamata kuwa ban kuma jin duriyarta ba,wani abun ya manta ta manta ni ko itama kasa gane gidan tayi Allah masani''ta qarashe maganar cike dq dacin rai da danasanin butulcewa ni'imar Allah da tayi,ta kasa zama lafiya a gidan aurenta bayan babu abinda ta rasa,dama ance idan baka godewa ni'imar Allah ba ka godewa azabarsa.

Tuni har zahariyya ta saki fitsari a zaune,gumin da take kuwa tuni ya ninka na dazu,ta tabbatar idan da za'a auna jininta banu makawa za'a ga ya hau over ma akuwa taya za'ayi ta zauna da wulaqantaccen mutum kamar malam na hayin Tayaya zata yarda ta zama mallakarsa,wallahi bazai yiwu ba''ta fada qarfi kuma a fili tana miqewa ta fara hada akwatunanta kallonta habiba tayi ''wai me kike shirin aiwatarwa''a fusace kuma cikin ficewar hayyaci ''wallahi sai na bar gidan nan ko da me malam yake taqama din ni ba kalarsa bace,kudin ma raina muku wayau yayi''dariya habiba tayi ''duk yadda kike jin isa taurin kai da kafiya na fiki,malam mutum ne da baisan kalmar imani ba bare tausayi,ina mai baki shawara ki haqura ki maida lamarinki ga Allah ki roqeshi,watan wata rana idan da rabo kowa sai Allah ya kubutar da shi,amma,ina mai tabbatar miki koda kin fita ba zaki iya tsira ba,idan kuma baki yadda ba kina musu bismillah''daga haka habiba ta miqe ta gyara daurin zaninta ta fice

ko kadan zancan habiban bai shiga kunnuwanta ba don haka bata fasa shirinta ba,ta hada kayanta ysaf ta canja kayan jikinta ta jawo akwatunanta tayo tsakar gidan,da ido suka bita duuu kamar ko yaushe,wanann karon sam bata damu da kallonsu ba burinta kawai shine ta ganta ckkin gidansu

Cak ta tsaya a qofar gidan tana wara ido,ruwa ne a gabanta yake ta qugi iya ganinta,,duk hanyar da zata bi ta wuce ta zam hamshaqin kogi wanda ko da kwale kwale zaiyi wuya ka iya tsallakeshi don har wani murdawa igiyar ruwan take,duk lokacin data yi taurin rai ta tunkari kogin ta yunqura dan shigewa ruwan sai yayo ambaliya yayo,kanta tilas ta koma da bay ta shafe fiye da awa biyu a gun tana abu daya daga qarshe ta gaji ta faahe da kuka don ta fara ganin alamun maganganun habiba

zubewa tayi a dandaganyar gun ta saki kuka tana addu'ar Allah yasa mafarki take,ya rayuwa zatq juya mata baya haka lokaci guda ba tare da ta shirya ba,dabara ta fado mata ta dauko wayarta ta soma lalubar nene don neman daukinta

Readers Also Read

More by Ayshacool 1