Abadan complete hausa novel - Chapter 40
Abadan complete hausa novel Chapter 40: Abadan complete hausa novel Chapter 40. Hada kai sukayi suka fashe da kuka kowacce da irin tata nadamar,sun qi…
560 words
Hada kai sukayi suka fashe da kuka kowacce da irin tata nadamar,sun qi Allah bayan ya musu ni'ima,idanunsu ya rufe basu ganin baiwar da yayi musu da tarin ni'imominshi a garesu sai yanzu da ya karbe abinsa,dama ya fada cikin littafinsa mai tsarki''idan kuka gode min zan qara muku,idan kuma kuka kafirce to haqiqa azabata mai tsanani ce'',sun yarda sun dauki hudubar shaidan,wanda dama bashi da burin da ya wuce batar bayan dama ya sani cewa tun can dama shi batacce ne,kuma dama yayi wa Allah alqawari sai ya batar dq bayinsa kamar yadda yazo cikin wasu surori na qur'ani lokqcin da Allah yace ya fita daga aljanna la'ananne ne shi ''kuma la'anata tana tare da kai har zuwa ranar qarshe'' sai shaidan din yace ''ya ubangiji ka jinkirta min izuwa ranar qiyama''sai Allah yace an jirka maka,har uzuwa rana da lokaci sananne,sai shqidan yqce da ubangiji ''na rantse da isarka da buwayarka sai na batar da su gaba daya,saidai bayinka daga cikinsu tsarkakakku''sai Allah yace da shi ''haqiqa bayina baka da wani iko a kansu sai wadanda suka bika dagq cikin batattu,kuma haqiqa jahannama ce makomarsu gaba dayansu,tana da qofofi guda bakwai''a wani gurin kuma shaidan din yace ''zanzo musu ta tsakaninsu data damansu data hagunsu mafi yawansu zaka samesu marasa godiya'' haka ya sake fada a wani gurin cewa ''sai na batar da su,sai na sanya musu buri sai na umarcesu su canza halittar Allah(kamar bleeching yana daya daga ciki) shi yasa Allah da kansa yake fada mana ''haqiqa shaidan abokin gabarku ne ku ruqe shi abokin gaba'',muna mantawa ne da ranar mutuwa ranar tonon asiri ranar hisabi,ranar da duk wata rai saita bi ta saman siradi ta wuce wanda qarqashinsa wutar jahannama ce,aikinka mai kyau gaskiyarka zumunci da ruqon amana ne kawai zai qetarar da kai cikin salama
Son zuciya ya mana yawa,muna biyewa soye soyen zuciyoyinmu baka iya hana zuciyarka aikata mummuna wanda hakan ke kaimu ga halaka,Annabi muhammad S A W yana cewa''an lullube aljanna da abinda rai baya so(kamar salla azumi zakka,zumunci,da sauran ayyukan alkahairi da bamu son yi ko muke jin wuya gun aikata shi)an kuma lullube wuta da sha'awe sha'awe(kamar zina,caca,cin dukiyar marayu,annamimanci,sata da sauran abubuwa da rai kejin dadi yayin aikashi)''
Allah ya sake cewa ba don falarlarsa da rahamarsa ba da duka munbi shaidan face 'yan kadan Allah kasa mu dace duniya da lahira
Sun jima cikin alhini da jimantawa kansu kafin habiba tace ''zahariyya nifa na gaji,anya ba kashe malam zamuyi ba?''duk da yadda taso ga neman mafita amma sai da shawara ta tsoratata,don bata manta ba irin wannan kuskuren taso aikatawa ya kawota ga wannan matsayin da take ciki yanzu ''habiba,in sake yunqurin aikata wani kuskuren kenan?'' ''kashe malam,zahariyyq rage mugun iri ne cikin al'umma,bakiji abinda yace babe,malam fa bazai taba shiryuwa ba,shin kin san shi mutum nawa ya kashe cikin wannan qazamar harkar tasa?(hmmm,sai yanzu data ritsa da su suka san qazama ce)'' cikin rashin gamsuwa ta girgiza kai ''wannan shi da Allahnsa amma mu dq muke neman kubuta kuma inamu ina kisa,shawara daya ce kawai tunda mu bamu tsaya munyi karatun addini ba boko muka sa a gaba,ba wasu addu'o'i garemu ba kawai kullum mu dinga karanta masa fatiha ba adadi,ai Allah yana jinmu,kuma nasan da yardaraa wata rana zamu kubuta'' take ta yarda da shawarar zahariyyan don tafi tata fidda maslaha
*mrs muhammd ce*
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽