Kenza eBookz

Abban sojoji complete book 1 by boss bature - Chapter 15

Abban sojoji complete book 1 by boss bature - Chapter 15

Abban sojoji complete book 1 by boss bature Chapter 15: Abban sojoji complete book 1 by boss bature Chapter 15. Kanal yusif yace "aɗan sakaya dai yayanmu,…

4,376 words

Kanal yusif yace "aɗan sakaya dai yayanmu, saboda ƙannenmu,"

Abba yace "ynx don rashin kunya, abbas agaban idona kake faɗin sunan masoyiyata kai tsaye? gaban kuma shalelena ? Junaid ya ƙara rakwabe fuska, dariya su kayi cikin nishaɗi suke firar kowa na ɗan tsoma bakinsa,

Azmi ce ta kawo musu abunsha kowa ya kar6a, dama ka'ida ne duk bayan ƴan minti na sai ansha tea ko coffee 😌

tura kopan ɗakin tayi ta shiga tana faɗin "Amani baki ga text ɗina bane nace ki same ni a ɗaki"?

aunty babba ce ta shigo ɗakin da amani ta sauka tana mata magana,

Amani dake kwance saman bed hannunta rike da waya tana daddanawa, jin muryar auntyn tata yasa ta tashi zaune, bakar jallabiya ce a jikinta, kanta ba ɗan kwali sai doguwar sumar kanta data zuba a shoulder ɗinta,

"Sorry aunty na ban ankara ba, na dai ji shigowar message ban duba ba,'

Ƙarasa wa tayi kusa da ita ta zauna a side bed din suna facing juna tace "hmmm amani kenan, wato tunda nayi miki hanyar arziƙi, ki kayi kyau kika ƙara haske, kwanciyar hankali ya samu ki ka daina tako wa kizo inda nake ko? Ko phone calls babu ? A whatsapp ma ina ganin ki online ba magana, wato naira ta zauna ko?

Yar dariya amani tayi "haba aunty na, pls stop saying that, ke fa ce silar shigata wannan daular taya zan share ki ? Ae kullum ƙara gode miki nake, sbd ynx ko a mate ɗin mu ba wadda takama kafa ta wurin arziƙi, ynx fa takai ga ko taro za'a yi na class mate ɗinmu indai ban halacci taron ba to fasa shi akeyi, kowa burinsa na zo ba don komai ba sai don aga wanka leshin da zan ɗauka da zinaran da zan sanya,'

jinjina kai Aunty babba tayi tana ƴar dariya "haka nake son ji my sister, nafi so naga kuna wuta ana binku da fetur, ku zama on top kai kuzama ma topic ɗin gaba ɗaya, inji kawai ana zancen ku a ko'ina,

ta ƙarashe maganar da cewa "ina fata dai baki raga masa ko? Kina tatsarsa sosai kina matso sa sbd kinsan fa abunda ya kawo mu family ɗin nan dukiya muka zo mallaka domin mu raya namu family ɗin,'

Zuru Amani ta ɗanyi tana kallon auntyn tata, cikin sanyin murya tace "Mallakar dukiya kuma aunty? banda kuɗaɗen da muke samu a hannun mazajen mu har wata dukiya zamu mallaka ?

dariya aunty babba tayi tare da dafa kafaɗar Amani tace "ke fa matsala ta dake wani lokacin baki da lissafi, bakya gane wa, ae ynx kowa ta kansa ya ke yi, kuɗi kawai dole mu nemi kuɗi kamar hauka, saboda ynx mun shigo wani zamani da in baka dasu ba'ayi dakai, ka zama tamkar non living thing, masu kudi sune living thing, masu rai kenan,'

Ta ƙare mgnr tana kallon Amani wadda ta ɗan dabarbarce sbd auntyn tata ta fara bata tsoro,

Aunty babba taci gaba da cewa "Oh wai ke da soyayya kika zo kisha wurin ABBAS? Ae ni ban haɗa auranki da abbas ba don soyayya kawai, face don ki rinƙa tatsar mana shi, sannan naga haryanzu babu ciki a jikin ki, uban me kika tsaya jira !?

Hankalin Amani fa ya tashi ganin yadda lokaci guda auntynta ta, ta bayyana mata mummunan ƙudirinta akan family ɗin Abban Sojoji,

Ajiyar zuciya tasaki kafin tace "aunty ra'ayinmu ne yazo ɗaya, shima bayason haihuwa da wuri munyi planing sai nan da 5yrs, ynx soyayya kawai muke sha....... "

Katse ta auntyn tayi da cewa "ko ba soyayya ba? Nabi soyayyar da gudu, ashe head fish gare ki sam bakya gane wa, to bari kiji in faɗa miki, ki aje wannan planing ɗin, ki ɗauki ciki kawai ! mun samu mai cin gado, nima nan da kike gani na, ba don lalurar da ta same ni ba, da tuni na jima da sauke wani,

Jinjina kai Amani tayi tana kallonta cikin mamaki,

ƙasa ƙasa da murya tayi kafin tace "ke nifa wani target gare ni akan wasu cikin family ɗin nan, kuma ina mai tabbatar miki da cewa it will work,'

Amani tace "me ke nan aunty"?

wani shu'umin Murmushi aunty babba ta saki kafin tace "BABBAN YAYAN su ! da MARSHAL OMER, "

zaro ido amani tayi tare da dafe kirji tace " aunty me kike nufi dan Allah, fahimtar dani, kaina ya ɗaure,'

ƴar dariya Aunty babba tayi sannan tace "So nake na sama ma, ƙannan mu gurbi acikin gidan nan ! Kuma waɗannan shahararrun su nake hari ! ta ƙarfi ta tsiya 😳

cikin tsananin tashin hankali Amani tace " Aunty anya ba giya kika sha ba ? kinsan suwa ki ke magana akai kuwa ? Babban yaya fa da marshal omer ?

Cikin jaddadawa Aunty babba tace "ƙwarai kuwa ! Su nake nufi kuma a shirye nake da nayi koma mai zanyi don na asirce su naja ra'ayinsu akan Hayaam da Abrah,"

Zuba wa juna ido su kayi suna kallon kallon, har ynx Amani ji take tamkar mafarki take yi ba gske ba, ƙarfin hali irin na auntynsu ya bata mamaki tarasa wa zata ce sai Rafayet da Omar ? Anya kuwa aunty bata sha wani abu ba?

Katse mata tunanin ta tayi da cewa "na lura har ynx bakisan me nake hari ba, bari nayi miki dalla dalla,

Rafayet da ki ke gani duk family ɗin Abban sojoji ba wanda yakama ƙafarsa wurin tarin dukiya, gashi matashi ga kyau, a binciken da nayi Rafayet ya mallaki billions of dollars nasa na kansa, bayan tarin gidajen dake gare sa a us da sauran countries ɗin da yake yawan zuwa, sannan kuma ya mallaki privet jet nasa nakansa, ga tsadaddun motoci dake gare sa ƙirar bugatti, ƙirar mercedes benz, ƙirar pagani da ferrari da sauransu, ke duk wani abu da kike sani mai tsada rafayet ya mallake sa, shi kanshi tsadar gare sa, ke nifa farko dana fara ganin shi wlh, sai da nayi danasanin auren ishaq, hmmm ke fa bakisan shi ba ko, ae zai zo ne,

Amani ta gama rikice wa da jin irin dukiyar Babban yaya, cike da mamaki tace "wai dagaske kike auntyna ?

Murmushi Aunty babba tayi "ƙwarai ma kuwa, Rafayet he's among the most richest men in the world, youngest billionaire ne, Kuma yana ɗaya daga cikin most handsome men saboda kyansa da structure ɗin jikinsa,

Jin jina kai kawai Amani take yi ta jin jinawa lamarin, Murmushi aunty babba tayi kafin taci gaba da cewa "Bayan Babban yaya kuwa a wurin arziƙi cikin family ɗin nan sai Hajiya azeema, wannan matar da ki ke ganinta ƙuruwa ce wurin arziki,business ɗin golds take yi da diamonds, ina wannan agogon ta hannunta ? Kin ganta ae ko ? ta faɗi cikin son fahimtar da Amani, "Eh aunty na ganta mai kyau kamar na sace wlh,' "Hmmmm to wannan da ki ke gani ƙirar graff diamonds ce, $40 millions a us dollars, a naira kuwa sun kai 24 billions,' dafe ƙirji Amani tayi gaba ɗaya tabi ta susuce, jin abun take tamkar a mafarki, sakin baki kawai tayi galala jin wannan daular, Aunty babba taci gaba da cewa "daga ita kuwa sai marshal Omer wurin arziƙi, shima billionare ne duk wani abu da Babban yayansu ya mallaka shima ya mallaka, don dai ya wuce shi da wasu abubuwan, sune kawai nayi bincike akansu, sauran kuwa kowa attajirin kansa ne, ya ki ke gani idan Hayaam ta samu shiga Wurin Rafayet ita kuma Abrah muka kutsa ta wurin Omar ? Washe baki Amani tayi tare da cewa "ae shikenan kawai ba sauran magana, mun gama kwaɗaice wa," dariya su kayi gaba ɗayansu a dai dai lokacin Azmee tayi knocking kopan ɗakin, cikin sauri suka gyara natsuwarsu,

Amani tace "Shigo ciki" tura kopan azmee tayi ta shigo da fara'a a fuskanta tace "dama an kammala dinner ne, naji shiru baku fito ba shine nace bari nazo na sanar daku,"

*Me zaku ce game da Aunty babba da Amani dake shirin mallake dukiyar da ba ubansu ya tara ba ?*😡*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

_written story by_ *HAFSAT BATURE*

~BossLady~

*Page 55 to 56*

Yinin ranar jin jikinta take yi cikin wani irin yanayi mara misaltuwa, shi dai gayanan wata ni'ima ni'ima , ga wata irin kasala da ta mamaye ta, sai wani lalaci da take ji, saukin ma aunty Azmee ta sanar da ita cewa bata da aiki ta zauna ta huta kawai, yau ranar hutun ta ce , yini tayi tana safa da marwa frm wall to wall, zullumi iri iri agame da su HUSANNA da JAHAD, ga kuma wani irin bugu da zuciyarta take yi mata, ita dai tunkan ta sa wannan Babban yayan nasu a ido take jin feelings agame dashi (kina ruwa 😂)

Har cikin bedroom dinta azmee ta shigo mata da dinner dinta, ba karamin dadi taji ba, kaunar azmi na kara shiga cikin zuciyarta, sbd tana kula da ita kamar yar cikinta, ta damu da ita sosai, Allah sarki,

Zuba wa meatballs din dake shake cikin plate din dake ajiye saman bedside drawer dinta tayi, ga fresh milk acikin glash cup, shiru tayi tana kallonsu, jikinta a mace yake, ga kamshinsa ya cika ta, amma a kullum ji take kamar batayi wa yan uwanta adalci ba, tana cin irin wannan dadin yayin da suke ciki mawuyacin hali, Zugudum tayi a yayin da take zaune a saman gadon daga baki baki, ta lankwashe kafanta a sama, Azmi ce ta sake turo kopan ta shigo hannunta dauke da fresh fruit acikin dan plate, "Ya akai har yanzu baki fara ci ba? me kike jira ? ajiyar zuciya sehrish tasaki tare da cewa "Aunty azmee zuciyata bata mun dadi in na tuna da yan uwana, sai naji bana son cin komai, Cikin nuna damuwa azmi takarasa ta ajiye mata plate din a hannunta, sannan ta zauna gefenta cikin natsuwa tace " kin yi imani da Allah!? daga kai sehrish tayi tare da cewa"Eh"

"Ina so aduk lokacin da zakiyi addu'a ki kasance mai cike da imani, kiyi imanin cewa addu'ar nan da kika yi Allah ya karbeta, don't doubt about it sbd karancin imanin kesa muna rasa wani abun, amma muddun ki kayi masu addu'a kina me cike da imanin cewa Allah ya karbeta, ba tare da kinsawa ranki kokwanton cewa Anya Allah ya karbi addu' a ta kuwa? Ko kuma kinji shiru har ynx ba ki ga sakamako ba, duk ba'a son wannan, kawai kisa ma ranki cewa duk in kikayi addu' a Allah ya amsa kuma tom insha Allah zaki ga sakamako mai kyau, kuma zakiji natsuwa acikin zuciyarki," Jinjina kai sehrsh tayi tare da cewa "ngde aunty azmee kuma insha Allah zanyi kamar yadda ki kace" Murmushi azmee tayi tare da cewa "yawwa rishi na, ko kefe yanzu dai ayimun wannan murmushin kashe zuciyar nagani" ta fadi cikin zolaya tana kallonta, Sunnar da kai sehrish tayi tana murmushi, itama azmeen murmushi take yi, hannu azmee tasa ta dauki yankakkiyar abarbar dake cikin plate din dake ajiye a saman hannun sehrish, A baki takai mata tare da cewa "Ha bakin nasa miki' Bude baki sehrish tayi tana yar dariya, zura mata abarbar tayi, sehrish ta taune, nan take zakin abarbar ya cika mata baki, takama lasar labba, Azmee tace "yawwa ko ke fa ynx naji magana, bari na baki meatballs din abaki," Cikin sauri sehrish tace "a'a aunty azmee zanci ynx, kunsha aiki kun gaji, gashi ban tayaku ba,' "Kada ki damu sehrish, ae ni nace ki zauna tun da gasu Chef ummu aiki na tafiya yadda ya dace, ina fata dai bakiyi tunanin BABBAN YAYA ba yau ?" Ta karasa maganar tana kallonta, cikin zolaya, Sunnar dakai tayi tana murmushi jin an ambaci sunan da ke mata kaikayi a cikin zuciyarta, "Bani da amsa kenan, tam ni zan tafi ynx kada ki manta, a daren yau kiyi sallolin nafila, kiyi addu'o'i wa yan uwanku da kuma sauran al'ummar musulmai," "Insha Allah aunty Azmee ngde sosai" Tashi Azmee tayi ta fice 👋

Hakika sehrish ta samu natsuwa a ranta, azmee ta iya kalami masu dadi masu sanyi da ratsa zuciya, zama tayi ta dinga cusa fruits din dake agabanta cikin bakinta, cikin dadi take shan su, bayan ta gama dasu ta ajiye plate din ta dauko na meatballs din ta shiga dauka tana jefawa a baki, kunnanta har motsi yake, yayi dadi sosai, yaji kayan kamshi, lokaci zuwa lokaci ta kan hada da cool milk din dake acikin cup, tana kurba 😋

Kwance suke rungume da juna, daga su sai dan towel a waist dinsu, da alama daga bathroom suka fito duba da ruwan dake a jikinsu, "Ayaan ba karamin dadi naji ba wlh' "game da me kenan ? Jahan ya tambaya yana kara shafa sumar kan ayaaan, "game da zuwan babban yaya, i felt so happy da junaid ya sanar damu cewa ba date ba time na zuwansu,' murmushin takaici Jahan ya saki tare da cewa "hmmm da alama bakasan wannan mutumin ba, ni nayi imanin cewa daker babban yaya zai wuce gobe baizo nigeria ba !!!! Ina ji araina ! dan dagowa Ayaan yayi daga jikin jahan yakasance yana kallon face dinsa, cikin kwarkwasa yace "pls stop thinking about that, kawai musa wa ran mu cewa ba nan kusa zai dawo ba, hakan zai bamu courage din ci gaba da jin dadin junan mu,," murmushi Jahan ya saki yana kallon cikin kwayar idon Ayaan wadda takasance ash colour ce, mai ruwan toka, mai kyan gaske , shima kallonsa yake yi cikin tsananin sha'awar junansu, zuciyoyinsu na kara azalzalansu akan su kara second round, hannu jahan yasa ya janyo ayaan bakinsu ya hade dana juna ya zura harshensa acikin nasa, nan suka shiga misayar saliva a tsakaninsu,

………………….AUNTY BABBA…………………

zaune take agefen amani sbd dama basu tafi ba, suna jiran zuwansu babban yaya, duk da ita amani acikin garin take , amma abbas ya bata iznin ta zauna ta kwana tunda auntyn ta na nan itama , Inyaso zuwa gobe sai ta dawo gida, Dukansu suna sanye cikin sleeping dress, riga da wando, masu kyan gaske, kowa ta zubo gashin kanta dayake Allah yabasu, "Ina sauraronki aunty na" amani tayi mgnr tana kallon auntyn tata dake gefenta saman gado, "Shiri na musamman ya kamata muyi wa lamarin domin cin nasara akan wadannan zafafan guda biyu, shawo kansu ba abu mai wuya bane, dole sai an hada da shahararrun bokaye, kamar wannan bokon na kurmin dajin nan dake a enugu, " Xaro ido Amani tayi tare dacewa "Aunty enugu fa kikace ? gsky da kamar wuya wlh,' Dariya aunty babba tayi tare da cewa "a wurinki ba, ae ni akan na cimma buri na wlh ba abunda bazan iya yi ba, hmmm ke dai kawai abar kaza cikin gashin ta har ynx bakisan wacece yayarki Laila ba, ' zugun Amani tayi tana kallonta hankali a tashe, lamarin ya fara bata tsoro "yanzu aunty yaushe zaki enugun? Cike da kwarin guiwa aunty babba tace "Ni bana aiki cikin gaggawa, a sannu zamu cimma nasara, amma kafin nan muna Bukatar kudade dayawa, don tunkarar wannan bokan ba abu bane mai sauki, dole mu hada karfi da karfe ki tatsar mana wurin abbas nima na tatso wurin Ishaq, daga bisa ni mayi mgnr zuwa can,' shiru amani tayi ita dai haryanzu akwai karaya atare da ita, cike da kasala tace " aunty nifa ina tsoro wlh," Mtswww aunty babba taja tsoki "ke dallah wane tsoro, aje wannan ma gefe, ke bakisan abunda nake hango mana ba, muddin muka ci nasara akan Babban yayansu da marshal omar to ina mai tabbatar maki da cewa gabadaya zamu rinka juya kowa na family dinnan, sai yadda muka so za'ayi" ta idasa magabar tana kallon Amani, wadda tayi tsuru tsuru, ajiyar zuciyata tasaki har zatayi magana wayarta dake saman saman pillow ta soma ringing, da sauri takai hannu ta duba sunan "Babyna" ya bayyana Aunty babba tace "halan Abbas ne ? Amani tace "eh shine,' "Yawwa maza ki daga, ki rinka kashe masa murya kina masa ladabi ko mun ci nasara akan kudin da muke bukata,' amani ta amsa da to, tare da picking call din ta kara a kunne tare fadin " baby na y kke? nayi kewarka sosae," Saurara wa tayi tana sauraran muryar abbas dake cewa "nagaza bacci ne, na fito daga wanka ne, naji ba abunda nake son ji face muryarki," Murmushi Amani tasaki tana kallon aunty babba data kura mata ido, cikin sanyin murya tace "nima haka babyna, ynx haka maganarka nake ma,' "Are u serious ? Zamu yi video call ne inaso naganki cikin sleeping dress din nan naki, ' Kallon aunty babba tayi taji me zatace saboda wayar a handsfree take, da ido tayi mata alamar tace masa eh, "Eh babyna a shirye nake , nima a kagare nake dana ganga, " Murmushi aunty babba, tayi tare da mike wa ta fita daga dakin tana ji aranta cewa burinta zai cika,

Dare yayi sosai Junaid na dakin abbansu , ya addabe shi ya hana shi sakat, shi ala dole ga auta, suna kwance atare saman king size bed dinsa, junaid ya aza masa kafarsa a saman jikin abbannasu, zallar rigima yake ji, "Junaid dan Allah ka barni na huta, ka tafi bedroom dinka ka kwanta mana, ko kaje Wurin yayyen ka kwana mana," abban nasu ne yayi maganar cikin jin bacci,' cikin shagawaba yace "nafi jin dadin kwanciya ajikin ka abba, In kuma kana so nadaina zuwa kwana nan, tam ka je ka dawo da mommyn mu, " rai a dan bace abban nasu yace " kada na sake ji ka kira min sunanta Allah," Cikin zolaya junaid yace "kaifa kace kana so Abba, ba wanda yayi maka dole, saboda dadin soyayya ko su Ammi basu sani ba kaje har us ka aurota, wato kaga kyakkyawa, doguwa fara mai dogon gashi ko ? Yunkura wa abban yayi tare da fadin "bismillah" ya janyo pillow, ya shiga bugun junaid dashi, dama sun saba ya maida shi tamkar tsaransa, kuma Abban ba karamin dadin hakan yake ji ba, cikin kukan wasa junaid kecewa " Abba dan Allah kadaina ae gsky na fada, wlh momyn mu akwai kyau, shi ya rudaka ma, Cikin mamaki abban yace "wai junaid ko dan muna kwana shimfida dayane yasa ka raina ni? dariya suke gaba dayansu, duk yadda yaso junaid ya rufe bakinsa ya daina masa maganar Alexandra (Alekzandra) amma yakiya, dakyar bacci ya kwashe su, su duka,

Insha Allah za'a samu Lunch ko dinner, in Allah ya yarda amma ✨ *💋💋SURGEON GENERAL RAFAYET & MARSHAL OMAR💋💋*

*Welcome to Nigeria* 😍

*finally our Stars Sun bayyana* 😂

*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

*ku kaddara cewa page 1 ne wannan domin kuwa yanzu labarin ya soma*

Page *57*

Writer *HAFSAT BATURE* ~BossLady~

Bayan ta kammala cin abunda azmee ta kawo mata kitchen ta mayar da kayan, sannan ta dawo ta shiga toilet ta daura Alwala, ta zura hija bi ta shiga jera salloli, bayan ta kammala ta rufe da zafafan addu'o'i tana nema ma rayuwarsu sauki, tasha kuka ayayin da ta daga hannunta sama tana rokon ubangiji, hawaye na gangarowa a idonta, Ba ita ta kwanta ba sai cikin dare ya taba, sannan ta kwanta, tare da rungumo pillow a chest dinta kamar yadda ta saba, tabbas ranta na bata cewa Babban yaya bazai wuce gobe ba bai dawo ba, saboda taji wani sanyi aranta, amma bata da tabbacin hakan , sai in Allah ya kaimu da rai da lafiya sai kuma in hafsat bature ta so hakan, dayake wuka da nama suna hannunta, 😜😜😜 **************************************** Mutum biyu ne suka san da zuwan su Abba da junaid sbd sunyi receiving call dinsu in d midnight, a time din mu na nigeria jirginsu zaiyi landing around 9:00am, A Wani irin haɗaɗɗen katafaren privet jet ne ya ɗauko su, wanda ya kasance mallakin Surgeon general RAFAYET, ya haɗu fiye da tunanin mai tunani, cikinsa bai da banbanci da hamshaqin parlour wanda yaji tsadaddun furnitures, saboda an ƙawata shi da jigunannun furnitures, Wato Aljannar duniya ce, acikinsa ya ƙawatu, 👌 Wasu hamshaƙan leather seats ne acikinsa jigunannun gaske, wanda ko a ido ka kallesu kasan zasu yi tafshi da daɗin zama, masu numfashi irin waɗanda kana zama zasu lumbutse dakai ciki, A jere suke biyu suna facing ɗin biyu zungura zungura, a tsakankaninsu wani ƙayataccen table ne haɗaɗɗen gaske, mai ɗauke da travel cups wanda abunsha ne acikinsu, tukunna ma shin su wanene acikin jirgin ? 😒 tunkan na fara zayyana su zan fara da faɗin tabarakallahu ahsanul khaliqin 😇 Haɗaɗɗiyar sura, dogaye ne masu cikakkiyar ƙira irin ta zakuna, irin ta mazan gaske sadaukai kuma jarumai, ƙerarrun gaske, duk inda namiji yakai to su sun zarce nan, komai nasu na kece raini ne ba wasa a tattare dasu babbar harka ne, duk iya haɗamar mace bazata wuce waɗannan handsome stylish guys ɗin ba, buri kowace ƴa mace nesu, a fage na kyau kuwa ba'a magana, ƙarshe ne su, a bangaren wadatar arziki kuwa basai an faɗa maka ba, kana ganin su kasan cewa sun wanku da pawns da dollars, fatar jikinsu kaɗai abun kallo ce, su huɗu ne zaune kowa ya hakimce, jirginsu kawai suke jira yayi landing, 3 daga cikinsu suna sanye cikin expensive dress na suits, biyu launin nasu blue ne ɗayan kuma black ne, Mutun ɗaya ne baya sanye cikin suits ɗin nan, shin wanene shi? Jikinsa na sanye cikin V-neck shirt , tayi tighting ɗinsa, white colour yayin da yake sanye da army trouser, Yana da wata irin sura mai matukar rikiɗarwa mai razanarwa mai matukar jan hankali da ƙayatarwa, saboda a halitta dogo ne, mai wani irin faffaɗan ƙirji a buɗe yake, ga wannan six pack din nasa baro baro, ya cika vest ɗin kana ganin zanen ƙirjinsa ga breast ɗinsa sunyi 6ul-6ul ata ciki kana hangensu, daga gani yana gym (motsa jiki) sosai, in ka kalli damtsen hannunsa sai ka tsorata, kana gani kasan cewa yana da matuƙar ƙarfi kamar ɗan wrestling (dambe) haka surarsa take, mutun ne mai ji da ƙarfi, Idan muka je wurin tommy dinsa kuwa a shafe yake ba alamar tumbi ko kaɗan, yayi flat, tamkar baya zuba abinci acikinsa saboda ɗamewarsa, Launin fatarsa fari ne sol irin hasken fatar ƴan korea, natural white kasancewarsa half cast (ruwa biyu) mahaifinsa hausa fulani, mahaifiyarsa baturiya, ya kuke ganin abun zai kasance? A wurin kyau kuwa sai dai muce tubarkallah, domin Allah yayi sa da wani irin ƙayataccen kyau mai matuƙar razanarwa, ko namiji jinsin sa ya kallesa sai ya ƙyasa balle mace, yadda kasan shi ya zana kansa, don duk mun haɗamar bil'ama aka basa damar ya tsara yadda kyansa zai kasance, bazai wuce nasa ba sai dai ma ƙasa da nasa 😯 Komai na halittar jikinsa dogo ne, kakkarfa domin Allah ya wadatasa da duk wani abu da mace zata buƙata ajikin ɗa Namiji! Idan muka koma kan haɗaɗɗiyar suman kansa kuwa mai tsayin gaske wadda ta sauko masa har saman kafadarsa , tasha gyara na musamman ya ɗaure ta, dark brown ce Allah kaɗai yasan nawa ake kashe ma wannan suman wurin gyara, Hatta gaban forehead ɗinsa sumarce a kwance, ga wani kwantaccen saje mai shegen kyau, eye brows ɗinsa kuwa tamkar an zana ta, tayi wani irin shape ga gashi cike da ita, kiris ya rage jagirarsa su haɗe da juna saboda yawaitar suma a wurin, idan muka koma kan idonsa kuwa yana eyelid (kwarin ido) wadatacce wanda ke lullu6e da eyeballs ɗinsa, yana da dogayen eye lashes masu cukowa da tsari, ga kyan gaske Allah yabasa kyawawan idanuwa ga girma ga su so sexy, farare tass tass masu ɗauke da kwayar ido, blue colour masu shining masu ɗaukar ido, daga ƙasa kuwa dogon hancinsa ne, ba wai irin ziƙau ɗinnan ba, a'a mai tsari dai dai wa daida, daga nan kuwa sai pink lips ɗinsa tamkar ya shafa jan baki, ga skin din la66ansa irin mai squeeze ɗinnan ce, Cikin natsuwa yake daddana laptop ɗin dake gabansa saman table, ƙirar Luvaglio wadda price ɗinta yakai $1 million ne (dala miliyan ɗaya) a naira kuwa yakai 600millions, miliyan ɗari shidda, cikin natsuwa yake daddana ta da zira ziran yatsunsa, hannunsa na sanye da wrist watch kirar piaget emperador temple ce, farashin ta yayi $3.5 million a naira kuwa ba'a magana billions ne ke magana, Zan iya cewa duk macen da zata so shi ba don Allah bane, zai yi wuya asamu macen da zata so shi hakanan kawai ba don wani abu nasa ba, kamar kyansa, tarin dukiyarda shi kansa baisan adadinta ba, surar jikinsa ga kuma ilimin addini dana zamani, komai ya haɗa komai nasa is Extraordinary, Basu kadai bane acikin jirgin akwai wasu gabza gabzan soldiers wadanda suke a matsayin security guards nasu, mostly dinsu black americans ne, ba wasa a tare dasu, basa ji basa gani umarni kawai suke jira su aiwatar 😳 Bakowa bane wannan face SURGEON GENERAL RAFAYET 😘 wanda kowa ke zumuɗin ganinsa, wanda hafsat bature da sehrish suke kwakwar ganinsa, tare da mamee da kuma readers😂

BABBAN YAYA wanda kowa ke shakkarsa ko sunansa aka ambata sai an girgiza, baya wasa da aikinsa, kaifi ɗaya ne,babu mai iya tankwara shi, sam mace bata gabansa a tsarin rayuwarsa baya da burin yin aure gaba ɗaya, cos bashi da interest akansu, mata bibiyarsa suke kamar hauka, ƴa'ƴan manya yayan shuwagabanni ya'yan sarakuna, amma ko kallo basu ishe shi ba, 😂 yadda yake kallon namiji haka yaje kallon mace ba banbanci, sam bai da shauƙin soyayya a tare dashi, Tun saura 30 mins jet dinsu yayi landing , manyan motoci suka isa airport din jibga jibga na sojoji, baka jin komai sai tashin jiniya kamar ana yaki, a cikin motocin akwai na gayu tsadaddun gaske kirar mercedes benz da aka zo daukarsu da ita, Time din da jirgin yayi landing, cikin isa kowannansu ya fito, yana saukowa daga matattakalar benen, a jere suka sauko gaba daya ido na akan Babban yaya tare da marshal omer, cika ido suke kamar kamar me, a bubbude suke tafiya irin tafiyar nigogin nan, wadanda suka ji karfi, shi marshal omar sam bai kai rafayet tsayi ba amma fa akwai kira ta mazajan gaske, Masha Allah, 🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶 Su wa ke farin ciki da zuwan *BABBAN YAYA*😍 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *page 57 to 58*

Ci gaban page 57 cikin nan

Not edited like always 👀

Readers Also Read