Abban sojoji complete book 1 by boss bature - Chapter 18
Abban sojoji complete book 1 by boss bature Chapter 18: Abban sojoji complete book 1 by boss bature Chapter 18. ganin sun soma ƙoƙarin ɗaga murya yasa ta…
4,331 words
ganin sun soma ƙoƙarin ɗaga murya yasa ta dakatar dasu da cewa "You have to trust me, ni turo ni akayi na taimake ku kuma dole sai ta wannan hanyar, Cikin mamaki Jahad tace "wa"? Murmushi tayi kafin tace "daga wurin ƴar uwarku SEHRISH," Jin ta ambaci sunan sehrish yasa su gyara zama suna masu tsananin mamaki, wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskarsu, "Dan Allah dagaske ne sehrish zata taimake mu ? dama tasan halin da muke ciki ne, Allah ne ya amshi addu'ar mu zamu fita daga wannan uƙubar," Jahad ce tayi maganar da tsantsar farin ciki aranta, husanna kam sam tagaza rufe bakinta murya na rawa tace "Dama nasani Sehrish bazata bari a cutar damu ba, nasan tana son mu sosai, dan Allah a fiddamu daga nan akaimu wurin ƴar uwarmu," Kallansu kawai inspector ɗin take yi, wani irin kallo na shu'umanci ganin sun miƙa wuya yasa tace "kun amince zaku amsa cewa kune ku kayi kisan!!"? Atare suka haɗa baki wurin cewa ehh mun amince,'
ƴar dariya tayi kafin ta fita daga cell ɗin, a harabar police station ɗin ta tsaya jikin motarta, hannu tasa a aljihun wandonta ta ɗauko wayarta ƴar nokia, daddanawa tayi kafin ta kara a kunnanta tare da cewa "Yaran fa sun amince, zasu amsa cewa sune su kayi kisan, yaushe zanji alert na cikon kuɗi na ? Natsuwa tayi tana sauraron mutumin da ta kira a waya, wanda ba'a bamu damar jin me yake cewa ba, Dariya inspector ɗin tayi kafin tace "nima fa shu'uma ce kamar kai, muddin banji alert ba na cikon kuɗi na, ina mai tabbatar maka da cewa, zansa su fasa amsa laifin,' Ta jima tana wayar kafin ta kashe wayar tana tikar dariya (to fa)
A can cikin cell ɗin kuwa, wani tunani ne yazo ma Jahad ita mai hankalin taya akai ƴar sandar nan tasan sunan sehrish !!!!? Kuma taya akai Sehrsh tasan halin da suke ciki ? Tabbas akwai makirci acikin lamarin,
Miƙewa tsaye tayi tana zagaye, can dai tace "husanna so ake mu amsa laifin kisan nan don akashe mu, ba don ataimake mu ba !! jiki a mace husanna tace "jahad ni nagaji da rayuwarnan, so nake na mutu kuma yanzun nan,!!
hankali atashe jahad tayi hanzarin komawa kusa da ita tazauna tare da dafa shoulder ɗinta tace "Husanna bakya jin daɗi ne,"
"Eh mutuwa zanyi yanzun nan," ta bata amsa, bin ta da kallo jahad tayi a tsorace ganin , jini ya soma biyowa ta hancinta, daga magana sai abu ya tabbata, kafin ta ankare husanna ta zube ƙasa, ba numfashi, Wata irin razananniyar ƙara Jahad tasaki tare da faɗin "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'una !!! Nashiga uku !!Wayyo Allah na Husanna ta mutu........... da gudu police ɗin dake waje suka shigo ciki, sun gigita da ganin halin da yarinyar take ciki tamkar ba numfashi, kuma sun son tabbas ta mutu a hannunsu sai anji dalili, hakan yasa aka kira women police guda biyu suka ɗauki husanna, hada jahad aka tafi da su cikin mota domin kaita asibiti, Sai faman kuka Jahad take kamar ranta zai fita saboda tana ji aranta cewa Husanna fa wannan karon dakyar zata rayu,
Ganinsu da ƴan sanda yasa, reception nurses saurin karbarsu, aka shiga da husanna ciki a (A&E) accident and emergency ward aka kwantar da ita, nan da nan likitoci suka shiga duba ta, Jahad na zaune a saman waiting seats dake daga waje Ward din, tasha kuka ido sunyi jawur, Ga ƴan sanda zagaye da su,kamar wasu 6arayi, addu'o'i kawai take karantowa abakinta , tana roƙon Allah yasa Husanna karta rasa ranta, tsananin ƙunci ne a ranta, kuma tasawa ranta cewa muddun *Husanna* ta mutu itama sai ta kashe kanta ❗‼⁉, 😭😭😭
...................SEHRISH..............................
Oya drop your comment after u finished reading i wll be waiting for u 😎
*🌹HAFSAT BATURE MOHD BOSS LADY🌹*
*page 65 to 67*
_Sannan daga numbers na pages ɗin littafin nan sun kai 80 zasu canza zuwa Episode one1_
.........Sehrish..................
gaba ɗayansu sun hallara, kowannan su ya sami gurbi a dining chairs ɗin, azmee ce ke ta faman ɗawainiya yin saving ɗinsu, saboda sehrish na can cikin yanayi
_kowannan su ya hallara a saman dining chairs ɗin, kwansu da kwarkwatarsu,
Yau suna gida ba fita aiki, a bisa umarnin Babban yayansu,
_Duk sunyi dress cikin Jallabiya, dama yana ɗaya daga cikin favourite dress ɗin su, basu cika son kaya masu nauyi ba_
_azmee ce ke saving ɗinsu, kowa tana zuba masa abunda yake so_
_duk sun natsu suna ci, hannu ayan yasa acikin aljihun jallabiyarsa ya zaro wayarsa dialing ɗinta ya shiga yi Jahan ya tura wa saƙo kamar haka_
_"ya maganar hotel room ɗin? Kayi mana booking?_
Jin ƙara shigowar message a wayarsa dake ajiye gefen plate ɗin abincinsa yasa shi duba ya karanta, ɗan murmushi yayi kafin ya bashi amsa da cewa _"Eh yaushe zamu fara zuwa don a matse nake wlh_
duba wa Ayaan yayi ya basa reply shima,
_"ko yau ka ce am ready to do it, am so horny dear kamar nayi hauka_😖
duba wa jahan yayi wit smile on his face ya tura masa reply shima, _" u must be horny dear, 2 days ba testing ɗin *Ak47* dole Mu shiga yana yi_
Before Ayaan ya bashi amsa muryar fawan ta katse su da cewa
*Ga Babban yaya nan kowa ya shiga taitayinsa*
Cikin sauri kowannan su ya mayar da wayarsa cikin aljihunsa, don ya hana ana cin abinci ana danna waya, Atare da junaid suke saukowa ɗga stairs ɗin, farar shirt ce ajkinsa ta ɗame sa, mai dogon hannu , daga ƙasa kuwa shorts ne launin ash, gaba ɗya surar jikinsa a bayyane take sboda duk yadda Sgr zai sa sutura sai halittun jikinsa sun fito muraran,ba abunda ke 6oyewa nadaga kyakkyawar surarsu, hakan ba ƙaramin tayar musu da hankali yake ba especially abbansu yayi fama dashi saboda bakin mutane tun da dai abu tubarkalla, Bai jin kunyar shiga ko wata iri ce da zata nuna tsiricinsa, bai sa suturar kirki sai in takama yafi son yasa sexy underwears sune best dres nasa, hada ƙarin hakan yasa ake kai masa farmaki,
tun da azmee ta ɗago so ɗaya batasake ɗagowa ta kalle sa, sbd tshn hankali, wannan kallonsa ma a wurin mace zai iya zama haramun,
Kujera ya ja ya zauna yana facing kowannansu, shima junaid ya zauna yana ta faman zabga murmushi,
cikin sauri azmee takai hannu zata zari plate ta zuba masa abun sawa abaki , amma abun mamaki sai fawan ya riga ta kai hannu ya ɗau plate ɗin jiki na rawa, ya buɗe warmer ɗin dake ɗauke da farfesun naman shanu, yasa saving spoon ya shake masa plate ya ajiye masa a gabansa, sanna ya haɗa masa da kakkauran tea a gefe,
Ƙiris ya rage azmee ta fashe da dariya, wannan fadancin na fawan ya bata mamaki, Bin su ya ke da kallo ɗaya bayan ɗaya, bayan sun gaishe shi, kowannansu ya shiga taitayinsa, don sun sani sarai bayason hayani ko kɗan, hakan yasa suka rage ƙarar spoon ɗin da hannunsa daga wannan sautin kwas kwas da ya ke yi,
Hannun sa ya miƙa acinkin wani empty bowl, azmee tasanya masa ruwa ya wanke, kafin ya tsoma hanun acikin naman, tsoka ya ɗauke ya jefa a bakinsa, a hankali yake taunarta, yana ci yana binsu da kallo One by one,
Ƙasa ƙsa da murya irfan yayi shi dake kusa da jabir yce "wannan kallon da babban yaya yake yi, bana lpy bane, duk ƴan ciki na sun kaɗa , jabir ya ɗauki cup of tea ɗin dake front ɗinsa ya kare fuskarsa dashi kamr zaisha, sannan yace "kai kenan ma, wlh jiki na kamar na mai zazza6i don fargabansa,' Khadeel dake sauraronsu ya ce"jikin wasu na ƙaiƙayi da alama,'
Sun gane me ya kenufi cikin sauri suka ja baki su kayi shiru, Kowa tsit kamar mutuwa ta gifta, sautin ƙarar cokulan da hannunsu twins yake yi ne (kwas kwas) ya cika masa kunne, ɗagowa yyi ya aza eye balls ɗinsa akansu, zo ka ga tashin hankali, bakomai ya haddasa hakan ba, face kermar da jikinsu ke yi, mirya na rawa ayaan ya ce "mun shiga uku, idon babban yaya akan mu jahan,'
"menene" ya tambaya a ɗan firgice suka ɗago suna Kallansa, ya sake cewa "are u not feeling well ? ganin yadda jikinsu ya ke rawa,
Ido luhu luhu Jahan yace" Ba mu jin daɗi ne, ni da ayaan, "
ɗgowa yusif yyi yana kallansu, jin zasu ja masa bala'e, tun Kan big bro yace wani abu, yusif yayi hnzarin cewa "but why u didnt tel me about ur sick ? ya tambya yana kallansu, cikin sauri ayan yace "dama tun jiya da dare ne, "Atlease u should inform me abt ursick, ko ƙarfe nawa ne zan duba ku ae,? shiru su kayi shi dae Rafayet binsu da kallo kawai ya ke yi kafin ya dakatarsu da cewa "its ok, after we finish the breakfast, yusif makes sure that u check them well,' ".Insha Allah babban ya ya" zuru su kayi jin za'a duba su, Bayan sun san cewa lfyarsu lou,
Mayar da idonsa yayi kan Junaid wanda ke ta faman murmushi, kamar zautacce, ada sun yi tuanin cewa yaron ta6in hankali gare sa, amma da aka bincika sa sai aka tabbatar da cewa haka Allah ya haliccesa wit smiling face,
ɗagowa junaid yayi suka haɗa ido da babban yayan, cikin sauri ya sunnar dakai yana ci gaba da murmushi, Shifa kallon dollar $ ya ke ma yayan nasu, shiyasa murnarsa ta ƙaru in ya kallesa $ kawai ya ke gani a fuskarsa, ya riga da ya kammala lissafin nawa zai amsa da nawa zai kashe wa sehrish ɗinsa 😥
.................SEHRISH........................
A 6angaren sehrish kuwa, zarce wa tayi da bacci, na ɗan mintina ta farka tana sauke ajiyar zuciya, sunan shi ne kawai zuciyarta ke ta faman ambato, idonta takai kan agogon bangon dake manne, ƙarfe 12:30am, ynx sun isa kammala breakfast ɗin,
tashi tayi ta kimtsa, ta fita taga me ke wakana, basa nan ciki duk sun fita, wayam kuma azmee ta gyara ko'ina yayi fess, a kitchen ta same ta, tana wanke dishes ɗin da su kayi amdani dashi, "Aunty azmee sannu da aiki," da fara'a a face ɗinta tace "Yawwa Sehrish ina fata kin washe yanzu,"
Murmushi sehrish tayi tare da cewa "eh Alhamdulillah da wani aiki da zanyi yanzu?. ta tambaya tana kallonta, Azmee tace "a'a yau fa hutu ki ke hajiya sehrish, na ma kammala komai sai zuwa anjima zamu shirya dinner atare amma pls karki maimaita shiriritar ɗazun,"
Ƴar dariya sehrish tayi kafin tace"Insha Allah" ta ɗan yi shiru tana so ta zuba abinci, taci amma ƙunya take ji saboda 6arnar da tayi na zubawa farfesu abun wanki,"
"Ke bakya jin yunwa ne wai? kullum sai na ce ki zuba abinci ki ci, ko saina fara sa miki bulala ne?
Azmee ce tayi maganar cikin zolaya, dariya sehrish tayi da cewa "dama ynx nake so na zuba ne," ƙara sawa tayi ta ɗauko tray, Bin ta da kallo azmee tayi ganin ta jera pancakes, ga sandwich ta kuma haɗa da scrambled eggs, duk a ciki a haka bai ishe ta ba sai da ta hada da fried chicken, taje ta ajiye ta kuma dawo ta haɗa cornflakes a cup ta zazzaga uwar madara, ta tsula sugar, Zama tayi asaman dining chairs ɗin na kitchen tana kallonsu, tunani take da me zata fara, muryar azmee ce ta katse ta da cewa "Sunyi miki haka? Ko zaki ƙara da wani abu ne? 😒 sunnar da kai sehrish tayi cikin jin kunya tace "sun isa haka," Wato su sehrish banza ta samu, dama talaka bai iya samun wuri ba, ni bama wannan ba, Soyayyar babban yaya tasa ta manta da halin da su Hosana ke ciki, ada in zata sa abu mai daɗi a bakinta sai ta tuna dasu tayi kuka sosai, amma ynx ba wannan mgnr, *BABBAN YAYA* kawai 😥
Sandwich ɗin tafara ɗauka tana ci, tunanin ta nakan *RAFAYET* azmee na lura da ita duk wani motsi da sehrish zatayi murmushi take yi, hankalin azmee bai kwanta da irin wannan zauce war da Sehrish tayi ba akan Babban yaya, tabbas soyayyace mai ƙarfin gaske take masa, tunkan tasa shi ma a idonta, da jin sunansa kawai ta faɗa tarko, balle ynx da tasa shi a ido? hakika jikin azmee yayi mugun sanyi tunawa da Junaid, bawan Allah wanda kullum burinsa ya ga yarinyar cikin farin ciki, Babu wanda yasan da zaryar da junaid ya ke yi izuwa ɗakin azmee, kullum roƙonta ya keyi akan dan Allah taba sehrish kulawa ta musamman, komai sehrish take buƙata, tagaya masa zaiyi mata, Junaid ba ƙaramin so ya ke mata ba, 😿 (Tabbas akwai tashin hankali, ni babban damuwa ta, waɗannan zuciyoyin guda biyu ❗‼⁉
Wane hali zuciyar sehrish zata shiga ita da ta kwallafa rai akan mutun da ya kasance misoganist ! ya ƙi jinin mata, baya sha'awarsu basa gabansa, balle ma maganar aure, shin wane hali zuciyar junaid zata shiga ❓shi da bashi da ƙoshin lafiya, ga soyayyar wadda bashi ke gabanta ba, yayansa take so ❗ wane hali hosanna da Jahad zasu shiga in suka amince da bukatar Inspector Eesha!? shin za'a yanke musu hukuncin kisa ne, ko zasuyi zaman gidan yari ne ⁉ 😭😭😭 Me zai faru idan su Aunty Babba Suka ziyarci Bokan nan na dajin enugu wato baba Iblis wanda muddin yayi asiri sai ya ci mutun jazamun, in ba wani iko na ubangiji ba 😿 dole fa ku gyara zama domin yanzu cakwakiyar ta soma 🔥🔥🔥
"Idan kin kammala cin abinci, inaso mu zagaye gidan nan tare dake ki ƙara ganin haduwarsa sosai," murmushi sehrish tayi wadda tuni cikinta ya fara birkice mata dakyar ta iya cewa "tom aunty azmee, amma sai na fara shiga toilet shaf shaf,'
Azmew tace "dama nasan wannan jazamin ne ae, zuba miki ido kawai nayi Allah, ni zan shiga ciki, in kin kammala ki same ni a bedroom ɗina, kyau ma mu fara sallar azhar naga time yayi,"
Sehrish ta amsa da toh, cikin sauri ta kammala, sbd dama a ƙagare take ta zagaye gidan, ta gaji da zama wuri ɗaya, daga bedroom sai kitchen, shaf shaf ta wanke kayan da ta 6ata, sannan ta wuce ɗakinta toilet ta shiga, bayan ta fito da alwalarta tayi sallah, sai wurin addu'a ta tuno da su hosana, tayi musu addu'a sosai, kafin ta cire hijab ɗin ta tura a wardrobe, dama already dress ɗinta na maza ne ajikinta, gashin baki kawai ta aza, tagyara sumar kanta, ta naɗe ta cikin hularnan tashi da kwakwa, daga sama ta bi da mayafi ta yi kamar turban, ta saki jelar mayafin gefe,
A tare da azmee su ka zagaya, sehrish tasha mamaki, ganin haɗuwar katafaren gidan, ko'ina take bi da kallo kamar wuyanta zai 6alle, muryar azmee ce ta katshe ta da cewa "kin ga nan, wurin motsa jiki ne wato gym, bi da kallo sehrish tayi an kawata abun wurin da komai na motsa jiki, kamar ta shiga ta jaraba itama haka taji, amma taci alwashin watarana sai ta shiga ciki tayi gym itama,
gaba su kayi suka sake zuwa wani room ɗin, "nan kuma ɗakin bincike kenan ," jinjina kai sehrish tayi ganin wasu matsiyatan Computers gava ɗaya na'urori ne a ɗakin ke sarrafa komai, wurare daban daban ta nuna mata Hada weapon's room ( ɗakin ajiye makamai) , hada haɗaɗɗen parlor wanda suka ware domin yin kallo acikinsa, an ƙawata shi da faskekiyar plasma tv, ga speakers na sauti, ga ƙawatattun kujeru aciki da sauransu,
daga nan suka fita can harabar wajen, sehrish tasha kallo sai taga kamar tabar 9ja ne, saboda cikin gidan duniya ne, bakomai ya ƙara burgeta ba face swimming pool ɗin da tagani, mai faɗin gaske ruwan ciki yayi blue sky, daga gefe a hada kujerun shakatawa da table, bata ga komai ba sai da su ka shiga garden Aljannar duniya, juyawa tayi ta kalli azmee tare da cewa "har yanzu muna cikin nigeria"? dariya azmee tasaki tare da cewa "of course," jin jina kai tayi wasu komai na cikinsa kore ne 🌲, sai aka ƙawata shi da Red & yellow flowers 🌹🌻, ga wani tsaftataccen ruwa dake guda na (waterfalls) yana gangarowa daga jikin dutsi zuwa ƙasa ya taru acikin pool yyi kamar lakes, Bakomai ya burge sehrish ba face agwagin dake ciki suna yawa farare,
"Aunty azmee gaskiya gidannan ina kokwanto anya ba hotel bane, girmansa da haɗuwarsa yayi yawa," tayi maganar tana kara bin ko'ina da kallo, azmee tace "haryanzu fa akwai sauran wuraren da baki gani ba, ynx dai na gaji mu zauna mana,
Wuri suka samu asamn garden chairs ɗin suka zauna auna facing juna, bin ta da kallo azmee tayi ganin tana ta faman murmushi, wato bakomai sehrish ke tunani ba fa ce ranar da zasu fara magana da baban yaya harsu shaku ssae su rinka zuwa garden ɗinnan atare suna kewaya wa, lumshe idonta tayi sbd wata iska da ta ratsa ta, aranta tana cewa "Ya Allah ka nunamin wannan ranar da raina da lafiya ta, ni da shi atare muna strolling Cikin farin ciki," 😥
"Me ki ke tunani ne"? Firgit sehrish ta yi jin maganar azmee a dodon kunnanta , cikin sauri tace "bakomai kawai ina mamakin haɗuwar gidan nan kamar a mafarki," Murmushi azmee tayi sbd sarai ranta ya bata cewa, tunanin ta na babban yaya ne,'
"Estate za'a mai dashi" cikin mamaki sehrish ta ce "dagaske aunty azmee? Amma zai fi kyau wlh girman yayi yawa," Azmee ta ce "eh naji da jima wa abbansu ya faɗi cewa za'a ƙara wasu part ɗin, yana so zai ware ma kowannansu nasa saboda baison in sunyi aure suyi nesa dashi, yace duk wanda yayi aure zai dawo ciki da matarsa, duk da sun mallaki gidajensu nakansu, amma shi yafi son hakan," Wani daɗi ne ya rufe sehrish, kamar anyi mata albishirin cewa itama zata kasance ɗaya daga cikin surukansa da zasu zauna agidan, 😒 Bayan sun ɗanyi shiru na wani lokaci azmee tace "i have something to discuss wit u,' "Menene aunty azmee" sehrish ta tambaya da ɗan mamaki a fuskarta, "Ko kinsan cewa a cikin sojojin gidan nan akwai wanda yasan cewa ke maca ce ba namiji ba !!" A firgice sehrish ta mike hannu dafe da kirji tace "Who"? fuskarta da tsananin tsoro, Dariya azmee tayi kafin tace " zan faɗa miki but firstly ina so ki mun alƙawarin cewa u will calm urself," Jiki a sanyaye ta koma ta zauna zuciyarta na bugu, tsoranta kar ace cikin jarababbun ne wato Fawan ko Twins,
"Aunty azmee wanene dan Allah.. .." tayi maganar tana haɗiye yawu, Murmushi azmee tayi kafin tace "king of smile" "Wanene haka azmee"? Ta tamvaya da mamaki, "Oh baki gane ba tom nabaki satar amsa kije ki gano waya dace da sunan,' duk iya tunanin sehrish bata gano wa azmee take nufi da *King of smile* ba, takasa samun natsuwa ta gano sa, sun jima suna fira bfr su koma ciki donyin sallar La'asar, *💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
~🔥the father of soldierd🔥~?
💋💋💋💋💋💋💋💋 ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ💞💞💞💞💞
ﻗﺼﺔ ﻛﺘﺒﻬﺎ ﺣﻔﺼﺔ ﺑﺎﺗﻮﺭ🌹🌹
_Story & written by_
*Hafsat Bature Moh'd*
~BossLady~ 💋
*page 68*
..........SEHRISH........................... bayan ta kammala sallar la'asar, kimtsawa tayi kafin ta fito ta wuce kitchen tayi mamakin jin shiru alamun duk sun fita ne, tunanin ta ko'ina Babban yaya ya ke, ta lura baya fita sai dai azo a same shi in da ya ke, tun kafin azmee ta iso, sehrish ta fara ɗauko abubuwan da zasu yi amfani dashi, doya ta fara ferewa tasan suna yawan amfani da ita, tana aiki tana ɗan murmushi, sa6anin da tana aiki cikin damuwa saboda tunanin halin dasu Hosana da Jahad su ke ciki, zuwan big bro ya canzawa sehrish rayuwa gaba ɗaya,
Sam bata ji shigowar azmee ba, sai dae muryarta taji "Sannu da ƙoƙari rishi hakan ya burgeni," murmushi sehrish tasaki tare da cewa "Yawwa aunty azmee ina wurina," "Lafiya lou ta faɗi tare da shige wa ciki domin fara gudanar da aiki, cikin lokaci ƙankani kitchen ɗin ya fara kamshin abinci,
"Wani kalar abinci ki ka fi so"? Azmee ce ta jefa mata wannan tambayar yayin da ta ke zuba kayan ƙamshi acikin sauce ɗin da ɗaura, sehrish tace "farar shinkafa da jar miya ina son abincin nan sosai aduk lokacin da akayi mana shi a gida zumuɗi muke yi kamar hauka saboda muna jimawa bamu ci ba, shine abinci mafi daɗi a wurin mu," ta karasa maganar muryarta a sanyaye ba don komai ba sai don tuna wa da hosana, a lokacin da su ke tare da mahaifiyarsu duk in akayi musu tuwo tafi kowa mita ta rinƙa sababi tana cewa "oumma wai mu kullum tuwo kullum tuwo, da rana ayi tuwo, da daddare ma tuwo, in safe tayi ma ɗumamen tuwo, ni wlh nagaji zanje gidan makwabciya in ciyo shinkafa da jar miya hada ma wasilla zata samun, "
Hawaye ne suka soma koƙarin zubowa a fuskar sehrish tunawa da rayuwarsu ta baya,
"Ni kuma nafison Tuwo arayuwata miyar ku6ewa da busasshen kifi wayyo daɗi in inaji kunne na har motsi ya keyi, musamman in ya kasance ɗumame ne,"
Azmee sai zuba ta keyi sam bata lura da sehrish ba wadda, take matsalar kwalla, jin shesshekar kukanta yasa azmee saurin ƙarasowa inda take tana faɗin "subhanallahi sehrish meke faruwa ne ? Cikin sauri sehrish ta dai dai ta natsuwarta, Murya na rawa tace "ba komai aunty azmee, zafin albasar da nake yankawa ne, ya shiga ido na,' "Eyyah sannu barshi na ƙarasa kawai," "A'a aunty azmee aikin zaiyi miki yawa, zan idasa,' "Sehrish akwai ayyuka dayawa ba dole sai wannan ba, kibarmun yankar albasar ki kula da miyar dana ɗaura," "Shikenan aunty azmee amma kafin nan, ayimun uziri zan shiga toilet," "Shikenan ba damuwa kije kawai,"
Cikin sauri sehrish ta fice, saboda tana so tasamu space ta matse hawayen dake son zubo mata, tana shiga bedroom ɗinta, ta fashe da matsanancin kuka, a gefen gado tazauna tana matse hawaye, Cikin murya kuka tace "Ya' Allah ka karemun ƴan uwana, aduk inda su ke, ka sauƙaƙawa rayuwarsa, Hosana da jahad kowane yanayi zan shiga na rayuwa duk mun daɗinsa I will neva forget about you, i will keep praying for u till d rest of my life 😭
haka ta dinga addu'o'i akansu, sai daga baya ta tuna da azmee wadda ta baro a kitchen tana aiki, cikin sauri ta shiga toilet, agaban wash basin ta tsaya, ta kunna fanfo ta wanke face ɗinta sannan ta fito,
ƙarar shigowar motoci taji, a lkcn da take ƙoƙarin barin ɗakin, nata cikin sauri tadawo ta tsaya agaban window ɗin da tasaba leƙe, janyen labulen tayi ta zuge glass ɗin tana kallonsu,
Motocinsu ne a jere, bayan sunyi parking wani Soja black american gabjejan gaske, ya fito ta gaba tare da buɗe mashi mota, a hankali ya zuro kafarsa dake sanye cikin slippers ɗin *Gucci* sun hau ƙafarsa raɗau ba ƙaramin kyau su kayi masa ba, idasa fitowa ya yi zuba mishi ido sehrish tayi sam batasan time ɗin daya fita ba, ashe baya gidan, Sanye ya ke da V-neck shirt light green color, sai dogon wando Army trouser, surar nan fa tafito raɗau bai matuƙar jan hankali, sumar kansa mai tsayin nan tasha gyara na musamman ta zubo masa abaynsa ya ɗaureta, Ba shi kaɗai bane tare da abbansu su ke, da Kanal yusif, gaba ɗaya jikin Sehrish ya gama mutuwa, zuciyarta ta gama narkewa, tafiyarsa ma kawai abun kallo ce, ta majiya ƙarfi *Rafayet* tamkar Zaki ya ke, wanda ke mulkar namun dawa a ƙarƙashinsa, Zuge glass ɗin window tayi, tare da cije le6enta, sam bata gajiya da kallonsa, cikin sauri ta fito ta wuce kitchen saboda tasamu damar ƙare masa kallo in sun shigo,' "Sannu da dawowa ya idon nake"? Azmee ce tayi mata wannan tambayar, "Alhamdulillah ae sun dawo dai dai aunty azmee," sai faman murmushi take tana ƴan kame-kame, Shigowa su kayi atare suna ɗan ta6a fira, anan main palor ɗin suka samu wuri suka zauna, abbansu na facing ɗinsu yayin da shi da Kanal yusif suke zaune a 3 seater, Murmushi abbansu ya ke ta faman saki ba don komai ba sai don jin daɗin zuwan Babban yayan, musamman yau da suka yawata atare, duk da kin sakin fuskarsa da kuma ƙarancin maganarsa, _muryarsa tsada gare ta, saboda daɗinta shiyasa wata'kil ya ke rowarta_ (nace ba, da zai faɗi farashinta dana ƙulkula nasiya😂)
Hannunsa na riƙe da wayarsa, yana daddanawa, bazan faɗi ƙirar wani company bace, sbd wata irin haɗaɗɗiyar waya ce, very expensive wadda takasance mallakinsa, kuma sunan sane ajikinta wato (SGR) ba mai iya controlling ɗinta sai shi duk bala'in mutun, saboda sometimes da Voice ɗinsa take amfani, daga ya faɗi abu zata nuno masa, 😔
gyaran murya abbansu ya yi tare da cewa "Ina magana," a hankali ya ɗago da sexy blue eyes ɗinsa ya aza akan abban nasu tare da cewa "Am all ears," Abba yace "Ina so kayi mun promise ɗin cewa har ka bar nigeria, bazaka ta6a kowa ba kayi shiru da bakin ka salin alin ka tafi cikin salama dan Allah,' wani irin kallo babban yayan ya ke wa abban nasu jin abunda yace, hannu ya kai tare da ajiye phone ɗinsa saman table ɗin da ke front ɗinsa, ya jingina bayansa jikin royal sofa ɗin, tare da aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya, duk abban nasu na kallonsa burin sa ya ji amsar da zai basa, murmushi kawai kanal yusif ya ke yi wanda ke ta faman danna wayarsa, amma kunnansa nakan maganar da suke yi, ɗan ta6e small lips ɗinsa ya yi kafin yace "*IMPOSSIBLE*" atakaice, Sauke ajiyar zuciya abban yayi dama yasan amsar kenan, Cikin takaici yace "Oh sai kayi kenan"? "Eh" ya bashi amsa ba wasa, Jinjina kansa yayi tare da cewa "ni narasa gane tsakanin kai da Momynka Alexandra waya fi wani taurin kai, kafiya da ji da izza,' da buɗen bakin babban yaya sai cewa ya yi "Ita,"