Abban sojoji complete book 1 by boss bature - Chapter 21
Abban sojoji complete book 1 by boss bature Chapter 21: Abban sojoji complete book 1 by boss bature Chapter 21.…
4,210 words
....................SEHRISH...................... Tsaye take tana leƙen su junaid dake buga ball a cikin filin kwallon dake a gidan , ta cikin window take leƙensu, tana murmushi, tashin ta kenan bayan ta koma baccin da suka kammala breakfast, Jersey ɗin dake jikinsa ba ƙaramin kyau su kayi masa ba, abunka ga farar fata, yellow ne kayan kwallon sai faman tsalle tsalle ya keyi, dama shi indai wurin wasa ne da ci a nan yafi auki, Tare da wasu daga cikin sojojin dake tsaron gidan suke buga ball ɗin, dariya kawai take yi masa, ganin sai zura wa da gudu yake yana taro ball ɗin su kuma suna kwace ta, tunano wa tayi da farkon zuwanta gidan, lokacin da motar Hajajju ta shigo da ita cikin gidan, tabbas tagansu a time ɗin suna buga wasan kwallo, kamar yadda dae take kallonsu a yanzu, amma awancan lokacin, shi dasu twins ne da fawan suke kwallon, sa6anin ynx da masu gadin gidan suke buga wasan, "Allah sarki junaid, ji bi yadda yake ta faman shan wahala wurin taro ball suna kwace mashi, maimakon yaji haushi amma sai faman murmushi ma yake yi, shi dae baya gaji da murmushi a face ɗinsa," Tayi maganar nan a lokacin da take ƙoƙarin zuge glass ɗin windon, ta janyo labulen ta rufe, tana sauke ajiyar zuciya, tunanin ta ya koma kan Babban yaya wanda tun da safe take jiran saukowarsa, amma bai fito ba, ko breakfast bai sauko ya ci ba, hakan yasa ta cikin damuwa sosai, "Bari dae na fita naje na tambayi aunty azmee, ko naje na tashe shi in bacci ya ke yi "? tayi maganar a fili, cikin sauri ta ƙarasa saman bed ɗinta, ta ɗauki dogon wandonta ta zura, dama daga ita sai riga dai-dai guiwa, Gashin bakinta kawai ta ɗauko a saman mirror, ta maƙala shi kafin ta fice daga ɗakin, A hankali take tafiya, a main parlor ɗin ta hangi su Abbansu tare da wani Amininsa Alhajin gaske daya kawo masa ziyara, Su biyu suna tattaunawa, saɗaɗawa tayi ta wuce kitchen, anan ta sami aunty aunty azmee tana shirya musu drinks a tray, cikin wasu kofuna masu kyau, "Yauwa rishi dama yanzu nake ƙoƙarin zuwa na tashe ki, kin barni da aiki ko," ? ta tambaya tana kallonta, Cikin jin kunya Sehrish tace"Am sorry aunty azmee wlh, ina shiga bedroom ɗina naje na watsa ruwa, kawai sai bacci 6arawo ya ɗauke ni," Dariya azmee tayi azmee tayi tare da cewa "Bacci 6arawo ko? mutun yaje ya saki baki yana bacci, kuma yazo yace wa mutane wai baisan ya akai bacci ya ɗauke sa ba,' Murmushi sehrish tayi tare da miƙa hannu ta kar6i tray ɗin da azmee ke miƙa mata, Amsa tayi tana cewa "Aunty azmee wanene baƙon da yazo "? "Ki je ki tambaye sa mana, ki ce wanene kai zai baki amsa," Dariya sehrish tayi jin amsar da azmee ta bata, ɗan zaro ido tayi tare da cewa "tab dana sha mari wlh," Azmee tace " ba wani mari wlh, amsa kawai zai baki da yaren da zaki gane," "Ae wannan bugu kenan," ta faɗi tana kokarin fita, har ta sa kai zata fice ta kuma juyo wa tare da cewa " Aunty azmee babban yaya fa, bai fito daga bedroom ɗinsa ba ko lpy,"? "Ki je part ɗinsa mana ki tambaye sa," ta faɗi cikin zolaya, ɗan ta6e baki sehrish tayi tana jinjina kai tace "wai Allah ! ni asuwa? ɗan wake a hotel,"? dariya azmee tayi tare da cewa "ynx dae kije ki kai musu, kin tsara surutu kamar ƴan jarida, " Cikin sauri sehrish ta fice izuwa cikin main parlor ɗin, cikin natsuwa take tafiya tunkan ta isa, tajiyo muryar abokin abban dayazo yana cewa "Ae ni ba ƙaramin daɗin zuwan nan nasu Rafayet da Omar naji ba, koba komai kafin su koma U.s zasu gyara wa wasu zama A Qasar nan," Abba yace "Oh damuwarka kenan, baka damu da bala'en da zai jawo mun ba, kwarama Omar shi da sauƙi, amma rafayet kana ganin last da yazo ya rinƙasa ana kawo masa ƴa'ƴan mutane har cikin gidan nan yana hukunta su, babu yadda zanyi dashi, sai dae nabishi da ido kawai, saboda yafi ƙarfi na,' Dariyar Alhajin yayi tare da cewa "Ae samun ƴa'ƴa kamar Omar da rafayet wlh abun alfari ne, kowane Uba zai so ya mallaki ƴa'ƴa irinsu, gashi ynx asanadinsu darajarka da ta family ɗinku ta ɗaukaka sosai a faɗin duniyar nan, Kowa yabonsu ya ke yi, yakamata karinka alfahari dasu, mu gana mu nan ƴa'ƴan shaggu kamar mata, basa iya ta6akawa ƙasa komai, ga Jabeer nan har asibiti na gina masa in yadawo daga Uk ya ci gaba da kula dashi, amma yaron nan ya watsa mun ƙasa a ido, wai shi yafin karfin ya yi aiki a nigeria, Naji haushi lokacin duk mun lalacewar kasarka ae ƙasarka ce," Cikin nuna takaici Alhajin yakewa Abban wannan bayanin da sallama Sehrish taƙarsa cikin girmamawa ta gaishe su, suka amsa mata sannan ta miƙa musu drinks din suka ɗauka suna sa mata albarka, bayan sun gama ta kama hanyar komawa cikin kitchen, wani irin son Babban yayan ne ya kara shiga ranta, jin yadda Abokin abban nasu ke yabonsa, murmushi kawae take saki, ynx ta kara jin ya kwanta mata luf acikin ranta, Shiga kitchen ɗin tayi tare da ajiye tray ɗin, azmee tace "yanzu sai ki je, ki gyara masa part ɗinsa ko? tayi maganar tana kallonta, Sehrish tace "Yana fa ciki, kuma kince baisan atashe shi yana bacci, kuma baisan ƙara, in nayi kwaratsi fa zai ji harya farka,"
Murmushi azmee tayi tare da cewa " to ina ruwanki da bedroom ɗinsa? Falonsa zaki fara gyara wa, kafin ya tashi sai ki gyara can ɗin ko ? Sehrish tace "To bari nace" tafice tana fargaba, tana jiyo muryar Aunty azmee tana cewa "Anaso ana kaiwa kasuwa," Ƴar dariya tayi tare da fi ce wa, kai tsaye part ɗinsa ta wuce zuciyarta na ɗar ɗar, Kamar kullum a buɗe door ɗin parta ɗinsa take, a hankali tashiga tana sanɗa kamar 6arauniya, Sai da tayi tsakiyar falonsa nasa tasoma tunanin wai me ma tazo yi? Saboda ko'ina agyare yake tsaf ba datti ko kaɗan, sai walwali wurin yake har yau tana jinjinawa haɗuwarsa, Murmushi tasaki tana wani tunani aranta, wanda bazai yiyu ba, 😔 Sai da tagama zagaye falon nasa tana tunani iri iri aranta, sannan ta soma gyara sa, babu wani aiki awurin, kawai ta ɗan yi goge goge ne, tsayawa tari riƙe da waist ɗinta, so take ta sashi a idonta, zuciyarta ce ta bata shawara da cewa "ki ɗan leƙa sa, mana,"
"Anya? idan kuma idonsa biyu fa? In ya kama ni karairaya ni zae yi Allah,' ta bata zuciyarta amsa,
"Ke sai ki bari ya ganki? Ae lalla6awa zakiyi a hankali sai ki dan leƙa,'
Murmushi tasaki tare da tafiya cikin sanɗa, ta tsaya a bakin ƙopan ɗakin nasa, taci sa'a kopan a bude take, curtains ɗin ta ɗan janye tana leƙensa, 👀👁️
Kwance ya ke yana sharar baccinsa, cikin natsuwa a saman Royal bed ɗinsa, kai ka ce da zallar gold aka ƙera gadon, yadda ya ke wani kyalli ajikinsa,
Half body ɗinsa yayi covering ɗinsa da lallausan blanket, hannunsa na dama, ya zagayo dashi har izuwa saitin left ear ɗinsa, yayin da hannunsa na hagu kuma ya ke a saman wide chest ɗinsa,
Bin shi take da kallo kamar kura taga nama, wannan haɗaɗɗiyar sumar tasa, ta rufe masa half face ɗinsa, dogon hancinsa kawai take hange, Lumshe ido kawai take, ita kaɗae tasan yanayin da ta shiga, Tana cikin wannan leƙen nasa ko ƙeftawa babu, taji an shaqi wuyanta da ƙarfin gaske, Shaqa ba ta wasa ba, Wani irin tsoro ne ya ziyarce ta, hankali atashe ta zazzare idanunta, Muryarsa ce ta ratsa kunnanta da cewa "meyasa ki ke leƙe na !!"? wata irin zufa ce ta wankowa sehrish, tsananin tashin hankali ne ya bayyana a idonta, lokacin da ta lura cewa babu shi asaman gadon nasa, yaushe har ya sauko yakuma wuce ta, ya zagayo ta bayanta,harya shaƙi wuyanta, Wani irin fitsari ne mai zafin gaske ya kufce mata, ji kake zirrrrrrrr yana zubo mata, Muryarsa ce ta sake karaɗe kunnanta, " baza'a bani amsa ba" 😳😳😳😳😳😳😳
*Hafsat Bature Moh'd Boss Lady* 💋✨👏 *I Need your prayers urgently* 😔💕💞💕💞💕💞💕💞💕💞💕💞
*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
_💞Extraodinary Love💞_
*Writer✍️✍️✍️✍️*
*💋HAFSAT BATURE BATURE BOSS LADY💋*
Full episode
~Page 73 -74
End of Chapter 1
*✨✨LAFAZI WRITERS ASSOCIATION* ✨✨
Not edited 😎
Jin shiru ba ta da niyar bashi amsar yasa shi harya fusata, a wani irin zuciye ya buga kanta jikin kopan da ƙarfin gaske, nan take sehrish ta fasa wata irin azababbiyar ƙara mai sauti tare da faɗuwa yaraf a sume, Wannan sounds ɗin da sehrish ta fidda ne ya farkar dashi daga dogon baccin da ya ke yi, a hankali yake buɗe eyes ɗinsa yana yamutsa fuska agajiye blue eyes ɗinsa na facing Ceilling,
Hankali tashe sehrish ta farka daga nap ɗin daya dauke ta, sai uwar zufa ke zubowa daga cikin sumar kanta, ashe bayan ta kammala gyara masa parlor insa bacci ne ya ɗauke ta a nan kasan lallusana carpet ɗin dake shimfiɗe, sai faman zazzare kyawawan idanuwanta take, tana shasshafa jikinta don ta tabbatarwa da kanta cewa mafarki ne take ba gaskiya ba,
Ajiyar zuciya ta saki tare da faɗin "Alhamdulillah Allah na gode maka," cikin hanzari sehrish ta miƙe tare da fice wa daga part ɗin nasa ta koma kitchen , Shiru tayi tana ƴan kame kame ashe tun ɗazu azmee na zaune tana jiran.dawowarta, Tana zaune saman daya daga cikin dining chairs dake a kitchen ɗin, ga tray da ta kammala shiryawa babban yayan breakfast ɗinsa ajiye a saman table ɗin gabanta, ta zabga tagumi tana jiran Sehrish, Bin ta tayi da kallo ganin yadda ta shigo a hargitse tana wurwurga ido, "Sannu ko'? Shanyar da ki kayi harta bushe," ta faɗi tana kallon ta, Sunnar da kai sehrish tayi tana wasa da fingers ɗinta tace "Am sorry aunty azmee wlh bacci ne ya kwashe ni a falonsa without my knowing...' tunkan ta ƙarasa azmee ta katse ta da cewa "bacci !!! A part ɗinsa!? Kin sha giyar wake ne?anya ko kinsan wanene SGR kuwa? You ave to be very careful sehrish, don't let that happen again if not u will Explain it !!," Azmee ta faɗi cikin faɗa faɗa, hakan ba ƙaramin tayarwa Sehrish da hankali yayi ba, ta tsorata sosai tuni eyes ɗinta sun cicciko da kwalla," . "Aunty azmee tsotsai ne, ba da sani na ba nima, wlh sharrin shaiɗan ne," Sototo tayi da baki tana kallonta cikin takaici tace "na gane Ki sehrish whenever u did something wrong sai ki ce sharrin shaiɗan ko? ga iya bada hakuri kamar matar aure tagari,' duƙar da kai sehrish tayi, jikinta ya gama mutuwa jin aunty azmeenta nayi mata faɗa, ganin halin da sehrish ta shiga yasa azmee sassautawa da murya cikin lallashi tace "Sehrish ba faɗa nake miki ba, i just wanna u to be very careful in this home, bana so asamu matsalar da zata sanya a kore ki daga aiki, Babban yaya da kike gani mutun ne mai hatsarin gaske !!!, sai kin kula," Cikin sauke ajiyar zuciya sehrish tace "Shikenan aunty azmee, insha Allah zan kula, i won't let that happen zanyi komai yadda ki ke so," Murmushi azmee tasaki tare da cewa "yawwa my daughter, ko da yake nafiso nace ƙanwata hakan yafi mun daɗi, yanzu dae ɗauki breakfast ɗin nasa ki kai masa," "Tom aunty azmee," sehrish ta faɗi tare da sa hannu ta ɗauki tray ɗin, da ƴar fara a a fuskarta ta fice daga kitchen ɗin, A natse take tafiya, zuciyarta na bugawa especially in ta tuna abunda Aunty azmee ta sanar da ita nacewa he's a dangerous man, hakan na kara tsoratar da ita, tana cikin tafiya taji dirar Ball a ƙasan kafarta, ƙiris ya rage ta saki tray ɗin saboda ta tsorata, bin ball ɗin tayi da kallo kafin ta ɗago taga wanene ya jefo mata ita, Sai faman murmushi yake ta saki, kamar gonar auduga, bawan Allah yasha wahala, kwallo kamar ibada duk zufa ajikinsa sai wanko masa face ɗinsa take, "Junaid" ta faɗi acikin zuciyarta, a fili kuma sai cewa tayi "Sannu da dawowa" Sam yaki mata magana, tun da yasa ta a idonsa, notikan kansa suka kwance, zallar ƙaunarta ce ke gudana a cikin zuciyarsa, karasawa yayi tare da duƙawa Yayi yakai hannu ya dauki ball ɗinsa, sannan ya ɗago tare da aza eyes ɗinsa cikin nata yace "Yunwa nake ji, ashirya mun snacks akawo mun a bedroom ɗina tare da coffeee i wll be waiting,, ya ƙare maganar yana kashe mata jiki da wannan smilling ɗin nasa, Ita ma kanta batasan time ɗin da, ta shiga mayar masa da martani ba, na murmushinsa, tarasa dalilin dayasa take jin wani sanyi a ranta aduk lokacin da idonta suka shiga cikin na junaid (Why?) daker ta amsa Iya amsa masa da cewa "insha Allah ynx zan kawo," "Ok" ya faɗi tare da bi ta gefenta ya wuce upstair duk tana, a tsaye tana kallonsa, ƙiriniyarsa na burgeta sosai,ko tafiya yake yi yana dan tsalle haka, . Sai da junaid ya 6ace mata, sannan itama ta wuce sashen sgr , Time ɗin da ta karasa a bakin kopan sai da ta tsaya ta karanta addu'o'in neman tsari da sharrinsa sannan, ta shiga ciki da sallama, Ba zato ba tsammani taji wannan sanyayyiyar muryar tasa so sexy ta amsa mata da cewa "Wa'alaikam salama," Wurgo ido tayi ta hangosa kishingiɗe saman royal sofa ɗin doguwa, kansa na saman hannun seater ɗinta, yayin da idonsa ke kan Laptop ɗinsa wadda ya aza ta saman stomach ɗinsa, kasancewar yana daga kwance, jikinsa na sanye da jallabiya fara, masha Allah kyau iya kyau, ba'a magana, masu sa kyau tayi kyau ba 😂 Jikinsa sai kamshin turaren imperial majesty ke tashi, wani irin daddaɗan kamshin kasancewar duk wani lotion da soap da yake using dasu bama perfumes ba kaɗae masu kamshi ne na fitar shari'a, kasancewar shi, ma'aboci son ƙamshi ga tsafta, Lumshe ido sehrish tayi, tana jin wani irin heart beating, kamshin sa na rikitar da ita, A hankali take tunkararsa, sai da taje dab dashi sannan murya na rawa tace "Gm sir," shiru bai bata amsa ba, hakan yasa ta jin fargaba, Zuru ta ɗanyi tana tunanin kawai ta ajiye masa ta fice, har time ɗin eyes ɗinsa nakan Laptop ɗinsa yana daddanawa, har ta ja da baya zata ajiye masa tray ɗin a samar tables ɗinsa muryarsa ta ratsa ta da cewa "Is this the right time daya dace a kawo min breakfast ɗina "? Shiru sehrish tayi gabanta na faɗuwa, a cikin zuciyarta kuwa tsantsar tashin hankali ne, tabbas akwai matsala, saboda ita azmee ta sanar da ita cewa ba'a tashin shi daga bacci in yana yi, and now kuma yana complain ba'a kawo masa breakfast ɗinsa da wuri ba? to tayaya mutumin da ba'a tashin sa daga bacci zaisan ankawo masa breakfast ɗinsa da wuri !!!? wannan jinkirtawar da tayi bata bashi amsa ba, ya sashi fusata, aiko tana a tsayan nan ba ta lura ba, ya ƴunƙura yasanya ƙafarsa da karfin gaske dama ga tsayi ya harba tray ɗin dake hannunta, nan take komai ya kife ƙasa, ya tarwatse food warmers ɗin da sauran tarkacen, zaro ido tayi tare da dafe ƙirji gabanta na faɗuwa, tsananin tsoro ne ya bayyana a fuskarta, Cije lips ɗinsa kawai ya keyi, ganin koma wanene yaƙi moving, wani irin motsi taji bana wasa ba, aiko da gudun gaske ta fi ce daga falonsa, wato da ace sehrish tabari wannan motsin da taji yayi da ba ƙaramin naushi zai kai mata ba, Kamar daga sama su ka ci karo da azmee wadda ke ƙoƙarin Fitowa daga kitchen ɗin, tana ganin sehrish gabanta ya faɗi, aranta tace "yayi tsiyar," Fashewa tayi da matsanancin kuka a lokacin da taganta, agaban azmee jikinta har wani jijjiga yake yi, sai kerma la66anta ke yi, Hankali tashe azmee tace "menene sehrish me ya faru,? ta faɗi tana jiran bayani daga wurinta, daker kukan da sehrish take yi ya tsagaita, cikin matsanancin kuka take korawa azmee bayani, " ...aunty ..azmee...baaa...ke ki ka ce ba'a tashin sa daga bacci ba....ynx fushi ya keyi ba'a kai masa breakfast ɗinsa da wuri ba..ba ki ga yadda yasa ƙafarsa ba ya harba tray ɗin abincin komai ya watse, bansan ya zanyi ba," tana magana tana yarfa hannu, sai faman jan majina take yi, duk ta firgice, Shiru azmee tayi saboda dama ba wannan ne karo na farko da yake faɗin cewa ba'a kaimasa breakfast ɗinsa da wuri ba, gashi mafi yawancin lokutta bacci yake yi, kuma ba uban da ya isa ya tashe shi yana bacci, saboda kamar ɗan wrestling haka yake, Naushi yake kaiwa, gaba ɗaya kannensa su fawan dasu Irfan ba wanda baije tashe shi daga bacci batare da ya naushe shi ba, shiyasa kowa yayi nesa dashi, ake barinsa sai ya kammala baccinsa ya tashi dakansa, sannan kuma ya hau jarabar ankai masa karin kumallonsa a makare," "Aunty azmee ba ki ce komai ba, ya zanyi? gashi can ya 6arar da abincin shima wata matsalar ne, ya za'ae abashi hakuri na samu naje na kwashe wanda ya zubar na zuba masa wani"? ta ƙare maganar tana kallon azmee wadda tayi zuru cikin rashin sanin mafita, yarfa hannu azmee tayi tare da cewa "wlh nima bansan menene solution ba, mutun ɗaya ne zai iya shawo kansa, kuma ba kowa bane face Junaid...."
"Naji kamar ana maganata a wurin nan," junaid ne yayi maganar wanda ke saukowa daga saman stair ɗin, jikinsa sanye da jeans da farar t shirt, Bin su yayi da kallo musamman sehrish wadda ke tsaye, ido luhu luhu tasha kuka, yau taga tashin hankali, Ajiyar zuciya Azmee tasaki ganinsa cikin sauƙi, "Junaid matsala aka samu," azmee ta faɗi tana kallonsa,. "Meya faru"? Ya tamvaya yana kallonsu," Nan azmee ta kwashe dukkan abunda ya faru ta sanar mishi, kamar yadda sehrish ta faɗa mata," Murmushi yasaki tare da kallon sehrish wadda ta sunnar da kanta kasa, yace "Calm down ur mind, in dai Babban yaya ne, ni ne controller ɗinsa, just wipe ur tears," ya faɗi yana nuna tears ɗin dake zubowa daga eyes ɗinta,.
Hannu tasa tana goge su kamar yadda junaid ya bata umarnin ta share su," Sannan yace da aunty azmee "a shirya masa wani breakfast ɗin, ynz zan zo na karba," yana gama faɗan hakan ya juya tare da wuce wa izuwa upstairs part ɗin Sgr," "Yanzu sai kiyi murmushi, junaid da ki ke gani shine masarrafin babban yayansu, shi ke juya shi kuma ya juyu," azmee ce tayi maganar tana kallon sehrish, Ita dae har yanzu bata dawo cikin hayyacinta ba, ta jima tana mamakin abunda sgr yayi, yadda ya hauro da ƙafarsa ya harba tray ɗinta ya kife kasa ba ƙaramin mamakin hakan tayi ba, maimakon taji haushinsa, sai ma taƙara jin ƙaunarsa na ninkuwa azuciyarta 💋 Da sallama junaid ya shiga falonsa yana faɗin " babban yayan mu, gani na iso, nazo na takura maka na hana ka sukuni," Jin Voice ɗin junaid yasa, Rafayet tashi zaune daga kishingiɗen dayake, ya mayar da laptop ɗinsa, saman desk ɗinta, a hankali ya ware idonsa akan junaid tare da cewa "sai ynx zaka so wurina? Ina ta fama da yunwa arasa wanda zai tashe ni ko"? yayi maganar yana lumshe sexy blue eyes ɗinsa,. da murmushi junaid ya karasa yana faɗin "am so sorry babban yayanmu, kaima kasani, na damu da cikin ka sosai, shiyasa ko breakfast banyi ba tun safe, kai kawai nake jira ka farka muci atare" ya karasa maganar tare da russinawa ya rungumosa sannan ya manna masa kiss a gefen face ɗinsa, Lumshe idonsa yayi, har cikin zuciyarsa, tsananin kaunar yaron ya keyi ba don komai ba, sai don kasancewarsaa mai tsananin biyayya ga iya magana, minti 5 yayi yawa ga junaid ya sace zuciyar mutun especially da wannan murmushin nasa, shiya sanya Hafsat bature ta kamu da tsantsar ƙaunarsa 😥 Juya wa junaid yayi ya kalli, tray ɗin da babban yayan nasu yayi watsi dashi a ƙasa, cike da daɗin baki yace "subhanallahi ya akai kayan abincin nan suka zube ƙasa, ni nasan aikin tukur ne bari na kwashe na canza wani," Ya karasa ya zuƙunna yana tattare kayan, duk rafayet nabinsa da ido, sai da ya kammala kwashe komai ya mayar acikin tray ɗin sannan ya ɗauka yana cewa "am coming now yayanmu," Sannan ya fice, ajiyar zuciya yasaki lokacin da ya fito daga part ɗin nasa, kitchen ya wuce, azmee kaɗai yasamu aciki ta kammala hada masa wani bf ɗin acikin tray, Miƙa mata na hannunsa yayi ta karba sannan ya ɗauki wanda ta haɗa masa asaman table, ya dago yana kallonta yace "Ina Sehrish take,"? Murmushi azmee tayi kafin tace "ta tsorata ne sosai, ta koma ɗaki ynz," . Yace "ok amma aunty azmee yaushe zaki faɗa mata cewa nasan cewa ita maca ce ? Inaso tasani pls !" yayi maganar da shagwa6a, Ƴar dariya azmee tayi kafin tace "insha Allah yau zuwa anjima, zan faɗa mata," Murmushi yasaki ya fice yana faɗin "Can't wait to see," dariya azmee tayi tare da cewa "Romeo kenan," Itama fice wa tayi daga kitchen ɗin don tajima yau tana aiki acikinsa since morning kamar enjine, Yana zaune yana jiran junaid, sai gashi ya shigo, hannu rike da tray, a saman table ɗin dake gabansa daga gefe ya ajiye masa shi, sannan shima yazauna gefensa tare da cewa "Babban yaya zan iya baka a baki," ɗagowa sgr yayi yana kallonsa face ɗinsa tamkar zaiyi murmushi yana kallonsa, wannan fadancin na junaid ba karamin tafiya yake dashi ba, Plate junaid ya ɗauka, ya shaƙe masa shi da chips har yayi sauro don yasan Babban yayan nasu baya wasa da cikinsa, akwai bama ciki haƙƙinsa 😉 Tura masa plate ɗin yayi agabansa, naɗe hannun jallabiyar jikinsa yayi, junaid ya zuba masa ruwa ya wanke hannunsa acikin bowl, sannan ya soma ya zura hannusa yana ɗibar chips ɗin yana turawa a bakinsa, in kaga yadda yake wawuro wa yana turawa a small mouth ɗinsa sai kayi mamakin tayadda akai abincin ke shiga, saboda ƙankantar bakin nasa, Robar cool milk ya dauka ya zuba masa acikin glass cup ya tura masa a side plate nasa, ga fresh fruits ya acikin hadadden plate ya ajiye masa ga sauran delicious," Junaid ne yazauna yana saving nashi, bayan ya tsagaita ya zuba msihi ido yana murmushi, ɗagowa sgr yyi suka haɗa ido yace "what" "Kyau nake kallo fuskar babban yayana," junaid ya basa amsa, "Duk kyau na, nakai ka junaid,"? Ya tambaya yana kallonsa, ɗan sunnar da kai junaid yayi tare da cewa "kai na musamman ne yayana, komai naka na musamman ne, haka kyan ka ma," dan ta6e baki sgr yayi yana kallonsa ayayin da yake mika hannu ya dauki cool milk ɗin dake acikin cup ya kurba sosai tare da mayar wa ya jiye, Sannan cikin natsuwa yace "Ni kam tunda nake aduniyar nan, tun da Allah ya halicce ni a duniyar nan , ban ta6a ganin yaro mai shiga rai mai sace zuciya ba irin ka! junaid u are so special to me i don't know how to explain it but I really really love u so much, just tell me whatever u want am ready to do it for u,"
daɗi kamar zai kashe junaid jin yadda babban yayan nasu ke yabonsa, sam ya gaza rufe bakinsa har sai da sgr ya maimaita cewa "ka faɗamin komai kake so nayi maka insha Allah," Cikin sanyin murya junaid yace "babban yaya murmushinka kawai nake so, dan Allah kayimun koda yaushe face ɗinka a daure..." ya ƙare maganar cikin shagwa6a hada ɗan bubbuga ƙafa, Shiru sgr yayi yana tunanin wai ma ya ake murmushi aduniya, ae shi yama manta when last yayi murmushi aduniyar nan, muryar junaid ce ta ƙara katse shi"smile 4 me plsssssss.." shiru su kayi gaba ɗayansu, zuba mishi ido junaid yayi yana jiran yaga murmushin babban yayan nasu, ɗagowa rafayet ya ɗanyi ya kalli junaid wanda ya ƙura masa iso yana jiransa, mayar da idonsa yayi kan plate ɗin dake gabansa mai dauke da farfesun da junaid ya zuba masa, wa'iyazubillah , A natse a hankali wani irin ƙayataccen murmushi na side face yafara bayyana a kyakkyawar fuskar sgr, Subhanallahi tabarakallahu ahsanul qalikin, wato wasu irin lotsattsun dimples ne suka bayyana a fuskarsa masu shegen kyau, dole babban yaya ya dinga rowar murmushin sa wato wani irin ruwan kyau, madarar kyau yake badawa, irin murmushin kashe zuciyar nan, irin wanda kai tsaye namiji yayiwa Mace shi duk min ji da izzarta sai ta susuce, A susuce junaid yadinga yarfa hannu yana fadin "wow!!wow !! Oh my God yaya rafayet am just speechless wannan heart killing smile ɗin naka ya tafi dani," Lokaci guda kuma ya mayar da face ɗinsa yadda take, kai kace murmushi bai ta6a wanzuwa a fuskarsa ba, sannan yace "Junaid sa hannu muci abinci atare," cikin sauri junaid ya zura hannu suka shiga ci atare abun gawanin burgewa, 💋•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·
*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
_❤🔥Extraordianary Love❤🔥_
*Writer*
*©️Hafsat Bature Boss Lady✍️✍️✍️*
End of chapter one
~page 75~
daga inda ku ka ga na sanya part 2, to daganan Labarin ya soma da zafi zafinsa 🔥🔥🔥