Kenza eBookz

Abban sojoji complete book 1 by boss bature - Chapter 23

Abban sojoji complete book 1 by boss bature - Chapter 23

Abban sojoji complete book 1 by boss bature Chapter 23: Abban sojoji complete book 1 by boss bature Chapter 23. Miƙewa tayi tare da cewa"Bari na kawo maka…

4,445 words

Miƙewa tayi tare da cewa"Bari na kawo maka snacks da abunsha," dakatar da ita yayi da hannunsa yace"No need thanks" Murmushi ta ɗan yi tare da komawa ta zauna, tana ci gaba da kallon fuskarshi, kafin ta mayar da idonta kan surar jikinsa tana haɗiyar yawu, "Banason Kallo," ya faɗi yana ci gaba da dannar wayarsa, cikin jin kunya Amani ta janye idonta, tana mai mamakin taya akai haryasan tana kallonsa, Cikin kashe murya tace " Babban yaya ae dole na kalle ka, kai fa abun kallo ne, kuma ni ban ta6a ganinka ba ido da ido, shiyasan ya,' ta ƙare maganar tana cizon pink lips ɗinta alamar ya cije ta, shi kuwa ba ta ita yake ba, burinsa yayansa Abbas ya ƙaraso, su ga juna, yayi kewarsu sosai, Muryarta ce ta ƙara ratsa shi "Babban yaya, ko dae baka farin ciki dani ne amatsayina na matar yayanku ishaq,'? ta yi maganar tana kallonsa, "Why'? ya tambaya har time ɗin bai ɗago ya kalleta ba, gyara zama tayi tare da cewa "to naga u don't even want to look at me, atlease u should put ur eyes inside mine," Amani ba ƙaramin takura masa tayi ba, ji yake tamkar ya tashi yabar gidan, don baisan nacin magana, "Plsss babban yaya," dogon tsoki yaja tare da cewa "becareful with me," gabanta ne taji ya faɗi jin gargaɗin da yayi mata, tabbas mace bata gabansa, Jiki a mace Amani tabar falon, cikin bedroom ɗinta ta koma, jiki na rawa ta ɗauki phone ɗinta dake ajiye asaman pillow ta dannawa AUNTY BABBA kira, Ringing 3 ta ɗaga kiran bayan sun gama gaisawa cikin zumuɗi Amani tace "Aunty ko kinsa cewa SGR na cikin gidan nan yanzu haka? tayi maganar da murmushi a face ɗinta, A can 6angaren kuwa cike da mamaki aunty babba tace "Are you serious? shi da kansa kuma"? dariya Amani tayi tare da cewa "wlh kam,baki ji yadda naji ba dana gansa duk da rashin maganarsa, yaci ka ji dakai wlh," Aunty babba ta fashe da dariya ta cikin wayar tare da cewa "ki barshi zai zo hannu ne yanzu dai ya maganar Ziyartar wurin bokan nan baba ibliss? kin sama mana kuɗin? Ajiyar zuciya amani tasaki tare da cewa "tukunna dae auntyna, ina nan ina tarairayarsa, ina so nabi komai a sannu, insha Allah nan ba da jimawa ba, zaki ji daga gare ni, da kaina ma zanzo kd na kawo miki ziyara," Aunty babba tace "To shikenan, Allah ya kaimu lpy, shiri na musamman zamuyi, domin ganin munci nasara akan waɗannan zafafan guda biyu," sun jima suna waya a tsakaninsu, agame da yarda zasu ziyarcin wurin hatsabibin bokan nan Baba iblisssss 👹 A can ciki kuwa, dirar Abbas kenan fuskar nan dauke da fara'a kamar gonar auduga jin cewa Sgr ya kawo masa ziyara da kansa, sanye yake cikin kakinsa na sojoji daga headquater yake, yana shiga falon Rafayet ya miƙe fuska a sake suka rungume juna sosae, kamar karya sake shi haka Abbas ya ji, "Am really glad to see u bros, nayi kewarku sosae kamar kamar me," abbas ya faɗi hakan cikin tsananin farin ciki, ruƙo hannunsa yayi suka zauna a mazauni ɗaya, suna kallon juna cike da kewa, Cikin sanyin murya babban yaya yace"Nayi kewarku sosae, har ma bazan iya faɗa ba," ƴar dariya abbas yayi tare da cewa "Wake koya maka hausa ne? nayi mamakin jinta raɗau abakin ka duk da har yanzu da sauranka, last time da kazo daker kake fahimta in anyi magana," Jinjina kai Babban yayan yayi tare da cewa " bana so nazo ƙasar nan ne arinƙa gulmata bana ji, that's why na dage na koya saboda su Ammi," Dariya abbas yayi sosae jin abunda Rafayet yace, a wasa wasa shima ya iya zolaya in yaso , bayan abbas ya tsagaita da dariyar ne yace "Am wai baku gaisa da Amani ba? naga ko abunsha ma bata kawo maka ba," "No tazo mun gaisa, ni nace bana son komai shiyasa," Jinjina kai Abbas yayi tare da cewa "meyasa baka son shan abu ko cin abu in kazo gidan mutanene nifa ɗan uwanka ne jinin ka, shikenan nima duk ranar da kayi aure nazo gidan ka, matarka tayi mun tayin abinci bazan ci ba," wani kallo babban yayan yayi masa tare da ɗan ta6e baki kafin yace "NEVER," wato bashi ba aure har abada, Murmushi abbas yayi yana kallonsa yace "hmmm haka dayawa irinka suke cewa but at the end sai ga lamarin ya sauya, irin ku ma mace tafi juya ku, sannan maza irinku da basa ra'ayin mata ko aure wlh basu iya faɗawa tarkon so ba, haukace wa suke yi idonsu ya makance lokaci guda," . Abbas ya ƙare maganar da zolaya yana kallon fuskar Sgr, wanda ya tamke fuska yana sauraran bayanin yayan nasa," . Miƙe wa yayi tare da cewa "Ni zan wuce," "Haba Babban yayansu, nasan magana tace tayi hurting ɗinka am sorry 4 that, it was a joke," Abbas ya faɗi tare da miƙewa shima ya ruko hannunsa cikin lallami,' "Ba abunda kake tunani bane yaya abbas, time ɗin tafiyana ne yayi, saboda ko wane lokaci na rayuwata yana da amfani, kuma a ƙirge yake" Murmushi abbas ya saki yana jinjina kai yace "kuma fa hakane, na tuna da wannan, ae nama gode ssae da ziyarar da ka kawomin, Allah yabar zumunci," ya faɗi hakan a yayin da ya matsa suka sake hugging junansu, sannan su kayi sallama, ........................SEHRISH............................ Bayan sallar La'asar wuraren ƙarfe 5 na yamma, suna kitchen ana ta faman girke girken abincin dinner, ƙamshi ya gauraye ko'ina, tana tsaye tana yayyanka kayan lambu a saman chopping board, fuskar nan a washe abubuwa biyu na mata yawo aranta, na farko shine wanene wannan wanda xata haɗu dashi yau a garden wanda yasan cewa ita maca ce, na biyu kuma shine new phone ɗin da aunty azmee tace an bata kyauta, bakomai take ɗauki da wayarnan ba fa ce shegen son kallon fina finai dake gare ta, ga son sauraron music gata mayyar selfy kamar hafsat bature 😇 "Ji mana, ki dubamin girkin nan , ynx zanje na dawo," azmee ce tayi maganar a yayin da take fi ce daga kitchen, .. Cikin sauri sehrish tace "To aunty azmee," Ajiyar zuciya tasaki tare da cewa "ko ƙarfe nawa yanzu i ave to check the time, ina da baƙo fa," ta faɗi cikin zumuɗi tana kallon agogon dake manna a bagon kitchen ɗin, shida saura murmushi tasaki tana faɗin "lokacin haɗuwa ya kusa Ya Allah ka bani ƙwarin guiwar tunkarar koma wanene wanna," ta faɗi tana nuni da knife ɗin da ke hannunta, Azmee kuma da ta fice bedroom ɗin junaid ta wuce, domin ta ƙara tunasar dani haɗuwar da ta shirya musu da sehrish," Sai faman knocking take yi, amma sam baiji ta ba, yana tsaye riƙe da ƙugu gaban closet ɗinsa ya buɗe yana kallon jerin kayansa, yama rasa wanne zai sanya domin haɗuwa da sehrish ɗinsa for the first time, sai zabga murmushi yake yi ba magana, tun da azmee ta sanar mishi da haɗuwarsa da sehrish yarasa tsaye ya rasa zaune, sai rawar kai da zumuɗi yake, kamar sabon ango 😌 daga shi sai short ajikinsa, sai da azmee ta ɗaga murya da cewa "Junaid ka buɗe aunty azmee ce inason magana da kai," Ae yana shaida muryarta a kunnansa jiki na rawa, yayi hanzari zuwa ya buɗe mata kopan, yana sakar mata murmushi, "Ango kasha ƙamshi," azmee ta faɗi cikin zolaya, "Ka ce ka shirya haɗuwa da amaryar taka kenan,"? Cikin ɗan jin kunya yace "Kai aunty azmee, nifa kunya nake ji," yadda yayi maganar da shagwa6a yasa ta yin ƴar dariya tace "uhm junaid kenan Romeo shugaban ƴan soyayya yau zai haɗu da juliet ɗinsa akaro na farko, yakama ka rubuta wannan a diary ɗinka saboda tarihi," . ɗagowa yayi da dariya a fuskarsa yana kallon azmee jin abunda yace, "Insha Allah aunty azmee, dole na rubuta wannan, saboda rana ce ta farin ciki da bazan ta6a mantawa da ita ba arayuwata," cikin sanyin murya junaid yayi maganar, alamar yana jin abun aransa sosae, Azmee tace "hakan yayi kyau, ynx dae ni zuwa nayi na ƙara karfafa maka guiwa kasan kai mutumina ne, inaso ka saki jiki sosae, sbd rishi yarinya ce mai shegen tsoro, tana da wani hali dana lura dashi yanayin yadda mutun ya tarbe ta itama haka xata kar6esa, i mean yadda kasakar mata fuska haka itama zata sakar maka tata, kuma zata saki jiki da kai sosai kamar ɗan uwanta, Junaid nasan baka da ƙanwa mace, gaba ɗayanku maza ne, to inaso ka ɗauki sehrish amatsayin ƙanwarka, kai kuma ka zama tamkar yayanta mai share mata hawayenta, kuma abokin shawararta," natsuwa junaid yayi yana sauraran maganar azmee har cikin ransa bayaninta ya kwanta masa aransa, Bayan ta kammala maganarta ta tace "Junaid ni zan koma kitchen, nasan gobe akwai labari mai daɗi daga wurinka, zanji ya haɗuwarka da juliat ta kasance," Dariya kawai junaid yake yi, yana faɗin "insha Allah aunty azmee, ngde ssae ke ce silar farin ciki na," Murmushi azmee tasaki tare da juyawa ta fice tana cewa "Karka manta kaifa ɗane a wurina junaid, cikina ne kawai baka zauna ba, amma ni na shayar dakai ina alfahari da hakan," Rufe door ɗin yayi, tare da daka uban tsalle na murna, runtse idonsa yayi tare da dunkule hannunsa yana faɗin "Can't wait to seeeeeee you Sehrish My dreamy Girl............. koma wa kitchen ɗin azmee rayi suka ci gaba da aiki, tana lura da sehrish cikin sauri take yin aikinta fuska ƙumshe da murmushi, ba don komai ba sai don tayi saurin taje tayi wanka ta kimtsa bayan sallar magriba ta wuce garden wurin wanda aka ce zata haɗu dashi 😘 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 ..............Twins.................................... kwance su ke rungume da juna a katafaren ɗakin da suka ɗauka na hotel ya haɗu iya haɗu, da alama sun gama biyan buƙatar junansu ne bacci ya kwashe su, sam babu sutura ajikinsu zir suke manne da juna kamar tip da tyre, Wayar Jahan ce dake saman bedside table ta soma ringing taken waƙar Shape of you ta Ed shareed," Almost 3 times tana ringing an rasa wanda zai ɗauka cikinsu saboda daɗin bacci, har calling ɗin yayi rejecting, wani ya sake shigo wa da ƙarar gaske, Ayaan ne yafarka cikin kasalalliyar murya ta wanda ke cikin shauƙi da jin bacci yace,"babe ur phone is ringing pls get up and pick the call, its disturbing my ears," ya ƙare maganar yana bubbuga ƙafadar Jahan da hannunsa, daker jahan ya buɗe idonsa da su kayi jawur ya kallesa da su kallon so da ƙauna yace "Honey bazaka gane bane, ko yatsana bana ji zan iya motsawa, wata irin kasala nake ji kasan fa mun jima muna yi," lumshe ido Ayaan yayi tare da ƴunƙurawa ya tashi shi, yakai hannu ya ɗauki wayar, jahan na cewa "Yawwa honey duba ka ga wane ɗan takurar ne, ke kira na, natsuwa yayi yana dubawa, cikin tsananin tashin hankali yace "Jahan!!!! wlh Babban yaya ne ke kira !!!" yayi maganar da ƙarfin, Ae tuni Jahan ya miƙe garas jin an ambaci sunan Babban yaya, jiki na rawa yasanya hannu ya karbe wayar dake hannun Ayaan yana kallon sunan da ya bayyana akan screen ɗin wayar," Wani irin kallo jahan ke bin Ayaan dashi cikin kashe murya ta masoya yace "Ayaan ka daina mun irin wannan abun Allah! kamin kowane irin wasa amma banda wannan,' Tuntsirewa da dariya Ayaan yayi yana masa gwalo tare da cewa "Ni zaka cema wae kasala kake ji ko yatsa ba ka iya motsawa, shiyasa namaka wannan wasan," Pillow Jahan ya wawura dake gefensa ya kifa masa a fuska, nan suka shiga wasa da junansu, A ƙarshe suka koma suka kwanta, ba tare da sun bibiyi kiran da ake masu ba, Jahan ne ya kwanta yayin da Ayaan ya kwantar da kansa a ƙirjinsa, shi kuma jahan ɗin yana shafa masa sumar kansa, cikin sanyin murya Ayaan yace "Jahan! anya kana tunanin ranar da asirin mu zai to nu? wane hukunci za'a mana," "Kisa," kaitsaye Jahan ya bashi amsa, cikin tsananin tsoro Ayaan ya janye jikinsa daga na jahan ya tashi zaune saman gadon yana kallonsa a tsorace yace "Jahan dagaske kisa ne? Kashe mu za'ayi,"? Tashi zaune shima Jahan yayi tare da cewa "Am serious Ayaan kai fa mai ilimi ne ! Sarai kasan hukuncin waɗanda ke aikata homo a addinin musulunci,! munsan da hakan kuma muke aikatawa tabbas duk ranar da Babban yaya yasani wlh kashe mu zaiyi bazae ƙyale mu ba, duk son da yake mana hakan bazae hana yaƙiyi mana hukuncin daya dace damuba domin nema mana sauƙi wurin Allah," Wasu irin hawaye ne ke zuba a fuskar Ayaan cikin tsananin tsoro yace "Jahan ni banso na mutu yanzu, banso na mutu ina aikata wannan mummunan zunubin wlh banso, Jahan kullum babban yayanmu yana ja mana kunne akan mu riƙe mutuncin mu, mu ji tsoran Allah mu guji sa6a mashi domin muyi kyakkyawan ƙarshe kuma mu tsira ranar gobe ƙiyama amma meyasa zamu zama na farko da zamu karya masa zuciya duk irin soyayyar da yake nuna mana"? cikin ƙunar rai Ayaan ke maganar yayin da idonsa ke zubar da hawaye masu raɗaɗi, Jikin Jahan ya gama mutuwa shima idon nasa cike tab da hawaye yace "Ayaan yaya zamuyi? bamu da za6i, kaima kasan bada san ranmu muke aikatawa ba, Ayaan....kafi kowa sanin azaba da raɗaɗin da muke sha in har mu ka wuce 24 hours bamu sadu da junanmu ba,' Cikin shesshekar kuka Jahan ke kora masa bayani, cikin sanyin murya ayaan yace "Babban yayan mu yazame mana komai arayuwa, ya sama mana rayuwar farin ciki, kullum yana ja mana kunne akan kar muja masa abun magana a family roƙonsa kenan amma mun gaza cika masa hakan, ko da yaushe dangin abbanmu suna cewa ƴa,ƴan momyn mu basu da kunya fitsararru ne, tabbas sunyi gaskiya tunda gashi nan, bamu tsoron Allah muna aikata zunubi irin wannan,......." . "Ya isa haka !!! Nace ya isa Ayaan , kadaina cewa bamu tsoran Allah, mu bayin Allah ne kuma masu tsananin tsoransa, Allah yana sane damu kuma asannu zai kawo mana ƙarshen matsalarmu, zai warware mana duk wata masifa dake damun mu," Jahan ne yayi wannan bayanin a yayin da ya komar da jikinsa ya kwanta tare da jan bedsheets a lullube jikinsa yana sharar kuka, . Shima ayaan ya kifa kansa jikin pillow yana matsar kwalla, suna masu danasanin rayuwarsu da tazo musu a haka," 😥 'Shin meke damun su TWINS ne ? da son ransu suke aikata hakan ko kuwa akwai wani abu a ƙasa ne? Nifa na rikice ina buƙatar ƙarin haske game da waɗannan bayin Allah,' . 😥

...............Sehrish.....................

Bayan sun kammala dinner ɗin, azmee tace "Sehrish ki je ki yi sallah, bari na idasa jera dinner ɗina, sannan karki manta ki isa a lokaci dan Allah," Azmee ce tayi maganar a yayin da take fice wa daga kitchen hannunta riƙe da warmers cikin tray , "To aunty azmee ynx kam zan kimtsa," tana gama faɗan hakan ta wuce bedroom ɗinta, bayan tayi sallar magrib tayo wanka shaf shaf tayi ta kimtsa, cikin dogon wando Jeans da riga ƴar ta maza, ta naɗe gashin kanta taturasa cikin hularta sannan ta laga mayafi daga sama, ta gyara gashin bakinta ya zauna daram, Tsayawa tayi tana kallon kanta cikin mirror ɗin, murmushi ta ɗanyi kafin tasa kai ta fice, tana Allah Allah acikin ranta, Babu kowa a babban falon, bi tayi ta wuce time din da tazo harabar gidan adai dai time ɗin motocin su suka soma shigowa hada ta sgr duk ba'a tare da suke ba, amma atare suka iso gidan hadasu kanal yusif dasu irfan fawan da sauransu, tsayawa tayi tana kallon motocinsu, firfitowa su kayi atare, kowanne cikin kakinsa, sai bayan sun fito sannan wani soja narkeke ya fito daga cikin motar Sgr ya buɗe masa ita, shima ya fito dama jeans ne da t-shirt ajikinsa, ganin sa yasa su kanal yusif ƙarasawa suna gaishe shi, Gwanin burgewa sehrish tabisu da kallo especially mutumin ta, sai da duk suka shige ciki sannan ta wuce cikin garden ɗin gidan cike da fargabar wa zata tarass,

Ko da ta isa cikin hadaɗɗen garden ɗin sai ta boye bayan bishiya tana leƙensa

Tsaye yake cikin dress na pakistani masu kyan gaske riga dogowa ta wuce guiwarsa sai wano burgujeje irin nasu,

Rigar mai dogon hannu ce purple tasha adon sparking stones, wandon kuma light pink ne zallah ba kwalliya jikinsa , daga gefen kafaɗarsa scarf ne (mayafin da mazan pakstan ke yarfawa a shoulders ɗinsu)

Zuba mishi ido sehrish tayi tana tunanin wanene wannan ? Saboda ya juya mata baya, bazata iya shaidasa ba,

Launin fatarsa da tagani fari tass da kuma kwantacciyar sumar kansa smooth black ya tabbatar mata da cewa bazai wuce Junaid ba ko Fawan ko cikin su twins saboda sune ke da wannan hasken 6ayau,

Shiru tayi tana ƙoƙarin gano kowanene da kanta, amma sam ta kasa canka har sai da muryarsa ta ratsa kunnanta mai sanyin gaske "Sannu da zuwa,"

Murmushi sehrish ta saki tare da cewa "Yawwa sannun ka,"

Shima yace "yawwa meyasa ki ka 6oye a bayan bishiya, kina shakkar ganin kowanene ya kamata ki fito,"

ƴar dariya sehrish tayi sannan ta fito daga bayan bishiyar ta tsaya daga bayansa tace "Wanene kai,' meyasa bazaka juyo ba mu fuskanci juna ba?

"Zan juyo amma firstly saikin fara faɗamin wanene Ni ki canka kawae,"

Wani irin daɗi ne ya rufe sehrish, natsuwa tayi tana kallon bayansa ciki da son gano ko wanene shi,

Shima shiru yayi yana jin duk wani motsinta, burinsa sehrish ta shaida shi kafin ya juyo mata da face ɗinsa,

"Am waiting 4 u Sehrish," ya faɗi da murmushi a face ɗinsa, Shiru sehrish tayi tana tunanin wani abu aranta, "Idan har zanyi zurfin tunani zan iya gano wanene, na farko wannan hasken shi fari ne sol, fawan kuma hasken fatarsa mai yellow yellow ne, Ayaan da jahaan kuma nasu yayi ja haka launin fatarsu, kai wannan fa kamar junaid ne,"

Tayi maganar acikin zuciyarta, wani tunani ne ya sake zuwa mata,

Junaid shagwa6a66e ne duk yadda yayi magana ana gane wa, yanzu bari na gwada wani abu a sanina da junaid baida jumuri in ya gaji sosai yaji naƙi bashi amsa dole yayi magana da shagwa6a,

Murmushi sehrish tasaki ta tsaya riƙe da waist ɗinta tana jiransa ya hasala yayi mata magana,

Aikuwa maganar sehrish ta tabbata, da yaji shiru shiru bata bashi amsa ba kuma tayi masa shiru,

Cikin shagwa6a ya buga ƙafarsa tare da cewa" wai ba zaiki yi magana ba, so ki ke ki wahalar dani koooo.. .' yayi maganar tamkar zaiyi kuka,

Fashewa da dariya sehrish tayi cikin tsantsar murna da farin ciki tace " *JUNAID*!!! Wlh kaine na gano ka ," tayi maganar da ƙarfi,

Wani irin farin ciki ne ya rufe junaid juyowa yayi fuskarnan tasa ɗauke da kyakkyawan murmushi ,

*Zubawa juna ido su kayi suna ta faman sakarwa juna murmushi, don ita sehrish hada dariya sosae Sam farin cikin ta ya gaza 6oyuwa* 😁😁😁

(Nace ba Romeo fa yau sun haɗe da juliet, don haka sai mun haɗu a next week)

Share 🪩*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

_🔥The father of soldiers🔥_

~hot novel drama~ 🌹 *Mallakin* *Hafsat Bature Moh'd*

~BossLady~✨

Not edited

*page 79-80*

daker suka dakata daga yiwa junansu dariya, junaid yace "bismillah sister tukur ga wuri ki zuna," yayi da maganar yana nuna garden chairs ɗin, Murmushi sehrish tasaki cikin jin kunyar abunda junaid yace wato Sister tukur, cikin natsuwa suka zauna suna fuskantar junansu haɗaɗɗun kujeru ne irin french bishro design ɗin nan, gabansu akwai table launinsu coffee color, Sai faman sunnar da kai sehrish take yi tana wasa da yatsun hannunta, Yayin da junaid ya zuba mata ido,bayan masu ƴan mintina yace "Can we talk"? "Yeah" sehrish ta bashi amsa Junaid yace "First of all, naji daɗin ganinki as a woman, ina fata ke ma haka? Jinjina kai sehrish tayi tare da cewa "Sosae ma," murmushi junaid yayi kafin yace "in da gaske ne, to inaso ki ɗago da idonki ki kalli cikin nawa muyi magana, sannan ki cire wannan gashin bakin da cap ɗin nan inaso na ganki da kyau," ɗan waro ido sehrish tayi tare da cewa "In wani ya ganni fa"? Junaid yace "ae babu wanda zai zo nan, duk ynx suka dawo agajiye so karki ji komai, Ajiyar zuciya tasaki tare da sa hannunta ta cire gashin bakinta, ta ajiye shi asaman table ɗin gabansu, sannan a hankali tasanya hannu, ta zame mayafin da ta naɗe hular dashi, sannan ta zame hular gaba ɗaya, ta ajiye su asaman table ɗin duka, Lumshe ido junaid yayi yana kallonta, a yayin da sumar kanta ta soma warwarowa da kanta ta zubo mata har ƙugunta, tayi mata tamkar hijabi, kwantacciyar suma dark black very smooth, Cikin sanyin murya ta wanda ya gama kamuwa yace "Masha Allah yanzu nan tukur ɗinmu ne ya koma haka? Ƴar kyakkyawar budurwa," Yayi maganar da zolaya, fashe wa da dariya sehrish tayi, sai da ta tsagaita sannan ta samun ƙwarin guiwar cewa "I want to ask you something pls," Junaid yace "Ina sauraron ki," ɗan gyara murya tayi sannan tace " yaushe ne ka gane cewa ni maca ce? kuma sannan ya kaji aranka," murmushi junaid yasaki kafin yace "Na jima da sanin hakan, but am sorry to say bazan iya faɗa miki ranar da nagane cewa ke maca ce ba, sai nan gaba, sannan maganar ya naji araina dana gane hakan, seriously i felt so happy bansan ma yanda zan misalta ba," Wani irin daɗi ne ya rufe sehrish sai faman satar kallonsa take tana sunnar da kai, "I ave a question too," junaid ya tambaya, Cikin sauri sehrish tace "What"? "It's just a question pls, don't feel anything, am... Kece ki ke mun amfani da wayata ko? Ya tambaya yana kallonta, Wurga ido sehrish tayi ta ɗan kalli ruwan dake gudana wurin, taƙi yarda su hada ido saboda jin kunyarsa, ƴar dariya junaid yayi kafin yace "tun da bazaki ban amsa ba, bari ni na baki, kece ki ke mun amfani da wayata kina kiran ƴan uwanki, da farko Nasanya security ɗin wayata finger print, wato sai kika rinƙa lalla6owa while i was sleeping kina using da yatsana kina buɗe wa, afterwards dana gane ana mun using da phone ɗinsa saina maida shi face security nan ma ki kayi kokarin ki sa a face dina don ki bude ko ? Anyi hakan ? Ya tambaya da murmushi a face ɗinsa yana kallonta, sai faman sunnar da kai take yi tana dariya, Junaid yaci gaba da cewa "ranar dana kama ki a bedroom ɗina, kina rarrafe zaki kin lalla6a zaki gudu, time ɗin na tashi daga bacci, muka haɗa ido dake zaki fice, kawai sai kika fashe mun da dariya ko ba haka akayi ba,'? Ya ƙare maganar tasa da tambaya, Hannu sehrish tasanya a bakinta, tana ta faman tiƙar dariya shima kansa dariyar yake yi, Bayan sun tsagaita da dariyar tasu junaid yace "bayan nan akwai time ɗin da kina saving ɗinmu abincin dinner, phone ɗina yayi ringing, nayi picking call ɗin kwatsam sai ki kaji muryar Sister ɗinki, wanda hakan yasanya arazane ki ka saki cup ɗin dake hannunki har ki ka 6arawa Ayaan ruwan coffee mai zafi, Anyi hakan? Ya sake jefa mata tambayar yana yi mata kallon MAGE TA KAMA 6ERA, Cikin jin kunya sehrish tace "Am so sorry pls," "why are u saying sorry to me sehrish? Ni baki mun laifin komai ba, abun ma sai ya zamar mun kamar drama, naji daɗin hakan," ya faɗi yana ci gaba da kallonta,

After some minutes duk sunyi shiru sai da arinƙa jefa wa juna murmushi ana satar kallon juna, rishi jin abun take tamkar a mafarki wai yau itace tare da ɗaya daga cikin ƴa'ƴan abban sojoji mai sauƙin kai haka, addu'arta shine Allah yasa sauran ma su kasance masu sauƙin kai a duk lokacin da Allah zai sa su gane cewa ita maca ce," Jin tayi masa shiru yasanya shi sake cewa "a matsayin me zaki ɗauke ni yanzu Aboki ko ɗan uwa"? Sehrish tace "Da so samune duka biyun, I need both,' Wani irin daɗi ne ya rufe junaid kamar kamar me, ji yake kamar ya rungume sehrish ajikinsa, farin cikinsa sam yagaza 6oyuwa,

Sun sha fira har wurin sallar magrib sannan suka tsagaita, sehrish ta maida gashin bakinta da hularta duka yadda suke sannan suka kama hanya atare suna ƙara tattaunawa kamar karsu rabu da juna, sai da rishi ta fara shiga ciki da jimawa, sannan junaid ya shiga saboda kar a gansu atare,

(Guys nima fa sun burgeni wlh, haɗuwarnan ta rishi da junaid ta tafi dani)💋 ________________________________

*Dama nace akwai annoucement to gashi, Littafin nan littafi ne mai yawan gaske Kuma idan nace zan datse shi to tabbas zan lalata littafin daɗinshi zai ragu sosae bama zai yi tsari ba don haka Part 3 of this Novel will be paid Book, abubuwa da dama waɗanda basai na faɗa ba Ina fata zaku goyi bayana, Nasan duk ranar dana ce na dakata da rubutun littafin nan babu wanda zaiji daɗi acikin readers ɗinshi don haka muyiwa juna Adalci, Sorry 4 the late annoucement* 😔🙏

Ci gaba _________________________

Zuba musu ido goggon katsina tayi tana kallonsu ko kyaftawa babu, kamar wadda tayi gamo da aljanu,

Zaune suke suna facing ɗinta sun matse juna cike da tsoran abunda tsohuwar zata ce musu, Ta jima da farka wa daga bacci amma batasan dasu acikin gidan ba, saboda suna can cikin ɗakin saude suna bacci, ita kuma sauden bata sanar da ita cewa Omar ya sa an kawo wasu ƴara ba sai yanzu bayan sallar magrib ta ke sanar da ita, shine tasa ta kira mata yaran tagansu,"

"Jahad me yasa take kallon mu? bata son mu ko? Korar mu zatayi ko"? Hosana ce tayi ƙasa ƙasa da murya tana raɗawa Jahad a kunne,

Jahad tace "nima bansani ba, amma ina tsoran kartace bata son mu, in ta kore mu, ina zamu sa rayuwarmu? Cikin raɗa suke maganar tasu, duk sai da suka gama raɗe-raɗen sannan su kaji goggon katsina ta fashe da dariya tare da cewa

"kun ta6a jin inda uwa ta guji ƴa'ƴanta !? Ku fa jinina ne, ƴa'ƴan abusufyan ae ƴa'ƴana ne halak malak,"

Kallon juna su kayi jin abunda tsohuwartace, atare suka hada baki tare da cewa "ABUSUFYAN kuma wanene shi ? mu bamu son shi ba,' ɗaure fuska goggon katsina tayi tare da cewa "Bansan shashanci in ma zolayata ku keyi to ku daina, ni ba amun irin wannan wasan yanzu na burkice, ku faɗamin gaskiya ku ba ƴa'ƴan abusufyan bane,?

Babu wasa a fuskarta tayi tambayar,

Readers Also Read