Kenza eBookz

Abban sojoji complete book 1 by boss bature - Chapter 26

Abban sojoji complete book 1 by boss bature - Chapter 26

Abban sojoji complete book 1 by boss bature Chapter 26: Abban sojoji complete book 1 by boss bature Chapter 26. ◻ "To rasa kunya 6eran tanka zaka fara mun…

3,406 words

◻ "To rasa kunya 6eran tanka zaka fara mun tsokanar taka ko,"? ◻ junaid yace "ae gaskiya na faɗa Abba, kallon ka kawai nake yi kai ta shan ƙamshi kamar baka son momynmu alhalin ko rannan kana bacci cikin mafarki naji kana cewa bana ji bana gani ni makaho ne agame da sonki Momyn junaid in bake ba sai rijiya in na rasa ki zan rungumi transformer akanki zan iya tunkararrrr ◻ bai idasa ba saboda jin saukar pillow din da abban nasu ya wurgo mashi, tabbas junaid ya bawa abban nasu dariya sosai ◻ "Kai ko? Yaushe akai hakan junaid Ƙaraya kke mun," ya faɗi yana kara janyo Wani pillow ya wurga masa, hannu junaid yasanya ya ca6e pillow ɗin da Abban nasu ya wurgo masa a ƙinjinsa ya rungumesa yana faɗin "thank u Abbana dole na gode maka domin gashi da hannunka ka miƙo mun juliet ɗita," ya faɗi hakan yana shafa filon dake ƙirjinsa yayin da yake kallon fuskarshi cikin madubin gabansa, ◻ Jin shiru Abban nasu bai sake cewa komai ba, yasanya junaid juyowa da kallonsa, samun sa yayi zaune tsakiyar gadon kansa na kallon ƙasa Allamar da damuwa a fuskarshi, ◻ tasowa junaid yayi jiki asanyayye ya haye saman gadon in da abban nasu yake yace "Abbana meya faru naga kashiga wani yanayi na damuwa,"? ◻ ɗagowa Abban yayi ya kallesa cikin sanyin murya yace "Junaid momynku ! kasan bana 6oye maka komai kaine abokin sirrina, babu wanda ke fahimtar zuciyata kamar kai," ya dakata da maganar yana dan jinjina kai, ◻ "Dad pls tell me may be i ave the solution of it," ◻ "Junaid mom ɗinku ta azabtar dani da soyayyarta, junaid ita tace tana so na tun kafin na fara sonta, amma kalli ynx ta kama hanya da aure na akanta ta koma australlia da zama, junaid ya zanyi? ◻ gyara zama junaid yayi suna fuskantar juna kamar zaiyi maganar arziki sai cewa "Abba dole sai ita? Ga zankaɗa zankaɗan mata nan ƴan goma shatakwas ƴan shila kyawawan gaske masu neman sugar daddy irinka wlh abba har rububinka zasu yi ka share ta kawai ka auri wata," in serious matter junaid yake magana, ◻ Takaici ya hana abban magana a tunaninsa junaid zai bashi shawara akan yadda zasuyi mom ɗinsu ta dawo wurinsu da zama, amma sai ga akasin hakan, in banda sangartaccen irin junaid waye zaiso ayiwa uwarsa kishiya" ◻ "Abba u didnt say anything, shawarata batayi bane,?. ◻ "Eh junaid batayi ba, ashe baka da hankali in rasa wa zanyiwa kishiya sae momynku, bakasan halinta bane, duk da bamu tare da ita amma tayimun gargaɗin cewa muddin na ƙara aure sai ta dasa Bomb acikin gidan kowa ma ya rasa," ◻ Fashewa da dariya junaid yayi, abban nasu yaci gaba da cewa "kuma in banda abunka wani magidanci ne mai ƴa'ƴa irinsu Sgr da Marshal Omar zai kara aure, auren ma ƴar shekara sha takwas ae wlh a ranar da ta sa ƙafarta acikin gidan nan aranar zasu balla ta gutsi gutsi ◻ Dariya kawai junaid yake kwasa wato ta ko'ina ba sauƙi, ita mommy tace zata dasa bomb su kuma su Babban yaya in an kawo ta gidan 6arar gyaɗa zasu yi mata,. ◻ "Enough junaid dariyar ta isa haka, zan baka lokaci daga yau zuwa gobe kayi tunanin shawarar da zaka bani akan yadda zamu shawo kan momynku ta dawo nan da zama," ◻ "Kana nufin muyi mata wayau abba,"? ◻ ɗan zaro ido abban yayi tare da cewa "kai ! wannan matar mai ɗan banzan wayau kamar dila tab ae banta6a ganin dakakkiyar mata ba irin momynku ae wannan ba wanda ya isa ya yayi mata wayau, ◻ Dariya su kayi gaba ɗayansu sun jima suna fira kafin su kwanta tare Abban yayi musu addu'a yabi ya shafe su duka, ◻ _____________________________________________ ◻ ƙaramar yarinya ce wadda bazata gaza shekara 12 ba ke tafama gudun saman titi sai faman kuka takeyi tana ambaton sunan "Oumma !! Oumma !!! ba tare da ta lura ba wata ƙatuwar motar ƙirar range rover tayi awon gaba da ita, nan take kanta ya fashe jini ya soma kwaranyo wa ta ko'ina ◻ A firgice sehrish ta farka daga mummunan mafarkin da take yi murya na rawa ta furta "Innalallahi wa'ina ilaihirraji'un," ta faɗi tana cusa hannunta cikin sumar kanta idonta sunyi jawur hawaye na bulbulowa daga cikinsu, tabbas ta tsorata da mafarkin da tayi, ◻ Jiki a mace ta tashi ta wuce toilet saboda lokacin sallama yayi, sai da ta watsa ruwa sannan ta ɗaura alwala ta fito tana ta faman sauke ajiyar zuciya, ◻ Wardrobe ta buɗe ta dauko hijab ɗinta ta shimfiɗa sallaya ta kabbara sallah, bayan ta kammala ta zauna saman sallayar ta ɗaga hannayenta tana addu'o'i, ◻ Bayan ta kammala komawa tayi ta kwanta saman bed batare da ta cire hijab ɗin ba, haƙiƙa mafarkin ɗazu da tayi ya tuna mata wani abu mummuna daya ta6a faruwa makamancinsa, ◻ Ta jima hawaye na gangarowa daga eyes ɗinta kafin wani baccin ya sake ɗauke ta, ba ita ta farka ba har sae wurin ƙarfe tara, jiki na rawa ta shirya kamar kullum ta wuce kitchen, ◻ tsayawa tayi tana zazzare ido ganin har azmee ta kammala breakfast ɗin, wanda zata je ta jera a dining kawai take shiryawa, ◻ "Ina kwana aunty azmee," tayi maganar tana ƴa kame kame, murmushi azmee tayi tare da cewa "Lafiya lou reesh, fatan kin tashi lpy," ◻ "Aunty azmee ai mun afwa ban fito da wuri ba," ◻ "Bakomai sehrish nifa da so samu ne ki koma kawai room ɗinki na kawo miki breakfast ɗinki ki ci acan ba sai kinyi wani aiki ba," ◻ murmushi sehrish tayi tare da cewa "hakan bazaiyiyu ba auntyna, nima bana so nabar miki aiki dayawa ke kaɗai, ◻ Sehrish tayi maganar tare da ƙarasawa ciki domin ta taya azmee shirya abincin da zasu jera, ◻ Kamar daga sama ya faɗo kitchen ɗin daga shi sai shorts ajikinsa ba riga, ◻ gaba ɗayansu sai da gabansu ya faɗi ganinsa kwatsam haka ba sallama, ◻ daker azmee ta iya cewa "wata sabon gani haroon yaushe ka dawo ne ? Amma dae saukar dare kayi ko,"? Ta tambaya tana kallon shi ◻ idasa shiga yayi yana sakin murmushi yace "Eh jiya da daddare na iso, nayi mamaki da banganki ba auntyna gaskiya i really missed u, nayi kewar delicious ɗinnan naki, ◻ da ƴar dariya a fuska azmee tace" ae yanzu tunda ka dawo sai ka dasa daga inda ka tsaya, halan yanzu ma yunwace ta koro ka,? ◻ "Eh auntyna fruits nake so da coffee haka ko tea, pls a shirya mun sannan abawa wannan mai aikin yakawo mun," yayi magana yana kallon sehrish wadda tunda ya shigo gabanta ke faɗuwa tarasa dalilin hakan, ◻ "Shikenan yanzu zan bashi ya kawo maka," ◻ Murmushi ya saki tare da juyawa ya fuce daga kitchen ɗin, ◻ "Wanene wannan aunty azmee"? Sehrish ta tambaya domin neman ƙarin bayani akansa, ◻ Azmee tace "Wannan haroon kenan, ki saki jiki dashi bai da wata matsala a iya sani na, shima ɗayane daga cikin matasan gidan nan," ◻ ɗan ta6e baki sehrish tayi tare da jinjina kai tace " Allah yasa bai da wata matsala," aranta kuma tace "sam ni baiyi mun kama da sauran ba, hasalima duk sun fishi kyau da natsuwa," ◻ Ba da son ranta ba azmee ta shirya mata fruit a tray da cup na coffee takai masa, ◻ sai da tabi kwatancen da azmee tayi mata sannan ta gano room ɗinsa a nan down yake kusa dana kanal yusif," ◻ a bude tasamu kopan sallama ta kwala masa daga ciki taji ance "Come in," ◻ Shiga ciki tayi gabanta na faɗuwa rass rass, daga kwance yake saman haɗaɗɗen gadonsa ya taso zaune yana ƙare mata kallo, ◻ Cike da girmamawa sehrish tace "Gm sir," ◻ bai amsa mata ba har ta ajiye masa fruits ɗin asaman table ɗin dake a front ɗinsa, ◻ Cikin sauri tajuya zata fita muryarsa ta katse ta"na sallame ka ne,"? Jiki a mace ta dawo ta tsaya daga tsaye tare da sunnar dakai tana kallon yatsun hanunta da take wasa dasu, ◻ Jin shiru yasa ta ɗan dago ta kallesa samun shi tayi yana bin jikinta da wani irin matsiyacin kallo tundaga kan yatsun ƙafarta har izuwa ƙirjinta, ◻ Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, ita burinta ya sallame ta tawuce taje wurin dining don ta taya aunty azmee ga kuma son sanya Babban yaya da take yi a idonta, ◻ Ganin ya tsayar da idonsa a gaban wandon jikinta yasanya tsigar jikinta tashi, ◻ da buɗar bakinsa sai cewa yayi "ina Ak47 ɗinka take, don ni banga alamarta ba anan,"? ◻ Cike da rashin farintar me yake nufi sehrish tace "bangane me kke nufi ba," ◻ Wani shu'umin murnushi haroon ya saki tare da kai hannu cikin tray ɗin da takawo masa ya ɗauko damin Banana ya cire guda tare da sa hannu yana 6are bawon ayabar yace "Ina nufin wannan," yayi nuni da ayabar dake hannunsa,. ◻ Jigum sehrish tayi sam tagaza fahimtar me haroon ke nufi, ganin bata da niyar bashi amsa yasa shi cewa "ina nufin abu na maza wannan," yayi maganar yana ruƙo abunsa dake cikin shorts ɗin jikinsa,. ◻ Zaro ido sehrish tayi gabanta na faɗuwa zuciyarta tayi mugun tashi ganin abunda yake nuna mata sai lokacin ta gane me yake nufi ma, ◻ Shiru tayi idonta na kallon ƙasa gabanta na faɗuwa ◻ "A cire mun wando inaso nagani na shaida," ◻ Ya faɗi ayayin da yake kai ayabar hannunsaa cikin bakinsa yana gatsa yana ci, ◻ Ji tayi gaba ɗaya komai ya tsaya mata tsak, tabbas ta tsorata da haroon sosae tun da take aiki a gidan bawanda ya ta6a lura da hakan farat ɗaya sai shi, ◻ "Baza a cire ba,!? ya tambaya a fusace ◻ Cikin en ena sehrish tace "kayi hkr dan Allah ! amma baxan iya yin abunda kke so ba......," kafin ta idasa maganar tuni yasanya hanunshi yaja zariyar wandonta nan take wandon ya tafi suuuuuuuuuu zai sabule jiki na rawa ta cafko shi tayi saurin maidashi ta ɗaure abunta a yayin da zufa ke wanko mata, ◻ Dariya haroon yayi kafin ya tsagaita yace "Ke !!! nifa tun jiya dana ganki nasan cewa Ke maca ce ba namiji ba !!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!! ◻ ɗagowa da ido sehrish tayi a firgice tana kallonsa tamkar a mafarki take jin kalaman haroon . ◻ Ƙara jaddada mata yayi da cewa "Ke maca ce ba namiji ba !! ki faɗamin uban miyasa kikayi shigar namiji kika zo gidannan? Da kwai wata manufa aranki ko !!? ◻ Muryar na rawa sehrish tace "innalallahi wa'inna ilaihirraji'una!! taya akai ka gane cewa Ni maca ce farat ɗaya!? ◻ Dariya haroon yayi tare da cewa "saboda ni Shu'umi ne ! Kuma cikakken ɗan duniya wanda idonsa ya buɗe a harkar barikanci ! ba wani abu da mutun zai 6oye mun batare dana gano sa ba," ◻ "Shikenan nashiga ukuna !! dan Allah ka rufemun asiri karka ce zaka tona cewa ni maca ce pls!! ◻ Ajiye ayabar dake hannunsa yayi cikin tray ɗin sannan yace "Okey, i won't expose ur secret but under one condition!!?. ◻ Ya faɗi yana kallonta a raunane sehrish tace "koma meye zanyi nidai karka tona mun asiri," tuni idonta ya ciko tab da kwalla, ◻ Har wani lumshe ido haroon yake yi yana kallonta " share hawayenki baby, bani da matsala muddin za'a biyamun buƙatata,' ◻ shiru sehrish tayi tana sauraron shi ◻ "Zamuyi magana anjima yanzu zaki iya tafiya naga kuna cikin aiki ne," ◻ tunkan ya idasa mgnr sehrish ta fuce tana shasshekar kuka , ◻ sai da ta dakata bayan ta fita ta tsaya ta share hawayenta tare da dai dai ta natsuwarta sannan ta sauka ƙasa, anan ta samu ma Aunty azmeen tana jera musu breakfast ɗin a dining, ◻ Karasawa tayi suka ji gaba da jerawa atare, ◻ Kallonta azmee tayi tare da cewa "Naga kin jima ! Lapiya dae ko? ◻ "Eh," ta bata amsa atakaice, ita kaɗae tasan yadda take ji aranta, brain ɗinta ta gama shiga ruɗu tashiga tashin hankali mamakinta taya akai farat ɗaya haroon ya gane cewa ita maca ce !? how many days ta share a gidan amma ba wanda ya ta6a lura in aka cire junaid sai shi wanda jiya jiyan nan yazo da daddare, tabbas abun ya ɗaure mata kai, kuma tasa mishi alamar tambaya, (?) Anya ba Aljani bane

◻ gaba ɗaya ta tafi duniyar tunani har batasan cewa masu gidan duk sun fito ba, domin yin breakfast, yawancinsu duk jallabiya ce ajikinsu, ◻ Fawan da twins ne suka fara hallara suka zauna a kusa da juna, sai Irfan da jabeer bayansu sai khaleed da kanal yusif, duk suka gaishe da Azmee ta amsa musu kafin ta ci gaba da saving ɗinsu, ◻ Har time ɗin sehrish bata cikin hayyacinta tana tsaye kamar gunki tana tunane tunane iri iri aranta, sam azmee bata lura da halin da take ciki ba, ◻ A tare Abbansu ya fito da baby junaid hannunsu cikin na juna, fuskar nan tasa a washe tun da idonsa su kayi Arba da sehrish ɗinsa, tunkan ya ƙaraso ya lura da cewa ta tafi duniyar tunani, ◻ Ganin Abbansu yasa suka haɗa baki wurin gaishe shi "Barka da safiya Abba, kun tashi lafiya," ◻ "Alhamdulillah My Sons ina fata kuma kuna lafiya," ◻ da fara' a fuskan kowannansu suka amsa mishi, ◻ Bayan sun zauna cike da tsokana junaid yace ◻ "Ni bazaku gaishe ni ba"? ya faɗi yana kallonsu, ◻ Tsoki fawan yaja tare da cewa "kabari sai ka fara ajiye gemu da ƴa'ƴa tukunna, ◻ "Wai junaid da gemu ba rana ba wata, don gsky ban ga alamar junaid zai yi gemu ba ko nan gaba,' ◻ Acewar Jahan, ◻ Abbansu yace "Talle zatai wa audu gori, ka fara duba fuskarka tukunna, muddin junaid bazaiyi gashin baki ba ko na gemu to kaima haka baza ta6a yi ba," ◻ dariya su kayi gaba ɗayansu kanal yousuf yace "Wai ina Haroon ne ? Shi bazai fito bane? ◻ Abba yace "taya zai fito bayan abunda ku kayi masa jiya, sam banji daɗi ba, tun da ya dawo ya kamata ku tarbi ɗan uwanku hannu bibbiyu, in baku ja shi ajiki ba taya zai shiryu ? Yayi maganar cike da nuna 6acin rai akan abunda su kayi jiya, ◻ "Abba amma ba ka ga irin yadda yake mana magana ba har agabanka batare da jin komai ba? Acewar Irfan, ◻ Ajiye cokalin dake hannunsa yayi tare da cewa " in da sabo ae ya isa ace kun saba da halinsa, addu'a kawai zaku bishi da ita Allah ya shirye shi," yana kai karshen maganar ya ɗauki spoon ɗin yaci gaba da cin abincin dake gabansa, ◻ Jinjina kai su kayi kawai shikam fawan ta6e baki yayi tare da cewa "Ashe dagaske yazo, ae ni nayi tunanin duk mafarki ne zuwan nasa jiya," ◻ Harararsa khaleed yayi "dole kace haka dama bakwa good time dashi ae," ◻ tun da suka ambaci sunan HAROON hankalin sehrish ya dawo jikinta, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi ga zufa na wanko mata, aza idonta tayi akan junaid wanda ke ta faman satar kallonta yana mata murmushi ◻ Murmushi itama tasakar mishi, ◻ So yake yayi mata magana amma ba hali sai dae daga inda yake ya rinƙa yi mata alama da bakinsa batare da sauti ya fita ba yace "Sehrish kin tashi lafiya," ◻ tagane me yake cewa don haka itama tayi kamar yadda yayi tace "lafiya lou junaid ina fata kaima haka," ◻ ɗaga mata kai yayi alamar eh, duk abunda junaid keyi akan idon Abbansu mamaki yake menene tsakanin junaid da mai aikin nan tukur, kodae sun ƙulla abota ne, ɗan murmushi ya saki domin yaji daɗin hakan, sbd duk wani abu da zai sanya shalelensa farin ciki son shi yake, ◻ "Ga babban yaya nan fa kowa ya shiga taitayinsa" fawan ne yayi maganar a yayin da yake cunkusa kebab abakinsa, ◻ Yadda fawan yayi maganar yasanya abbansu yin dariya, wai ga babban yayanan kowa yashiga taitayinsa, Kanal yusif yace "wato kaine annoucer duk in big bro zai fito sai kace kowa ya shiga taitayinsa, nawa ake biyanka salary ne ? ◻ Dariya sukayi gaba ɗayansu cikin nishaɗi in ka cire Twins dake ta faman jin bugun zuciya,

◻ A tare suka fito su biyu shi yana saukowa daga saman stairs yayin da shi kuma Haroon ke fitowa daga part ɗinsu dake a nan down, ◻ Jikinsa na sanye da tank top riga ce kamar singlet haka take fara, sai wando jeans, sumar nan tasha gyara, ◻ Shi kuma Haroon shirt ce da gajeran wando ajikinsa, ga uban gashin jiki da Allah yayi masa don ma Allah yasa kwantacce ne amma duk da haka ba kyan gani, ◻ Ganin Sgr yasa shi fara yi mashi kirari "Barka da Fitowa Babban yayanmu Namijin Zaki Uban dawa, mai mulkar ƙananun ƴan iska kai ɗaya tak kake tada runduna, gabanka Bullet bayanka Bomb ka ga Ingarmar Namiji ƙasaitacce takawarka lafiya Namijin duniya,' ◻ wannan kirarin na haroon yasa su Yousouf dariya, shi kuwa Sgr ko kallo haroon bai ishe shi ba, ◻ A tare suka ƙarasa ya zauna a empty chair ɗin dake kusa da Junaid, haroon ma yasamu wuri ya zauna, ◻ "Barka da safiya Abbana abun alfaharina," ◻ Murmushi Abba yayi tare da cewa "Yawwa barka dae Haroon ya gajiyar tafiya ? ◻ "Abba ae ta washe tun jiya, yanzu garass nake jina," ◻ Jinjina kai Abba yayi tare da cewa "Naji kace ka ƙaro wulaƙanci dagaske ne? ◻ Cikin sauri haroon ya saci kallon Babban yayan nasu yace "Bana cikin hayyacina ne, shiyasanya nayi maganar," ◻ Murmushi su kayi gaba ɗayansu,bayan nan suka shiga gaishe da babban yayan nasu, bai amsa ba sai dai ya rinƙa yi musu alamar yaji da kansa, gyaran murya abbansu yayi hakan yasa Sgr ɗagowa ya kallesa cikin sanyin murya yace "Gm Dad," ta6e baki Abba yayi tare da cewa "sai ynx ka ganni? Ni fa narasa ganewa, nan gaba ina ga sai na rinƙa gaishe ka dakaina da alama, "Insha Allah hakan bazata ta6a faruwa," sgr yayi maganar ayayin da yaɗauke idonsa daga nakan Abban, Murmushi Abban yayi, yarasa dalilin dayasanya yake jinshi sosae aransa ko dan yana kama da Momynsa alexandra,

Sehrish kuwa ◻ Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta time ɗin da tayi arba da kyakkyawar fuskar Sgr duk da a firgice take ganin yadda haroon ke satar kallonta,

◻ tunkan azmee tayi yunkurin zuba mishi breakfast ɗinsa sehrish ta riga ta, plate ta ɗauka ta zuba mishi Chips ta shake mashi shi, sannan ta tura mishi agabansa ta kuma haɗa masa da hot coffee a acikin cup, ◻ "Mlm tukur ni baza'a zuba min bane"? Haroon ne yayi mata maganar yana binta da wani irin shu'umin kallo, ◻ Jiki na rawa sehrish ta ɗauki plate hannunta har kerma yake yi, tama rasa me zata zuba mishi, ◻ Muryarshi ce ta katse ta da cewa "Snacks nake so",

Cikin sauri sauri ta zuba mishi snacks ɗin sannan ta haɗa masa da lemu a cup ta tura mishi,

◻ "Yawwa Good Job," ya faɗi yana kai hannunsa cikin plate ɗin ya ɗauki donuts yakai bakinsa,'

◻ matsawa tayi daga bayan sgr ta tsaya saboda ta ◻ samu damar da zata rinƙa kallon sumar kanshi da kyau, tana shakar turaren shi, ◻ Ji take tamkar takai hannunta ta shafi sumar nan tashi, tun da ta tsaya abayan sgr bata motsa ba, duk wanda ya faɗi yana buƙatar wani abu sai dae azmee ta zuba mishi, ita kawai Babban yaya take saving abunda yake so, ◻ ɗagowa junaid yayi da idonsa ya ɗan kalle ta dayake tana tsaye daga bayansu, mamaki ne ya kamashi ganin yadda sehrish ke ta faman kallon Babban yayan nasu ko kyaftawa batayi, sam bai kawo wa ransa komai ba game da kallon nata kawai yasanwa ransa cewa wata'ƙil respecting ne yasanya sehrish tsayawa abayan, kallonsa kuma da take yi may be burgeta yayi ne, amma yaso ace shi sehrish take ma wannan kallon dayaji daɗi, mayar da kansa yayi jikinsa a sanyaye yaci gaba da shan farfesun naman dake gabansa cikin plate, ◻ Sun jima suna ɗawainiyar zuba musu breakfast ɗinsu kafin daga bisani kowa ya fuce, banda junaid da haroon suna acikin gidan, Sgr sun fita tare da abbansu headquater

_______________________________________________

Readers Also Read