Abban sojoji complete book 1 by boss bature - Chapter 3
Abban sojoji complete book 1 by boss bature Chapter 3: Abban sojoji complete book 1 by boss bature Chapter 3. Dawowa azumi tayi hannunta dauke da tray ,…
4,465 words
Dawowa azumi tayi hannunta dauke da tray , plate ne mai dauke da snacks , sai 2 cups da jug , a jiye su tayi a sman table sannan ta janyo shi izuwa gabansu ta ajiye ,
Koma tayi tazauna tana murmushi , Sehrish kuwa sai kallon matar take yi har taji ta burgeta saboda tana son mutum mai fara'a ,
Lemu ne a cikin jug din zuba musu hajjaju tayi ta mika ma sehrish , cikin sauri ta karba dama kishi take ji , kurbarsa tayi wani irin sanyi ya ratsa ta ga dadin gaske ,
Azumi ta bi ta da kallo cikin mamaki tace "in ce ko wannan ne d'an aikin da akace za'a kawo mana"? hajjaju ta danyi guntun murmushi tace "eh shine sunan shi tukur kwararre ne wurin iya sarrafa abinci ," saboda jin karyar da hajjaju ta shirgo akanta yasa ta kusa fetsar da lemun da takurba a bakinta , abunda ya kusa sata ta shake shine da ta ce kwararrene wurin iya sarrafa abincin shin yaushe ta son da wannan ?
Sauraron hajjaju ta ci gaba dayi jin tana introducing dinta a wurin azumi " yaro ne mai matukar basira ga wayau , zakiji dadin yin aiki dashi ," takarsa maganar tare da ajiye cup din dake a hannunta saman table din gabanta , sannan ta kalli sehrish tace "tukur wannan itace azumi , itama y'ar aiki ce a gidannan amma taji ssae tana kula da yaran gidan hakan yasa ta zama tamkar uwa agaresu , ina fata zakuji dadin yin aiki da juna ,"
Dakyar sehrish ta kakaro murmushin dole tace "Insha Allah hajiya ,"
Ita kadai tasan halin da ta shiga , wannan zaman da tayi ji ta , kamar ta dosa na ass dinta a saman wuta , saboda tsabagen tsoro , A ranta sai maimaita kalmar 'yaya goma sha takwas kuma duk sojoji take yi ,
Azumi ta janye idonta daga kan sehrish (tukur) ta mayar da idonta kan hajjaju tare da cewa "am inaso na tambaye ki tundazu maganar ke shigemin meyasa kika daina leko mu bayan ina da tabbacin cewa kina zuwa abuja zuwane kawae ke baki yi ,"
Murmushi hajjaju tayi tare da yin yar dariya tace "ai dole zuwa gidannan ko jaraba ! oh kin manta Abunda ya faru last time dana zo ko ? Ina wannan BABBAN YAYAN nan nasu wani mai shegen kyau tubarkalla kamar d'an sarkin aljanu mai kirar zakunan nan ," dariya azumi tayi tare da cewa "wai wa kike nufi cikinsu , kinsan suna dayawa , akwai major , akwai Captain ga janar , akwai Marshall ga kuma Canal da sauransu , kowa da sunan da ake kiransa " takarasa maganar tana kallonta
Sarai tasan wa take nufi amma tafiso taci gaba da zuzutashi don hajjaju ta iya bada labari ,
taci gaba da cewa "oho nidai nasan shi kadai suke ce ma babban yaya , ina gaya miki last dana zo , lokacin nazo dubiyar wannan younger bro dinnasu mai asthma wanda aka fidda kasar waje akayi masa aikin a kirjinsa , " azmi tace "oh nagane junaid kike nufi ae suna waje suna buga ball ynx yaji sauki Alhmdllh ,"
Hajjajun ta ci gaba da cewa "ina fadamiki daga zuwa abun arziki , wlh ina shigowa falon nan ni bansan meya faru ba , nasame shi da y'an uwannan nasa sae faman rirrike shi sukeyi sai huci yake yi just like a hungry lion from the bush gaba daya yayi watsi dasu kasa , ya daga dining table yayi wurgi dashi , gabana ya fadi rass banyi aune ba naji yace "don ubanki kama hanya ki fice, ashe ya ganni "
Wallahi a tsorace a fujajen nabar gidan don tsabagen rudi , da kafa nakama hanyar fita babban gate din saida wani soja cikin security din gidan nan yace mun hajiya kin manta motarki , sannan fa natuna jiki na rawa nakoma nadauko,"
Tun kafin ta idasa labarin azumi da sehrish suke ta faman tikar dariya , kamar cikinsu zai kulle , ita kanta hajjajun dariyar take yi , dakyar azumi ta tsaida dariyarta tace
"Hmmm sai ynx nagane wa kike nufi , ai da kinsani ba ki daina kawo mana ziyara ba domin shi ba sojan nigeria bane , US ARMY ne ba a kasar nan yake ba yna dai zuwa sometimes in yasamu hutun aiki ,"
Hajjaju tace "bazaki gane ba ne , yadda na tsorata , ai ko ba don shi ba , wadannan tantiran na gidannan marasa jin magana..." Azumi ta katse mata maganarta ta da cewa "twins kike nufi , tom & jerry suna nan haryanzu basu canza ba sai ma abunda yayi gaba ",
Hajjaju tace "ehen su nake nufi",
Ci gaba da fira sukayi , yayin da hankalin sehrish ke atashe , tunda taji sun ambaci babban yaya sai taji tsoransa har ya shiga ranta , sam ta nemi natsuwarta ta rasa ,
Sun jima suna fira har time din ba wanda yashigo daga cikin soldiers din , har hajjaju tayi shirin tafiya , bayan ta yiwa azumi bayanin akan nemawa tukur wato sehrish alfarmar in tayi one month da fara aiki ta taimaka a ansar mata kudin wata uku a dunkule ,
A tare suka fita har bakin motar ta , sannan suka tsaya suna idasa takarkare zancen "meyasa bazaki jira abban ba yazo? koya yi miki sallamarki ne "? hajjaju tace "ae indai abba ne bani da matsala dashi nasan zanji alert kinsan hannunsa a bude yake , kuma Abunda yasa nake sauri zan shiga gwarinpa ne gidan wata goggo na " Murmushi azumi tayi tana kallonta,
Ita ma murmushin tayi mata , harta bude mota zata shiga tasake juyo wa ta kalli azmi tace "pls game da tukur na baki amanarsa , ki kula da duk wani motsi nasa pls ,"
Azmi tace "in dai nice u don't ave to worry about it I will look after him insha Allah ," sallama sukayi hajjaju ta shige cikin motarta ta ja ta ,
Bayan fitarsu sehrish ta zabga uban tagumi tana jin kewar kasancewarta ita kadai a wannan hamshakin gidan da batasan kowa a cikinsa ba , gashi tazo a matsayin namiji , duk in ta tuna wannan hankalinta tashi yake , abu dayane ke kara mata karfin guiwa , y'an uwanta in ta tuna su sai taji ba irin kasadar da bazata iya shiga ba ,
Dawowa ciki azumi tayi fuskarta a sake tace da sehrish " tashi mu shiga ciki na nuna mka bedroom din ka , in ka huta zuwa anjima before magrib zamu shiga kitchen",
Sehrish ta amsa da toh tare da mike wa tabi bayan azmi , suka shiga ciki tayi mamakin bedroom din da azmi ta nuna mata a matsayin nata na yar aiki , wannan koda amayarce tasamu wannan falillahil hamdu , ba tarkace a ciki , single bed ne , ga beside drawer mai dauke da bedside lamp a samanta ga wardrobe madai-daiciya ta manne jikin bango , ga wadatattun curtains a kowane window , komai na cikin bedroom din brown color be banda labulayen da suka kasance milk colour , da zanen gadon ,
Ba abunda ya kara burgeta sai dressing mirriow din da tagani , duk da ba cosmetics a samansa , madubin yayi mata da yar chair din dake gabansa ,
Murmushi azumi tayi ganin yadda yaron yake ta farin ciki don haka tace "komai yayi ko "? da sauri ta amsa da "eh hajiya harma yayi yawa "
Dariya azumi tayi jin yace harma yayi yawa , "Ynx dai ni zan shiga ciki , ka zauna ka huta , sannan akwai bedsheets a cikin wardrobe din nan , in zaka canza saika dauka ," tana gama fadan hakan ta fice ,
Kamar jira takeyi azumi ta fita tahau ihu tana tsalle , kafin ta tsagaita da haukan nata ta shiga bathroom din dake ciki ,
Nan fa ta soma wani sabon kallon , ko a mafarki bata taba tunanin zata mallaki irin wannan tsantsararren bathroom dinba mai kama da bedroom saboda haduwarsa ,
Dakyar ta samu natsuwa , ta dauro alwala tafito , a cikin wardrobe din ta samu prayer mat (sallaya) ta dauko ta shimfida , ta kabbara sallah , duka ta hada tayi zuhr da isha saboda batasamu damar yi ba a kan hanya , gashi ynx ankira isha'e shiyasa ta hadesu duka tayi ,
Bayan ta idasa sallar , ta daga hannayenta sama tana addu'ei at the end ta fashe da kuka , Sbd tuna wa da halin da y'an uwanta ke ciki , magana ta soma yi cikin kuka " har ynx na gaza yarda cewa nice zan yi rayuwa a cikin wannan daular ba tare da y'an uwana ba , taya zanji ddin rayuwata batare dasu ba , ni ina nan sukuma suna asibiti cikin wani hali , Allah sarki rayuwa ! bazan taba yafe ma wanda yayi silar shigarmu cikin wannan tashin hankalin ba , Ya Allah ka hana sa jin dadin duniyar nan gaba daya , Ya Allah ka kaskantar da rayuwarsa kamar yarda yayima ta mu....." kuka ne yaci karfinta har ta kifa kanta saman sallayar tana cewa "I will never forgive u in my life and I will neva forgt u ! i must take revenge koda ace nikadai ce na rageda zan yafe maka ka shiga aljanna to tabbas bazaka taba shigar ta ba. *_Hafsat Bature_* ~(Boss Lady)~
Page 9-10
Bata tashi daga saman sallayar ba har aka kira Magriba tana tunanin abu daya, sai da ta kammala sallar sannan ta nad'e carpet din ta turasa cikin wardrobe , tare da hijab din duka.
tsayawa tayi gaban dressing mirror tana kallon kanta a cikinsa , sak namiji ba wanda zai gane mace ce sai yanayinta ya koma kamar d'an daudu , hannu tasa tare da shafa gashin bakin da ma'reeya ta sanya mata , murmushi ta d'an saki a ranta ta ce "Sehrish ke nan dramatic girl."
Kara kimtsa kanta tayi saboda azmi tace mata akwai aiki a kitchen da zasuyi, sai da ta fara rufe kofar dakin gudun kada Azumi ta same ta tana canza kaya , ta gane cewa maca ce ita ,
Cire kayan jikinta ta yi , ta maida su cikin bag dinta , sannan ta dauko wasu riga da wandon , ta rige a hands sinta gaban mirror din ta koma ta tsaya tana kallon jikinta , ziririn pant ne a ajikinta , takai hannu tasha fa flat tommy dinta , wanda yake a dam'e kaman bata cin abinci saboda shafewarsa ,
Mayar da hannun tayi saman boobs dinta wadanda ta matse su gam , da abun matse belly , har cikin ranta ba taso hakan ba tana son abunta ssae , amma ba yadda zatayi duk cikin aiki ne ,
ga hairs dinta da aka maida mata shi guntu , amma hakan bai dame ta saboda a iya sanin ta in aka aske mata gashi irin hakan cikin one month zai koma yadda ya ke tsayinsa ma harya karu ,
Jin alamar tafiyar mutun kamar bedroom ta ake nufowa shine ysa ta yin saurin , zura dogon wandon tare da rigar sa , tayi gaggawa gyara daurin da m'reeya ta yi mata , mai kamar rawani ,
Kwan ! kwan !kwan taji an knocking , cikin sauri ta karasa ta bude kopan azmi ce tsaye fuskanta da murmushi tace "tukur ina fata ka shirya sbd ynx zamuje na nuna maka yarda abun aikin yake ,"
Cikin girmamawa sehrish tace "toh hajiya ,"
Azmi tayi mata wani irin kallo har gaban sehrish ya tashi a tunaninta ta gano lagwanta , amma sai taji tace "stop calling me hajiya , my name is azmi call me by my name , cos we re d same , am a house maid just like u ,"
taka rasa mgnr tare da fice wa tana cewa "follow me" rishi ta bi bayanta tana d'an murmushi ,
Kitchen suka shiga amma sehrish ta gaza gane a ina suke , haduwar wurin ce ta rikitar da ita , an kawata komai na kitchen din da dukkannin abubuwan da akeso,
Sam ta manta aiki ya kawosu sai faman kalle-kalle take yi , sai da taji muryar azmi a kunnanta sannan ta dawo dai dai
"tukur ynx bamu da enough time , we'll make a dinner now in yaso zuwa tomorrow i will explain everything to u , Especially zama da samarin gidan nan darasi ne me zaman kansa duk zan koya maka ,"
sehrish sai take ganin maganar azmi kamar shiriri tace , ynx har akwai mutumin da za ace sai an koyi darasin zama dashi ?
haka suka fara aiki , azmi ce ke yin girkin , yayin da tabarma sehrish ferar dankalin turawa , ga yankan albasa , acewarta tafara da karamin aiki ,
Suna cikin aiki sehrish tafara jiyo karar shigowar motoci , rass taji gabanta ya fadi , da jiniya motocin ke shigowa ,
"Hmmmm wannan alama ce mai nuna cewa masu gidan sun dawo " a cewar azmi ,
Zuciyar sehrish sai harbawa take yi saboda tsananin firgicin da wa zata fara cin karo ,
"Ka'ida ne daga sun shigo babban falo zasu fara kwalamin kIra ka saurara kaji ," azumi ta fada tana murmushi ,
Hannun sehrish sai kakarwa suke yi ,
ita dai baza ta iya tantance muryar mutun nawa bace amma taji sauti iri iri
"Azumi ! Azmi !! Azam zam !!!" da karfi suke kwala mata kiran without any respect , cikin sauri azmi ta fice tana ce ma sehrish "pls ka kula da girkin am coming back now ,"
Sehrish ta amsa da toh , daga inda take tana iya hangosu saboda kitchen din irin model design dinnan ne wanda ba kopar shiga gare sa a bude yake bata iya identifying faces dinsu ,
Hankali a tashe azmi takarasa wurunsu tana fadin "welcome back Sirs ," ko arziki amsa bata samu ba sai complaining da suka soma yi mata, "Ina fata angyara min bedroom dina don bansan kazan ta ! in ma kinsan baki gyara ba let me know ," daya daga cikinsu ne yayi wannan maganar ,
matsawa tayi kusa dana gefensa don taji shi mai zaice , hannu ysa yana shafa ciknsa yace "Ni matsala ta abunda zansa ma cikina pls kafin na shiga ciki nayi bath na tarar da abinci jere saman dining table if not kinsan sauran ,"
matsawa azmi ta sake yi kusa dana gefensa dayake duk suna a jere kusansu takwas,
" Na fadamiki Injin wanki na ya samu matsala dazu da safe ga shi na tara kayan dauda , gajerun wanduna na ma duk sunyi dirty dafatan kin wanke mun su ,"
Haka ta dinga sauraransu ba wanda baiyi magana ba acikinsu , bayan ta gama sauraransu one by one tace " Komai da kuka lissafamin na kammala sa , abinci ne kawai shima ynx zan idasa ,"
Kama hanya suka yi kowa ya wuce bedroom dinsa , wasu na upstairs wasu na a downstairs,
Babu abunda ya burge sehrish sai kakin sojojin dake jikinsu , abunka ga handsome guys ga tsawo ga hadaddiyar sura sai abun ya bada citta 😘
tunanin ta soma yi a ranta "oh ni ko wanene babban yaya acikinsu , koda yake naji azmi tace ba sojan nigeria bane U.S ARMY ne , zanso nagansa daga ji ya hadu yadda hajjaju ke zuzu tashi ,"
takarasa tunanin tana murmushi ita kadai abunta , shigowa azumi tayi tana fadin "maza tukur a shirya abinci a dining before su fito, ai ina ji girkin ya isa ya kammalu ,"
Wasu hadaddun kuloli ta dauko daga kitchen cabinet kamar ranar aka budesu daga kwalinsu tsantsar kyansu kamar ba abinci za'a zuba ciki ba , saboda yadda murfinsu ke glowing har face dinka zaka iya gani aciki just like mirror ,
A wani faffadan tray ta shirya komai ciki , ta mika wa sehrish azuwan taje ta fara shiryasu a dining ,
Gaban ta na faduwa ta karba tsoranta da wa zata fara cin karo a cikinsu , time din da ta isa dining room din , mutun d'aya ta samu zaune shi ya rigasu fitowa jikinsa na sanye da white tshirt da black short , bai lura da ita sai da yaji cool voice dinta ta sauka a kunnan sa " sannu da hutawa " a natse ya dago yana kallonta ,
lokacin da suka hada ido kara ware idonta tayi ganin irin kyawunsa , dan matashi ne ba zai wuce 18years ba , a tunaninsa zai ga mace amma sai ya ga namiji tabbas shi muryar mace ya ji mai dadin gaske a kunnan sa ,
Wani kayataccen murmushi ya sakar mata , wanda yasa ta shiga yanayi , cool voice dinsa ce ta ratsa ta "am nace ko sabon mai aikin da akace za'a kawo mana ne?daga masa kai tayi alamar eh , Jinjina kansa yayi tare da d'an tabe small lips dinsa , Soma jera abincin tayi , bayan ta gama ta koma ta dauko sauran abubuwan da bata kawo ba ,
Allah Allah take ta kammala jera abincin kafin sauran su karaso , muryarsa ce ta kara katse ta " chicken pepper soup din nan zaka zuba mun ka hadamin da irish cikin plate din ," ta amsa toh kamar wata munafuka haka take sunnar dakai , Ji take kamr asirinta zai to nu ,
Plate ta zaro daga cikin set na filattan da takawo , bude daya daga dana cikin kulolin tayi , nan da nan kamshi ya gauraye wurin , saving spoon ta dauko ta soma zuba kazar a cikin plate din , sai faman hadiye miyau take yi , ga hannun ta dake kakarwa ga wani gumi dake sauka daga gefen sajenta ,
Kammala zuba kazar tayi sannan ta bude kular da ke dauke da irish ta zuba masa k'adan muryarsa ta sake ji "yayi mun k'adan ka take mun plate din "
cika masa plate din tayi dam sannan ta tura masa gabansa , cikin sauri ta kama hanya zata koma ciki "spoon din fa ko so kake na dauka da kaina ne sannan a gidan ku haka ake ba mutun abinci ba tare da drinks ba '? har zuciyarta taji wannan maganar a tunanin zaiyi saukin kai ganin da farko yayi mata murmushi ,
lallai ta jinjina wa izzarsa , ga cokulan kusa da shi ga kuma drinks din da ta jera amma yafi karfin yasa hannu ya dauka sai da ita ta mika masa ,
guntun murmushi tasaki koma tayi ta mika masa cokalin sannan ta zuba masa lemu a cikin glass cup ta mika masa , yamutsa fuska yayi tare da sa hannu ya karba yana cewa " gsky kana bukatar training don da ace babban yaya ko captain kayima haka da ka gane barno gabas take don sai kayi tsallan kwad'i ,"
Ya karasa maganar yana kurban lemun da ta mika masa , a wani irin yanayi sehrish ta juya wannan ne karo na biyu da taji an ambaci BABBAN YAYA , hakan nakara sa mata tsoransa a zuciyarsa ,
Komawa tayi kitchen ta samu azumi tana gyara wuraren da suka bata , jin shigowarta yasa ta dagowa tare da cewa "subhanallah meyasa ka dawo ka kammala saving dinsu ne "?
"A'a naga basu fito bane shiyasa na tafo ," tayi maganar fuska a yamutse sbd rashin natsuwa da take ciki , azumi tace "maza ka koma karka ja mun bala'i , bakasan halin mazan gidannan ba ,"
Ba haka sehrish taso ba , jiki a sanyaye ta kama hanyar komawa dining room din , hannu azumi tasa ta rike habarta alamun mamaki tace "lallai dole na mike tsaye akan yaron nan ! yana abu kamar mace anya wannan ba dan daudu bane ? ta tambayi kanta ,
Tunkan takarasa ta ke hangensu , a lokacin suke karasawa saman dining din kowannen su yaja kujera yazauna , Kasancewar table din dogone mai mazaunin mutum goma sha 12,
Tana jin dayansu na cewa "wai uban wa ake so ya zuba mana abincin ne? cikin sauri sehrish ta karasa tana cewa "ni ce yallabai ,"
Gaba daya suka d'ago suna kallon ta sai ta tsorata tayi wuri wuri da ido. 👮🏻♂️ *ABBAN SOJOJI* 👮🏻♂️ ```The father Of Soldiers```
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```
```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________
https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•
Page 11-12
'Yan kame-kame ta shiga yi hankali a tashe tana wurwurga ido, " wannan d'an daudun daga ina kuma aka samo shi?" Daya daga cikinsu ya tambaya yana kallon ta , hantar cikinta ce ta ji ta kad'a , su duka sauraren ta suke yi su ji mai zata ce?
Motsi ta soma yi da lips dinta alamar tana so ta ce wani abu "Amm... Amm.." Duk ta bi ta dabarbarce. Jin muryar Azumi yasa Sehrish sauke ajiyar zuciya, karasowa ta yi tana fadin "Afuwan y'an samari ban yi maku bayani game da sabon d'an aikin da aka kawo domin ya rinka taya ni aiki ba."
Kasa kunne suka yi suna sauraron ta , dafa kafadar Sehrish ta yi tare da cewa "Sunan shi tukur daga yau zai rinka taya ni aikace aikacen cikin gidannan ,'
Ta kare maganar tana kallon kowannan su tabe baki yyi ba tare da sunce komai ba dama haka ta yi tsammani , don haka taci gaba da cewa "tukur bari na gabatarka maka da kowannan su saboda ka kiyayi zama dasu ,"ita dai ba ta ce komai ba saboda a rud'e take ,
Azumi ta soma gabatar mata da su daga na farko "Wadannan biyun da ka ke gani sune tagwaye in ka lura komai nasu iri d'aya , suna da son zolaya musamman idan abun mugunta ne sun fi auki a nan na farkon sunansa Jahan shine babba sai twin brother dinsa Ayaan"
Tana gama wa dasu ta matsa na kusa dasu tace "wannan kuma sunan shi Kanal yusif sarkin tsafta , bai cika son surutu ba kuma baya son kallo , na gefensa kuma shine Khaleed bai da matsala shi indai za ayi masa abunda ya ke so ba tare da ya tambaya ba ,
Duk Sehrish na sauraron wannan bayanin na azmi , bayan ta kammala da na hannun damarta ta koma other side din taci gaba da cewa "wannan Junaid kenan sarkin murmushi, duk yadda za'a bata mai rai baya fushi sai in an kuresa , yana da son wasa faran faran da jama'a, burinsa a bashi kulawa a bangaren ci kuwa ba'a magana ," karasa maganar tayi tana y'ar dariya , shima dariyar yake yi haka zalika wasu daga cikinsu sun d'an murmusa ,
Sehrish tagane sa shine wanda ta fara zuba ma abinci mai kyakkyawan murmushin nan
"n6a kusa da shi kuma fawan kusan halinsu daya da Junaid , sai jabir da irfan basu da matsala in dai ba tsokanarsu akayi ba."
Murmushi sehrish tayi taji dadin wannan gabatarwar , sai dai ranta na bata cewa wadannan kananun ne , akwai sauran mutun goma daga cikin sojojin da basa nan , su kuma koya zasu kasance !?
A tare da azmi suka yi saving dinsu abincin har suka kammala kowannnen su ya kama hanyar makwancinsa , tattara plates din da kulolin sukayi a tare suka kakkauda komai izuwa ma'ajiyarsa , daga nan sehrish tayi ma azmi sallama ta koma bedroom dinta , tana mai jin dadin fara kasancewarta a wannan awesome family din Babbar damuwarta shine , da tazo a matsayin namiji a maimakon mace batasan ya abun zai kasance ba ranar da asirin ta ya tonu.
Tunda samu gadon nan ta haye ta soma minshari bata kara sanin meke wakana ba sai da tajiyo kwankwasar kopar da azumi take yi mata ,
A firgice ta farka tana neman mayafin da take nad'e kanta da shi , can ta hangosa kasa ashe anan tayi wurgi dashi, daukowa tayi ta hanzarta daure kanta dashi, sannan ta tashi ta nufi kofan ta bude mata, fara'a azmi ta sakar mata " am sorry na Katse maka bacci ko naga ana kiran sallah ne raina ya bani baka yi ba nasan an sha gajiyar tafiya ga aikin da mukayi da dare ,"
Cikin y'ake sehrish tace "a'a wlh naji dadi da ki ka tashe ni saboda banyi sallah ba amma ynx zanje na yi,
Azumi tace "ok in ka kammala karfe 7 ka fito akwai aikin breakfast na jiran mu" reeshi ta amsa da "toh " sa'annan tajuya ciki"
Cikin sauri ta shiga toilet, sai da tafara cire gashin bakin da aka sa mata ta tura sa cikin aljihun wandon ta, sannan taje bakin fanfo ta daura alwala , ta fito tana yarfa hannun ta, hijabi ta dauko ta zura sannan ta shimfid'a kafet, ta soma yin sallar,
Bayan ta kammala sallar wata irin hamma ta rinka ji, ga bacci bai ishe ta ba ga kuma yunwa don jiya da daddare bata nemi abincin ba gashi available
Agogon dake manne jikin bango ta kalla akwai sauran lokaci don haka sai ta baje saman sallayar taci gaba sharar bacci, ba ita ta tashi ba sai wurin karfe 9 na safe hankali a tashi ta wartsake, ganin cewa wannan ce rana ta biyu da fara aikinta gashi zata fara bada matsala, cikin hanzari ta cire hijab dinta ta hada da kafet din sallan ta adana su a saman gadonta, sannan ta zaro gashin bakinta da take likawa ta manna sa a fuskarta, ta gyara nad'in mayafin kanta ta fi ce,
A kitchen ta Sami azmi ta kammala shirya komai na kalacin safen , duk sai taji ba dadi sukuku ta isa gare ta ta ce "barka da safiya nayi laifi dan Allah ayimun uziri,"
Babu alamun bacin rai a fuskar azmi ta ce " karka damu tukur, ba wani abu nan gaba dae aguji yin hakan"
Sehrish ta amsa da toh insha Allah yanzu wani aiki zan yi ?
Ba wani aiki kawai abunda ya rage ynx kabi bedrooms din kowannan su ka Sanar dasu su fito su yi breakfast ya kammalu," azmi ta karashe maganarta ta tana kallon ta,
Cikin zullumi sehrish ta fita ta tunkari jerin dakunan dake a downstairs , na farko ta fara kwankwasa wa shiru ba'a bude ba , kara knocking tayi da karfi , har sai da ya isarwa mai dakin , muryarsa tajiyo ashake yana cewa "who's trying to disturb me? d'aga murya tayi tare da cewa "tukur ne sabon mai aiki,"
"Shigo ciki" ya ba ta izni , turo kofar tayi tare da kutsa kai ciki, har cikin ranta dakin ya yi mata kyau bedroom kamar na mace saboda kyau ga tsafta sabanin wasu mazan da idan ka shiga dakunansu kamar wurin safkar y'an gudun hijra saboda tsaban tarkace da har mutsi,