Kenza eBookz

Abban sojoji takun karshe complete - Chapter 10

Abban sojoji takun karshe complete - Chapter 10

Abban sojoji takun karshe complete Chapter 10: Abban sojoji takun karshe complete Chapter 10. Wuraren ƙarfe 10 sun kammala Komai,an gyara kitchen ɗin…

4,450 words

Wuraren ƙarfe 10 sun kammala Komai,an gyara kitchen ɗin tamkar ba'a ta6a girki acikinsa ba,tun da wuri Abokanan Abba suka fara zuwa,Hada wasu daga cikin abokan Abusufyan wanda ke zaune a Nigeria,tuni gida ya fara ciki,tun da su sehrish suka tashi daga bacci ko arziƙin yin wanka basu samu damar yi ba,saboda kiransu da ake tayi,duk wanda yazo saiya buƙaci a kira mashi su ya gansu,daga sunje haka za'a dinga yabon kyawunsu ana sanya masu albarka,gashi duk wanda sukaje gaidawa cikin abokanan Abba,sai Yayi masu kyautar makudan kudi,babu wanda yayi masu kyautar ƙasa da naira dubu ɗari biyar,hosana duk tabi ta susuce,sae faman lissafin kuɗaɗen da suka samu takeyi,daga sun dawo cikin ɗaki zata fara fadin Abokin abba mai farin gemu ya bamu kyautar Dubu ɗari takwas,sae wannan abokin nasa mai sanye da kaki da yazo ya bamu kyautar gonaki guda uku,kuma ya haɗa mana da dawakai,Sai kuma wannan mai ƙaton tumbin shine ya bamu kyautar miliyan Uku,Ni miliyan ɗaya,Jahad miliyan ɗaya,sae sehrish itama miliyan daya,bayan shi kuma sae wannan abokin daddyn namu ɗan fari mai kumatu,wanda ya biya mana Umrah,Ashe da rabon zanje in ta6a ka'aba ɗakin Allah,harma in roƙe shi akan ya yaye mun haukan dake damuna,don banson jin anace mun Zararriya,haka ta dinga sambatu har sai da suka fara gajiya da surutun hosana,

Sehrish na cikin toilet tana wanka,amma hankalinta gaba ɗaya ya tafi akan Sgr,kalamanshi na jiya ne suka shiga dawo mata acikin kanta,dole tayi aiki a ƙarkashin shi batasan meyasa yake son ganinta a matsayin ƴar aikinsa ba, Tana cikin wannan zancen zucin tajiyo muryar jahad,daga waje tana cewa"Sehrish dan Allah kiyi sauri ki fito,inaso nima nayi wankan,kafin asake kiran mu," jin haka yasa tayi saurin kammala wankan ta fito,ɗaure da towel a waist ɗinta,shiga ciki jahad tayi,don tayi wankan itama,duk hosana na zaune gefen gadonsu hannunta ruƙe da biro da memo din Sehrish sae faman lissafin kyaututtukan da suka samu takeyi," Girgiza kai sehrish tayi tare da cewa"Aiki ya same ki hosana,kowa na ɗokin zuwa yayi wanka amma ke hankalinki na akan kuɗin da muka samu,abunda baki sani ba,idan mukayi wanka mu kayi kwalliya,sae mun samu ninkin abunda muka samu a yanzu," Juyowa hosana tayi tare da waro ido jin an ambaci kuɗi tace"dagaske kike sehrish idan mukayi wanka mukayi kwalliya zamu samu fiye da wannan kuɗin da muka samu"? Jinjina kai sehrish tayi tace"kwarai kuwa,ke dai kawai ki tashi ki fara yin wanka,jahad na fitowa,ki shige ciki," Cike da zumuɗi ta miƙe ta koma ta tsaya a kopar shiga toilet ɗin tana kwankwasa ma jahad, "Ki fito nima in shiga," Murmushi sehrish ta saki,dama wayau tayi mata,don taji ɗazu suna magana da jahad tana cewa ita ba yanzu zatayi wanka ba,sae da marece,bayan tun yanzu akeso su shirya,don agansu da kyau, Gaban dressing mirror ta zauna,tana shafa mai ajikinta,sae faman sauri takeyi saboda taje part ɗin Sgr,kamar yadda ya umarce ta akan taje da safe ta kai mashi breakfast ɗinshi,kuma ta gyara mashi bedroom ɗinsa,light makeup tayi a fuskarta,saboda wannan wankan safe ne zata ɗauka,da anjima Azmee tace za'ayi masu makeover,tamkar brides haka zasu fito,

Bayan ta kammala yin kwalliyar,komawa tayi wurin wardrobe din kayansu ta buɗe tana ƙare masu kallo,dama kullum zata zura kaya ajikinta sai ta tsaya yin ruwan ido wurin za6en kayan da zata sanya, "Da rana zan sanya shadda lace ɗita,da marece kuma zan ɗauki wankan Swiss lace,yanzu dae bari na sanya wannan Arab gown ɗin,naga sai faman ƙyalli takeyi,in na sanyata ajikina,ba ƙaramin kyau zanyi ba,"ta ƙarasa maganar tare da janyo rigar,golden colour ce,gaba ɗaya jikinta adon stones ne masu ƙyalli da ɗaukar ido,batare da 6ata lokaci ba ta shiga kiciniyar zura rigar ajikinta,daƙyar ta shigeta saboda ta matse ta,gaba ɗaya tabi shape ɗin jikinta,kirjinta ya fito sosai,ga wani uban hips daya bayyana ajikin kayan,dama akwaita da diri sosai,don dai bata cika sanya kayan da zasu bayyana surar jikinta bane,hannun rigar na net ne,dogo ne ya kawo har wrist ɗinta,kana hangen fatar hannunta ta ciki, siririn mayafin ta ɗauko,ta sanyashi asaman kafaɗarta,wa'iyazubillah,ba ƙaramin wankuwa sehrish tayi ba,juyowa tayi tare da kallon Hosana wadda ta saki baki tana kallonta,tace"Nayi kyau," Yadda hosana ta saki baki,tana kallonta ko kyaftawa batayi ba ƙaramin dariya ya bata ba,har saida ta ambaci sunanta,sannan hosana ta iya buɗe baki tace"Wlh kinyi kyau Sehrish sosai,kamar ƴar matan aljanna," Dariya Sehrish tayi yayin da ta koma gaban mirror tana kallon kanta,hannu tasa tare da daukar kwalbar turarenta,tabi jikinta ta feshe,sannan ta fuce daga ɗakin,tun da tafito idon kowa ya dawo kanta,abokanan matasan gidan da suka hallara a babban falon,duk saita tsargu,kitchen ta wuce anan ta samu Azmee tana zuzzuba ma saude abinci acikin warmers tana fitarwa waje,wurin baƙi tana kai masu, Ae tunda azmee tayi arba da ita tashiga zuzuta kyanta, "Aunty Azmee ni nasan ban kai haka ba,kawai kina hura mun kaine,".

Azmee tace"ae kin zarce duk yadda nake faɗi maki,dama shi mai kyau bai gane yana da kyau,sai in ana faɗi," murmushi kawai ta saki tare da cewa"Aunty azmee ina kayan breakfast ɗin babban yaya inaso nakai mashi," "Oh kin manta cewa abusufyan ya hanaki"? "Nasani Aunty azmee,bansan ya zanyi bane,babban yaya jiya yace,baison ki ƙara aiki part ɗinsa,ni kawai yakeso in dinga zuwa inayi mashi aiki,kuma har faɗa mashi nayi akan cewa daddy ya hanani amma yace shi babu ruwanshi,kawai nayi mashi aiki, Jinjina Kai azmee tayi tare da cewa"Tabɗijancan,aikuwa akwai matsala!don wlh Abusufyan yaji wannan maganar bazai yadda ba,kuma ke in banda abunki kin manta wanene abusufyan a wurinki,mahaifinki fa ne,taya zaki tsallake umarninsa kibi na babban yayanku?hakan na nufin cewa yafi iko dake akan mahaifinki?kina ganin cewa abusufyan zaiji daɗi idan yaji cewa kin cigaba da yi mashi aiki"? Jin wannan maganar ta azmee yasa jikinta yin sanyi,sunnar da kanta ƙasa tayi,tuni idonta sun ciko da kwalla, Gyaɗa kai azmee tayi tare da cewa"Nasan don baki da yadda zakiyi ne sehrish,zan shirya maki breakfast ɗin ki kai mashi,amma karki kuskura ki bari Uncle abusufyan ya gani,kuma koda ya kamaki,kada ki sanya sunana aciki," Amsa mata tayi da toh, Batare da 6ata lokaci ba,Azmee ta shirya mata warmers da sauran tarkacen abincin acikin kayataccen tray ta bata takai mashi,' Tunda sehrish ta fito daga kitchen ɗin gabanta ke faduwa sai faman waige waige takeyi,tsoranta kar daddynsu ya ganta,cikin sa'a ta haye upstairs batare da taci karo dashi ba, Ajiyar zuciya ta sauke lokacin data ƙarasa cikin falonshi,babu kowa aciki,hakan yasa ta tunanin ko bai tashi daga bacci bane,tana ƙoƙarin shiga bedroom ɗinshi,taji muryar namiji a bayanta, "Ji mana,"a firgice ta juyo don taga wanene,ɗan zaro ido tayi tana kallon matashin daya biyota,acan falo ta ganshi tare dasu kanal yousouf da alama abokinsu ne, Murmushi ya sakar mata tare da cewa"Am sorry na biyo bayanki batare da saninki ba,nagaza jurewa ne shiyasa na yanke shawarar yin hakan,' muryar sehrish na kerma tace"Am...um..dan Allah ka jira ni awaje,yanzu zan fito, "Okey,zan tsaya awaje,but pls don't stay long," Ya faɗi hakan tare da juyawa zai fita,har ya sakai zai fita daga falon,ya kuma juyowa tare da kallonta har lokacin tana a tsaye yace"Kin tafi da imanina sosai,zan iyayin komai don na mallake ki,"ya ƙarasa maganar tare da fucewa, Ajiyar zuciya Sehrish ta sauke aranta tace"Kowanene wannan jarababben,baisan nan part ɗin wanene ba,so yake yaja mun masifa,ya wani kwaso kafafunshi ya biyo ni,' kamar ance ta juya,idanunta suka sauka kan Sgr dake tsaye ya goya hannayenshi asaman faffaɗan ƙirjinshi,fuskar nan kwata kwata babu annuri,daga shi sai short fari ajikinsa,

Gabanta ba ƙaramin faɗuwa yayi ba,ƙiris ya rage ta saki tray ɗin hannunta,tuni jikinta ya soma rawa,

"Zoki wuce ciki,"yayi maganar babu alamun wasa a fuskarshi,jiki na rawa ta nufi bedroom ɗin nasa,matsa mata hanya yayi ta wuce,sannan ya kama hanya azafafe ya fito daga falonsa,anan waje ya samu saurayin nan,tsaye yana jiran fitowar sehrish bawan Allah,ya ɗauki wankan suits,sae faman zabga murmushi yake yi, ..jin an ta6a kafadarshi yasa shi juyowa don yaga wanene,gabansa ne ya faɗi Rasss lokacin da yayi arba da sgr tsaye agabanshi ya ruƙe qugu,tamkar zaki haka ya koma mashi,mugun tsoranshi suke ji,saboda ko magana bata ta6a haɗashi da abokanan ƙannenshi ba,labarinshi kawai suke ji a wurin su Irfan,babu wanda baisan Sgr ba,wato babban yaya, Fuskarshi a tamke yace"Wani ganganci ne yasa ka biyota har cikin part ɗina!"? Muryarshi na kerma yace"wlh ni ba ita na biyo ba,zuwa nayi kawai don in gaishe ka,dama Jabeer ne yace yakamata muzo mu miƙo gaisuwa wurin babban yayansu,kaji dalilin dayasa na kwaso ƙafata nazo," Wani irin kallo sgr ya wurga mashi,jin ya sharara mashi ƙarya bayan yaji duk abunda yake faɗa ma sehrish, Sunnar dakai saurayin yayi yana faman mazurai,tsoranshi karya kai mashi naushi, Hannu Sgr yasa tare da ruƙo neck tie ɗinsa yace"menene sunanka" Cikin sauri yace"Jazz," Sgr yace"Jazz ko?let me warn u,ka tsaya a iya matsayinka,in ba so kake ka kwana a gadon asibiti ba,ka rufe idanunka daga kallon matan mutane,hakan zaisa ka zauna lafiya,'yana kai ƙarshen maganarshi yace"just u can leave....."ae tunkan sgr ya ƙarasa maganar,Sir Jazz ya watsa da gudu jiki na rawa ya sauka downstairs, Ajiyar zuciya sgr ya sauke tare da juyawa ya koma ciki,

a ƙopar shiga bedroom ɗin ya tsaya,yana kallon sehrish dake ƙoƙarin gyara mashi gadonshi,har ta ajiye mashi kayan breakfast dinsa,yadda ta rankwafa shape ɗin hips ɗinta ya fito sosai,ba ƙaramin kyau tayi masa ba,sai yanzu ya gane dalilin dayasa wannan saurayin ya biyota,tunda yaga babban kaya dole ya zauce,baisan cewa babban goro sai magogin ƙarfe,

gyaran muryar da yayi ne yasata yin saurin ɗagowa,tana ganinshi tasha jinin jikinta,ƴan kame kame tashiga yi kamar wata mara gaskiya,ƙarasa shiga ciki yayi tare da samu wuri daga gefen gadon ya zauna,sannan anatse yace"Am hungry," cikin sauri ta dawo gaban table ɗin tashiga ƙoƙarin yin saving ɗinshi,coffee mai zafi ta fara miƙa mashi acikin cup,hannu yasa tare da kar6a,yana cikin kur6ar coffeen kamar ance mashi ya ɗago,idanunshi suka sauka akan Boobs ɗinta da suka fito sosai,tamkar zasu fasa gaban rigar,zukunnawar da tayi ne yasa suka yi hakan, Nan take ya shaƙe,ba arziƙi ya ajiye cup ɗin dake hannunshi,gaba ɗaya duk yabi ya susuce ya shiga yin tari,tamkar maƙoshin shi zai 6allo,ganin haka yasa sehrish dakatawa daga yin saving ɗinshi da takeyi,tashiga yi mashi sannu, daƙyar ya samu ya daidaita natsuwarshi,muryarshi ashake yace"Ke!ina scarf ɗinki yake"? Muryarta na kerma tace"gashi nan agefenka,da zanyi gyara ne,na ajiye shi anan don karya takuramin, Harara ya ɗan watsa mata tare da cewa"ɗaukarshi ki yafa,banason na ƙara ganinki haka kina yawo," "Toh,"ta amsa mashi,sannan ya kai hannunshi a gefenshi ya ɗauko mata mayafin ya miƙa mata,tana kokarin kar6a ta aza hannunta asaman nashi,ɗagowa yayi da idanunshi kai tsaye suka shiga cikin nata,agigice tayi saurin kawar da nata idanun, Tunda yake arayuwarshi wata ƴa mace bata ta6a jan hankalinshi ba,da surar jikinta,harya shake irin haka ba,mata dayawa suna kawo mashi kansu,wasu har cire kayansu sukeyi don suja ra'ayinshi,amma basu ta6a cin nasara ba,donshi bashi da wannan Sha'awar ko kaɗan,akan sehrish ne kawai ya ta6a ganin wani sauyi,A ranar da suka faɗa saman gadon shi atare,har yau yana mamakin wannan abun,

*Aunty Babba*

Tuni sun kammala shirinsu na zuwa abuja,wankan shadda ta ɗauka,doguwar rigace ta kashe ɗaurin ɗan kwali abun sai wanda ya gani,Hafsat kuwa Code lace ta sanya ajikinta,riga da skirt milk colour,su aunty babba hada trolley na kayan sawa,ta sanya abayan boot ɗin motarsu,dama tace in taje sai tayi sati biyu,hafsat dae kallonta kawai takeyi,ita kadae tasan me zai biyo baya,hafsat ce take tuƙin motar yayin da aunty babba ke zaune agefenta, kafin su fita daga garin Kaduna,Hafsat tace"Mommy,yakamata mu tsaya a kasuwa ki saya mana niqabi," aunty babba tace"Niqab kuma?daughter me zamuyi da niqabi sai kace wasu munafukai," murmushi hafsat ta saki tare da cewa"Mommy zaiyi mana amfani sosai,tunda nace maki mu sayi niqabi akwai dalilin dayasa nace maki haka,' .....guntun tsoki aunty babba tasaki tana cewa"Ni ba wani niqabin da zan siya,kedai in kina buƙata ga hanya nan kije ki siya," Parking ɗin motar tayi,adai dai bakin wani shopping mall, "Ni zanje in siya,kina bukatar wani abu"? "A'a adawo lafiya," Fita hafsat tayi daga motar,kusan 15 mins sai gata tadawo hannunta ruƙe da sabon niqab,ta siyo,komawa tayi cikin motar,sannan ta tashi motar,suka miƙi hanya,

A 6angaren Amani kuwa tuni ta kammala shirinta,sun ɗau wankan lafaya itada Amal,Abbas da kanshi ya ɗaukosu acikin Motarshi,

Wuraren ƙarfe biyu da rabi na rana,wasu matsiyatan motoci haɗaɗɗun gaske,suka shigo cikin layin gidan,irin motocin nan na jigunan masu kuɗi,masu rai da numfashi,su huɗu ne motocin tare da security guards suke,kowace mota soja ne ke driving ɗinta,har suka ƙetara gate ɗin gidan, A jere motocin suka tsaya,da gudu wani soja,jiki na rawa yazo ya buɗe mata ƙopa, Tunkafin ta fito daga cikin motar,hayaƙin tabar da take sha ya fara fesowa waje,tashin hankali da ba'a sama shi date !Ko wacece Wannan

*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃

*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*

*LOCATION KANO*

08062073990 Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka Wadrobe balls Madarar kulleccham Vaseline kulleccham Kajiji Halut Couscous Khumrah Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining. Snack Awarah Farah Zobo Samosa Cup cake etc Contact me 09063302182or 09012179727.

[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Ƙarasa fitowa tayi daga cikin motar,jikinta na sanye da wani jigunannan lace,anyi mata riga da zani,rigar takai har guiwarta,ta coge ɗaurin ɗankwalin nan ture kaga tsiya,tun daga kan wuyanta zuwa hannayenta,duk zinari ne,tsohuwa mai ran ƙarfe,hajiya Ammi kenan Ummu Hossein,Ummu Azeema,Ummu Abusufyan,kaka ga su junaidu da kuma sehrish,fara ce tass bafullatanar asali doguwa kuma siririya,tsufanta bai hanata yin gayu ba,tsohuwar soja ce wadda tasha gwagwarmaya,kuma itace mace ta farko a lokacinsu data fara ruƙe muƙamin Major General,kaifi ɗaya ce ita,mace mai wuyar sha'ani,mutum mai tsananin haƙuri ne kawai zai iya jurar zama da ita,hannunta ɗaya na ruke da sandar karfe ta alfarma,yayin da ɗayan kuma yake ruƙe da sigari,tana tafiya tana busa ta,har ta hanci hayaƙin ke fitowa,

Babu wanda yayi tunanin cewar zatazo da wuri,bata sanarma kowa ƙarfe nawa zata zo ba,duk sunyi tunanin sae wuraren marece zata ƙaraso,Atare da MG Osman da Captain Adam suka zo,sae Hajiya Sarah ƴar wurin yayanta Modibbo,tare da ya'yanta mata su biyu Yasmeen da noor,dukkansu ba zasu wuce shekara ashirin da biyu ba,tunda matasan gidan sukaji zuwan ammi nan fa kowa yasha jinin jikinshi don sun san zuwanta bai cika zama alkhairi ba,duk in tazo sai wani abu ya faru,wannan karan basu san dame tazo ba,gaba ɗayansu sun hallara a main palour ɗin suna jiran ƙarasowarta ciki,mutun ɗaya ne bai fito wurin tarbarta ba,bakowa bane face Abusufyan,tun da yaji zuwanta ya kasa samun sukuni,sae faman safa da marwa yakeyi acikin bedroom ɗinshi,jikinshi nata kerma ba don komai ba sai don zullumin abunda zai biyo baya,idan tayi arba da triplet ɗinshi,duk da yayi ma kanshi alƙawarin cewar,koda ace ta koresu to tabbas ƙafarsu ƙafarshi,bazai ƙara barin rayuwarsu ta wulaƙanta ba,duk inda zasu je zai kasance atare dasu,

hayamm kuwa tana la6e jikin window tana leƙen Ammi,tun fitowarta daga mota,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta saboda tana sa ran cewar tuggun da suka shirya,zaiyi aiki,

Lokacin da suka shiga falon,nan fa kowa ya shiga miƙa gaisuwa,abun da zai baka mamaki,ko amsawa wannan batayi kamar mai fama da ciwon baki,sai dae ta ɗaga masu hannu,Azmee ce ta kaisu ɗakunan da aka gyara masu,domin su sauke gajiyar da suka kwaso,kafin zuwa anjima,kowa sai da ya kara zuwa gaishe ta ɗaya bayan ɗaya har ɗakin data sauka,mutun uku ne kawai basuje gaishe ta ba,Sgr,Abusufyan sae junaid wanda bai kaiga fitowa ba daga bedroom ɗinshi,

Mg Osman kuwa a nan falon suka zauna tare da Marshal Omar,suna gaggaisawa,saboda anjima ba'a haɗu ba sunyi kewar junansu sosai,

Hayaam tana ƙoƙarin zuge glass ɗin windon da take leƙe sai ga Motar Abbas tayi parking cikin gidan,tsayawa tayi tana jiran ganin su wanene kuma suka ƙara zuwa,kodai Aunty laila ce ta ƙaraso ne,bata ƙarasa zancen zucin nata ba,Abbas ya fito daga cikin motar,daga bisani kuma Amani da Amal suka fito atare daga cikin motar, Ƙura ido Hayaam tayi tana ƙare ma Amal kallo,cike da mamakin wacece wannan Kyakkyawar yarinyar da Amani tazo da ita,A iya saninta dae Amani bata ta6a haihuwa ba,balle harta haifi ƴa kamar wannan,duk yadda taso ta gane wacece yarinyar nan amma hakan ya gagara,kwakwalwarta a toshe take,saboda tsabar mugunta irin tasu tun Amal na ƙarama suka canza mata kamanni saboda uƙubar da take sha a hannunsa,dole hayamm ta kasa gane wacece ita, "Hayam!"muryar Azmee ce ta karaɗe kunnanta,da sauri ta rufe glass ɗin windown tare da juyowa tana kallon Azmee,shigowarta kenan ɗakin jikinta na Sanye da jallabiya baƙa,anyi mata kwalliyar zanen flower blue,veil ɗin data yafa ma blue ne,ba ƙaramin kyau azmee tayi ba,ta wanku sosai, Ƙarasawa hayaam tayi wurinta tana faɗin"Aunty Azmee sae yanzu za'a tuna dani?yunwa kamar zata kashe ni,kowa yana rayuwarshi acikin gidan nan sai ni duk a ƙuntace," "Ke kika so ki ƙuntata kanki hayam,Sgr yanzu haka ya manta da cewar ya koreki daga gidan nan,zai iya yiwuwa ma ya manta dake gaba ɗaya,kuma kinga yau ranar Walima ne mutane duk sunzo,ba dole bane ya ankara dake ba,bama haka ba mutumin da kafin ya ɗaga ido ya kalli wani aiki ne a wurinsa,don haka ina baki shawarar ki daina kullan kanki," Tun kan azmee ta ƙarasa maganar hayaam ta soma washe baki,la66anta har rawa sukeyi wurin cewa"An..aunty Azmee kina nufin sgr ya manta da laifin da nayi mashi kuma zan iya fita inyi yawo na acikin gidan nan kamar kowa,' Jinjina kai azmee tayi tare da cewa"Of course,amma fa hayaam koda gigin wasa kada ki kuskura ki ƙara yunƙurin zuwa sashen shi!duk yawon da zakiyi ki tsaya a downstairs babu ruwanki da abunda ya shafi upstairs ina fata kin gane"? yatsina fuska tayi tana fadin"dama ni Aunty azmee me zai kai ni,waccen karan ma tsautsayi ne da ƙaddara," "Sannan kuma,kada ki kuskura ki ƙara shiga shirgin Sehrish!kinsan dai yanzu tafi ƙarfinki nesa ba kusa ba,ƴar masu gida ce ita,kuma shalelen daddynsu,ga kuma yayyanta maza muddin kikace zaki ta6ata wlh zaki ta6o ma kanki ne,akanta sae abaki Red card na barin gidan nan," ta6e baki hayaam tayi,tana faman hura hanci,maganar ba ƙaramin ƙona mata rai tayi ba,don bata da yadda zatayi ne, Murmushi azmee tasaki tare da juyawa ta kama hanyar fita tana faɗin"Yakamata kiyi wanka,ki shirya saiki fito ayi shagalin dake," Cikin sauri ta ruƙo rigar Azmee tace"Aunty Azmee don Allah ki taimakamun wlh yunwa nake ji,tun jiya da daddare rabona da Abinci," "Its Okey,zan kawo maki yanzu," Komawa ciki hayaam tayi tana jiran azmee ta kawo mata abinci taci,kafin tayi wanka ta kimtsa, bayan su Amani sun shigo cikin main palour ɗin,anan suka zauna suna gaisawa dasu kanal yousouf,kafin tabar wurin tare da Amal,wurin Azmee taje suka gaisa tayi masu kwatancen ɗakin Hajiya Azeema da kuma na gwaggo,duk saida tabisu ta gaishe su,hatta ɗakin Abusufyan saida suka je,sukayi mashi Allah sanya Alkhairi,daga nan suka dawo kitchen,lokacin Azmee tana haɗa ma Hayaam lunch ɗin da zata kai mata, Juyowa tayi jin sallamarsu tace"har kun dawo"? Amani tace"Eh,duk naje nayi masu Allah sanya alkhairi,yanzu abunda ya rage mun inason zuwa wurin dasu yaran suke,bansan a wani ɗaki suke ba,' Azmee tace"Ae suna nan ɗakin da Sehrish take,ae kinsan ɗakinta wanda ke a kusa da namu,yakamata kuje wurinsu,' Murmushi Amani ta saki aranta tace"ba dole inje ba,ni da nakeson na gyara tsakanina da Sehrish," A fili kuma tace"okey,nagane ɗakin bari muje wurinsu," Juyawa sukayi atare da Amal suka nufi ɗakinsu sehrish,abakin ƙopar ɗakin suka tsaya,Amani ta kwankwasa ƙopar,jahad ce ta buɗe kopar,ba ƙaramin kyau tayi ba,wankan swiss lace ne ajikinta wanda aka haɗa da bazin shadda,stones work ne ajikin kayan wanda ya ƙara fito da ɗinkin sosai, Murmushi Amani ta sakar mata tare da cewa"Sehrish ce ko"?ta tambaya ne saboda Abbas ya sanar da ita cewar kamanninsu ɗaya sak, Martanin murmushin jahad ta mayar mata kafin tace"A'a,ba ita bace,tana ciki in kira maki ita ne,"ta ƙarasa maganar tana kallon Amal wadda itama jahad ɗin take ta kallo, Amani tace"bari mu shiga daga ciki,sai mu gaisa," Matsa mata hanya jahad tayi suka shiga cikin ɗakin, A lokacin Sehrish na kwance saman gadon ta ɗan kishingiɗa,tana hutawa,saboda ba ƙaramin gajiya tayi ba,sun sha zurga zurga,gashi Anjima za'a fara walimar bayan Sallar la'asar,shiyasa ta dawo ɗaki don ta huta,kafin lokaci yayi,ganin Amani yasa ta miƙewa daga zaune tana kallonsu, Wuri Amani ta samu daga gefen gadon ta zauna,Amal ma ta zauna,tun kafin ma Amanin tace wani abu sehrish tace"Sannunku da zuwa,"hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma Amani ba,tayi tunanin zata ga akasin haka ne, "Yawwa,fatan mun same ku cikin koshin lafiya"? Sehrish tace"Lafiya lou Alhmdllh," Amani tace"kin gane ni ko"?murmushi kawai sehrish ta saki,taya za'ae ta manta da matar da tace zata iya rasa ranta idan ta cigaba da shisshige ma matasan gidan, "Ina fata dai baki ruƙe ni aranki ba?dan Allah ki manta da komai dana ta6a faɗa maki,komai ya wuce,yanzu zumunci ya ƙullu atsakaninmu,ko wancen karon ma da nayi maki wannan maganar,wlh bada wata manufa na faɗa maki hakan ba," Jinjina kai Sehrish tayi tare da cewa"babu komai,ae ya riga ya wuce," Ba ƙaramin daɗi Amani taji ba,juyawa tayi tare da kallon jahad dake tsaye tace"zo ki zauna mana,inaso muyi fira tare daku,"zagayawa jahad tayi ta 6angaren hannun hagu ta zauna daga gefen gadon, Amani tace"ina cikon ta ukun take ne?Abbas ya faɗamun cewa ku ƴan uku ne," Jahad tace"hakane,hosana ce babu,taje wurin yaya Omar ne" shiru Amani ta ɗan yi tana maimaita sunan hosana a cikin zuciyarta,kamar ta ta6a jin sunan abakin wani,"ke ya sunanki"? "Ni sunana jahad," jinjina kai amani tayi tare da cewa"Suna mai daɗi,amma nifa bansan komai ba,agame daku,sehrish kawai nasani tana aiki a gidan nan," Jahad tace"ae mu muna a wurin ya Omar ne,shi ya taimake mu a lokacin da muke cikin mawuyacin hali,bayan ƙaddara ta rabamu da ƴar uwarmu," ..A ruɗe Amani tace"Hannun Ya Omar" Jahad tace"eh," Cike da son jin ƙarin bayani Amani ta kuma cewa"Kun zauna a kaduna ne"? Ita kanta jahad sai da gabanta ya faɗi jin Amani ta ambaci kaduna kai tsaye,taya akai tasan cewa sun zauna a kaduna, Daƙyar ta iya bata amsa da cewa"Eh,mun zauna acan,daga baya ne Ya Omar ya dawo damu Abuja,gidan daddynmu," Tashin hankali,miƙewa amani tayi da sauri jikinta na rawa tace"Ga Amal nan ƙanwata ce,in ba damuwa ta zauna a wurinku," Amsa mata sukayi da toh,cikin sauri ta fuce daga ɗakin,kallon juna jahad da Sehrish suka yi atare,duk sun lura da yadda Amani ta ruɗe, "Wacece wannan Sehrish"?jahad ce tayi mata tambayar,sehrish tace"matar yaya Abbas ce,Aunty Amani," Taso ta ƙara tambayarta,amma saboda Amal dake zaune a wurin yasa tayi shiru,tabbas ta so taga kamannin Aunty babba kaɗan a fuskar Amani,duk da Amani tafi kyau sosai,kuma ita bata da jiki irin na Aunty Babba,miƙewa jahad tayi tare da cewa"Zan fita yanzu zan dawo," Sehrish tace"adawo lafiya," Bayan jahad ta fita,Sehrish ta kalli Amal dake zaune,rashin sabo yasa ta kame kanta wuri guda, Murmushi tasakar mata tare da cewa"ki saki jikinki mana,naga duk kin gaza samun natsuwa,ko dan bamu ta6a haɗuwa bane?" Sunnar da kai Amal tayi tana murmushi,wata irin kunyace da ita,daƙyar ta iya cewa"banta6a zuwa nan ba,yau nafara zuwa,bazan iya sakin jikina ba,tunda bansan kowa anan ba," Sehrish tace"Ae kuwa yanzun nan zansa ki saba dani,da farko dai ki dinga kirana da Aunty Sehrish,saboda ina kallon ƙaramar fuskar nan taki nasan cewa na girme ki,tsawo ne kawai gare ki,amma a shekaru ba zaki wuce sha huɗu ba,ko nayi ƙarya"? dariya Amal tayi tana girgixa kai tace"A'a bakiyi ƙarya ba,shekarata sha huɗu amma na kusa kai shekara goma sha biyar,nan bada jimawa ba," "Kice zamu zo yanka cake ko"?acewar sehrish, Amal tace"Eh,zan gayyace ku idan lokacin yayi," Sehrish tace"Nima na kusa cika shekara sha takwas,banma sani ba ko na kai shekara sha takwas ko ban kai ba,nifa banma son ranar da aka jefo ni duniya ba,ni dai kawai na ganni ina yawo na ne....'kasa ƙarasa maganar tayi saboda dariyar da Amal ta kwashe da ita,abu kamar wasa sai gashi cikin lokaci ƙankani sun saba da juna,nan suka zauna suna ta fira atsakaninsu,

Amani kuwa tun bayan da ta fita daga ɗakinsu sehrish,tarasa inda zata tsoma kanta,abun ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,Aunty babba ta sanar da ita cewar tasa an zubar da yaran da Omar ya kawo mata,kuma tace mata ƴan biyu ne yaran,hakan na nufin cewar jahad ne da hosana a wurinshi?kamar yadda jahad ta sanar da ita cewa su A wurin yaya Omar suke,indae dagaske hakane to taya akai Yaran suka dawo wajen Marshal Omar bayan tasa an zubar dasu!?kodai Omar ya sanya ɗan leƙen asiri ne acikin gidan?tabbas hakan zai iya faruwa,indai kuwa hakane Watan cin uban Aunty laila ya tsaya,Zuwa maiduguri ba fashi, Acewar Amani wadda ke ta faman yin safa da Marwa a tsakanin corridor ɗin ɗakunansu sehrish,daga bisani tace"Allah yaso ni ban tsoma hannu na ba,a wurin cutar dasu ba,ashe da rabon aure na yayi lasting,Aunty babba kam ta shiga uku,taja ma kanta bala'e,kwara ma da hakan ya faru,da nayi niyyar ɗaukar ma Amal fansa,amma yanzu na fasa,zan zuba idone kawai inga yadda dramar nan zata kaya,"ta ƙarasa zancen zucin nata,fuskarta ɗauke da murmushi,ba komai take hangowa ba face yadda rayuwar Aunty babba zata ƙare,........'

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull