Kenza eBookz

Abban sojoji takun karshe complete - Chapter 14

Abban sojoji takun karshe complete - Chapter 14

Abban sojoji takun karshe complete Chapter 14: Abban sojoji takun karshe complete Chapter 14. Sam ta manta da hafsat dake kwance a ɗakinta,baiwar Allah tun…

4,078 words

Sam ta manta da hafsat dake kwance a ɗakinta,baiwar Allah tun bayan fitarta daga ɗakin hayaam,ta wuce ɗakin azmee batare da sanin kowa ba azmee ce kaɗae tasan cewa tana a ɗakinta,anan tayi wanka,ta kuma ci abinci ta kwanta,saboda wani irin zazza6i daya saukar mata ajikinta,kwata kwata zuciyarta ba daɗi,tayi danasanin rayuwarta fiye da a ƙirga,idanunta na tsananin son ganin Su Jahad,amma tsoran tunkararsu takeyi,gashi har tsaraba tayi masu don ta basu hmmm,duk in ta tuna irin uƙubar da suka sha a hannunsu,sae ta fashe da matsanancin kuka,tun azmee na rarrashinta har ta gaji ta ƙyaleta,idanunta sun kumbura suntum haka la66anta ma,bakomai take yi ma fargaba ba,fa ce irin hukuncin da Mahaifinta zai yanke mata,don kuwa tasan muddin yaji abunda suka aikata masu jahad,Wlh ba zasu sha ba,su dukan su sae sun fuskanci mummunan hukunci a wurinsa,gaba ɗaya tayi nisa cikin zurfin tunani,taji shigowar azmee cikin ɗakin,buɗe idanunta tayi tana kallon azmee dake shigowa,yanayin yadda taga fuskar azmee ya tabbatar mata da cewar tana cikin damuwa,gefen gadon ta zauna zugudum yayin da idanunta ke cike tab da kwalla, "AUNTY AZMEE" muryar hafsat ce ta dawo da ita cikin hayyacinta,juyawa tayi bayanta tare da kai idanunta kan fuskar hafsat dake kawance,ƙoƙarin 6oye damuwarta tayi kafin tace"har yanzu bakiyi bacci ba? Miƙewa hafsat tayi daga zaune,sannan tace"Bazan iyayin bacci ba aunty azmee,inajin tsoron abunda zai biyo baya,nasan cewa daddy bazai ƙyaleni ba,"ta ƙarasa maganar tana faman matse kwallon dake gangarowa akan fuskarta, "Kidaina sa damuwa aranki hafsat,a yadda kika bani labarin irin ruƙon da kuka yi masu jahad,da farko atare kuka azabtar da rayuwarsu ke da mahaifiyarki amma kuma daga baya kin nuna masu soyayya,ina mai tabbatar maki da cewar wannan soyayyar da kika nuna masu daga baya itace zata cece ki a hannun mahaifinki...." "Taya kike tunanin hakan zai zame mun mafita aunty azmee?bayan ni ce dakaina,na ɗauki su jahad acikin mota ta,na fitar dasu daga cikin gidan,na damƙa su a hannun wannan mugun mutumin wanda mommy tasa ya zubar mata dasu a daji!"tana magana hawaye na zuba a fuskarta, "Amma Ae kin sanar dani cewar,Mommynki yaudararki tayi akan cewar gidan marayu zaki kai su ashe zubar dasu take so ayi," "Hakane aunty azmee,amma ae su hosana basu son da haka ba!nasan cewa sun tsaneni yanzu,kallon mayaudariya suke yi mun,kuma ba kowa ne ya jawo mun haka ba,fa ce Mommy," Ta ƙarasa maganar tare da fashewa da wani sabon kukan, "Ga shawara"! Cikin shessheƙar kuka Hafsat tace"Ina...sauraronki,koma wata irin shawarace inaso," "Gobe da safe tun kafin Abbanki ko Omar suyi yunƙurin tunkarar Su jahad akan maganar,ke ki fara yin hanzarin zuwa wurinsu ki nemi yafiyarsu sannan kiyi masu bayanin cewar bada saninki ba,wannan mutumin ya ɗauke su ya kaisu daji don ya zubar dasu ba,Mommynki ce ta yaudareki akan cewar gidan marayu zai kai su....." "Aunty azmee kina ganin in na faɗa masu hakan zasu yarda dani?hosana fa tana da ta6in hankali,daƙyar zata fahimce ni," .."kada ki damu,zasu fahimce ki,ki kwantar da hankalinki kawai,kamar kina acikin jirgi mai ya qare,"murmushi hafsat ta ɗan saki,har taji sanyi aranta,fatan ta Allah yasa gobe in taje wurin su Jahad,su fahimce ta, Sun jima suna tattaunawa atsakaninsu kafin daga bisani,azmee tabar ɗakin hafsat kuwa bargo taja ta lullu6e kanta,sannu a hankali bacci ya ɗauke ta,

Acan falo kuwa bayan komi ya lafa,Ammi tace"Yakamata kowa yaje yayi sallah,ya kwanta ya huta,"amsa mata suka yi da toh,sannan kowannansu ya miƙe tare da nufar Bedrooms ɗinsu,atare Su jahad suka miƙe,saida suka fara yi ma su ammi sallama,ta amsa masu fuskarta asake tare da tunasar dasu akan in zasu kwanta kar su manta suyi addu'a,a ƙarshe dae falon ya rage babu kowa cikinsa,irfan shiya jagoranci Modibbo har zuwa ɗakin da zai zauna kafin gobe,Bayan ya kaishi ɗakin,Azmee ta shirya mashi kayan tea takai masa,kamar yadda ya buƙata,

*Boss Bature*

🤍❤🤍

A 6angarensu sehrish kuwa,bayan sun koma bedroom ɗinsu,alwala kowannansu yayi sannan su kayi salla atare,bayan sun kammala suka haye saman gadonsu,cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya ɗauki Jahad da Hosana,banda sehrish wadda bacci ya ƙaurace ma idanunta,tabbas ɗazu ta tsorata sosai da Ammi ta koresu,abun ya razanar da ita,ta kuma ji matuƙar tausayin Daddynsu,duk in tazo rufe ido,fuskarshi take gani a lokacin daya fashe da kuka yana faɗin cewa sai dai ta tsine mashi amma sai yabi ƴa'ƴan shi,bazai bari rayuwarsu ta wulaƙanta ba,tabbas ba ƙaramin so yake yi masu ba,yana tsananin ƙaunarsu fiye da tunaninsu,lokaci guda abunda ya faru a babban falo ya shiga dawo mata acikin kanta,mikewa tayi daga zaune,ta jingina bayanta a headboard din gadon,yayin da hannayenta ke rungume da pillow,a hankali tashiga tariyo abunda ammi tayi,na bijirema umarnin iyayenta,wanda hakan yasa ita ma ƴa'ƴanta suke bijire mata,Wannan abun ba ƙaramin tsoratar da sehrish yayi ba,saboda tunawa da Umarnin da mahaifinta ya bata na hana ta zuwa sashen sgr da sunan yi mashi aiki,amma taƙi bin umarninsa,hakanan ta dinga jin gabanta na faduwa,runtse idanunta tayi tare da buɗesu a hankali,wasu siraran hawaye ne suka shiga gangaro mata a fuskarta,a hankali la66anta suka soma motsi,ƙasa ƙasa take magana,matsar da kunne na nayi don inji me take cewa, _Ya Allah ka yafemun!bani da hankali nayi kuskure,saboda kawai son wanda baisan inayi ba,saboda na faranta ma wanda nakeso,naƙi bin umarnin mahaifina,wlh bazan ƙara ba,inajin tsoron nima ƴa'ƴan da zan haifa suƙi bin umarni na,bana fatan hakan ya faru,zan daure nayi mashi biyayya_ Tafin hannunta tasa ta goge hawayen dake zuba a idanunta,bakomai idanunta ke hango mata ba,fa ce kyakkyawar fuskar SGR,tabbas yau yayi masu abunda ba zasu ta6a mantawa ba arayuwarsu,yana da matuƙar kirki sosai,bakowa ne zai gane hakan ba farat ɗaya,shi na musamman ne,samun mutun mai irin kyakkyawar zuciyarshi a wannan zamanin da muke ciki,zaiyi matuƙar wuya, Zuro ƙafafunta tayi ƙasa daga saman gadon,ta miƙe tsaye,jikinta na sanye da riga da wando na bacci,milk colour,takawa tayi izuwa gaban door ɗin dakin,ta buɗe bayan ta fita ta janyo masu ƙopar ta rufe, A hankali take tafiya,ga wani irin sanyi dake ɗan ratsa sassan jikinta,amma sam bata jin sanyin,saboda daɗinshi take ji,zura hannayenta tayi acikin aljihun wandon jikinta,kai tsaye ta wuce main palour din,wayaam taga babu kowa kamar yadda tayi tsammani,da alama ma mutanen gidan duk sunyi bacci,hakanan taji tana marmarin tasha Cornflakes acikin wannan daren,juyawa tayi da sauri ta nufi kitchen,within minutes ta fito hannunta ɗauke da Cup,ta cika shi da cornflakes haɗi na musamman tayi mashi,ta zuba uwar madara da bornvita duka ta sanya,ta kuma Tsula sugar,' Dawowa tayi falon,ta zauna saman sofa tare da aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya,nace sannu ƴar masu gidan, Motsa cornflakes ɗin ta shiga yi,da cokalin hannunta sae faman jujjuyashi takeyi aciki,kafin daga bisani ta shiga ɗebowa tana kaiwa abakinta tana sha,tana taunarsa kunnuwanta na motsi saboda daɗin da yayi,bakowa ne ya faɗo mata aranta ba fa ce junaid,abokin shiriritarta,murmushi tayi tare da cewa ɗan uwana rabin raina nasan yanzu haka yana can yana sharar baccinshi,da ace idonshi biyu da atare zamu sha wannan cornflakes din,i really missed u junaid,rashin kwanciyar hankali yasa,mun nisanta da juna,amma insha Allah tunda komai ya dai²ta,yanzu bamu da sauran wata damuwa,zamu dinga fita yawan shaƙatawa atare mu dukkan mu,

Ita kaɗae abunta sai faman sambatu takeyi,kamar wata zautacciya,tana cikin shan cornflakes ɗinnan,ta wutsiyar idonta ta hango mutun a tsaye ƙiƙam,aikuwa hankalinta yayi mugun tashi,kasa juyawa tayi saboda tsoron kar ace dodo ne,tuni jikinta ya fara kerma,dama gata da shegen tsoro,zuciyarta ta shiga bugawa da ƙarfi da ƙarfi,tunaninta wanene mutumin data hango tsaye a upstairs,tsabar tsoro ya hana ta juyawa ta kalleshi da kyau,wani irin wahalallan yawu ta haɗiye,ajiye cup ɗin dake hannunta tayi,sannan ta lalla6e tare da saukowa daga saman sofa ɗin,ta durƙushe ƙasa tayi sujjada,kamar maiyin sallah,duk don saboda kar dodon ya ganta,a hankali ta shiga rarrafawa a ƙoƙarinta na tabar falon,ta koma ɗakinsu, Shikuwa mutumin dake tsaye goye da hannayenshi asaman ƙirjinshi,zuba ma sarautar Allah ido yayi,abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba,tsoran yarinyar harya so yayi yawa,ko kallon inda ya ke bata yi ba,ta wutsiyar ido kawai taga inuwarsa amma ta sama ranta cewar wani mugun abunne,sam baiso ta tsorata ba,don bada niyar wannan yazo wurin ba, Wani abune ya faɗo mashi aransa,cikin sauri ya koma cikin part ɗinsa,jimmm kaɗan sai gashi ya dawo hannunshi ɗauke da wayarsa,tsayawa yayi tare da saita wurin da take yana ɗaukarta video kasancewar akwai haske sosai a main falo din, Ba ƙaramar wahala sehrish tasha ba,da wannan rarrafen ta ƙarasa har wurin da zata shiga corridor ɗin ɗakinsu,gaba ɗaya zufa ta wanke mata fuskarta,tana ƙokarin shiga,wani abu ya faɗo mata aranta,tsayawa tayi tana tunanin kodai ta juya taga wanene shi tunda dae ta iso wurin da zata shiga ɗakinsu,koma menene ai bai isa ya cutar da ita ba,da zarar ta juya taga dodo ne,sae ta watsa da gudu ta shige ɗakinsu,taja ƙopa ta rufe,fakat, Jikinta na kerma,amma ahaka ta daure ta ɗan juyo da kanta,takai idanunta saman upstairs din,ae batasan lokacin da taƙarasa juyowa gaba ɗaya ba,ta baza idanunta donta tabbatarma kanta abunda take gani,ƙura ido tayi tana son gano wanene saboda yayi mata nisa,wannan hasken fatar nashi ne ya fara sa ta tunanin kamar sgr ne,ƙara zuba ido tayi anan ta hango wannan doguwar sunar kan tashi,tabbas kuwa shine,ajiyar zuciya ta shiga saukewa a fili tace"Ashe babban yaya ne,nasha wahalar banxa,Allah yasa dai ban zubar da cornflakes ɗina ba, ganin tana kallonshi,yasa ya janye phone dinsa,ya kashe camera ɗin ya tura wayar a short pocket dinsa,da hannu yayi mata Alamar taxo, Waro ido tayi tare da nuna kanta,don ta tabbatar in ita yake kira,nuna ta ya kuma yi da hannunshi, Gabanta ba ƙaramin faɗuwa yayi ba rasss,tsoranta kar ya tuhumeta akan meya hanata zuwa part ɗinsa kai mashi Cofee don yau bata je ba,

Miƙewa tayi kamar wata mara gaskiya,haka ta tunkaresa,kamar an zare mata lakar jikinta,a hankali take tattaka matattakalar stairs ɗin,harta ƙarasa ɗan nesa dashi tukunna ta tsaya,tunda ta saci kallonshi sau ɗaya,tayi arba da faffaɗan ƙirjin nan nashi,gashi babu shirt ajikinsa,Shorts ne kawai black colour ya sanya,kuma ma dai ba ƙaramin kyau yayi masa ba, Ganin ta tsoge wuri guda,yasa shi moving ya ƙarasa inda take dab da ita,don har saida ta ɗan ja da baya,saboda ƙure matan da yayi, Lokaci guda tarasa natsuwarta,sai ƴan kame kame take,a ƙarshe ma ta zura hannunta acikin sumar kanta,tana ɗan sosawa,ƙamshin turaren jikinshi ba ƙaramin illa yake yi mata ba,saboda wani yanayin da take tsintar kanta aciki, gaba ɗaya idanunshi na akan lips ɗinta,mutsu mutsun da takeyi da bakinta,ba ƙaramin tafiya yake yi dashi ba, Almost 5 mins suna a haka sannan ya buɗe baki da wannan Sexy voice ɗin tasa yace"Meyasa baki yi bacci ba"? Muryarta na kerma tace"bana jin bacci ne," "Okey,that's y You came out to disturb those who are sleeping"?

sunnar dakai ƙasa tayi tana girgiza mashi kai,alamar a'a,ganin ta dage sai faman sosa gashin kanta takeyi,yasa shi kai hannunsa ya damƙo wrist ɗin hannunta da ta zura acikin sumar kanta yace"ƙaiƙayi kike ji ne"? A ruɗe tace"eh," Jinjina kanshi yayi tare da sakin hannun nata, .."lemme help u.......'ɗagowa tayi a razane jin abunda yace,ko amsarta bai tsaya ji ba,ya sanya hannunshi tare da zagayo dashi ta gefen waist ɗinta ya tallabota sosai, ya janyota gaba ɗaya ta faɗa asaman wide chest ɗinsa,nan fa hankalinta yabi ya tashi,ta susuce ta zauce ta rasa uwar ubanta,a hankali ya ɗago da right hand dinsa,ya tsoma shi acikin lallausar sumar kanta,wani irin massage ya shiga yi mata,wanda ya haifar mata da wata irin matsananciyar kasala ajikinta,ita kanta batasan lokacin da ta zagaye waist ɗinshi ba da hannayenta duka,ta ƙankame shi sosai kamar zata koma cikin cikinshi,yana jin yadda numfashinta ke fita da zafi zafi,tausasan la66anta sai gogar masa fatarsa suke,sosai sehrish ke shaƙar daddaɗan ƙamshin jikinshi,tana jin kanta a wata irin duniya,wadda ba kalar tamu ba,just like in the dream haka take kallon lamarin,ta rasa gane wai shin SGR sosa mata kanta yake yi ko kuwa,saboda daɗin dake ratsa jikinta yafi ƙarfin a kirashi da daɗin susa kawai,tamkar zata zauce haka take ji,ga wani irin abu dake yi mata yawo a jikinta tamkar zufa,'

Duƙar da kansa ya ɗanyi tare da kai hancinsa ya cusa sa shi acikin sumar kanta,ƙamshin man da take shafama kanta ne ya daki hancinsa sosai ya shaƙe sa,lumshe idanunsa yayi tare da ɗan ware su a hankali ya buɗe su,kafin ya mayar da la66ansa asaman fatar kunnanta,tamkar mai yin whispering haka ya shiga yi mata magana"tell me What did you do in the kitchen when you entered"? Yayi maganar tare da raba jikinshi daga nata,idanunshi tamkar na mai jin bacci, "Cornflakes na haɗa,saboda in sha,"ta bashi amsa a yayin da idanunta ke kallon yatsun hannunta data haɗesu wuri guda tana wasa dasu,. "Okey,ɗaukomin cornflakes ɗin,inaso nasha nima," Batare da musu ba,ta juyawa da sauri da sauri ta sauka downstairs,a nan saman table,ta ɗauko cup ɗin da ta ajiye,sannan ta dawowa upstairs ɗin ta kawo mashi,miƙa mashi tayi,ya sanya hannu tare da kar6ar kofin,spoon ɗin ya ɗauka tare da ɗan jujjuya shi,kafin ya ciko cokalin yana ƙokarin kaiwa bakinsa yaji tace"Kamar yayi yawa,'ɗan ɗagowa yayi da idanunshi ya kalli fuskarta da sauri ta kawar da nata idanun gefe,saboda taga ya ɗebo da yawa ne kuma mouth ɗinsa is too small shiyasa tayi mashi magana,a ganinta cokalin bazai iya wuce wa ba,ta cikin bakinsa,amma sai gashi ya shanye abunsa,bayan ya tauna cornflakes din,ya ɗan dakata tare da cewa"Bana shan sugar sosai,sannan milk ɗin ma tayi yawa acikinsa,meyasa kika sanya da yawa har haka"? . shiru tayi tana faman wurga ido, Miƙa mata cup ɗin yayi tare da cewa"Kar6i kayan ki"hannu tasa ta kar6a,sannan tace"Zan iya tafiya,"? Hanya ya nuna mata tare da cewa"na ruƙe ki ne"? Ajiyar zuciya ta sauke,kafin ta juya da sauri da sauri ta sauka donwstairs,duk yana binta da kallo,kitchen ta shiga a tsaye ta ƙarasa shanye cornflakes din ta ajiye cup ɗin,sannan ta fito tare da kai idanunta Upstairs taga in yana nan,a tsaye ta same shi,idanunshi a lumshe, Juyawa tayi ta kama hanyar zuwa bedroom ɗinsu,adai² corridor din ta kuma tsayawa tare da ɗan waiwayawa don taga in yana nan koya tafi,Again ta ƙara ganinshi a tsaye kuma da alama ita yake kallo,ranta ne ya bata cewar kodai tayi masa bye bye da hannunta,may be ya mayar mata da martani, ɗaga hannunta tayi tare dayi mashi bye bye,abun mamaki sai gashi ya ɗaga mata hannu yana yi mata bye bye din shima,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta,har batasan lokacin da ta fashe da dariya ba,da gudu ta juya tare da faɗawa bedroom dinsu, Ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa ya koma cikin part dinsa,bayan ya shiga bedroom ɗinsa,toilet ya fara shiga,bada jimawa ba,ya fito tare da hayewa saman shimfiɗeɗen gadonshi ya kwanta,tare da janyo pillow ya rungume shi asaman wide chest dinsa,yayin da blue eyes ɗinsa ke kallon haɗaɗɗen ceilling ɗin ɗakinsa,ya rasa gane meke damun shi,amma tabbas yana jin missing ɗin wani abu sosai atattare dashi,yana tsananin buƙatar wani abu,wanda baisan menene shi ba~~~~~~~ [3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Gaba ɗaya Aunty babba idonta bai hango mata su hosana ba,kutsa kai kawai takeyi cikin falon,hafsat dai tana la6e a bayanta,cike da fargaba, Ƙarasawa sukayi wurinsu,daga bayansu Sehrish suka tsaya,hakan yasa bata samu damar ganin fuskokinsu ba,sai faman washe baki take yi,gaishe dasu Abba suka farayi,fuskar kowannansu awashe,"Ishaq shine baka sanar dani zuwansu ba,"acewar Abba,General ishaq yace"Ni kaina bansan sun karaso ba,nadaisan munyi dasu kan cewa zasu taho," Abusufyan yace"masha Allah hafsat ta girma sosai,ba don ina ganin hoton ta ba,da bazan iya gane ta ba, Sunnar da kai ƙasa hafsat tayi tana murmushi ƙasa ƙasa,yayin da zuciyarta ke a cunkushe, duk su hosana basu ɗauki muryarta ba,amma da zarar tayi magana sai sunji tamkar sun ta6a jin muryar matar dake magana, "Muna taya ka murna Abusufyan,ƴa'ƴa har ƴan uku Allah ya albarkaci rayuwarsu,Alla ya.........'bata ƙarasa maganar ba sakamakon juyowar da sehrish tayi,Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu ji kake daram!!!dararam!!!yadda kasan ana buga ganga,Saboda tsabar kiɗima bata san lokacin da ta furta"Kutumar Uba...."gaba ɗaya hankalin kowa ya dawo kanta,jin ashar ɗin data buga,Hakan yasa Jahad da Hosana juyowa atare,Waro ido waje tayi hankalinta a matuƙar tashe,lokaci guda duk tabi ta gigice ta ruɗe ta rikice ta fita hayyacinta abunda batayi tsammani ba,la66anta har kerma sukeyi wurin nuna su da hannu tana ƙoƙarin tayi magana amma kermar da bakinta keyi ya hanata cewa komai, Hankalin jahad ba ƙaramin tashi yayi ba,ganin matar da ta azabtar da rayuwarsu,ta ƙuntata masu ta kusa halakasu,hosana kuwa a matuƙar tsorace ta faɗa bayan Marshal Omar ta ƙanƙame shi tana faɗin"Ya Omar,bansan ganinta,tsoranta nake ji,itace matar da ta azabtar da rayuwarmu,itace tasa aje a jefar damu cikin daji,har wannan tsohon mutumin ya kusa cutar dani,don Allah ya Omar ku kureta,azzaluma ce macuciya ce,bata tsoran Allah,bata da tausayi kuma bata da Imani, Hankalin kowa dake a wurin ya dawo kansu,gaba daya Abba dasu Abusufyan da sauran mutanen dake a wurin duk sun ruɗe sun gaza gane inda zancen nata ya dosa,Ishaq kuwa tun da yaga jikin Aunty babba na kerma,zufa na keto mata,ranshi ya bashi cewar tabbas ta aikata wani abu ne,saboda yasan halinta,muguwace kuma bata da gaskiya,Bashi ba hatta Marshal jikinshi yayi mugun sanyi,musamman da yaji hosana na fadin ta cutar da rayuwarsu nan ya fara tunanin Wasu abubuwa da yake zargi a lokacin baya,da kuma maganar da major ya ta6a sanar dashi na cewar baya son ya shiga tsakaninshi da matar Yayan shi, hannu Aunty babba ta aza akanta tana faɗin"Shikenan An yanka ta tashi,amaimakon ta mutu,nashiga ukku ni laila,Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un wani tsautsayi ne da ƙaddara suka kawo ni gidan nan,' Tunda Abbansu junaid yaji hakan yasan cewa tabbas akwai wani abu daya ta6a faruwa a tsakaninsu,koma dae menene bai kamata,su tuhumeta ba agaban ƙannen mijinta,a bainar jama'a kuma,ko ba komai Matar babban yayansu ce, "Ya Omar dan Allah,tabar wurin nan wlh bansan ganinta,kashe mu take son yi,shiyasa ta biyo mu har nan,"gaba ɗaya kukan hosana ya cika kunnuwansu,' Wani irin wahalallan yawu Aunty babba tazo haɗiyewa,nan take ta yanke jiki a wurin ta faɗi asume,da sauri hafsat ta tsugunna tare da tallabo ta,tana jijjjigata,

Gaba ɗaya duk sun kashe ma ishaq baki yama rasa abun cewa,tsananin baƙin ciki da takaici ya hanashi cewa uffan,jikinshi sae faman tsuma yake yi,burinshi kawai yaji abunda suka aikata ma yaran,da har suka tsorata da ganinsu,tabbas sai sunci Ubansu,muddin yaji wani da ba dai dai ba,don bazai yarda suja mashi tozarta ba a idon ƴan uwanshi,

Aunty Azmee ce ta taimaka wurin ɗebo ruwa suka yayyafa ma Aunty babba a fuskarta,ae tana farfaɗowa kamar wata zautacciya tayi zumbur ta miƙe,ko waiwayonsu ba tayi ba,ta watsa aguje,tayi cikin gidan,Allah kaɗae yasan inda ta kutsa kanta,

A fusace General ishaq zai bi bayanta,Abbansu junaid yayi saurin ruƙo hannunshi tare da cewa"kada ka bita,yakamata mubi komai a sannu,yanzu bamu kaɗai bane a wurin nan ba,akwai ƙannenka kuma akwai bare a wurin nan," Jinjina kanshi kawai yayi ba don ya haƙuri ba, Batare da sanin kowa ba,hafsat ta zame jiki daga wurin,saboda wani irin mugun kallo da taga Daddynta nayi mata,bashi kaɗae ba hatta Marshal kallon tuhuma yake yi mata,hakan ne yasata ta sulale tabar wurin,sauƙinta ma basu ambaci sunanta ba,amma tasan dole sunanta ya fito aciki,kuma daddynta in ya tashi yanke hukunci hada ita zai haɗa ya yanke mawa,tabbas tayi dana sanin biye ma mahaifiyarta wurin cutar dasu hosana,gayanan sunja ma kansu, Ruƙo hannun hosana yayi tare da janyota,ta dawo ta gabanshi,fuskarnan tayi jawur,sae faman kuka takeyi tana faɗin"ya Omar a koreta tabar gidan nan,bana son ganinta,bata da Imani,itace ta rufe mu acikin store tayi mana horon yunwa,ta dinga bugunmu da bulala,kuma ta dinga samu aiki,har gadon asibiti sai da aka kwantar dani.......' Cikin sauri Omar ya sanya tafin hannunshi ya toshe mata baki,cikin lallashi yace"its ok hosana,na fahimce ki,zansa sojoji su koreta daga gidan nan hakan yayi maki," ɗaga mashi kai tayi alamar eh,sannan yace"kada na sake jin kukan ki to,ya isa haka,kalli fa ki gani duk kin 6ata kwalliyarki da hawaye," Curo handkerchief Abusufyan yayi daga gaban aljihunsa,ya ruƙo hosana,tare da sanyashi a fuskarta yana goge mata hawayenta,"Daddy matar can bata da Imani ko kaɗan,taso ta kashe ni,dan Allah ku sakar mata karnuka su rakata bakin gate,tabar gidan nan," Muryar abusufyan tamkar zaiyi kuka yace"Kiyi haƙuri kinji hosanata,zansa a koreta kamar yadda kikeso,amma yanzu kiyi shiru da bakinki,ki daina magana,banason ganin hawayenki," "Daddy bakasan yadda nakeji bane,zuciyata tafarfasa takeyi,raɗaɗi takeyi mun kamar ana rura garwashin wuta acikinta,wlh daddy waccen matar bazata ga Manzon Allah ba,sai ta shiga wuta,' Hankali atashe Marshal ya daka mata tsawa har saida ta dawo cikin hayyacinta,fuskarshi a daure yace"kar na sake jin kince uffan a wurin nan,surutun ya isa haka!banace za'a kore ta ba," Saboda tsoratar da tayi da tsawar da yayi mata ne yasa ta faɗa jikin daddyn nasu ta ƙankameshi,tana faman sauke ajiyar zuciya,' jikin kowa yayi sanyi,musamman Ishaq,bawan Allah duk yabi ya takure kansa,idanunshi sunyi jawur saboda tsabar 6acin rai, Abba ne yayi ƙoƙari wurin dawo dasu daidai daga yanayin da suka shiga,daƙyar aka samu hosana ta zauna itama amma duk da haka tana yawan firgita wannan ya ƙara tabbatar masu da cewa ba ƙaramin Abu Aunty laila ta aikata masu ba,wuri kowa ya samu ya zauna agaban table ɗin dake a wurin wanda ke shaqe da abinci kala kala,nan fa kowa ya shiga bama cikinsa abinci,jikin Sehrish ba ƙaramin sanyi yayi ba,saboda ta gane dalilin dayasa su jahad suka tsorata da ganin matar,wato itace matar da Omar ya kaisu gidanta,wadda ta azabtar da rayuwarsu,kamar yadda jahad ta bata labarinta,kowa ya lura da yanayin yaran,sun kasa sakewa suci abinci sosai,ƙarshe sai dae Abusufyan ya dinga binsu one by one yana sanya masu abinci abakinsu suna ci,a haka har ya samu suka ci sosai,bayan sun kammala cin abincin,Junaid ya ɗaukko Camera ɗinsa,nan fa aka shiga ɗaukar hotuna,abun gwanin burgewa,Happy family,kowa sai da ya fito Hajiya azeema,su gwaggon katsina Saude,Dr harris,hatta ƴan matan da hajiya sarah tazo dasu,sae da suka fito akayi masu hotuna,mutun uku ne kawai babu a wurin Ammi wadda kowa ke fargabar fitowarta,bayan ita sae Haroon wanda ke ƙumshe acikin ɗakinsa,Sgr kuwa baya cikin gidan,tun wuraren ƙarfe uku yabar gidan, Anyi masu hoto tare da mahaifinsu sun sanyashi atsakiya,sae wanda akayi masu tare da Abbansu junaid tare dashi kanshi junaid ɗin,kowa saida yayi hoto tare dasu,hatta Su twins da fawan dasu irfan,kowannansu sae da yayi hoto dasu,sun sha hotuna ba ƙadan ba,

Basu suka kammala ba sae wuraren sallar magrib,sannan kowa ya shige ciki domin yin alwala,

Kamar jira jahad takeyi su shiga ɗaki ta rufe hosana da faɗa,tamkar zata bugeta,"Sai yanzu na tabbatar da cewar ke cikakkar zararriyace baki da hankali,meyasa ba zakiyi shiru da bakin ki ba?don me zaki tona mata asiri agaban mutane"? Fashewa da kuka hosana tayi tana faɗin"kada ki ƙara cemun zararriya,kuma naje na tona mata asirin,Ni bazan ta6a yafe mata ba wlh,kamar yadda ta cutar da rayuwarmu itama sai ta fuskanci sakamakon abunda ta aikata mana,' "Hosana,karna sake jin kin tada wannan maganar,idan ba so kike ranki ya 6aci ba," "Wlh saina faɗima Daddy da Abba,kuma saina faɗa ma yaya Omar,sai dai duk abunda zai faru ya faru,' rai a6ace tayi maganar,cakumar rigarta jahad tayi,tare da yin wurgi da ita,ta faɗa saman gadon tana kuka,fitowa Sehrish tayi daga cikin toilet,ganin jahad na ƙoƙarin bugun hosana yasa tayi saurin zuwa tare da ruƙo hannunta"karki kuskura kice zaki hukunta hosana!abunda tayi dai dai ne,koda ace ita bata faɗa masu ba,to ni saina faɗa masu abunda waccan matar ta aikata maku,saboda bata da Imani,muguwace ita,muddin akace za'a cigaba da yafe ma mutane irinta to tabbas bazasu ta6a canza halinsu ba!Suna buƙatar a ladabtar dasu,a hukuntasu,idan suka aikata ba dai dai ba,Ni hakan da hosana tayi ta burgeni,!" Shiru jahad tayi,ta wani 6angaren zancen sehrish gaskiya ne,muddin ba'a ɗauki mataki ba akanta taga an ƙyaleta to tabbas bazata ta6a canzawa ba,amma yanzu idan suka hukunta ta dole nan gaba taji shakkar ƙara yin irin kuskuren da tayi abaya,

"Kin faɗi gaskiya sehrish,ni banyi tunanin hakan ba,kuma koda nake yi ma hosana faɗa,saboda 6arin zancen da tayi ne agaban mutane,bai kamata ta yi magana akan idon kowa ba,in ma faɗin ne Ya Omar yakamata ta sanar mawa,sae su yanke mata hukuncin da suka ga ya dace da ita," Ta ƙarasa maganar tare da ɗauke idonta daga kan sehrish ta mayar dasu kan hosana dake baje saman gadon tana kuka,nan take taji bata kyauta mata ba,hawa saman gadon tayi tare da janyota jikinta,tana lallashinta,daƙyar ta samu tayi shiru,daga bisani suka tashi domin yin sallar magrib,

*Aunty Babba*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull