Abban sojoji takun karshe complete - Chapter 31
Abban sojoji takun karshe complete Chapter 31: Abban sojoji takun karshe complete Chapter 31. Fitowar shi kenan daga cikin toilet,Waist dinshi ɗaure da…
4,487 words
Fitowar shi kenan daga cikin toilet,Waist dinshi ɗaure da towel hannunshi kuma na ruke da wani short yana goge ruwan dake ɗiɗɗigowa daga jikinshi, "Ya Omar"muryar hosana yaji acikin kunnanshi,da sauri ya juya don yaga ko itace,Kwance ya sameta saman gadonshi ko kayan baccinta bata cire ba, Cike da mamaki yace"Kee!me kike yi acikin bedroom ɗina"? "Ya Omar nifa zuwa nayi kawai don na gaishe ka"tayi maganar a ɗan shagawa6e, "Haka ya dace kizo gaishe dani?ko sallama babu,kawai sai dai na fito daga toilet na same ki a kwance saman gadona,"Yayi maganar fuskarshi aɗan daure, Murguɗa mashi baki tayi tare da cewa"Ae ɗakin Mijina ne" Harara ya watsa mata"waye mijin naki?Allah ya kiyaye in auri mai ɗan kai irin naki," Gwalo tayi mashi tare da cewa"Oho dai,a haka ka gani kuma kake so,"_ ƙiris ya rage ya fashe da dariya,amma sai yayi saurin kawar da dariyar don kada taga kamar ma wasa yake yi mata, "Get out from my bedroom!"a ɗan tsawace yayi maganar tare da nuna mata hanyar fita daga bedroom ɗin, Maƙe mashi kafaɗa tayi,"Wlh ba inda zani ya Omar,Kazo ka ɗauke ni,ka fitar dani idan ba ka son gani na," girgiza kai kawai yayi tare da ƙarasawa gaban mirror dinshi, "Kaya fa zansa,pls ki fita daga waje idan na kammala saiki dawo,kin ji My baby" "Ae wlh ba inda zani je,Ae ba wani abu bane don ka sanya kaya agabana,tunda aure zamuyi," Shiru yayi bai kara tanka mata ba, Jin yayi banza da ita yasa ta kuma cewa"Ya Omar"shiru yaƙi amsa mata kiran nata, Ci gaba da magana tayi"Wai ya Omar,idan munyi aure,to taya zamu haihu muma"? Banza yayi bai tanka mata ba, Bata damu da hakan ba,sai ma ci gaba da maganar tayi, "Ya Omar,kana ganin nima zan iya haihuwa?Kuma ma Taya za'ae na samu cikin"? Hauka maganinka Allah,ya furta hakan acikin Zuciyarshi, "Ji ya Omar ina magana ka wani share ni,idan baka faɗamun ba,to taya zan sani,"? Ƙin tanka mata yayi,a hasale tace"Shikenan tunda ba zaka bani Amsa ba,wlh idan Daddy ya dawo zanje in tambayeshi ne,don ni bazan bari ayi abun kunya ba,Ayi mun aure bansan komai ba, A ƙule ya juyo tare da kallonta yace"Ke,Tashi ki fuce mun daga ɗaki" Maƙe mashi kafaɗa ta kuma yi"anƙi a fita Ya omar," Abun ya ɗaure mashi kai,ita ko shakkarshi bata ji,neman ma abunda zata yi mashi ya bugeta take yi don tasan cewa bazai iya ta6a lafiyar jikinta ba, "Idan kanaso in fita cikin lalama,to ka fara faɗamun taya zan samu ciki idan munyi aure" "Shine abunda kikeson sani"?yayi tambayar yana kallonta hadi da dage mata gira,ɗaga mashi kai tayi alamar eh, Aikuwa Nan take ya sanya hannunshi ya zame towel ɗin daya ɗaure qugunshi dashi, Tashin hankali! A gigice Hosana ta fasa wata irin razananniyar ƙara,Kafin kace me kamar walkiya haka tabar ɗakin da gudu tana kuka,ta firgita sosai Mayar da towel ɗin yayi ya ɗaure waist ɗin sosai,sai faman tiƙar dariya yake yi,har da dafe cikinshi, "Maganinki kenan,nasan daga yau ba zaki sake yi mun irin wannan question ɗin ba,Yarinya sai kace mai iskokai,Ni bansan ya zan ƙare da ita ba,A haka dai nakeso,kuma zan kula da abuna"ya ƙarasa zancen zucin fuskarshi ɗauke da murmushi ya wuce wurin wardrobe ɗinshi,sai daga baya ya dinga tunanin kada hosana fa taje ta faɗa ma wani abunda ta gani tunda ba hankali gareta ba,Tuna wannan yasa yayi saurin ɗauko jallabiya ya zura ajikinshi,da sauri ya sauko downstairs yana nemanta,
Azmee ya hango tana jera kayan abinci asaman Dining na breakfast dinsu,da sauri ya tunkareta,tunkan ya ƙarasa wurinta tajiyo takun takalmin mutun,ɗagowa tayi tare da kallonshi,ganin Marshal yasa ta saki fuska tare da gaisar dashi, "Barka da safiya Omar,an tashi lafiya," A gaggauce ya amsa mata"lafiya lou,amman pls ko kinga gifcin Hosana,"? "kamar dai naso naga giftawarta,lokacin ina ƙoƙarin fitowa daga kitchen,kuma naji kamar shessheƙar kuka ta ke," "Ina kike tunanin ta shiga ne," Shiru Azmee ta ɗan yi tana tunanin wurin da taga hosana ta nufa, "Yawwa,ina tunanin bedroom ɗinsu ta nufa," Tunkan ta ƙarasa maganar ya kama hanya da sauri da sauri ya nufi ɗakinsu,a buɗe ƙopar take hannu yasa ya turata,tunkan ya shiga ciki,Ya jiyo shessheƙar kukan Hosana,Yana yin sallama taji muryarshi da gudun gaske ta sauko saman gadonsu ta faɗa toilet ta datse ƙopar,tana ci gaba da yin kukan, ..Sehrish na kwance saman gadon,ta ƙudundune cikin bargo,tun da Asuba da ta farka asaman gadon Sgr lokacin ya shiga toilet domin yin alwala,ta saɗaɗa tabar bedroom ɗin nashi,ta dawo ɗakinsu,
Kaitsaye ya wuce ƙopar toilet ɗin ya tsaya tare da ambaton sunanta"Am really sorry Hosana,nasan ban kyauta maki ba,ke ce kin takuramin that's why nayi maki hakan,kuma ni fa amsar tambayarki kawai na baki ba wani abu ba, Cikin shessheƙar kuka yaji tace"Ya Omar baka da kunya wlh,Ni babu ruwana dakai,Wlh bansan ganinka,bansan ganin wannan abun naka" Hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba, A ruɗe ya shiga faɗin"hosana!baki da hankaline?so kike ki tona mun asiri,har wani ya ji mu?kin manta ni zan aureki,"? A tsiwace tace"wlh saina faɗama daddy idan ya dawo,ince ka nuna mun abunka," Hannu yasa tare da dafe kanshi,ya furta"Wayyo Allah na,Ni Omar,naja ma kaina," Ƙasa ƙasa yayi da muryarshi cikin lallashi ya soma magana, "My Hosana pls,ki yafe mun,bazan ƙara ba wllh,kome kikeso zanyi maki," "Wlh ya Omar,ko kukan jini zaka yi saina faɗama daddy cewa kai ɗan iska ne,Ni bazan aure ka ba," Tsawa ya daka mata tare da cewa"Ki faɗima duk wanda zaki faɗimawa ƴar rainin hankali,Wlh kuma kika kuskura kika faɗama wani sai na sa6a maki,kuma babu ni babu ke,Ƙasar ma zan bari gaba ɗaya in tafi can in auri baturiya,". Rai a6ace ya juya tare da barin ɗakin nasu, Sai da taji alamun fitarshi daga ɗakin,sannan ta wanko fuskarta ta,ta buɗe ƙopar toilet ɗin ta fito waje,abun ya dameta sosai buɗe ƙopar ɗakin tayi ta fuce,A dining ta same shi zaune shi da junaid suna yin breakfast,Azmee na yin serving ɗinsu, Kamar wadda aka zarewa lakar jikinta haka ta ƙarasa ta samu wuri kusa dashi ta zauna, "Aunty Azmee ina kwana"?fuskar Azmee ɗauke da murmushi ta amsa mata,"Lafiya lou Jahad,kin tashi lafiya...."da sauri junaid yace"Aunty azmee wannan ce jahad?kalli fa ƴan kumatun fuskarta ki gani,Hosana ce," Dariya azmee tayi,shi kanshi Omar yaso ya ɗan dara,ita kuwa tsuke fuska tayi tare da jifarshi da harara tace"ina ruwanka da kumatuna"? murguɗa mata baki junaid yayi dama basu jituwa atsakaninsu,Ƴar tsama sukeyi, juyawa ta ɗan yi gefenta tare da kallon Marshal,Ya tamke fuskar nan babu annuri acikinta, Saitin kunnanshi takai bakinta cikin sanyin murya tace"Ya Omar bazan ƙara ba,kuma bazan tona maka asiri ba,dan Allah kada ka tafi ka barni," side smile yayi tare da cewa"Its okey,nima wasa nake yi maki,bazan iya tafiya nabarki ba," Murmushi ta saki,har hankalinta ya kwanta, Hannu Azmee takai zata ɗauki plate ta zuba mata abinci,ganin ta zura hannunta acikin plate ɗin Omar suna ci atare yasa ta fasa,Abun ba ƙaramin burgeta yayi ba,
*KANO TA DABO TUMBIN GIWA KODA ME KAZO AN FI KA* acewarsu ba,Don ni ban yarda ba,
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Bayan *Jahad* ta fito daga toilet, hijab ta ɗauko cikin wardrobe ta zura ajikinta,wurin gadonsu ta koma ta haye sama tare da kai hannu tana bubbuga hosana, "Get up hosana,Time ɗin sallah yayi," hosana bata motsa ba,sae ma cigaba da jan minsharinta da tayi, "Hosana ki tashi mana!ba zaki tashi ba wai,kullum sai kin bani wahala idan nazo tashin ki daga bacci"tayi maganar fuskarta a ɗaure, Hosana kuwa,gyara kwanciyarta ta ƙara yi,har wani ƙara jan minsharin takeyi da ƙarfi don ma jahad tasan cewa tayi nisa a baccinta,alhalin tun a first call da tayi mata ta farka, A ƙule jahad tace"kada Allah yasa ki tashi,kuma saina faɗa ma ya Omar cewa baki yin....."tunkan taƙarasa maganar,hosana ta diro daga saman gadon da gudun gaske ta nufi toilet ta buɗe ta shige ciki,dariya jahad tayi sosai kafin ta sauka daga saman gadon ta koma ta shimfiɗa carpet ta kabbara sallah,
Sehrish kuwa tana a ƙudundune cikin bargo tayi lamo tana faman sauke ajiyar zuciya,kokwanton abunda ya faru tsakaninta da Sgr takeyi,ta kasa gasgata abunda ya faru last night,shin dagaske ne ko kuwa mafarki ne tayi,Don tasan cewa hakan zai yi wuya ya kasance gaskiya,Abun ya matukar ɗaure mata kai,ya caza mata brain ɗinta,tana cikin wannan zancen zucin bacci yayi awon gaba da ita,
*Junaid Romeo*
Bude ƙopar bedroom ɗinsa yayi tare da fitowa daga ciki,Still kayan baccin jiya ne ajikinshi,ya kara wayarshi a saman kunnanshi,hakan na nuni da cewar waya yake yi,Ashagwa6e yake magana yana faman tura baki, "Abba pls come back Soon,nafiso na ganka a kusa dani,"ya ɗan yi maganar yana bubbuga ƙafarshi ƙasa, On the other hand,Abbansu yace"ka ji tsoron Allah junaid!Nafa gano ka,So kake in dawo gida,saboda ayi maganar aurenka ko"? Murmushi junaid ya saki yana ɗan sosa ƙeyarshi da ɗayan hannunshi"eh dan Allah Abba,nidai duk atakure nake,Allah jina nake kamar a prison,Ayi mun aure kawai in ana son zaman lafiya," Abba yace"idan ba'ayi maka auren ba fa"? Ƙuƙuni ya shiga yi ƙasa ƙasa yana cewa"zan addabi kowa ne,in kuma kama ɗaki a hotel....." Bai ƙarasa maganar ba,Jin dariyar Abbansu ta cikin wayar,ashe duk yaji abunda yake cewa, "Junaid wa kayi mawa?kasan cewa yayyenka gaba ɗaya soldiers ne,Wlh kayi kuskuren yin badai dai ba,kai kasan inda za'a kai ka,". Jin wannan maganar ta Abba yasa shi ɗaure fuskarshi, Yana tafiya yana waya,da alama part ɗin Sgr zai wuce,saboda can ya nufa, Lokacin daya shiga falonsa,babu kowa,a saman sofa ya zauna,sai da ya kammala yin wayar da Abba,Su kayi sallama,Sannan ya miƙe tare da wuce wa bedroom ɗin Sgr, Sallama yayi mashi,jin shiru yasa shi shiga cikin ɗakin kaitsaye,a kwance ya same shi saman katafaren gadon nashi,ya lullu6e jikinshi har zuwa chest ɗinshi,jallabiya ce sanye ajikinshi,tun daga kan yadda yake yin baccin nashi zai tabbatar maka da cewa,yana cikin kwanciyar hankali da natsuwa, Lalla6awa Junaid yayi ya ƙarasa kusa da gadon,yana ƙoƙarin hawa idanuwanshi suka sauka asaman bargon Sgr,turus yayi ya tsaya yana kallon ikon Allah,Ya jima yana tunanin kome ya jawo hakan,abu dai gashi nan kana ganinshi ta cikin bargon,hawa sama yayi har zuwa saitin fuskarshi sannan ya tsaya tare da furta sunanshi a hankali"Babban yayanmu,"shiru bai amsa mashi ba,ƙara ɗaga murya yayi'babban yaya," Hannu ya kai tare da shafa gefen fuskarshi ya sake cewa"Babban yaya..," Har cikin dodon ears ɗinsa yaji kiran nashi,daƙyar ya iya ware blue eyes ɗinshi,biji biji ya fara gani kafin idanuwan suka ɗan washe,da wata irin kasalalliyar murya ya ambaci sunan shi"Junaid," Murmushi junaid yayi tare da cewa"nazo ne don na takura maka,Jiya na jira naga dawowarka,amma baka dawo gida ba,har bacci ya ɗauke ni,'_ Zuba mashi ido Sgr yayi yana kallonshi, Hakan yasa junaid ya ɗan tsuke fuskarshi yace"haba yaya rafayet,in zauna in tayi maka zuba kamar parrot maimakon ka mayar mun da martani saika zuba min ido kana kallona," a hankali ya lumshe idanuwanshi kafin ya sake ɗan waresu akan Fuskar junaid ɗin, "Me kake so ne"? Muryarshi tamkar zaiyi kuka yace"Yanzu babban yaya sai inason wani abu zanzo wurinka?jiya fa na dawo daga tafiya,ko farin cikin ganina ma baka yi ba," Ruƙo hannunshi Sgr yayi tare da janyoshi ya kwantar da kanshi saman ƙirjinshi,yana ɗan shafa bayanshi yace"Am glad to see you,Ya gajiyan tafiya,?kayi mun tsaraba"? Ashagwa6e junaid yace"Eh mana,munyi tsarabar fura,da zuma,da sauransu dai,idan kanaso zan yi ma rishi magana ta dama maka fura kasha,Wlh akwai daɗi sosai,nima in nasha kunne na har rawa yake yi,' Ya ƙarasa maganar tare da ɗagowa daga jikinshi,da buɗar bakin Sgr sai cewa yayi"you mean tafi abun da nasha last night daɗi"? A ruɗe junaid yace"babban yaya,me kasha jiyan?Ae ni bansan shi ba balle in san cewa ko yafi furar daɗi, Shi kanshi baisan ya furta hakan ba,it was just slip of the tongue,saboda ya kwana da abun aranshi,kuma yanzu haka ma shi yake tariyowa acikin brain ɗinsa,abun ya tsaya mashi arai,yadda har surar jikinta taja ra'ayinshi har ya fita hayyacinshi ya fara romancing ɗinta,ƙiris ya rage jiya ayi abun kunya, (Allah yaso bai ƙarasa headquater ɗin ba,da shikenan an buge boss,(in jini ba,don na lura wasu in ina kara wannan bayanin suna tsammanin cewa Sune sukeyin zancen zucin,sometimes ina ƙarawa da nawa bayanin)
"Yaya rafayet,"junaid ne ya ambaci sunanshi,ganin ya shiga zurfin tunani, hankalinshi yayi wani wurin,mayar da idanuwanshi yayi kan junaid tare da cewa"don't disturb me pls,Inaso na ɗan huta junaid," Ranshi ya ɗan sosu,jiki asanyaye ya juya zai sauko daga saman gadon,Sgr ya dakatar dashi"Wait,'ɗan tsayawa yayi tare da juyawa yana kallonshi, "Tell me what do u want from me"? Shiru junaid yayi yana lissafin adadin kuɗin da zai kar6a a wurinshi,Don sunyi da jahad zasu fita yawo,gashi ƴan kuɗaɗen acct ɗinsa duk sun ƙare,Yayi broke,' ɗaga yatsun hannunshi yayi yana yin lissafin,hakan ba ƙaramin dariya yaso yaba Sgr ba,dama sai da ranshi ya bashi cewar wani abu ne ya kawo shi bedroom ɗinshi,tunda sassafe ko wanka bai yi ba,balle aje ga maganar breakfast,A tsiyacen shi yazo, "Zan koma bacci,tunda naga lissafin na ka bamai ƙarewa bane," Da sauri yace"pls babban yaya kada ka koma bacci,yanzu ma daƙyar na tashe ka,". ta6e lips ɗinshi yayi tare da nuna wurin dressing mirror ɗinshi da hannunshi,Yace"idan kuɗine kake buƙata a wurina gasu can ka ɗauki iya yadda kakeso,idan ma na cikin nan isn't enough for u,Zan ƙara maka ta acct,hope hakan yayi maka"?yayi tambayar yana kallonshi,. Washe baki junaid ya shiga yi yana cewa"Babban yaya nagode sosai,wlh duk gidan nan kafi kowa sona,har Daddy ma kafi shi sona," Harara Sgr ya ɗan jefa mashi kafin yace"Saboda ina baka kuɗi ko"?_ fashewa junaid yayi da dariya,tare da saukowa daga saman gadon ya nufi wurin dressing mirror,
Mayar da idanuwanshi yayi ya lumshe su,shikaɗai yasan irin feelings ɗin da yake ji,kamar yayi hauka,Kuma shi irin mutanan nan ne,waɗanda basa wasa da lafiyar jikinsu,Komai yaji jikinshi na bukata yinshi yake yi don ya samu cikakkiyar lafiya,shiyasa gashi nan ta ko'ina masha Allah,tun daga kan skin ɗinshi zakasan cewa ba ƙaramin gyara take sha ba,haka sumar kanshi,da sauran parts na jikinshi,yanzu kuma ga wani new abu da yake bukata Urgently,
Zuƙunnawa junaid yayi agaban drawer ɗin,ya buɗe middle ɗinta,Dollars ne ya gani a jere,cike fam da ita,har wani ƙyalli kuɗin sukeyi acikin idanunshi,murza hannunshi ya shiga yi,har wani ƙaiƙayi suke yi mashi,Bandir ukku ya ɗauko ya tura su daƙyar cikin aljihun wandonshi,duk da haka basu isheshi ba,sae daya ƙara da naira,A gida na ƙarshe daya buɗe ajikin drawer chest din,kuɗin nigeria ne,Suma ya ɗauki Bandir uku na dubu dubu kusan dubu ɗari uku kenan,Ya turasu cikin ɗayan aljihun daƙyar suka shiga,Bayan ya kammala ya rufe mashi ita,yana ƙoƙarin miƙewa,idonshi ya sauka akan hoton daya faɗo ƙasan tiles,baisan daga ina hoton yake ba,duk a tunanin shi hoton Babban yayansu ne, Zukunnawa yayi tare da kai hannu ya ɗauki hoton da ya kife,ya juyo dashi yadda zai ganshi da kyau, Da karfi ya furta"Sehrish!"miƙewa yayi tare da tunkarar wurin gadon hannunshi ruƙe da hoton yaci gaba da cewa"wlh itace," jin sambatun da junaid keyi ne yasa Sgr ya ɗan buɗe idanuwanshi tare da wurga eye balls ɗinsa wurin junaid dake tunkaroshi Zama yayi daga gefen gadon fuskar nan tashi awashe cike fal da farin ciki,ya kuma yace"Wlh itace,Yaya rafayet ina ka samu hoton rishi tana ƴar ƙarama," "Junaid what are u talking about"?yayi tambayar a yayin da yake ɗan miƙewa zaune,tare da jingina bayanshi akan gadon, "Sehrish mana!wadda take yi maka aiki," Cike da mamaki Sgr yace"Kana nufin itace a pic ɗin"? Jinjina kai junaid yayi"ƙwarai kuwa itace," Cike da mamaki Sgr ya kuma tambayarshi "taya akai ka gane cewa itace?cos i even asked her last time,amma ta sanar dani cewa ba ita bace' Junaid yace"ae duk cikinsu,babu mai ɗigon tawada asaman wuyanshi sai ita,duk sauran basu dashi asaman neck ɗinsu,Idan ka kalli hoton nan dakyau,zaka ga ɗigon baki asaman wuyanta,'. "Lemme see"ya buƙaci ganin hoton,da sauri junaid ya mika mashi,hannu yasa ya kar6a,sannan ya ƙura ma hoton ido yana kallonshi,ɗigon tawadar ya gani asaman wuyanta,closing eyes dinsa ya ɗanyi,yana tariyo kallon da yayi ma ƙirjinta adaren jiya,har izuwa saman wuyanta,tabbas yaga black point ɗin nan,amma abun ya daure mashi kai,ta yadda har ita kanta,bata gane cewa ita bace a hoton, Buɗe idanuwan nashi yayi akan fuskar junaid sannan atsanake yace"Junaid,dama kallonta kakeyi?" cike da tuhuma yayi mashi tambayar, Sunnar da kai junaid ya ɗan yi yana sosa ƙeyarshi yace"Nifa ba kallonta nake yi ba,tun lokacin baya ne,kafin ta bayyana amatsayin mace,muna da kusanci sosai da ita,shiyasa ma har nayi mata wannan kyakkyawan sanin," "Its okey" ya furta hakan,tare da mayar da idanuwanshi kan hoton,Abun ya daure mashi kai,sai lokacin ya shiga tunanin ko meyasa Uncle Abusufyan ya basu hotonsu shi da Omar? Muryar junaid ce ta katse shi da cewa"Ka taso muje dining muci abinci pls,nasan kana jin yunwa,' Runƙo hannun Sgr yayi,har sai da ya samu ya sauko daga saman gadon,Sannan suka fito atare,har lokacin hoton na hannunshi,daga bayane ya zura shi cikin aljihun jallabiyarshi
Saukowa downstairs suka yi,tunkafin su ƙarasa dining ɗin,suka hango Uncle Abusufyan tare da Marshal Omar,ga Jahad da Hosana ma,duk suna azaune suna cin breakfast ɗinsu,Azmee ce atsaye take yin serving ɗinsu, koda suka ƙarasa,da sauri su jahad suka gaisar dashi"babban yaya ina kwana,an tashi lafiya,"? "Lafiya,sannunku"ya ambaci hakan kafin ya samu wuri ya zauna,junaid ma ya zauna a kusa dashi, "Big bro,jiya na jira dawowarka gida baka dawo ba,ina fata kana cikin ƙoshin lafiya,"acewar Marshal Omar, "Am ok,"ya bashi amsa atakaice,dama fushi yake yi dashi saboda yaso su dawo gida atare,Amma Omar yace sai ya ɗan ƙara kwanaki, Juyawa ya ɗanyi tare da kallon Abusufyan,wanda shima kallon nashi yake yi,jira yake yaga iya gudun ruwan nashi,zai gaisar dashi ne?ko kuwa jira yake yi shi ya gaishe da shi Ne? a hankali ya furta"Uncle,ya gajiyar tafiya,jiya kun dawo time ɗin bana nan" Murmushi Abusufyan ya ɗan saki tare da cewa"lafiyalou Alhamdulillah,gajiya tabi jiki,' Matsawa azmee tayi ta ɗauki plate ta shiga zuba masu abincin da zasu ci, Hosana tace"Daddy,rishi fa?kada acinye ita bata ci komai ba," Jahad tace"bacci takeyi tun ɗazu,kuma har tashinta nayi tazo muci abinci,amma tace mun in ƙyaleta,bata jin daɗin jikinta,' "Me ya ke damunta ne"?Omar yayi tambayar, "Nima bansani ba,tunda asuba dai kamar bata da lafiya,duk ta canza mun,har tambayarta nayi meke damunta amma bata sanar dani ba," Abusufyan yace"bai kamata a ƙyaleta ba,yakamata ku kirata tazo muji menene matsalarta," Jiki na rawa junaid ya miƙe zaije kiranta,karaf idanuwanshi suka sauka kan fuskar Sgr,wani irin kallo ya wurga mashi mai kama da harara,batare da kowa ya lura ba,komawa junaid yayi ya zauna,tare da cewa"Jahad kije ki kirata mana,"_ "Amsa mashi tayi da toh,kafin ta mike cikin sauri ta wuce bedroom ɗinsu, Cike da zolaya Marshal yace"Wato har ka fara bata Command ko"?_ Kunyace ta rufe junaid,har ya kasa shan Tea ɗin da ya ke sha cikin cup,Satar kallon Abusufyan yayi,Suna haɗa ido nan fa ya ƙara kame kanshi, Hakan ba ƙaramin dariya ya basu ba,Hosana tace"Ya Omar,wai yaushe ne abun nan?kace idan kuka dawo za'ayi magana nifa na kagara wlh," Gabanshi ne ya fadi rass,Hankali aɗan tashe ya ɗago ya kalleta,ko ajikinta sae ma tura pancake takeyi acikin bakinta,wata irin kunyace ta rufe shi,. Shi kanshi Abusufyan,kunyarce ta rufeshi,sai faman jujjuya fork yake acikin plate,ya kasa cin Abincin, Sgr kuwa har ɗagowa yayi ya kalli Hosana da tayi maganar, Ƙiris ya rage azmee ta fashe da dariya,jurewa kawai takeyi, Junaid ne yayi ƙokarin dakatar da ita ta hanyar yi mata raɗa acikin kunnanta, "Hosana waike baki da burki ne?meyasa zakiyi mashi haka,Duk kinsa sunji kunya,daga shi har Daddy ɗin naku,bai kamata kice haka ba,"_ Turo baki ta ɗan yi tare da cewa"zunubi na aikata ne?kawai kawai saboda nace....."bata ƙarasa maganar ba,sakamakon kallon da taga Omar yayi mata,nan take ta shiga taitayinta,
After some minutes,Jahad ta shigo Dining area ɗin,tunkan ta karaso Junaid yace"ina rishi ɗin take ne"ganin ta dawo ita kaɗai batare da Sehrish ba, "Tana aciki,yanzu zata fito,"ta karasa maganar tare da samun wuri ta zauna,
A hankali ta zuro da kafarta,har yanzu jallabiyar ce ajikinta,ta laga gyale akanta,ƙafarta kuma na sanye da flat shoes,jikinta sae kerma yake yi,saboda zazza6in daya rufar mata,amma bata so kowa ya gane halin da take ciki,hakan yasa tun kafin ta ƙaraso wurinsu,ta daidaita natsuwarta sosai,sannan ta shigo dining area ɗin,takun takalminta ne ya janyo hankalinsu,duk suka juyo suna kallonta,gabanta ne ya faɗi Rasss ganin Sgr zaune,aikuwa a ruɗe ta juya zata koma ciki,. Abusufyan ya dakatar da ita,ta hanyar ambaton sunanta"Sehrish,"tsayawa tayi cak,batare da ta ƙara ɗaga ƙafarta ba,wani irin wahalallan yawu ta haɗiya,kafin a hankali ta juyo ta ci gaba da tafiya,hankalinta duk yabi ya tashi kamar taga wani mugun abu, Wurin Abbansu ta tsaya,tare da gaisar dashi,"daddy ina kwana,". Fuskarshi ɗauke da murmushi yace"lafiyalou Daughter,meyasa baki fito ba tun ɗazu,"? "Bana jin daɗin jikina ne,Amma naji sauƙi yanzu" "Alhamdulillah,samu wuri ki zauna,"cike da kulawa yayi maganar, Gabanta sai faɗuwa yakeyi,ta rasa ta ina zata zauna,inda bazata fuskance shi ba,balle har su haɗa ido, Ganin taƙi samun wuri ta zauna sai ƴan dube dube takeyi,Hakan yasa Omar nuna mata gefenshi yace"Zo ki zauna,"hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,saboda yana a left hand ne kuma suna fuskantar su Sgr dake ta dama,kuma kujerar da zata zauna,ita ke fuskantarshi,jiki a mace ta ƙarasa gefen Marshal ta zauna,muryarta na kerma ta gaisar da Marshal"ina kwana yaya Omar," Da fara'a a fuskarshi ya amsa mata,"lafiyalou sister,ya jikin naki," "Da sauƙi,"ta bashi amsa, "Allah ya ƙara sauki," "Ameen" "Yaya rafayet,ina kwana,"daƙyar ta iya gaishe shi,sai dai ko kallo bata ishe shi ba,balle har tayi tsammanin zai amsa mata gaisuwarta,lokaci guda ta gane dalilin dayasa yaƙi amsa mata gaisuwar saboda bashi ta fara gaisarwa ba,a matsayinshi na boss ɗinta,wanda ke asama da mahaifinta, "Bro baka ji ana gaishe dakai bane"?acewar Omar Batare daya ɗago ya kalleshi ba yace"Naji,"yayi maganar tare da ɗaukar cup na coffee yana sha, Murmushi marshal yayi,saboda ya gane reason ɗin dayasa yaƙi amsa gaisuwarta, Zagayowa azmee tayi kusa da ita,ta ɗan duƙa saitin kunnan sehrish tace"Amaryarmu,me kikeso a zuba maki ne?farfesun nama ko Snacks,"? Murmushi sehrish tayi har dimple ɗinta ya lotsa,sannan tace"Aunty azmee pls kidaina zolayata,yanzu idan yaji fa?ni zaki jamawa,"cikin raɗa tayi maganar don kada suji mai take cewa, Azmee tace"Shikenan Mrs rafayet,na daina,yanzu dai me kikeso"? Sehrish tace"farfesun zaki samun,saboda bakina babu daɗi," Su6ul da baka azmee tayi wurin cewa"kice mun kusa samun ƙaruwar baby kenan,"karaf maganarta ta sauka akan kunnan Sgr,kuma cikin whispering tayi maganar,amma wani iko na Allah yaji abunda tace,ko kuwa yayi amfani da motsin la66anta ne Oho, Kamar daga sama taji yace"Keee!"a ɗan firgice azmee ta ɗago,ba ita kaɗai ba hatta su Uncle sai da suka ɗago suna kallonshi,ya haɗe fuskar nan babu annuri acikinta,. Da cokalin hannunshi yayi mata nuni da tabar wurin,Jiki asanyaye azmee ta juya da sauri tabar wurin, Sam sehrish bata ji daɗin hakan ba,duk sai taji babu daɗi,bata so Sgr ya kori Azmee ba,agaban kowa da kowa wannan kamar Cin fuska ne,Su kansu sauran dake zaune a dining ɗin basu ji daɗin hakan ba,shiru kawai su kayi,tunda basu da yadda zasuyi dashi, Ganin ya sallami Azmee yasa ta shiga ƙoƙarin yin serving ɗin kanta,plate ta ɗauko acikin jerin plates ɗin dake ajiye saman table din,Warmers din tashiga bubbuɗewa harta buɗo wadda ke ɗauke da farfesun naman kaza,serving spoon ta sanya,ta shiga ɗibarta tana zubawa acikin plate din,sai da tacika shi,sannan ta rufe warmer ɗin,
Sosai ta shiga shan farfesun,har wani lasar baki takeyi saboda daɗinshi da takeji,cinyar kaza ta ɗauko tana ƙoƙarin kaiwa bakinta,Sgr ya ɗago da idanuwanshi,karaf suka shiga cikin nata,nan take tasha jinin jikinta,kasa ƙarasa kazar tayi cikin bakinta,cak ta tsaya,tana kallonshi, Wannan karon kallon da yake yi mata yasha bambam da irin kallon daya saba yi mata a baya,gaba ɗaya sun shagala da kallon junansu,babu wanda ya lura a wurin,tunani tashiga yi komai yasa yake kallonta har haka batare da ya janye idanuwanshi ba? Shikuwa gogan jira yake ta kawar da idonta daga kallon da takeyi mashi,kada raini ya fara shiga tsakaninsu,saboda abunda ya faru jiya,musamman da ta ganshi tsurararshi babu kaya a jikinshi, ƴar harara ya watsa mata,tare da janye idanuwanshi daga kanta,kawar da nata idon tayi,mayar da cinyar kazar tayi cikin plate,gaba ɗaya taji komai ya fita ranta,ba don ta ƙoshi ba,ta miƙe zata bar dining ɗin, "Whe're u going"muryarshi ce ta dakatar da ita, daƙyar ta iya buɗe baki tace"Na koshi," Zuba masu ido Abusufyan yayi yana kallonsu, "Koma ki zauna,"Yayi maganar yana nuna mata seat ɗinta,Tamkar ta fashe da kuka haka taji,juyawa ta dan yi suka haɗa ido da daddynsu,kafin ta zauna,taci gaba da shan farfesun da ta rage, Hannu yasa ya yago tissue,yana goge mouth ɗinsa,kafin daga bisani ya miƙe ya wuce part ɗinsa, Sai da ya bar wurin sannan,ta samu natsuwa, "Daddy,ya maganar zuwa kano?sehrish ta faɗamun cewa,da zarar kadawo daga damaturu zaku wuce kano,Wurin neman Oumman mu,"jahad ce tayi maganar, "In sha Allah gobe nake son tafiya,tunda Asuba before ku tashi daga bacci ma" Yana kai ƙarshen maganarshi,Hosana tayi saurin cewa"daddy,pls dani za'a tafi,wlh inason zuwa kano," Harara marshal ya ɗan wurga mata kafin yace"a haka za'a tafi dake?me kika sani?Faɗamun a wata unguwa kuka zauna a kano" Wurga ido sama tayi tana ƙoƙarin tunano anguwar da suka zauna a kano Yatsina fuska tayi tare da cewa"Dawanau ko"? me zasuyi in ba dariya ba,gaba ɗayansu suka fashe da dariya,ɗaure fuskarta tayi,don ita ba ta faɗi don ayi mata dariya ba,bilhaƙƙi da gaske take ita, Jahad tace"kai hosana dawanau fa kika ce?Anan ne muka zauna?,' murguɗa mata baki tayi batare da ta ƙara cewa komai ba, "Daddy dan Allah ka tafi dani,nafi kowa son naje,"acewar sehrish, Mayar da idanuwanshi yayi kanta tare da cewa"Kin tambayeshi ne?ko kin manta yadda muka yi dake,"_ Jin haka yasa ta ɗan ɗaure fuskarta don tasan cewa,daƙyar ne Sgr yabarta ta tafi kano, "Ki je ki tambayeshi,idan ya barki tun yau ki fara shiri don da asuba zamu tafi,idan kuma ya hana to zan tafi da jahad ne" Tuni idanuwanta suka ciko tab da kwalla saboda tasa ran zuwa kano, Mikewa tayi daga saman kujerar tace"shikenan daddy,zan tambayeshi,Allah yasa yabarni,"ta ƙarasa maganar tare da barin wurin da sauri ta wuce ciki,
Bayan sun kammala yin breakfast ɗin,kowa ya kama gabansa,
A 6angarensu Aunty babba,tafiya ta kankama,Domin kuwa tun yau sun kammala shirinsu na tafiya Enugu,sun kimtsa kayansu da zasu tafi dasu,da asussuba zasu bar Abuja,da farko zasu fara sauka a hotel ne,a washe garin ranar zasu wuce,Cikin dajin da Bokan yake,taci alwashin cewa Sai taga bayan Hosana,saboda itace silar tonuwar asirinta,kuma A sanadinta ne tarasa igiyar auranta ɗaya,Bayan haka kuma taci alwashin saita Sanya soyayyar Abra acikin zuciyar Sgr,fiye da yadda ya Ke son iyayenshi, Tashin hankali!Rayuwar hosana na cikin haɗari,
Shin ina hayaam dake a kwance gadon asibiti cikin mawuyacin hali,har yau ba ta dawo cikin hayyacinta ba,Gashi likitocin sun nemi wani makusancinta sun rasa,babu wani atare da ita,baiwar Allah,bamu son ya zata ƙare ba,