Kenza eBookz

Abban sojoji takun karshe complete - Chapter 36

Abban sojoji takun karshe complete - Chapter 36

Abban sojoji takun karshe complete Chapter 36: Abban sojoji takun karshe complete Chapter 36. Wuri Amani ta samu gefen gadon ta zauna,Amal kuma ta zauna…

4,487 words

Wuri Amani ta samu gefen gadon ta zauna,Amal kuma ta zauna saman plastic chair ɗin dake fuskantar gadon,a ƙasa ta ajiye kwandon hannunta, a ruɗe Amani tace"Hayaam!meya faru dake haka?hatsarin mota kikayi ne"? Girgiza mata kai hayaam tayi alamar a'a,kasa buɗe baki tayi,saboda bata da amsar da zata basu ga kukan dake cinta, "Hayaam dan Allah ki sanar dani meya faru dake ne,Nayi mamakin ganinki ke kaɗai a asibiti a wannan halin,batare da Laila ba," "Aunty Hayaam,Sannu ya jikin naki"?Amal ce tayi maganar fuskarta da alamun tausayinta,daƙyar ta iya amsa mata,Duk kunya ta rufeta, Cikin sanyin murya tace"Aunty Amani nayi danasanin rayuwata gaba ɗaya,Na tsani kaina,Komai ya fita raina,Ban yi tsammanin zaki zo ba,Har na fidda rai da cigaba da rayuwa acikin duniyar nan,Amma ganinku da nayi ba ƙaramin farin ciki nayi ba,"tana magana hawaye na zuba, Juyawa Amani tayi tare da kallon Amal tace"Ki jirani a waje,Zan kira ki,inaso muyi magana da hayaam,ki tafi da wayata,ko game ne ki buga," Miƙewa Amal tayi tare da matsawa wurin Amani,ta kar6i wayarta,kafin ta kama hanyar barin ɗakin, mayar da hankalinta tayi sosai akan Hayaam tace"ina sauraronki,faɗamun meya faru dake?meyasa kike zaune a asibiti ke kaɗai batare da Laila ba?duk me ya jawo hakan"?a ƙagare Amani take da taji amsoshin tambayarta, Hayaam bata 6oye mata komai ba,Tun daga kan Abunda ya faru tsakaninta da haroon har izuwa farfaɗowarta da tayi a gadon asibiti,Hannu tasa tare da ɗaukar wasiƙar da ta cukuikuye agefenta ta miƙa ma Amani ita,kar6a Amani tayi a atsanake ta shiga karanta wasiƙar da Aunty babba ta rubuta mata,wasu irin hawaye ne suka soma shararowa daga kan fuskarta,Saboda tsabar ƙululun baƙin ciki kamar ta haɗiyi zuciya, "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!wannan wani irin rashin Imani da rashin tausayi ne?Anya kuwa laila tana son tagama da duniya lafiya?yanzu duk don saboda neman abun duniya ta tafi ta barki a gadon asibiti rai hannun Allah?Anya matar nan tana da Hankali kuwa?Ya salam"rai a6ace take maganar,abun ya ƙona mata ranta sosai, Hayaam tace"bata da imani,wlh duk rashin hankalina,banajin zan iya tafiya in bar Aunty laila a gadon asibiti,Amma haka ta haura ƙafa ta barni,Sai kace ba ciki ɗaya muka fito da ita ba......"kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan da yazo mata, Itama Amanin kukan takeyi sosai,cikin shessheƙar kuka tace"Ha..hayaam ki faɗamun sunan wanda yayi maki wannan aika aikar,inason nasan Wani mara imanin ne"? Daƙyar hayaam ta tsagaita da yin kukan tace"HAROON ne ɗan gidansu Ya Abbas,Mijinki," Saboda tsabar kiɗima a razane Amani ta miƙe tsaye hankalinta a matuƙar tashe take maimaita sunan haroon abakinta, Hannu ta aza akai tana faɗin"Nashiga Uku!Hayaam kina nufin haroon shine yayi maki wannan ɗanyen aikin"?ɗaga mata kai hayaam tayi Alamar eh, "Wlh bazan ta6a ƙyaleshi ba,Sai na tona mashi asiri wurin Abbas!Fasiƙi kawai mugu,dama ni bai ta6a kwantamun araina ba,Allah kaɗai yasan abunda yake aikatawa"ta ƙarasa maganar tare da komawa gefen gadon ta zauna, "Aunty Amani ki ƙyaleshi kawai,kada kice zaki tona mashi asiri,koma me ya faru dani laifina ne,Da ace tun farko na kama mutuncin kaina,da babu namijin da zai nemi aikata fasiƙanci dani,Zan yi haƙuri in rungumi ƙaddarata,Kibarshi kawai,Allah shi zai sakamun," girgiza kai Amani ta shiga yi tare da cewa"Wlh bazan ta6a ƙyaleshi ba,Shikenan yaci bulus kenan?wannan mutumin fa,ba ƙaramin mugu bane,bai kamata a dinga ƙyale irinsu ba,Suna aikata abunda suka ga dama,batare da an yanke masu hukunci ba,Yanzu kika san irin matan da ya lalata ta ƙarfi ta tsiya kamar yadda yayi maki?shiru hayaam tayi tana sauraronta, "Dole ya gane kuskurenshi,kuma ni bazanso duk wani abu da zai 6ata sunan family ɗinsu ba,Yana so ya zubda masu mutuncinsu ne a idon duniya,Don haka dole na ɗauki mataki akanshi,"ranta a 6ace tayi maganar,tare da kai hannunta cikin food basket din da suka zo dashi ta zaro plate tare da warmer,Buɗe kular tayi,Soyayyan naman kaza ne acikinta wanda yaji uban kayan haɗi,sae ƙamshi ke tashi,tuni jikin hayaam ya soma rawa sai faman haɗiyar yawu take yi,kamar ta kaima warmer ɗin wawura haka take ji,. Acikin plate Amani ta zuba mata naman tare da miƙa mata,Sannan ta dauko mata ruwa mai sanyi na roba,tare da fresh milk,ta shiga tsiyaya mata su acikin Cup, ganin yadda hayaam ke taunar cinyar kazar hada ƙashin duka take haɗawa,yasa Amani cewa"Ki ci a hankali mana,kada kija ma kanki wata matsalar,"kasa natsuwa tayi saboda yunwar da take ji, Sosai hayaam taci naman nan,tasha fresh milk ɗin mai sanyin gaske,sai da taci ta ƙoshi,sannan ta samu natsuwa, "Itama Laila bazan ƙyaleta ba,nasan cewa zata nemi Abra ne don ta rakata wurin bokan,wama yasani ko har sun tafi,Kuma ina da tabbacin cewar,bazata ta6a sanar ma wani cewa tabarki a asibiti ba,don kada a tuhume ta,"dakatawa ta ɗan yi da yin maganar kafin taci gaba da cewa"muguwar ashe ko ƙannenta da suka fito ciki ɗaya bata iya raga mawa,inajin tsoron tace zata kai Abra wurin fasiƙin Bokannan,don muddin takaita,zaiyi wuya bai nemi ya kusanci ɗaya daga cikinsu ba," Jin wannan maganar yasa hankalin hayaam ya tashi,don ita yanzu tayi nadama,kuma tana jin tsoron halin da Aunty babba zata jefa Abra,kamar yadda tayi mata,

"Yanzu ya zamuyi mu dakatar da Abra daga zuwa wurin bokan nan"?hayaam ce tayi maganar, "Ina ganin idan muka kira Abra muka sanar da ita abunda laila tayi maki na barinki a gadon asibiti,zata fasa bin ta ne," Zama suka yi suna yanke shawarar yadda zasu dakatar da Abra,a ƙarshe suka yanke shawarar kiranta a waya,

*Boss Bature*

*JUNAID*

Tsaye yake a gaban dressing mirror,ya ɗauki wankan pakistan ajikinshi masu kyan gaske farare sun ƙara fito da hasken fatarshi,Fuskar nan har wani kyau ta ƙara,ya gyara sumar kanshi sosai ta kwanta luf a bayan wuyanshi,Slowly ya miƙa hannu gaban mirror ɗin ya ɗauki kwalbar turarenshi,yabi ko ina na jikinshi ya feshe shi,bayan ya mayar da ita,ya ɗauko wrist watch ɗinshi ta diamond da Hajiya azeema ta bashi,Yana ƙoƙari sanyata a hannunshi,Wayar shi ta soma ringing,da sauri ya ƙarasa sanya agogon,tare da tunkarar saman gadonshi inda ya ajiye wayar yakai hannu ya ɗauketa,tare da kollon screen ɗin wayar,Sunan Mommyn su ne ya bayyana akai,tur6une fuska yayi kafin ya ɗaga wayar,cike da shagwa6a ya soma magana"Mommy,ni fushi nake yi dake," On the other hand,Alexandra tace"haba romeo ɗina,why are u angry wit me?laifin me na maka da kake fushi dani" "Mommy,u forgot about me,tunda na dawo baki kira layina ba,babu wanda ya damu dani," Cikin lallashi tace"Sorry my own son,pls kadaina fushi dani," Bubbuga kafarsa yayi cikin shagwa6e yace"Nidai Mommy indai kina son farin cikina,Ki dawo gida kawai ke da daddy,dasu yaya Fawan,kowa ya dawo gida,nayi missing ɗinku sosai," Alexandra tace"shi ne kawai abunda kakeso," "Eh,adawo gida,acigaba da rainon baby junaid"yanayin yadda yayi maganar ba ƙaramin dariya ya bata ba,yana jiyo muryarta ta cikin wayar tana dariya, Bayan ta tsagaita da yin dariyar tace"Calm down ur mind,This week zamu dawo," Fuskarshi ɗauke da farin ciki yace"Mommy pls,Ki tursasa daddy,ko da baya son dawowa,ni dai ku dawo gida kowa da kowa,tare da su yaya fawan,Twins su irfan and sister hafsat,inason ganin kowa a kusa dani," "Don't worry ur self,my romeo kowa zai dawo saboda farin cikinka," Ba ƙaramin daɗi yaji ba Sun jima suna waya kafin daga bisani,su kayi sallama,ajiyar zuciya ya sauke tare da yin wurgi da wayar saman gadon,kwankwasa ƙopar bedroom ɗinshi akayi,da sauri yace wanene "My Romeo,its Me ur juliet,am ready for the outing,"wani irin ƙayataccen murmushi ya saki jin muryar jahad, A ƙagare yake daya ga wankan data ɗauka,jiki na rawa ya ƙarasa tare da buɗe mata ƙopar,Gabanshi ne ya faɗi rass,Tun daga kan takalman ƙafarta ya fara kallonta,High heels ne ƙafarta,farare,abun ya bashi mamaki ganin tayi shigar white gown,launin kayanshi daya sanya,tayi rolling veil akanta,lips ɗinta kuwa Red ta sanya masu,wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke fitowa daga jikin ko wannansu,

Ruƙo hannunta junaid yayi tare da janyota cikin bedroom ɗin,lumshe idanuwanshi yayi tamkar maijin bacci,da wata irin kasalalliyar murya,yace"Jahad,You look so beautiful,kayan nan sunyi maki kyau sosai," Hannu tasa tare da shafa side face ɗinshi"Duk kyawuna ae bankai ka ba,kaifa na dabanne,ta ko'ina Allah ya baka,". Aɗan shagwa6a yace"Amma ni bana jin kaina a matsayin cikakken mutun," A ɗan ruɗe tace"Saboda me,'? Hugging ɗinta yayi tare da kai lips ɗinsa saitin kunnanta sannan yace"Saboda,ban mallake ki ba,sai dake ne zan zama cikakken mutun,' Wani irin matashin murmushi jahad ta saki,taji daɗin kalaminsa sosai, "Nikaina junaid,bana jin kaina amatsayin cikakkiya,har saina mallake ka," kalaman soyayya suka shiga gayawa junansu, Duk wannan abunda da suke yi akan idon Haroon wanda ke la6e,ya ɗan buɗe kopar ɗakin ya zuro kanshi yana kallonsu, Jinjina kanshi yayi tare da cewa"Ta kwana gidan sauƙi,"yana faɗin hakan,ya rufo masu ƙopar ɗakin,hannu yasa tare da zaro wayarshi,Contact ya shiga,Tare da rubuta wasu numbobi,ya danna kira,tare da manna wayar asaman kunnanshi, Muryar wani kakkauran mutunne yace"Ya haroon,Ya ake ciki ne?ina fata kazo mana da labari me daɗi," ƙasa ƙasa da murya haroon yayi don kada wani ya juyo shi, "Ka saurare ni dakyau,Yanzu junaid zasu fita tare da ƴar wurin uncle ɗinmu,Abunda nakeso daku,Karku kuskura ku ta6a lafiyar jikin yarinyar saboda ba akanta zamuyi aiki ba,Junaid kawai nakeso,Ku bi ta kan motarshi da truck,Yadda ko fuskarshi ba'za a gane ba,idan tayi dameji," Fashewa mutun yayi da wata irin Mahaukaciyar dariya,hhhhhhhh kamar zai fasa screen ɗin wayar,Bayan ya tsagaita da yin Dariyar yace"AN GAMA OGA,SAI DAI UWARSHI TA HAIFI WANI," Jinjina kai haroon yayi tare da sakin shu'umin murmushin nan nashi yace"ku kasance a ankare,Yanzu zai fito da motarshi,banaso yaron nan ya dawo gidan nan araye,Gawarsa kawai nakeson gani,jaga jaga da jini,"

[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

⭐💫⭐💫⭐💫⭐💫⭐💫⭐ *MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI*💃🏻💃🏻

Sis ko kinsan illar rama ajikin mace in tayi yawa ??? Rama Sam batayi ba mijinki kullum yana iya kokarinshi akanki amma da yawa mutane sai suyi maki kallon kina cikin matsala ne saboda ramar da kikeyi , sannan zaki zquna a abushe bawata mat'aba ajikinki 🤣🤣 wannan yasa nazo maki da maganin kiba mai inganci hajiya yadda zaki ciko sosai ki murje abunki bawai kiba mai yawa ba aa zaki ciko dai kikoma yar dai dai misali ke ba katuwaba ke ba ramamma ba yadda kema zakiji dadin yin kwalliyar da zataja hankalin mijinki agareki😉😉 mmn Yusuf fa ta shirya tsaf domin gwangwaje Ku da zafafan kayanta uwayen gida da Amare👍🏼👍🏼👍🏼👍🏼07069711327

*Boss Bature ✍️*

*HAROON*na kammala yin wayar,ya mayar da ita cikin aljihun wandonshi,da sauri da sauri ya saukko down kaitsaye ya nufi part ɗinsu,Sautin murya yaji ana raira waƙa da sauri yakai idanuwanshi wurin,Hosana ce zaune saman Sofa,ta aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya,ta ɗauki wankan jeans da t shirt ajikinta sam bata lura dashi ba,jinjina kai haroon yayi tare da sakin wannan shu'umin murmushin nashi,A ranshi yace"Zan dawo kanku ne,dake da Omar ɗin,tabbas idan na ta6aki tamkar na ta6a zuciyarshi ne,don haka ta wurinki zan biyo mashi,Saina sa ya zubda hawayenshi kamar yadda nima yasa na zubar da nawa,"ya ƙarasa zancen zucin nashi tare da wuce wa part ɗinsa,bedroom ɗinshi ya shige ya fara zarya acikinshi,burinshi kawai yaji Saƙon mutuwar Junaid~

*JUNHAD*

Saukowa sukeyi downstairs hannunsu ruƙe acikin na Juna, "Tun ɗazu nake kiran Layin Rishi,Amma bata ɗagawa,I don't know why,nashiga damuwa,"jahad ce tayi maganar,fuskarta da ɗan damuwa, Junaid yace"may be tana busy ne,amma ki bari zuwa anjima sai mu jaraba kiranta,may be ta ɗaga wayar," Cikin palour suka saukko,hosana na ganinsu ta miƙe tana sakar masu murmushi, Ba ƙaramin burgeta su kayi ba yarfa hannu ta shiga yi tana faɗin"Wow,jahad junaid kunyi kyau kamar sabbin kuɗin da Central bank suka fitar,"gaba ɗaya suka fashe da dariya, camera ta shiga,tare da ɗaukarsu hotuna da wayarta,kafin suka wuce tare da barin palourn,komawa hosana tayi saman sofa ɗin tana jiran dawowar Ya Omar,

Wurin motarshi suka nufa,da kanshi ya buɗewa jahad mota,ta shiga,kafin ya zagaya other side ɗin,ya buɗe ma kanshi motar ya shiga, juyawa ta ɗan yi tare da kallon fuskarshi,Murmushi ta samu akan fuskarshi, Cikin sanyin murya tace"Babyna," "Na'am" ya amsa mata tare da wurga idanuwanshi akanta, Kashe mashi ido ɗaya tayi kafin tace"Junaid,I love u so much,I can sacrifice my life for u," Ƙayataccen murmushi ya saki,tare da cewa"Me too,",yana ƙoƙarin tashin motar yaji gabanshi yayi wani irin mugun bugu mai sautin gaske ji kake daraaam!har razana sai da yayi,lokaci guda yanayin fuskarshi ya canza,ganin ya kasa tashin motar yasa jahad,cewa"Babyna,Lafiya naga yanayinka ya canza"? Ashagwa6e yace"jahad,faduwar gaba nake ji,kamar wani mummunan abu zai faru dani,haka nake ji,"muryarshi a kasalance yayi maganar, Cikin sanyin murya tace"In sha Allah babu abunda zai faru da kai babyna,idan har fitar nan da zamuyi bata kwanta maka arai ba,ni inaga kawai mu koma gida..."tunkan ta ƙarasa maganar,yace"a'a,Bazamu fasa ba,na sa rai sosai akan fitar nan," Jinjina kai jahad ta ɗan yi tare da zura hannu cikin ƴar purse ɗinta dake ajiye saman laps ɗinta,Phone ɗinta ta curo tare da buɗeta,adai adai lokacin app ɗin da take amfani dashi na V muslim wurin yin azkhar yayi mata alert na cewa time ɗin yin evening azkhar yayi, Juyawa ta ɗanyi tare da kallon junaid,wanda jikinshi duk yayi sanyi, "Babyna,yakamata muyi azhkar kafin mu fita daga gidan nan," Ashagwa6e yace"jahad ni ban iyaba,bansan ya zanyi ba," Moving tayi close to him tare da nuna mashi screen ɗin wayarta"kalli ka gani,App ne nake using dashi yana da matuƙar amfani,kuma yana taimaka mun wurin tunasar dani lokuttan yin sallah da kuma yin azhkar,koda ace baka iya ba,zaka iya yi yayin da kake kallo kana karantawa acikin zuciyarka," Murmushi ya ɗan saki kafin yace"Its ok my juliet,mu fara atare," Nan suka shiga yin azkhar ɗin acikin zuciyarsu,har suka kammala,tukunna yaja motar da gudu ya nufi hanyar fita daga gate ɗin gidan,a bakin gate ɗin ma sai da jahad ta ƙara tunasar dashi akan yin addu'ar fita daga gida kuma atare suka furta"Bismillah,Tawakkaltu Alallah,wala haula wala ƙuwwata illa billah",

Fitar motarsu keda wuya,Sai ga motarsu Marshal Omar na shigowa cikin gidan,Hatta gifcinsu sai da marshal Omar ya gani, "Yalla6ai,kamar motar junaid ce ta wuce yanzun nan"major ne yayi maganar, Omar dake zaune a back seat na motar yace"I think so," "Amma yalla6ai,kada kace nayi shisshigi,ni dai aganina bai kamata junaid na fita yawo shi kaɗai ba without security guards atare dashi,duk da munsan Allah ke tsare bayinsa," shiru Marshal ya ɗan yi yana nazarin wani abu kafin yace"Ni kaina na jima ina tunanin hakan,last time har maganar mu kayi da Rafayet,amma daga baya kowa ya share maganar," Major yace"gaskiya yakamata aduba,saboda yaron yana da farin jini sosai,kuma kowa yasan irin son da kuke yi mashi,duk wani mai hakon family ɗinku zai iya biyowa ta wurinshi ne"_ Jin wannan maganar ta Major,yasa hankalin Omar ya tashi,saboda an sha faɗa masu cewa junaid,Shi ne lagwansu,Duk wani wanda zai kawo masu hari acikin masu son ganin bayansu,dole sai an ƙuntatawa junaid sannan za'a ta6a zuciyoyinsu,

"Major thank u so much for ur advise,and in sha Allah zanyi wani abu akai,'

Bayan Major yayi parking ɗin motar,Ya buɗe ya fito tare da zagayawa ya buɗewa Marshal,Saukowa marshal yayi,ya nufi cikin gidan,lokacin da ya shiga babu kowa a main palour ɗin,Bedroom ɗinshi ya wuce,Shaf shaf ya cire kakin dake ajikinshi,Ya wuce cikin toilet,after some minutes ya fito daga cikin toilet ɗin,sanye da short a jikinshi,Agajiye yake ga wani irin bacci da yake ji,Saman gadonshi ya haye,in a short time bacci ya ɗauke shi,

A hankali Hosana ta turo ƙopar dakin nashi,tun tana kabbara sallar la'asar ta jiyo shigowar mota cikin gidan,jiki na rawa ta sallame bayan ta gama sallar ta fito,saboda tana da tabbacin cewar Ya Omar ɗinta ne ya dawo,murmushi ta saki ganinshi kwance da gajeran wando ajikinshi,ya baje sai faman sharar bacci yake yi,lalla6awa tayi cikin sanɗa ta haye saman gadon,saman jikinshi ta hau,har zuwa saitin fuskarshi,ta ƙura mashi ido tana kallon kyakkyawar fuskarshi,bata da da burin da ya wuce ta takura mashi arayuwarta, "Bari nagani,idan na toshe mashi hancinshi da bakinshi,ta ina zai yi numfashin," Hannu tasa,cike da mugunta,ta toshe mashi hancinshi da bakinshi,ta danne su da tafin hannunta,aikuwa nan take numfashinshi ya soma tattokarewa,A razane ya farka lokaci guda,ya rarumeta batare da ya ankara ba,yayi wurgi da ita,da iya ƙarfinshi na ƙarshe,kai tsaye hosana ta faɗi ƙasan gadon yaraf!kanta ya bugu sosai,fashewa tayi da matsanancin kuka tana fadin"Wayyo Allah na,Ya Omar ka kashe ni wllh," Tunda yaji muryarta,ranshi ya 6aci sosai,saboda ita taja har yayi mata hakan,ko kwanakin baya ta ta6a yi mashi irin hakan har yayi wurgi da ita,miƙewa yayi daga zaune tare da kai idanuwanshi wurin da take yashe a ƙasa tana kuka, Da wata irin kasalalliyar murya yace"Why Hosana!why!"? Sai faman shessheƙar kuka take yi,tama gaza ɗagowa da kanta, Guntun tsoki yaja,kafin ya sauko saman floor ɗin,hannu yasa ya janyota jikinshi ya rungumeta a saman faffaɗan ƙirjinshi,yana ɗan bubbuga bayanta,Cikin lallashi yace"Am so sorry My Hosana,duk laifinki ne,meyasa kike son takuramin ne? Cikin shesshekar tace"ya..ya..Omar,nifa wasa nake yi maka fa..." "Haka ake yin wasa a garinku?You are trying to kill me,and u are saying that it was a joke!" "Ya Omar,nima fa a wani Chinese film ne nagani,Na jakican,shi ne na kwaikwaya," A ruɗe ya ɗago da kanta daga saman ƙirjinshi yace"Ke!ashe dagaske baki da hankali,saboda kawai kin kalli film kinga anyi haka sai kice nima zaki jaraba akaina?angaya maki cewa abunda ke cikin film dagaske ne?Su idan sunyi sun rayu,to ni idan kika yi mun kashe ni zakiyi," Runtse idanuwanta tayi ganin yadda yake ta surfa mata faɗa, Tsagaitawa tayi da yin kukan da take yi"Am sorry Ya Omar bazan ƙara ba," Harara ya ɗan watsa mata"kinfi kowa iya bada haƙuri,idan kikayi laifi kamar matar aure ta gari," Murguɗa mashi baki tayi,lokaci guda ya samu kanshi cikin wani irin yanayi,zuba mata ido yayi yana kallon dress ɗin dake ajikinta,Jeans da t shirt sunyi matuƙar bin shape ɗin jikinta,jin yayi tsit yasa ta ɗan buɗe idanuwanta,ganin ya zuba mata ido ko ƙyaftawa baiyi ba,yasata fara tunanin kome yake kallo ajikinta,Ganin yana kallon ƙirjinta yasa tace"Ya Omar sun ƙara girma ko"? Waro ido ya ɗan yi tare da cewa"Mekenan?" Hannu tasa tana nuna mashi breasts ɗinta, "Ya salam,"ya furta hakan tare da ɗan rufe idanuwanshi yace"nifa,basu nake kallo ba,kayan jikinki ne suka burgeni,sunyi maki kyau sosai,"ya ƙarasa maganar tare da miƙewa tsaye yana kallonta, "Idan kana jin yunwa in kawo maka abinci"?tayi tambayar tana kallonshi, ɗaga mata kai yayi alamar eh,sannan yace"pls,inaso in ɗan kwanta in huta kinga baccin bai ishe ni ba,idan kika kawo mun Lunch ɗin,ki ajiyemun shi saina farka zanci," Amsa mashi tayi da toh,kafin ta miƙe da sauri da sauri ta fuce daga ɗakin,saman gadon ya koma ya kwanta,bakomai bane ya faɗo mashi aranshi ba,fa ce maganar da suka yi da Major dangane da Junaid,hakanan ya dinga jin kamar yayi kuskuren barinshi ya wuce da motarshi,dama ya sani tun a time ɗin yasa security sun bi Bayan Motarshi...........

*Boss Bature*

Ƙarar shigowar Message,da ta ji ne yasa takai hannu tare da ɗaukar wayarta dake ajiye agaban mirror,yayin da take zaune asaman kujerar gabanshi,tana yin makeup,janyo wayar tayi tana karanta message ɗin daya bayyana akan screen ɗin wayar, _Abra,inason magana dake,amma bana so kowa ya sani,koda Aunty Laila ce_ Mamaki ne ya kamata ganin anyi mata saƙo da new number,kowaye wannan,ɗaukar wayar tayi tare da miƙewa tsaye,a lokacin Aunty babba na cikin toilet tana yin wanka,

Arab gown ce ajikinta,pink colour abunka ga fara tass,ba ƙaramin kyau tayi mata ba,fitowa tayi daga cikin bedroom ɗin nasu,ta miƙi hanya kamar zata fita daga corridor ɗin,Sai da ta bada tazara sosai,Sannan ta dannama numbar kira,tana fara ringing aka ɗaga, Tun kafin tayi sallama,taji muryar hayaam tace"ABRAH"!tun daga kan yadda ta kira sunanta yasa gabanta ya faɗi rass, "Aunty hayaam kece"? Bata amsa mata ba,sae ma fashewa da tayi da kuka mai sautin gaske,hakan ya ƙara ɗagawa Abra hankali,a ruɗe ta shiga faɗin"Aunty hayaam meya faru dake ne?meyasa kike kuka?dan Allah kiyi mun bayani,"

On the other hand,Hayaam ta miƙa ma Amani wayar tare da cewa"kiyi mata bayani," Gyaran murya Amani tayi tare da ambaton sunan Abra, Duk sunbi sun ɗaga mata hankali,muryarta har kerma takeyi wurin cewa"Dan Allah kuyi mun bayani,kun sanyani acikin duhu," "Abrah!ki natsu ki saurareni,"jinjina kai abra ta shiga yi tana fadin"ina sauraranki Aunty Amani,meya faru ne naji Aunty hayaam tana kuka, Amani bata 6oye mata komai ba,game da abunda ya faru da hayaam da kuma guduwar Aunty babba daga asibitin,da kuma wasikar da ta bar mata,wasu irin zafafan hawaye ne suka soma gangarowa akan fuskar Abra,hankalinta a matuƙar tashe tace"Nashiga uku!kenan nima wata rana idan ƙaddara ta same ni,Aunty laila zata iya guduwa ta barni? Amani tace"ƙwarai kuwa!saboda bata da Imani kuma bata da tausayi,karki so kiga yadda na samu hayaam a asibitin nan a wulakance,kamar wadda tayi hatsarin mota amma a haka laila tabarta,saboda bata da amfanin da zata yi mata,To kema muddin kika kuskura kika bita wurin bokan nan rayuwarki ta faɗa halaka,Kuma wlh da zarar amfaninki ya ƙare a wurinta shikenan kin zama Waste product!Zata yi watsi dake ne,"jin wannan maganar yasa Abra ta fashe da matsanancin kuka,wani irin tsoro ne ya kamata,don Aunty babba ta zama abun tsoro a wurinta,ta girgiza da jin rashin imaninta, Da gangan Amani ta dinga tunzura abra don ta tsoratar da ita akan karta goyi bayan Aunty babba suje wurin bokannan, "Abra!ina ƙara jan kunnanki,karki kuskura ki bi ta,Kiji tsoron Allah,ki tuna cewa wata rana zaki koma gare shi,kada kiyi silar da za'a cutar da rayuwar wasu,Aunty laila bata da Imani,tanaso ta jefa rayuwarku cikin haɗari ne,kuma tana yin amfani da ku ne don ta cimma burinta,kuma da zarar amfanin ku ya ƙare a wurinta,zata yi watsi daku ne,ta kama gabanta,Ga hayaam nan dai yanzu ta gane kuskuren da tayi,tana mai dana sanin abunda ta aikata," Amani nakai ƙarshen maganarta,ta miƙa ma hayaam wayan"kiyi mata magana," Kar6ar wayar hayaam tayi tare da karata a kunnanta,Kukan da Abra keyi har cikin zuciyarta,dama tasan dole taji raɗaɗin acikin zuciyarta,ɗan uwa ba wasa ba, Cikin Sanyin murya tace"Abra,baki ga yadda na koma ba,bani da wani abu daya rage na ƴa mace a jikina,komai ya lalace,Yanzu ma bana jin kaina amatsayin mace," Wani sabon kukan Abra ta ƙara fashewa dashi,cikin shessheƙa tace"Aunty hayaam wlh bazan bi ta ba,sai dai taje ita kaɗai,Ashe ba son mu take yi ba,bata ɗauke mu abakin komai ba,Amfani kawai take yi damu don ta cimma burinta,Ni wlh bansani ba Aunty hayaam,harfa tambayarta nayi ina kike amma tace mun wai batasan inda kika tafi ba,kinacan kina yawon gantali,Ashe kina gadon asibiti rai hannun Allah,yanzu haka fa da nake yin maganar nan,tun jiya muka iso Enugu da ita,Yanzu haka ma shirin zuwa wurin bokan muke yi, Hayaam tace"Abra,ki natsu ki saurare ni,kada ki bari tasan da shirinki naƙin binta wurin boka,saboda bata da imani tana iya kasheki,in kika 6ata mata rai,Abunda nake so dake shi ne,Duk wani kuɗi dake a wurinta,ki tattarasu gaba ɗaya ki sanyo su acikin jakarki,muguwar rabi da kwata na kuɗin dake a hannunta nawa ne,amma saboda tsabar rashin Imani ta kwashe hada nawa ta gudu dasu," Jinjina kai Abra tayi yayin da take share hawayenta, "Aunty hayaam,yanzu tana acikin toilet,bari nayi sauri na tattara kayana,in biyo mota in dawo nan," Hayaam tace"Yawwa,kiyi sauri kada fa kiyi kuskuren da zai sa ta gane cewa guduwa zakiyi ki barta,". "In sha Allah bazan bari ba," .daga haka su kayi sallama,

Ajiyar zuciya hayaam ta sauke tare da kallon Amani dake zaune gefen gadon,tace"Har hankalina ya kwanta,So nake Aunty laila ta ɗanɗani kuɗarta,taji irin raɗaɗin dana ji acikin zuciyata, Murmushi Amani tasaki,tare da cewa"Nafi ki jin daɗi Hayaam,A shirye nake dana taimaka muku wurin ganin kun gyara rayuwarku,"acikin ranta kuma tace"Ita kuma waccen bijimar,Sai nasa ta tsani kanta,duk wani makusancinta saina kwace shi ya dawo a ƙarkashin ikona,So nake ta gane kuskuran da ta aikata arayuwarta,"

A 6angaren abra kuwa,tun bayan da suka kammala yin wayar,jiki na rawa ta koma Room ɗin nasu,A hankali ta tura ƙopar ta fara leƙawa ciki,don taga ko ta fito daga wankan,Ajiyar zuciya ta sauke,ganin bata fito ba,da sauri ta faɗa cikin ɗakin,Jikinta sai kerma yake yi,asaman bedside drawer,ta samu jakar Aunty babba,hannu tasa ta ɗauki handbag ɗin,tare da zagayawa ta Other side ɗin ta ɗauko ƴar purse ɗinta,saboda tsabar sauri jin Aunty babba na motsi kamar zata fito daga cikin toilet ɗin,aikuwa a gigice ta buɗe ƙopar ɗakin ta fuce,da gudun gaske,mutanen dake kai komo a cikin hotel ɗin sai kallonta sukaye,wasu kallon burgewa suke yi mata saboda rigar jikinta,ba ƙaramin kyau tayi mata ba,gashi bata sanya mayafi akanta ba,ƙafafunta ko takalma babu,

Hankalinta bai kwanta ba,har sai da ta fito daga cikin hotel ɗin,gudu gudu sauri sauri ta miƙi hanya tana tafiya tana waiwayon bayanta kada ace Aunty laila ta biyota,Masu motoci sai parking sukeyi agabanta suna yi mata tayin shiga motarsu,amma taƙi sauraron kowa saboda gudun kada wani ya cutar da rayuwarta,kamar yadda aka yiwa Hayaam,baiwar Allah ta tsorata sosai,gashi babu wanda ta sani a garin,haka bata san ko ina ba,ba ƙaramin galabaita tayi ba,

*Koya Abra zata ƙare?Shin ina Aunty Babba dake a cikin toilet tana wanka?Batasan an yashe ta ba*

*Boss Bature*

❤🤍❤

Kano state

Wuraren ƙarfe 6 na marece,Slowly motocin Sgr suka shiga cikin unguwar batare da jiniya ba,saboda patient ɗinsu da suka ɗaukko,a back seat na motar Abusufyan suka kwantar da ita,Abusufyan shi ne ke driving ɗin motar,fuskarnan tashi a washe,kamar wanda aka yima Albishiri da Gidan Aljanna,Sehrish na agefenshi sae faman sakin murmushi take yi tana waiwayawa,bakinta yaƙi rufuwa,a ƙagare take dasu ƙarasa gidan,ko ta samu ta kira sauran ƴan uwa ta sanar dasu cewa An samo Oummansu,

Bayan motar su Abusufyan Motar dake ɗauke da Baban Sadeeq ce,tare da Maman Sadeeq,ɗaya daga cikin motocin Sgr ne,wanda wani soja ke driving ɗinsu, Mamaki yaƙi barinsu,musamman Maman sadeeq,abun ya ɗaure mata kai har tagaza rufe bakinta, Kasa kasa tace "Baban Sadeeq kaga wani iko na Ubangiji"? Murmushi Baban sadeeq yayi tare da kallonta yace"dama ae naji ma ina sanar dake cewa,Allah yana tare dasu,kuma shi zai kula da abunshi,Yau nasan kin shaida maganata," Murmushi ta saki tunawa da wannan kalami na Baban sadeeq,a duk lokacin da ta rufe shi da faɗa kan cewa sunƙi ɗaukar mataki akan Ya sayyadi,yana ta cutar da bayin Allah,an zuba mashi,sai babban sadeeq yace mata"Bazan iya tunkarar mutumin nan ba,Mutumin da kana ja mashi ayar ƙur'ani yana fassara maka?taya zan iya tunkararshi?in dai akan yara ne Allah yana tare dasu,Kuma shi zai kula da abunshi," "Amma gaskiya Baban sadeeq,nayi matuƙar mamaki,har yanzu fa ji nake yi kamar mafarki nakeyi wlh,wai yanzu waɗannan danginsu rishi ne?bayin Allah,wlh na tayasu murna sosai," Baban sadeeq yace"Ni ji nake kamar nafi kowa farin cikin wannan ranar wlh,Alƙawarin dana ɗaukarwa kaina,Ya cika yau ga abu ga Ƴa'ƴanta,ga kuma danginsu,Godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata'ala,"

A bayan motarsu dasu Baban sadeeq suka,Motar dake biye da tasu,nurse ce ɗaya tare da Dr,An zo dasu ne don a nuna masu gidan,Saboda sune zasu ci gaba da zuwa suna duba lafiyarta,security guards sun sanya motocinsu a tsakiya,gaba da baya duk motocin Soldiers ɗinne,Sgr baisamu ya biyo bayansu ba,Sun wuce Hotel shi da Armstrong,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull