Abban sojoji takun karshe complete - Chapter 4
Abban sojoji takun karshe complete Chapter 4: Abban sojoji takun karshe complete Chapter 4. Lokacin da sehrish ta shiga main palour din nasu,anan ta samu…
4,445 words
Lokacin da sehrish ta shiga main palour din nasu,anan ta samu matasan gidan duk tsaitsaye akan junaid,dake kwance saman doguwar sofa ɗin da Abbansu ya kwantar dashi,a lokacin har sun yayyafa mashi ruwa ya farfaɗo,bakinsa sai faman kerma yake yi kuma har lokacin bai daina faɗin "Rishi guda uku"ba, Abusufyan yace"bawan Allah,nidai naji an saki ƙara ashe wai junaid ne,bansan time ɗin daya shigo ba,lokacin ina bacci ne,ae da ban bari hakan ya faru ba,da tun lokacin na fahimtar dashi,ashe har yanzu junaid na nan da wannan firgitar tashi,ae nayi tunanin ya daina,' Shafa gefen fuskarshi abba yayi a yayin da yake zaune daga gefen daman kujerar yace"Ya tsorata ne sosai,ae ni kaina banyi tsammanin zaije ɗakin nata bane,naso ace saida na fara yi mashi albishir sannan yaje wurinsu,' Jahan dake tsaye yace"Aikin ayaan ne,shine ya tura shi ɗakin nata,'ya ƙarasa maganar yana hararar ayaan dake tsaye yana dariya, Duk Alexandra na tsaye tana sauraronsu,sam batasan inda zancen nasu ya dosa ba, Koda sehrish ta ƙaraso,zuba mata ido Alexandra tayi tana kallonta,gaban sehrish ne ya faɗi lokacin da tayi arba da ita,har sai da ta ambaci Innalillahi acikin zuciyarta,ba komae ya firgitar da ita ba face ganin fuskar sgr a fuskar matar,kuma batasan da ita acikin gidan ba, sai dai lokaci guda taji aranta kaman ta ta6a ganin hoton matar, Cike da mamaki Alexandra tace"wacece wannan kuma"?tayi maganar tare da yin nuni da sehrish wadda tuni ta koma bayan abusufyan ta tsaya, Jahan ne ya bata amsa da cewa"Ƴan ukun uncle abusufyan ne,'. "Abusufyan kuma?dama ya ta6a aure ne? "Eh,ya ta6a aure batare da sanin kowa ba,sai daga baya abun ya bayyana cewar ƴa'ƴansa ne,kuma ƴan ukune kamanninsu iri ɗaya sak,abunda yasa kika ga junaid ya ruɗe kenan,baisan cewa su uku bane,ɗaya ya sani acikinsu,muma sai jiya Allah yasa mukasan da zamansu muka san cewa ƴa'ƴanshi ne,Nasan abba zai sanar dake komai,' Jinjina kai Alexandra tayi tare da ɗan ta6e bakinta,yayin da ta janye idanunta daga kan sehrish ta mayar dasu kan junaid dake ta faman sambatu, "Abba pls ku fahimtar dani mana!meyasa nake ganin Sehrish guda uku?ko na samu ta6in hankali ne,' "Junaid u should calm down ur mind,in baka natsu ba taya zamu fahimtar dakai,"acewar abbansu, Jin hannun mutun acikin nata yasata yin saurin juyawa,sai lokacin ta lura dashi sam bata ga fitowarshi ba, "Mommy,"ya ambaci sunanta cikin sanyin murya,cike da farin ciki tace"Fawan!ka farka daga baccin kenan"?tayi maganar ayayin da take janyo shi jikinta,sosai ta rungume shi, "Mommy tun yaushe kika zo ba'a sanar mun ba?sae dai na fito na ganki unexpected" "Tun jiya nazo fawan,muna tare da junaid acan gidana muka kwana tare dashi sai yau da safe muka dawo atare,da fatan na sameka cikin ƙoshin lapiya,' "Alhamdulillah mommy munyi missing ɗinki sosai da sosai,' "Nima nayi missing ɗinku fawan,'magana suka cigaba dayi atsakaninsu, Duk wannan abun dake faruwa alexandra bata tanka ma abusufyan ba,shima kuma bai tanka mata ba,tun lokacin daya shigo falon yayi arba da ita,yaga ta kawar da kanta gefe tun daga lokacin shima ya share ta,dama bata shiri dashi,tun lokacin da Abba ya aurota,ya ta6a zama agidan,yanayin yadda take wahalar da yayanshi ne yasa yayi mata rashin kunyar da ta haddasa gaba atsakaninsu,saboda shi bakinshi bai rufuwa muddin yaga tana gaya ma Yayanshi hossein magana saiya mayar mata da martani mai zafi,wannan dalilin ne yasa Abba yace ya tattara ya koma wurin ammi don bazai iya jurar zama dashi ba,kullum haɗa mashi Bomb yakeyi acikin gida,shiyasa abusufyan bai zauna agidan yayan nashi ba,kuma ammi bata kawo shi gidan ba lokacin daya addabeta da rashin jin maganarshi,kawai ta yanke shawarar kai shi gidan hajiya Ameenatu, Kowa daya fito tun daga kan su irfan jabeer,khaleed da kanal yousouf babu wanda baiyi farin cikin zuwan mommynsu junaid ba,daya bayan ɗaya saida tayi hugging ɗinsu ajikinta,kanal yousouf ne kawai ta manna ma kiss a gefen fuskarshi,ji suke tamkar mahaifiyarsu ce Maryam ta dawo gidan,Allah sarki Allah ya jiƙan rai,tun daga yanayin yadda alexandra ta kar6esu hannu bibbiyu tana rungumarsu ransu ya basu cewar ta shiryu yanzu,da alama babu wannan girman kan nata da kuma Zafin ran nan, Sehrish dae duk jikinta yayi sanyi tun daga kan irin kallon da taga Mommynsu junaid nayi mata,ranta ya bata cewar akwai matsala,sam fuskarta babu yabo babu fallasa lokacin da Jahan ke sanar da ita cewar ɗiyar uncle ɗinsu ce, Abbansu na ƙoƙarin fahimtar da junaid,suka jiyo muryar sgr yana tambayar"Meya faru ne!"yayi maganar ne ayayin da yake saukowa daga saman stairs ɗin,jikinshi na sanye da shirt fara ta ɗame jikinshi sai kuma dogon wando jeans,ba ƙaramin kyau yayi ba, Gaba daya suka juyo suna kallonshi,Marshal Omar na biye dashi abayanshi,atare suka sauko, Wani irin farin ciki ne ya lullu6e alexandra lokacin da tayi arba da first born dinta wato Surgeon General Rafayet,gaba ɗaya tagaza rufe bakinta saboda ba ƙaramin so take mashi ba,tana matuƙar alfahari dashi, Sehrish kuwa tunda taji muryarshi taji gabanta ya faɗi rass,tabbas tayi kewarshi sosai,jiya abubuwan da suka faru ne suka hana takai mashi dinner ɗinshi,tasan cewa daƙyar ne idan yaci wani abu ajiyan nan, Aranta tace"bansani ba ko yana farin ciki da kasancewata ƴar uwarshi,ɗiyar ƙanin Mahaifinshi,ko yaya yaji aranshi"? Jahan ne ya sanar dasu abunda ya faru da junaid, ƙarasawa Sgr yayi wurin Mommyn tasu,ita tafara manna mashi kiss a gefe da gefen fuskarshi sannan shima yayi mata kamar yadda tayi mashi,daga bisani kuma suka rungume junansu, Abun ba ƙaramin burge sehrish yayi ba,har sai da ta ɗan saki murmushi kaɗan a fuskarta, "Am really glad to see u mom,"ya furta hakan ayayin da suka raba jikinsu daga na juna, Shafa gefen fuskarshi tayi tare da cewa"Yanzu ka kyauta mun?tun yaushe rabon dana sanya ka a idanuna Alex?ka daina zuwa wurina,kusan 1 year kenan baka tako ƙafarka kazo ba,' Ganin hawaye sun cicciko a idanunta yasashi yin saurin ruko hannayenta tare da cewa"pls mom just forget about the past,nasan ban kyauta ba,amma kullum kina araina,kuma ina kiranki awaya muna gaisawa....' Abbansu ne ya katse firar tasu da cewa"Ashe ba daɗi,Rama mun yayi Nima,ƙiri ƙiri kin rabani da aurena kinsa anata yi mun kallon Tazuru,' Dariya sukayi gaba ɗayansu,banda sehrish dake tsaye jugum tana sauraronsu, Matsawa Omar yayi cike da zolaya yace"Oh Mommy abun ƴar wariyar launin fata ce ko?atare da bro ɗina muka fito,amma ko kulani bakiyi ba...'yayi maganar yana ɗan ɗaure fuskarshi, murmushi alexandra tayi tare da komawa wurin marshal,ta manna mashi kiss agefen fuskarshi sannan ta dafa shoulders ɗinshi tare da cewa"Omar ni bazan iya cewa komai ba,so nake nafara huce haushina akanshi kafin nadawo kanka,dama kaine mai ɗan son zumuncin,duk lokacin da kuka samu hutun aiki kana janyo shi kuzo wurina,amma yanzu duk kun juya mun baya,ni nasan duk shirin Abbanku ne yasan cewa dole nayi kewarku....' Omar yace"no ba haka bane mommy,rayuwarce sai a slow,bamu manta dake ba,kuma kamar yadda rafayet ya fadi,muna kiran ki fa awaya kullum mu tambayi lpyrki,da ace kin ƙara 1 week baki zo nigeria ba,da kin ganmu munzo,ba don ma aiyuka da sukayi mana yawa ba,ae da mun rigaki zuwa....' Ba ƙaramin daɗin kalaman Omar taji ba,yasan duk wata hanya da zaibi don ya kare kansu a wurinta,ba kamar SGR ba,shi kai tsaye kawai yake maganarshi ba wata kwana kwana,' Sai da suka samu natsuwa sosai,sannan suka tattara hankalinsu kan junaid, "Ina sehrish take ne"?Abbansu ne ya ambaci sunanta,saboda yaga gifcinta a wurin, Da sauri ta amsa mashi da cewa"Gani nan Abba,"tayi maganar tare da fitowa daga tsayen da take abayan daddynsu, Haɗa ido sukayi da Sgr,da sauri ta kawar da idonta,zuciyarta na harbawa da ƙarfi da ƙarfi,daƙyar ta iya ƙarasawa wurin abban nasu ta gaishe shi, Bayan ya amsa mata yace"ki fahimtar da junaid,ina tunanin in yaji daga bakinki zaifi yadda cewa ku ƴan uku ne,' Murmushi sehrish ta ɗan yi tana kallon fuskar junaid wanda ke kwance saman kujerar duk yabi ya rikita kanshi,tunda tayi magana yasan cewa itace saboda yaji muryarta, Cikin sanyin murya ta soma magana, "Junaid ka manta kwanaki na ta6a sanar dakai cewa Ina da ƴan uwa?waɗanda nake kira da wayarka? "Amma ai kince mun baki da wasu ƴan uwa lokacin da muka yi maki magana akansu ni da aunty azmee,"yayi maganar yana faman hura hanci, "Junaid a lokacin bana cikin hayyacina bansan ya akai na manta dasu ba,amma yanzu nadawo hayyacina kuma Zan iya tuna komai a game dasu,idan baka yadda dani ba,bari na tuna maka,ko ka tuna Yarinyar daka ɗauko a school cikin motarka?tun lokacin saida nayi ƙoƙarin fahimtar dakai cewar bani bace,ni ina a makaranta ka barni,shine dalilin da yasa nasha wahala aranar,' Jin wannan maganar ta sehrish yasa junaid miƙewa daga zaune,bakomai ne ya faɗo mashi aranshi ba face,yadda jahad ta kasa sakewa dashi,kuma launin gashin kanta baƙi ne ba irin na sehrish ba,hatta muryarsu ma akwai ɗan bambanci,haba no wonder shi dae ya jima yana tunanin cewa al'jana ya ɗauko a motarshi ashe ashe mutunce,indae dagaske ne xancen sehrish hakan na nufin cewa ƴar uwartace ya ɗauko a motarshi?to kodai sune yaran da Ya Omar ɗinsu yasa su gyarama gidan uncle ɗinsu zai kawosu suyi rayuwa aciki......'bai ƙarasa zancen zucin nashi ba,Muryar Omar ta katse Hanzarin shi"Junaid!maganar da take faɗa maka dagaske ne!they're triplet,kuma ƴa'ƴan uncle abusufyan ne,dukanmu bamu son da haka ba sai jiya Allah ya bayyana mana komai,' Yana kai ƙarshen maganar tashi ya juya tare da kallon fawan yace"Kaje ka kira mun su hosana da jahad suzo ya gansu da idanunshi don ya shaida cewar mutane ne ba aljanu ba,' Cike da zumuɗi fawan ya wuce bedroom ɗin sehrish a lokacin har jahad ta kammala shirya kanta cikin riga da skirt na sehrish,ba ƙaramin kyau tayi ba, Kwankwasa ƙopar fawan yayi kafin ya turo tare da cewa"Ya omar nason ganinku yanzu,'jin haka yasa sukayi saurin kimtsawa,duk suka yafa gyala a kansu, Atare da fawan suka shigo cikin main palour ɗin, Jerawa sukayi kusa da sehrish duk sun sha jinin jikinsu tsoransu kar ace wani abun ne kuma ya taso, zuba masu ido junaid yayi yana kallonsu,idan ya kalli jahad sai ya kalli hosana, A ƙarshe ya tsaida idanunshi kan jahad,ta hanyar gashin girarta ya gane cewa itace ya ɗauko a motarshi,har suka sha Love, Dafe kanshi yayi tare da cewa"OMG!Abba kenan reesh ƴar uwata ce,jini na,ɗiyar uncle ɗinmu abusufyan!taya hakan ya faru?kuma dama rishi ƴan uku ne su ba ita kaɗae bace!idan har dagaske ne meyasa basu taso atare damu ba!!!!!!!_ Karaf maganganun da junaid ke faɗi suka dira a kunnan Hayaam,wadda fitowarta kenan,yunwa ta korota daga bedroom ɗinta ta gaza jurewa shine ta lalla6a ta fito don ta shiga kitchen, Gabanta ne yayi wani irin bugu ji kake rasss!rarasss!hankali amatuƙar tashe ta ɗago da idanunta ta sauke su akan Mutanen dake tsaitsaye acikin falon,waro ido waje tayi ganin Sehrish dasu jahad,anan ta tuna abunda azmee ta faɗa mata jiya na cewa ƴan uku ne su,kuma kamanninsu iri ɗaya sak,a fili ta ambaci"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!Ya Allah ka rabani da mugun Ji da kuma mugun gani!nashiga uku Ni yau Hayaam,bari dae na ƙara kasa kunne naji uban da suke tattaunawa,ya Allah kasa korar shaggun za'ayi daga gidan,
"Junaid sehrish ɗin daka sani da kuma waɗannan biyun masu kama da ita sak,ƴa'ƴana ne,ni ne mahaifinsu,Na auri mahaifiyarsu ne ba tare da sanin kowa ba........'ataƙaice Abusufyan ya fayyace ma Junaid komai, Saboda tsabar kiɗima hayaam ƙiris ya rage ta fasa ƙara a wurin,ta matukar firgita da jin abunda abusufyan ya sanar ma jahad,tashin hankalin da ba'a sama shi date,gudu gudu,sauri sauri hada tuntube wurin komawarta cikin bedroom ɗinta,jikinta sae faman kerma yake yi kamar wadda sanyi ya kama,hannu ta aza asaman kanta tana faɗin"nashiga uku!na bani na lalace!ƙarshe na yazo acikin gidan nan!taya akai haka ya faru duk ina nan sake da baki bansani ba,wai yanzu dagaske yarinyar nan mai aikin gidan dana raina,nake ganinta ƙaskantacciya yar wurin uncle ɗinsu ce Abusufyan,Tabɗijancan,Kallo ya koma sama!kai anya kuwa banyi kuskure wurin sauraran maganar shi ba? Turo ƙopar da akayi ne yasa ta yin firgit ta juya, Tana ganin azmee hannunta ɗauke da plate na breakfast ɗin da ta kawo mata, Jiki na rawa hayaam ta ƙarasa wurinta tare da cewa"Aunty Azmee wai dagaske ne Seh...seh..rish ɗiyar uncle ɗinsu ce abusufyan!" Ƙayataccen murmushi azmee ta saki tare da cewa"Dagaske ne mana!Nima sai da asuba nakejin wannan labarin a wurin Hajiya azeemarsu....'tunda azmee ta soma magana hayaam ta fita hayyacinta, Har sai da azmee ta ambaci sunanta"Hayaam!naga kamar kin tafi duniyar tunani ne?lafiyarki kuwa? Murmushin yaƙe ta saki tana ƙoƙarin danne damuwarta tace"Azmee bana jin daɗi ne,zuciyata tafarfasa takeyi ne," .azmee tace"Allah sarki,dama saida raina ya bani cewa baki lafiya,To Allah ya sawake,yanzu dae ga wannan ki fara karyawa nasan kina jin yunwa.....' Wani irin bugu Hayaam takai ma plate ɗin dake hannun azmee nan take yayi gefe guda ya tarwatse ƙasa,snacks ɗin dake aciki suka 6are, Ita kanta hayaam sai da ta firgita saboda ba'a cikin hayyacinta tayi hakan ba,tsananin 6acin rai ne da ƙiɗimar da tayi, Hankali tashe azmee tace"Hayaam!!' Tunkan ta karasa maganar hayamm ta zukunna jiki na rawa tashiga kwashe snacks ɗin dake zube aƙasa tana mayarwa cikin plate din, Muryarta na rawa tace"dan Allah aunty azmee ki tafi kawai,nagode sosai zanci....' Ƙiris ya rage azmee ta fashe da dariya,ganin yadda la66an hayaam ke kerma kamar gandar nama,tasan cewa duk akansu sehrish ne, "Allah ya baki lafiya,"ta ambaci hakan tare da juyawa tabar mata ɗakin, Azmee na fita hayaam ta jefar da plate ɗin, . miƙewa tsaye tayi nan fa tashiga safa da marwa tana zagaye ɗakin,bakowa ne ya faɗo mata aranta ba face Aunty laila,tabbas ya kamata tayi gaggawar sanar da ita halin da ake ciki, Jiki na rawa ta ɗauko wayarta dake ajiye saman mirror,tana danna wayar yatsun hannunta na kakarwa,daƙyar ta tsaida hankalinta wuri guda ta danna ma Aunty Babba kira.
[3/19, 2:56 PM] +234 810 388 4440: *💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
_Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari sannan a kula wannan itace numbar wayata,Wasu suna ɗaukar numbar Wanda suka bani tallarsu kayansu suna kiransu a matsayin ni,bayan ni ga numbar dana bada nan itace numberta_
*Nagode sosai da addu'o'inku agare ni,da kuma uzurin da kukayimun,har zuwa wannan lokacin,Allah yabar zumunci a tsakaninmu daga nan har gidan aljanna💃*
*nace ba Masu satar littafi suna fitarwa ta bayan fage,mai yasa baku ƙarasa masu labarin ba?kuma kenan saida kuka jira ni?ae nayi tunanin cewa zaku ƙarasa masu labarin ne ashe dai sai anjira Boss*😂🤣😅
Bismillah
Kai tsaye sautin ringing ɗin wayar ya daki dodon kunnan Aunty babba dake baje saman gadonsu tana Bacci,a lokacin ko yatsanta bata jin xata iya motsawa saboda baccin dake a idanunta,yatsina fuska tayi alamar an takura mata, Ishaq dake tsaye agaban mirror yana gyara jikinshi ya ɗan gyara murya tare da cewa"Madam ki daure ki tashi ki ɗaga kiran nan!da alama kira ne mai muhimmanci tun ɗazu wayar ke ta ringing," Uban tsoki Aunty babba ta buga tare da yunƙurawa daƙyar ta tashi daga zaune,jikinta na sanye da sleeping dress,riga da wando purple colour, Fuskar nan tayi suntum kamar wadda aka nausa,hannu takai tare da ɗaukar wayar dake ajiye saman bedside drawer,duba screen ɗin wayar tayi ganin sunan Hayaam ya bayyana yasa ta ƙara tamke fuska kamar ta shanu,ɗaga kiran tayi tare da kara wayar a kunnanta,rai a6ace tace"Meyasa kika kirani fitsararra!ko kin kira ne don ki ƙarasa yimun rashin kunyar taki don ubanki," on the other hand hayam tace"haba aunty laila,ni harna manta da abunda ya faru atsakanin mu.....'tunkan hayaam ta ƙarasa maganar Aunty babba ta katse mata hanzarinta da cewa"Idan kin manta ae ni ban manta ba,Ki faɗamun uban miyasa kika kira ni,idan ba haka ba ni zan kashe wayar, Zuba mata ido Ishaq yayi yana kallonta aransa yace"Zagi kamar ƴar maguzawa,ko kunyata bata ji,sae faman ɗura ashar take yi,ni dae Allah ya haɗani da Guyaba,' cike da damuwa hayaam ta sassauta muryarta,tare da cewa"Aunty laila,na shiga uku,ko ince mun shiga uku,Akwai gagarumar matsala,Gaba daya duk wani plan ɗinmu ya tashi aiki,' Tunda Aunty babba taji hakan,gabanta ya faɗi rasss,ƙasa ƙasa da murya tayi tace"Hayaam meya faru?wata irin matsala kike magana akai? "Aunty laila,Ashe yarinyar nan mai aikin gidansu,ɗiyar uncle ɗinsu ce Abusufyan!!!!!" tamkar saukar aradu haka aunty babba taji maganar Hayaam aikuwa a matuƙar gigice ta miƙe tsaye tana cewa "kutumar uba!inji ubanwa!yaushe Abusufyan ya ta6a aure,Wlh ƙaryane koma wani ɗan ƙaniyar ne ya faɗi maki hakan babban maƙaryaci ne....' Gaba daya hankalin ishaq ya dawo kanta,maganar dayaji tana fadi ta tsaya mashi aranshi, "Wani abusufyan din kuke magana akai," Firgit Aunty babba tayi tare da ware ido tana kallonshi sam ta manta da cewar yana acikin ɗakin, Hankali a matuƙar tashe ta miƙe tsaye da nufin ta fuce daga cikin ɗakin,Saboda tsabar ruɗu ta nufi hanyar shiga toilet, gyaran murya ishaq yayi mata tare da cewa"kada fa ki shiga toilet da waya a kunnanki,' A zabure ta juya ta kuma nufi wardrobe da alama ruɗu yasa ta manta hanyar fita daga ɗakin,zuba mata ido yayi yana mai mamakin irin kiɗimar da tayi,to ko lafiya?ya tambayi kansa, Bata ankara ba sae da goshinta ya bugi jikin wardrobe din kayan nasu,sannan ta gane inda ta dosa,Rai a6ace ta kama hanya ta fuce daga dakin,saukowa downstairs tayi ta miƙi hanyar wannan tsohon store ɗin data ta6a garƙame su hosana aciki,anan corridor ɗin ta tsaya tana sauraran Hayaam, "Wlh Aunty laila da gaske ne,Ni shaidace,Naji komai lokacin da Uncle ɗin nasu yake korama junaid bayani,bama haka ba Aunty azmee da kanta ta gasgata mun hakan,Babban abunda yafi rikitar dani Yaran fa triplet ne ashe,kuma dukkansu Mata ne kyawawan gaske,kamannin su sak iri ɗaya,Kuma kina kallonsu zaki gane cewa ƴa'ƴanshi ne......' Hannu ɗaya Aunty babba tasa ta dafe tsakiyar kanta,yayin da dayan hannun ke ruƙe da wayarta data kara a kunnanta, "Hayaam bazan ta6a yarda da zancenki ba,Taya hakan ma zata faru!mutumin da bai ta6a yin aure ba,Shi za'ace yana da ƴa'ƴa har ƴan uku!Cikin shege kenan ya ta6a yima wata harya same su!Ni ban yarda da kalamanki ba,Hayaam kinsan cewa babu kyau tsoratar da musulmi,Idan wasa kike mun ki daina!!!!! 6acin raine yasa hayaam ta kashe wayar Fashewa da kuka tayi saboda ƙululun baƙin cikin daya tokare mata maƙoshinta,ga zuciyarta dake ta faman tafarfasa,Gaba daya bata jin daɗin jikinta, Zubama wayar ido Aunty babba tayi tana kallonta, Tsoki taja tana jinjina kai tace"dama saida raina ya bani cewa ƙarya take yi mun,tayi mun hakan ne saboda ta tsoratar dani don in saukko,Shashasha kawai, "Mommy kin farka kenan" Muryar hafsat ce ta katse mata zancen zucin nata, Juyowa tayi tana kallonta,atsaye take fuskar nan ɗauke da murmushi jikinta na sanye da riga da wando na jeans,ta ɗaure sumar kanta da ribbom,yayin da hannunta ke ruƙe da Cup mai ɗauke da Tea mai zafi sai faman tiriri yake yi, Tunda Aunty babba taga hafsat na murmushi tasan cewa akwai matsala,hakanan dae ba zakaga fuskar hafsat da murmushi ba tunda farar safiya, ƙaƙalo murmushin yaƙe Aunty babba tayi tare da cewa"Lafiya naga kina murmushi"? "Lafiya lou mommy,kawai wani abun farin ciki ne ya faru,nasan cewa muddin kema kika ji,zaki yi farin ciki sosai,' Murya asanyaye aunty babba tace"Faɗamun daughter har na ƙosa naji wannan abun farin cikin?halan an ƙara maku albashi ne?ko matsayi aka ƙara maki wurin aiki"? Dariya hafsat tayi tana girgiza kai tace"Mommy baki canka dai dai ba,wannan albishir ɗin da nakeso inyi maki yafi ƙarfin duk waɗannan abubuwan da kika lissafo,kar6i tea ɗin nan ki fara korawa kafin na faɗa maki," Hannunta na kerma ta kar6i kofin da hafsat take miƙa mata,a hankali takai cup din bakinta ta kur6i Tea ɗin,kusan sau uku tana kur6arsa,kafin ta ɗan jinkirta bayan ta janye kofin daga bakinta tace"daughter dan Allah ki faɗamun wannan wani abun farin ciki ne!wlh duk na ƙosa naji,' "Zan faɗa maki mommy amma mu shiga daga cikin palour mu zauna,' "Ba inda zanje,idan zaki faɗamun ki faɗamun kawai,Sae ja mun rai kikeyi," tayi maganar tana faman tamke fuska, Hafsat tace"bada jimawa ba,Na kira Aunty azeema,don in gaishe da ita,Anan take sanar dani cewa ƴa'ƴan uncle abusufyan Sun bayyana...! Tunkan ta ƙarasa maganar a gigice Aunty babba ta saki kofin dake hannunta,Ya tarwatse ƙasa,Ruwan tean dake ciki ya fallatsar masu a ƙafa, ja da baya hafsat ta ɗanyi tana kallonta tace"haba mommy,so kike ki ƙonamin ƙafa ta,daga faɗin abun farin ciki? Rai amatuƙar 6ace tace"Ki 6ace mun da gani sakarya kawai,Maƙaryatan banza,bazan ta6a yadda da kalamanku ba,duk bakinku ɗaya da Hayaam,' Ta faɗi hakan tare da kama hanya fuuuuu kamar zata tashi sama,ranta duk a jagule,bin bayanta hafsat tayi da kallo harta haye upstairs,ta6e baki tayi tare da watsa hannayenta tace"I don't care, Ni dae farin ciki nakeyi,Daddy ma nake jira in tambayeshi yaushe zamu je gidan saboda a qagare nake dana ga ƴa'ƴan uncle ɗinmu Abusufyan,tunkan na gansu har naji ina sonsu sosai,in ma na tashi tafiya hada tsaraba zan tafin masu dashi,' Cike da farin ciki hafsat take maganar,zuƙunnawa tayi tana tattare kofin da aunty babba ta fasa,
Lokacin da Aunty babba ta ƙarasa bedroom ɗin nasu,har ta ɗaga ƙafarta zata zura acikin ɗakin taji muryar ishaq yana cewa"Alhamdulillah!Alhamdulillah!Alhamdulillah!Abba nayi farin ciki sosai,Meyasa tun jiya ba'a sanar dani ba,ae da tunda sanyin safiya zanyi maku dirarr mikiya,Amma ina taya uncle murnar ganin ƴa'ƴanshi,kuma ina tayamu murnar samuwar ƴan uku acikin zuri'ar mu,gaskiya bazan ma iya jurewa ba,Zan shirya nazo ne kawai,saboda na qosa naga ƴan ukun mu bayin Allah.... Abba yace"wani abun ma sai kayi tozali da yaran,kyawawan ƴan mata dasu,Yadda kasan photo copy ɗin abusufyan haka suke,kamanninsu sak iri ɗaya da nashi,' Murmushi Ishaq yayi tamkar yana agabanshi yace"Abba kafin na ƙaraso,dan Allah a isar musu da saƙon gaisuwata,Ace yayansu General ishaq yana gaishe su sosai da sosai,kuma saboda suma zaiyi zuwa na musamman,' "Insha Allah zan sanar masu yanzun nan,Allah ya kawoka lfy," "Ameen Abbana," Sun jima suna waya kafin sukayi sallama ishaq ya ajiye wayar, tashin hankalin da ba'a sama shi date!!!!!!! Magana dae ta tabbata da gaske ne zancen da hayaam da hafsat suka faɗa mata,Tabɗijancan, Dakyar ta iya shiga cikin ɗakin,lokaci guda ta rasa kuzarin jikinta kamar wadda tayi Zazza6i na sati ɗaya, Jin takun tafiyarta yasa ishaq juyawa yana kallonta fuskarshi a washe har ya kammala shiryawa cikin haɗaɗɗiyar shadda, Ganin yana ƙoƙarin buɗe baki yayi mata magana yasa tayi saurin katse shi da cewa"Naji abunda ya faru,Hafsat ta sanar dani komai,ina tayaku murna,'ko amsar shi bata tsaya ji ba,ta faɗa cikin toilet, Tana juyo muryarshi daga cikin bedroom ɗin yana cewa"Ni yanzu zan wuce Abuja ne,inyaso kun biyo ni daga baya ko zuwa gobe ko jibi haka,duk dae yanda kuka yanke shawara keda hafsat, daga cikin toilet tace"Allah ya sauke ka lpy,in anje agaishe mana da mutanen gidan," "zasuji insha Allah," ya amsa mata tare da kama hanyar fita daga ɗakin.
❤🤍❤
Acan 6angaren kuwa har lokacin suna a falon kan junaid da Uncle abusufyan ya gama fahimtar dashi game da Su Hosana da jahad, jiki asanyaye yace"Amma meyasa su ba suyi rayuwa atare damu ba?meyasa Abba?uncle why?cike da tuhuma yake maganar yana kallonsu,yayin da fuskarshi ke ɗauke da damuwa, abban su ne yace"Junaid,mu kanmu bamu san dasu ba,da ace munsan da zamansu da bamu bari hakan ya faru ba,ƙaddara ce kawai ta riga fata," Shiru junaid ya ɗanyi yana ƙare ma su Jahad kallo,yaso ace tun fil azal tare da yaran ya taso,da ba ƙaramin kulawa zasu samu a wurin ƴan uwansu ba,Allah sarki rayuwa kenan,Rashin sani yafi dare duhu,su kansu su Sehrish sae dama dama suke da sun san cewa suna da wannan family ɗin daba abunda zai hana su nemi danginsu,Tabbas an cuci rayuwarsu ƙiri ƙiri an rabasu da Ubansu kuma an hanasu danginsu,wata shari'ar dae sae a lahira,
"Nasan yanzu kowa yana jin yunwa,saboda halin da muka shiga jiya babu wanda ya samu damar cin abinci acikin mu,Yakamata yanzu komai ya wuce,Lokacin farin ciki ne,Za'a shirya gagarumar walima saboda ƴan ukun mu,munaso su manta da duk wani abu da ya faru a rayuwarsu kuma su ƙaddara cewa tamkar yau ne suka faɗo duniya,ko ba haka ba"? Ya yi maganar yana kallon matasan gidan dake atsaye,Kowannansu fuskarshi asake,su fawan ne suka haɗa baki wurin cewa"Wannan haka yake Abba,In sha Allah zamu nuna masu soyayyar ƴan uwantaka,har sai sun manta da dukkan wani ƙunci da suka fuskanta na rayuwarsu,' murmushi kawai Abusufyan ke saki don ba ƙaramin daɗi yaji ba, Marshal Omar yace "Sannan kuma muna ƙara baku haƙuri game da halin da kuka tsinci kanku,duk da ba laifin mu bane,amma mun ɗaura ma kanmu laifin,Muna neman afwarku,Hosana Sehrish and Jahad,forgive us pls,' gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi,lokaci guda kuma sukaji wata irin soyayyar ƴan uwansu ta kamasu, Jahad ce tayi ƙoƙarin cewa"duk wani abu daya faru damu dama can rubutaccen ne!Allah ya riga da ya ƙaddara faruwan hakan,mun gode ma Allah da muka cinye wannan jarabawar,da juriya kuma da haƙuri,yanzu gashi gaba ɗayanmu muna farin cikin wannan rana da Allah ya haɗamu da danginmu,Babban abun farin cikin ma da ya kasance Uncle abusufyan shine mahaifinmu ba waccen fasiƙin mutumin ba.......'kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan daya zo mata,Janyota Abusufyan yayi tare da rungumeta ajikinshi,yana ɗan bubbuga bayanta, "Ya Omar," hosana ce ta ambaci sunan shi,tana faman kumshe dariya abakinta,gaba ɗaya suka mayar da hankalinsu akanta,nuna shi tayi da yatsanta sannan ta nuna kanta,kafin ta haɗe yatsun wuri guda ta ƙullasu,Alamar ita dashi sun zama ƴan uwan juna, ƙayataccen murmushi Marshal ya saki yana kallonta, Duk wannan abun dake wakana akan idon Sgr dake atsaye,ya goya hannayenshi asaman wide chest ɗinsa,Har lokacin bai sauko ba,hankalinsa fa bazai kwanta ba har sai yayi tozali da YA SAYYADI,
Suna cikin magana muryar azmee ta katse su da cewa"Abba an kammala shirya breakfast ɗin,yakamata ku hallara a dining ɗin," tana magana idonta na akan su jahad fuskar nan ɗauke da murmushi, Batare da 6ata lokaci ba,gaba ɗayansu suka hallara asaman zungureran dining table ɗin wanda ke shake cike tab maƙil da kayan makwalashe naci dana sha,mutun goma shabiyu yake ɗauka,akwai kuma wanda Abban su junaid yasa aka ƙara cikin wanda aka shirya walimar jiya dasu,Ansanya shi a gefen nasu mai mazaunin mutun shida,Aunty azmee ta jera wasu kayan kalacin asaman shi,anan Abusufyan ya zauna tare da su sehrish jahad da hosana,
Tun daga kan yadda kowa ke zuba abinci acikinshi zai tabbatar maka da cewar ba ƙaramar yunwa suke ji ba,ko azmee basu jiya tayi serving ɗinsu ba suka shiga zuba abincin da kansu,Sgr ne kawai tayi serving ɗinsa sae kuma Abbansu,amma sauran ba wanda ya tsaya jira,wurin yayi tsit bakajin hayaniyar komai,sai sautin Cokulla,kwas kwas kwakwasss,