Kenza eBookz

Abban sojoji takun karshe complete - Chapter 46

Abban sojoji takun karshe complete - Chapter 46

Abban sojoji takun karshe complete Chapter 46: Abban sojoji takun karshe complete Chapter 46. "Samu wuri ki zauna mana"Mommynsu Junaid ce tayi mata magana…

4,116 words

"Samu wuri ki zauna mana"Mommynsu Junaid ce tayi mata magana ganin ta tsaya atsaye kiƙam, Sunkuyar da kanta ƙasa tayi,tana wasa da yatsun hannunta sam taƙi motsawa, "Ki zauna mana baki ji ana magana ba"Abusufyan ne ya tunasar da ita, Tafiya ta soma yi zata zagaya ta zauna, "Ina azmee take ne?naga yau tunda ta jera abinci,bata fito tayi serving ɗinmu ba kamar yadda ta saba,kodai bata lafiya ne"Abba ne yayi maganar cike da son jin ƙarin bayani daga wurinsu Abusufyan yace"Nima tun ɗazu na lura bata a wurin nan,yakamata a dubo ta aji ko lafiya," "Bari naje na kirata,"Ko sauraron amsarsu batayi ba,dama so take ta gudu daga Dining area ɗin, Gudu gudu sauri sauri ta nufi corridor ɗin ɗakinsu,a ƙopar ɗakin azmee ta tsaya tare da sanya hannu ta kwankwasa ƙopar,kusan sau uku tana buga ƙopar,ana ƙarshe ne tajiyo muryar azmee daga cikin ɗakin tana tambayar wanene, "Sehrish ce Aunty azmee,su daddy ne ke nemanki,Sun ji shiru shi ne suka ce a kirawo ki," "Okey,gani nan zuwa,bana jin daɗi ne," Tsayawa sehrish tayi a bakin ƙopar ɗakin har saida azmee ta fito jikinta sanye da hijabi, "Aunty azmee ya jikin naki"? Daƙyar ta iya buɗe baki"da sauki,ciwon kai ne,kuma nasha magani," "Allah ya ƙaro sauki Aunty azmee,"ta ƙarasa maganar tare da ruko hannun azmee cikin nata,suka kama hanyar zuwa dining ɗin atare,

Lokacin da suka ƙaraso dining area ɗin,hankalin kowa ya dawo kansu, "Oumma ga Aunty azmee nan,kallatta ki gani,itace muke baki labarinta jiya mai girka mana abinci"a wani slow abu ta wurga eyeballs ɗinta akan fuskar Azmee,karaf idanuwansu suka shiga cikin na juna,Zumbur abu ta miƙe tsaye tana kallonta,kallon kamar nasanki,Itama Azmeen kallon Sani take yi mata, Ganin sun ƙurawa juna ido,babu mai magana acikinsu,yasa Abusufyan tanka masu"Ko kunsan juna ne"? Girgiza kai abu tayi"a'a gani nake yi kamar na santa ne,tayi mun kama da wata dana ta6a sani arayuwata,Amma bazan iya tunawa ba, "Aunty azmee kefa?kinsan Oumma ne"?Sehrish ce tayi mata tambayar,girgiza kai azmeen tayi"A'a nima dai kallon sani nake yi mata,kamar na ta6a sanin wata mai irin fuskarta,amma dai ba ita bace ba,sunyi kama ne" Murmushi sehrish ta ɗan saki tare da cewa,"tunda baku san juna ba,bari na gabatar da kowannanku," "Aunty Azmee wannan itace Oummanmu,mahaifiyarmu," Sannan ta nuna Azmee"Oumma ga Aunty azmeen da muke baki labarinta jiya,ba iya girki kaɗai ta iya ba,tana da kyakkyawar zuciya,mutuniyar kirki ce ita," Murmushi abu ta saki tare da miƙa ma azmee hannu suka gaisa da juna,kowa fuskarshi ɗauke da murmushi,

Ajiyar zuciya Sehrish ta sauke,ganin hankalin kowa ya koma kansu yasa tayi saurin lalla6awa ta wuce kitchen,shaf shaf ta shiga haɗa mashi breakfast ɗinshi,

"Sehrish ta faɗamun irin halarcin da kikayi mata,bansan da wasu kalmomi zanyi amfani dasu ba wurin gode maki,Allah ne kaɗai zai iya saka maki" Murmushi Azmee tayi"Ae duk yiwa kaine,na dauki sehrish tamkar ƴar cikina,"dakatawa ta ɗan yi da yin maganar,ta mayar da idonta kan Abusufyan"ina tayaka murna sosai,Allah ya ƙara haɗa kan zuri'arku,"addu'o'i ta shiga yi masu suna amsa mata da Ameen,kafin daga bisani Abba yace"Samu wuri ki zauna,Ke ma Azmee daga yanzu bana so kina wannan tsayuwar,don yanzu kinfi ƙarfin ƴar aiki a wurinmu,pls kada kiyi mun musu kamar yadda kika saba," Murmushi Azmee tayi tare da samun wuri a table ɗinsu Abusufyan ta zauna,Abu ma ta zauna,a tsanake kowa yake cin abincinshi,Abunda zai ɗaure maka kai,ya baka mamaki shine duk bayan ƴan mintina sai abu ta saci kallon Azmee,da alama dai tasanta ne,kuma tana ƙoƙarin tuna wurin da suka ta6a haɗuwa,itama Azmeen satar kallon nata take yi,kowa da abunda yake sakawa aranshi, Fitowa tayi daga cikin kitchen ɗin hannunta ruƙe da ƙayataccen tray,hannu bibbiyu ta ruƙo shi,cikin sanɗa ta wuce upstairs,direct ta nufi part ɗin Sgr,a bakin ƙopar shiga falon ta tsaya sallama tayi jin shiru ba'a amsa mata ba,yasa ta wuce ciki izuwa bedroom ɗinshi,tana ƙoƙarin shiga,tajiyo maganganunsu shi da Omar,kasa kunne tayi tana sauraronsu, "Yanzu ya zamuyi?duk mun jefa kanmu cikin haɗari,idan har Abba yasan cewa ƙaryane ba kidnapping ɗin su Junaid akayi ba daga ranar zai ƙullace mu aranshi,kuma girmanmu zai faɗi agaban ƙannenmu ne,nayi regretting wlh,"Omar ne yayi maganar,a yayin da yake zaune gefen gadon, "Omar,nima ina danasanin yin hakan,na shiga damuwa sosai,bansan ya zamu yi ba,remain just one week and some days,daddy tare dasu fawan jiranmu kawai suke yi mu kawo masu Junaid"yayi maganar ne yayin da yake tsaye gaban mirror yana gyara jikinshi dake sanye da Bathrobe,ga danshi danshin ruwa da alama bai jima da fitowa wanka ba, Kowanne fuskarshi akwai tarin damuwa,abun ya tsaya masu aransu, Jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba, "Assalamu alaikum,"jin muryarta yasa suka tsagaita da yin firartasu, "Who's there"Sgr ne yayi tambayar "Sehrish ce,breakfast ne na kawo maka" Murmushi Omar ya fara saki,yana kallonshi,harara Sgr ya ɗan wurga mashi, Miƙewa Omar din yayi"kar na takura maka,bari na baka wuri,idan Mun haɗu zamuyi magana,"bai tanka mashi ba,Ya nufi hanyar fita daga ɗakin, Sehrish na ganinshi tayi saurin gaisar dashi"Ina kwana ya Omar," Fuskarshi ɗauka da fara'a ya amsa mata"Lafiya lou,ina fata kema haka". "Ina lafiya,"daga haka ya matsa mata hanya ta wuce ciki,Shi kuma ya fuce daga ɗakin,

A hankali take tafiya ta cikin mirror yake ƙare mata kallo,A saman table ta ajiye mashi tray ɗin,sannan ta ɗan juya tare da kallon bayanshi,gaisar dashi tayi"Gm ya Rafayet,ka tashi lafiya,"shiru bai amsa mata ba,kamar bashi bane ya gama magana yanzu tare da Omar,

Juyawa tayi saɗaf saɗaf zata bar bedroom ɗin nashi, "Where are u going?kin kammala aikin ki ne?" "A'a,naga kamar kana shiri ne,Zan jira a falo,idan ka kammala zan shigo daga ciki in yi aikin," A wani slow ya juyo tare da kallonta,adai dai lokacin itama ta waiwayo shi, Har sai da gabanta ya faɗi lokacin da idanuwansu suka haɗu cikin na juna, Da hannu yayi mata alamar ta dawo,kamar wadda aka zarewa laka,haka ta dawo daga ciki duk tasha jinin jikinta,ƙoƙarin gyara Mashi bedroom ɗin ta shiga yi,kamar daga sama taji ya cire mata mayafin jikinta,da sauri ta juya tana kallonshi "Taya zaki ji daɗin yi mun aiki da wannan abun a jikinki"? Shiru tayi batace komai ba,Sae ƴan kame kame takeyi, Jefa mata shi yayi asaman bayanta,"ki san inda zaki ajiye shi," Ruƙo mayafin tayi tare da ɗaure ɗamararta dashi kamar yadda ta saba yi,mayar da hankalinta tayi wurin gyara mashi gadon, Cike da tsantsan sha'awarta yake bin jikinta da kallo,bai ta6a sanin kyawun launin ja ba sai da yayi arba da rigar jikin Sehrish wadda ta kasance Red colour,ga shi hannu ɗaya gareta,Soft skin ɗin bayanta mai matukar jan hankali sai fisgarshi takeyi izuwa gare ta,

Tana cikin gyaran taji motsinshi a bayanta,A firgice ta juya karaf suka haɗa idanu,Zazzare mashi kyawawan idanuwanta ta shiga yi,farare ƙyal dasu masu ɗauke da kwayar ido brown colour,ja da bayan da take ƙoƙarin yi ne yasa ta kusa faɗawa saman gadonshi saboda ta ƙure mashi,da sauri ya cafko Waist ɗinta da hannu ɗaya ya janyota izuwa jikinshi,gaba ɗaya yayi hugging ɗinta so tightly,ta ko'ina ƙamshin turarenta neman yi mashi illa yake yi yana ƙoƙarin Zautar dashi,natsuwa Sehrish tayi yayin da kanta ke kwance luff asaman faffaɗan ƙirjinshi,wannan daddaɗan ƙamshin turaren nashi ne ke dakar hancinta,Gaba ɗaya jikinta ya mace, Moving hands ɗinshi yayi tun daga kan Ass ɗinta ya tarboshi,ya jinjina girman hips ɗinta,slowly yayi sama da hannun zuwa cikin sumar kanta,sosai ya shiga murza gashin da yatsun hannunshi,tamkar yana yi mata susa haka ta dinga ji,ga wani irin daɗi mara misaltuwa,almost 5 mins ya rabata da jikinshi,Yayin da idanuwansu ke kallon cikin na juna kamar masu jin bacci,dawo da hannun nashi yayi saman Hips ɗinta tare da pulling ɗinta ya haɗe gabansu sosai,Ji yake tamkar kawai ya aiwatar da abunda zuciyarshi ke raya mashi,but this is not the right time da yake son wannan abun ya kasance, "Meyasa baki gaishe ni ba"?da wata irin kasalalliyar murya yayi maganar, Muryarta na kerma tace"wlh na gaishe da kai,tunda na shigo," "Haka ake gaisuwa?"? Abun nashi ya fara ɗaure mata kai, Cigaba da magana yayi"Ni ba haka nake son ana gaishe dani ba,a kowani lokaci idan kika zo part ɗina,lemme teach u.."moving face ɗinshi yayi izuwa gefen fuskarta,Ya manna mata kiss,side by side na fuskarta,slowly ya dawo da sweet lips ɗinshi saman nata soft lips ɗin ya haɗesu wuri guda,kissing ɗinta ya fara yi,da niyyar ya koyar da ita yadda yake son ta dinga gaisar dashi,Boss man ɗin sai gashi ya fara Hawa kan Network,sosai ya matseta ajikinshi,A susuce ya shiga sucking lips ɗinta,Mayar mashi da martani ta shiga yi hakan yasa shi ƙara zaucewa,gaba daya ya sabeta izuwa saman gadonshi ya kwantar da ita,yabi kayansa ya turmushe,Zage zip ɗin rigarta ya fara yi,ƙankame hannunshi tayi saboda bata kaiga fita hayyacinta ba,kuma ta jiyo motsin mutun a falo,a rude yake faɗin"feed me pls,i really need it,"hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,ya zauce gashi wani yana tunkaro ɗakin, Girgiza mashi kai ta shiga yi tana faɗin"Akwai mutun a falo,bazan iya ba," "I don't care,just feed me,ƙoƙarin sabule mata rigar jikinta yake yi,don ya samu yasha ko ya kore kishin ruwan da yake ji,don maƙoshin shi a bushe yake, "Rafayet"!muryar Abbansu ce ta karaɗe kunnuwansu,jiki na rawa Sehrish ta janye jikinta daga nashi,A hanzarce ta diro daga saman gadon ta faɗa bayan labule ta 6oye,tana faman sauke ajiyar zuciya, Kasa amsa mashi kiran nashi yayi numfashin shi na fita da wani irin huci huci,yayi Uban goho asaman gadon,Sumar kanshi duk ta rufe mashi fuskarshi, Shigowa cikin bedroom ɗin Abba yayi,yana kallonshi cike da mamaki yace"Rafayet baka da lafiya ne"? Daƙyar ya iya motsa lips ɗinshi"Am ok," Ƙarasa shiga cikin ɗakin Abbansu yayi tare da samun wuri ya zauna daga gefen gadon yana ƙare mashi kallo,Yaƙi yadda ya ɗago da kanshi,gudun kada Abbansu ya gano shi,Don kallo guda zai yi mashi ya shaida cewa wani abu ke faruwa,ga janbakin sehrish daya 6ata mashi chest ɗinshi, "Rafayet,inason magana da kai game da Junaid,na kasa cin abinci ko isasshen bacci bana samu,Raina yana bani cewa kamar bazai dawo ba,idan har akwai abunda kuke 6oye mun kaida Omar dan Allah ku sanar dani,Don in fidda rai da dawowarshi," Gyara bathrobe ɗin jikinshi yayi,ya ɗaure igiyoyin jikinta,sai da ya fara daidaita natsuwarshi sannan ya miƙe daga zaune ya zuro da ƙafafunshi ƙasa,kallon juna su kayi shi da Abbansu,hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba,Ganin hawaye asaman fuskar Abbansu, "Daddy,don Allah kadaina zubar da hawayenka,before end of this month,in sha Allah daddy,zan sanar dakai komai," "Har yaushe ne zaku cigaba da samun ran dawowarshi?Idan mutuwa yayi ku sanar dani mana,na fara zargin hakan acikin raina,da ace kidnapping ɗin Junaid akayi dagaske,Even one day bazaku bari yayi ba,batare da kun dawo dashi cikin gidan nan ba,Amma almost 3 Weeks Junaid baya a gidan nan?kullum ƙara samana ran dawowarshi kuke yi"miƙewa yayi daga tsaye jikinshi na kerma ya soma tafiya daƙyar yake iya tafiya,har sai da yakai bakin ƙopar sannan ya dakata da yin maganar ya juyo tare da kallonshi har lokacin bai motsa ba daga zaunen da yake, Cikin sanyin murya ya Ambaci sunanshi"RAFAYET" "Na'am Abba,"ya furta hakan yayin da yake kallonshi,jikinshi ya gama yin sanyi, "In cigaba da sa ran dawowarshi ne?ko in fidda rai,"shiru Sgr yayi batare daya tanka mashi ba,Nazarin maganar shi ya shiga yi,muddin yace mashi ya fidda rai,to tabbas zai fahimci cewa Junaid ya mutu ne, Muryarshi tamkar zai fashe da kuka yace"Am really sorry Abba,dan Allah ka bani time,zan baka amsar tambayarka,Amma ba yanzu ba,akwai wani investigation da nakeyi,Zan sanar dakai komai," Gyaɗa kanshi yayi tare da kama hanya ya fita daga cikin ɗakin,Yana juyo muryarshi yana fadin"Zan cigaba dasa rai," Sun jefa kansu cikin tsaka mai wuya,kifa kanshi yayi A saman mattress ɗin, Sehrish dake la6e abayan curtains ɗin sai faman shessheƙar kuka takeyi,tausayinsu ne ya kamata,ta jima tana kuka abayan labulen kafin ta fito tana tafiya izuwa gefen da Sgr yake a kwance, Tsayawa tayi tana kallonshi,yatsun hannunshi sae kerma sukeyi kamar wanda sanyi ya kama, A hankali ta furta sunanshi"Ya Rafayet," "Pls,Just Leave am not in the mood,"da gudun gaske Sehrish ta kama hanyar fita ɗakin tana kuka,bata ji zafin maganarshi ba,

Yinin ranar ko abinci Sgr baici ba,Yadda takai mashi kayan abinci haka ta kwaso su,bai ta6a koda Coffee ba,

After 5 days,bayan kwana biyar,wanda yayi dai dai da sati uku da kwana Biyu da rasuwar baby Junaid!!!!!saura kwana 5 ya rage masu su bayyanar da Junaid,komai ya gama hargitse masu babu wani sauran kwanciyar hankali da suke dashi,

Wuraren ƙarfe 9 na dare,Suna kwance a ɗakinsu,har lokacin Atare suke kwana da Oummansu,Har ɗaki aka ware mata haɗaɗɗen bedroom amma tace ita tafi son ta kwana tare da ƴa'ƴanta,Su uku ne saman gadon suna bacci,Oummansu tare dasu Hosana da Jahad,Sae faman sharar bacci suke yi, Sehrish kuwa sam ta gaza runtsawa,ta sanya damuwa sosai aranta,ta ɗaurawa kanta nauyin alhakin Ƙaryar dasu Ya Omar su kayi ma Abbansu, Tana zaune saman sallaya bata jima da kammala yin nafilfilin dare ba,hannayenta ta ɗaga saman tana addu'a,yayin da hawaye ke shararowa akan fuskarta,kusan minti 30 Sehrish bata dakata da yin addu'ar ba,sai da tayi mai isarta aƙarshe ta fashe da matsanancin kuka,da sauri ta sanya tafin hannayenta saman fuskarta ta toshe bakinta gudun kada sautin kukanta ya tashi su Oummansu, A saman dardumar ta kwanta,tana ci gaba da yin kukan,taso ace zata iya taimaka masu sai dai babu halin yin hakan,tafi damuwa da Sgr don tun ranar da Abbansu ya ƙara tunasar dashi akan Junaid,ita shaidace bai ƙara cin abinci ba,Sai dai lemu da yake sha,babu bacci a idanuwanshi,kullum babu lafiya ajikinshi,duk yabi ya hargitse,

A cikin wannan yanayin bacci yayi awon gaba da ita, _Sae da suka kammala hoton sannan ta lura da zoben diamond ɗin dake hannunshi,sae faman ƙyalli yake yi_ _Waro ido waje tayi alamar mamaki tace"wow junaid wannan fa,waya siya maka shi_ _Mommy azeema ce ta bani shi,dama ɗazu na sanar dake cewa zan nuna maki gift din da takawo mun,to itace wannan_ _Ya ƙarasa maganar yana nuna mata zoben da Wrist watch din_ _Junaid sunyi kyau wlh,musamman daya kasance kaine ka sanyasu_ _Thank u reesh,sunyi mun kyau amman idan ke kika sanyasu sae sun fi yi maki kyau,bari na ciro maki su ki sanya,nafison su kasance a hannunki_ _cikin sauri tace mashi"no junaid that's impossible,Auntynku azeema ce ta baka shi,muddin ta neme shi a hannunka bata ganshi ba zata nemi jin ba'asin inda ka kai su,kuma ma in banda abun ka junaid wannan ae irin naku ne!kamar diamond ne fa,nida ko zoben azurfa ban ta6a sanyawa a hannu ba,balle diamond_

A firgice Sehrish ta farka daga baccin da ya dauketa,mafarkin da tayi yayi matukar ɗaure mata kai,Zurfin tunani ta shiga lokacin guda ta gane wannan zoben da Junaid ya ta6a nuna mata Shi ne tagani a ɗakin Aunty azmee kamanninsu ɗaya Sak!tabbas kuwa shi ne na Diamond wanda Aunty azeema ta siya mashi mai harafin *j*

Wata irin zufa ce ta shiga gangaro mata agafe da gefen fuskarta,tunani ta soma yi mai yakai zoben Junaid a dakin Aunty azmee?Yakai mata ajiya ne,?sam bata kawo komai aranta ba,Amma tunawa da tayi cewa junaid duk inda zaije zoben nan na ahannunshi wannan yasa ta fara kokonton wani abu,Zumbur ta miƙe daga saman sallayar ta nufi saman gadonsu,

Lalla6awa tayi ta haye saman gadon,saitin wurin da Jahad take a kwance,hannu tasa tana ɗan bubbugata yayin da take ambaton sunanta a Hankali don kada ta tashi Oummansu, "Jahad!jahad!"can cikin bacci jahad tajiyo muryarta,dakyar ta iya buɗe idanuwanta masu ɗauke da bacci,ganin Sehrish yasa ta dan mike daga zaune"lafiya rishi?dama baki yi bacci ba?" "Jahad duk ba wannan ba,wata tambayace nakeso nayi maki,A ranar da kuka fita tare da Junaid shan ice cream shin kin kula akwai agogon diamond da ring a hannunshi ko babu"? 'Meyasa kikayi mun wannan tambayar Sehrish!So kike ki tayarmun da hankalina?Kinsan fa banaso ana tunamun mutuwar Junaid,"tayi maganar hawaye na zuba akan fuskarta Arude Sehrish tace"dan Allah ki sassauta muryarki Jahad,bana so kowa yaji,nasan baki so amma dan Allah ki yi hakuri ki amsa mun tambayata," Shiru Jahad ta ɗan yi da alama ta shiga zurfin tunani,kusan minti 5 kafin tace"Kamar naso naga zoben a hannunshi,Amma bazan iya tunawa ba gaskiya" "Ko hoto baku ɗauka tare dashi ba"? Rai aɗan 6ace Jahad tace"haba Sehrish sai kace wata ƴar jarida,irin waɗannan tambayoyi haka? "Nidai ki amsa mun tambayata,"a kule tayi maganar, Ganin ranta ya 6aci yasa Jahad cewa"Am Sorry,munyi hoto da junaid,hada ma videos muka ɗauka,Amma wayar bata a hannuna,Tana a wurin Ya Omar....."tunkan takai ƙarshen maganar Sehrish ta fuce daga cikin ɗakin a fujajen. [3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋𝔹𝕠𝕤𝕤 𝔹𝕒𝕥𝕦𝕣𝕖💋

𝑗𝑜𝑖𝑛 𝑡𝒉𝑖𝑠 𝑙𝑖𝑛𝑘 𝑡𝑜 𝑓𝑜𝑙𝑙𝑜𝑤 𝑚𝑦 𝑇𝑖𝑘𝑡𝑜𝑘 𝐴𝑐𝑐𝑜𝑢𝑛𝑡👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت❤🤍❤ 𝐹𝑎𝑡𝒉𝑒𝑟 𝑂𝑓 𝑆𝑜𝑙𝑑𝑖𝑎𝑟𝑠

*🔥𝕋𝕒𝕜𝕦𝕟 𝕂𝕒𝕣𝕤𝕙𝕖🔥*

Abun ya ɗaurewa Jahad kai,irin wannan tambayoyi haka,Anya ba aljanu bane suka shige ta ba,

Babu kowa a babban falon,ko tsoro bata ji haka ta nufi Upstairs,gudu gudu sauri sauri take tattaka staircases ɗin,kaitsaye ta wuce bedroom ɗin Marshal Omar,sallama tayi jin anyi shiru ba'a amsa mata ba,Yasa ta fada cikin falon nashi,babu kowa a falon,da sauri ta nufi bedroom ɗinshi,a bakin kopar ta tsaya tare da Leƙawa cikin ɗakin nashi,A kwance ta same shi yana ta bacci,Ajiyar zuciya ta sauke,Cikin sanɗa ta shiga cikin ɗakin nashi,saɗaf saɗaf ta nufi side drawer dinshi dake a righ hand na gadon,Zuƙunnawa tayi agaban drawer chest din,Ta sanya hannu tana bubbuɗesu a hankali,tare da bincikawa ko zata ga wayar jahad,babu ita aciki,a hasale ta miƙe ta nufi wardrobe din kayan shi,gaba daya duk ta hargitsa kayan amma bata ga wayar ba,tsayawa tayi a tsanake ta shirya mashi kayanshi yadda suke,Bayan ta kammala jiki asanyaye ta nufi hanyar fita daga ɗakin dakatawa ta yi da yin tafiyar,Waiwayowa tayi tana kallon cikon ɗakin,tunani take yi kamar akwai wurin da bata duba ba,can ta tuna da Drawer ɗin dake ɗauke da mirror,da sauri ta juya izuwa gaban mirror ɗin,Janyo gida na farko tayi lokaci guda ta sauke ajiyar zuciya,ganin Wayar Jahad ajiye aciki,

Saukowa downstairs tayi,a main palour ɗin ta zauna saman Sofa tare da kunna wayar don akashe take,Allah yaso babu password a wayar,

Direct ta shiga Gallery ɗin wayar,videos ta gani tare da hotunan dasu Jahad sukayi tare da juna,A hanzarce ta shiga kunna videos ɗin ta ƙura ido tana kallonsu, Cikin motar Junaid shi da Jahad suka ɗauki video ɗin da take kallo,da hannu ɗaya yake ɗaukarsu video,yayin da dayan hannu ya rungumo jahad ajikinshi yana dariya,yana fadin"With My Juliet,My wife to be in sha Allah" Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu rass!rass!a zabure ta miƙe tsaye tana kallon yatsun hannun Junaid dake sanye da diamond ring ɗinsa,ya Aza hannu saman sumar kan jahad Sosai Zoben ya fito mai ɗauke da harafin *J* sai ƙyalli yake yi

Abun yayi matukar ɗaure mata kai,a rude tace"Kai!junaid ya fita da zoben shi aranar!Ya akai zoben kuma ya koma ɗakin Aunty azmee?Taya akai hakan ta faru?Ta yaya zoben shi ya koma ɗakin Aunty azmee..?" tuni zufa ta wanke mata fuskarta,Still bata kawo komai aranta ba,

Jiki na rawa ta nufi bedroom ɗinsu,asaman side drawer ta ɗauki wayarta da ta ajiye,kafin ta ajiye wayar Jahad asaman drawer ɗin,

Gaban mirror ta koma ta zauna saman kujera,Layin Aunty Azeema ta kira,Cikin sa'a wayar ta soma Ringing,'natsuwa tayi tana jiran ta amsa kiran nata,jikinta sae kerma yakeyi,Allah Allah take yi acikin ranta ta samu Aunty azeema ta ɗaga kiran, Almost 15 missed Calls hajiya Azeema bata ɗaga kiran ba,A ƙarshe dole ta haƙura da kiran nata,ba don taso ba,saboda akwai wani muhimman abu da take so ta tambayeta kuma a wurinta ne kaɗai zata iya samun amsoshin tambayoyin da take dasu,

Ajiye wayar tayi gaban mirror ɗin,Kafin ta miƙe tsaye tare da kai idanuwanta ta kalli wall clock ƙarfe 2 na dare,

Dafe kanta tayi saboda matsanancin ciwon kan da ya farmata lokaci guda,a sakamakon tunanin da take ta yi,Zuciyarta tayi nauyi sosai,ga kokwanton da take yi,ga fargabar da take ji,Abubuwa dak sun tarar mata,

Don bala'e a zaune ta kwana,batare da ta runtsa ba,sai wuraren sallar asuba bacci ya ɗauketa can cikin kunnanta taji ana ambaton Sunanta sehrish sehrish,a firgice ta farka,idanuwanta a zare,

Oummansu ta gani atsaye tana kallonta"Sehrish A zaune kika kwana?meyasa baki tafi ɗakin Auntyn taku ba"? Muryarta da alamun bacci bai isheta ba tace"Oumma,bansan bacci ya ɗauke ni ba," "Ki tashi kiyi sallah,Anata kira"ta ƙarasa maganar tare da wuce wa cikin toilet,

Miƙewa tayi dakyar take iya ɗaga ƙafarta saboda baccin da take ji,zuwa ta fara yi ta hau saman gadonsu ta tayar dasu Hosana suka farka tukunna ta sauko,bayan kowa yayi al'wala,Abu ta shimfiɗa masu Sallaya suka kabbara Sallah,a tsanake suke yin sallar,Bayan sun kammala sallar ne sun zauna kowa ya ɗaga hannunshi suna addu'a,Sehrish ta ɗan yi gyaran murya tare da cewa"Oumma,Jahad Hosana,dan Allah ku tayani da addu'a,Akan abunda nake yi,"

"Kada ki damu indai addu'a ce kin samu rishi,"acewar Oummansu,hosana tace"A nawa"? Harara Sehrish ta wurga mata batare da ta tanka mata ba,

Suna cikin yin addu'ar nan,Wayar Sehrish dake ajiye gaban mirror ta soma ruri,A zabure ta miƙe tare da nufar wayarta, "Kira kuma tunda Asuba?Wanene ke kiranki"?tsayawa tayi cak jin abunda oummansu tace,juyawa ta ɗan yi tare da kallonta,ɗan murmushi ta sakar mata"ummm dama Ina tunani ko Aunty Azeema ce ke kira ne" "Okey,ki amsa kiran"da sauri Sehrish ta ƙarasa gaban dressing mirror ta dauki wayar tare da duba screen ɗin,Wani irin farin ciki ne ya lullu6eta ganin kiran Aunty Azeema,

Juyawa ta ɗan yi kamar mara gaskiya ta saci kallon Oummansu dake zaune saman darduma,Hosana harta fara hammar bacci sai cewa takeyi"Wai Oumma addu'ar bata isa haka ba?Dan allah mu koma mu kwanta,murmushi abu tayi tare da kallonta, "kije ki kwanta mana,Wani ya ruƙe maki ƙafafunki,ibadarma baki iya yi da abinci ne duk mun yawanshi sai kin tada shi....."jahad ce tayi maganar tana harararta, Ganin hankalinsu ya koma kan Hosana yasa ta lalla6a ta fuce daga cikin ɗakin,Gudu gudu sauri sauri take tafiya,kaitsaye ta nufi hanyar nan da zata sadaka da wajen gidan,fitowa tayi ta nufi garden don batason kowa yaji ta,

A gefen wata bishiya ta tsaya,tare da duba Screen ɗin wayar missed call har 3 Aunty azeema tayi mata,Danna mata kira Sehrish tayi cikin sa'a Auny Azeema ta ɗaga kiran,

A hanzarce Sehrish ta kara wayar a kunnanta,tun kafin tayi magana Aunty Azeema tace"Sehrish lafiya kuwa?kin tashi hankalina,kawai ina farkawa yin sallar asuba sai naga missed calls ɗinki"

Muryar ta har shaƙewa takeyi saboda tsabar saurin tayi magana"Aunty azeema,babu abunda ke faruwa,lafiya lou nake,Dan Allah wasu tambayoyi ne nakeso nayi maki,Wani Assignment ne aka bamu a school,"

"Okey,Allah yasa nasani" "Aunty azeema,Malamar da ta bamu assignment ɗin tana buƙatar muyi bincike akan wani accident daya faru ne,Sai mu sanar da ita amsar da muka samo,"

Natsuwa hajiya Azeema tayi tana sauraronta, "Saurayi ne da budurwa,suka shirya zuwa shan ice cream,to akan hanyar zuwansu,sai suka dakata agefen titi,ita budurwar ta tsallaka titin zata siya musu ice cream,ta bar saurayinta acikin motar,kwatsam sai ga wata truck ƙatuwa tabi ta kan motarsu,nan take kuma sai wuta ta kama ci da motar,kafin ƴan kwana kwana su ƙaraso wurin,Wutar taci ta cinye,ba'a samu komai ba daga sassan jikin saurayin,

Katseta Aunty azeema tayi"ita malamar taku me takeso ku gano mata ne,"

"Bari na kai maki ƙarshen labarin,shi saurayin ya zama toka,sai ƙarahunan motar aka samu,to abun mamaki kawai sai kuma ga Zobenshi na Diamond an tsince shi a hannun wani dattijo,zoben bai yi komai ba,sai ƙyalli yake yi kamar sabo,to shine take son kowa yayi nazarin labarin ya fada mata abunda yake hasashe"

Abun mamaki tana kai ƙarshen labarin sai taji Aunty azeema na dariya,bubbuga ƙafa Sehrish tayi kamar tana agabanta"Wayyo Allah mommy azeema,meyasa kike dariya,dan Allah ki taimaka ki bani amsar tambayata,"

Tsagaitawa tayi da yin dariyar,sannan tace"Abun mamaki abun Al'ajabi,kawai sai aka tsinci zoben diamond ɗin saurayin a hannun wani,bayan shi mamallakin Zoben ya ƙone ƙurmus,Gaskiya Sehrish ta baku Assignment me wuya,Amma fa ni abunda nake tunani,in har babban Diamond ne kamar irin wanda na ta6a siya ma Junaid,nasan kin ta6a ganinshi a hannunshi mai harafin J,"

Muryarta har kerma takeyi wurin amsa mata"eh naganshi ahannunshi" "Yawwa,so kin ga kalar wannan Diamond ɗin,In har wuta ta ta6a shi baiyin komai,Sai dai akwai wani abunda yake yi idan wutar ta haura mintuna tana ci ajikinshi,Stone ɗin jikinshi zaiyi duhu sosai,kuma ba hakan yana nufin ya mutu bane,Lafiyarshi ƙalau Amma fa wannan duhun da dutsen jikinshi yayi,A nigeria basu da chemical ɗin da zasu gogeshi,Sae dai anan dubai Companyn da nake siyayyar Diamonds ɗin a wurinsu ne kaɗai zasu iya goge wannan baƙin ya dawo yana ƙyalli"

"Amma Aunty Azeema me kike tunani game da Zoben da aka tsinta hannun wani dattijon?Wanda kuma ba'a gabanshi hatsarin ya faru ba,kuma shi saurayin da zoben ya shiga cikin motar Har ya haɗu da hatsarin"ta ƙarasa maganar tana jiran amsarta,don a ƙagare take,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull