Abban sojoji takun karshe complete - Chapter 62
Abban sojoji takun karshe complete Chapter 62: Abban sojoji takun karshe complete Chapter 62. Slowly mommy ta sauke idanuwanta saman katafaren gadon,Mutun…
4,469 words
Slowly mommy ta sauke idanuwanta saman katafaren gadon,Mutun ta gani kwance saman gadon,lullu6e da white bedsheet,ba'a rufe fuskarba,Amma daga inda take bazata iya tantance fuskar wanene ba,kuma daga gani patient ne,Hannun mara lafiyar hada kanula ajiki,da alama Jini aka ƙara mashi,Ga kuma allurorin dake ajiye tare da magunguna gefen side drawer ɗin,
"Ki ƙarasa ciki mana,"harriet ce tayi mata maganar,tana ƙoƙarin ɗaga ƙafarta ta shiga daga ciki,Taji an buɗe kopar toilet ɗin ɗakin,da sauri takai idanuwanta akan mai fitowar,bakowa bane face SGR daga shi sai short ajikinshi,Rass yaji gabanshi ya faɗi lokacin da yayi arba da Mommynsu,Zuba mashi ido Tayi ƙuri tana kallonshi,mamaki ƙarara akan fuskarta,
Duk yasha jinin jikinshi,a ruɗe ya juya zai koma cikin toilet ɗin,Tayi saurin dakatar dashi"Rafayet!"a sukwane ya juyo,duk ya sauya tamkar bashi ba,Jiya zuwa yau har ƴar rama yayi, A hankali ya ambaci sunanta"Mommy"juyawa ta kuma yi tana kallon Sehrish dake kwance saman gadon sai da taga Sgr sannan ta gane cewa itace, "So u are here?meyasa baka sanar damu ba,gaba ɗaya ka tashi hankalinmu rafayet,Duk mun damu akan son sanin halin da kuke ciki' "Mommy,I ave no choice,Nasan babu wanda zai saurareni awannan lokacin shiyasa kawai na yanke shawarar in baro gidan da ita,Omar ma ya juyamun baya,"cikin sanyin murya yayi maganar,kana kallon fuskarshi zaka gane cewa Ba ƙaramin kuka yayi ba,idanuwan duk sun kumbura suntum,hatta la66ansa,Ga Sahun yakushin Sehrish nan a asaman kafaɗarshi da kuma damtsen hannunshi,duk da anyi dressing ɗin ciwukan ' Shigowa ciki Harriet tayi tana kallon kowannansu,kafin ta soma magana"Jiya da suba Alexander ya kirani a waya ya sanar dani cewa Yana da patient zai kawota private hospital ɗina,Sai na bashi shawarar cewa Ya kawota gidana,tunda dama aikina ne,kuma dayawa masu irin matsalarta a cikin gidana nake dubasu,Gaskiya Yarinyar tasha baƙar wahala sosai,don nayi mamaki data kasance araye bata mutu ba,don ma Allah yasa munyi mata aiki cikin gaggawa batare da 6ata lokaci ba,Amma taji jiki sosai,ta zubda jini,don kusan leda biyu na Jini muka ƙara mata,Alex ne ya bata jininshi aka sanya mata,ni tun da nake duba patient irinta banta6a zubda kwallata ba,Sai akanta Mun sha kuka,daga ni harshi,yarinyar ce ga ƙananun shekaru......."cikin harshen spanish take maganar idanuwanta cike tab da kwalla,Mommy kuwa tuni ta fashe da kuka,dakyar ta iya matsawa gefen gadon da Sehrish take kwance ta sanya hannu ta yaye bedsheet din,Riga ce ajikinta blue colour dai dai guiwarta rigar ta tsaya,duk jikinta ya bushe,kamar matacciya haka take yin bacci,
Yatsun hannunta na kerma ta ɗaurasu asaman fuskar sehrish,tsananin tausayinta ne ya kamata,Juyawa tayi wurin da Sgr yake tsaye ya duƙar da kanshi kasa,duk jikinshi yayi sanyi,Ya karaya sosai, "Rafayet yanzu ka kyauta abunda ka aikata mata"?idanuwanta jawur take kallonshi, "What i neva expect from u,kai da kanka kake hukunta masu aikata laifi makamancin wannan amma yau kaida kanka kayiwa ƴar uwarka ta jininka,Why rafayet?ko laifi tayi maka ta cancanci wannan hukuncin?balle kuma batayi maka laifin komai ba!saboda kawai sun 6ata maka rai sai ka huce haushinka akanta?Yanzu kalli halin da ka jefata!Ka ƙiyasta irin raɗaɗin azabar da take ji a lokacin da kake kusantarta da kuma wannan lokacin da take halin jinya......'
Tuni idanuwanshi sun cicciko tab da kwalla,Sam ya kasa ɗagowa su haɗa ido da ita, "Pls Alex,bai kamata muna tuna abunda ya wuce ba,Wannan abu ya riga daya faru,Sai dai kawai mubi ta da addu'a,Allah ya kawo mata sauki,very soon zata wartsake," Cike da takaici Mommy tace"don bakisan Halin da iyayen yarinyar nan suke ciki bane,sun damu sosai akan rashin ƴarsu,ni banma san me zance masu ba idan suka ganta,"dakatawa ta ɗan yi da yin maganar tana share hawayen dake zarya akan fuskarta, "Baikamata asanar dasu ba,Don ta yanzu,Gaskiya in suka ganta a halin da take ciki yanzu zasu shiga matsananciyar damuwa,saboda har yanzu bata dawo cikin hayyacinta ba,da zarar ta farka sai ta dinga sambatu akan abunda Alex yayi mata," Ajiyar zuciya mommy ta ɗan sauke before tace"What's the solution now?zata kai tsawon wani lokaci kafin ta dawo hayyacinta," "Koda wani lokaci zata iya dawowa cikin hayyacinta,Yanzu ma baccin nan da kikaga tanayi munyi mata allurar bacci ne,abunda za'ae yanzu shine kada ki sanar da kowa inda suke,Har sai ta dawo cikin hayyacinta,zan sanar dake,Sai asan yadda za'ae a mayar da ita can gidan taci gaba da jinya,ina ga kamar hakan zaifi," Mommy tace"Hakan yayi,thank u so much Harriet,bansan da wasu kalmomi zanyi amfani wurin gode maki ba,kin taimakemu sosai,Yanzu zan koma gida kada su nemi ni,"ta ƙarasa maganar tare da mikewa tsaye, Rungume juna suka kumayi ita da harriet kafin Ta mayar da idanuwanta kan Sgr, Tausayinshi ne ya kamata,a hankali ta furta sunanshi"Rafayet" ɗagowa yayi da idanuwanshi ya kalleta, "Don't u need me"? Yana jin haka jiki asanyaye ya nufeta,sosai ta rungumeshi ajikinta, "Mommy i need ur prayer,am in serious dilemma,bani da wani sauran kwanciyar hankali daya rage mun,Mommy i ave regretted wlh,Nasan Uncle da Daddy fushi suke dani" Cikin sigar lallashi ta sanya hannunta abayanshi tana ɗan bubbugashi tace"Allah ya bata lafiya,nasan zaka bata kyakkyawar kulawa,dan Allah rafayet ka rage wannan zafin zuciyar naka,baida amfani,ni nasan cewa kana son yarinyar nan,ka mika wuya kawai ka nuna masu cewa kana sonta,Zaka tafi da ita a matsayin matarka,Shine fa kawai abunda suke buƙata a wurinka,simple and short amma ka kasa yi masu,har sai da ka illata masu yarinya,
Sun jima suna magana dashi,Kafin tayi masu sallama ta fuce daga gidan,
*Boss Bature*
Tun bayan da Mommy ta koma gidan bata sanarwa kowa game da inda rafayet yake ba,kamar yadda suka tsara,duk da tashiga damuwa sosai akan halin da Abusufyan yake ciki,Shi da Omar da kuma Abba,ko abincin kirki basu ci,Bacci kuwa tuni ya ƙauracewa idanuwansu saboda damuwa,Yanzu kowa na cikin gidan Ya gane cewa Mutun biyu basa nan,Sgr da Sehrish,Amma mommy bata bari sun gano wani abu ba,Da zarar sun soma tambayarsu sai ta sanar dasu cewa Sunyi tafiya ita da Sgr,wannan dalilin ne yasa basu tashi hankalinsu sosai ba,,yau a ƙalla kusan 2 weeks kenan babu su babu alamarsu,
Wuraren ƙarfe 1:30 na dare,Sgr na rungume da ita ajikinshi,dayake shi yake kula da ita,koda yaushe yana manne da ita,tamkar jinjira haka yake riritata,jikinta yayi sauƙi sosai sai dai abunda ba'a rasa ba,Saboda har yanzu bata ida dawowa hayyacinta ba,can cikin bacci ya dinga jin sambatunta"Ya rafayet bazan iya jurewa ba,mutuwa zanyi,Wayyo Allah na,Daddy kazo ka taimaki rayuwata,Ya rafayet baisona,Kashe ni yake so yayi,ƙoƙarin ƙwace jikinta take yi daga nashi,Da sauri ya zura hannunshi ya ta6o bedside lamp ya kunnata,Haske ya ɗan kawo,
Slowly ya mayar da idanuwanshi kan fuskarta,har sai da gabanshi ya faɗi ganin yadda ta zazzare idanuwanta,suna haɗa ido dashi,A gigice ta soma ƙoƙarin zame kanta daga ruƙon da yayi mata,
Yunƙurawa yayi tare da miƙewa zaune Ya taimaka mata ta zauna,Ya sanya mata pillow daga bayanta, "Are u feeling hungry?"yayi tambayar yana kallonta,shiru bata bashi amsa ba,Sai dai kallon da take binshi dashi,Saukowa yayi daga saman gadon Ya nufi fridge ɗin ɗakin Ya ɗauko mata fresh milk mai sanyi,tare da ruwa,
Hawa saman gadon yayi dab da ita suna fuskantar juna,buɗe murfin robar yayi tare da kafa mata ita saitin bakinta,Buɗe baki tayi sosai tasha madarar,kusan duka ta shanye,Magungunanta ya soma bata tana sha,har ta kammala,
Sai faman lumshe idanuwanta takeyi da alama baccin bai isheta ba, Nuna mata fuskarshi yayi"Look at my face,Kin gane ni kuwa," A hankali ta ware kyawawan idanuwanta akan fuskarshi,ta jima tana kallonshi batare data tanka mashi ba,hannu yasa tare da janyota jikinshi,ya zaunar da ita saman laps ɗinshi,ya kasance kanta yana asaman ƙirjinshi,a hankali ya ɗaura hannunshi asaman sumar kanta,shafa sumar kan nata yaci gaba dayi,kafin ya duƙo da fuskarshi zuwa gefen tata,tsinin hancinshi yana gogar fatar wuyanta, Calmly ya soma magana"I made a mistake,but I still have time to correct it,idan nace kiyi haƙuri nasan nacuce ki.......'ya ɗan dakata da yin maganar,baisan ko tana fahimtarshi ba, "Amma ashirye nake dana kar6i koma wani irin hukuncine daga gareki,"cikin sanyin murya ya ƙarasa maganar,shi kaɗai yasan yadda yake ji acikin zuciyarshi,still bata nuna mashi wata alama da zata nuna cewa tana acikin hayyacinta,tunda ta kwantar da kanta saman wide chest ɗinshi,bata ƙara motsawa ba,ta lumshe idanuwanta, "Reesh,"ya kuma ambaton sunanta,bata amsa mashi ba,sai dai motsin hannunta dayaji abayanshi,dayake ta zagayo dasu, "Can't u talk to me?i know you're hearing me," Tabbas kuwa tana jinshi,duk abunda yake cewa kaf acikin kunnanta,domin kuwa ta dawo hayyacinta,a ƙule take dashi,don taci alwashin sai yabata takardar sakinta,bazata ta6a cigaba da rayuwa dashi ba,ta tsorata da irin rashin imanin daya gwada mata,Yanzu ta daina kallonshi a matsayin mutun Dodo ya koma mata,a zaunan da suke bacci ya ɗauketa,shima ya fara gyangyaɗi,A hankali ya kwantar da ita,kafin ya kwanta tare da janyota ya ƙanƙameta jikinshi,
A washe garin ranar wuraren ƙarfe 7 na safe,Dr harriet ta kira Mommy awaya take sanar da ita game da cigaban da akasamu na Lafiyar Sehrish,ba ƙaramin daɗi taji ba,suna cikin yin wayar nan,tajiyo knocking daga waje,Da sauri tayi rejecting kiran,Ta juya bakin ƙopar ɗakin ta buɗe, Omar ta gani atsaye,duk ya rame kamarshi ya aikata laifin, "Ina kwana Mommy,". "Lafiya lou,"ta amsa mashi fuskarta asake, "Mommy still Rafayet bai tuntu6eki ba"? Shiru tayi tana tunanin kodai ta faɗa mashi inda suke,ganin yadda ya shiga damuwa over, "Omar,i won't hide it for u,Nasan inda rafayet yake,bansanar ma kowa bane saboda gudun halin da ƴan uwanta zasu shiga idan suka ganta a halin da take ciki na jinya," Tunda ta fara magana Omar,Ya zuba mata ido yana kallonta Ya rasa me zaiyi farin ciki ko baƙin ciki,Duk irin halin da suke ciki na neman Sgr ashe ta sani? Daƙyar ya iya buɗe baki yace"A ina suke mommy," "Banaso kowa ya sani Omar,nafiso saita samu sauƙi sosai,Yadda hankalin Abusufyan zai kwanta," Jinjina kai yayi"bazan fada masu ba," "Yana gidan Dr harriet,Nasan kasanta," Tunkafin takai ƙarshen Maganar,Omar yayi hanzarin juyawa a gaggauce Ya fuce daga cikin gidan,Mota ya shiga,Major yajasu da gudun gaske zuwa gidan,dan bazai manta kwatancen gidan ba,tunda sun ta6a zuwa a lokacin baya,
Yana yin parking ɗin motar,tunkafin Major ya zagayo ya buɗe mashi ƙopa,Yasa hannu ya ture murfin motar,kaitsaye ya nufi cikin gidan,A buɗe ya samu ƙopar da zata sadaka da palourn gidan,ko sallama baiyi ba ya faɗa cikin gidan,A saman dining ya taras da Harriet tare da twins ɗinta matasan ƴan mata su biyu suna yin breakfast,Tana ganin shi ta soma sakin murmushi, "Omar yau kaine a gidana,"bai amsa mata tambayarta ba,Sai cewa yayi"Ina Rafayet yake,"?jim ta ɗanyi tana kallonshi Sam babu natsuwa atattare dashi,dama tayi mamakin ganinshi, Nuna mashi upstairs tayi"Suna acan sama,"ko kwatancen ɗakin bai tsaya tayi mashi ba,Da gudun gaske ya haye stairs ɗin,cikin sa'a ya gano ɗakin,Yana turo ƙopar Ya samu Sehrish zaune ta jingina kanta jikin headboard na gadon,Duk atakure take,
"Sister,"ya ambaci sunanta da wata irin kasalalliyar murya, Firgigit sehrish ta ware idanuwanta akanshi,tana ganinshi wani irin farin ciki ya lullu6eta,"Ya Omar",Da sauri ya ƙarasa gefen gadon ya zauna,Zuba mata ido yayi yana kallon Canzawar da tayi,Ta rame sosai takuma yi haske,
"Ya jikin naki"?bata amsa mashi ba,saboda kukan daya ciyota,Sosai ta fashe mashi da kuka,ruƙo hannayenshi tayi"Ya Omar dan Allah ka tafi dani gida,Wlh banjin daɗin zama anan,nafison na ganni cikin ƴan uwana" Tsananin tausayinta ne ya kamashi,tuni hawaye sun wanke mashi fuskarshi, "Ya Omar wlh ka tafi dani gida tunkafin Ya rafayet Ya fito,don bazai ta6a bari ka tafi dani ba,Ni kuma natsani zama a gidan nan,duk a ƙuntace nake babu daɗi," "Yana ina rafayet ɗin"? "Ya shiga wanka" Jinjina kanshi ya ɗanyi,kafin yace"Zaki iya tafiya," Girgiza kai tayi"a'a bazan iyaba",don tasan in dae da kafafunta zata taka to kuwa har sgr ya fito ya gansu, Batare da 6ata Lokaci ba Omar ya ɗauketa saman kafadarshi ya sauko downstairs da ita,Dr harriet na ganinshi da ita,Hankalinta ya tashi aruɗe ta tare shi tana faɗin"Omar where are u going with her?Rafayet ne ya baka izni?Ko alex ce tace kazo ka ɗauketa, Tunkafin Omar yayi magana Sehrish tace"Ya Omar kada ka saurareta,wlh in ka barni acikin gidan nan Poison zansha in mutu,"yana jin haka ya ƙara harzuka, Ko kallon Harriet baiyi ba Ya fuce daga falon,Major ya bude mashi mota ya shigar da sehrish yana cewa"nasan idan ya fito yaji cewa Mun tafi da ita,dole ya dawo gida,"
Da gudun gaske Motar major ta fuce daga cikin gidan,Sehrish sai faman sauke ajiyar zuciya take yi,baiwar Allah daga ita sai wannan rigar mai kama da uniform,Ƴan ƙafafuwan ko takalma babu,Kanta ko mayafi babu sai dai gashin kanta dake a cukurkuɗe,duk ta ƙosa taga Mahaifiyarta da mahaifinta,da kuma ƴan uwanta,Rafayet ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,ya ƙumsa mata baƙin cikin da bazata ta6a mantawa ba,Ya sanya mata ƙiyayyarsa acikin zuciyarta,
A hankali Major Ya shigar da motar ta cikin babban gate ɗin gidan,Bayan yayi parking ɗinta,Ya fito da sauri Ya buɗe mashi Mota,Saukowa marshal yayi tare da zura hannayenshi Ya kinkimo Sehrish asaman kafaɗarshi, "Thank u Major"Yana ambaton hakan ya wuce da ita cikin gidan,A lokacin babu kowa a palour sai dai mutanan dake kitchen suna shirya breakfast,Yana yin sallama hankalinsu Ya dawo kan Omar dayake suna hangenshi daga inda yake,Koda abu tayi arba da matashiyar dake kwance asaman kafaɗarshi,nan take taji aranta cewa Sehrish ce,Da gudun gaske ta fito daga kitchen ɗin,Hajiya azeema tare da Mommy suka biyo bayanta,Ai koda Mommy taganshi ɗauke da sehrish sai da gabanta Ya faɗi,Har warning tayi mashi akan kar ya sanarwa kowa inda ta suke,Sai gashi ɗungurugum Ya ɗauko ta,
Aruɗe abu take kallonta"Sehrish ce?Meya faru da ita"?tayi tambayar tana ƙare mata kallo,har lokacin bai sauketa daga kan faɗarshi ba, Hajiya azeema kuwa Alhamdulillah ta soma faɗi,fuskarta ɗauke da murmushi,duk da ta damuwa sosai ganin yadda ta rame, "Dan Allah ku faɗamun meya faru da ita,Meyasa nake ganinta haka?kamar bata da lafiya," Omar na ƙoƙarin Yin Magana,Sehrish Tace"Oumma,Lafiyata qalou,Yaya Omar ka kaini ɗaki inaso inga ƴan uwana," Wucewa bedroom ɗinsu yayi,da sauri suka bi bayanshi,jikin abu duk yayi sanyi,koba a fada mata ba tasan cewa babu lafiya atattare da ita,tunda har bazata iya tafiya da ƙafafuwanta ba,Suna ƙarasowa kopar ɗakin,Oumma ta buɗe mashi Ya shiga da ita,A lokacin Jahad na zaune gefen gadon Tana karatun al'qur'ani,Hosana kuma ta kabbara sallah,Don bata samu yin sallar a lokacinta ba,
A firgice Jahad ta miƙe tana kallon Ya Omar dake ɗauke da Sehrish,da ƙarfi ta ambaci sunanta Sehrish!Ae Hosana najin an kira sunan Sehrish Ta katse sallar da take yi dama tunda suka shigo take ƴan waige waige,A hankali Omar ya zaunar da ita samam gadon,Ya sanya mata pillow a bayanta,ɗaya bayan ɗaya take bin fuskokinsu da kallo kamar yadda suma suke binta da kallon ƙurulla,Hosana sai tsalle take yi tana ambaton sunanta saboda murna,
Fashewa Sehrish tayi da matsanancin kuka,Da sauri ta sanya tafin hannunta asaman fuskarta,tsananin tausayinta ne ya kamasu,da sauri Oumma ta zauna gefen gadon"Sehrish meya faru dake ne?na damu sosai akan rashin ganinki,Har Abusufyan na tambaya yake sanar dani cewa kunyi tafiya keda babban yayanku,"kasa buɗe baki sehrish tayi,saboda ƙululun baƙin cikin da ya tokare mata makoshinta,A duk lokacin data tuna abunda Sgr yayi mata, Zuƙunnowa Hajiya azeema tayi saitin fuskarta"Pls stop crying,Wlh nashiga damuwa sosai akan rashinki,banji daɗin abunda ya faru ba,Amma kiyi haƙuri haka Allah ya ƙaddara maki,Yanzu dai ki sassauta kukan nan naki,kodan saboda mahaifiyarki zata shiga damuwa sosai"tayi maganar ne ta yadda abu bazata iya jiyota ba, "Koda sun tambayeki meyake damunki,Kice baki da lafiya zazza6ine ya kamaki,"cikin shessheƙar kuka Sehrish ta ɗaga mata kai alamar zatayi yadda tace,Miƙewa Hajiya azeema ta yi,Jahad ta zauna saman side drawer na gadon tana tambayarta Lafiya, Cikin shessheƙar kuka tace"Bani da lafiya ne,Amma jikin da sauƙi,kawai nayi kewarku ne sosai," Kallonta kawai Jahad take yi ba don ta yadda da abunda tace ba, "Tana buƙatar hutu,Bai kamata mu takura mata da tambayoyi ba,idan ta huta sai muyi magana da ita,"acewar Hajiya Azeema,daga haka babu wanda ya ƙara tambayarta, Matsawa abu tayi kusa da ita,ta sanya hannunta ta rungumota jikinta,wani irin zafi dama kullum cikin zazza6in take, "Allah ya baki lafiya Sehrish," "Ameen Oumma,"_
Mommy kuwa bayan fitar Omar da sauri tabi bayanshi, "Why omar meyasa zaka ɗaukota?haka mukayi dakai"? Juyawo yayi fuskarshi sam babu annuri acikinta,. "Haba mommy,don me zan barta acan?An ƙuntata rayuwar yarinyar nan sosai,Na farko an cutar da ita,na biyu kuma an kaita wani wuri inda batasan kowa ba,Hakanan ya rabata da kowa nata,lokacin dana je kuka ta dinga yi mun tana ruƙe hannuwana akan in tafi da ita gida kota kashe kanta,Shiyasa na yanke shawarar ɗaukota,Tunda jikin nata da sauƙi," "Shikenan Omar,Nima nayi tunanin a dawo da ita gidan,Kawai ina fargabar halin da Zasu shiga ne idan suka ganta," "Kada ki damu Mommy,rashin ganinta a kusa dasu shiya fi haɗari,Amma in tana atare dasu,To da sauƙi,ita kanta tafi son cikin ƴan uwanta," Jinjina kai Mommy tayi"Wannan haka yake,nagode sosai Omar,"ta ƙarasa maganar tare da juyawa Ta nufi kitchen,shi kuma Ya wuce ɗakin Abusufyan,Hannu yasa yana kwankwasa kopar,A lokacin Abusufyan yana ta faman zarya cikin ɗakin,Damuwa duk ta isheshi,jin knocking ɗin ƙopar yasa shi yin hanzarin juyawa yaje ya buɗe mashi, Tunda yaga fuskar Omar awashe ranshi ya bashi cewa Akwai labari me daɗi,. Muryarshi na kerma yace"Omar,An gano inda suke,". Fuskar Omar ɗauke da murmushi yace"yanzu haka Sehrish tana aɗakinsu,"tunkan yakai ƙarshen maganar Abusufyan Ya fuce da sauri har yana tuntu6e,
Suna zaune saman gadon sun zagayeta,Sai gashi Ya banko ƙopar dakin Yana ambaton sunanta"Sehrish!"yadda kasan makoshinshi zai 6allo, "Daddy,"ta amsa mashi fuskarta ɗauke da murmushi,Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarshi,Da sauri ya ƙarasa suka matsa mashi,Ya hau saman gadon Ya rungumota jikinshi,Wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya Ya sauke,Wasu irin zafafan hawaye ne suka wanke mashi fuskarshi, "Daughter,Am sorry for everything,i ave regretted already,duk nine silar halin da kika tsinci kanki,"sosai yayi tighting ɗinta ajikinshi,tamkar zai mayar da ita cikin cikinshi, tamkar raɗa haka yake yi mata maganar don kar suji abunda yake cewa,tunda bakowa yasan ainihin abunda ya faru da ita ba, Cikin shessheƙar tace"Daddy kamar Bazan rayu ba,Nasha wahala,Lokacin mutuwa nane kawai baiyi ba,' "Nasani,wlh naji ajikina Daughter,danasan hakan zata faru da ban tursasa mashi akan ya sakeki ba,da duk hakan bata faru ba,"Sai lokacin Sehrish ta gane dalilin dayasa Sgr yayi mata hakan, Janyeta yayi daga jikinshi,tare da sanya hannunshi asaman fuskarta yana share mata hawayenta yace"Ina babban yayan naku?nayi tunanin atare dashi zaku dawo,' Girgiza kai ta ɗan yi"A'a,Sai zuwa anjima zai dawo,Ya Omar ne ya kawo ni,Na matsa mashi ne akan inaso na dawo gida," sunyi pretending ne don kada Oummansu ta gano gaskiyar abunda Ya faru da ita, "Allah ya baki Lafiya Daughter," "Ameen daddy," Turo kopar ɗakin akayi,Mommy ce ta shigo hannunta ruke da plate mai ɗauke da farfesun nama,da zafi zafinshi sai ƙamshi yake yi,
Ƙarasowa ciki tayi fuskarta a ɗan sake tace"Ya jikin naki," Batare da sehrish ta kalleta ba ta amsata"da sauki Mommy," Miƙa ma Abu plate ɗin tayi"Ga wannan nasan zata buƙace shi,Akwai tea dana haɗa mata,bari naje na ɗauko mata shi," Hannu bibbiyu Oumma tasa ta kar6i plate ɗin"Mun gode sosai," "Kada ki damu,duk yiwa kaine"takai ƙarshen maganar,tare da juyawa a hanzarce tabar bedroom ɗin,Abusufyan ya lura da sehrish,tunda Mommy ta shigo bata kalli fuskarta ba,tayi hakanne saboda ta tsani ganin fuskar Sgr,Ita kuma Mommy dashi take kama shiyasa taƙi kallonta, Shafa fuskarta yayi"Daughter,"murmushi ta ɗan saki batare data ɗago da idanuwanta ba,Sun cika tab da kwalla, Juyawa yayi tare da kallon Abu dake tsaye hannunta ruƙe da plate,. Kar6ar plate ɗin yayi daga hannunta, Ruƙo hannun Oumma Mommy azeema tayi"mu koma kitchen munbar Aiki acan,In sha Allah zata samu sauƙi,"atare suka fuce daga ɗakin, Ya rage daga Abusufyan Sai Hosana da Jahad dake kewaye da ita, jim kaɗan Mommy ta dawo hannunta ɗauke da Cup wanda ta haɗa mata Kakkauran tea acikinsa, Asaman side drawer ta ajiye mata Cup ɗin, Kafin ta juya tabar dakin, "Rishi wai ina kika shiga ne?Kin tafi kin barmu da tunani,"Hosana ce tayi maganar fuskarta a yamutse, Jahad tace"Dan Allah kibarta ta huta,Ba kiga bata da lafiya ba,Sannu Sehrish Allah ya baki Lafiya,muryarta ƙasa ƙasa ta amsa mata da Ameen, Abusufyan da kanshi Ya zauna yana bata farfesun abakinta,Cike da kulawa,ba ƙaramin daɗinshi taji ba,sosai tasha,kusan duka ta shanye duk da hosana ta tsoma masu hannu,Ta dinga ɗaukar naman tana turawa abakinta wai ae itama bata ci ba,
Bayan ta kammala Ya ajiye plate ɗin Ya dauki cup of tea ɗin da mommy ta ajiye mata,A baki ya kafa mata shi,Sosai ta shiga kur6arshi abakinta, "Amma nima ka bani tea ɗin abaki"? Hosana ce tayi maganar,tana tura mashi bakinta,Hakan ba ƙaramin dariya yaso ya basu ba,murmushi sehrish ta ɗan saki tana kallonta, "Daddy ka bata tasha," Cike da zolaya Abusufyan yace"Na mara lafiya ne,Hosana kiyi hakuri wannan na sehrish ne,bata baki tausayi ba Kalli fa ki gani duk ta rame," A shagwa6e Hosana ta langwa6ar da kanta,tasa hannu tana nuna mashi ƙashin wuyanta, "Daddy ae nima banda Lafiya,Kalli ka gani," Kallon wuyanta yayi acike yake babu wani ƙashin daya leƙo, Harara Jahad ta ɗan watsa mata"Saboda kofin tea zaki jama kanki ciwo,Tirr da wannan halin naki,Shegen Ci kamar gara" Guntun tsoki Hosana taja"eh ɗin ina ruwanki,Ƴar shigar shugula,ba'a kasa dake ba,kin tsomo mana baki,". Dariya sosai Abusufyan yayi yana kallonsu,ita kanta Sehrish murmushi ne kwance akan fuskarta,Hankalinta Ya kwanta sosai,gata ga iyayenta ga kuma ƴan uwanta,
Kwankwasa ƙopar ɗakin akayi,Abusufyan yace"Wanene"? "Nice Amrish," "Okey shigo daga ciki,"turo ƙopar ɗakin tayi,jikinta sanye da hijabi dai dai guiwa,Waro ido waje tayi ganin Sehrish Da ƙarfi ta ambaci sunanta"SEHRISH" Wani irin farin ciki ne ya lullu6ete,har ta manta da abusufyan dake zaune,Da gudu ta ƙarasa gefen gadon,Ta haura sama ta rungumota ajikinta, "Sehrish ina kika shiga ne?ina ta nemanki?Oumma tace mun kunyi tafiya keda Babban yayanku," Fuskar Sehrish ɗauke da murmushi tace"Am sorry Amrish,Nayi laifi ban sanar dake ba,Tafiyarce ban shirya mata ba,ni kaina bansan da ita ba," ɗagowa amrish tayi daga jikinta ta sanya tafin hannayenta ta tallabo fuskar Sehrish"Duk kin rame,Baki lafiya ne " "Zazza6i nake yi," Gyaran murya Abusufyan yayi mata,Da sauri Amrish ta sauko daga saman gadon ta zuƙunna tana gaishe shi"Ina kwana daddy,An tashi lafiya,Ya mai jiki," Murmushi Abusufyan ya sakar mata tare da cewa"Lafiya Lou,yaushe rabon dana sanyaki acikin idanuwana,bakyason zuwa kina gaishe ni ko"? Sunnar dakai ƙasa tayi cike da jin kunyarshi tace"A'a,inason zuwa," "Baki ɗaukeni a matsayin mahaifinki bane"? Da sauri tace"Na ɗauke ka," "To meyasa bakya sakin jiki dani ne"? Shiru tayi batace Komai ba, "Daga yanzu inaso ki saki jikinki dani,Dake dasu Sehrish duk ɗaya kuke a wurina,duk wani abu da kike buƙata na rayuwa,ki sanar dani ni kuma zanyi maki shi," "Nagode sosai Daddy,"ta ambaci hakan tare da miƙewa, "Sehrish wayarki na ɗaki,bari na ɗauko maki ita," Da sauri ta juya ta fuce daga ɗakin,Kallonta Abusufyan yayi, "U need a rest,ki kwanta ki huta,Zuwa anjima zan sake zuwa dubaki,Yanzu hankalina ya kwanta,ashe da rabon yau inyi bacci hada minshari don tunda kuka tafi wlh ban runtsawa sai dae bacci 6arawo ya dan dauke ni Daughter," Murmushi ta ɗan saki,mikewa yayi tare da kallonsu Jahad yace"Ku kulamun da ita pls," Atare suka amsa mashi da toh,kafin ya bude kopar ɗakin ya fuce,
Baijima da fita ba,Amrish ta shigo ɗakin hannunta ruƙe da wayar Sehrish,zama gefen gadon tayi tare da miƙa mata wayar,hannu tasa ta kar6i wayar, "Ya jikin naki"? "Am feeling better now,nayi missing dinku sosai," Fuskarta ɗauke da murmushi tace"Nima nayi missing ɗinki sosai,Kullum saina tambayi Oumma yaushe zaki dawo," "Allah sarki,nagode sosai da nuna damuwarku akaina,"
Bayan fitar Abusufyan kaitsaye ya nufi ɗakin Ammi,A lokacin khadija da nafeesat suna acikin ɗakinta,Suna tattaunawa game da bikin da za'ayi,
Da sallama ya shiga ɗakin,atare suka amsa mashi,da sauri suka soma gaisar dashi,fuskarshi asake ya amsa masu,Suna zaune ƙasa sun lankwashe kafafunsu,Ammi kuma na zaune gefen gadonta, Agabanta ya zuƙunna"Ina kwana Ammi,kun tashi lafiya," "Lafiya lou,Autana,Ina fata kaima haka," "Alhamdulillah"ya amsa mata, "Da alama yau akwai labari me daɗi akan fuskarka,murmushi ya saki tare dacewa"Ammi Sehrish ta dawo,Yanzu haka daga ɗakinsu nake," "Masha Allah,Kai amma naji daɗi sosai wlh,Amma waye ya kawota? "Omar ne ya ɗaukota," "Amma ya lafiyar jikin nata" "Da sauki ammi," Miƙewa tayi hannunta ruƙe da sandarta,kallonsu Nafisat tayi"yanzu zan dawo,Zanje na duba jikin jikata ne," Mikewa sukayi atare"Muma zamu je ammi," Murmushi tasaki"shikenan bismilla,"Abusufyan Ya shiga gaba suka bi bayanshi,har zuwa ɗakin Su Sehrish, Ba ƙaramin farin ciki ammi tayi ba,Ganin yadda sehrish take ta faman sakin murmushi,tashi Amrish tayi daga gefen gadon,Ammi ta sauna suna fuskantar juna ita da sehrish, Atare suka haɗa baki suna gaishe da ita,Bayan ta amsa masu tace"Ya jikin naki"? "Naji sauki," Jinjina kai ammi tayi"Alhamdulillah mun godewa Allah,Haka mukeso,"Takai ƙarshen maganar tare da kallonsu Khadija dake atsaye,Ga ƴar uwarku nan,ɗaya daga cikin ƴan ukun Abusufyan ne,Bata da lafiya ne,"
Har suna hada baki wurin yi mata Ya jiki,fuskarta asake ta amsa masu,kafin ta soma gabatar masu dasu, "Jikokin modibbo ne,Ƴa'ƴan ƙanwar Mahaifiyarsu Omar,sannan kuma nan bada jimawa ba,Zasu zama surukan Abba,ta 6angaren Adam Da Osman"
Farin ciki ne ya lullu6esu,Ammi taci gaba da cewa"su kuma waɗannan zasu bi sahunku suma,Wato zasu Zama surukan Abba,Ga Sehrish nan Amaryar Babban Yayansu,ɗan wurin Fatima," tunda ammi ta ambaci hakan ran Sehrish ya 6aci sosai,tuni ta ɗaure fuskarta,Sam babu wanda ya lura da ita, "Bayan ita kuma Sai Jahad,Amaryar shalelen Abba wato Junaid,"da sauri jahad Ta kife kanta saman katifar saboda kunya, "Ita kuma wannan,Mai hankalin cikinsu,Amaryar Omar ce in sha Allah," Fashewa Hosana tayi da dariya,kowa najin kunya banda ita, "Inason nayi magana da ita, ku ɗan bamu wuri,"
Amsa mata suka yi da toh,Gaba ɗaya suka fuce daga dakin,A waje suka tsaya suna fira atsakaninsu,Amrish dai tayi shiru saboda ita batasan matsayarta ba,Amma taso ace hada ita za'a ɗaurama aure,Itama ta zama ɗaya daga cikin amaren gidan,
Bayan fitarsu Ammi ta zauna tayi mata nasiha sosai,ta kuma nuna mata 6acin ranta akan abunda Sgr yayi mata,A ƙarshe ta ruƙe hannayenta"Bazanso abunda zai cutar dake ba,Dama jiran dawowarki nake yi,Saboda inaso inji ra'ayinki game dashi,Kina son Cigaba da rayuwa dashi,Ko kuwa A'a," kamar jira takeyi da sauri tace"Banaso ammi,dan Allah ku rabani dashi,wlh bazan iya rayuwa dashi ba,Ni dai kawai asanyashi Ya sake ni,"hada hawayenta, Shiru ammi ta ɗan yi tana kallonta,Kafin tace"Amma fa yana sonki sosai,Wanda silar hakan ne yajawo har ya aikata maki hakan,Saboda anyi ƙoƙarin rabashi dake," Cikin shessheƙar tace"Nidai bana sonshi ammi,wlh yafita araina," Ajiyar zuciya ammi ta sauke, "Shikenan,In sha Allah zan shiga tsakaninki dashi"
WANNAN KENAN!
*masu yi mun ya jiki nagode sosai da irin kulawarku,kuma in sha Allah kamar yadda nace very soon zan kammala maku littafi in Allah ya yarda,koda ba lafiya indai yatsun hannuna na motsi zan daure inyi ne,Don in gama akan lokaci,kafin watan ramadan,*Ga mai buƙatar karanta Littafin Abban Sojoji from Book one to 3,Yayi mun magana ta whatsapp 08103884440* [3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Father of soldiers*
*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*
Story And written By
*Hafsat Bature*
Not edited