Kenza eBookz

Abban sojoji takun karshe complete - Chapter 66

Abban sojoji takun karshe complete - Chapter 66

Abban sojoji takun karshe complete Chapter 66: Abban sojoji takun karshe complete Chapter 66. Hand dryer ta fara ɗaukowa,ta jona ajikin socket,busar da…

4,159 words

Hand dryer ta fara ɗaukowa,ta jona ajikin socket,busar da gashin kanta tayi,bayan ta kammala ta kashe ta,jikinta ta soma gyarawa,ko'ina ta shafe shi da mai,

Turo ƙopar ɗakin Hajiya azeema tayi da sallama abakinta ta shigo,Sehrish ta amsa mata,fuskarta adan sake ta amsa mata, 'Ina yini aunty azeema," "Lafiya Lou daughter,Ya jikin naki"? "Alhamdulillah,ina samun sauƙi sosai," "Naga gashin kanki,Yayi tsayi sosai,ga yawa,yakamata ku shirya in kaiku wurin Saloon dake da ƴan uwanki,amma fa idan kinji sauki,"_ "Ae nama ji sauƙi,warwarewa kawai zan ƙarasa yi," Hararar wasa Azeema tayi mata"A haka din,kina ɗan gyasa ƙafa shine kinji sauki? Dariya sehrish ta ɗanyi"bari nayi maki make up,"acewar hajiya azeema, Ba don taso ba,Saboda yanzu bata buƙatar yin kwalliya,tunda wanda take yi dominshi,Rabuwa zasuyi, Within mins hajiya azeema tayi mata make up,fuskar ta fito sosai,jan bakin data shafa mata red ne mai ƙyalli ajikinshi,daga sama ta shafa mata lip gloss,fuskar ta lindu da foundation mai kyan gaske,ga eye brows ɗinta natural amma ta ƙara mata da brown eye pencil, "Masha Allah my daughter,Allah yayi maki kyau,ki godewa Allah,Son kowa ƙin wanda Ya rasa," Murmushi sehrish ta ɗan saki, "Bari na ɗauko maki,kayan da zaki sanya,"ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta nufi wardrobe ɗin kayanta, Can ta hango wata Atampa,Golden glitter,Brown Colour,Riga da skirt ne,ɗinkin ya haɗu over, Juyawa tayi tare da kallon Sehrish"Har na hangoki acikin wannan," "Sunyi kyau sosai,Amma dare yayi,koda na sanyasu,zan cirene in na tashi kwanciya," "Duk da haka,ki sanyasu,in yaso daga baya kin cire," Gyaɗa kai tayi"shikenan,"ta ambaci hakan tare da mikewa,taje ta kar6i atampar daga hannunta, "Bari naje,na kawo maki dinner dinki,"tayi maganar tare da nufar hanyar fita daga dakin,Harta ruƙe handle ɗin kopar ta juyo ta kalli sehrish"Munyi magana da Amrish,tace tana so taje gidansu ta kwaso kayanta,bansani ba kota fada maki" "Bata faɗamun ba," "Okey,in Allah yakaimu,Zuwa gobe zanyiwa wani magana cikin matasan gidan nan,yakaita gidan ta dauko kayanta," "Allah yakaimu Lafiya," "Ameen"ta amsa mata tare da juya ta fuce daga ɗakin,

Shaf shaf ta shiga zura kayan ajikinta,sun zauna mata sosai sunbi dirin jikinta,bata ɗaura ɗankwalin ba,don bata iyaba,zama tayi gaban mirror ɗin tana jiran dawowar,Hajiya azeema don ta ɗaura mata shi,

After some minutes hajiya azeema,ta shigo hannunta dauke da tray mai fadi,Asamanshi food stuff ne,Saman table ta sauke tray ɗin,kafin ta nufo Sehrish, "Banta6a ganin budurwar da atampa keyi mata kyau ba irinki,yadda kasan donke companyn suka ƙerata,"fashewa sehrish tayi da dariya,don ba ƙaramin nishaɗi ta sanyata ba,

Bayan ta kammala ɗaura mata ɗan kwalin,style me kyau,tace"Aikina ya qare,ga abincinki can kije ki zauna ki ci," "Nagode sosai,"tana kai karshen maganarta,ta fuce daga dakin,

Murmushi sehrish ta ɗan saki tana kallon kanta ta cikin madubin,miƙewa tayi daga gaban madubin ta dawo gefen gadon ta zauna,sae ƙamshi ke tashi ajikinta,

Tsaf Ya kammala Shiryawa cikin shadda Ash colour,wa'iyazubillah,kyau iya kyau,a tsaye yake gaban mirror yana gyara agogon diamond ɗin hannunshi,

Omar dake zaune gefen gadonshi sai faman sakin murmushi yake yi,yayin da yake kallonshi, "Kasan Allah duk macen data mallake ka ba ƙaramar me sa'a bace,cos you're expensive,komai naka Extraordinary ne,wlh mace koda Ilminta koda kyanta koda arzikinta sai da rabonta,"Sai faman zuzutashi Omar yake yi,Shidai baice mashi uffan ba,a hankali yakai hannu tare da ɗaukar turaren nan nashi,Yabi ko'ina na jikinshi ya feshe, "just ka bayyana mata irin son da kake yi mata,ka ƙaddara cewa yau zaka fara dating......" Slowly ya juya gefe tare da kallon Omar"how can i do that"? "Ni zan koya maka," Girgiza kai yayi,Omar kasan ban iya soyayya ba,' Matsalarka kenan,tunda baka iyaba ka bari in koya mata,natsuwa sgr yayi yana sauraronshi "Kece sanyin idaniyata,bana iya runtsawa in bakya a kusa dani....." Kwata kwata Sgr baya fahimtar abunda Omar ke koya mashi, "Na lura baka fahimtata,Zamuyi amfani da bluetooth,zaka manna shi a kunnanka,Idan kaje wurinta,zan dinga karanto maka,kai kuma kana faɗa mata,haka yayi"? Ɗaga mashi kai yayi"yeah,i can try it,

[3/19, 2:58 PM] +234 810 388 4440: _💋The father Of Soldiers💋_

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Story & Written by *_Boss Bature_*

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

Dedicated to my beloved sisters. 😍

Proud Of My First Novel💋

_Warning banyarda wani yayi amfani da wani sashe na littafina ba, kada a ta6amin komai na littafina,Sannan kar a kuskura a haɗamun document,Ga mai buƙatar karanta Littafin Abban Sojoji from Book one to 3 yayi mun magana ta whatsapp 08103884440_

Canza ra'ayi yayi"Omar,bana buƙatar using the bluetooth Just komai ya dace ka sanar da ni," Murmushi Omar ya ɗan saki don yasan cewa Sgr zai iya,A nan ya shiga kwatanta mashi yadda zai bayyanar da Soyayyarshi,bayan Ya Kammala Sgr yace"thanks,sai nadawo,"yakai ƙarshen maganar tare da juyawa ya nufi hanyar fita ɗakin,Yana jiyo muryar Omar Yana faɗin"Wish u all the best,"

A lokacin Sehrish tana zaune ta tasa abincin da Aunty Azeema ta haɗa mata sai ci take yi,bayan ta kammala ta yagi tissue tana goge bakinta,A dai dai wannan Lokacin taji an turo ƙopar ɗakin,dakatawa tayi tana jiran ganin mai shigowar,Natsuwa tayi tana shaƙar daddaɗan kamshin turaren dake kai ma hancinta ziyara,tunkafin ma Ya shigo ƙamshin jikinshi ya gauraye ɗakin saƙo da lugu,

A hankali ya sako ƙafarshi kafin ya ƙarasa shigowa ciki,Har sai da gabanta ya faɗi rass,Saboda razana da tayi da kyawun da Sgr yayi,Kayan hausawa ba ƙaramin kyau suke yi mashi ba,yadda kasan danshi kamfanin shadda suke ƙerata,cikakkiyar surar jikin nan nashi ta ƙara fito da kyan shaddar, Tunda ya ɗaura idanuwanshi akanta,gaba ɗaya wankanta ya tafi da imaninshi,natsuwa yayi yana kallonta,from head to toe,Atampar jikinta ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,Ya kasa kawar da idanuwanshi kamar yadda itama take Kallonshi,

Sallama yayi mata cikin sanyin Murya ta amsa mashi,kafin ya ƙarasa shiga ciki,gefen gadon ya zauna dab da ita,tuni kasala ta fara baibaye kowannansu,

Almost 15 mins,tsit kake ji ba wanda yace uffan acikinsu,Ajiyar Zuciya ya ɗan sauke kafin Ya soma magana, "Ya jikinki?"A hankali tace"da sauki" jinjina kai yayi yana cigaba da kallonta,hakan yasa ta Sunkuyar da kanta tana kallon hannuwanta,

"Reesh,nasan nayi maki laifi wanda yasa kika juyamun baya,But Why can't u forgive me?komai ya wuce mana,Idan har bana ƙaunarki serious bazan kulaki ba,kuma abunda ya faru,duk don saboda ƙaunar da nake yi maki ne,Naji fargabar su rabani dake,I thought yi maki hakan da nayi will be the solution,sai dai nayi mistake na kusantarki a lokacin da nake cikin fushi,wanda duk Iyayenmu ne suka jawo hakan,"ya ɗan dakata da yin maganar Yana mayar da numfashi,jin yayi shiru yasa ta dago,yayin da idanuwansu ke kallon cikin na Juna, "Ina neman alfarma a wurinki,For the Last time,ki bani dama,zan gyara kuskure na,Zan canza maki kamar yarda kikeso," Jikinta ya ɗanyi sanyi da jin kalamansa,Amma still tana kokwanto akanshi,gani take kamar Sgr bazai ta6a sonta don Allah ba,sai don ya mayar da ita abun biyan buƙatarshi kamar yadda ya saba yi mata,Zurfin tunani ta shiga,ba zato ba tsammani,taji ya ruko hannuwanta Acikin nashi,sosai ya ruƙe hannun yana shafa lallausar fatar hannun,a hankali ya fara matsawa yana niyyar rumgumeta.... "Reesh,I've Fallen for you...... "Tunkan yakai ƙarshen Maganar,Rai a matuƙar 6ace Sehrish Ta ƙwace hannunta daga nashi tare da yin wurgi da hannunsa ta dan ja baya,Abunda bai ta6a tsammani ba,Waro idanuwanshi yayi waje yana kallonta, A fusace take magana"Wlh ba sona kake yi ba don Allah,Ni nasani don kawai biyan buƙatarka yasa kake so naci gaba da kasancewa dakai,idan har dagaske kana sona,Meyasa tuntuni baka sanar dasu cewa kana sona ka maida ni matarka ba,kuma tun farko kayi accepting aurena don kawai naci gaba da yi maka Aiki,Saboda kafi ƙarfin kayi soyayya dani,bankai matsayin da zan zama Matarka..... "Kasa ƙarasa Maganar tayi sakamakon gigitacciyar tsawar da Sgr ya daka mata,A firgice ta zazzare idanuwanta tana kallonshi,tuni idanuwanshi sun Canza launi sosai,Ranshi yayi Mugun 6aci,Zuciyarshi ta hasala,har ya ɗaga yatsu biyar cuf zai wanka mata mari,Ta fashe da matsanancin kuka,Ta dinga ja da baya har ta ƙurewa kan gadon,ta runtse idanuwanta sosai,'

Yarfar da hannun gefe yayi,wani irin raɗaɗi yake ji acikin zuciyarshi,tuni idanuwanshi sun cicciko tab da ƙwalla,takaicin Duniya ya ishe shi,ƙaramar yarinya kamar wannan ce take gaya mashi Magana,gudun kada ya karya ƙasusuwan jikinta ne Yasa yayi saurin miƙewa da saurin gaske har yana tuntu6e ya fuce daga ɗakin,A makance yake tafiya Allah yaso babu kowa a babban falon,A zafafe ya nufi twin stairs ɗin Ya haye,yana taka staircases ɗin wasu Zafafan hawaye suka wanke mashi fuskarshi masu ɗumin gaske,har wani zazza6i yake ji ajikinshi,Sehrish ta hasala shi sosai,

Yana shiga Bedroom Yasa hannu Ya tu6e rigar jikinshi yayi wurgi da ita ƙasa,A haukace Yakai hannu Ya damƙi bedsheet din gadon Ya yayeshi tare da Jefar dashi gefe guda,Dunƙule hannunshi Yayi da ƙarfin gaske Ya naushi Dressing Mirror ɗinshi,gaba ɗaya madubin ya farfashe ya zube,hatta hannunshi sai da glass din ya faffasashi,jini ya shiga tsastsafowa,raɗaɗin da yake ji a hannunshi bai kai raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi ba,lokacin da Sehrish ke faɗa mashi wannan maganganun,Biji biji ya fara gani acikin idanuwanshi,Jiri ya soma ɗaukarshi,tangal tangal yayi zai faɗi,kaitsaye ya faɗa saman gadonshi,numfashin shi na fita da wani irin huci,ga wani matsanancin ciwon kai daya farmasa,

Wuraren ƙarfe 12 na dare,Omar ya faɗo part ɗinsa,fuskarshi ɗauke da Murmushi,Yazo cike da sa ran sunyi nasara,Tun a palour Yake ƙwala mashi kira"Bro!bro!"shiru ba Amsa,har yayi tunanin ko bai kaiga dawowa bane,Acikin ransa har yana cewa"Yanzu haka yana can manne da ita suna shan Soyayya,"ya ƙarasa zancen zucin yana kokarin juyawa kwatsam Idanuwanshui suka sauka akan Agogon Diamond ɗin Sgr,dake yashe a ƙasan tiles, Har sai da gabanshi ya faɗi,don yasan cewa ba ƙaramin abu bane zaisa Sgr ya yarda watch dinsa ba,zuƙunnawa Omar yayi tare dakai hannu ya ɗauki wrist watch ɗin,A fili Ya ambaci Sunanshi Rafayet,Da gudun gaske Omar Ya faɗa bedroom ɗinshi,A kwance ya samu Sgr tamkar baya numfashi,hankalinshi yayi Mugun tashi,A sukwane ya haye saman gadon saitin fuskar Sgr,hannu yasa yana shafa fuskarshi"Rafayet meya faru dakai?Meyasa kayi hakan?duk ka hargitsa ɗakin ka fasa glass,"ɗago da kanshi yayi tare da ɗaurashi saman laps ɗinshi,Omar sarkin tausayi tuni idanuwanshi sun cicciko tab da ƙwalla, Muryarshi na kerma yace"Dan Allah Rafayet ka fadamun meya faru da kaine?nashiga damuwa sosai pls....."tuni hawayen fuskarshi sun soma sauka saman fuskar Sgr,

Sai lokacin Sgr Ya yunƙura tare da miƙewa daga zaune,yana faman fitar da huci, "Omar,Reesh batasona,She hates me completely,i can see dat in her eyes,danasan zata ci mutuncina haka da banje ba,nafi ƙarfin wulaƙancin mace,Saboda Allah ya jarabce ni da son ta shiyasa har take ƙoƙarin gaya mun magana".....Ya ɗan dakata da yin maganar,Omar ya kasa kunne yana sauraronshi,. "tana tunanin cewa Jikinta nakeso!Me take dashi?Mata nawa ne suka sha kawomin kansu wanda suka fita komai don kawai nayi lalata dasu,Amma banta6a kula ɗaya daga cikinsu ba,sai ita da Allah ya bata dama? Jinjina kanshi ya ɗanyi kafin yaci gaba da cewa"As a Surgeon General,I stoop too low don kawai inason cigaba da rayuwa da ita,wata ƴar ƙarama da ita,if not love dat's Crazy me zanyi da ita.........."tuni hawaye sun wanke mashi fuskarshi, "Itace mutun na farko da ta fara sani zubar da ruwan hawayena," Jikin Omar ba ƙaramin sanyi yayi ba,Hannu Yasa tare da janyoshi jikinshi lallashinshi ya shiga yi,Yana tausarshi,

"Omar,dama kadaina Wahalar da kanka,Na yanke shawarar gobe zan tafi U.s," "Dan Allah Rafayet mubi komai a sannu,Ni nasan cewa tana sonka,zata sauko ne,amma tafiya U.s will not be a Solution," "Na riga na yanke shawara Omar,i will distance Myself from her,nasan hakan zai sa nasamu kwanciyar hankali in na daina ganinta,So Zan tafi kawai first thing tomorrow Morning", Shiru Omar yayi,don kuwa yasan Sgr bazai canza ra'ayinshi na tafiya ba, "Shikenan,bazan hanaka tafiya ba,bari na taimaka maka,Hannunka yana bleeding," Girgiza kai yayi"a'a,kabarshi kawai,"yana faɗin hakan ya sauko daga saman gadon Ya nufi toilet ɗinsa Ya shige,

Saukowa Omar yayi daga saman gadon,Ranshi ya 6aci sosai baiji daɗin abunda Sehrish ta yiwa Sgr ba,bai ta6a tunanin zata Iya furta mashi waɗannan kalaman ba,

Gyara mashi Bedroom ɗin ya tsaya yi,Sai da ya kwashe glass ɗin daya zube duka ya kawar da komai,kafin Ya sauko Downstairs Ya nufi Medical Room ɗinsu,P.A box ya ɗauko Kafin Ya koma up part ɗin Sgr,Ya ajiye mashi asaman gadonshi don yayi dressing ɗin hannunshi,

Bayan Omar ya fito a hanzarce ya nufi ɗakin Azmee,A lokacin Sehrish tana ƙumshe cikin bargo,tajiyo bugun ƙopar ɗakin,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,duk a tunaninta Sgr ne ya dawo,gabanta sai faɗuwa yake yi,ƙin buɗe ƙopar tayi Har sai da Omar ya ɗaga Murya tare da cewa"Sister Omar ne,Zo ki buɗe mun ƙopa," Cire blanket ɗin tayi cike da fargaba ta ƙarasa gaban door din tasa hannu ta buɗe mashi,tunda take bata ta6a ganin Omar cikin 6acin rai irin na yau ba,jikinshi har wani jijjiga yake yi,sam babu annuri akan fuskarshi, Muryarta na kerma ta ambaci sunanshi"yay...ya Omar," Shiga cikin ɗakin yayi bayan ya sanya hannu ya garƙame kopar, A fusace Ya damƙi kafaɗunta tare da jijjigata yace"Ke!Ashe baki da hankali bansani ba?Anya kuwa kinsan ciwon kanki?kin bani kunya kin kuma bani mamaki,Ki rasa abun wulakantawa Sai Sgr?tsaran wasanki ne?dan Kin samu Allah ya mallaka maki shi shine har kike kokarin banzatar dashi?Idan saboda laifin da yayi maki ne baya baki hakuri ba!shine bazaki hakura ba!........"fashewa tayi da wani irin matsanancin kuka,

"Don me zaki ce wai jikinki yake so?ke kinsan adadin matan dake bibiyar rayuwarshi don kawai su samu shiga awurinshi koda da sunan lalatane bada aureba,Sai ke don Allah ya jarabceshi da Sonki,ni shaidane Akan Sgr,wlh da ace baisonki bazai ta6a sha'awar ta6a jikinki ba,don yana sonki ne yasa har yake yi maki hakan,shi baturen mutun ne shiyasa yake nuna maki so ta hakan........"dakatawa ya ɗanyi da yin maganar yana mayar da numfashi,zufa duk ta wanke mashi fuskarshi,Sehrish kuwa sai faman shessheƙar kuka take yi,

Sassauto da Muryarshi yayi kafin yaci gaba da cewa"Yanzu hankalinki ya kwanta,kin kaishi ƙarshe,Gobe zai koma U.s,duk don saboda abunda kikayi mashi,Kuma inaso ki sani da zarar ya ɗaga ƙafarshi yabar ƙasar nan,Akwai mata dayawa dake jiranshi,daga Cikinsu akwai Eva his Uncle's Daughter,dawowarshi kawai take jira don a ɗaura masu aure...tun suna yara take sonshi,ba abunda bata mallaka ba da duk wani ɗa Namiji zai buƙata a wurin ƴa mace..,......" Tunda ya soma maganar tafiyar Sgr U.s da kuma Maganar Eva,hankalin Sehrish yayi mugun tashi,duk tabi ta ruɗe ta susuce, "Sgr baya kula mace don bashi da ra'ayin yin aure,kuma shi ba ɗan iska bane bai ta6a kusantar zina ba balle har ya aikata ta,baisan menene so ba,baisan kuma ya akeyin shi ba,Amma wannan karon Akanki Yasan menene So,ya kuma san daɗin mace,Kinga kuwa da zarar yabar ƙasar nan Ya koma can,zai amince da Auranta ne,kodan ya nema ma kanshi mafita,ke kuma zakiyi dana sani ne,domin kuwa duk macen data samu miji kamar Sgr tayi watsi dashi wlh sai tayi danasani na har Abada,"

Fashewa ta kuma yi da wani sabon kukan tamkar ranta zai fita,Sam ta kasa buɗe baki tayi magana,

"Ya Sauke duk wani girman kai nashi,Ya ajiye matsayinshi duk don saboda ke ɗinnan,Don Ya samu soyayyarki,da kanshi ya nemi da in koya mashi soyayya saboda yana son ya faranta maki,Yana kuma son ki gane cewa ba jikinki yake so ba,Zuciyarki yake so,kuma kinyi kuskure da iliminki da hankalinka,kika bari Mijinki yake kwana da baƙin cikinki acikin zuciyarshi!?"

Rass taji gabanta Ya faɗi,girgiza kai Omar yayi,tare da juyawa rai a6ace ya nufi hanyar fita daga ɗakin har ya ruke handle ɗin ƙopar ya kuma juyowa ya kalleta, "Ina ƙara tunasar dake,Gobe da Safe zai tafi,shawara ta rage taki,wlh don kina ƴar uwata ne yasa na zauna ina yi maki wannan gargaɗin,Saboda ina sonki dashi,Kuma kema kina sonshi,wannan damarkice ta ƙarshe kiyi tunani kafin nan da safe,nabarki lafiya,"

Yana kai ƙarshen Maganarshi,Ya buɗe kopar ya fuce waje,

Tashin hankali,Wani irin zazza6ine Ya lullu6eta,hawaye ta ko'ina saman fuskarta,wani irin tuƙuƙin baƙin ciki take ji acan ƙasan zuciyarta,sunan Eva ya tsaya mata aranta,saboda ta ta6a jin sunyi magana akanta a lokacin baya shi da Omar,har yake cewa in ma akwai Macen da ya dace ta mallake shi,to itace,

A hankali ta soma ambaton"Innalillahi wa'inna ilahirraji'un,"

Maganganun Oummansu ta shiga tariyowa acikin kanta,daƙyar ta iya lalla6awa ta haye saman gadon ta kwanta,sosai tashiga raira kuka kamar jinjira jikinta sai kerma yake yi,Wani irin kishine ya rufeta,cikin shesshekar kuka take faɗin"Ya Rafayet zai tafi U.s ya barni,zai je ya aureta,"nutsar da fuskarta tayi jikin pillow tana ta raira kuka,

A daren Ranar Mutun biyu basu runtsa ba,Waɗanda zuciyoyinsu ke cikin halin ha'ula'e,kamar yadda Sgr ya kwana kwance saman gadonshi cikin mawuyacin hali,Haka itama Sehrish ta kwana da tunanin abu biyu,kalaman Oummansu da kuma kalaman Marshal Omar sun tsaya mata aranta,shi kanshi Omar ɗin bai samu isasshen bacci ba,saboda damuwar daya shiga duk akan Ɗan Uwanshi,

Wuraren Sallar Asuba Sehrish tana a kwance kamar matacciya,jikinta duk ya saki,ga zazza6in da take fama dashi tare da matsanancin ciwon kai,daƙyar ta samu ta sauko daga saman gadon ta shiga toilet,agaban Sink ta tsaya tana kallon kanta cikin Mirror,fuskarta tayi jaga jaga da hawaye hada majina,jan bakin data shafa duk ya 6ata fuskar,duk ta harmutsa gashin kanta,tasha kuka sosai,lips ɗinta duk sun kumbura,hancinta yayi jawur dashi saboda matsar daya sha,tajima acikin Toilet ɗin kafin ta samu tayi alwala,

Lalla6awa tayi ta fito daga toilet ɗin ta tunkari wardrobe ɗin kayanta,hijab ta ɗauko tare da darduma ta shimfiɗata,daƙyar ta samu ta tattara natsuwarta kafin ta kabbara sallah,bayan ta kammala Sallar ta zauna tare da ɗaga hannuwanta,tana Addu'a hawaye na shararowa akan face ɗinta,jikinta duk yayi sanyi,A saman dardumar bacci ya ɗauketa,

Baccin bai kaiga yin nisa ba aka soma kwankwasa ƙopar ɗakin,kwan kwan,can cikin bacci take jin bugun ƙopar,firgigit ta farka,zufa sharkaf akan fuskarta tamkar an watsa mata ruwa,bakomai bane ya fado mata aranta ba fa ce Maganar Omar na cewa Yau Sgr zai koma U.s,A hargitse ta miƙe tare da nufar ƙopar tasa hannu ta bude,Amrish ce a tsaye jikinta sanye da hijabi,ganin Sehrish cikin damuwa yasa tace"Meya faru ne?baki da lafiya ne?a ruɗe tayi tambayar,

Sehrish bata tsaya jin amsarta ba,duk hankalinta ya tashi,ta gefen Amrish tabi da gudun gaske ta nufi babban falon gidan,babu kowa duk basu tashi daga bacci ba,Upstairs ta haye har tana tuntu6e wurin taka matattakalar,Idanuwanta sun makance tana tsoran ta rasashi,a fujajen ta faɗa part ɗinsa,shigarta falon keda wuya,Sai ga Sgr Ya turo trolley a hannunshi,Ya kammala shirin shi tsaf zai tafi Airport,Jikinshi nasanye cikin jeans da T-shirt,fuskarshi sam babu annuri akanta,ga hannunshi daya jima rauni,

Cikin sanyin Murya ta ambaci sunanshi"Ya Rafayet,"ɗagowa yayi da idanuwanshi akan fuskarta,ita kanta ta tsorata da ganin launin idanuwanshi,Sun yi jawur dasu gwanin ban tsoro,tsantsar 6acin raine acikinsu,bai amsa kiran sunanshi da tayi ba,tamkar ma baisan da zuwanta ba,janyo trolley ɗinshi yayi kaitsaye ya nufi hanyar fita daga falon inda take a tsaye,tayi tunanin zai kula ta,amma ko kallo bata ishe shi ba,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,tuni hawaye sun wanke fuskarta,Yana ƙoƙarin bi ta gefenta ya wuce,a hanzarce tayi saurin sanya hannu ta ruko damtsen hannunshi, Muryarta na kerma tace"Ya Rafayet,idan ka tafi ni kuma fa?ya kakeso nayi da rayuwata"?

Runtse idanuwanshi yayi"ki sakarmun hannuna,tunkafin ranki ya 6aci,"A kausashe yayi maganar,

"Na yarda kayi mun duk wani hukunci da ya dace dani Saboda bani da hankali,amma dan Allah kada ka tafi ka barni," Tana kai ƙarshen maganar,ta faɗa saman faffaɗan kirjinshi ta rungumeshi sosai tare da fashewa da matsanancin kuka,har cikin zuciyarshi yake jin kukan nata, "Ya rafayet am sorry,bazan ƙara ba,"cikin shessheƙar kuka tayi maganar,lokaci guda kuma ta ɗauke ɗuff,a hankali ya buɗe idanuwanshi tare da sauke su akanta,tayi tighting ɗinshi sosai,kamar ance za'a ƙwace mata shi, Nauyayyiyar ajiyar zuciya ya shiga saukewa,wani irin sanyine ya ratsa zuciyarshi,sakin trolley ɗin hannunshi yayi tare da ruƙota,ya ɗago da kanta daga jikinshi,da alama ta sume,fuskar nan tayi jaga jaga da hawaye,ta jigata sosai,jikinta yayi zafi sosai,tsantsar sonta da ƙaunarta ne acikin zuciyarshi,kamar ya haɗiyeta cikin cikinshi haka yake ji, Gaba ɗaya ya sa6eta saman kafaɗarshi,ya juya da ita zuwa bedroom dinshi,a saman katafaren gadonshi ya sauketa,ya gyara mata kwanciyarta,ya kasance tana fuskantar ceilling,hijabin jikinta ya cire mata,ganin yadda take zufa,a gefe ya ajiye hijabin,ya sauko daga saman gadon ya fita palour,within minute ya dawo hannunshi ɗauke da bottle water mai sanyi,gefen gadon ya zauna bayan ya buɗe murfin ya tarfa ruwan a hannunshi ya yayyafa mata shi asaman fuskarta,nan take taja dogon numfashi haɗi da sauke ajiyar zuciya ajere,tunkafin ta buɗe idanuwanta,ta soma sambatu"ya rafayet kada ka tafi ka barni,bazan iya rayuwa batare dakai ba,'

Ajiye bottle din yayi saman drawer,kafin ya hau saman gadon gaba ɗaya,a dai dai saitin fuskarta yakai tashi fuskar,zuba mata ido yayi yana kallon yadda take ta sambatu "Reesh!You know you love me, but why kike wahalar dani"?he said calmly,jin muryarshi yasa ta buɗe idanuwanta,sunyi luhu luhu cike tab da ƙwalla, A hankali take kallonshi,yayin da shima yake kallonta,batare da kyaftawar ido ba,tamkar zasu haɗiyi junansu,saboda tsabar so, Ganin tana ƙoƙarin sake fashewa da kuka,yasa shi yin saurin toshe mata bakinta,da tafin hannunshi"its ok,u don't ave to cry,tunda gani a kusa dake," Lumshe idanuwanta tayi tare da sake buɗesu akan fuskarshi,zame hannunshi yayi daga kan fuskarta, "Ya rafayet,Am really sorry,pls don't leave me,i can't survive without you," Kalamanta ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya sukeyi ba, "why reesh?kin tada mun hankalina,ko bacci bana iyayi just because of you,kin fusata ni sosai,kin sanyani zubar da hawayena,' Girgiza mashi kai tayi"Bazan ƙara ba," "Kin yarda cewa inasonki?ba jikinki nakeso ba?kuma kin amince zaki rayu dani a matsayin Mijinki Uban ƴa'ƴanki"? Jinjina mashi kai tayi alamar eh, Kafin tace"na aminta dakai,Na yarda da irin son da kake yi mun,kuma ina namen yafiyarka,akan misunderstanding din da muka samu,ban kyauta maka ba,its all my fault,nice ƙarama koba haka ba,kai ɗan uwana,Yayana kuma Mijina,nice a ƙasa dakai,amma ban duba hakan ba......" Bata kai ƙarshen maganar ba,ya dakatar da ita,ta hanyar sanya yatsanshi ɗaya asaman lips ɗinta, "Komai ya wuce a wurin,nima ina neman yafiyarki akan laifin da nayi maki," Kallonshi kawai take yi,ba ƙaramin mamaki Sgr ya bata,ta ƙara yarda da irin son da yake yi mata,ya canza mata ba kamar da ba, "Nima komai ya wuce A wurina,amma pls,ka fasa tafiya U.s din,idan ma zaka tafi ƙafata ƙafarka,don bazan bari na rasaka ba," Ƙayataccen murmushin gefen fuska Sgr ya sakar mata,gaba ɗaya ya tafi da tunaninta,natsuwa tayi tana kallon kyakkyawan murmushinshi,ƙurawa juna ido sukayi wani irin kallon so suke jefawa junansu,

A wannan yanayin na shauƙi,Marshal Omar ya faɗo bedroom ɗin,Yazo da niyar ya lallashi Sgr akan ya fasa tafiyarshi,tun a palour yaci karo da trolley an ajiyeshi,yana zuwa bakin ƙopar ɗakin,ba zato ba tsammani ya hango romeo da juliet,abun ya bashi mamaki,Yadda ya samesu,manne da juna,sun ƙurawa juna ido,kamar zasu cinye junansu,Ƙayataccen murmushi marshal Omar ya saki,yadda kasan wani zautacce,Su suke yin soyayyar amma yafi su jin daɗinta,a hankali Ya furta Alhamdulillah Ya Allah,Na gode maka daka cikama ɗan uwana burinshi,Nima Ya Allah ka cikamin burina na ganin na mallaki hosana,A matsayin matata,Uwar ƴa'ƴana,Ya Allah ka dawwamar da farin ciki acikin zukatanmu,Ya Allah ka ƙara haɗa kan masoyan nan,ka albarkance da samun zuri'a ɗayyiba,

Bai bari sun ganshi ba,juyawa yayi da sauri yabar part ɗin,A ƙopar palourn Ya tsaya tare da zura hannu cikin aljihun wandonshi,Ya zaro wayarshi,Layin hajiya azeema ya dannawa kira,sae faman sakin murmushi yake yi,kamar wanda Akayiwa Albishir da gidan Aljanna,yafi kowa farin cikin wannan ranar,

A lokacin da kiran Omar ya shiga,Hajiya azeema na kwance bata farka daga baccin asuba ɗin data koma ba,ringing ɗin wayartane Ya tayar da ita,hannu takai saman side drawer ta ɗauki wayar,ganin sunan daya bayyana akan screen ɗin wayarna yasa ta cewa"to fa,Omar ne ke kira tunda safe,to Allah yasa muji alkahiri, Ta ambaci hakan tare da ɗaga kiran nashi,ta manna wayar a kunnanta, Gaisawa suka fara yi kafin tace"Ya Andace ko kuwa har yanzu ba canji"? Muryarshi da alamun farin ciki atattare da ita,Yace"Congratulation Mommy azeema,munyi winning,"tunkafin Ya karasa maganar tace"Alhamdulillah Ya Allah,'ta ambaci hakan yayin da take miƙewa zaune, "Omar shaƙa mun naji,wlh aƙagare nake,Meya faru,sun shirya,Sehrish ta janye maganar sakin," Dariya omar yayi sosai,jin yadda take ta jero mashi tambayoyi, "Aunty ae yanzu haka daga part dinsa nake,Na same su manne da juna,maganar saki ta ƙare,Zama na har abada,"daga haka Omar ya kwashe duk abunda ya faru tundaga daren jiya har zuwa yau da safe daya same su,Ya sanar da ita, Saboda tsabar farin ciki,Saukowa tayi daga saman gadon hannunta manne da wayar,Ta shiga yin rawa,tsantsar farin cikine akan fuskarta, "Mommy,suna buƙatar wasu abubuwa da zasu ƙara danƙon soyayyarsu,amma kafin nan,Yanzu dai suna buƙatar lafiyayyen breakfast,don jiya ɗan uwana baici komai ba," Murmushi hajiya azeema tasaki kafin tace"in sha Allah,Yanzu zan tafi kitchen don in shirya masu," "Yawwa aunty,mun gode sosai,sai munzo yin godiya nida rafayet," "Haba dai,ae duk yiwa kaine,kada ka wani damu kanka,Amma ya tsakaninka da hosana?Ba tada matsala"? Omar yace"Nikaɗai zan iya da hosana,Bata da matsala," Jinjina kai tayi"shikenan omar,duk da haka zan dage damtse wurin ganin na koya mata abubuwan da suka dace," "Thank so much auntynmu,mai son ganin farin cikinmu," Murmushi ta saki"yanzu bari naje na shirya masu breakfast din" Daga haka su kayi sallama dashi,Ajiyar zuciya ta sauke fuskarta ɗauke da murmushi ta ajiya wayar sama drawer,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull