Abdulmalik bobo complete na billyn abdul - Chapter 12
Abdulmalik bobo complete na billyn abdul Chapter 12: Abdulmalik bobo complete na billyn abdul Chapter 12. A6angaren Rahma kam suna fita babu dad'ewa saiga…
4,485 words
A6angaren Rahma kam suna fita babu dad'ewa saiga Khursiyya da khairiyya sun iso damasu decoration, nandanan aka share harabar gidan suka fara aikinsu, tsaf suka gyara ko ina yad'auki k'yau, suka jere kayan kid'ansu.. Haba zuwa k'arfe biyu ai gida yafara cika da yara, matansu ya sulaiman da yaransu duksun iso, tare suketa hidimar had'a abinci, ga kayan rabonan ank'ukkula, zuwa k'arfe hud'u duk Wanda suka gayyata ya iso gidan. Awannan lokacin kuma bobo da nawal suna can sun lodo kaya daya sayama Nawal sun kamo hanyar dawowa gidan, dukda abinda Rahma ta masa da safe saiyaji baiji haushintaba sosai, tun awaje yakebin motocin da akayi fakin awaje da kallo, aransa ya ce, "k'ila wani gidanne a anguwar sukayi bak'i, yay hon maigadi yalek'o, ganin shine yasa yak'araso wajen mortar batareda yabud'e masa gate ba. A'a yabaka bud'emin gate ba kuma?. Aii oga wlhy babu wajen fakinne aciki. Kamar ya babu wajen parking?, mike faruwa acikin Gidan?. Mai gadi yad'an Sosa kai Dan Rahma ta ce, " karya fad'a masa, ya ce, "saidai kashigo kagani oga. Bobo yagirgiza kai kawai batareda ya tankaba yanemi waje awaje yay fakin suka fito shida Nawal, wayoyinsa kawai yad'auka amotar Yakama hannun Nawal suka nufi cikin gidan, bin ko ina yake da kallon mamaki yajinjina kai tareda nufar cikin gidan, suka shiga falon nanma shiru babu alamar akwai mutane awajen, baigama tunanin mike faruwaba yaji yara suna tafi dafad'in. *_“happy happy birthday to you, happy happy birthday to you...... Saikuma gasu Rahma suma sun fito”._* Aibaisan sanda yasaki lallausan murmushiba, dama abinda Rahma tashirya kenan shiyasa tak'i binsu?, jiyayai tak'ara girma da daraja azuciyarta. lol
Na ce, " hummm gaba gabadan bobon Appa.
------------------------ Daganan aka shirya Nawal cikin kaya masu k'yau, shima ogan kwalliya yakuma ci, aka fara gudanar da biking birthday d'in Nawal. Masha ALLAH komai ya k'ayatar abin burgewa. Wajen bada cake Nawal tacuro tasakama babanta tasakama Rahma, tabi sauran iyayen matansu ya hamza dukta basu, su khairiyyama haka, daganan aka fara cashiya. Biki dai bai tashiba sai gab da sallar magriba. Masu tafiya suka tattafi, akabar yaransu ya hamza kawai da matansu, bayan isha'i suma mazansu suka iso, saida sukaci sukasha akasha hirara zuminci sannan kowa ya kwashi family nasa sai gida. Bobo ya tsarama kansa wani Abu yau, amma saiyaji wai agidan su khursiyya zasu kwana, ba k'aramin haushi abin yabashiba amma saiya dake tunda bashida yanda zaiyi.
_bayan kwana hud'u_ Duk burin da bobo yaci akan Rahma ya rushe Dan har sannan su kursiyya suna gidan, doledai yad'aga k'afa. Ranar Litinin da safe su khursiyya suka koma gida abinsu, shima bobo yafita aiki, Nawal kuma tana makaranta sai Rahma kawai agidan. Tayi aikinta tagama komai tsaf, 1:30pm tana zaune afalo tana kallo wayarta tayi wringing da sauri ta kalli wayar bak'uwar no. ce, shiru tayi Dan yau tunda tatashi gabanta ke fad'uwa, har wayar ta yanke bata d'agaba aka sake kira, ganin babu dacewa arashin d'aukar yasa ta d'auka tunda batasan ko wayeba. Sassanyar muryarsa tadaki kunnenta, ta sauke ajiyar zuciya wadda yajita har yatsan kafarsa, yad'an lumshe idanunsa yabud'e tareda jingina da kujerarsa, ahankali yake d'an lulita, ya ce, ''matsoraciya da kinzata waye to?. Murmushi tayi ta ce, "nifa ba tsoro najiba, baki yata6e tamkar yana gabanta ya ce, " dama zancemikine kid'aukko babynki a school yau aiki yamin yawa a office bazan samu damar d'akkotaba. Okey babu damuwa. So zaki iya deriving d'in ko?. Eh zan iya. Okey tom ALLAH ya tsare, saina sake kira....... d'if ya kashe kafin tayi magana, murmushi tayi kawai tamik'e tacanja kayanta. d'akinsa tashiga Dan key d'in motarta yana hannunsa, tagama dube dubenta bata ganiba, sai wani na jar motarsa a durowar gefen gadon, shita d'auka tafito. Tashiga motar daketa tashin k'amshi, tana mamakin turaren da Bobo yake amfani dashi haka, komai nashi Yakama k'amshin turarensa, mai gadi yabud'e mata gate tafice. Tafiya take ahankali saidai wani Abu mai kama da tsoro yana ta6a zuciyarta Dan tunda tafito daga gida take gani kamar wata bak'ar mota nabinta abaya, ajiyar zuciya tayi dataga motar kamar ta6ace, dahakadai tak'arasa makarantar su Nawal ta d'akkota. Labarin makaranta Nawal keta bata, amma itafa hankalinta yafara tashi Dan yanzuma k'ara ganin motar d'azu takeyi. Sunzo daidai danja ta rik'esu saikawai taga anbud'e motarsu anshigo, atsorace takalli bayanta saitaga wasu zaratan samari majiya k'arfi zaune tamkar motar gidansu, d'aya yanunata da bindiga, d'ayan kuma yatoshe bakin Nawal. ga Motar bak'in Gilas ce, nawaje baya ganin naciki...............
*_“😳masu karatu nikamdai atsorace nake, kosuwaye wad'annan mutane?, mikuma zasuyima Rahma da Nawal?.”_* Hummmm koya zata kaya?????????.
_kutayamu murna my sister d'ina ta haihu mace._
*_luv u oll my fan's_* *_(((S))).....2017_* [11/12, 2:56 PM] mrs bilkisu: 👩🏻💻typing........
❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _•{🅱🅾🅱🅾}•_
*_NA_* _*Bilyn Abdul*_
_sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_*
5⃣1⃣
Babu dad'ewa aka basu hannu, tuni jikin Rahma yajik'e da gumi dukda AC dake aiki amotar, jikinta sairawa yakeyi, duk addu'ar datazo bakinta karantawa takeyi. Dakansu suke nuna mata hanyar dazatabi, sunyi nisa sosai datafiya awata hanyar k'auyen da Rahma batasan ko inaneba, wayartace tayi wringing harzata d'auka Wanda yake rik'e da bindiga yadaka mata tsawa, kina d'agawa zan tarwatsa kanki. Janye hannunta tayi da sauri akan wayar, Wanda yake rik'eda Nawal ne yad'auki wayar, saidai kafin yad'aga ta katse, wata uwar dariya yashek'e da ita Dan ganin sunan daya kira Rahman, *_dadyn Nawal_*. Wani gida suka kaisu, zuwa sannan Nawal tayi barci, Dan sun shak'a mata wani abune, Rahma tarungume Nawal tana kuka maiban tausayi, aranta tana tunanin misukayima wad'an nan mutane dazasu kawosu nan??.
Bobo kam hankalinsa yafara tashi Dan ganin yayima Rahma kira wajen 10+ amma bata d'agaba, dukda d'umbin aikin dake gabansa haka ya tureshi yabaro office d'in. Makarantar su Nawal yafara zuwa, auntyn su ta ce, "aii tund'azu bayan yakira kamar yanda ya ce, " momynta ce tazo ta d'auketa, to babu dad'ewa tazo ta d'auketa..... Bai tsaya yagama saurarentaba yayo waje, daga nan gidansa yanufa, tun a gate yatambayi mai gadi, amma ya ce, "basu dawoba. Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un kawai yake ammabata azuciyarsa, amma dukya birkice, da sauri yaciro wayarsa a aljihu yakira khursiyya, itama ta ce, " basu zoba, Abu kamar wasa dukya rewad'e dangi dakira amma kowa amsa d'aya yake bashi *_basu zoba_*. Cikin rawar jiki yakira Appa yaturo masa number Abbansu Rahma. Cikin girmamawa ya gaidashi, tareda masa bayanin shine, Abba ya ce, "ALLAH sarki Abdulmaleek ngd ALLAH yayimaka albarka, ya su Rahma d'in?. Tun anan jikin bobo yayi sanyi, murya asark'e ya ce, " dama ita zantanbaya ko sunzo nan gidan?. Kai A'a gsky Rahma batazoba, kunyi da'ita zatazone?. A'a Abba dama...... Nan yafad'a masa yanda akayi. Abba yaja numfashi, to mud'an k'ara hak'iri zuwa d'an anjima mugani kota biya wani wajen, dukda dai nasan wannan baya d'aya daga cikin halayen Rahma, tabbas da Safna cema bazan damuba Dan nasan tanada rawarkai, amma Rahma kam batada wannan halin. To abba. Kawai bobo yafad'a ya yanke wayar, kuma kiran Number Rahma yayi amma ank'i d'auka, yadafe Kansas tamkar zai FASA ihu, yana nan tsaye ak'ofar gate saiga ya ishaq da ya Hamza, suka tambayi yanda akayi yasanar dasu. Ya hamza ya ce, "kasanarda Ammar ne?.” Girgiza kai kawai bobo yayi danya kasa magana, ya Hamza yakira Ammar yayamasa bayanin kimai, salati ammar yashiga yi, bai tsaya 6ata lokaciba yabaza yaransa ki ina.
Al'amarifa kamar wasa hardare babu wani bayani, zuwa yanzun labari yakarad'e dangi, bobo kam dukya fita hayyacinsa, sai kuka yake tamkar mace, shidama haka yake akwai jarumta amma Abu kad'anne ke karya azuciyarsa. Duksun dawo daga sallar isha'i, suna zaune afalo gidan Appa zugum², harda Abban Rahma da Umminsu, momyn ya Kamal da dad d'insu Ameera ihsan ya Muneer ya shaheed duk suna gidan Appa, Safna CE kawai babu, dantana makaranta abin yafaru, bayan tadawo mai gadi yashaida mata komai, yad'ora da fad'in 'yangidanma duk suna gidan surukan Rahma d'in. Safna ta ta6e Baki ta ce, " kaga baba bud'emin gate nashiga nahuta tukunna, Dan bazan iya zaman jigum jigum ba wlhy tunda ba mutuwa akace sunyiba. Maganar tata tarazana baba mai gadi, bayan yabud'e mata gate yabi mortar da kallo yana jin kina kai, aransa ya ce, "lallai yau nakuma shaidawa yarinyarnan batada mutumci ko kad'an, inbanda rashin mutumci d'an uwanka uwa d'aya uba d'aya ya6ata kanuna rashin damuwarka, kai ALLAH dai ya k'yauta to. Safna dai bamatasan yanayiba Dan tuni tashige cikin gida abinta, sai wata fara'a takeyi wadda nadad'e ban ganiba daga gareta.
🤔araina Na ce, " safna Kodai kidai??.
*_3days_* Tsawon kwana uku kenan da 6atansu Rahma, Abu tamkar wasa, zuwa yanzu kam aii kowa yajigata, Appa yabaza rok'on ALLAH amasallatai, hakama gidan redio Dana TV, social media ma haka, amma shiru kakeji wai malam yaci shirwa, kuma tun ranar ba'a sake samun number Rahma ba. ALLAH sarki bobo acikin kwana ukunnan Yayi wata uwar Rama, ko abinci bayasonci sai ammi ta tsareshi tamkar yaro tabashi abaki, shima lauma hud'u zuwa Biyar zaice yak'oshi, saitata lalashinsa sannan zaiyarda yak'ara kad'an.
Nikaina yabani tausayi k'warai da gsk😥.
Yanzuma suna zaune afalo Ammi tana lalla6ashin sa akan yasha shayi amma sai yatsine baki yakeyi, ya mararairaice murya tamkar zaiyi kuka, ALLAH Ammi nak'oshi. A'a mukarram kadaure kasha koda kad'anne, kaga rabonka da abinci tun jiya da yammafa, komai na rayuwa hak'uri yakeso, Addu'a suke buk'ata daga garemu kaji, ALLAH ya ku6tar mana dasu idan suna Raye. Hawaye suka ziraro bisa kumatunsa, Ammi ta share masa.. Yana shirin yin magana sukaji sallmar ammar, suka amsa, yashigo ya zauna. Ammi yarissina yagaida sannan yabama bobo hannu suka gaisa🤝, cikeda tausayi Ammar yake kallon bobo. Ka kwantar da hankalinka Abdulmaleek insha ALLAHU za'a gansu, yanzu inaso naji time d'in Daka kira Rahma kafin tatafi d'aukar Nawal?. Wayoyinsa yakwaso dukya yamik'ama Ammar Dan yanzun bayason yawanyin magana sosai. Bincike sosai Ammar yakeyi a wayoyin Bobo yanayi yana waya da office d'insu, bayan sun kammala yabama bobo wayoyinsa, ya ce, "kabar wayiyinka akunne daga yanzun Duk Wanda yakiraka zamu gani, zakuma mu iyabi ta wannan hanyar dangano ko waye. Jinjina kai kawai bobo yayi batareda yayi maganaba. Ammi ta ce, " Ammar karinga yima abokinka fad'a yaringa cin abinci jibifa yanda yaketa ramewa. Ammar ya ce, "kik'ara hak'uri Ammi insha ALLAHU zai ringaci yanzu yana cikin rud'anine. To ALLAH yasa Ammi tafad'a tana mik'ewa tabasu waje. Haka Ammar yatsare bobo yad'ansha shayin da soyayyen dankalin sannan yaymasa sallama yatafi.
Tafiyar Amma babu dad'ewa saigasu ya Hamza sudukansu. Guri suka samu suka zauna suna k'ara kwantarma da bobo hankali, yana kwance saman doguwar kujera yana jinsu, badai ya iya cemusu komai amma sunsan yana saurarensu, wayar bobo tafara wringing yayi burus da ita tamkar baijiba harta tsinke aka sake kira, ya ishaq ya ce, "kad'auka mana, 6ata fuska yayi tamkar zaiyi kuka amma baice komaiba, ganin wayar tana niyyar tsinkewa ya sulaiman yay saurin d'auka ya ce, " hello. Muryar data daki kunnensa CE tasakashi mik'ewa zumbur yana fad'in Rahma Rahma....... Kuna ina ne?.....miya faru daku?........ Aiikafin yafarga bobo ya warce wayar, muryarsa har rawa take ya ce, "Rahma Ku........ Bai k'arasaba wata muryar takatseshi da fad'in ba ita bace ta cancanta tabaku amsar tambayoyinku mine nan. Ku suwaye!!!?, Bobo yay maganar Afusace. Daga canma aka Daka masa tsawa, kai malam karka d'aga mana murya. Bobo ya ce, " kaga bawannan bane damuwata, miyasa kuka kamamin matana da d'iyata?, misuka muku?, waye yasakaku?, mukuke buk'ata?, idan kud'ine kufad'i konawane za'a Baku, pls karku cutar dasu. A'a a'a muba kud'i muke buk'ataba domin anrigaya an biyamu, kai kanka muke buk'ata, inkuwa bakazoba tom ran 'yarka da matarka zaizama fansar ranka amaimakonka. Bobo yarintse idonsa tareda cije le6ensa, saboda 6acin rai yagaza cewa komai. Daga can akace haba zaki kardai ace ka tsorata?, hhhhhhhh, bai kamata kaji tsoroba, munbaka daganan zuwa jibi idan bakazoba tom zaka tsinci gawar matarka da 'yarka, idan kuma kana buk'atarsu darai tom fine sai ka fanshi ransu. Saidai zuwan naka yanada sharad'i, wlhy koda wasa kada kayi gangancin zuwa da police zamu gane, na biyu saika taho zamu ringa fad'a maka hanya,, na uku idan ka 6ata mana lokaci zamu kacaccala matarka da 'yarka mu watsar, gashi kasakejin muryarta. Kafin bobo ya ce, "wani Abu saiyaji muryar Rahma cikin kuka tana fad'in dadyn Nawal karkazo pls, Dan ALLAH karka bada ranka akanmu, insha ALLAHU zanfanshi rayuwarku dagakai har Nawal, Nawal tana buk'atar mahaifi tunda tarasa uwa pls karka salwantar mata da ranka, Dan girman ALLAH karkazo, I luv you so much my Abdulmaleek. I luv you too my cute Rahma na, bobo yafad'a da saurin Baki,....kafin yakuma cewa wani Abu suka kwace wayar, cikin k'araji sukace kai wawa harka samu damar yimana soyayyane??. Wlhy kacika mana baki sai munmata fad'e hhhhhhhhhh dama gata daga gani zata bada feeling. Kaiiiiii!!!!!!!!!! Wawa, Bobo yadaka masa tsawa, wlhy kabari zuciyarka takuma kissima maka wani Abu akan matata saina tarwatsa kanka da bullet, na rantse maka da ALLAHn daya halicceni saina shayar dakai gidauniyar azaba, tabbas ni *_Zakine_* kujira zuwan zaki gareku, saina lak'umeku!!!!!!!!!, yanda yayi maganar cikin tsawa harsu ya ishaq da Ammi Appa su khursiyya duksun tsorata da yanayinsa, gabad'aya jikinsa yayi jajur abinka da fari, gashi jikinsa dukya mimmk'e, hakama jijiyoyinsa duksunyi rud'u², yay jifa da wayar, da sauri ya Hamza ya cafeta. Kowa yasan kuma ransa ya6aci kenan, k'arasawa yayi gaban Appa da Ammi yana yawaye ya ce, "iyayena kusamin Albarka zanje nataho dasu yanzun nan da kaina. Yanda yake magana dukya basu tsoro da tausayi, Ammi ta ce, " mukarram kayi hak'uri Ammar yazo kutafi tare, kai yagirgiza mata ya ce, "Ammi kedai sakamin Albarka kawai, basu musaba suka dafa kansa tareda saka masa Albarka da k'yak'yk'awar addu'a. Ya mik'e afusace zai fice, ya sulaiman yay saurin shan gabansa, wata irin hankad'awa bobo yayma ya sulaiman yay taga taga zai fad'i ALLAH yasoshi ya ishaq nakusa yarik'eshi yafad'o jikinsa. Bobo kam kota kansu baibiba yayo waje, yana fitowa ammar yashigo gidan, da sauri yatsayar da bobo, badan yasoba yatsaya yana kallon ammar dayaci wanka cikin shadda harda babbar Riga, wani d'an guntun tsaki bobo yayi danshi Ammar d'in yabashi haushin kwalliyar dayayi. Ammar baice masa komaiba yamik'o masa babbar Riga ta shadda. Galala bobo yatsaya kallon Ammar, wannanfa? yafad'a yana huro hanci. Kaga kasaka mutafi, Dan mungano Inda suke tasanadin wayar dakukayi yanzu, kasandai babu yanda za'ayi muje kai tsaye dole saimun canja kama gudun karsu San da zuwanmu su cutar dasu. Bobo yanajin haka yakar6i babbar rigar shaddar yasaka shima harda hula, duk abinda ke faruwa su Appa Ammi ya sulaiman ya ishaq ya Hamza khursiyya khairiyya duksun futo sunajinsu. Appa ya ce, " ALLAH yayi muku Albarka yayi taimako. Amin suka amsa. Bobo da Ammar dawasu police uku suka shiga mota d'aya, su ya ishaq ma mota d'aya, saikuma mota biyu itama duk police ne aciki amma da kayangida Dan kowa shadda yaci tamkar zasu d'aurin aure, ganin haka shima Appa saiya shiga motar su ya Hamza, su khursiyya sukace zasuje suma, AMMAR ya ce, "suyi hak'uri su zauna suyi ta musu addu'a. Ammi ma kuka takeyi, hakadai suka fice. Amota Ammar yake sanarma bobo yatura mutane biyu amashin dansuyi gaba. Jinjina kai bobo yayi Dan har yanzun ransa a6ace yake Musamman idan yatuno da maganar wawan nan wai Rahmar sa zata bada feeling, wlhy saiya cirema d'an iskannan hak'ora....
Da sauri yashige cikin wata gona ya6oye bayan bishiya, boss gafa wasu motocinan har guda hud'u suna zuwa. Akwai motar 'yan sandane?. A'a gskiya wad'annanma duk wankan shadda sukayi. Mtsoooww kaiwane irin wawane, bana gayamaka akwai wani d'aurin aure daza'ayi acikin k'yauyen damuke ba, na tabbata wannan d'aurin auren sukazo, angayamaka su wawayene dazasu taho tun yanzu?, ko ka manta yanzu muka gama waya dashi?, nasan saisunyi shiri sosai kafin su ce zasuyi gigin zuwa, tabbas nasan zuwa gobe saisunzo nan Dan haka karka damu da wad'annan motocin. Okey boss nafahimta, yafad'a yana gyad'a kai tamkar k'adan gare. Yana yanke wayar yaji anshak'eshi tabaya, ido ya zazzaro waje Dan mamaki, shikuma wannan daga ina haka? Yaya maganar azuciyarsa. Wani wawan naushi musaddiq yabama guy d'in tareda k'ar6e wayar, a ina suke?, musaddiq yatambaya yana k'ara shak'eshi. Zan zan zan fad'amaka kaga sakeni Dan ALLAH karka kasheni. Wani wawan mari yasake bashi, fad'amin ahaka, cikin Rawar baki yasanarma musaddiq, shikuma yakira su Ammar yafad'a musu. Musaddiq yakuma fad'in kunawane aka baza Dan kawo rahoton zuwanmu?. Mu mu mu mu goma shabiyar ne. Murmushi musaddiq yayi, yad'auki waya yakira sauran 'yan uwansa yace su bazu akwai sauran mutum goma sha hud'u.
_(ALLAH sarki musaddiq bayan Ammar yaturosu amashin su biyu, sunyi shiga k'auye kamar 'yan k'auyen gsk, shikuma yazagaye yakuma samun 'yansanda goma suka taho batareda sanin Ammarba, shine yanzu yakira su dansu bazu adajin)._ Su bobo kam sunatabin hanyar kamar yanda waya take nuna musu, suna zuwa daidai wani wajen mararraba wayar tatsaya wannan alamune na sun iso wajen. Mutum biyune suka fito suka k'arasa ga wani matashin saurayi dake tsaye yana kallonsu, da alama shima yana cikin mutum 15 da'aka baza Dan kawo rahoto, Dan kallo d'aya Ammar yay masa yagane bashida gsky. d'an saurayi Dan ALLAH tambaya Muke?. ALLAH yasa nasani yay maganar yanata zazzare idanu. Wani hanyar k'auye muke nema da ake d'aurin aure. Ajiyar zuciya saurayin yayi tareda wale baki, ya ce, "to to zan nuna muku, yana motsawa danufin nuna musu hanya d'ansanda d'aya yanuna masa bindiga, kana motasa zan tarwatsa kanka, ina kuke 6oye dasu?. Yawu saurayi ya had'iye ya ce, " zan nuna muku yanzun nan.... K'asa yay da bindigar yanda baza'a ganeba yatasashi gaba, suma su bobo suka fiffito, amma sun rarrabu.
Compilied By Abubakar Saleh AlQuyraemey Whatsapp Number 08138873799 Visit www.rumbunlabarai.com For More Complete Documents
Su Rahma suna zaune tana rungume da Nawal suka farajin k'arar harbin bindiga, da sauri takali Wanda yake tsaronsu, duk taron 'yan iskannan shikad'aine mai bindiga ahannu, ganin yana barci Dan tund'azu yake lodama cikinsa wuywuy, mik'ar da Nawal tayi ahankali daga jikinta, cikin sand'a tak'arasa inda yake him akujera zaune, tamik'a hannu ahankali zata d'auki bindigar saiya motsa, tayi saurin ja baya tamak'ale ajikin bango, zamansa yagyara yakoma barci, takuma kai hannu zata d'auka Nawal ta ce, "mo...... Da sauri Rahma tayi mata alamar tayi shiru, lek'awa tayi ta window saita hango k'artai biyu suna zuwa aguje, takuma hangawa d'ayan gefen ta hango uku, innalillahi tashiga ambata dantasan yau saidai ALLAH kam. Hannun Nawal takama da sauri suka shige bayin d'akin taisaurin buga k'ofar tarufe dak'yar.... Adaidai lokacin ogan yafarka yamik'e zumbur yanufi hanyar bayi, shigowar yaransa biyu da gudune yadakatar dashi.. Oga oga wlhy 'yan sandane...... Basu k'arasaba sauran ukun suka k'araso suma, 'yansanda wajen hud'u suna take musu baya, harbi ogan yayi, yasamu d'ansanda d'aya ak'afa, suma suka fara harbi, nanfa aka fara musayar wuta, suma 'yan sandan suka samu nasarar Harbin mutum d'aya acikin 'yan iskan. Ana cikin haka bobo yak'aso wajen, tuni duk sun cire Babar riga, bullet yak'arewa oga, 'yan sanda biyu kuma sun sami harbi, ga yaran oga sun k'aru Ashe sunada yawa, danbe aka fara tsakanin bobo dasu dansu Ammar sunacan nesa da wajen shikad'aine saikuma 'yan sanda biyu anharbi biyu.
Hummm masu karatu yaufa inashan kallo😳.
Dukan juna sukeyi sosai Dan suma gardawane majiya k'arfi babu abinda bobo zai nuna musu, gashi sunfisu yawa, sun daki juna duksun galabaita, kowa yaji ciwo sai sukaji k'arar harbi, gaba d'aya suka juyo Dan ganin Wanda yay harbi daga cikin d'akin, Rahma ce tsaye abakin k'ofa ta harbi Wanda yake k'ok'arin sokama bobo wuk'a ta baya, shikuma yana can hankalinsa nakan ogansu dasuke cin uban juna. Gaba d'aya sukayo kanta, ALLAH yabata sa'a takuma harbin wani ak'afa shima yazube, gani suka itama anyi kutubal da ita tadaki bango goshinta yafashe yafara jini. Adaidainan su Ammar suka k'araso da sauran gayyar 'yan sandan, dakuma 'yan dabar da aka kamo. Hankad'a Rahma musaddiq yayi da sauri Dan hango Wanda yabugata da bango yayo harbi. Fiyyyy bullet d'in yawuce tagefen hannunta, harya d'an ta6ata, tayi taga taga zata fad'i ya ishaq yay nasar rik'e hannunta. Gaba d'aya anyi nasarar kamasu, Nawal tafito dagudu daga inda Rahma tasakata ta 6oye, bobo yadurk'ushe k'asa tareda bud'e mata hannunsa tafad'a jikinsa, yarungumeta tsam yana hawaye. Papa yaushe kukazo?, wad'annan mutanen sunata dukan momyna, papa niko inata kuka ina kiranka, momyna ta ce, "su kasheta subarka da rai, kuma tana hana su dakeni.. Kowa kallonsu yakeyi cike da tausayi, bobo yad'ago ido yana kallon Rahma dake tsaye agefe itama tana kallonsu tana hawaye, murmushi yayi mata tareda mik'ewa tsaye, yaware mata hannayensa alamar itama tazo.................
*_luv you oll my fan's_* *_(((S)))....2017_* [11/12, 2:56 PM] mrs bilkisu: 👩🏻💻typing........
❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _•{🅱🅾🅱🅾}•_
*_NA_* _*Bilyn Abdul*_
_sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_*
*_gaisuwar takuce 'yan TASKAR LITTATAFAN HAUSA, alkairin ALLAH yakaimuku har gidajenku, ina sonku sosai wlhy, ALLAH yabar mana zumunci da k'aunar juna._* _luv u wazga wazga❤💋😂._
5⃣2⃣
Kafad'a ta d'an nok'e tana girgiza kai dantanajin kunyar mutanen dake wajen. Tayi k'asa da kanta tana kallon k'asa, bata ankaraba taji an rungumeta, ahankali tasauke ajiyar zuciya, shima ajiyar zuciyar ya sauke, cikin kunnenta ya ce, "haba my cute bakiyi missing d'inaba ko?. Batace komaiba saidai yanajin alamar murmushin datakeyi. Ya sumbaci wuyanta, Ya hamzane dayaga bobo na Neman ruftawa gakuma Appa awajen sai ya k'araso inda suke, ya ce, " baban soyayya kuzo muje gida saikuyi ko?. Da sauri Rahma tazare jikinta, bobo yad'an kalleta sannan yadawo da kallonsa ga ya Hamza, Yaya karfa kazama..... Hummm kodayake baradai nayi shiru kawai. Dariya ya Hamza yayi ya ce, "a'a fad'i karta kasheka. Um um bazan fad'aba narufa maka asiri dai, my cute kona fad'a miki?. Girgiza kai Rahma tayi tana murmushi. Ya Hamza ya ce, " karki damu Rahma cemasa yafad'a mana, nima saina tona aii yanzunnan. 'Yar dariya bobo yayi Yakama hannun Rahma suka tafi, ya Hamza yabiyosu abaya suka tafi. Yanzun ya Hamza da bobo da Rahma amota d'aya suka tafi, Nawal kam tana wajen Appa, tunda bobo yarungume Rahma Appa yakama hannun Nawal sukabar wajen yana murmushi.
Suna zuwa gida asibiti aka wuce dasu Rahma, Alhamdllh babu wata matsala saidai 'yan raunukan da Rahma taji, ya sulaiman ya dubata tareda basu magunguna sai gida. Tunkan su iso gidan yacika da dangi, su Rahma suna shigowa dangi suka rungumesu anata kuka, bayan gama murnar ganin juna Rahma tashige d'akinta tayi wanka tayima Nawal. Aka kawo musu abinci sukaci sukasha magani sai barci.
.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*. Haba ummi yazakice bandamu da 6atan su Rahma ba?, 'Yar uwatace fa, Dan ALLAH kibar fad'a kadama wani yaji zata gskyne. Oh da k'yarya nakeyi?. A'a ummi nidai bance kina k'aryabafa. Banza ummi tayi da ita, tajuya zata fita. Safna ta marairaice murya ummi toyanzu mikikeso nayi dazai sakaki farinciki?. Kafin ummi tabata amsa sukaji sallamar baseera. Tarisina ta gaida ummi, cikin fara'a ta amsa sannan tafice. Ummi na fita basira tamatso Kusada safna, k'awata mike faruwane wai naga ummi akanki?. Mtsoooww kibari kawai akan 6atan Rahma ne........ Takwashe komai tafad'a mata. Baseera tazunguri safna kefa banzace miyasa bazakice zakije kizauna da ita harta samu lfy ba, daganan basaiki gwada sa'arkiba kema. Kai hakanefa baseera, wlhy banyi wannan tunaninba ma, duk kaina yakulle baya kawo wuta. Aikin 6urrr inji tusa, kinga tashi maza ki shirya. Gudu gudu sauri Sauri safna tashirya kayan dazasukai fiye da sati d'aya, tad'auki duk abinda zata buk'ata ta shirya sanan sukanufi d'akin ummi. Tana zaune da Alana tana wayane da wata 'Yar uwar tata Dan tana bata labarin 6atan Rahma dakuma dawowarsu yau. Tsayawa sukayi harta gama, takalli safna da akwatin kekuma INA zaki da kaya haka?. Ummi zanje gidan Rahma na zauna danna ringa taimaka mata har jikinta ya daidaita, naga baikamata ace anbarta da dangin mijiba tamkar batada kowa. Baki ummi ta washe ta ce, "kai naji dad'i wlhy safna ALLAH yayimiki albarka, aihaka akeso, kuma tahakane zuminci ke k'ara dank'o. Ki gaisheta muma insha ALLAHU gobe zamuzo mu dubasu. ALLAH yakaimu ummi, saikunzo safna tafad'a tana murmushi. To saimunzo, baseera kigaida mutanen gidan. To ummi zasuji.
Safna da baseera suka fito sai gidansu Rahma, sanda suka iso mutane duksun tafi, daga Ammi da inna sai khairiyya da khursiyya suka rage, har k'asa su safna suka durk'usa suka gaida su Ammi. Safna ta ce, " Ammi inasu Rahman?. Murmushi Ammi tayi ta ce, "aii har yanzu barci sukeyi safna, yawajen su Maman taku?. Lfy lau suke Ammi, suma saigobe idan ALLAH yakaimu zasuzo. To ALLAH yakaimu lfy. Inazaku haka da akwati? Ammi tayi tambayar tana kallon safna. Safna tagyara zamanta tana k'ara marairaice fuska tamkar mutuniyar kirki, Ammi dama canayi bara nazo na zauna da ita harta samu k'arfin jikinta, Dan baikamata atakura su khairiyyaba ga bikinsu yana matsowa. Murmushi Ammi tayi ta ce, " lallai kinyi tunani Safna, ALLAH yay miki albarka. Bobo dake bakin k'ofar Rahma yana niyayyar fitowa yatsaya sauraren tattaunawar Ammi da safna. Ransa a 6ace yakalli Ammi suka had'a ido, yaturo baki gaba, murmushi Ammi tamasa tareda yimasa magana da idanu, wai karyace komai. Kauda kai yayi yana d'an sassauta turo bakinsa, shifa wlhy yatsani yarinyarnan, amma shine yanzu za'ace tazauna taredasu mtsoooww yaja siririn tsaki. Takowa yayi ahankali zuwa cikin falon, jin k'amshinsa da takunsa yasaka safna da baseera juyowa, kan ubancan kai, aii ba safnaba har baseera yau saida tashiga rud'ani. Dukda yad'an rame amma k'yawun haibarsa na nan, kuma yak'ara haske sajennan yakwanta luf luf, sai k'amshin turarensa ketashi afalon mai sanyin dad'i, har yazauna Kusada Ammi idon baseera da safna na Kansa, baseera ta ce, "a ranta lallai dolene safna ta haukace,” Ashe haka guy d'in ya had'u masha ALLAHU. Bobo yay d'an guntun tsaki Dan baya son kallo, ganin bazasu daina kallonsaba shikuma sun gundureshi, saiya katsesu dafad'in yakuke?. Dandanan suka dawo hayyacinsu danjin saukar muryarsa mai ratsa jiki da 6argo. Cikin in ina suka gaisheshi, ya amsa da lfy, tamkar yanda yasaba. Khursiyya da khairiyya suka fito saga kichin bobo ya kallesu, harkun mammala abincin?. Ya Abdulmaleek ai yau abinda kafiso muka dafa zakacidai ko?. Murmushi yamusu tareda gyad'a kai kawai. Suma dariyar sukayi suna mai farincikin ganin yayansu yau acikin farinciki, khairiyya ta CE, " Yaya tunda aunty Rahma tadawo yanzu saika Dage dacin abinci kayi k'iba. Harara bobo yasakar musu yana fad'in Ammi wlhy yarannan sun rainani. Ammi da inna suka tuntsure da dariya, inna ta ce, "Abdulmaleek aiko kura da 'ya 'yanta take wasa a daji, ammi ta ce, " wlhy kuwa inna. Ammi takalli su khairiyya ta ce, ''kutaso heebba mutafi gida hakannan ko?, tunda kungama aikin, fuska suka shagwa6e, khursiyya ta ce, "Ammi wai kina nufin harda mu?, harararsu ammi tayi hardaku mana, tunda ga safna nan tazo kukuma basaiku koma gidaba, dama ga hidima fall cikinku, dasafe saikuringa zuwa ko?. Su saima yanzu suka kuladasu safna dake zaune. Ammi takallesu tareda fad'in kuna 6ata mana lokacifa gakuma Deriver yana jiranmu. d'akin Rahma suka shiga sunata zum6ura baki, haryanzu su Rahma barci sukeyi abinsu. Hibba dake barci suka d'akko suka fito, suna son yarinyar sosai, yanzu haka komai NATA Yakoma d'akinsu, har anmaida mata suna Autar Ammi. Har mota safna da bobo suka raka ammi.