Kenza eBookz

Abdulmalik bobo complete na billyn abdul - Chapter 17

Abdulmalik bobo complete na billyn abdul - Chapter 17

Abdulmalik bobo complete na billyn abdul Chapter 17: Abdulmalik bobo complete na billyn abdul Chapter 17. Bobo yakalli wayarsa dake wringing ganin Ammar…

4,234 words

Bobo yakalli wayarsa dake wringing ganin Ammar yasashi d'aukar wayar da hanzari, gaisawa sukayi tareda tsokanar juna kamar yanda suka saba. Bobo ya ce, "dama kobaka kiraniba zan kiraka. To miya faru angon Rahma?. Murmushi bobo yayi, ya ce, " so inaga anjima zanshigo gidan saimuyi magana atsanake yanzu time d'ina k'urarrene nanda 'yan mintuna kad'an zanshiga wata shari'a. Okey babu damuwa to saina ganka, nima inada ganawa da Governor nanda minti 10. Hummm mutumina kuna sha'aninkufa, idan kukayi wasa duk ad'aure zakuje lahira Dan daku ake mulkarmu ak'asarnan. Dariya Ammar yayi ya ce, "masheranci aii kaima ad'auren zakaje indai hakane. Can abakinka d'an fatan tsiya sai anjima. Yanke wayar sukayi suduka suna dariya. Harzai ajiye wayar saikuma yafasa yakira Rahma. Tana zaune afalo ita kad'ai tana kallon wani India film, takalli wayarta dake wringing, ganin sunan dake a screen d'in yasakata murmushi, *_Nurulk'albee_*, d'auka tayi muryarta can k'asan mak'oshi tace amincin ALLAH ya tabbata agareka ya *_Nurulk'albee._* Wata sassanyar ajiyar zuciya bobo yasauke, murya akasalance ya ce, " kema amincin ALLAH ya tabbata agareki my *_Nusfulhayat_*. Ina fata kina cikin k'oshin lafiya da kuzari?. Alhmdllh sai godiyar ALLAH kam. Wani k'asaitaccen murmushi yasaki Wanda hartanajin sautinsa akunnenta, ya ce, "nagodema ALLAH da kika kasance cikin k'oshin lfy, kinga kenan yau za'a kar6e ni 100/100 abani kulawa ta musamman awajen barci. Kamar tana gabansa tafara buga k'afafu cikin shagwa6a ta ce, " nidai a'a wlhy inajin tsoro kuma har yanzu wajen akwai zafi. Yanda take masa magana cikin shagwa6a yasaka jikinsa yin sanyi, k'ara lafewa yayi acikin kujerar yana shak'ar kamshin turarensa dana office d'in, yakuma narke murya can k'asan mak'oshi haba my Angel kedai kincika tsorone kawai, amma yau kwana hud'u ace haryau anajin zafi?, kodai ana gudunane?. Hannu tasaka tarufe fuska wai ita kunya kamar tana gabansan, nidai Dan ALLAH kabarmin wannan maganar banaso. 'Yar sassanyar dariya yayi harda shashsheka wadda tasaka Rahma shagala tana saurarensa, ya ce, "shikenan idan nadawo gida zamuyi aii, kafinma nadawo kisaka d'iyarki tayi barci, ummuch💋 yamannama wayar kiss, batareda yajira amsartaba ya yanke Kiran. Lumshe ido Rahma tayi tana murmushi, afili ta ce, ''kai maza sai'a barsu sudai ko kunya basaji?. Shimadai a can murmushi yayi, yamik'e yana had'a takardu, yad'auki k'atuwar rigarsu ta lauyoyi tareda hular yarik'e sannan yad'akko siririn farin Gil's d'insa yasaka yafice domin gabatar da shari'a...............

*_luv you oll_*. *_(((S))).........2017_* [11/12, 2:58 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ _•{🅱🅾🅱🅾}•_

*_NA_* _*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_*

*_masu karatu bara namuku gulmar Xoxo da 'Yar ficika,😎 hummm Xoxo cedai Xoxo cedai da Yar Ficika, saimukaje gidan Hafsat Rano aka kawo mana gasashshiyar kaza da lemo🍗🍹🍾hummm ina gaya mukudai, shikenan dai shikenan dai, sai.....🙊um bara nayi shiru kar zarah Bukar da hajja sufad'a musu gobe su sassambad'i k'eyata alungu🏌, kekuma Rano saura kifad'a ehe♀😏._* _😂luv you so much, my sweet sisters, Hafsat xoxo, Hafsat Rano, 'Yar Ficika & Zarah Bukar, hajjace, Ayusha ilyasu, gaisuwa agareku dafatan Alkairi._ 😘😘😘😘😘👌🏼.

6⃣1⃣

*_5:12pm_* bobo yamik'e tareda harhad'a takardun dazai buk'ata agida, yacire laptop d'imsa daga caji yasaka a jakka, bayan yagama had'a komai yakashe kayan wutar office d'in sannan yad'auki rigarsa ta lauyoyi ya sak'ala ahannu, yarataya jakar aikinsa akafad'a yafito. Da sauri Kamilu yataso yana fad'in oga kafito?. Nafito kamilu, zan wuce gida kuma. Kamilu ya washe baki tareda kar6ar key d'in hannun bobo ya kulle k'ofar, fitowa sukayi har wajen mota yarakishi, Dan tuni sakatariya Madeena tana gida, k'arfe hud'u da rabi yake sallamarta ita. Saida yashiga motar sannan yad'ago yana kallon Kamilu, to kashigo muwuce mana Dan naga garin kamarma hadarine. Dariya Kamilu yayi yabud'e mortar yashiga yana fad'in oga ai damunar tafara kankamane, nanda 'yan satittika zakaga ruwa yafara wadata. Murmushi kawai bobo yayi danyasan surutun Kamilu baya k'arewa, ahankali yake Murza kan motar yana kuma sauraren karatun alkur'anin dake tashi amotar cikin k'ira'ar shriek Abdurrahaman sudes, har k'ofar gida yakai Kamilu yamik'a masa kud'i yana fad'in gashi asaima uwargida kaza. Cikin washe baki Kamilu yakar6a yana godiya, wannan dalilin yanasakashi k'ara ganin kimar ogan nasu, kwatakwata bashida k'yankyamin talaka bare girmankai irinna alhazan birnin nan, gashida alkairi kullum baya gajiyawa. Har bobo yafice daga anguwar Kamilu natsaye yana kallonsa, saida ya6acema ganinsa sannan yashiga gida cikeda farinciki. Ganin hadarin nak'ara tasowa yasaka bobo k'ara gudun motarsa cikin 'yan mintuna k'alilan ya Isa gida, guri yasamu yay parking sannan yakwashi tarkacensa yanufi ciki, zuwa sannan anfara yayyafi. Rahma tana kichin Dan k'ok'arin had'a abincin dare taji ana kwankwasa k'ofa, fitowa tayi da hanzari dakuma tunanin wanene haka? Acikin hadarinnan. Batayi gaggawar bud'ewaba saida ta ce, "wayene?. Jin haka yasa bobo niyyar tsokanarta, ya mak'e murya kamar mace ya ce, " nice hafsat Xoxo budurwar bobo. Gabantane yafad'i gakuma wani k'ululn bak'inciki aranta, cikin masifa ta ce, "ai bayanan saiki koma sai sanda yadawo kizo. Pls madam ki taimakeni ruwafa na jik'ani. Yo ya kasheki mana, Rahma tafad'a ak'ufule tareda juyawarta kicin. Magana yasakeyi yaji shiru, ga ruwa yafara jik'ashi, da Sauri yanufi baya yaduba ko k'ofar kichin abud'e take ta baya, yana turawa tabud'e, yashigo da hanzari Dan tasowar wata iska mai sanyi. Da sauri Rahma tajuyo dansan ganin waye, ido tad'an zaro waje Dan mamaki, sannu dazuwa tayi maganar a cunkushe Dan tuna abundana yafaru yanzu tsakaninta da Xoxo. Dariya tabashi danganin kishi k'uru k'uru kwance afuskarta, amma saiya gimtse ya ce, " yawwa. K'arasowa tayi inda yake tsaye takar6i jakarsa da rigar, sai wani kakkauda kai takeyi. Lfy kuwa?, naganki haka?. Lfy lau tafad'a tana nufar cikin falo. Binta yayi da kallo yana murmushi, zame rigar suit d'insa yayi danta d'an jike yaja kujerar dake kicind'in ya zauna yana cire takalminsa. Rahma tadawo kichind'in ganinsa azaune yasata binsa da kallon mamaki, dukda yaji shigowarta amma bai d'agoba saida yagama cire takalmin yad'ora k'afarsa fara Sol Asama. Rahma ta ce, "azuciyarta, hummm jik'afa kamar ba'a takata ak'asa........ Bobo yad'ago shima yana kallonta, nikam Nusfulhayat wana ganin ak'ofar falo tsaye kamar mace?. Baki Rahma taturo gaba, ta kauda kanta gefe, nima bansaniba. Ido yazaro waje bakisanibafa kikace?, datazo batayi Knocking bane?. Hawayen datake mak'alewa suka zubo akumatunta, cikin shagwa6a ta ce, " bakai tazo nemaba, kuma ta ce, "budurwarkace ita. Yaso ya shek'e da dariya amma saiya dake, yamik'e da Sauri yana fad'in amma kika barta awaje ruwa na dukanta, yanzunan cute sokike kifara korarmin 'yammatane?, kwasar takalmansa yayi ahannu yawuce cikin falon. Rahma taduk'e kanta ajikin cabinet d'in kicin tana kuka. Shikam bobo d'akinsa yanufa yana 'Yar dariyar farincikin ana kishinsa Ashe?, kayansa yacire yafad'a wanka. Itakam Rahma saida taci kukanta ta more sannan tad'ago tacigaba da girkin, jitake dama batayi MASA girkinba, tsaf ta kammala komai tajere a dinning sannan tagyara kichind'in tsaf. Dubanta takai ga agogon falon, ganin lokaci yayi nisa tanufi d'akinta ta tatada Nawal dake barci Dan magriba ta k'arato, hannunta taja zuwa bayi tawanke mata fuska sannan suka dawo falo tabata ruwa.......hummm ni shinema yau ko ruwan ba'a baniba bare akula dani, maganar bobo tadaki dodo kunnenta. Da Sauri Nawal takwace hannunta taje tarungumeshi tana fad'in my papa oyoyo. Shima d'aukarta yayi yad'aga sama, my baby INA kika shigane bangankiba?. Papa barci nakeyi yanzu momyna ta tadani magriba tayi. Oh 'yargatan momynta yafad'a yana sumbatar kumatun yarinyar. Rahma dai tana tsaye tana kallonsu cikeda sha'awa, hannunsa yasa yakare fuskar Nawal sannan yad'agama Rahma gira, kauda kai tayi tanad'an murgud'a baki. Ya ce, "Niko?. Nidaifa banceba ehe, itama tafad'a kamar badashi takeba. Murmushi yayi sannan yadire Nawal, baby sauka nasha ruwa tunda an hanani. Da d'an gudu Rahma taje gaban firij tad'akko ruwa da cup takawo MASA. Bobo yayi dariya tareda fad'in ashedai ana tsoron kishiya. Gaba tayi tashige d'akinta tana tura baki, shikuma yazuba ruwa a cup yasha yana dariya. Nawal ta CE, " papa yaushe zamu tafi gidan Ammi?, gobene bikinsu aunty khursiyya. Saida ya shanye ruwan sannan ya ce, "jekiyi sallah idan nadawo masallaci zan sanar miki. d'akin momynta tanufa shikuma yadoshi hanyar fita, yabud'e sannan yad'an lek'a, ruwa akeyi sosai Dan haka yahak'ura yajuya d'akin Rahma dansuyi jam'i. Shigar tasa tayi daidai da fitowar Rahma daga bayi, da alama alwala tayi, baice da ita komaiba ya gyara shimfid'ar sallayar, itama ganin haka yasa tagane abinda yake nufi. Yana gaba suna baya itada Nawal yajasu jam'in magriba. Bayan sun idar Rahma ta d'akko alkur'ani tana koyama Nawal, shima yana zaune yana kallonsu cikeda jin dad'i, har lokacin sallar isha'i yayi suka mik'e domin gabatarwa. Saida yamusu doguwar addu'a sannan kowa yamik'e suka fito falo. Bobo yazube saman kujera yana fad'in wash ALLAH na, Nawal tazauna kusadashi my papa bakada lafiyane?. A'a baby nagajine kawai....... ga abinci fa....Rahma takatse musu zancen tana kallonsu. Fararen idanunsa yad'ago yana mata wani shu'umin kallo, ta kauda idonta daga kansa shima saiya ta6e baki. Nawal tamik'e shikuma ya ce, "nidai nagaji bazan iya hawan dining ba. Yanda yay maganar ashagwa6e saiyabama Rahma dariya, dinning tanifa tana murmushi, komai saida suka sakko dashi tsakkiyar falon. Tana niyyar zuba abincin taji ya ce, " kihad'amana a filet d'aya kawai, batace k'alaba tacigaba da zuba abincinta, bayan tagama ta tatura gabansa. Gyara zamansa kawai yayi yafara cin abincin atsanake, Rahma azuciyarta ta ce, "guy d'innan komai yahad'a, cin abincinsama abin kallone. Hakadai suka gama cin abincin anutse, daganan aka koma kallo, Nawal najikin papanta kwance yana shafa kanta ahankali. Tuni barci yad'auketa, yakalli Rahma dake kwance a 2sita tana game da wayarta, momyn Nawal zoki d'auketa tamin barci ajiki. Mik'ewa Rahma tayi domin d'aukar Nawal amma saiya jawota ta zauna akusadashi, hannunta yarik'e gam sannan yashiga k'ok'arin janye Nawal daga jikinsa cikin dabara. Rahma ta turo baki gaba, yatsu biyu yasa ya d'alli bakinta, da sauri tasaka hannunta awajen Dan zafi, cikin shagwa6a ta ce, " wayyo bakina. Habawa yarinya nagafa kamar kinfara rainani, bobo yay maganar yana matseta ajikinsa. Shinwai ni sa'ankine?. Da sauri Rahma ta ce, "a'a dantaji zafin d'allar mata baki dayayi. Ya ce, " to miye kiketa wani kumbura fuska?, nifa babu komai kaina yake ciwone. Ayya my Angel sorry, namiki kamu?. Kai tad'aga masa alamar eh. Ahankali ya kwantar da ita acinyarsa, maimakon yamata kamunkai saitaji bakinsa akan nata, tabud'e baki zatayi magana yasamu damar zira harshensa......

🚶🏻‍♀baya najuya musu karsuce nacika saka musu ido. Saida aka d'auki tsawon lokaci sannan na juyo Dan inada tabbacin komai ya kammala. Raham nagani tana cusa kanta acikin bobo suna dariya, da alama wani abun yafad'a mata taji kunya. Ya ce, "kinga tashi muje mu kwanta, mik'ewa tayi cikin jin kunya, ta d'auki Nawal takai d'akinta, kayan barci ta canja mata itama ta canja, tana k'ok'arin hayewa gado saiga Bobo yashigo sanye cikin kayan barci shima. Kallo d'aya tamasa ta kauda kai, shima baibi ta kantaba yamatsa kusada Nawal yamata kiss akumatu sannan yaja bargon yarufeta yana fad'in saida safe d'iyar albarka. Itadai Rahma batace komaiba Dan harta kwanta agefen Nawal, jitayi anyi sama da ita, tafara wutsil wutsil da k'afafu wayyo ya Abdulmaleek kabarni barci nakeji, nidai yau bazanbar Nawal ita kad'aiba, pls kabarmu mu kwanta. Bai sauraretaba har yakaita d'akinsa yadire agadon, tana k'ok'arin tashi yasa k'afa ya danneta, wayoyinsa yad'auka ya kashe sannan shima yahaye gadon yakwanta tareda jawota jikinsa. Itakam tuni tafara kuka zuciyarta cike fal da tsoro, jin yafara mata abinda hankalinta bazai d'aukaba tafara kuka tana zame zame. K'ara matseta yayi ajikinsa yana k'ara rud'a jikinta da sakwanni wad'anda sukeyin tasiri ajikinta da zuciyarta, amma kuzarinta na k'ok'arin turesu domin ku6tar kai. Ina mutumin naku baiko saurara mataba Dan tuni jikinsa da ruhinsa sun Lula duniyar begen aika aikar dayakeyi, da zafifi yake aikamata sak'wannin soyayyarsa, kafin tafarga yad'auki hanyar mallakarta daga ita har zuciyarta Dan tuni itama tabada kai dukda d'unbin tsoro da fargaba dasuka kanainaye ilahinrin lungun da sak'on zuciyarta.

_Hummm masu karatu nima bara naja camryn 🚶🏻‍♀k'afafuna nanufi wajen angona kuma sarkina mamallakin zuciyarta da ruhina_ *_{Abdus'salam)_* d'ina adon zuciyata😘😂.

_washe gari_ Hummm yaukam na iso amakare Dan natarar har Rahma tagama tsaftace ko ina na gidan, takuma had'a breakfast mairai da lafiya. Zaune na isakesu a dinning suna karyawa, Rahma da bobo dasun had'a ido saisu sakarma juna murmushi, bobo kam harda d'aga mata gira, takan kauda kai tana murmushi Dan gudun kar Nawal tafahimci wainar da suke toyawa. Bayan sunci sun k'oshi suka mik'ewa tareda yin hamdala ga sarkin sarakuna mai k'yauta da k'ari. Bobo yad'auki jakar aikinsa ya rataya, yaukam sanye yake cikin wani farin yadi mai laushi, Wanda akaima ado da bak'in zare, rigar dakad'an tawuce d'uwawunsa amma yayi d'as aciki kamar kazauna kayita kallonsa, _Hummm karkuma ka kalla k'ilu tajawo bau, Rahma ta ce, "kana kalan mata miji🤥, my Xoxo ki kalleshi kad'an keda Rano_o😎. Rahma tasakama Nawal jakarta abaya sannan tad'auki d'an kwandon abincinta suka fito, itama Rahma sanye take da shadda ruwan k'asa mai turuwa zani da Riga, tasaka farin hijjabi har k'asa Asama. Saida suka fara sauke Nawal a school sannan Bobo yad'auki hanyar gidan Appa. Juyowa yayi ya kalleta hayateena awajefa zan saukeki dannayi latti. Itama kallonsa tayi sannan ta kalli agogon motar ta ce, " k'arfe 7:34am yanzu". Eh nasani, sonake naje office dawuri yau, nayi duk aikin dazanyi zuwa 4 nadawo gida mukasance tare. Hannu Rahma tasa tarufe fuska tana 'Yar dariya, ALLAH kana bani kunya. Murmushi yayi idonsa atiti ya ce, "tom nadaina baki kunya Nusfulhayat d'ina mai kuka, yaya Dan ALLAH kabini ahankali, daddyn Nawal wlhy yauma a kwai zafi, wayyo ummina kizo ki cecen........... Bata bari yak'arasaba tasaka MASA kukan shagwa6a. Ohh sorry my cute nadaina fad'a, cikin dariyar shak'iyanci yay maganar. Maigadi yabud'e masa gate yashiga, ko gama tsayawa da motar baiyiba tafice tayi cikin gida. Binta kawai yayi da kallo yana murmushi, afili ya ce, "wato idan ka auri yarinya k'arama tana maka ta6ara kaima saika zama ta6ararre, ya shafa sajensa daya kwanta luf, yad'an lumshe ido yana fad'in ALLAH yak'arama ANNABI daraja da fadila da Wasila. Rahma kin mallake *_Barrister Abdulmaleek Aliyu Abdulmaleek hamshak'i_* gaba d'ayansa da komai nasa, kin mantar dani damuwata gabad'aya, ya ALLAH kak'ara mana soyayyar juna, kakuma nisanta shaid'an daga garemu.

Na ce, " Ameen bobon Rahma.

Fitowa yay shima yanufi cikin gidan, babu kowa afalon sai kamshi dake tashi da sanyin AC. Shiru yay atsaye yana nazarin gidan, sallamar Baba hansai mai Aiki yasakashi juyowa, ta ce, "a'a Alhaji kaine agidan. Murmushi yamata sannan yarisina ya gaisheta, baba hansai masu gidan basu tashi bane?. Khairiyya da khursiyya sun tashi tun d'azu, amma banga Ammi ba gsky. Okey bara to nawuce office kawai saina dawo. To Alhaji bazakaci komai bane?. Ahhh baba nidanake da mata, ai tuni nafita agandu. Dariyar jin dad'i baba hansai tayi, ta ce, " to madallah Alhaji, ina Nawal da mamanta?. Nawal na makaranta, mamanta kam tana nan cikin tare mukazo, kud'i yazaro a aljihu yamik'a mata yafice. Itakuwa tarakashi da k'yawawan addu'oi.

Rahma kam koda tashigo taga falon babu kowa saita wuce d'akinsu khursiyya, cikeda ihun murnar ganinta suka tashi suka ruk'unk'umeta, akan gado suka zube suna dariya. Daga nan hira suka farayi. fitar bobo badad'ewa safna tafito daga bayi, dama tana wanka sanda Rahma tashigo. Rahma ta gaisheta, da k'yar ta amsa, itakam batabi takantaba Dan abunda su khairiyya suke nuna mata ya d'auke hankalinta. Khursiyya ta ce, "aunty Rahma wai waya kawokine?." Ya Abdulmaleek mana Rahma tafad'a tana dariya. Kai yana ina?. Inaga yakoma Dan yace dama bazai shigoba sauri yakeyi. Ajiyar zuciya Safna ta sauke aranta ta ce, "yagama guje gujensa yazo yasameni daram. Sudai su Khairiyya dabasusan tanayibama hirarsu suketa zugawa suna kwasar dariya kamar wasu k'awaye.................

*_💃🏻Taka rawar gani akalla kome kayi kanka duniyace, mai jimirin zama cikinta, shike zuga kansa d'an magori._*

(zancenka haka yake nura m inuwa😎).

*_luv u oll_* *_(((S)))........2017_* [11/12, 2:58 PM] mrs bilkisu: 👩🏻‍💻typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣ 🅱🅾🅱🅾

*_NA_* _*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_ *_Abba Gana_* *_Batul mamman_* *_Billy giro_*

*_yau gaisuwar da shafin duk nakune sister Fertymerh xarah & Nafi Anka, alkairin ALLAH yakai muku aduk inda kuke, bilyn Abdul na gaisheku tareda bobon Rahma._* _I Luv you manya manya😘😂_ 6⃣2⃣

Sai wajen k'arfe biyar su bobo suka dawo gidan, kamar had'in baki suka dawo kusan lokaci d'aya suduka hud'un, bayan kowa yafito daga motarsa suka gaisa cikeda k'aunar juna. Ya Hamza ya ce, "lallai gida yafara kar6ar bak'i irin wannan hayaniya. Dariya sukayi gabad'aya, ya ishaq ya ce, " tokumu k'arasa ciki.. Cikin falon suka nufa suna 'Yar hirarsu da dariya.

Na ce, "masha ALLAH, biki ya kankama Dan falon yad'an cika da bak'i wad'anda suka iso yau, ga hayaniyar yaransu ya ishaq daketa wasa da yara sa'anninisu bak'i.

Su bobo suka rissina suna kwasar gaisuwa, kowa kallonsu yake cikeda sha'awa, bayan gaisuwa aka ta6a 'Yar hira da tsokanar juna, shidai bobo banda murmushi babu abinda ya iya, dama haka yake ko tsokanarsa kakanni sukeyi iyakarsa murmushi, amma baya iya maida murtani, saidai 'yan uwansa idan suna kusa su kare masa. Yanzuma wata 'Yar tsohuwa ke tsokanarsa, ta ce, " mai sunan Alhaji wai kaidai kana nan babu canji?, maganama wahala take maka bare dariya?. Nanma murmishi kawai bobo yayi kamar yanda yasaba baice komaiba. Ya sulaiman ya ce, "Hajiya iya aii maganar Abdulmaleek tsada gareta saikin saya da kud'i. Yo sule mizanyi da maganarsa nikam barema na siya, wannan sai matarsa dai amma baniba. Dariya suka saka gabad'aya falon. Bobo Yakama gemunsa nagayu yana shafawa fuskarsa cikeda murmushi, ganin zasu saka rayuwarsa gaba yamik'e ya haye saman benen, aiko suka rakashi da dariya, ya ishaq ya ce, " Hajiya iya kinga kin koreshi?. Isahaqa ai dankar yayi maganane yatashi, nibansan halinwa mai sunan Alhaji yakwasoba?, tunda nake ban ta6a ganin muskilin mutum irinsaba, mifa zan iya k'irga maganarsa mai tsawo danaji atsawon rayuwata, mutum kulum dund'un dunkum, sai murmushi shima idan ya gadamar yi. Dariya aka sakeyi, su ya Hamza suka mik'e suna dariya, suma sama suka haura, cikin dariya da zolaya ya Hamza ke kiran Dund'un Dunkum! Kana inane?. Bobo dake zaune kusada Ammi yaturo bak'i gaba, ammi kingansu ko?, wlhy nasan dani suke. Murmushi Ammi tayi kafin tabashi Amsa su ya sulaiman suka shigo d'akin suna dariya dacigaba dakiran dund'un Dunkum. Ya Hamza ya kalli bobo haba Dund'un Dunkum ya munata kira kaki amsa mana?. Hararsu yayi cikin sigar wasa, ya ce, "halan faratun tsohurcan ce tafad'i sunan nan?. Ammi dake k'unshe bak'i tana dariya ta rankwashi kan bobo, mukarram k'aniyarka wace faratun?.. Uhhhchch bobo yafad'a Dan zafi yana dafe kai, wayyo Ammi ALLAH da akwai zafi. aidama dankaji zafin namaka tayi maganar tana k'ara kai masa wani rankwashin. Da Sauri ya kauce, su ya ishaq suka saka dariya, gefe bobo Yakoma yana turo bak'i kamar wani k'aramin yaro, sai shafa Inda Ammi ta rankwasheshi yakeyi. Sudai su ya hamza dariya suketa masa. Ana cikin haka Appa yashigo d'akin da sallama, duk cikin dariya suka amsa harda ammi, Amma banda bobo dake gefe zaune ya shagwa6e fuska. Tofa dariyarmi kuma akeyi uwa da 'yayanta?, Appa yafad'a yana zama abakin gadon Dan duk su ya Hamza suna ak'asan kafet ne zaune. Bak'i bobo Yakuma turowa ya shagwa6e fuska kamar zaiyi kuka, Appa nifa sukema dariyarnan. Kai kai kowa ya saurara, yazaku tasamin babana a gaba kuna dariya?, haba Ammi harda ke?. Babana zonan naji miya faru?.. Tasowa bobo yayi yazo yazauna kusada k'afafun Appa, yad'ora Kansa bisa cinyarsa, Appa yasaka hannu yana shafa kan bobon dayawani narke kamar yayayye. Babana mikayi ake maka dariya haka?. Appa ba Hajiya iya bace tacemin wai Dund'un Dunkum shine suka tasani gaba da dariya, ita kuma Ammi Dan nacema Hajiya iya 'Yar fara shine tarankwasar min kai, kumafa kaina harya fara ciwo. Shima Appa sunan yabashi dariya wai Dund'un Dunkum, amma saiya gimtse saidai yayi murmushi, yacigaba da shafa kan bobo kaga mukarram d'ina barsu duksai na Rama maka, kowa saimun za6i suna sannan musaka masa. d'agowa bobo yayi yana dariya shima, aii Appa harnama tanadi sunan dazan saka musu sai ranar deener zan fad'a idan za'a gabatar da manyan yayye yakare maganar dayimusu gwalo. Appa yasaka dariyashida Ammi, sukam su ya ishaq kowa ya tsaya da dariyarsa suna hararar bobo Dan sun San zai iya aikatawa sarai. Ya sulaiman ya ce, "haba bobon Ammi garadai kafad'a anan komai ya wuce. Hum'im ban yarda da wayonba a can zan fad'a dankuji ehe. Kaga sulaiman barsa yafad'a d'in , ALLAH yakaimu muma aisaimu fad'a, muce INA yayansu Amarya Dund'un Dunkum. Appa ka gansuko?, bobo yay maganar cikeda shagwa6a. Yanzunkam kowama saida yadara harsu aunty Rasheda dake k'ok'arin shigowa Dan gaida Appa, dama duk suna tsaye tun d'azun sunajin diramar family d'in, kowa sai kunshe bak'i take tana dariya dankar ajisu, zuwa yanzun sun kasa rik'eta Dan haka suka sheke da dariya suduka suna shigowa cikin d'akin. Ya Hamza ya ce, "ALLAH bobo kaji kunya, wai yaushene zaka daina shagwa6ar nan takane?, Rahma kina fama gsky. K'asa Rahma tayi da kanta tana dariya, Dan maganar ya Hamza tabata kunya. Bobo ya kalli Rahma dake dariya tana to she bak'i da hannu, ba k'aramin birgesa tayiba. Safna ma dai yau ba abarta abayaba Dan dariyar takeyi, ba k'aramin birgeta shagwa6aar bobo tayiba. Saida aka tsagaita da dariya su Rahma suka gaida Appa, ya amsa fuskarsa wasai. Mik'ewa su Aunty Sameera suka fara da zummar Fita su basu waje. Appa ya ce, " a'a INA zakuje kuma?, kuzauna ayi hirar zumunci asamu ladan juna, komawa sukayi suka zazzaauna cikeda kunya da k'aunar sirikan nasu masu kamala da dattako. Hira aka cigaba dayi cikin farinciki har aka kira sallar magriba kowa ya mik'e mazan suka wuce masallaci, sukuma kowa yayi alwala sukayi agida.

Basu dawoba saida akayi isha'i. Safna dake la6e ajikin motoci tayi saurin rik'o rigar bobo. Da Sauri yajuyo dansan ganin waye?, ganin Safna yasashi saurin zare ido, ya maida kallonsa gasu ya ishaq yaga babu Wanda yajuyo harma sun shige falo, hamdala yayi azuciyarsa dabasuga aika aikar da Safnar tayiba. Juyowa yayi yana kallonta fuska a gimtse ya ce, "sakarmin Riga. Babu musu tasaki Dan gizagon fuskarsa yabata tsoro, ta marairaice fuska kamar zatayi kuka ta ce, kacika "alk'awari. Yagane mitake nufi amma dukda haka saiya yatsine fuska ya ce, " alk'awarin mi?, ke nifa kin addabawa rayuwata. Safna ta marairaice fuska saiga hawaye sharrrr, ta ce, "bobo kana wulak'antani saboda ALLAH ya jarabceni da Sonka ko?, pls ka taimakeni ka taimaki rayuwata, wlhy sonka zai kasheni Abdulmaleek, bana iya barci, Sonka yana neman haddasa k'iyayya tsakanina da 'Yar uwata, Dan ALLAH karda kayadani Abdulmaleek wlhy Sonka zai halakani, inasonka INA Sonka fiyeda son dAnakema kaina..... Takasa k'arasawa saboda kuka dayaci k'arfinta. Shikam tsayawa kawai yayi yana kallonta, zuwa yanzu tafara basa tausayi, jiyayi zuciyarsa tana shawartarsa daya taimaketa koda da nasihane k'ila tagane ta farka daga nannauyan barcin daya d'auketa. Yad'an lumshe idanunsa yabud'e akanta, kinga tashi yafad'a cikin muryarsannan mai dad'i da amo. Safna ta tashi tsaye tana share hawayen fuskarta.

A can ciki kuwa saida su ya sulaiman suka zauna sannan sukaga babu bobo. A'a INA Abdulmaleek ya tsaya?, cewar ya ishaq. Kasansa shida baba mai gadi yanzu haka yana can. Ammi ta ce, "Rahma jeki kira mijinki yazo yaci abinci tukunna saiya tafi suyita hirar. Akunyace Rahma tamik'e, zata fita Appa yafito shima daga d'akinsa, ya kallesu ya ce, " a'a INA mukarram d'in?. Gashi can antafi kiransa wajen baba mai gadi. To Aida kun k'yalesa babu dad'i suna hira kuma akatsesu, shima bazaiji dad'iba malam salen, daga yau kar a k'ara haka kunji?. Insha ALLAHU Appa baza'a sakeba suka had'a baki wajen fad'a.

Rahma kam tana fita domin kiran bobo, harta kusa tsakkiyar gidan saita hango safna da bobo tsaye safna tana masa murmushi, badai ta hango fuskar bobo ba Dan ya juyasaiata baya, Dan haka batasan shi miyakeyiba, amma wata zuciyarta tana shaida mata shima murmushi yakeyima safna, tsayuwar sojan badakkare tayi, bata gama farfad'owaba ta hangosu sun nufi hanyar lambun gidan, jitai hawaye nabin kumatunta, yaukam abinda take zargi ya tabbata, inhar bobo da Safna ba soyayya sukeyiba a6oye mizaisasu ware kansu alambu kuma arin wannan lokacin?. Ta share hawayenta tareda cije le6enta da k'arfi, juyawa tayi takoma cikin gidan, ta daure ta ce, "yana tareda baba suna hira awaje. Appa ya ce, " kinga Rahma barsa kawai, idan sun gama yazo yaci abincin. Jinjina kai tayi cikin ladabi ta ce, "to Appa." Amma azuciyarta saitace aibama saiyaci abinciba soyayya zata k'osar dashi, d'akin su khairiya tashige tashiga bathroom tasha kukanta San ranta, zuciyarta sai tafarfasa takeyi Dan bak'in ciki, jitake gaba d'aya yau tatsani bobo dakomai nasa. Haka tasha kukanta, bata fitoba saida taji aunty ummy na kwala mata kira tazo suci abinci, wanke fuskarta tayi tafito tana murmushin yak'e, ganinan aunty ummy wani abune yashigarmin ido shine nake cirewa. Ayya sannu yafita ko?. Eh ya fita aii ruwa naita sakawa. To sannu, muje muci abinci ko. To kawai tace mata suka fito falon k'asa inda kowa yake har Ammi, mazan ne kawai babu suna sama tareda Appa. Aunty Sameera ta ce, "a'a INA safna wai?. Da sauri Rahma ta ce, " tana waje tana waya, aii muci abincinmu kawai wannan ba yanzuba, idan tafara waya sai ALLAH. Dariya sukayi gaba d'aya, aunty rasheeda ta ce, "wlhy kubarta ta soye abinta, itama muje musha biki, tunda tak'i bobon mu, madai gani ko guy d'in nata yafishine haka?. Babu Wanda yace komai saidai anyi dariya, harda Rahma datayi na yak'e, tasan sarai habaici aunty Rasheeda tayima Safna, amma bataga laifintaba tunda itama ga aunty Safnar can suna cin dunduniyarta itada mijinta datad'auki so ta d'ora masa ayanzun. Hakadai sukecin abincinsu, Rahma tanacine kawai badan dad'iba, amma jitake kamar tana cin magani.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull