Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 19
Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 19: Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 19. Na rufe ido ina dariya, ta tambaye ni sunansa da kuma inda muka…
3,373 words
Na rufe ido ina dariya, ta tambaye ni sunansa da kuma inda muka hadu na fada mata komai, a take yanayinta ya sauya, sai ta karbi wayar hannuna tace zata aje sai idan mai gidanta ya dawo kasancewarsa matafiyi, idan sun tattauna abun da ya dace zata ba ni wayar, ban jidadi ba amman haka na daure na cigaba da waya da Khaleepa da wayar mai aikinta. Wata rana sai ta kira ni tare da mijinta suka zauna da ni suka fada min ilolin da suke cikin auren musulmi, ta yi ta fada min kalamai marasa dadi akan musulmai da kuma yan arewa, ita da mijinta burinta su cusa min kyamar musulmi kamar yadda ake yi sauran yara, ta fada min na yi kankanta da fara soyayya a yanzu, kuma Khaleepa ba ajina ba ne domin shi achaba yake yi, ni kuma a yanzu na kalli irin gidan da nake rayuwa.
Soyayya bata da hankali bata ji bata gani, duk ban ji abun da suka fada min ba, a haka na nuna musu ni dai ina son Khaleepa ba zan rabu da shi ba, sai suka saka min dokar ba zai sake zuwa na fita ba, kuma ba zan sake waya da shi ba, haka kuma ba zan ma taba aurensa ba, idan ma ina wannan tunanin na aje. Suka saka min kulli mai tsanani bana zuwa koma'ina daga gida sai makaranta sai kuma idan mun fita siyaya, ko kuma ranar Sunday muna fita zuwa church. Sun min gata sun nuna min soyayya suna kashe min kudi amman duk bana gani saboda Khaleefa ne a rayuwata, kullum cikin kuka da damuwar rashinsa nake, ban sani ba a lokacin ashe hawaye ba su cancanci zuba saboda shi ba. Wata rana mun je Church, na sulale na ari wayar wata mata na kira shi na fada masa dokokin da Momy ta saka min ita da mijinta kuma sun ce ba zan aure shi ba, a wayar ya rika kuka yana fadin Innalillahi idan na rabu da shi zai halaka zai mutu, ni ma na rika kuka ina jin kamar ma na kashe kaina domin ban taba soyayya da kowa ba sai da shi.
"Emily zaki iya aurena a kowane hali?"
Na rasa taya zan amsa masa.
"Amman ba addininmu daya ba Khaleepa"
"Karki damu da wannan addinin musulunci ya yarda mu auri wanda ba addininmu daya ba, kuma na san idan kina so na zaki musulunta domin ki aure ni"
"Zan iya ina kaunarka sosai Khaleepa"
"Emily zaki iya bina mu gudu? Idan ba haka ba ban san wata mafita da nake da ita ba, daga wannan wayar ma ban san ta ina zan sake jin muryarki ba, kuma muna nan ba za su bari mu kasance da juna ba"
"Idan mun guda ina zamu je"
"zan gudu dake mu koma kaduna gurin iyayena, zaki zauna a can a daura mana aure mu zauna a can"
"Ina tsoro ba zan iya ba Khaleepa"
Duk wata kalma da zata raunata ni ta sanyaya min guiwa da zuciya sai da ya nemo ta ya fada, amman ban yarda be shi ba. Na koma gida ina ta tunanin mafita amman ban samu ba sai wanda ya kawo, gashi kaunarsa sai kara ruruwa take a zuciyata, da kaina na samu Momy a dakinta ina kuka na fada mata ina son Khaleepa ta bar ni na aureshi, madadin ta tausaya min sai tace idan na sake mata maganarsa sai ta min duka kuma ko zan mutu ba zata taba bari na auri musulmi ba. Ranar mutuwa ce kawai ban yi ba tsabar bakinciki da nadamar kin bin shawarar Khaleepa na bishi mu gudu. Da sati ya zagayo muka je church Momy ta saka pastor ya dafa kaina ya rufe ido yayi min addu'a, bayan an zauna zaman church ana tsaka da wakar church na saci kafa na fice daga cikin church din daman Momy tana zama a gaba ne mu muna zama baya. Na fito na ari wayar mai gadin church din na kira Khaleefa na fada masa yanzu na amince zan bishi mu gudu.
Sai ya fada min inda zan je na jira shi, haka kuwa aka yi ba bawa mutumen wayarsa na fice daga church din na tari okada na fada masa inda zai kai ni, ko da na isa na samu Khaleepa a gurin tsabtsab da shi kamar kullum, yana jirana. Ya sallami mai okadan ya goya ni ya tafi da ni wani kangon gidan ya aje ni a nan, be dawo ba sai dare ya dawo da kudi mai yawa ya fada min ya siyar da babur dinsa kudin ne zamu hada da wanda ke gareshi mu tafi garinsu. A gurin ya bar na kauna ni kadai shi kuma ya kwana a inda ya saba washe gari da asuba dai gashi tare da kayansa, ba bishi muka isa tasha ni da shi muka kama hanyar Kaduna. Shi a tsorace ni, a tsoroce hankali be kwanta ba sai da muka isa cikin garin kaduna. Garin da ban taba zuwa ba kuma ban taba saka ran zuwa ba ko a mafarki sai ranar. A cikin tashar ya saka ni saka hijabi, kusan ko'ina muka bi kallona ake saboda farin fatana ba fari ba ne na sauran mutane, fari ne mai haske sosai da ya fi kama da na turawa ga kuma idanuwa blue. Tashar muka bari muka isa wata dabam muka hau motar garinsu Khaleepa, garin da basa son tubaben, basa marasa ba ni, bana tausayin kaddara da kuma kuskure da na aikata, garin da suka koya min hankali da sabon karatu, suka maida ni wulakantacciya.
_________________________
A jiya na yi mistake a page 17, na yi page din ne kamin na canja akalar labarin, bayan na canja kuma sai ya zama na manta ban yi editing ba, wadanda suka karanta wanda na yi ba edited one ba, za su ga Nace Emily baka ce, ku manta wannan kuskuren ku shafe shi a Kwakwalwarku, ni yar adamce ina kuskure dole na. Emily fara ce kamar yadda aka fada tun a farkon labarin.
Shin zaku iya fada min abu daya zuwa biyu da kuka fahimta a page din yau kawai?
Kuna son a karo? Zo na gani a kasa, ance da kare ana biki a gidanku yace mu gani a kasa😁
Ma'ana ku suburbudo comments na suburbudo muku pages🤙
Don't forget to follow my channel https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
*Karku manta ku yi Sharing* [5/1, 8:59 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy
🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 2️⃣0️⃣
Mun sauka garin Rizaga (Sunan garin kirkiren ne) Da dare sosai kusan sawun mutane da yawa ya dauke. Daga tashar garin ya dora ni a babur shi ma ya hau daya muka kama hanyar gidansu, tafiya muka yi mai nisa sannan muka isa. Da duk inda muka bi muna ganin mazan garin kwance wasu a bakin kofafin gidajensu wasu kuma a fili. Bayan mun sauka ya biya mai achaban su biyu sannan ya nufi kofar gidan data kasance katuwa da aka yi da gambun kwano.
"Su waye a nan?"
Na ji an tambaya, sai Khaleefa ya nufi daya daga cikin maxan da suke kwance a wajen yace ni ne baba, mutumen ya dauko fitilarsa ya haska fuskar Khaleefa duk kuwa da kasancewar akwai hasken wutar nepa.
"Lafiya? Hamza kai ne a dare haka?"
"Lafiya kalau Kawu, bari na shiga ciki"
Sauran mazan duk suka tashi zaune suna gaisawa da shi suna tambayar lafiya ya ce musu lafiya kalau.
"Da muka a kuke tare?"
Ya tamabaya bayan ya haska fuskarta.
"Zuwa da safe za ku ji komai ba Kawu"
Ya nufo ni muka doshi cikin gidan, Tun kamin mu shiga gidan na gama fahimtar gidansu family house ne, ashe kuwa na canka daidai da muka shiga ciki sai na bangare bangare na gidan, yana gaba ina biya har muka isa bangare da mahaifiyarsa take, tana cikin bachi ya tasheta ta zabura tana daura dankwali.
"Hamza lafiya? Saukar dare? Kuma baka fada mana zaka zo ba?"
"Lafiya kalau Inna, ga dai bakuwa na zo da ita a bata gurin ta kwanta, kuma idan akwai abinci a bata ta ci zuwa sa safe za mu yi magana"
Ta kalleta daga sama har kasa a lokacin ina sanye da jean sai hijab din da Khaleepa ya siya min
"Sannu da zuwa zo nan ki zauna"
Na gaisheta ta amsa min, na karasa na zauna a inda ta nuna min zuciyata cike da tsoron abun da na aikata da kuma wanda zan tarar. Tuwon gero aka kawo min da miyar kuka, luma daya na yi na gagara ci domin ban san miye tuwon gero ba a lokacin, miyar kukar ma ban taba jin sunanta ba sai a ranar. Haka na kwana da yunwa, washe gari tun da asuba na ji garin ya karade da kiran sallah, Wallahi idan na ce ban jidadin sautin da na ji ba na yi karya, natsuwa ta sauko min, sai na ji kamar ina cikin wata duniyar ta dabam...
A daki aka maida min shimfidar su kuma suka yi sallah a ciki, tun da na shiga bachi mai nauyi yayi gaba da ni, ban farka ba sai karfe tara na safe, ban sani ba ashe Khaleefa yana nan yana rigima da iyayensa akan cewar ba zai maida ni domin shi a yanzu tsoron komawa garin Lagos yake, kuma ni na yarda na biyo shi ba cilasta ni yayi ba. Suka kira ni aka tsare ni a gaban manyansa suka tambaye ni, da amincewata ya taho da ni na fada musu cewar eh ni na mince masa na ce masa mu gudu domin iyayen dake rikona ba za su bar ni na aure shi ba, kasancewar shi musulmi ne, suka sake tambayata shin zaki musulunta ki auri danmu? Na amsa musu a take cewar eh zan musulunta.
Sai suka yi farinciki suka nuna jindadinsu musamman mazan, amman mahaifiyarsa kamar bata yaba da hakan ba. Da yamma aka aiko mai gari yana neman yarinyar da aka zo da ita da kuma Khaleefa. Muka tafi har da iyayensa irin bayani na yi a nan shi na yi a can shi kuma haka, mai garin ya gamsu yace gobe idan Allah ya kaimu za a kai ni gurin limamin garin na musulunta kuma a daura mana aure, suna tambaye ni wane suna kike so nace musu Aisha Muhammad, haka nake son sunana ya zama.
A lokacin farinciki ne kamar ragagge ne, sai ya zama ban ji wani dauki na auren ba sosai ba, wata kila kuma ishara ake min cewar babu alheri a ciki. Yadda mai garin ya fada haka aka aiwatar washe gari aka kai ni gurin wani limani na musulunta kuma suka daura mana aure, kusan kowa zuwa yake kallona har sai an boye ni, abubuwa biyu ke kawo su, jin cewar ni ba musulma bace da kuma yanayin hallitata.
A dakin mahaifiyarsa na fara zama kamin ya gina mana karamin dakin da zamu zauna a tare a bangaren mahaifiyarsa, ya siya mana katifa da zanen gado da dan abubuwan bukata na aikin gida domin ni ba ni da kowa kuma bani da kudin siya. Sannnu sannu ya fara koya min sallah karatun sallah da wasu gajerun addu'o'i kasancewata mai saurin gane abu sai na fara fahimtar yadda zan yi ibada ta.
Kusan a lokacin bani da wata matsala kamar yadda idan na gaishe da mahaifiyarsa take amsa min kamar dole, ga kuma rashin iya girki, ya siya min gawayi da murhun gawayi ina girki da shi, akan girka shimkafa ko taliya, ko indomie na girka chabewa take saboda ban taba girki ba, shi kuma yana da saurin fushi, ko kirana yayi na dade ban amsa ba ko ban zo ba sai ya fusata, ya fara fushi da ni, ko gaba, idan ya fara gaba da ni sai ga na zama kamar marainiya yake kula ni, domin ba ni da kowa a garin, gashi mutanen gidan sun ki su saba da ni, ni ma naki sakewa da su, kullum ina ciki daki.
Abun da na fahimta bayan aurenmu shi ne Khaleefa yana da farin jinin yan matan garin, shi ka kansa ya fada min kuma kanwarsa da ke dan leko ni muna taba hira wani sa'in ta fada min. Ban kuma yi mamaki ba domin yana da kyau ni kaina kyaun ne ya dauki hankalina a lokacin, gashi ya iya wanka idan ya shirya ba zaka taba yarda a kauye yake zaune ba, su kan shigo gani na wasu wasu kuma idan na fita tsakar gidan nake ganinsu ko su gan ni.
Akwana a tashi dan abun da Khaleepa yake da shi ya kare domin ciki muke ci, ga mahaifiyarsa ko gishiri ya siyo min sai ta karba ta raba biyu ta bani rabi, taliya ma idan daya ce to rabi zamu aje mu bata rabi. Da kudinsa suka kare sai ya rika karbo mana abincin da suke, da safe kunu ko dumame, da rana kuma sai dai ayi kwado ko kuma asiyo abunci na siyarwa a ciki da dare kuma tuwon gero.
Bana iya cin tuwon kunun ma kadan nake sha domin babu suga, da rana kuma sai na wuni da yunwa, na ga alamar yunwa zata halaka ni idan aka ba ni tuwon geron sai na dukula na hada da ruwa na rika hadewa ba sai na saka miya ba. Washe garin ranar Inna da kanta ta sallama min na fito ta ba ni tabarya wai ai da ni ake cin abinci yanzu, ta saka ni turfe ban iya ba amman haka na rika yi ba, daker na samu yayi na kwashe mata, na dawo daki ina duba hannayena da suka yi kwancin jini suna ciwo. Sai yace
"Da sannu zaki saba, mu a nan garin yawanci duk gidan da ake cin tuwon gari a gidan ake surfe, Inna ma bata yi, amman da kin lura dayan bangaren ai har na siyarwa suna yi"
Ban ce masa komai ba, gudun kar na yi wata maganar ya fusata. Wasa wasa matar nan ta fara sani surfen siyarwa idan aka kawo kudin kuma sai ta karba tace za a hada a kudin cefane. Gashi haka nan nake wuni da rana babu komai a ciki, domin Khaleefa be da kudin siya min abinci yanzu, sai can wata rana idan an yi kwado ta aiko min idan na ci cikina yayi ta ciwo, da dare kuma abinci kadan nake ci haka da safe. Kan kace me na rame na lalace ba kadan ba, idanuwana suka cicciko suka fito fuskar ta koma karama, kassana suka bayyana. A lokacin ne Khaleefa ya dauki katifar dakin ya siyar mahaifiyarsa ta hada masa da wasu kudi yayi kudin mota ya tafi Nijar gurin nema, ya bar ni babu komai sai damuwa, kullum da fargabar daka nake kwana nake tashi, ga abinci bana iya cin na kirki. Sai aka fara rade raden wai ina da kanjamau shiyasa na yarda na biyo shi. Wata rana ina cikin surfe matar da muke zaune da ita gida daya wadda take kamar matar kawunsa ce ta dube ni tace.
"Aisha amman kamin Khaleefa kina da wasu samari ko?"
Na yi murmushi ina gyara rigar atamfar da ta yi min yawa, daman tufafina gaba daya kala shida ne a gidan.
"AA ban taba yin saurayi ba sai Khaleefa"
"Ban yarda ba gaskiya yadda kike da kyaun nan haka ai sai maza sun yi ta kawo miki hari, ko da yake ance ku baku dauki wannan komai ba, ance dan miji ya yayi mu'alama da ku ba komai ba ni shiyasa sai an gwada mace ake aurenta"
"Ba kowa ba, wasu dai suke yin haka"
"Toh Allah yasa wannan rama taki dai ta yi yawa"
Ban fahimci inda ta dosa ba dan haka ban maida hankali akan zancenta ba, na gama surfen na dauka na wanke na kawo na aje na nufi dakina. Na shimda tabarma na dora zane na kwanta, nan da nan sai bachi yayi gaba da ni, can cikin bachin na ji ana tashina kanwarsa ce wai na tashi na yi sallah, na tashi ina jin kamar na yi kuka, domin sallah na daga cikin abubuwan da suke wahalar da ni a lokacin saboda rashin sabo haka dai nake daurewa na yi. Bayan ta fice na dauki buta na zagaya bandakin, kamar ance saurara ki ji sai na ji muryar mahaifiyarsa kasancewar bandakin yana like da dakinta ne ta gafe.
"Badan halin Hamza na son karya, shi gaba daya rayuwarsa ta karya ce ta son burge mutanen, ka tsallake garinku jiharku ka tsallaka har kudu kudun ma Lagos ka dauko mata, Allah kadai ya san dalilinta na biyosa, wannan ramar da take yanzu na fara tsorata da ita"
Na kai hannu ma dafe zuciyata idona ya cika da hawaye, can na ji wata kanwarsa mai da da zo ta karba mata.
"Yawanci fa yan kudun nan ance idan suna da hiv suke bin yan arewa saboda su lika musu, gashi nan a gari sai rade rade ake wai Ya Khaleefa ya dauko mai ciwo, wasu har da cewa wai ciki yayi mata aka korosu"
"Ai yaje dai ya dawo, aure zan saka ya kara yaushe zai zauna da zabiya kalli idonta ma kamar matsafiya, ance a can fa kowa da kalar tsafinsu na gado, kuma nan gaba idan suka haihu ai zata iya kwashe yaranta ta koma can"
Kasa fitsarin na yi na fito na dawo dakina na zauna na ci kuka na har na koshi. Sannan na fito na yi sallah, kalaman da na ji ya saka na ja jikina daga mutanen gidan domin idan wani abu ya faru za su iya cewa ni ce. A lokacin damuwa ta kara yi min yawa gashi tun da ya tafi be taba kiran waya yace a ba ni mu gaisa ba sai dai ya yi waya da mahaifiyarsa. A haka ya shafe shekara daya be waiwaye mu ba, sai dai yayi mana aike idan kuma ya aiko komai yana hannun mahaifiyarsa babu wani canji. Yanayin yadda ya turo kudi aka siya masa fili a kusa da gidan aka fara masa gina na fahimci ko wane kalar kasuwanci ko aiki yake can toh ya karbe shi, ina ta jindadin ina murna mijina zai gina gida mu koma a can mu tare, ashe ba ni yake yi ma ginin ba.
Ranar da na yi ma mahaifiyarsa maganar ina son ta rika ba ni kudin surfen da nake na rika siyen abinci ranar ta yi min tatas wai duk abun da take min bana gani, ba zata sake min komai ba daman hakkin ciyarwarta ba a hannunta yake ba, har tana fadar musuluntar kawai na yi amman zuciyar kafirarce a kirjina. Da mutanen gidan suka taso madadin su shiga tsakani su bawa mai gaskiya gaskiyarsa sai duk suka goya mata baya, wasu suka dauki gaba da ni ciki har da kanwarsa da nake shiri da ita. Tun daga ranar ba a sake bani abinci ba, sai dai idan na yi surfe dan abun da na samu sai na siya abinci da shi, bayan surfe sai na rika hadawa da wanki domin na samu kudin su min auki, wahala sai ta taru ta yi min yawa har wasu kujera suka fito min kamar na sauyin ruwa kamar na wahala. Idan na samu matsala kadan da mutanen garin sai min gori akan kudin surfe na ko wanki, ko aika ko kuma wani abun dabam, sai min gori, wasu su zage ni ni da iyayen da ban san a ina suke ba, wasu suce min zuciyar kafirar ce tana cikin kirjina, wasu suce min tsintacciyar mage.
Gashi idan ina son abu sai dai na fita na yi da kaina, babu mai bari na aiki danta, idan na fita mutanen su yi ta kallona. Ana sauran wata uku ya dawo wata rana ya kira waya sai aka kawo min na karba da murna ina kai masa gaisuwa sai ya rufe ni da fada. Wai an fada masa na yi fada da mahaifiyarsa na ci mata mutunci, kuma ina fita yawon gantali a cikin unguwa, shi ba zai dauki wannan ba.
"Ba zan iya daukar wannan rashin kunyar da rashin tarbiyar kafiran lagos ba, yadda kike tubababiya dole ki dauki halinmu da al'adarmu wannan kiristancin da bakin hali ki aje shi a gafe, ba ni da kamar mahaifiyarsa"