Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 21
Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 21: Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 21. Na mata godiya na fito jikin a sanyaye domin na san babu wani kudi…
3,353 words
Na mata godiya na fito jikin a sanyaye domin na san babu wani kudi da zan samu a gurin Khaleefa, ashe ma abun da ban sani ba gidan yana nan ya kusa kamawa da wuta saboda na fita tun safe ban dawo ba har la'asar. Dan canjin da na rage min ne na hau achaba da shi na iso gida sai da na fara biyawa na fadawa Malika halin da nake ciki ina kuka sannan na shigo gidan.
"Idan uban wa kika fito?"
Ita ce madadin amsa sallamata da yayi kasancewar yana cikin dakin na yi sallama.
"Asibiti"
Na amsa jiki ba kwari murya na fita daker.
"Ina kika samu kudin zuwa asibiti? Da izinin wa kika fita"
"Idan na tambaya ba zaka bar ni ba, kudin kuma daman ina da shi"
"Karya kike sai dai idan satar min kika yi ko kuma kin fara bakin halinku na kafirai, wato yanzu ya kai ki fara fita baki fada min ba"
Na kalleshi cike da takaici da nadama da bakinciki na ce.
"Wai kai Hamza wane irin zuciya ce a kirjinka? A matsayinka na musulmi mai addini be kamata na same ka haka ba, dabi'unka da ka nuna min ba su na tarar ba, ka zalince ni kai da iyayenka kunci amanata"
Ban gama rufe baki ba ya rufe ni da duka.
"Me kika sani akan addini da zaki tsoma baki a ciki? Kafira diyar kafirai? Bubabbiya marar alkibila, rashin kunyarki ya kai ki kira da Hamza gatsatsa ko? Irinki ma son haihuwa ake da ke? Mugun iri irin kafirci wadanda basa tuban Allah da ma'aiki, na haihu da ke kije gaba ki maida yarana kafirai"
Ban taba sanin rashin imanin Khaleefa ya kai haka ba sai ranar, baya ji baya gani duka yake ina tare cikina yana kai masa halbi da kafarsa, Matar nan da ta taimaka min da kudin tafiya asibiti Maman Luratu ita ce ta shigo tana ba shi hakuri tana jansa sannan fa sauran suka shigo suna jansa suna fadin ban kyauta ba amman dai yayi hakuri ko dan cikin dake jikina.
"Na gaji da ke na gaji da halinki kowa ya san ba haka na tsara rayuwar aureba amman ji yadda kika maida gidana, Aisha na sake"
Maman Luratu ta yi hanzarin rike shi.
"Abun he kai can ba Hamza ka yi hakuri ga ciki kuma ta tafi ina?"
"Ta tafi duk inda zata tafi, ba gaji da halinta bata da tarbiya"
Nasan ma'anar saki a musulunci kamar yadda na san ma'anar aure, wato ya barranta kansa daga gareni, ni din nan na haramta a garesa, sanin ba ni da gurin zuwa ba ni da kowa ya saka ni ba shi hakuri ina rokon mutanen gidan su ba shi hakuri na zauna. Sai suka ce na bari sai ya huce na zauna a gidan idan ya huce zai maida ni. Na san yadda suke kina sai zuciyata ta raya min kamar abu ne mai wahala su saka ya maida aurena. Dan haka na tashi cikin daren nan na tafi gidan mai gari na fada masa halin da ake ciki, ashe fita ma matsala domin har an kira an fada masa, mai garin ya aiko kiransa ya zo take a gurin kamin a mana umarni da komai ya ce.
"Da zu na sake ki ne da nufin saki daya, toh yanzu na kara miki na sake ki saki uku babu aure tsakanina da ke har abada"
Na rude na kama kafafuwansa na rike ina kuka ina rokon gafara, ban wayi addinin sosai ba saboda haka ban san idan an yi saki uku aure ya kare ba kenan.
"Khaleefa ka san ba ni da kowa ba ni da komai dan Allah karka min haka, Alkawari be ce haka ba, ka yafe min Wallahi ba zan sake ba"
Ni kam rokonsa kawai nake ina son ya maida sai da matar mai garin tace min ai auren ya kare kanan babu zancen gyara. Na yi tunanin ko mai garin zai ce na zauna a gidansa har sai na haihu, daman iyayensa kam ban saka ran za su ba ni gurin zama ba. Ina dawowa gidan na ji na zaba bukatar kowa a tare da ni sai na shiga dakin na dauki can chanjina da fitila da number da Maman Luratu ta ba ni na fice ba tare na dauki komai daga suturar da na samu a gidan ba. Na karasa inda yake zaune a kofar dakin mahaifiyarsa sai duk idon yan gidan ya koma kaina wata kila suna tunanin ko zan rokeshi gafara ne ko kuma ya bar ni na zauna a gidan ne, na tsaya a tsaya ina kallonsa ido cikin ido na ce.
"Ka ci amanata Khaleefa, ka yaudare ni, ba ni da kowa ba ni da komai wannan tabbas haka ne, saboda kai na zo gidan nan kuma yanzu aure ya kare zan tafi, ka sani na rayu kamin na hadu da ni, na rayu babu uwa babu uba, babu daya daga cikin danging uwa ko uba, yanzu ma zan rayu domin mai rayawa ya kashe be manta da ni ba, Hamza na barka da Ubangijin da ya aiko Annabinsa da Addinin Musulunci, na barka da Ubangijin da be kwana be haifa ba ba a haife shi ba, Hamza na barka da ALLAH... "
Mikewa yayi tsaye yana kallona baki a sake, matan gidan kuma kowa yayi tsit kamar babu abu mai rai a gidan. Bayan wannan wata kalar bata sake fitowa daga baki ba har na doshi kofar fita gidan na fice, ban yi nisa ba na ji ana kirana Maman Luratu ce ya biyo ni tana kuka.
"Aisha ina zaki"
"Koma ina ne zan tafi Wallahi yau ba zan kwana a gidan nan ba"
"Toh Allah ya miki mafita, dan Allah idan kin samu waya ki kira ni, Allah ya sauke ki lafiya, ungo ga dubu biyar ki rike"
Ina karba kudin na fashe da kuka sai ta rumgume ni tana kuka, na dago godiya ma kasa yi mata na yi na kama hanya, achaba na fara hawa ya kai ni tashar garin, ina zuwa kuwa na samu mota sanin kudin ba zai ishe ni na je Lagos ba na hau motar Kaduna, idan ma naje Lagos din gurin waje zan je? Matar da na yi butulci? Ko gidan marayun da ba lallai su karbe ni ba zan koma? Lokacin da na hau motar ba zai wuce karfe goma ba kasancewar garin da kowane lokaci ka je ana samu direba saboda akwai masu cin kasuwa, kuma ranar da abun ya faru ranar kasuwa ce. A ranar ban kwana a garin ba da cikina da ciwon da nake ji da kuma bakincikin dake kumshe a zuciyata na kwana a tashar Kaduna...
Follow my channel domin samun update https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
And don't forget to SHARE [5/6, 8:51 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 2️⃣2️⃣
Da gari ya waye sai na yi ta raba ido a cikin tashar ina kallon mutane, daman na kwana a kusa da massalaci ne a wani guri da ake aje sako tare da wasu matafiya da dare yayi musu. Na zauna a gurin har zuwa karfe daya na rana saboda ban san a inda zan je ba, ba zan iya komawa lagos ba idan ma nace zan koma ba ni da kudin motar idan kuma na koma ba ni da tabbacin a karbe ni.
Jama'ar gurin da suka lura ina zaune a gurin har ana daf da ayin la'asar sai suka same ni suna tambayar na san a inda nake kuma wana sani a garin Kaduna? Nace musu na sani kuma bani da kowa a garin kaduna. Sai suka tambaye ni ni matar aurece? Nace musu aa domin a halin da nake ciki babu aure a tare da ni, idan ma akwai vana bukata domin na gama kakkabe Khaleefa a rayuwata yanzu, sai kuma suka sake min wata tambayar da na rasa amsar da zan ba su.
"Toh cikin dake jikinki fa?"
Na shafa cikin ina hade wani abu mai daci, dole kowa zai yi zaton cikin shege ne, wata kila su yi tunanin ko na gudo daga gidanmu ne.
"Dan Allah inda ake bada taimaka idan mutum yana cikin matsala?"
"Kamar wani irin taimako?"
Dayan ya tambaya.
"Kamar wata kungiya ta musulmai da take bada taimako haka ko masallaci"
"Toh sai zakka da wakafi"
Dayan kuma yace na tafi massallaci, wani kuma ya tambaya wani irin taimako nake nema, na ce na wanda zai rike ni har na haihu.
"Wannan cikin ba shi da uba ne?"
"Yana da uba, ni ba ni kowa marainiyace ni, kuma mijina ya sake ni, kuma musulunta na yi ban san kowa a nan ba"
Ina rufe baki daya daga cikin dattijan dake tsaye a gurin ya rufe da fada kamar zai dake ni. Wai na tashi na bar gurin haka muke muna zuwa muna cikin shege mu zo tasha mu tare muna haifa musu yara yan iska muna bata musu tasha.
"Idan baki da kowa ki koma garinku mana, karya ce suke saboda kawai a tausaya musu, cikin shege suke yi"
Ban san lokacin da na fashe da kuka ba, daman wai waye zai yarda da ni, suna da gaskiya suna bukatar tabtace tashar su. Haka na tattara na bar tashar na fito na kama hanya ina tafiya ban san inda zan je ba, can na samu guri kusa da wata mai wara na zauna na siya wara na ci saboda ban saka komai a cikina ba tun safe.
"Dan Allah ina ne? Zakka da wakafi?"
Ba tambaye ta, sai ta kwatantamin na bata kudin wararta na siye ruwan leda na sha, na tari mai achaba na hau na fada masa inda zai kaini ban tambaya nawa ba sai da muka isa yace min 500 zan bashi a lokacin 2300 ne suka rage min, na ba shi 500 na doshi gurin gabana na faduwa, domin maraicina be taba saka ni rokon kowa ba. Mai gadin gurin ya fara tambayar ina zanje na fada masa taimako nake nema a take na bayyana masa abun da ke tafe da ni da kuma taimako da nake bukata.
"Kin tabbatar cikin nan baki ba na shege ba ne? Domin suna yin bincike idan za a bada taimako"
"Wallahi gaskiya ne, ba karya nake ba"
Sai yace na jira a nan ya shiga ciki ya fito da wani mutum mutumen yayi min tambayoyi ya yi rubutu akai sannan yace min yanzu kowa ya tashi aiki saboda yamma ta yi, amman na tafi zai saka sunana a cikin mabukata na dawo wani sati, sannan ya tabbatar min kamin su bada taimako suna yin bincike saboda akwai bata gari da suke zuwa suna karya nace masa na yarda su yi duk abun da ya kamata.
"Amman yanzu idan na tafi ba ni da gurin zama ban san a inda zan zauna ba"
"Ki yi hakuri dai wani satin ki dawo da wuri kamin rana ta yi"
"tohm"
Na amsa ina kuka, sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi naira budu daya ya ba ni wai na hau abun hawa. Na karba na juya na kama hanya daman kam wa zai karbe ni a haka dole kowa zai yi zaton karya nake saboda cikin dake tare da ni ga shi kuma ina fadar ba ni da kowa kuma nace ban san kowa a garin Kaduna ba, ga ina cewa musulunta na yi wasu ma sai su dauka karyar ma ta yi yawa. Daga gurin na kama hanya ina ta tafiya a kafa ba dan na san inda zanje ba, har dare ya fara yi na siye ruwan leda na yi alwala na raba gefen wani icce dake kan hanya na yi sallah, ina addu'a ina kuka ina rokon Allah ya kawo min mafita. A gurin na yi ta zama har aka yi isha'i a nan ma na yi sallah.
Da yake akwai mai shayi nesa da inda nake zaune kadan da na yi yunwa ta matsa min sai na tafi na siya birede da ruwan lipton na koma gefe daya na sha, sai wani azababben ciwo ya taso min, da na kawo masa kofin kowa kallon wulakantacciya yake min domin mace mai daraja ba zata saya tea ta raba gefe ta sha ba, gashi na zama kamar mahaukaciya duk na firgice ga rama cikin ma yayi min nauyi haka dai nake ta fama. Da na bashi kayan sai na raba ta wata hanya dake kusa da shagon na bi na lulla da wasu kananan gidaje, a gurin na samu inda na raba. Na wahala a gurin domin ciwon ba kadan nake jinsa ba, sai da na bari sawu ya dauke na tabbatar da dare yayi sosai sannan na tashi na koma inda na fito yadda na ayyana haka na samu. Mai shayin nan ya tashi ya kwashe kayansa a gurin na kwana, washe gari tun da asuba na yi sauri na tashi na koma gurin hanyar na zauna, da haske ya fito sai na shiga wani gida dake kusa na roki ruwa dattijiwar ta ba ni na yi alwala na fito nan na yi sallah.
Rayuwa ta zama min haka, da dare sai na kwana a shagon mai shayi da rana kuma na shiga gari Bara da neman taimako. Ta inda Allah ya taimake ni babu wanda ya taba cewa me nake a gurin ko ya kure ni, ko da yake bana dawowa gurin sai dare yayi, idan kuma sawu ya dauke sai na kwana a shagon mai shayin da be san ina yi ba. Ranar da na kwana uku a gurin ciwon ya matsa min sosai har na tafi yawon bara na dawo na shiga gidan matar dake bani sadakar ruwa ina ta gumi na roki ta ara min wayarta na kira wata number. Har tace min bata da waya na juya sai kuma ta kira ni ta ba ni amman tace na zauna a kusa da ita na yi wayar bata yarda na fita ba kuma ta saka wayar a speaker saboda bata yarda da ni ba. Na warware zanena na dauko number Maman Luratu na saka a number na kirata, babu jimawa tana ringing ta daga wayar da sallama
"Maman Luratu nice Aisha ce"
"Aisha Allahu akbar sannu Aisha ya kike ina kike yanzu"
"Ina wani guri, maman luratu dan Allah ko kin san abun da zan yi na daina jin ciwon cikin da baya? Wallahi ciwon nan ya tsananta min yanzu sosai yau ma kamar bana iya tafiya"
Ina fada ina kuka.
"Toh ko haihuwarce? Amman cikin ai be isa haihuwa ba ko?"
"Eh wata bakwai ne, amman ina jin wahala sosai"
"Ko nakuda kike yi? Oh Allah gashi bana kusa, amman dai ki daina yawo nesa"
"Idan haihuwar ce me zan yi?"
"Kina tare da wa ne?"
"Babu kowa ni kadai ce"
"Ki nemi reza ki aje kusa saboda yanke ciki, kuma idan da hali ki tafi asibiti Aisha kin san baki da lafiya tun a nan ma"
"Tohm"
Na amsa sannan na kashe wayar na mikawa matar ina godiya, sai matar ta tambaye daga ina nake.
"Labarin mai tsayi ne ko na fada miki ba zaki yarda ba, na gode"
Na fice daga gidan ina ta sharar kwallah. A rabar ne zuciyata ta debeni na yanke shawarar ziyartar coci ba dan komai ba sai dan na samu kudin da zan tafi asibiti kuma na samu kulawa. Dan canjin da ya rage min na hau abun hawa bayan na tambaye shi wace coci ce a kusa na fada min, da muka isa na bashi kudinsa na doshi gurin gabana na faduwa a zuciyata ina jin kamar hakan ba daidai ba ne amman ya zan yi? Dole ce ta saka. Na isa gurin na yi magana da mai gadin coci na fada masa damuwata da abun da ke tafe da ni, sai yace na jira a gurin ya shigo ciki ya fito da wata Sister tace ba shigo ciki na shiga nayi mata bayanin damuwata sai ta kira wani pastor shi ma ya kira wani muka shiga wani office na sake karanta musu damuwata, da na yi hakan ne saboda kawai su taimaka min.
Sai dayan yace za su taimaka min da gurin zama da abinci amman sai idan zan yarda na koma gidan jiya, ma'ana na zama christen kamar baya, har ita macen take ce min ko da ace ban taba yin addinin a baya ba zan shiga a yanzu su kuma za su bani duk abun da nake bukata kuma za su shirya ni da mai rikona ma dake Lagos."
***. ****. *****.
Ta daga kanta sama, Aliyu ya tashi daga inda yake zaune ya zaro tissue ya mika mata, ta karba ta share hawayen da suka ki tsaya mata. Ta kalleshi da fuskarta da ta yi ja tsabar kukan da take.
"Ni na sani a yanzu ba akan shiriya nake ba, na sani ba akan daidai nake ba, na san addinin musulunci shi ne addinin gaskiya, a wacan lokacin ban yarda da tayinsu ba duk kuwa da kasancewar ina cikin tsananin bukatar taimako a lokacin, amman akwai wani abu da Allah yake sakawa a zuciyar wanda ya so da shirya, na musulumta saboda Khaleefa da aurensa ban san cewar ina son addinin ba sai a lokacin, sai kawai na ji raina ya bace akan me za su ce na koma addinin da bana samun natsuwar zuciya da kwanciyar hankali irin na ruhu sai da na bar shi, ni dai a lokacin na san ina son musulunci dan haka sai na ki yarda, na fada musu ni taimako kawai nake nema ba wai ina nufin barin addinin ba ne, su kuma suka ce ba za su taimaka min ba haka na taso na fito"
Ina jin kamar shi kadai ne wani hukunci da na taba yankewa kuma ban yi nadama ba, da kafa na dawo saboda ba ni da kudin da zan hau abun hawa na dawo, sai kuma na sha wahala a hanya saboda ni ba har gari bace hanya da mai achaba ya bi da ni na bi ina tafiya, idan na rikice sai na tambaya mutane da sannu har na kawo kaina unguwar da nake zaune. Na iso ban isha'i sai na samu guri na zauna ina ta jin ciwon cikin da ban gane nakuda ce ba, daker na iya roko ruwa na yi rama sallolin da ban samu yi ba, na kwanta a gurin azabar ciwo cikin bata karu ba sai da dare ya raba. Na koma gurin da nake kwana na kwanta da ji abun ba zai daina ba na taso na fito na dawo gidan matar nan na kwankwasa mata gida sai jikanta ya bude yana haska ni da fitila.
"Dan Allah matar gidan nan nake nema"
"Lafiya wacece"
"Ni ce"
Na leka sai ta ga fuskata.
"Dan Allah ki taimaka min da ruwa na sha, kuma idan kina sa wani magani dan Allah ki taimaka min na sha, kar na mutu ciwon ciki nake da na mara"
"Ba ni da magani amman dai zan baki ruwa ki sha"
Ta shiga ta dauko min ruwa na karba da hannu biyu na sha na juya na koma shagon na zauna ina ta kuka domin ciwon ya matsa min ga kuma abu ina ji a kasana kamar zai fito, ban san lokacin da na fara ihu ina rike teburin mai shayin dake gurin ba, sai matse kafa nake ina juyawa, tsabar bala'i da azabar da ciwo har wani juri nake ji ina jin kamar ba a duniya nake ba, ashe haihuwa tana da zafi ban sani ba sai a ranar, gashi babu kowa a kusa da ni, duk zafin nan na haihuwa a haka iyayena suka wofintar da ni? Ina cikin tsananin nakudar dana na farko dan wata bakwai matar da ta taimaka min da ruwa ta iso gurin ta dafa ni, ta haska ni da fitila ina jin jikanta na fadar Gwaggo kika sani ko jikin shege ne. Sai tace.
"Ko cikin shege ne ai ba za a kyaleta ba Kabiru rayuwa ce"
Ta bude kadata ta haska sai ta saka salati.
"Haihuwa ce zaki yi kuma kafa nake gani ba kai ba subhanallahi"