Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 54
Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 54: Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 54. "Dan Allah Ummi ki amsa min, abun da na ji gaskiya ne?"
3,303 words
"Dan Allah Ummi ki amsa min, abun da na ji gaskiya ne?"
Ummi ta dauke wayar daga kunnenta ta mikawa Mama Barakat.
'Tana son sani idan ke ce mahaifiyarta ko akasin haka, ban san amsar da zan bata ba"
Mama Barakat ta karbi wayar ta kara a kunne.
"Hello... Emi... Eim...emi...emilllllyyy lyyyyy"
Ta amsa murya can kasa.
"Na'am"
Sai kuma ta yi shiru.
"Kina ina dan ki dawo"
"Da gaske ke ce mahaifiyata?"
Mama Barakat ta fashe da kuka.
"Ni na haife ki da cikina... Ni ce uwarki... Mahaifiya..."
Emily ta yi murmushi mai hade da hawaye da kuka.
"Waya raba ni da ke? Miyasa ban tashi tare da ke ba? Taya zan yarda ke kika haife ni ma?"
"Ba magana ce da za'ayi ta ta waya ba, magana ce da ya kamata ace ina kusa da ke kina kusa da ni"
"Ki amsa min dan Allah, tsawon rayuwata na karar da ita ne akan nema da son sanin su waye iyayena su waye dangina, dan Allah ki fada min waya raba ni da kowa? Ko kuma dai kina nufin kin san inda iyayena suke?"
Mama Barakat ta fashe da wani irin kuka.
"Ni ce...."
Emily taja numfashi, tana mamakin wace irin uwa ce zata raba yarta da kowa.
"Bari na canka, saboda kin haife ni ba ta hanyar aure ba ne ko?....."
Mama Barakat ta fashe da sabon kuka mai karfi ta kasa amsawa na tsawon lokaci.
"Dan Allah ki yafe min Emily ki zo mu yi magana ki fahimce ni, zan fada miki komai"
Emily ta dauke numfashi na wucin gadi, a take duk wani farinciki da ta taba sani ya rushe, ko ba ta amsa mata da eh lallai ba ta hanyar aure ta haife ta, ta fahimci amsar domin shirun da tayi kamin ta amsa da kuma kukan da ya kwace mata sun tabbatar da hakan gashi kuma tana neman gafararta.
"Sanin wannan amsar da dade ina tambaya, ya fi duk wani furuci da halin kunci da na taba shiga a rayuwata"
Ta katse kiran ta share hawayenta, sauran da suka rage a ramen idonta suka kafe a nan take, kukan ya yanke zuciyarta ta kafe, ashe akwai ranar da bakinciki zai ninku hawaye su tsaya. Wayarta ta sake ruri wannan karon data duba sai ta ga number Aliyu ta daga jiran ta kara a kunne.
"Assalamu Alaikum"
Ta yi shiru.
"Emily"
"Aliyu... Ka gafarce ni dan Allah, na shiga rayuwar ka na rusa farinciki da amincin dake tsakaninka da matarka, na yi sanadin kwanciyarka Asibiti"
"Me kuma ya kawo wannan maganar? Ni na kira ne saboda Ummi ta fada min kin tafi gidansu Turhan kuma har yanzu baki dawo ba ta ce na turo mata number ki tana son ta ji ko lafiya, Emily me yasa kika tafi? Already mun yi magana da Daddy kuma ya fada min yayi magana da mahafin Turhan komai zai zo karshe cikin lokaci, amman ban so kika tafi gidan ba"
"Ba amfani Aliyu... Turhan ya riga ya sake ni, ranar da ya kamata ta zama ta farinciki a gareni wata mata daga dangin Kameela mai ikirarin ita Mahaifiyata ce da kuma yata sun rusa duk wannan, Fatima ta zabi ubanta ta ce ta tsane ni Turhan take so, a yau kuma na gane da wacece ni, tambayar da na dade ina yi a yau na samu amsarta, na gano inda tabarbarewar rayuwar ta samo asali ba ni da sa'a tun gurin haihuwa shiyasa kowa yake taka ni yake guduna, indai har uwa zata haifi ya kuma ta jefar da ita saboda gudun jin kunyar duniya ko shiga wani hali, ta zabi farinciki akan na yarta, ta fifita mutumcin akan na yarta, toh taya kake tunanin wani zai ga yar nan akan hanya kuma ya bata farinciki? Ashe har da uwar data haife ni bata bukata ta"
"Ban fahimci me kike magana kai ba Emily amman dai ko minene ni ina da bukatarki, kuma ke ma kina bukatar kanki, karki damu da abunda Fatima ta yi daman na hango from miles away, ita ai yarinya ce wacce ta dade tana mafarkin samun uba, kowa yace zai tsaya a matsayin ubanta karba zata yi balle kuma ta hadu da ubanta na gaskiya, shiyasa data tambaya ni ban musa mata ba, sai na fada mata kin yi zaton baya raye ne shiyasa kika fada mata cewar bata da uba, idan kuma kin hadu da wata tace ita mahaifiyarki ce baki san uzurinta ba"
"Wane irin uzuri ne zai saka uwa ta jefar da yarta? Shin bata yi tunanin ya rayuwa zata kasance min ba bayan babu ita babu kowa a kusa da ni? Shim bata damu ta san a wane hannu na fada ba? Saboda ta haife ni bata aure ba ni miye laifina ne? Miyasa bata yi tunani ba kamin ta aikata?, na girma cikin tsangwama da rashin daidai da abokin tafiyarsa, da kowane faruwa tambayar kaina nake ina iyayena suke? Ta san bata bukatata miyasa ta haifo ni? Ashe uwa zata iya jefar da yarta ko danta saboda jin kunyar duniya?"
"Ita ta fada miki bata hanyar aure ta haife ki ba Emily ko kuma dai baki saurareta ba na fa san halinki, dan Allah karki jefa kanki a wata matsala, ki daina tunanin babu mai bukatarki ni ina da bukatarki ina son farincikinki"
"Ni da kai kamar mafitar rana ne da mafadarta, dukanmu muna fuskantar mabanbanta hanyiyi ne. Baka bukatata a rayuwarka Aliyu, indai har mahaifiyata zata ji cewar ni illa ce a rayuwarta, yar da raina da azaba da damuwa ta zabi mahaifinta sama da ni to babu mai bukatata a rayuwarsa. Ni dai yau gaji na yi yaki har karfina ya kare, na yi iya yadda zan iya na kasa cin ma muraduna, an rusa rayuwata da farinciki tun ina karamata, a yau na haka rame na binne burina zan bar wannan shafi famko ba tare da digon tawada ko zanen alkalami ba, na ga rayuwa rayuwa ta gan ni, na wahala iya wahala daga karshe kuma na hadu da bakin labari, ni dai na fahimce wacece ni yau, tambayar dake yawan yi ma kaina na samu amsarta a yau. Na yi ta kokarin ganin kaiwa ga hasken farin wata, da na isa kusa da shi, sai kuma na fahimci daga nesa ya fi kyaun kallo, duk yakin da nake na samun kwanciyar hankali ne"
"Kar idonki ya rufe ki aikata abun da za ki sake dawowa kina nadama, ni dai bana nufin komai a gareki sai alheri, ina son na same miki wani tsanin hawa ne a duk lokacin da kasar da kike taku ta yi miki zafi, ina son na zama wata igiya da zaki rika ki cimma burikanki, na so na zama kamar uba ko dan'uwa a gareki a duk lokacin da ruwan sama ya sauka akanki, na so in kasance wanda zai kawo miki laima, a duk Lokacin da hawaye suka zubo daga idonki, na so in kasance wanda zai share su, a duk Lokacin da kika ji kadaici na so in kasance wanda zai rarrashe ranki kuma ya kwantar da zuciyarki..."
"Na gode amman ni a yanzu bana da bukatar ABOKIN RAYUWA, ko wane iri ne na nesa ko na kusa, zan nisanci kowa zan rayu kamar yadda aka bar ni, har zuwa lokacin da da rayuwar ita ma zata gaji da ni ta bar ni.. Sai wata rana Aliyu..."
Aliyu ya lumshe idonsa yana jin kamar ya sauka kan gadon, ina ma ace tana kusa da shi a yanzu ya kwantar mata da hankali...
"Wata ranar da bata da rana..."
Ta sake maimaitawa sannan ta katse kiran ta cire dankunnenta ta juya wayar ta cire layin ta saka a bakinta ta tauna har ta raba shi biyu ta jefar a gurin, sannan ta mike tsaye ta fara tafiya sai da ta fita kwararon sannan ta jefar da wayar.
ALIYU POV.
"Emily..."
Ya furta a hankali idonsa a lumshe, kamin ya bude idon ya sake gwada number wayarta sai ya jita a kashe. Tun da yake a rayuwarsa be taba jin tausayin wani yadda ya ji tausayin Emily a yanzu ba, duk halin da take shiga be taba jin tausayinta irin tausayin da ya rasa ma'aunin dora shi balle ya auna ba irin yau. Emily ta wahala har a yanzu bata samu gatan daya dace ta samu ba, gashi kuma abu ta dade tana nema ya zo mata a ɓaragurbi, da wanne zata ji? Be samu amsar tambayarsa ba, daya daga cikin masu tsoronsa ya kwankwasa ya leko kofar dakin ya sanar masa wai wani Turhan yana son ganinsa.
"Ce ya shigo"
Aliyu ya fada ba tare da ya kalli kofar ba ma balle kuma mutumen dake tsaye yana sanar masa isowar Turhan. After 3 min Turhan ya turo kofar dakin ya shigo cikin takun sarauta da da martaba. Sai da ya karewa dakin kallo kaf sannan ya kalli Aliyu.
"Na biyo sawun Aisha, sai Ummi ta fada min ta bata, wai nemanta suke... Na yi kyautata zaton tana nan ko kusa da nan, zuwan kuma ba na iya nemanta ne kawai ba har da na gargadi"
"Da nine kai, ba zan taba bibiyar matar da na nake ganin ba ajina ba ce, ba zan taba bibiyar matar da na rusa mata ragowar farinciki ba, ban ga dalilin da zai saka na yi amai kuma na bibiyi aman na lasa ba, kazanta ai ta kazanta"
Aliyu ya fada ba tare da ya kalleshi ba.
"Toh ai ba ni ne kai ba Aliyu, ban iya cin amana ba"
"Har abada, Turhan ba sai taba zama kamar Aliyu ba, namiji yana cika namiji ne da karfin tunana da hakuri da adalci da kyautata, ba da izza ko nuna isa ba, da kai wani mai wayo ne tun a lokacin da mahaifiyarka ta yi maka kyauta da ka riketa da hakuri wata kila da duk ba mu kawo a wannan ba"
"Turhan ya fi karfin Aliyu, shiyasa Aliyu ba zai taba zama kamar Turhan ba, ta ko'ina na damaka na shanye Aliyu"
Aliyu ya juya ya kalleshi.
"Da ko wace dakika idan na yi maganarka Emily rokon take na boye maka sirrin saninta, saboda tana jin zaka rusa ragowar farincikinta, da ko wane numfashi idan na tuna na boye maka sai na ji cewar ban kyauta ba, daga lokacin da ka gane gaskiya sai na gagara samun salama na abun da nake zaton cin amana ce na aikata, amman a yau na gane abun da na aikata daidaine, na fahimci karatun da Emily take karanta min a yanzu biye da lokacin da take min bitarsa, yanzu a haka sai ka kira kanka namiji? Ka cutar da yarinyar iyakar cutarwa ta raini yarta da dadi babu dadi har ta yi wayo, rana daya ja dira a rayuwarta ka raba ta da yarinyar da ita kadaice ta rage farincikinta? A haka kuma kake neman yafiyarta? Wallahi....! Da ace zan iya sake rubuta farkon faruwar wasu abubuwa da na goge shafinku a tarihin rayuwar Emily...! Zaka gane kana sonta kawai idan ka rasa ta, kuma ka rasata...!"
"Ka iya bakinka, karka sake ka sake aikata kuskuren tsoma kanka ko bakinka a tsakanina da Aisha, balle kuma ka sako zancen yata, kuma babu kai babu Aisha babu Fatima daga yau, kallon matata ma karka sake yi, na san inda ka dosa ai, shiyasa kake zugata kake hore mata kunne kuma ka boye gaskiyar komai har sai da matarka ta gaji ta bayyana, ba kai babu Aisha daga yau, kaga dai kamar mutumen kirki mai tarbiya ashe dai kura ce lullube da fatar akuya, tirrr da kai... "
Turhan ya juya, sai Aliyu ya gyara zamansa.
"La la lala Aliyu. Bari na fada maka wani abun da baka sani ba, a lokacin da Emily zata haifi Fatima ni na dauke ta da hannuna na saka ta a mota na kaita asibiti, gurin aikinmu daya da ita, Fatima ta shaku da ni fiye da kai, na san ciki da wajen na halin Emily fiye da kai, babu abun da bata fada min ba na zamantakewarku, a Part hartcour muke zaune dukanmu, a duk lokacin da na so ganinta ziyara kawai nake kai mata. Yanzu ina son ka je ka mutu..."
Turhan ya ji zuciyarsa kamar zata fado tsabar bakin ciki da kishi numfashinsa har daukewa yayi ya dawo. Turhan ya juyo
"Kana magana kamar wanda yayi nasara, Jarumi ne kai haka kake son na kira ka? Ko kuma na taba ma? Ka taba ganin wanda yayi cin amana yayi nasara? Ko yanzu kasuwa ta watse dan kwalli ya ci riba, Fatima bata da wani Uba sai Turhan, bata da wasu family sai nawa, har abada kuma alaka ba zata yanke tsakanina da Aisha ba, kuma zaka ga sakamakonka... Ko da yake kq fara gani ai, tun a gurin matarka, yanzu kuma gaka kwance a asibiti waya san mi zai biyo baya kuma..."
Ya dauke kai ya juya ya fice yana jin wani irin bakinciki da be taba ji ba irin yau, ba a taba fada masa magana mai daci kamar ta yau ba.
KAMEELA POV.
"Au baki ci abincin ba?"
Hajiya ta tambaya sannan ta zauna bakin gadon da Kameela take kwance jiki ba kwari domin ta kwaracewa komai tun a ranar da Aliyu ya sake ta, bata fahimci girman laifin data aikata ba sai sakin ya shiga tsakaninsu, sai dai kuma sakin ya kara tabbatar mata Aliyu yana son Emily domin ko a lokacin da ta saka masa guba be sake ta ba sai a yanzu dan kawai ta dauki yarta ta kai gurin ubanta, hakan ya kara karantar da ita cewar Aliyu yana son ya auri Emily ne ko kuma shedan ya ci karfinsa yana son ya shirya zaman banza da ita. A duk lokacin da ta yi yunkurin daukar waya ta kira Aliyu da nufin ba shi hakuri sai zuciyar ta ta tuna mata ya fifita wata banza ne akanta fa, bayan marinta da yayi har da saki a cikin gidan iyayenta, gashi kuma ita ma nata iyayen sun dauki zafi sosai kuma sun goyi bayan abun da ta aikata, har suna farincikin mutuwar auren, sai dai ita ta san abu ne mai wahala ta iya cigaba da rayuwa babu Aliyu a tare da ita.
Ta yi ta sauraren ko zai gane kuskuren abun da ya kamata mata ya dawo ya bata hakuri kuma ya gyara aurensu, sam a rayuwarta bata taba tunanin Aliyu zai iya furta kalmar saki a gareta ba, kuma abun abun bakincikin ma saboda wata karuwar banza. Bata gane rabuwa da wanda kake kauna bata da dadi ba sai a yanzu da igiyar aure daya ta warware tsakaninta da Aliyu, a yanzu ne ta fahimci ashe duk son da take masa a baya karya ce yanzu ne take ainahin kaunarsa, washe garin ranar da ya sake ta ma sai da ta yi kamar zata yi karamar hauka, kamar wata mai aljannu haka ta zame musu a gidan, ta hanyar ihunta ne Mama Barakat ta san abubuwan da suke faruwa...
"Ke kan dai Allah ya wadaran wannan hali na ki, wai anya Aliyun nan ba magani yayi miki ba kamin ya zo neman ki ma? Akanki aka fara saki ne? Ina ce ga yar uwarki nan damuwa kika ga ta yi? Sai ke? Sai kace Aliyu ne autan maza, toh bari kiji na fada miki ko ma dawowa yayi ba zaki taba komawa ba, aure tsakaninki da shi ya kare har abada, da ma ya sani saki uku yayi miki ba daya ba, sai mu san shi dan iska ne"
Kameela ta tashi zaune ta sauka daga kan gadon tana share hawayenta ta fice daga dakin kasa ta sauka ta fice daga bangaren na su gaba daya, ta nufi bangaren Mama Barakat domin acan ta san ta saba jin sanyi idan wani abu ya faru tsakaninta da Aliyu, ko ba komai Mama Barakat tana bata shawarar yadda zata bullowa lamarin, ba kamar mahaifiyarta da yar;uwanta dake kara bata abun ba. A lokacin da ta shiga falon Mama Barakat ta samu ita ma shigowarta kenan daga cikin gari idonta ya kumbura yayi ja kamar zai fashe. Mama Barakat na ganinta ta katsi hanzarinta.
"Dan Allah indai kin san kin zo ne saboda Aliyu to ki tashi ki koma bangarenku, ni ma ina da nawa tarin matsalolin a gabana, Emily ce kin riga kin yi nasara akanta to me ya rage kuma?"
"Wallahi har yanzu ban yi, amman dai zan yi, sai na ga bayan yarinyar nan, kuma na zan sake zuwa neman shawara a gurinki ba"
"Karki sake ki sake zagin Emily"
Kameela har ta juya ta juyo tabe da baki jin abun da Mama Barakat ta fada.
"Tohmmmm ko dai ta miki maganin ne ke ma?"
"Emily ƴata ce...!"
Kameela ta yi dariyar da bata shirya ba, ta rike kumkuru ta kara matsawa kusa da Mama Barakat.
"Eeehhhh? God Forbid Wallahi karya ne, to ta ina? A zaren ma ba kalar yadin ba ne, sai idan dai Lake lake dangin nepa, ko lake laken ne ma Wallahi babu kama, Mama Barakat ki ma daina alakanta kanki da watsan yar iskar yarinyar kafirar ba..."
Bata kai karshe ba Mama Barakat ta dauke fuskarta da mari.
"Fita daga falon nan"
Kameela ta juya da sauri ta fice daga falon babu shiri, domin da take da Mama Barakat bata taba ganin bacin ranta irin yau ba, gashi har ya kai ga ta mareta.
"Ahhh Ahhh ni fa duk ban gane wannan ba, anya shekarar nan ba so ake na haukace ba? To ta ina ma zata zama... Oh.... Hadin kai aka yi da Aliyu ko Ummi wai ni ake son durawa bakinciki"
Ta shiga bangarensu rike da fuska tana ta mamaki sai tunani take. [7/21, 9:49 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=r_t
*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
Page 5️⃣6️⃣
Tana jefar da wayar ta cigaba da tafiya, a yanzu ta yi giving up akan rayuwarta da duk wani abun da ya shafe ta, ta sha wahala iya wahala, daga karshe kuma burinta da mafarkin da take da shi ya rushe. Jin tsayawar motar bayanta be saka ta juyo ba har sai da ta ji an fisgota an juyo da ita da karfi. Wani mutum ta gani wanda bata sani ba, ya rike ta gam sai ga wasu maza biyu sun fito daga motar wacce ta kasance ta jigila ma'ana motar haya, dukansu suna sanye da kayan gida ne.
"Ke ce Emily?"
Dayan dake rike da ita ya tambaya, sai ta daga kai ko kadan babu tsoro ko faduwar gaba a tare da ita, domin a yanzu ta shirya ko da mutuwarce tana ra'ayin a mutuwar.
"Kina tare da wani a nan ne?"
Ta girgiza kai. Sai ya ciro wayarsa ya kira.
"Mun same ta"
Yana fadar hakan ya amsa da
"Okay Sir"
Sai ya kashe wayar.
"Su waye ku?"
"Jami'an farin kaya ne"
"Me aka ce na yi?"
Yayi shiru be ce mata uffan ba kuma be sake ta ba duk kuwa da irin kokarin da take na kwatar kanta. Sai da wayarsa ta sake ringing ya daga yayi magana.
"Abunda muke gani dai babu wani rauni ko matsala a tare da ita"
Ya saka Hands-free ya mika mata.
"Emily ki shiga mota za su taho da ke"
"Waye wannan?"
"Sunana Adam Bello"
"Dr A-B, suwaye dan nan me aka ce ana yi?"
"Baki yi komai ba, na kira baki daga ba, sai na sake kira na ji kina waya bayan kin fada min kina neman taimakona, shiyasa ni kuma na nemi taimakon Babana aka yi tracing dinki"
"Na nemi taimakonka a dazun saboda ina tunanin kamar ƙwaƙwalwata ta tabu, amman yanzu na samu lafiya, bana son taimakon kowa bana son kowa kusa da ni"
"Emily ko da tsiya ko da arziki za su zo da ke, dan haka ki bada hadin kai su zo da ke ta arzikin zai fi"