Kenza eBookz

Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 64

Abokin rayuwa by khadeeja candy - Chapter 64

Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 64: Abokin rayuwa by khadeeja candy Chapter 64. Ya mike tsaye ya fice daga dakin yana murmushi don ya san duk yadda…

3,282 words

Ya mike tsaye ya fice daga dakin yana murmushi don ya san duk yadda zai buga misali ko ya ayyana Ummi ba fahimtarshi zata yi ba, nata tunanin take dabam. Falon ya sake dawowa ya nufi Kitchen kamin ya shiga Emily ta fito tana rike da hullar da ya bata, kamar mai tsoro haka ya waiga ya kalli upstairs sannan ya mika mata hannu.

"Zan iya samun hulata yanzu?"

Ta karasa ta mika masa sai ya karba ya saka a kansa tana kamshin gashin Emily da ya sha gyara da mayuka da turare.

"Mama Baraka ce ta kira waya wai tana son ki zo yau gidanta, kuma yanzu nan ma"

Emily ta dan wara ido.

"Jiya ai ta zo nan, shekaranjiya ma ta zo kamin shekaranjiya ma ta zo kullum tana zuwa"

"Toh yau so take ki tafi, kin san daman na mata alkawarin zan kawo ki, amman dai na zan samu zuwa ba direba zai kaiki, ki shiga ki shirya yanzu?"

"Ni bana marmarin tafiya gidan"

"Haka zaki daure, umarni ne ai nake baki ba neman ra'ayinki ba I'm your boss"

Ta bude ido sosai da mamakinta.

"Ai ba a gurin aiki muke ba, a nan gida ne, baka isa kamin dole ba"

Ya saka hannayensa alhaji duka biyu.

"Really?"

"Yeah..... Kuma gwada ka gani"

Yayi murmushi kawai.

"Kin san daman mun saba fada ko? So kike mu tuna baya kenan? Direba yana jiranki?"

Ya fada yana nuna mata kofa da ido, sai ta nufi upstairs ta canja riga da skirt din dake jikinta zuwa gown din atamfa har lokacin kanta babu dankwali bata samu Aliyu a falon ba, kai tsaye ta nufi kofar fita ta bude ta fita sai ta hango shi tsaye jikin wata mota dake kunne, na yi kyau? Ta tambaya da motsin baki ba tare da ta fitar da sautin ba, sai ya girgiza mata kai alamar aa ya dauke idonsa tare da hade rai yadda ake yi ma yara, ta san ba zai wuce saboda bata saka dankwali ba sai ta yi murmushi ta karasa gurin motar daya bude mata ta shiga ta zauna tana ta kallon fuskarsa domin kallonsa na daga cikin abubuwan da take so, shi kuma be yarda ya sake hada ido da ita ba ya rufe motar ya juya ya nufi hanyar shiga Falon.

Direban yaja motar suka fice daga gidan, tana zaune cikin motar shiru shiru sai kallon titi take, can kuma sai ta yi murmushi. "Aliyu" ta furta sunansa a hankalita kwanta jikin motar tana juya ido zuciyarta cike da nishadi, sai da direban ya shiga gidan sannan ta saita kanta tana kallon rayuwar baya da ta taba shigowa gidan, ta kai hannu zata bude Direban ya ce.

"Hajiya dan jira, Alhaji Aliyu yace kar na bari ki fita motar sai matar ta fito, tun da ban san wane bangare take ba"

Ya daga wayarsa ya kira Aliyu ya sanar masa suna cikin gidan. Babu jimawa Mama Baraka ta fito ta dayan bangaren da farinciki ta nufo motar da suke ta budewa Emily. Emily ta fito bata wani dauki sosai Mama Baraka ta rumgume ta tana jindadin zuwanta, sannan ta kama hannunta suka nufi bangaren da ta fito, da suka shiga gate din ta ratsa da ita suka shiga falonta, suna shiga falon Emily ta yi arba da Dr AB zaune sai ta saki hannun Mama Baraka ta nufi shi, shi mike tsaye da sauri yana murmushi suka rumgume juna.

"Kina lafiya?"

Ya tambaya bayan ya dago ta daga jikinsa, sai ta daga mishi kai.

"Ina lafiya, yaushe ka zo ya aka yi ka zo nan?"

"Saboda ke"

Ya kama fuskarta ya rike.

"Madam Baraka ta fada min komai, a washe garin da kuka bar gidan, kuma na jidadi da ya zama ina da alaka da ke"

Hawaye ya sauko mata ta runtse ido tana jin wani sanyi na sanin cewar shi dan"uwanta ne kuma ya karbeta.

"A yanzu na gane dalilin da yasa nake ta son kasancewa da ke Emily, kowace haduwa kaddara ce take shirya mana ita, amman na kasa cireki a raina na kasa manta duk wani abu daya shafe ki, ada ina tunanin kamar na samu mata ne, ban sani ba ashe ke jinina ce, tun dawowarki gidanku zuciyata ta fara raya min kamar kina da alaka da mahaifina saboda kamar da kike da shi ta yi yawa, amman sai na rika tambayar kaina ta ina? Taya yaya? Da kika ba mu labarin rayuwarki, sai na fara tunanin ko sace ki aka yi aka jefar a can? Ko kuma dai bayan Momy mahaifina ya zauna da wata matar? Ita kanta Momy ta fada min kina kama da Mahaifina"

"Ina Momy take?"

"Tana gida, ni na saboda ke na zo, kuma yau zan koma"

"Ta samu labarin abun da ya faru?"

"Eh sai dai bata yi maraba ba, bata shirya karbarki yanzun ba"

Emily ta kalli Mama Baraka sannan ta kalli Dr AB

"Tana da gaskiya, kuma be zama dole ta karbe ni ba, shi kanshi be zama lallai ya karbe ni ba idan ma yana raya"

"Yana raye, na kan je na ganshi a duk lokacinda bukatar hakan ta taso, kuma shi mutum ne mai son yara zai yi farinciki dake na tabbata"

Emily ta zauna.

"Ina son na ganshi, kamanin da ake cewa ina yi da shi ina son na ga ya fuskata take a jikin wani" Dr A-B ya zauna kusa da ita ya ciro wayarsa ya kama hotonshi ya mika mata wayar. Yaran Mama Baraka duk suka fito suka zauna suna kallon Emily. [8/13, 10:39 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*

*© Khadeeja Candy*

Page 6️⃣6️⃣

Mama Baraka ta gabatar mata da yaranta suka gaisa da Emily suka rumgumeta. Emily ta zauna tana hawaye.

"A tsawon rayuwata, na yi ta ne ni kadai, idan na hango wani mai dangi ko iyaye sai abun ya burge ni, saboda na yi tunanin ni ba ni da kowa, ba uwa ba uba ba yan'uwa ban san yadda ake ji ba, amman hakika iyali suna da dadi"

Dr A-B ya kai hannunsa ya rika nata.

"Wani lokacin kaddarori sukan faru da mu, wadanda ba mu isa mu canja komai daga karesu ba, idan ka hango wani yana rayuwa mai kyau sai ka ji ina ma kai ne, idan kuma wani yana rayuwa marar dadi sai ka ji dadi da ya kasance ba kai ba ne, hakan yana nuna mana ba mu da ikon canja komai daga kaddarar mu, domin da za mu iya da mun zama irin wadancan da su ke burge mu, tun da ba za mu iya ba, ai sai mu yi hakuri mu da yadda muka samu kan mu, abun da duk ba zaka iya canja shi daga halitta ko kaddara halayya ba toh be kamata ya zama abun damuwa ba"

Emily ta daga mai tare da kai dayan hannunta ta rike hannunsa daya da duka hannayenta, ita kadai ta san me take ji lokacin da bata da kowa, haka kuma a yanzu ita kadai ta san yadda take ji da ta samu yan'uwa.

"Na san idan Daddy ya ganki zai yi farinciki domin ko yayansa da suke can ba su yi kama da shi sosai kamar yadda ke kike kama ba, kuma mutum ne mai son yara, na kan ziyarce once in a while"

Ta yi murmushi ta sauke kai kasa tare da kai hannunta daya ta share hawayenta, jin an taba kofar falon ya saka ta dago ta kalli kofar sai suka yi ido hudu da Turhan, murmushin dake fuskarta ya gushe ta kalli Mama Baraka dake zaune, sai Mama Baraka ta girgiza mata kai ta juya ta kalli Turhan da ya tunkaro inda Emily take zaune, idonsa a kanta zuciyarsa na bugawa ganin hannun Emily cikin na Dr A-B.

"Ban ce ya zo ba, ban san da zuwansa ba, yana zuwa nan mu yi magana amman yau ban fada masa zaki zo ba, kuma ba saboda shi na shirya wannan ba, na shirya miki wannan liyafar ne saboda ina sha'awar ki zo kusa da ni, kuma ina nufin baki mamaki da Dr A-B ne, ba Turhan ba"

Mama Baraka ta fada cike da tsoron batawa Emily rai.

"Ni na ce ya zo"

Emily ta kalli Dr A-B.

"Ya kamata mu zama masu yafiya Emily, dukanmu muna laifi wa junanmu, kuma akan daga mana kafa a yafe mana, na san abun da ya aikata be kyauta ba, kin ba mu labari, shi ma kuma ya maimaita min cikin nadama, kusan shi ne dalilin zuwa ba wai domin Madam Baraka kawai ba"

Emily ya maida kanta kasa tana jin kamar suna son mata dole ne. Dr A-B ya matsa kusa da ita yana mata magana a hankali yadda zata fahimta. Turhan ya zauna a kujerar dake fuskantarsu yana maida numfashi da karfi, be tana sanin yana kishin Emily har haka ba sai a yau da wani wanda ba Aliyu ba ya zauna kusa da ita kuma ya rike hannunta, saukin abun ma tana da alaka ta jini da shi, da ba haka ba wata kila na zai iya zama ya kalli wani yana kallar masa mata har ya rika hannunta ba.

"Ni ma na ba shi rashin gaskiya na abun da yayi, kuma ya karba ya nuna min ya fada min kuma na ga hakan cewar yayi nadama, ban fadawa Madam Baraka ba, amman ya fita matsawa na zo saboda yana ganin ina da alaka da ke kamar idan na saka baki zaki iya yafe masa"

"Na yafe masa ai, na fadawa Ammy tun satin da ya wuce, komai ya wuce yanzu gaba nake hari"

Dr A-B yayi murmushi.

"Haka nake so, daman na san baki da wahalar sha'ani, na gode"

Turhan yayi murmushi, Dr A-B ya daga ya kalleshi.

"Ka yi farar dabara da ka biyo ta gurina gashi ya yafe maka"

"Na jidadin hakan, kuma ina son na kora da bayanin yadda aka yi na san Dr AB dan'uwanki ne, na biyo ta bangaren Mama ne, na fada mata komai kuma na roki yafiyarta na roki ta nema min taki, sai ya zama ita ma tana jin tsoro, hakan ya saka na yi kamun kafa da Dr Adam bayan Mama ta fada min komai na rayuwarki, Congratulations Aisha yanzu komai ya samu, ina miki murna"

Emily ta kalleshi kawai ta dauke kai. Emily bata sake sakewa ba a falon saboda Turhan yana ciki, not because of bata yafe masa ba, ta yafe masa har zuciyarta sai dai ta kasa jin walwala saboda yana kusa da ita, idonsa akan duk wani motsi nata. Da suka hadu dinning gurin cin abinci Turhan ya zauna saitin da Emily take, abincin kadan ya ci, Emily ma kadan ta ci tana murmushin dole.

"A yanzu nan zaki zauna ne?"

Dr A-B ya tambaya.

"Aa ina zama gurin Ummi ne"

Ya dan tabe baki.

"Haka Madam Baraka ta fada min, gidansu wannan yaron ko?"

Emily ta kalleshi tana murmushi

"Aliyu ba yaro ba ne"

"Yayi kamar ni?"

"Aa amman dai ba yaro ba ne"

"Okay, idan kina zon zama can ba laifi, amman dai ki kula da kanki"

"I will"

Ta aje spoon ta mike tsaye.

"Zan shiga bandaki"

"Muje na nuna miki"

Daya daga cikin yaran Mama Baraka ta fada, ba musu Emily ta bita zuwa sama ta nuna mata bandakinsu sannan ta fito. Emily na shiga ta maida kofar dakin ta rufe ta jingina ta busar da numfashi.

"It's okay Emily, that's how life is komai ya wuce, Turhan shi ne uban yarki, na zaki iya canja wannan ba, dole alaka zata shiga, akan yarsa kawai ba akanki ba, yanzu komai ya wuce"

Ta fadawa kanka da nufin karfafawa kanta guiwa, sannan taja numfashi ta sauke har sau uku ta bude kofar ta fito. Ta sauko sai ta zauna a sitting room bata koma dinning din ba, ba su san ta sauko ba sai da suka gama cin abinci suka taso. Sai kuma ga Mahaifin Kameela ya shigo cikin sakin fuska ya mikawa Dr A-B hannu suka gaisa.

"Ban san ka zo ba, sai da muka yi waya da Mai gida yake tambayar ya ka sauka kuma an mata tarba mai kyau"

"Tafiya ce ta gaggauwa shiyasa ban fadawa kowa ba, shi ma ya sani ne saboda wasu dalilai, na zo ne saboda kanwata Emily fatan na same ku lafiya"

"Alhamdulillah, muna maka maraba da zuwa, mu shiga ka gaisa da sauran yan gidan mana"

Mahaifin Kameela ya rike hannun Dr A-B suka fita falon suna magana ya shiga da shi bangarensu Kameela ya gaisa da su da sauran yaransa, yayi hakan ne saboda Dr A-B da duk sauran business partners dinsa ba su san Hajiya ba, Mama Baraka aka sani da ita yake yawo, a yanzu kuma basa tare. Da suka fita sai ya zama falon daga Mama Baraka sai Misra second born dinta after Emily, and Turhan.

Mama Baraka sai jan Emily take da hira sama sama a kasan zuciyarta kuma bata jidadin abun da mijinta yayi ba, domin da ya shigo be kalleta ba balle yayi ma Emily yayi magana, ko da yake a yanzu ba zata kira shi da mijinta ba sai dai uban yayanta. Turhan kan idonsa na kan Emily wani irin kallo yake mata da ya tafi da hankalinsa ya kusa hango masa yadda jini yake yawo a jikinta. Emily ta mike tsaye.

"Bari na jira Dr a waje"

Mama Baraka ta kalleta.

"Ba a nan zaki kwana ba"

"Aa maybe wata rana amman ba yau ba"

Turhan ya bita da kallo har ta fice falon sannan ya kalli Misra dake kallonsa ya kalli Mama Baraka ya ciro wayarsa ya shiga tabawa. Da Emily ta gaji da tsayuwa sai ta fita gaban gate din bangaren Mama Baraka tana kallon katon gidan, hakan yayi daidai da fitowar Dr A-B bangarensu Kameela suna tafe Alhaji na masa hira, Kameela da yan'uwata da kuma Hajiya suna tsaye jikin gate din bangarensu.

Alhaji be karaso ba ya tsaya nesa da bangaren Mama Baraka, Dr A-B ya karasa shi kadai ya kama hannun Emily da bata san Turhan na tsaye bayanta ba domin nata idanuwan suna gurin Kameela dake aiko mata da wani kallo mai cike da tsana da kiyayya.

"Ka dawo"

Mama Baraka da fitowarta kenan ta fada.

"Eh zan wuce yanzu, mun gaisa da su, ashe kina da co-wife ban taba sani ba sai yau"

Mama Baraka ta yi murmushi.

"Ka ga zuwan ai yayi amfani, daman ba ni kadai ba ce mu biyu ne ita ce uwargida"

"Maa Shaa Allah, Emily a nan zan barki ne ko kuma zaki raka ni Airport?"

"Zan raka ka Airport"

"Okay"

Ya mikawa Mama Baraka hannu.

"Thank you so much Madam Baraka i appreciate everything"

Mama Baraka ta gaisa da shi, kusan abu nw da ya sana shaking hands da kowa. Sannan ya dafa kafadar Emily to him ita ce kadai yar'uwa ta jini da yake da a kusa a yanzu yana jin muhimamcinta fiye da baya. Tare suka nufi mota ya bude mata gidan baya ta shiga shi ma ya shiga yana dagawa Alhaji hannu. Mama Baraka ta shiga dayar motarta tare da Misra. Kameela ta bisu da kallo har motocin suka fice zuciyarta kamar zata fashe saboda bakinciki.

"Hmmm, wai ni aka zo a nuna bakinciki, ga mijinta a gafe ta hada da nawa Aliyu ta zabi wanda take so ko? Ga wani yayanta wai shi mai kudi, ga ubanta bature, ga ta kyakkyawa arziki na daya ma ba da aure aka haife ta ba, da yanzu ina zan kai bakinciki nan? Ga Mama Baraka tana kishi da uwata, diyarta kuma ta karbe min miji, ta hada da nata, wannan bakinciki da me yayi kama? Shekarar nan idan ba so ake na haukace ba me ake so na yi?"

Ta fada cikin kuka bayan mahaifinta ya bar gurin.

"Ke yanzu miye hadinki da Aliyu? Idan ma dafa shi zata yi ta ci ai sai ta yi"

Anty Shafa ta fada, Kameela ta kalleta a fusa.

"Aliyu mijjna ne, kina tambayar alaka ta da shi? Duk ba ku kika kashe min auren ba? Kullum mijina yana cikin bakinku cin mutunci babu wanda baku masa, idan ku ba ku san shi ni ina son mijina, yanzu ai gashi nan ya sake ni"

"Uban waye ya aikeki saka masa guba a abinci? Ke ba dan ya sake ki ya kyale ki ba ai da yanzu ma gidan yari za a kaiki, karyar banza karyar wofi har ke fada mana wani wai kina son shi, kina son shi kika tashi kasheshi? Ko kina son shi kike daukar sirrinki ki kaiwa Bakar Mama Baraka? Yanzu wa gari ya waya?"

Anty Shafa ta maida mata da martani.

"Idan ban tafi da damuwata gurin Mama Baraka ba ina zan je? Saurarata kuke yi? Burinku Aliyu ya sake ni kuma ya sake ni, ita kuma zata dauki bakar kafirar yarta ta aura masa ai"

Hajiya ta daka musu tsawa.

"Miye haka wai? Sai yayanta sun kwashe komai sun fada mata an dawo amana mana dariya? Ke kuma Aliyu autan maza ne da zaki zauna kina fadawa yar'uwa ki magana saboda ya sake ki? Ke daga kin auna arziki ma baki haihu da shi ba? Nan da kwana biyu zaki shige wani gidan, daman can Aliyu ba sa'ar auren ki ba ne, manyan mutane suke sonki kika nace sai shi waya sani ma ko ba banxa ya barki ba? Ɗan makiyinmu kika dage sai kin aura kuma kika aura uwarsa ta mana cin mutunci"

Kameela ta fashe da kuka ta juya ta koma ciki a fusace.

Turhan da ya shiga motar ya dauki hanyar gida, yana jin farinciki sosai domin Emily bata taba sake masa haka ba and he feel something special about her today.

"Ina son Emily ba ki sani ba ne, na yi farin ciki kin samu family a yanzu, kuma na miki alkawari idan kika ba ni dama ta biyu ba zaki yi nadama ba, zan maida ke sarauniya zan baki gatan da ba a taba baki ba, ke kika fara dandanin dadin zama uba, ke kika fara saka ni wannan farinciki, kuma kika yarda kika aure ni saboda Ammy, na yi kuskure na sani, amman yanzu na miki alkawari zan jiyar da ke dadi na wadata ki da komai zan ninka miki farinciki fiye da wanda kika sani, shiyasa na yi alkawarin zan yi hakuri zan jira har ki aminta da ni, kalli yadda kike da kyau da shiga rai, kika ba ni ƴa mai kamanina, to me kuma zan nema a gurinki? Sai dai ni na nemi saka miki, ina son komai naki Emily ina son duk wani abu daya shafe ki, zan kaiki inda ban taba kaiki ba, zan siya miki tufafi mai tsada, zan rumgume ki na nuna miki yadda nake kaunarki na baki kulawa"

Yana tuki da hannu daya dayan hannunsa kuma yama shafa kansa yana magana da kansa sai murmushi yake kai kace Emily ce kadai matar da ta rage masa a duniya. Ya isa gidansu tun kamin ya faka motarsa harabar gidan Ammy ya fahimci akwai baki a gidan domin yayi arba da manyan motoci da be tantance na waye ba. Ya faka motar ya fito yana kallon motocin ya tun kari kofar falon, sai kamshin turaren masarautarsu ya tunkari hancinsa. Ya tura kofar da hanzari ya shiga, dogaran da ya fara arba da su suka saka shi fadada murmushinsa, ya kai tsakiyar falon yana jin wata madarar dadi sakamakon arba da yayi da mahaifinsa zaune a falon na Ammy.

EMILY POV.

"Na ga nadama sosai a gurin mutumen nan, kuma na jidadi da kika yafe masa, kuna da ƴa a tsakaninku ya kamata ace kun fahimci juna"

Emily dai ta yi shiru bata ce komai ba sai kallon titi take.

Readers Also Read