Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy - Chapter 13
Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 13: Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 13. "Akan su aka fara faduwa zabe ne? Kujerar sanata…
4,490 words
"Akan su aka fara faduwa zabe ne? Kujerar sanata tuwon gidansu ne da za ace dole ko wane zabe sai sun ci? Yanzu saboda sun fadi Allah yace mahaifinka ne zai ďana sai abu ya zama dan zane? Har yana neman zama cin mutunci?"
"Ayi hakuri Ummi In Shaa Allahu hakan ba zai sake faruwa ba"
"A'uzubillahi wannan hassada ta yi yawa, idan son suke su kashe auren su aura mata Governor su sani dai yarsu ba daraja zata yi a idonsa yanzu ba, kuma wahala kawai zata je ta sha da wannan bakin kishin nata, kuma ya ma yi aurensa me zai yi da ita yanzu"
"Ummi kin hau da yawa, Allah ya huci zuciyarki amman dai idan tunaninsu kenan sun yi kuskure domin babu saki tsakanina da Kameela, ko ba ita ba daman na kudurta a raina duk abun da zai faru ba zan taba iya sakin matata ba, kuma na mata magana In Shaa Allahu irin wannan ba zai sake faruwa ba"
"It better, domin na fara gajiya sai kace kansu aka fara siyasa, shekara nawa Engr yana hakurin faduwa zabe sai bana dan Allah ya ba shi sai kuma su juyar da siyasa kiyayya"
"Ummi ayi hakuri"
Ta masa kwatankwacin abun da yayi ma Kameela, ita ta kashe wayar a cikin fushi. Ya sauke ajiyar zuciya.
"Daddy ma lalabawa yake da Ummi, balle ni da nake ďa, iyayen Kameela suna neman kunno min wuta"
Ya fada cikin yanayin damuwa. Sai bayan bayan sallah magariba Kameela ta kira shi tana bashi hakuri suka jima suna waya, yawanci abun da take bincikarsa na ina yake cin abinci ne sai kuma inda yake zuwa yanzu da bata gidan.
"Ina zan je? Ina gida mana"
"Yaushe zaka zo"
"Soon"
"So soon"
"Not so soon"
"Okay, ka kula min da kanka, kuma dan Allah kar ganin bana nan ya saka ka rika kula mata ko kallonsu"
Yayi murmushi kawai ya girgiza kai.
"Toh ranki ya dade"
Ta yi dariya, ya mata kiss a wayar sannan suka yi sallama.
KAMEELA POV.
Tana sauke wayar Farida ta shigo kiranta wai Abbansu yana son ganinsu gaba daya a bangarensa, haka suka dunguma gaba daya suka tafi bangarensa suka zauna har Mama Barakat da Kameela ke ta harara. Alhaji Tukur Nazifi Ataka ya fara kallon Hajiya Asma'u ya ce.
"Waya ce a mai da kayan barkar da aka kawo?"
"Alhaji ba fa wani kayan kirki bane, kamar gidan nan za a kawo kayan barka akwaiti 10, ko ya muke riko a gidan nan ai ta fi karfin haka balle kuma jininka, da gangan suka yi saboda su walakanta mu"
A take Alhaji Tukur tsohon sanata ya rufe ta fada.
"A wane dalili za a maida? Idan ma sun yi ne saboda abun da kike tunani miyasa za ki fiye masu? Wannan ai rashin dattako ne, kuma ba kowa ya janyo ba sai Kameela, su basa tunanin komai sai soyayya, gashi nan tun ba aje ko'ina ba sai abubuwa ake samu na rashin jindadi, toh daga yau sai yau kar a sake aiko wani abu daga gidan Bappa Mudallab a maida shi, ko ba can ko daga ina ne kar hakan ya sake faruwa"
Ya kalli yaransa daga mazan har mata a fusace ya ce.
"Ku kuma a cikinku kar wanda ya sake dauko ya ko dan makiyinmu yace sai zai aureshi last warning, shiyasa na tara ku a nan"
Mama Barakat ta ce.
"Alhaji ayi hakuri, kar a bari siyasa ta yi tasiri akan rayuwar yau da kullum, na san faduwar nan bata yi ma kowa dadi ba, amman kar a hana yara abun da suke so"
Hajiya Asma'u taja tsaki.
"To ke me kika sani a siyasa Barakat? Da har zaki fadi haka? Siyasa ai mu muka santa ciki da waje, domin Alhaji tun yana ba shi ba nake fadi tashi da shi akan siyasa har ya zama wani abu a yanzu"
Alhaji Tukur ya kalli Hajiya Asma'u domin ya san da biyu ta fadi maganar.
"Me ya kawo wannan maganar yanzu? Ku tashi na sallami kowa"
Mama Barakat ta yi murmushi ta mike tsaye ta fice daga dakin, Hajiya Asma'u ta watsawa bayan Mama Barakat harara ta jin haushin yadda take karkada mazaunai kai kace da gayya take yi. (Mtssss kayan kashi) ta fada a ranta sannan ta mike tsaye suka fice ita da yaranta.
ALIYU POV.
A yau ya shigo aiki da wuri domin gidan yayi masa ba dadi, saboda hatsaniyar da aka samu tsakanin iyayensa da na Kameela gashi kuma Kameela bata gidan baya jin motsin kowa sai hakan ya saka shi jim gidan yayi masa girma. A nan yayi breastfeed yana gamawa ya kira Kameela suka gaisa ya ji tashinta, a nan ta saka masa kukan yaron da ta haifa ya koma, wai sai a yanzu take jin babu dadi abun yana damunta har mafarki take. Rarrashinta yayi ta yi sannan suka yi sallama, ya dauko qur'anensa dake office din yayi karatu daidai gwargwadon yadda zai iya sannan ya aje bayan yayi addu'a ya amsa kiran Turhan dake shigowa wayarsa ta WhatsApp video call.
"Salam.."
"Hey Aliyu ya gidan ya aiki?"
"Lafiya kalau, ya Ammy?"
Aliyu ya tambaya yana karantar ramar da abokinsa yayi.
"Tana kaduna"
Yanayin yadda ya amsa masa ne ya bashi tabbaci ya bar kasar.
"Ka koma Sudan ne"
"Eh jiya, abun da naje nema ban samu ba, still Ammy bata duba hakan ba, anyway na kira ne na maka barka matar ta haihu ashe?"
"Eh amman yaron be zo da rai ba"
"Eh Allah ya baku hakuri, kara kai ai kana haihuwar ba kamar ni ba, ban ma san ya ake ji ba idan aka rumgumi yaro"
Tausayinsa kadan ya fada zuciyar Aliyu.
"Kai ma wata rana zaka rumgumi yayanka In Shaa Allahu"
"Ina fatan haka, agaishe da Madam"
"Zata ji"
Daga haka suka yi sallama, Aliyu yana jin kansa kamar wani mai laifi, meyasa Emily zata daure shi har haka? Ya kasa fadawa abokinsa a inda take tare da yarsa. Ya dago yana kallon kofar dakin da aka kwankwaso.
"Yes"
Nick ya shigo ya sanar masa Emily tana son ganinsa, Aliyu yayi shiruuuu yana kallon wani gurin kamin ya bash izinin shigowa da ita. Ya mike tsaye ya nufi windows din office din ya bude ya tsaya a gurin yana kallon kasan benen. Emily ta turo kofar office din ta shigo tana sanye da short gown black color gaba daya ta daure gashin kanta a baya tana rike da makulli mota da wayarta, sai kuma agogonsa a dayan hannunta. Ta dade tana kallon bayansa sannan ta matsa kusa da teburinsa ta dora agogon.
"Zumudin zuwa ganin mutumen da ya taimake ni a yau, be bar ni na runtsa ba, da na zo ban san office din ba da tambaya na kawo kaina a nan. Kullum mafarki da buri na yadda zan maida alherin da aka yi min ne da alheri, na kasa manta yadda ka ceto rayuwata, a lokacin da ba ni da kowa babu mai taimako na, Vito yana yawan cewa na jefar da agogon nan ko na manta da shi, sai na fada masa indai har zan iya manta alheri to zan iya mantawa da agogon, manufar ba ta agogon ba ce kawai, ta mamallakinsa ce, ashe kuma na aje kwarya a gurbinta ne, ashe dai ka cancanci ko kasa ka taka na jimke na aje"
Ta share hawayen idonta.
"Ka taimake ni a lokacin da iyalinka da kai kanka kuke neman taimakon juna na karfafa guiwa, baka damu da addinina ko kazantar da take jikina ko ciwon yarona na ba ka taimake ni, hakika Aliyu kai mutumen kirki ne, kuma na yarda a ciki musulmai akwai na gari"
Sai a lokacin ya juyo ya kalleta kallo daya ya dauke idonsa.
"Duk abun da na yi na yi ne saboda Allah"
"Fada min me zan yi na rama daya bisa ukun abun alheri da ka yi min?"
Ya nuna mata kujera sannan shi ma ya zauna.
"Wacece ke? Tun farkonki har zuwa yau, yadda kika hadu da Turhan har zuwa rayuwarki ta yanzu, shi kawai nake da bukata a gurinki yanzu"
Ta nuna kanta tana hadiye bakin cikin daya tsaya mata.
"Ni... Ńi ni ce kawai, ni ce wata yarinya data tashi a gidan marayu bata san kowa ba sai kanta da mafarkinta..."
Taja numfashi ta lumshe ido, Aliyu ya kalleta a karo na biyu kwarjin farar fata a cikin bakin tufafi ya cijeshi, ya dauke idonsa da hanzari ya maida akan agogon da ta aje masa. [4/28, 6:57 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 1️⃣8️⃣
*June 4 2014* *Lagos State Nigeria.* *Little Saints Orphanage (ABULE EGBA HOUSE) 149, Carpentar B/stop, Ekoro Road.*
*MAFARI...*
Tafiya na ke a hankali ina kallon sababin talkamin da suke kafata wadanda wata kungiyar taimakon kai da kai ta kawo mana tun satin daya gabata. Talkamin sun min kyau sosai a kafa kamar daman dan ni akai su.
"Emily.."
Ina jin muryar mai kiran na juyo fuskata ba yabo ba fallasa na kalleta.
"Ibo lo lo?"
Ta tambayi gurin da zanje da yaren da mafi yawan marayun da suke zaune a wannan gidan na marayu suka fi ji, wato yarbanci.
"Mo n lọ si ọja lati ni awọn eso diẹ. kilo de ti o bere?"
"Ohunkohun. irin ajo ailewu"
"O dara emi yoo pada wa ni titọ"
Na karasa amsa mata tare ta mikawa mai gadin gate din gaisuwa
"E kaaro arabinrin"
Sai ya amsa min da murmushi.
"O dara, Ọlọrun yoo bukun fun ọ"
"Amen"
Da kansa ya bude min gate din duk kuwa da kasancesarsa dattijo, amman yana ganin girma da kuma mutunci. Wani dogon numfashi na ja na sauke sakamakon iska mai dadi da take kadawa, daga kaina nai sama ina kallon hadarin da ke haduwa a tsararin samaniya rana tana ta lumshi tana budewa gwanin sha'awa. Babu mutane sosai daman unguwar ekero road, kamar gra take abu ne mai wahala ka ci karo da hayaniya ko kaikawo na jama'a kamar cikin tsakiyar lagos. Mini skirt ne a jikina mai aljihu sai wata farar vest mai kama da ta kwana wuyana na sanye da sarkar cross hannuna ma yana rataye da warwaron wanda akai da farin dutse. Kitso ne jan gashin dake kaina, na yi parking dinsa da ribbon tsorayen sun sauko har bayana.
Tafiya nake cikin natsuwa da aminci, zuciyata kuma nata rara min wakar da muke a coci duk da kasancewar bana jin natsuwa da da wakar amman sabo yasa ni yake jin dadinta. Sai da na fito daga unguwar gaba daya na nufi hanyar da zata sadani da wata karamar kasuwa da take layin. A bakin titi na tsaya sai da motocin suka gama wucewa sannan na tsallaka zuwa gaban teburin wani mai siyar da kayan marmari. Na tarar da mutum biyu a gurin so hakan na nufin dole nai hakuri na jira har ya sallamesu. Da yaren igbo suka yi magana dayan ya siyar masa da abaya da kankana dayan kuma mai zubin hausawa sai ya mika masa dubu biya yace ya hada masa kayan marmarin da turanci. Na saba siyayya gurinsa magidanci ne mai jin yaren igbo domin shi baya jin turanci balle kuma yarbanci, rike kudin da mutumen ya mika masa dan be san abunda zai bashi ba, shi ko kyakkyawan saurayin mai kama da mazan novel ya dage sai bayani yake masa da turanci.
"Kaji matsalar rashin jin yaren mutane"
Ya fada cike da jin haushi.
"Kuma ba zaka nemi taimakon kowa ba?"
Da mamaki ya kalleni jin na masa hausa.
"What did you just said?"
Murmushi nai ban bashi amsa ba, na kalli mai siyardar kayan marmarin na fada masa cewar ya hada masa na dubu daya da dari biyar kamar yadda ya fada masa da yalshen turanci da farko ni kuma na fada masa da yaren da yake ji wato yaren igbo.
"Nye ya puku akwukwo nri"
Sai ya amsa da okay ya shiga hada masa. Mutumen ya matsa kusa da ni.
"Kina jin yarena?"
"Duk mutumen daya zauna lagos dole ne yaji yare kala biyu, ko dai ya iya turanci ko kuma yarbanci, har da igbo ma idan ta kama, domin shi wannan mutumen baya jin yarbacin igbo yake ji, ya kamata ka koya"
Na fada masa ba tare dana kalli inda yake tsaye ba. Murmushin kasaita ne ya bayyana a fuskarsa da alama na burgeshi jin ina hausa kamar jakin kano.
"Amman ina kika koyi yare nan har hudu turanci, hausa, yarbancin, igbo wace yare ce ke?"
Kallonsa nai muna hada sai yayi saurin kawar da nasa, ba mamaki blue eyes dina ne suka firgita shi.
"Ban san yarena ba"
"Why?"
"Because ni marainiya ce"
Fuskar tausayi yai ya zuba hannayensa a aljihu.
"Ayyah I'm sorry"
"You shouldn't, it's not your fault"
"Yeah i know, mi zaki siya a nan"
"Ayaba ina son ayaba"
"Owk you look cute"
Ya fada yana kallona.
"Thanks handsome"
Na fada still ban kalleshi ba. Sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro dubu uku ya mika min.
"Gashi ki siya"
"No na gode"
Na fada ba tare da na kalli kudin ba.
"Wow ba kasafai zaka bawa yarinya kamarki a lagos kudi ba ta ki karba"
"Likewise, ba kowa zai iya kyautar kudi a take ba a Lagos sai bahaushe"
"Yeah musulumci ya koyar da mu rika kyauta saboda halin Annabin mu ne, by the way sunana Hamza Ali ana kirana Khaleefa"
Cike da burgewa na ke kallonsa, ban san abunda yasa na ke son naji ana maganar abunda ya shafi musulumci ba Hannu na mika masa
"Ni kuma sunana Emily Emmanuel"
Kin karbar hannun yai.
"Mu musulmai bama gaisawa da mace musulumci ya hana mu sorry"
"Never mind"
Sai da mutumen ya mika masa ledar kayan marmarin sai ya karba yana kallon.
"Fada masa ya rike canjin"
Da yaren Igbo na fada masa cewar ya ce ya bar canjin, sai ya mikawa mutumen dubu ukun.
"Ki fada masa abunda kike so ya hada miki, nice to meet you young lady"
Ya fada yana kallona kasa da sama, kamin ya buga babur dinsa ya daga min hannu yana murmushi ya wuce. Murmushi nai na rashin dalili na bishi da kallo har na daina hangoshi.
*** *** ***
Godiya mutumen igbo yai min sannan na fada masa abunda zai bani ya hada min da sauran canjina na kamo hanya cike da farincikin da ban san dalilinsa ba, kawai dai ina jin nishadi ya cika min zuciya da ruhi. Ina tafe ina wasa da dayan hannuna mai nade da sarkar cross sai aka fara yayyafi, kowa ya fara gudu an fakewa a wani gurin domin ruwan ya sauka da karfi, ni kam tafiyata na ke da dai daya ina daga kaina sama ruwan yana saukarka min a fuska da kai. Hango bakin shagon wani mutume dake road din mu babu kowa a gurin yasa naje gurin a guje na aje ledar hannuna na fito tsakiyar titi da babu motoci na tsaya ina waka da ruwan saman ina juyawa ina rawata domin babu abunda ya dame ni. Shakaf ka jike a guri a gurin idan na hango mota tafe sai na koma gurin shagon a guje na fake dugun kar a min daukar mahaukaciya sai motar ta wuce sannan na fito na cigaba haka nai ta yi har aka gama ruwan a kaina. Sannan naje na zauna bakin teburin mutumen na saka hannuna a aljihu na ciro yar karamar wukar da babu wanda yasan ina yawo da ita na dauki lemu daya na yanka na sha. Sai da naji na koshi da kayan marmarin sannan na faki idon mutane na maida wukar ajihuna, na dauki ragowar kayan marmarin na kamo hanyar gidan marayu wanda zan iya kiransa da gidanmu ko kuma na ce gidana. Kamar dai dazun yanzu ma sai da muka gaisa da mai gadin gurin har yake min sannu da jikewar da yai sannan na wuce sashenmu wato block C. Rossy na ganina ta rugo da gudu ta tare ni, daman ta saba min haka ita ba ma ita kadai ba har da sauran an block din, domin ni mutuniyar kowa ce komai nawa na kowa ne, idan na samu bana iya ci nidai ko da basu san da shi ba.
"Ku aabọ pada. arabinrin mi"
Ta min sannu da zuwa da yaren yarbancin tana kokarin karbar ledar hannuna. Sakar mata ledar nai ina murmushi na ce.
"Kije ku raba tare da du Elina"
"Wow wato oga shakur yayi miki sallama ta kwarai kenan nan yau"
Da yaren yarbancin muka yi maganar ni dai murmushi kawai nai na kama hanyar dakinmu, daman na san kowa zai dauka cewar kyautar oga Abdulshakur ce, domin ya saba min irin wannan sallamar idan rana tai hi kyau. Oga Abdulshakur wani oganane a gurin aikin gyara mota, shi yake da gurin a gurinsa nake zuwa ina koya duk kuwa da kasancewarsa musulmi, na fara aikin ne a lokacin dana kare makarantan kuma ban samu damar shiga babba ba, an rubuta takarda zuwa ga gabnatin Lagos domin daukar nauyin karatun mu zuwa mataki na gaba mu yan wannan shakarar da muka gama, amman har yanzu babu wani abu da ya fito daga can, wata kila dan aikin har yanzu be kai ba, ko kuma ta manta da sha'aninmu ne. Ni kuma bana son zaman banza ba aiki, bayan kuma shugaban gidan marayu ya bawa kowa damar mai son aiki ko sana'a yayi domin tallafawa kansa. Ko da na shiga dakinmu babu kowa sai Nine ackor ita kadai a gafenta tana bachi, dakinmu babban daki ne mai daukar mutum takwas kamar sauran dakunan, an kawata dakin da kananan gadaje na kwanan mutum daya da yar karamar waduruf ta saka tufafi. Gadona kusa da window yake hakan kuma na min dadi duk kuwa da kasancewar wani lokacin ina jin tsoro. Tufafin jikina na fara cirewa na canja zuwa wata yar karamar gown, sannan na dauki wukata na saka a cikin jakata inda na saba ajeta, gado na hau na kwanta fuskata da murmushi mutum dazun ne har yanzu na kasa daina ganinsa a idona, yana da kyau sosai kamar wani aljani gashi fari ni kuma ina son fararen mutune duk kuwa da kasancewata fara.
'Musulmi ne fa!'
Zuciyata ta fada min, miyasa zan yi tunanin musulmi bayan a coci ana yawan fada mana cewar musulmi yan ta'adda ne kuma basa son kistoti irina, a take gabana ya fadi sai na ji kamar nayi wani sabo, take nai saurin praising Jesus na roki gafarsa, nai saurin tasowa na baro dakin gudun kar tunanin ya sake dawo min na samu zunubi.
Haka muka raya yammacin ranar da laraba tare da yan'uwana marayu, sai da dare yai sai na nufi gurin dana saba zama na zauna karkashin wata bushiyar lemu na jingina jikina ina kallon sama, yadda taurarin suka jera abun ya burgeni sosai, sun yi ma sama ado sai sheki suke, kirgasu na fara yi da yatsana duk kuwa da kasancewar na san ba zan taba iya kirgesu su duka ba, wata maganar taurari ce dake cikin Bible ta fada min a rai.
"Sa'an nan sarki Yosiya ya umarci Hilkiya, babban firist, da firistoci masu daraja ta biyu, da masu tsaron ƙofa, su fitar da tasoshin da aka yi wa Ba'al, da Ashtoret, da dukan taurarin sama, daga cikin Haikalin Ubangiji. Sai ya ƙone su a bayan Urushalima a saurar Kidron, sa'an nan ya kwashe tokarsu zuwa Betel"
Murmushi nai ina mamakin yadda wani zai iya kona taurarin nan na samaniya har ya kwashe tokarsu. Wani lokacin bana son zufafa bincike akan addini na amman ina ganin kamar akwai gyara a litattafin bible domin kuwa wasu kalaman ko nace surorin da suke ciki sai kaji kamar abun ba zai yiyu ba wani abun ma nakanji kamar labari ne irin na shaci fadi.
"Kina nan kina aikin kallon taurari ko?"
Maganar marry ce tasa na dawo da dubana izuwa gareta, kokarin zama take kusa da ni.
"Wata rana za ki zauna tare da mijinki ku kirga taurari"
Na kalleta
"Marry kina da ban dariya"
"Miyasa na ke baki dariya idan nai maganar miji? Baki taba daukar hakan da gaske ba"
Shiru nai kamin na ce mata.
"Ina ganin wani abun kamar ba zai faru ba, akwai wadanda suka girmemu a nan gidan kuma suna nan basu yi aure ba balle kuma ni da ke, balle ma ba zamu auri mutumen da zai ga girman mu saboda ba mu da iyaye"
"Wata kila ke din kina da iyaye Emily, ina ji a raina kamar muna da iyaye yawancin mu da muke gidan marayu muna rayuwa kawai a matsayin marayu, amman wasu iyayensu sun yi cikinsu ne sun jefar da su"
"Indai har haka iyayena suka min bana kaunar ganinsu, domin sune silar shigata wannan hali"
"Idan kuma iyayenki suna tsoron ki wahala ne suka kawo ki nan fa? Ko kuma wani ne ya sace ki ya kawo ki nan?"
"Zan iya yafe musu idan wani ne ya kawo ni nan, zan yafe musu amman talauci ba hujja bace komai talaucinsu kara su yi hakuri da ni a haka mu zauna a haka, tun da suka kasa hakurin zama da ni ba zan yafe musu ba"
Na fada idanuwa na cika da kwalla, sai ta saka hannunta ta lakamoni.
"Zaki yafe mata Emily, lokacin da mijinki zai risina a gabanki ya roka mata yafiyarki ba kisan lokacin da za ki yafe ba"
"Ba zan iya yafewa ba marry, i just can't"
Dariya tai jin yadda nai maganar ina son yin kuka. Mun dade zaune a gurin sannan muka tashi muka shiga block din mu ta nufi dakinta ni ma na nufi namu. Babu wuta a dakin amman an kunna hitila kamar yadda aka saba idan ba wutar, ban kula kowa ba dukuwa da irin wasan da abokina na dakin ke jana da ita, ganin bana cikin yanayin wasan yasa suka kyaleni na hau gado na kwanta wata kofar tunanin ta bude min.
'Suwaye iyayena? Yarbawa ne, igbo ne ko ibra ko hausawa? Ban sani ba, wane addini suke? Miyasa suka jefar da ni? Basa sona ko wani dalilin ne na dabam?'
Da wannan tunanin nai bachi kuma har gari ya waye ban samu amsar tambayoyina ba. Ban farka da wuri ba kasancewar ban yi bachi da wuri ba, shiga nai bandakin mu dake can kusa da kofar shigowa dakin nai fitsari ba tare da tsarki ba na wanke bakina kuma nai wanka sannan na fito. Mai kawai na shafa, ni ma ina da kyau kamar mutumen jiya duk kuwa da kasancewarsa namiji. Karamin wandon jean na saka wanda iyakar tsayinsa guiwa na saka wata t-shirt black na dauko kofina na jika gari na sha domin an san by this time an gama raba abincin safe kuma wanda be je ya karbo ba ba za a aje masa ba indai ba wani ne ya karbo masa ba. Bayan na gama sha na rufe waduruf din na saka wukata a aljihu tare da makullin lokar na dauki jacket dita na daura a kwankwaso na sannan na fito zuwa gurin gyaran mota wato gurin aikina. Nayi ta sauri a hanya ganin na yi latti ba kasafai nake son oga na rigana zuwa gurin ba, naje latti sai dai duk da haka oga Abdulshakur be fito ba wata kila wani abun ya tsayar da shi a gida ko wani gurin, rigar aikin na dauka na dora saman tufafina na soma gyara gurin sannan fito da kayan aikin a waje, na kusan awa biyu a gurin sannan ya iso. Cikin girmamawa na gaishe shi ya amsa min da far'a kamar kullum, sannan ya shiga aikin gyara motocin da ke gurin a lokacin ne mutane suka fara zuwa ciki kuwa har da yaran da muke aikin tare da su yan gareji. Ni nake tsaye kusa da shi ina aikin miko masa abubuwan bukata kamin ya bani list din abubuwan da zan je na siyo a kasuwar da ake siyar da jarafuna a unguwar Orile Iganmu a nan lagos. Zuwa nai dakin dake garejen na cire rigar aikin na dawo ya bani kudi na saka a aljihu sannan na kama hanya. Ba mu da nisa sosai da unguwar dan tafiyar bata wuce ta awa daya da rabi ba, so i decided naje a kafa na rike kudin babur din ko wani abu zan iya siya da su. Na tafiyar minti arba'in kamin na kama hanyar da ke kusa da kasuwar, hanyar kamar unguwarmu take babu mutane sosai duk kuwa da kasancewar da rana ne. Gungun wasu mutane na hango za su kai mutum hudu zuwa biyar a tsaye gefen titin, ban ji tsoron ganin mutanen masu kama da yan ta'adda ba domin na saba ganin irinsu da ma wadanda suk fisu a lagos. Ban lura da abunda suke da niyar aikatawa ba har sai da na isa kusa da su, mutumem jiya ne suke kokarin karbewa mashin suna masa barazana da katuwar wukar da ke hannunsa.
"Bamu makulli"
Dayan ya fada da yaren turanci ni kuma na katsa masa tsawa da yaren yarbancin ganin zagen fuskarsa da yana nuna cewar shi bayarabe ne.
"Ba zai bayar ba, ku kananen yan iskane da kuke yawo da wuka, kuma duk wanda ya kuskura ya taba shi ai cikinku sai nasa an kasheshi ba kune yan apapa ba?"
Duk tsayawa sukai cirkocirko suna kallona yadda nai musu barazanar yasa sun dan tsorota, ban san su ban san yan ina ba ne amman yawacin yan iskan lagos apapa suke, sun dauka a yadda nai musu kamar na sansu ne ko kuma ina da wani mai tsaya min ne.
"Wacece ke?"
Dayan ya tambaya da yaren yarbancin kamar yadda nai masa magana dazu.
"Idan kun taba ni zaku san ko wacece ni"
Na fada ina zaro wukar dake cikin aljihuna na nuna musu ina yatsine fuska kamar yar ta'addar gaske.
"Ku wuce daga nan"
Kamar umarnina suke jira suka kama hanya suka kyaleshi suna ta waigena. Sai da suka wuce sannan ya kalleshi na ce
"Kai sakarene zaka tsaya haka a kwace maka babur?"
"Kamar ke ce yarinyar da kika taimake ni jiya"
Ya fada cike da mamaki yana nuna ni.
"Yes kuma yau ma na taimakeka ba, dan ka zama dolo"
Murmushi yai.
"No ina tsorone amman kin san su ne?"
"Ai a lagos ba dole sai ka san kowa ba, as long as kasan sana'ar mutun barazana kawai zaka masa, idan har kace kyalewa zaka yi kowa zai cuce ka ne, shiyasa na ke yawo da wukata"
Na fada ina maida wukar aljihuna sannan na kama hanya tafiya kasuwa ta ba tare da na jira abunda zai ce min ba.
"Na gode Emily"
Ya fada sai na juyo na kalleshi ina murmushi.
"Baka manta sunana ba?"
"Taya zan manta sunan Jaruma"
Ya fada da dariya nima dariyar nai na cigaba da tafiyata.
_________________________
Want more? *Comment*
*Share*
*Follow* my channel https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01 [4/29, 6:17 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: 🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 1️⃣9️⃣