Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy - Chapter 15
Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 15: Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 15. "Ban yarda ba gaskiya yadda kike da kyaun nan…
4,445 words
"Ban yarda ba gaskiya yadda kike da kyaun nan haka ai sai maza sun yi ta kawo miki hari, ko da yake ance ku baku dauki wannan komai ba, ance dan miji ya yayi mu'alama da ku ba komai ba ni shiyasa sai an gwada mace ake aurenta"
"Ba kowa ba, wasu dai suke yin haka"
"Toh Allah yasa wannan rama taki dai ta yi yawa"
Ban fahimci inda ta dosa ba dan haka ban maida hankali akan zancenta ba, na gama surfen na dauka na wanke na kawo na aje na nufi dakina. Na shimda tabarma na dora zane na kwanta, nan da nan sai bachi yayi gaba da ni, can cikin bachin na ji ana tashina kanwarsa ce wai na tashi na yi sallah, na tashi ina jin kamar na yi kuka, domin sallah na daga cikin abubuwan da suke wahalar da ni a lokacin saboda rashin sabo haka dai nake daurewa na yi. Bayan ta fice na dauki buta na zagaya bandakin, kamar ance saurara ki ji sai na ji muryar mahaifiyarsa kasancewar bandakin yana like da dakinta ne ta gafe.
"Badan halin Hamza na son karya, shi gaba daya rayuwarsa ta karya ce ta son burge mutanen, ka tsallake garinku jiharku ka tsallaka har kudu kudun ma Lagos ka dauko mata, Allah kadai ya san dalilinta na biyosa, wannan ramar da take yanzu na fara tsorata da ita"
Na kai hannu ma dafe zuciyata idona ya cika da hawaye, can na ji wata kanwarsa mai da da zo ta karba mata.
"Yawanci fa yan kudun nan ance idan suna da hiv suke bin yan arewa saboda su lika musu, gashi nan a gari sai rade rade ake wai Ya Khaleefa ya dauko mai ciwo, wasu har da cewa wai ciki yayi mata aka korosu"
"Ai yaje dai ya dawo, aure zan saka ya kara yaushe zai zauna da zabiya kalli idonta ma kamar matsafiya, ance a can fa kowa da kalar tsafinsu na gado, kuma nan gaba idan suka haihu ai zata iya kwashe yaranta ta koma can"
Kasa fitsarin na yi na fito na dawo dakina na zauna na ci kuka na har na koshi. Sannan na fito na yi sallah, kalaman da na ji ya saka na ja jikina daga mutanen gidan domin idan wani abu ya faru za su iya cewa ni ce. A lokacin damuwa ta kara yi min yawa gashi tun da ya tafi be taba kiran waya yace a ba ni mu gaisa ba sai dai ya yi waya da mahaifiyarsa. A haka ya shafe shekara daya be waiwaye mu ba, sai dai yayi mana aike idan kuma ya aiko komai yana hannun mahaifiyarsa babu wani canji. Yanayin yadda ya turo kudi aka siya masa fili a kusa da gidan aka fara masa gina na fahimci ko wane kalar kasuwanci ko aiki yake can toh ya karbe shi, ina ta jindadin ina murna mijina zai gina gida mu koma a can mu tare, ashe ba ni yake yi ma ginin ba.
Ranar da na yi ma mahaifiyarsa maganar ina son ta rika ba ni kudin surfen da nake na rika siyen abinci ranar ta yi min tatas wai duk abun da take min bana gani, ba zata sake min komai ba daman hakkin ciyarwarta ba a hannunta yake ba, har tana fadar musuluntar kawai na yi amman zuciyar kafirarce a kirjina. Da mutanen gidan suka taso madadin su shiga tsakani su bawa mai gaskiya gaskiyarsa sai duk suka goya mata baya, wasu suka dauki gaba da ni ciki har da kanwarsa da nake shiri da ita. Tun daga ranar ba a sake bani abinci ba, sai dai idan na yi surfe dan abun da na samu sai na siya abinci da shi, bayan surfe sai na rika hadawa da wanki domin na samu kudin su min auki, wahala sai ta taru ta yi min yawa har wasu kujera suka fito min kamar na sauyin ruwa kamar na wahala. Idan na samu matsala kadan da mutanen garin sai min gori akan kudin surfe na ko wanki, ko aika ko kuma wani abun dabam, sai min gori, wasu su zage ni ni da iyayen da ban san a ina suke ba, wasu suce min zuciyar kafirar ce tana cikin kirjina, wasu suce min tsintacciyar mage.
Gashi idan ina son abu sai dai na fita na yi da kaina, babu mai bari na aiki danta, idan na fita mutanen su yi ta kallona. Ana sauran wata uku ya dawo wata rana ya kira waya sai aka kawo min na karba da murna ina kai masa gaisuwa sai ya rufe ni da fada. Wai an fada masa na yi fada da mahaifiyarsa na ci mata mutunci, kuma ina fita yawon gantali a cikin unguwa, shi ba zai dauki wannan ba.
"Ba zan iya daukar wannan rashin kunyar da rashin tarbiyar kafiran lagos ba, yadda kike tubababiya dole ki dauki halinmu da al'adarmu wannan kiristancin da bakin hali ki aje shi a gafe, ba ni da kamar mahaifiyarsa"
"Baka saurara ka ji bangarena ba, yadda kake da addini Khaleefa be kamata ka yanke hukunci ba tare da jin dayan bangaren ba"
"Bana son jin bangarenki marar kunya, rashin tarbiyace zaki nuna min ko? Da an yi magana kice baki da kowa sai ni baki da kowa amman baki kokarin rike mahaifiyata? An fada min kuma gaba kika da kowa a gidan, ki gyara halinki Wallahi kamin na dawo Aisha"
Ban iya cewa komai ba na fashe da kuka domin shi dai ba zai saurareni ba yan'uwansa kuma ba za su fada masa gaskiya ba. Madadin ya rarrashe ni sai ya kashe wayarsa na mikawa kanwarsa wayar ina kuka.
"Baki san dadin yan'uwan ba, saboda baki tashi da kowa ba, kuma baki samu zuciyar kwarai ba shiyasa kike son idan ya dawo ya bata da kowa saboda gaki yar gwal ko?"
Ban rama kalma daya daga maganarta ba domin a lokacin ban iya maida marta ni ba, kallonta kawai har ta fita. Haka na cigaba da rayuwa ta bakin ciki a gidan suka gade min kai bana jindadin zama da kowa, idan suna surfe su ta yi min haibaici tun bana fahimtar habaicin na su har abun ya fara damuna. Ina kofar dakina ina wanki mahaifiyarsa na madafa tana girka shimkafa da miya, sai gashi ya shigo dauke da kaya yayi burun burun gashi duk ya tarar masa kai yayi jiki sosai sai dai kuma yayi duhu a lokacin. Da gudu na je na rumgume shi ina murna, a take mahaifiyarsa ta daka min tsawa.
"Ke ba mu san wannan rashin kunyar da rashin tarbiyar ta mutanen Lagos ba karki bata mana tarbiyar gida"
Na sake shi ina murmushin karfin hali, domin idan na ce ban ji zafin maganarta ba na yi karya, ta taso ta sauri ta karbe kayan da ya zo da su ta kai dakinta kanwarsa ta kai masa ruwa yayi wanka, ya shiga dakin mahaifiyarsa ya canja kaya ya gaisa da mahaifinsa da yake kamar fanko a gidan, sannan ya shigo dakina ina ganin haka na tattara wankin na aje na bi bayansa wai ni mai miji. Abun da ban sani ba ashe shigarsa dakin ta shirya masa karya da gaskiyar abun da ban yi ba, sai ganin na yi yana ta hade min fuska.
"Sannu da zuwa tun da ka tafi ko waya babu Khaleefa"
"Tafiyata ai ta miki rana domin gashi nan kin samu sana'a kina yi, kin fallasani a gari kowa ya san bana iyar da ke"
"Ko kawa ba ni da a garin nan balle na fada sirrina, ban taba fadawa kowa baka ciyar da ni ba, ban taba ba khaleefa"
"wannan wanki da kike ai da shi da fadar duk daya ne"
"ina yi saboda na samu abun da zan ci"
"Matsalar auren yare kenan baku da tarbiya baku da rufin asiri ga rashin yarda da kaddara"
Na nuna kaina ina kallonsa zuciyata na raya min kamar na Khaleefa da na sani ba ne.
"Khaleefa ni kake fadawa wadannan maganganun? Ka chanja min ba, yanzu duk ka manta irin sadaukarwa da na yi? Ka yi tafiya shekara daya da wata uku amman daga dawowarka sai ka rufe ni da fada kana ta bani rashin gaskiya?"
"Okay mahaifiyata zan bawa rashin gaskiya ke kuma na baki gaskiya kenan? Da kika zancen sadaukarwa sadaukarwar me kika yi? Ai ni na sadaukarwa ni da na dauko ki na kawo ki cikin yan'uwana, na musulumtar da ke, ba dan haka ba ai da yanxu ko mutuwa kika yi wuta zaki tafi"
Kalleshi kawai na sauke kaina kasa kuka, daman idan ba kukan ba to me zan yi.
"Tun da kin zabi haka, ki ta zaman wankewa jama'ar ga tufafi, sai ki ciyar da kanki"
Ya fada, ashe kuma zai iya, sai gashi babu abun da ya sauya bayan dawowarsa, sai ya zama kamar yana kyamata saboda kurajen dake jikina na sauyin ruwa da kuma wahala, mu'amalar aure ma dan kawai ta zame masa kamar dole ne da ko kallona ba zai yi ba. Idan yana son abinci mai kyau zai fita waje ya siya ya ci ko ya siyo mahaifiyarsa ta girka masa... Wata rana na kebe kaina a daki ni kadai ina ta kuka, da nadamar da somin tabi ne a lokacin."
***. ***. ***
Emily ta mike tsaye hawaye shar a fuskarta ta nufi dayar kujerar dake office din ta zauna jiki ba kwari ta kalli Aliyu dake kallonta cike da tausayi marar misaltuwa ta ce.
"Akwai matukar zafi, da bacin rai a auren mutumen da baka so, akwai da ci a auren mutumen da aka cilasta masa aurenka, akwai tsananin bakinciki da nadama a auren mutumen da baya sonka, ba ka son shi...! Yawancin irin waɗannan aurarraki sakamakonsu nadama ne, da dana sani, wanda kan iya haddasa ciwon zuciya da kan iya silar ajali mai shi. Amman ina makomar auren da aka gina akan soyayya? Miye tukuicin kyakkyawar alaka da kaunar da aka gina aure da ita? Shin minene ribarta?' Soyayyah ruwan zuma! Haka na ke jin sunanta a bakinsu, haka na ke kallonta. Hakan yasa ni shiga dakinta. Da fari tai min marhabun tare da yi min shimfida mai laushi, sai da na mika duka karfina na kwanta a ciki sai ta shammace ni, ban sani ba ashe a saman k'aya da k'usoshi tawa soyayyar tai min shimfidar, tai min matashin kai a saman narkaken garwashin wuta, daga lokacin sai na soma kiranta da dayan sunanta, wato soyayya ruwan guba! Ruwan daya fi ko wane ruwa haɗari a duniya, ruwan da kan aika mai yinta a lahira nan take ta, ruwan da wanda ya dandana ta zai gwammace mutuwa da rayuwa...'
Na yi zaton idan na samu matsala da Khaleefa mutanen garin ko na gidan za su rike ni kamar dai yarsu ko yar uwa domin sun san ba ni da kowa, ban sani ba ashe ni shashasha ce, idan na samu matsala da Khaleefa har ta kai ga duka Wallahi babu mai raba mu sai mazan garin idan suna cikin gida, ta zama na yayi masa dadi sai ta kai ko numfashi na yi da karfi sai ya rufe ni da duka, idan na yi magana yace na kai karar duk inda zan iya, ko yace na fadawa duk wanda nake ganin zai zame min gata, wai takamarsa kawai a lokacin ba ni da kowa kuma ba ni da gurin zuwa.
Tun kamin ya dawo ake gina, zuwansa karasa kawai yayi, aka yi fanti aka saka wuta, sati daya da gyaran na ga ana ta hada hadar biki a gidan, ashe aure Khaleefa zai kara aure be fada min ba sai ranar da aka daura masa aure, ina zaune a dakina na ga an shigo da katifa sabuwa ya siyo min, na karba na yi godiya na shimfida zanen gado sai ya jefo min turmin atamfa guda daya, a nan na san hausawa suna da wata al'ada wai idan namiji zai kara aure yana yi ma matarsa ta gida kayan fadar kishiya. Na karbi atamfar na masa godiya sai yace.
"An daura aurena yau, wannan atamfar fadar kishiya ce, a kuma ga katifa nan na siyo miki a al'adar garin nan ko kuma mu arewa idan aka yi aure ana kawo yarinya da komai, ke kuma na ga ba wasu kayan kike da su ba, dan haka ki zauna a nan tare da su Inna, anjima za a kawo amarya a sabon gidan da na gina, bana son tashin hankali kun zauna lafiya, ki bita sau da kafa kin ga dai baki da kowa a garin nan ita kuma yar gari ce"
Ina daga zaune na daga kai na kalleshi.
"Ba zaki ce komai ba"
Bance masa komai ba bayan kallonsa da nake har ya gaji ya kada kai ya fice. A lokacin na sauko daga kan katifar na ji ba zan iya kwanciya akanta ba, na fara yi ma kaina wadansu tambayiyin da ba ni da amsarsu.
"To wai ni mi na yi ma iyayena suka jefar da ni? Miyasa na gujewa matar data rike ni kamar yarta? A wane dalili na tsallake shawararta da dokokinta? Na yi sadaukarwa ga wanda be san darajata ba, na bar ki na zabi iyalin da ba su san kimata ba"
Na kwanta a gurin ina wani irin kuka mai karfi ina jin kamar zuciyata zata fashe...
Don't forget to follow my channel https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
Kuma karku manta ku yi sharing [5/4, 6:26 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 2️⃣1️⃣
Ban san a addinin musulunci idan namiji yayi aure yana sati a gurin amaryarsa ba idan budurwa ce, idan kuma bazawara ce kwana uku, dan haka da aka kwana biyu ban ga mijina ya shigo dakina ba sai na sami wata makociyarmu da nake siyen kayan girki gurinta wato Malika ita ma dai yarinya ce sai dai ba kamar ni ba domin tana da yara har uku. Na fada mata cewar ina son ta rakani gurin mai gari saboda ina son na kai karar Khaleefa, ita kam bata yarda taje ba wai gudun kar ace ita take zuga ni nake abun da nake, amman ta kwatanta min gidan kuma ta dorani akan tsarin yadda zan yi magana da shi idan na tafi.
Ina fita gidanta ban zame ko'ina ba sai kofar gidan mai gari na aika a sallamo min shi sai iyalinsa suka ce na shigo ciki, na shiga na yi musu sallama suka amsa muka gaisa na gabatar musu da kaina sai dayar tace.
"Oh ke ce wadda aka ce an musuluntar ko?"
"Eh"
Na amsa ina maida kaina kasa, babu jimawa Mai garin ya fito muka gaisa na gabatar masa da korafina cewar Khaleefa ya aje ni a daki daya ita kuma matarsa ya kaita gidansa kuma ya siya mata abinci mai kyau ni kuma ya daina ba ni, gashi kuma kusan kwana biyu be shigo dakina ba, ko da ya shigo gaishe da iyayensa babu ruwansa da dakina, ga kuma duka da yake yawan yi min. A take Mai garin ya aika aka kirashi tare da iyayensa na zayya abun da na fada da farko, sai ya tambayi ba'asi, Khaleefa yace karya nake yana bani abinci kuma baya shigo bangarena ne saboda ai kwana bakwai ake idan aka aure budurwa, ban san mace na zuwa da abinci ba idan aka aureta sai ranar. Yace da abincinta ta zo da komai nata, kuma wai bana masa biyayya abu kadan zan fara cewa ba shi da adalci ina masa ihu da Allah ya isa. Iyayensa ma suka goya masa baya mai garin ya rufe ni da fada.
"Ke mu fa irin tarbiyar da kuke a can ta arna ba ita muke a nan ba, tun da har kin yi aure kuma kin musulunta ya kamata ki watsar da wannan dabi'ar"
Mahaifiyarsa tace
"Ai matsalar auren tun farko bata san musulunci ba ko kuma bata tashi a cikinsa kenan, su fa tarbiyar su da auratayyarsu dabam take, musulunci ma ai suna yi ne kawai a baki"
Mai gari ya fadi nasa iyayensa da shi kansa su fadi na su, na rasa ya zan yi sai kuka nake ina bashi hakuri. Da muka dawo gida sai ya fara dukana irin dukam da be taba min ba, dukan da zaka rantse dansa na kashi ko na aikata wani criminal abu, ina bashi hakuri yana duka wai abun nawa ya wuce ina fada a makota cewar yana bari na yunwa da sirrin gidansa ya kai har na dauki kararsa na kai gurin mai gari a nemi tozartashi.
Duka yayi min ba na wasa ba, yana dukan yana min gorin wai daga ya taimaka ya tsamoni daga wuta da yanzu idan na mutu wuta zan tafi. "Iyayenki ma suna can cikin azaba, saboda sun yi shirka da Allah, kuma Allah kadai ya san ta hanyar da aka same ki, shiyasa kike butulu, matar ma data rike ki yanzu ai gudowa kika yi kika barta, ni kuma na dauko ki na musuluntar da ke na aureki amman kina min butulci, idan ba ni ba wane namiji ne zai auri arniya ya kuma ba a kawo ta da komai ba, marar asali ma irinki"
A lokacin ne kalamansa suka fi yi min zafi da daci fiye da dukan da yayi min, na ji kamar ace ina da ikon da zan zare numfashi daga jikina na manta da kowa da komai. A daren na sha kuka washe gari na dora haka na kwashe kwana uku bana iya komai sai kuka. Abun da ban sani ba be sani ba shi ne, ashe lokacin da ya doke ni ina dauke da cikin dansa, shi be sani ba saboda ba nice a gabansa ba, ni kuma tunani da tashin hankali da nake ciki be bar ni na ankara ba, daukewar da al'ada ta yi min na tsawon wata hudu ban gane ba saboda hankalin ba nan yake ba, gashi kuma cikin fari ne ban san komai akan ciki ko haihuwa ba, domin a gidan marayun da muke zaune ban da karatu da sana'a ban maida hankali gurin koyon komai ba ko kuma sanin wani abu wai shi ciki da haihuwa.
Sai da ciki ya kai wata biyar sannan na gane cewar ina da ciki shi ma Malika ce ta fada min.
"Wata nawa ne Aisha"
"Ni ban sani ba, ni na dauka ko yunwar da nake fama da shi ne ya janyo cikina yayi girma"
Ta yi dariya.
"Kai Aisha kina da wauta, ga abu har ya fito yaushe rabon da ganin al'adarki?"
Na tsaya tunani ni kam bana ma iya tunawa. Ta bani shawarwarin yadda zan yi kuma ta fada min na tafi asibiti. Na dawo gida ina ta murna da dare da Khaleefa ya shigo na masa maganar sai yace min ai ya sani, shi mahaukaci ne da ba zai gane ba. Na yi mamaki ya gane amman be taba min maganar ba kuma be nuna min komai ba? Da na masa maganar zuwa asibiti sai yace shi ba shi da kudi yanzu na bari sai gaba idan ya samu kudi. Ma zan yi a lokacin idan ba hakuri ba, na san ba dan ba shi da kudin ba, domin yana cikin shirye shiryen bude shago a kusa da gida ne, idan kuwa ba shi da kudi ba zai bude ba, nice ba ya son kashewa kudin, sai na bawa zuciyata hakuri na saka masa ido, na jidadi samun ciki domin ya dauke min damuwa sosai ban sani ba ko dan saboda ina da son yara ne ko kuwa dai saboda ina kurciya ne, wata kila kuma saboda ina jin cewa zan samu iyali ne, ma'ana dai zan samu dan'uwa na jini daga gareni. Kusan sai ya dauke min rabin damuwa da tunanin da nake idan na ji motsinsa sai farinciki ya baibaiye ni.
Ina cikin wata na shida ne da ciki, na ji yan'uwansa suna shelar Amaryarsa Hindu tana da ciki, shi kansa na lura da farincikin da yake da cikin, amman a nawa shi da yan'uwansa ba su nuna min jindadinsu ba kamar wanda zata haihuwa ba da igiyar aure ba, ashe wai kallon suke wata rana zan iya komawa kafira saboda iyayena da asalina ba na musulunci ba ne tun farko, kuma zan iya komawa da rayana, kusan a lokacin zamana a gidan da kuma aurena kamar ya zamewa Khaleefa dole ne. Wallahi akwai zafi akwai ciwo, ka ga mijinka yana zumudin zuwan wasu yara amman ban da naka, bayan wankin da nake na siyarwa da ya dauke me sakamakon abincin da Mahaifiyarsa ta dawo tana ba ni a kullum babu wani abu da Khaleefa yake min, ko dan siya min wani abun kwadayi babu ruwansa.
Ashi ma kwadayi mace mai ciki guri yake samu, domin ba kasafai nake jinsa ba, idan ma naji sai dai na yi hakuri ko kuma na tafi makota gurin Malika na samu idan tana ta ba ni. Amaryarsa ita take girkinta a ranar girkinta ni kuma aka fashe da cewar ban iya girki ba sai idan mahaifiyarsa ta girka ta ba ni. Da cikina ya shiga wata na bakwai sai na fara rashin lafiya da amai domin ban yi laulayi a farkon cikin ba, da na masa maganar tafiya asibiti sai yace min na bari sai wani sati. Haka kuwa na hakura na zubawa sarautar Allah ido.
Wata ranar jumma'ah gidan babu kowa sun tafi bikin yan'uwa mazan musu wasu sun fita wasu kuma sun tafi masallaci, ina zaune cikin dakina bayan sallah la'asar daya daga cikin matan gidan da bana magana da ita saboda yadda suka hade min kai. Sai gata a dakina da sallamarta na amsa ina kallonta sai ya duka ta ce.
"Aisha, na zauna na yi nazari abun da ake miki a gidan nan an zalince ki, ki yi hakuri ki yafe min, ban gane ba sai da kika samu cikin nan, kalli yadda ake farinciki da cikin Hindu amman ke kamar kin kumsa cikin shege, kuma Hindu tana zuwa asibiti amman ke baki zuwa"
Ta kowance gefen zagenta ya ciro kudi yan dari biyu da naira dari ta miko min.
"Ungo wannan duku uku ne, ki shirya ki tafi asibiti a duba lafiyarki da abun da yake cikin ki"
Na saka hannu biyu na karba na mata godiya sai ta gargade ni akan kar na fada ma kowa, ta miko min takardar da number waya a rubuce.
"Kin ga number wayata, idan kina son magana da ni ki tafi wani guri ko makota sai ki kira ni ki tambaya, kin ga ba zai yiyu mu yi magana da juna idan Inna na nan ba, sai mijinki da ita kanta Inna da sauran jama'ar gida su ce na yi munafurci, amman idan kika fita makota kika ari waya sai ki kira mu yi magana ba san mun yi ba, amman ba karki bari a gane da ni kike waya"
"Toh na gode"
"ba komai Allah ya saukeki lafiya"
"Ameen"
Ta fita ni kuma na boye kudin, washe gari ban ma fada masa zan tafi asibiti ba saboda gudun kar ya hanani ko yace na bari sai lokaci kaza, domin ina jin rashin lafiya a lokacin, sai na shirya na fita ba tare da na fadawa kowa inda zan je ba, a tunaninsu na shiga makota ne. Kuma tabbas na shiga amman gidansu Malika na tambaye ta wace asibiti ce mai saukin kudi domin dubu uku ne da ni ina son na je, sai ta fada min na kama hanya na tari achaba na tafi, duk abubuwan da ake bukata na yi da na shiga ganin likita sai ta yi ta fada wai miyasa ban zo awo da wuri ba gani yarinya kuma haihuwar fari, ai yanzu an daina wannan dabi'ar ta kauye, sai na fada mata mijina ne be aminta ba yanzu ma ba da saninsa na zo ba. Ta auna ni bayan na fada mata abun da nake ji tace naje na yi hoto a yau din na kawo mata, na je na yi hoton wa inda aka fada min na biya 1200 a lokacin na dawo Allah yasa na same ta da ta duba sai ta fada min abun da ke ciki jirkice yake madadin kan yaro ya juyo ta gurin marata sai ya zama kafafuwansa ne a nan.
"Hakan yana da wata matsala ne?"
Na tambaya domin ban san kan abun ba.
"Sosai kuwa mace zata iya mutuwa ko ta kasa haihuwa sai an fasa ta, ko kuma ta samu matsala ko danta ya samu, za a iya rasata ko a rasa dan, gashi kuma baki da jini sosai ba ki da ruwan jiki da yawa baki cin abinci mai kyau"
A take hankalina ya tashi, zancen abinci mai kyau kam bata taso ba domin abinci ma bana iya ci na koshi balle wani mai kyau ko mai gina jiki.
"Za mu dora ki akan magani, kuma kije ki shirya ki dawo gobe, akwai abun da zamu fara miki da juyo da kan yaronki kamin ki cika wata tara, dan yanzu cikinki yana da wata bakwai da kwana sha takwas"
Na mata godiya na fito jikin a sanyaye domin na san babu wani kudi da zan samu a gurin Khaleefa, ashe ma abun da ban sani ba gidan yana nan ya kusa kamawa da wuta saboda na fita tun safe ban dawo ba har la'asar. Dan canjin da na rage min ne na hau achaba da shi na iso gida sai da na fara biyawa na fadawa Malika halin da nake ciki ina kuka sannan na shigo gidan.
"Idan uban wa kika fito?"
Ita ce madadin amsa sallamata da yayi kasancewar yana cikin dakin na yi sallama.
"Asibiti"
Na amsa jiki ba kwari murya na fita daker.
"Ina kika samu kudin zuwa asibiti? Da izinin wa kika fita"
"Idan na tambaya ba zaka bar ni ba, kudin kuma daman ina da shi"
"Karya kike sai dai idan satar min kika yi ko kuma kin fara bakin halinku na kafirai, wato yanzu ya kai ki fara fita baki fada min ba"
Na kalleshi cike da takaici da nadama da bakinciki na ce.
"Wai kai Hamza wane irin zuciya ce a kirjinka? A matsayinka na musulmi mai addini be kamata na same ka haka ba, dabi'unka da ka nuna min ba su na tarar ba, ka zalince ni kai da iyayenka kunci amanata"
Ban gama rufe baki ba ya rufe ni da duka.
"Me kika sani akan addini da zaki tsoma baki a ciki? Kafira diyar kafirai? Bubabbiya marar alkibila, rashin kunyarki ya kai ki kira da Hamza gatsatsa ko? Irinki ma son haihuwa ake da ke? Mugun iri irin kafirci wadanda basa tuban Allah da ma'aiki, na haihu da ke kije gaba ki maida yarana kafirai"