Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy - Chapter 17
Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 17: Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 17. Bata amsa tambayarsa ba ta kashe wayar ta fito ta…
4,408 words
*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
FOLLOW ME ON 👇🏻
FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914
TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Page 2️⃣3️⃣
Ta dauki wayarta da sauri ta kira Vito.
"Ban ga London ba ko'ina na duba baya nan, kuma na yi waya da Chidimma tace ta bar shi gurinka ta fita"
"Ina Lisa?"
Fatima yake nufi domin haka yake kiranta wani sa'in saboda ya tsani sunan hausawa da aka saka mata.
"Tana.... Fatima tana...."
Ta juya ta kalli agogon falonta lokacin dawowarta daga makaranta har ya gota.
"Ina kika je? Jiya ma kin fita ina kika je?"
Ta kashe wayar ba tare da ta ba shi amsa ba. Vito ya kalli wayar har ya aje sai kuma ya dauka ya kira Chidimma.
"Hello ranka ya dade"
Ta amsa da nishadi da girmamawa.
"London yana gurinki?"
"Aa ai tare na barku da shi da zan fita"
"Baki koma gidan ba? An duba ba a ganshi ba"
"Wata kila ko yaji muryar mahaifiyarsa ne ya boya, dan yanzu rashin kulawar da take ba shi ya saka baya son zama kusa da ita, madam bata kula da shi yadda ya kamata"
"Chidimma ki yi hankali da bakinki, ki daina fada min laifin Emily, idan ma wani abu take marar kyau ki bari na gani da kaina, karki sake fada min tana gida ko bata nan sai idan na tambaye ki, madadin na ga laifinta ke zan tsane ki ne"
Yana kaiwa nan ya kashe wayar ya dauki rigarsa dake aje kan gadon ya saka ya fito dakinsa sai ya samu mahaifiyarsa a falo tana hira da mai dafa masa abinci.
"Fita zaka yi"
"Eh"
Ya amsa a takaice sannan ya dauki daya daga cikin keys din da suke lake a kofar fita falon ya fice. Ta dayam bangaren kuma Emily na aje wayar ta nufi harabar gidan tana tambayar mai gadi ko Fatima ta dawo? Sai ya fada mata bata dawo ba amman direban dake daukota daga school ya fita da mota tun dazun.
"Amman ka ga London ya fita?"
"Aa be fita ba indai ba Oga ne ya fita da shi ba a mota a kafa kam be fita ba wani kuma be fita da shi ba"
"Ya bata ban ganshi ba"
"Kin duba ko'ina?"
"Eh"
Ta amsa masa sai ta nufi kofar gate din ta bude ta sauri ta fita tana ta kalle kalle bata yarda yana cikin gidan ba domin ta duba ko'ina bata ganshi ba, haka ta fi hanya ko talkami babu a kafarta tana tafiya tana kalle kalle idan ta ga mutane sai ta tambaya ko sun ga wani yaro, kowa yace mata a'a.
"Yaro ne sosai fari yana ihu idan ya ga mutane wani lokacin yana da jin tsoro kuma yana yin abu kamar marar hankali amman ba mahaukaci ba ne Autism ne, yana da matsalar data shafi kwakwalwa"
"Ba mu ganshi ba"
Gungun mashayan sun fada suna kallon cinyoyinta dake waje. Ta dora hannu akai har zata fasa kuka sai kuma ta karfafawa kanta guiwa ta kara gaba tana nemansa. Sai da ta kusa kai karshen unguwar tana duba kwararo ko lungu bata ganshi ba kuma kowa ta tambaya sai yace be ganshi ba. Can wata zuciyar ta raya mata ko ya bi direban da zai dauko Fatima makaranta gashi bata fito da waya ba balle ta kira, ta juya ta koma da sauri duk nisan hanyar bata gani ba cikin mintuna ta dawo gidan ta buga gate din da karfi mai gadin ya bude yana kallonta sai dai be ce komai ba ita ma bata bi ta kansa ba ta nufi cikin gidan da gudu sai ta samu kofar falon a bude Fatima na zaune rike da jakarta ta makaranta tana kallon mahaifiyarta a tsorace. Da sauri ta nufeta ta dafa ta.
"Fatima kin dawo? Da direba zai je daukarki a school tare da London aka je? Ya bata ban ganshi ba"
"Be bata ba, ruwa ya fada Vito ya zo nan ya tsamo London a swimming pool ya tafi ya kai shi asibiti"
Emily ta fadi zaune idonta na cika da hawaye wata sabuwar fargaba na tunkarota, tunaninta be bata zai tafi can ba even though ta leka bata ganshi ba amman bata saka ran zai fada ruwa ba. Ta saki Fatima ta nufi staircase ta haura sama zuwa dakinta ta dauko wani makullin motar domin wacan motar data fita da ita da safe tana can gurin aikin su Aliyu ta baro. Ta sauko da sauri tana jin numfashi na sama kamar zai dauke gudu take amman kamar ana daure mata kafafuwa haka take ji, rashin kuzarin nan da ya same ta a office din Aliyu a dazun bayan ta gama gutsura masa labarinta ya dawo mata a yanzu.
Gurin shiga motar ma sai da ta yi da gaske sannan ta iya bude motar ta shiga, cikin karfin hali ta yi ma Motar key ta yi reverse, a hanya ma tana jan motar motar na janta sai ta taka burki ta tafi sai kuma ta tsaya ko ta yi baya kamar wanda ta sha wani abu haka ta samu kanta duk wanda ya ganta sai yayi zaton ko ta sha wani abu ne, fakawa ta yi gefen hanya ta dora kanta a sitiyarin motar tana ta sauke ajiyar zuciya ta rufe ido tana maida numfashi, ta yi hakan ya fi a kirga sannan ta samu kuzari ya dan zo mata, ta sake tuka motar ta nufi asibitin da aka saba kai shi a duk lokacin da bashi da lafiya.
Ta faka motarta a emergency ta fito ta rufe motar, ta nufi entrance din Emergency din tana kokarin daga kafarta ta taka gurin gabanta ya fada ras ras ras dudududummmm har sau uku, kamar wadda ta tuna wani abu sai ta fasa bata dora kafar, ta ja baya ta tsaya tana kallon Kofar Emergency din dake can ciki wato second door da mutane suke fitowa, ta kasa shiga ta gagara komawa ta tsaya a gurin har na tsawon minti 5. Tana tsaye a gurin sai ga Vito ya fito tare da wani yana hangota sai ya tsaya da sauri kamar mai jin tsoro, sai kuma ya taka ya karasa inda take tsaye.
"Mu tafi gida"
"Dana ya mutu ko? London ya mutu?"
Vito ya dafata kamin ya sake cewa komai ta ce
"Na jiya a jikina, an sanar min saboda ni ma uwace, ban taba samu kaina a irin yanayin da na samu kaina a yau ba, ban taba jin abu makamancin wannan ba, saboda ban taba rasa makusanci na jini ba sai yau, na ji abun da ake ji, na ragu yau na koma daga ni sai Fatima"
Tana maganar wasu masu tsananin zafi suna sauko mata.
"I'm sorry, zan kasance a tare da ke a cikin kowane irin hali Emily"
Ta fasa wani irin ihu kamar mahaukaciya Vito ya rike kamin ta kai kasa, wani irin kuka take daya saka hankalin kowa dawowa gareta, bata san yadda ake ji idan an rasa wani ba sai a ranar domin bata taba rasa kowa ba sai yau. Shi ya saka ta mota ya tuko zuwa gida wanda suke tare kuma ya taho da gawar London, ta shiga falonta tana kuka Fatima ta tarbeta ita ma tana Kukan domin tun a dazun jikin yayi sanyi saboda yanayin yadda ta ga an ciro dan'uwanta a ruwan kamar tsumma.
"Ya mutu Momi"
Emily ta kasa magana ta rumgumeta tana ta kuka. Vito ya nemi guri ya zauna ya dafe kansa ya runfe ido, domin ba kadan yake son London ba, dama Fatima ce wata kila ba zai ji damuwa da bakinciki kamar haka ba, amman London yana son yaron yaron ma yana sonsa, shi ya canja masa suna Ibraheem zuwa London ya canja masa addinin kuma ya yarda, ba kamar Fatima ba dake nuna masa kiyaya da rashin kunya, kuma ta ki yarda da sunan Lisa da ya saka mata, haka kuma har gobe idan ibadar ta tsikareta sai ta yi sallah ko taje Islamiyar da mahaifiyarta ta sakata. Chidimma na shigowa falon ita ma ta fashe da kuka, kusan idan aka cire Vito London ya fi sabo da ita fiye da mahaifiyarsa musamman a yan kwanakin nan da baya yarda da Emily.
KAMEELA POV.
"Hhmmm sai yau kika tuna da ni?"
"Ke tunawa kike, ke da ba kira kike ba sai dai a kira ki?"
"Baki san na haihu ba halam?"
"Tohm yaushe?"
"Yau kwana takwas, amman abun da na haifa be zo da rai ba, ina gida"
"Allah sarki Allah ya bada rayayye"
"Ameen kina PH har yanzu"
"Eh mana kin san sai na yi shekara a nan ai"
"Okay Allah ya taimaka"
"Ameen, shi mijinki yana nan kenan?"
"Tasmia ina ruwanki da mijina da har zaki tambayi mijina bana fa son haka"
Tasmia ta kalkale da dariya
"Kameela kina bani mamaki, wai ke lafiya kike kar kishi ya haukata ki fa"
"Ke ya haukata ni din ina ruwanki? Toh miye na tambayar mijina"
"To ai na ga yadda kike da kishi ne na yi zaton ko ba zaki iya barinsa a can ba tare kuka zo wanka gidan"
"Mtssschesssss"
Ta yanke kiran. Tasmia ta kyalkyale da dariyar mugunta.
"Yau da kin san abun da mijinki yayi da sai kin kusa kashe kanki dan kishi, gashi nan daga tafiyarki ya tsallaka gurin wata da ba addinmu daya ba"
Ta sake fashewa da dariya.
"Ko da yake gayen ya hadu dole ki yi kishi ki yi taka tsantsan ai"
Ta fada tana murmushi kamin ta tashi daga kwancen da take ruf da ciki ta yango Food flask dinta mai two set da ya siya gurin Khadeeja Candy ta bude ta zubawa kanta tsemo da miyar agutsi. Ta sake daukar wayarta ta kira layin Emily sau biyu tana maka miss calls sai a uku aka daga.
"Hello..."
"Wacece wannan"
"Kawar tace"
Dip ta ji an kashe wayar ta duba wayar tana mamakin waya daga? Ta sake jira sai ta ji wayar kashe. Ta tabe baki ta aje wayar kusa da ita ta cigaba da cin abincinta.
ALIYU POV.
Ya kalli harabar gidan da iska mai dadi ke kadawa sannan ya amsa.
"Ina gida"
"Gida a ina?"
"Compound"
"Me kake yi a nan toh?"
Yayi murmushi.
"Wai ke me kika dauke ni ne? A harabar gida gidan dai ba aljannu ne za su tsallako su shigo nan ba ina zan ga mata?"
"Baka kallon mata amman ai akwai social media kuma wasu ma za su iya samun numberka su kiraka"
"Saboda ni kadai ne namiji a duniyar nan? Kameela wai wane irin kishi ne yake damunki? Ke har alkawarin da na yi miki ba ki yarda da ni ba"
Ta yi shiru.
"Na san kowa da yadda Allah ya halicce shi, amman ya kamata ace muna damuwa da wasu abubuwan ba wai kishi ba a koda yaushe, already kin aure ni, ina sonki kina sona kina da kishi wannan abu ne da na sani tun kamin na aure ki kuma na aureki na miki alkawari ba zan miki kishiya ba, toh miye kuma abun daga hankali da bin diddigina?"
" Mata shedanu ne wata zata iya sakawa ka karya alkawarin da ka yi min"
"Akwai abubuwan da ya kamata ace mun damu da su, wata ma kokarin ganin ta samu kwanciyar hankali take, wata bata da iyaye bata da yan'uwa bata da kowa, damuwarta na samun canjin rayuwa ne, bata ta kishi take ba, be kamata muna damuwa da wasu abubuwan Kameela"
"Damuwar wasu ba tamu bace, kowa ai da kalar kaddararsa, ni tawa kaddarar kishi ne da kaunarka yaushe zaka zo?"
"Sai idan zaki koma zan zo na tafi da ke"
"Saboda me? Yanzu baka yi marmari na ba?"
"na yi idan na zo mi zan yi? Aiki nake a nan fa Kin sani, zan zo amman dole sai na dauki hutu"
"Toh ka dauki hutu mana"
"Okay, zan dauka shikenan"
"Eh i love you"
"I love you more, ki kula min da kanki"
"I will sai da safe"
"Okay"
Ya aje wayar yana daga kansa ya kalli sama, labarin Emily halin da ta shiga kawai yake hangowa, ya kan ji labari kala kala na ban tausayi amman be taba jin kalar nata ba, be taba arba ido da ido da wata mata da ta sha wahalar rayuwa kamar ita ba. Duk kuma labarin da ta bashi na rabin wahalar da ta sha ne na rayuwar da Khaleepa, be san wane irin zama suka yi da abokinsa ba, be san ya ya riketa ba, da alama shi ma bata sha da dadi ba shiyasa har take guje masa kuma ta biyowa yarsa cewar tana da uba a raye.
Ya sauka daga bayan boot din motar da yake zaune yana mamakin yadda zuciyar wasu mazan take bushewa su saka rashin tausayi a ciki har su cutar da abokiyar zamansu, ba su yarda ana hisabi ba ne ko kuma dai gani suke kamar matan ba su da hakki su kadai ne suke da hakki akan matansu? Abun takaici ne kuma abun haushi ace Khaleefa ya juya mata baya ya san wacece ita kuma ya amince ya aureta. A yadda taba shi labarinsa mutum mai addini amman ya take saninsa ya rufe ido ya zalinci wanda bata da kowa sai shi. Bata da uwa ba uba sai shi ko da yake har a yanzu a cikin wahala take a ganinsa saboda Vito ya mata duka a gabansa ranar da yaje gidan, shi ma yayi mata hakan ne saboda ya san bata da kowa. Ya tabbatar da ace tana da iyaye a raye wannan kangi da wahalar rayuwar da cin zafin ba za a yi mata shi ba.
"Rashin iyaye masifa ne"
Yana maganar yana danna kiran mahaifinsa bayan sun gaisa ya nemi ya ba shi Ummi ita ma suka gaisa sannan yayi musu sallama ya kashe wayar. Ya gwada kiran number Emily har sau biyu ya ji ta a kashe sai ya ji duk ya damu ya san halin da take ciki domin ya aje ta gidanta a dazu a wani yanayi marar dadi, yanzu kuma ya ji wayarta a kashe, waya sani ko mutumen dake nuna mata fin karfi ya ga lokacin da aja aje ta a dazun ko kuma wani ya fada masa, waya sani ko ma ya mata duka akan haka saboda kowa ya maida ita baiwa saboda bata da gata. Gashi ya tuna mata da baya ya san yanzu damuwar zata mata yawa, a yanzu ya gamsu da hujjarta na son gina rayuwarta ita kadai da take ba tare da neman taimakon kowa ba.
"Idan kin ga wannan sakon ki kira ni, ina son na san halin da kike ciki"
Ya aika mata sakon yana jin zafin yadda suka cutar da ita har cutarwa ta yi nasarar sauya tunaninta akan musulunci da musulmai. Ya dan jima a tsaye a waje, labarin da ta ba shi kawai yake ta hararowa yadda ta yi zaman. Sai kuma ya ji ya kagu ya ji irin zaman da ta yi da Turhan yadda ta hadu da Vito kuma taya halittar jikinta ta canja zuwa siririya bayan Turhan ya fada masa tana da jiki sosai a labarin da ta bashi a yanzu kuma ta fada masa ta yi rama sosai a gidan Khaleefa saboda wahalar data sha. Ya bude motarsa ya zauna a ciki yana kai dubansa gurin agogon da ta aje masa dazun a office. Ya kai hannu ya dauko agogon yana ta juya shi a hannunsa.
"Kai wasu mazan akwai bakar zuciya"
Ya fada yana mamakin yadda wani zai aikata abun da shi ba zai iya kusantar makamancinsa ba me balle ya aikata.
"Waya sani shi ma ko yana can yana nemanta"
Ya ayyana da nufin Khaleefa a ransa kuma yana jin haushin Turhan tun gabanin ya san wane irin zama suka yi.
EMILY POV.
Ya aje wayar a hankali kusa da ita bayan ya kashe wayar gaba daya. Ya zauna kusa da Emily da bata iya daga ido saboda kukan da ta sha idon ya rufe mata sai ciwo yake.
"Za a maida shi mutuware su aje shi a can kamin ki samu salama a shirya bikin mutuwarsa"
"London Musulmi ne, musulmi na haife shi please ka bari a birne shi a makamartar Musulmi, ina jin kamar ban masa adalci ba idan na masa haka, ban bashi kulawa data dace ba, da ace na san zai mutu da na zauna da shi a kowane second da minute"
Vito ya rumgume ta.
"Ai kin bashi kulawa, shi ne yake kyamarki ba laifinki ba ne"
"Amman ai shi ba shi da lafiya ya kamata na masa uzuri"
"Baki da laifi a gurin kowa Emily, lokaci yayi da ya kamata ke ma ki so kanki ki dagawa kanki kafa ki yi ma kanki uzuri, kin bashi rayuwa mai kyau ki tuna shi ya rayu da uwa da yar'uwa hakan ma abun farinciki ne a gareki"
Ta daga kanta daga jikinsa ta kalleshi duk da kasancewar bata iya bude kwayar idon.
"Na gode Vito na gode daka taimaka min gurin bashi gata da rayuwa mai kyau, na gode da baka taba gajiyawa da shi ko maganinsa ba, baka taba kyamarsa ba"
Ya maida ita kirjinsa.
"Ba zan taba kyamar abun da ya fito daga jikinki ba"
Ya shafa bayanta a hankali alamar rarrashi.
_______________________
Slowly slowly🥺 VITO is my favorite 🤭
Team VITO iya wuya🫶 [5/10, 7:12 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL
*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
FOLLOW ME ON 👇🏻
FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914
TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1
INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0
CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08
Page 2️⃣4️⃣
"Har yanzu zuciyarki tana sha'awar musulunci ko Emily? Har yanzu baki dauki darasi daga azabar da muslmai suka koya miki ba? Da biyu kike zaune a cikin addinin kiristiyaniti ko?"
Ta dago ta kalleta inda take kyautata zaton fuskarsa take domin bata iya gani da kyau.
"A yanzu kake son mu yi wannan maganar?"
"idan har babu wata manufa a zuciyarki a wane dalili zaki ce a kai shi makabartar musulmai? Ina ruwanki da kasancewarsa a baya musulmi? Ai kin canja masa addini ko? Ubansa da yake a cikin addinin be damu ba sai ke da kika haura kika leka ciki?"
Ta rasa abun cewa, domin ta san ya fita gaskiya, Ubansa be damu ya san halin da take ciki ba balle abun da ta haifa gashi har London ya bar duniya be taba ganin ubansa ba.
"Ba ni da alaka da musulmi ta kusa ko ta nesa, ba zan iya tafiya makabarta na tambayi wani yadda za a binne London ba, ina son kin Emily ina son yaranki, amman hakan ba zai saka na kusanci addinin da ba ni da makiyi irinsa ba"
Ya mike tsaye ya dauki wayarta ya saka aljibu, ba tare da ta gani ba domin idonta a rufe suke.
"Ka bar min dana bana son ka masa biki"
Be juyo ba kuma be ce mata komai ba ya fice daga dakin, ko da ya sauko ya samu Chidimma zaune a falon har lokacin tana kuka sosai ita ma idonta ya kumbura domin mutuwar London ta zo mata a bazata. Wayar Emily ya ciro ya mika mata.
"Ki aje wannan a gurinki karki bata har sai idan na bukata"
"Okay Sir"
Ta fada cikin kuka sannan ta karbi wayar ta tashi ta fice daga falon zuwa bangaren da dakinta yake ta boye wayar sannan ta dawo ta shiga dakin da Fatima take. Cikin karfin hali Emily ta tashi tana lalabe har ta isa bandaki ta kunna fanfo ta jika kanta da jikinta ta dauki karamin tawul ta zuba ruwan zafi ta gasa idonta, sannan tana iya daga su ta kalli abu but still tana jin ciwo. Ta fito bandakin ta nufi wardrobe dinta ta sauko short gown ta saka ta nufi gurin da makullin motar yake ta ga baya gurin, sai ta tuna yana cikin aljihun gown din data cire motar kuma tana can asibiti, gashi dare ne yanzu idan ta fita ba lallai ta samu abun hawa in time ba, haka kuma ba lallai ne ta tafi inda take nufin tafiya ta samu mutane a gurin ba. A nan ta fara neman wayarta ita ta rasa ina ta aje wayar, ta dafe kanta ta busar da numfashi sannan ta bude gurin da Vito yake aje mata kudi ta dauka ta fito daga dakin ta sauka kasa.
Har ta nufi kofar fita sai kuma ta dawo ta sake haurawa sama zuwa dakin Fatima ta tura kofar a hankali ta leka sai ta hango Fatima kwance a jikin Chidimma, jan kofar ta yi ta rufe ta sauko ta fice daga gidan gaba daya. Ta yi tafiya mai nisa sannan ta samu abun hawa, ta kwatanta masa inda zai kaita wato gidan Tasmia, domin bata manta inda suka hadu ba har ta yi mata tayin shiga gidanta bata yarda ta shiga ba a wacan karon, da suka isa ta sauka ta bashi kudin da bata san nawa ba ne ta doshi gurin da kofar gidan mai kama da BQ yake ta kwankwasa, babu jimawa aka bude mata bayan Tasmia ta tambayi waye tace mata ita ce. Da maimaki take kallonta.
"Lafiya? Me ya same ki?"
"Zan iya shigowa?"
Emily ta furta muryarta na rawa. Tasmia ta matsa jikin kofar ta bata hanya kana ra leka waje ta ga ko tana tare da wani ne. Ta shiga ta zauna sai wani sabon kuka ya zo mata.
"Lafiya?"
Tasmia ta tambaya tana dafata cikin tashin hankali.
"I lost my Son"
"Subhanallahi yaushe? Me ya faru?"
Cikin kuka Emily ta fada mata yadda London ya mutu.
"Na fi son yaron nan fiye da komai na duniya, saboda lalurar da take tare da shi, ina matukar tausayinsa"
Tasmia ta kwantar da Emily jikinta tana hawaye.
"Ki yi hakuri Emily amman na tausaya miki"
Sai da ta yi kukanta ta koshi sannan ta fada mata dalilinta na zuwa gidan a cikin daren.
"Gaskiya ban san wani makabarta ta musulmai ba, ban san inda za a iya binne shi ba, kin ga ni ma bakuwa ce a garin, ban da gidan yar'uwa da kuma wata kawata ban san kowa a nan ba sai ke, ita kuma kawar tawa bata nan ma kuma ba zata yarda ba, yar'uwa ta ma bana saka ran haka, saboda ba jini daya muke ba, cousin dita ce, kuma kin ga a yanayinki nan ba kowa zai yarda danki musulmi ba ne"
"Ni ina jin kamar be dace a rufe shi a makabarta da ba ta musulmi ba, domin na san ni kaina ba a daidai nake ba"
"Toh yanzu ya zamu yi?"
Emily ta share hawayenta.
"Akwai wanda nake saka ran zai iya taimaka min amman yanzu ban san inda zan same shi ba, saboda dare ne ya bar gurin aikinsa kuma ban san gidansa ba"
"Wanene?"
"Mutumen da ya kawo ni dazun ogana ne a gurin aiki, kuma mun taba haduwa da shi tun da dadewa, yana da kirki da zuciya mai kyau wata kila zai iya taimaka min"
"Aliyu..?"
Emily ta kalleta
"kin san shi?"
"Ba wanda na tambayi me yayi miki ya min bakar magana ba?"
"Eh"
"Mijin kawata ne, na san gidansa amman da gaske ba wani abun yayi miki ba?"
"Be min komai ba, tuna rayuwarta ta baya ne da kuma mutuwar da London zai yi, ya taba ni yasa na zama yadda kika gan ni, kina da number wayarsa?"
"Aa ke baki da ita?"
"Ban san inda wayata taka ba, ina zan same shi yanzu"
"Muje na kai ki gidansa, daman kuma matarsa bata nan"
Sai da ta mike tsaye sai kuma ta fara tunanin inda za su samu abun hawa.
"Amman anya zamu samu abun hawa yanzu?"
"Ina motarki?"
"Ba motata bace ta yar'uwa tace nake karbowa ina zuba mai sai na yi yawo da ita, amman muje wata kila ba zamu rasa samun abun hawa ba"
A tare suka fito Tasmia na sanye da abaya da mayafi Emily kuma da tufafin jiki, sun yi tafiya mai nisa sannan suka samu texi suka shiga, Tasmia ce ta yi jagora har suka isa kofar gidan. Emily zata bawa mai motar kudi Tasmia ta hana ta biya kudin motar sannan suka fara kwankwasa gate din gida. Mai gadin ya bude yana musu kallon rashin sani.
"Mai gidan yana ciki?"
Tasmia ta tambaya da turanci be amsa mata ba sai ya tambayi lafiya.
"Ka fada masa Emily tana nan waje tana son magana da shi"
Ya juya ya koma ciki, babu jimawa ya dawo ya bude musu gate din suka shiga, Tamia ta wuce gaba domin ita ta taba zuwa gidan sai da suka isa gurin kofar shiga sannan ta koma baya ta bar Emily a gaba, Emily ta tura kofar falon ta shiga Aliyu na tsaye sanye da jallabiya yana raga volume din wa'azin da African Tv suka saka, sannan ya juyo ya kalli kofar yana amsa sallamar da Tasmia ta yi domin Emily bata yi sallama ba ta shiga. Be gama mamakin zuwansu gidan cikin dare nan ba, yayi arba da Fuskar Emily da idonta da suka kumbura. A take zuciyarsa ta raya masa mutumen nan ne yayi mata duka wata kila saboda ya kaita gida.
"Me ya same ki? Ko dukanki yayi?"
"Danta ne ya mutu"
Tasmia ta amsa masa sai yayi kalmar shahada ya zauna ya dafe kansa cike da tausayinta, yaron data gama bashi labarin wahalar da ta sha akansa shi ne kuma ya mutu a yanzu.
"Mun zo nan ne saboda tana son ayi masa jina'iza irin ta musulunci, ni ma kuma bakuwa ce a garin nan ban san kowa ba amman ita tace...."
Tasmia ta fada masa abun da yake tafe da su domin Emily bata komai sai hawaye. Aliyu ya sauke ajiyar zuciya.
"Yaron yana ina yanzu?"
Sai a nan Emily ta iya amsawa muryarta na rawa.
"Yana can dakinsa yana gida"
Aliyu ya dubeta duban da ya dauke shi tsawon dakika 120 yana kallonta.
"Emily"
Ta dago ta kalleshi ba tareda ta amsa ba, a zatonta zai ce mata ba zai samu damar aiwatar da kudirinta ba ne.
Chapter notes and social links
Bata amsa tambayarsa ba ta kashe wayar ta fito ta sake komawa dakin London din ta duba ko'ina har kasan gado bata ganshi ba, ta fito falo tana dubawa nan ma baya nan, ta fara duba lungu da sako na falon wai ko ya boya domin dabi'arsa boya a wani gurin musamman idan yana fushi, a nan ma bata ganshi ba. [5/8, 8:18 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL