Kenza eBookz

Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy - Chapter 34

Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy - Chapter 34

Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 34: Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 34. Kameela ta buge hannu. Ammy ta karasa ta dafa…

4,480 words

Kameela ta buge hannu. Ammy ta karasa ta dafa Fatima tana kuka ta kama fuska tana kallo, ta zube a gurin tana ta taba taba jikin Fatima

"Allah na gode maka, Allah Aisha kawai nake nema amman ka hado min har da yarta, jikata Allah na gode, Allah ya miki albarka Kameela"

Kameela dai bata ce komai ba ta juya ta fice da sauri.

"I want my momy"

Ammy ta dorata a cinyarta tana kuka ta rumgumeta. Turhan ya ka dagowa daga inda ya fadi durkushe ya kara karasa gurin da Fatima take jikinsa da zuciyarsa sai rawa suke abun ya zo masa kamar mafarki, ya rasa ta yi zai yi ya yarda wannan abun ba mafarki ba ne, shi dai Emily kawai yake nema shi ma kuma saboda Ammy. Da rarrafe ya karasa gurin tana kallon Fatima ya kai hannunsa zai taba ta sai ya kasa ya maida hannu, ya shafe hannunsa jikin rigarsa gaba da baya kamar mai kokarin cire kazanta ya sake mika hannunsa zai taba ba a nan ma ya kasa jikinsa sai rawa yake.

"Yarka ce Turhan, jinin ya fi ruwa kauri, jini be karya, yarka ce"

Ammy ta kama hannun Turhan ta kai a jikin Fatima, sai ya ji wani abu kamar shokin Fatima kuma ta zabura da karfi, a take ya tuna da abun da ya faru a airport lokacin da suka hadu da Aliyu ya taba babyn da yake dauke da ita tana bachi amman sai da ta zabura. Turhan ya fisge Fatima a jikin Ammy ya rumgumeta da karfi jikinsa ya mike tsaye yana kuka kamar wani karamin yaro, a take kukan Fatima ya yanke ta yi shiru kamar ba ita ba, ita m ta ji wani abu na dabam gashi ta ji yana kuka bata san dalilin ba, daga tsayen kukan ya kasa rike shi ya zube kasa yana rumgume da ita, kusan kowa a falon kuka yake har Nurse din da bata san hawa da sauka ba. Ammy ta daga hannunta tana magana.

"Haka na yi nufi, ku zauna tare ku yi zuri'a ta dalilina, Alhamdulillah ko a yau na mutu burina ya cika, na ga jininka Turhan, ashe ba a banza na ke jin bukatar ganin yarinyar nan ba, ashe akwai abun da Allah ya shirya min da ban sani ba Allah na gode"

Ta shafa kan Fatima ta shafa kan Turhan hawaye da murmushi, Turhan ya kwanta jikinta yana rumgume da yarsa Fatima. Wayar dake Hannun Fatima ta yi ringing Turhan ya dago da sauri ya karɓi wayar, Emily ya gani rubuce a wayar ya amsa kiran amman ya kasa cewa komai.

"Hello Fatima My Baby Girl where are you?"

Muryar da ya dade yana nema ta daki kunensa, amman ya kasa amsawa.

"Hello baby girl talk to me, ina kike?"

Muryar matar daya wulakanta ya nuna mata rashin gata da kiyayya ce take sake magana, ya rasa ta ina sauti zai fito daga bakinsa.

"If you hurt my baby Kameela, sai na kashe ki Wallahi sai na halaka ki"

Daker ya iya hada kalmomin bakinsa cikin wata iri siga ta kwantar da hankali da rarrashi da be taba sanin yana da ita ba ya furta.

"Your Baby is in safe hands....Aisha.... Emily...."

Daga nan be sake jin komai ba, aje wayar yayi ya kara rumgume Fatima a kirjinsa yana motsawa a hankali kamar wanda ke rike da sabon kwai.

"Momy ta fada min ba ni da mahaifi waye kai?"

Fatima ta tambaya tana ta sauke ajiyar zuciya na kukan da ta yi da karfi, Turhan ya girgiza kai ya rufe ido ya kasa cewa komai.

KAMEELA POV.

Ta kama hanyar komawa gida wata zuciyar na raya mata ta koma ta dauko yar mutane abun da ta aikata zai batawa Aliyu rai, wata zuciyar kuma na raya mata abun da ta aikata daidai ne domin idan ba haka ba Aliyu ba zai fita sabgar Emily ba, gashi abun har ya fara wuce gona da iri, ta san yadda Emily take da kyaun nan komai zai iya faruwa, idan ba haka ba bata ga dalilin Aliyu na boyewa Turhan lamarin ba. Ta isa ta faka motar waje ta fita ta shiga dakinta amman ta kasa natsuwa gabanta sai faduwa yake tana ta jin tsoro da tunanin abun da Aliyu zai fada mata, iyakar abun dai yayi fada yayi fushi, ko kuma yace ba zata koma yanzu ba, idan kuma ya wake ni fa? Ta raya ma kanta. No ba zai ma taba farawa ba da na saka masa guba ma be sani ba balle dan wannan.

Kiran wayar Aliyu na shigowa wayarta sai da ta zabura tana kallon wayar har ta gama ringing bata daga ba, ya sake kira baya daga ba har yayi mata kira uku, tasowa ta yi ta fito daga dakinta ta zauna falo tana ta sake sake ta san ko ta koma Turhan ba zai bata yarinyar nan ba, ko da ya bata ai aikin gama ya gama ta fada musu komai, ta saka wannan ta kwance ita kadai ita dai babban hujjarta ita ce Emily tana kokarin anshe mata miji alhalin ga mai nemanta har da ya a tsakaninsu. Tana jin tsayawar mota ta leka Window ta hango motar Aliyu sai ta nufi kofar falon da sauri ta bude kamin ta saka kafarta waje har ya iso bakin kofar falon cikin wani irin yanayi da bata taba ganinsa a ciki ba, kuma bata taba tsorota da bacin ransa kamar na yau ba. Baya baya ta yi hakan ya ba shi damar shigowa falon fuska kamar bakin hadari.

"Ina yarinyar da kika dauka take?"

"Tana gurin da ya kamata ta kasance, gurin mahaifinta"

Aliyu ya dauke ta mari da bayan hannunsa, sautin mari yayi mata chauuuuuuu har cikin kunen, ta dafe kuncinta ta zaro ido kamar za su fado.

"Saboda wata banza zaka mare ni a cikin gidan Ubana Aliyu?"

Ta daga hannu zata rama ya rike hannu ya jefar ya sake sauketa da mari sai da ta fadi. Mai aikinsu ta fito da sauri, kanwarta Farida ma ta fara saukowa da gudu. Aliyu ya nunata cikin tsananin fushi.

"Abun da kika aikata ba kishi ba ne, hauka ne da rashin tunani, kin dauki yarinya kin dankata a gurin mutumen da bata taba sanin waye shi a duniya ba, kin rusa abota da aminci da ke tsakanina da Turhan na shekaru da yawa, kin yi sanadin karya alkawarin da na daukarwa Emily, kin zubar da kimar da Ammy take kallona da ita, wace irin mace ce ke? Alkawarin da na miki be wadatar ba? Bibiyar wayata be gamsar da ke ba? Kokarin kashe ni be saka kin natsu ba? Toh babu abun da zai sauya halinki Kameela, na gaji ko diamond ce ke haihuwar gold na hakura dake Kameela, na dauki abun da zan iya dauka yanzu kam anyi na karshe... NA SAKE KI... Enough is enough"

Ya fada kai tsaye sannan ya juya ya fice daga falon ya koma motarsa, yaja ya fice daga gidan rai a bace, gidansa ya sake komawa domin a can ya baro Emily. Ya shiga cikin gidan ya faka ya fita motar ya shiga falon gidan, tsakiyar falon ya samu Emily duke dafe da kanta wayarta kuma a kasa.

"Emily..."

Be fadi abun da yayi nufi ba ta katse shi.

"I want my baby"

"Ta... Ta... Tana.... Gurin... Turhan..."

"I know ka kawo min yata, ba zan je can ba saboda bana son ganinsa bana son jinsa"

"Okay but i want you to know ba ni na shirya wannan ba?"

Ta mike tsaye ta daka masa tsawa.

"To waya shirya?"

"Calm down Emily ki kwantar da hankalinki"

Ta zaburo masa ta yi cikinsa da masifa idonta na cika da hawaye.

"How dare you told me that? Kana son kwanciyar hankalina ka taho min da ƴa? If you didn't plan all this taya ka san Turhan ya zo? Meya ka zo garin nan just for two days? Ka taho da Fatima ba tare da na sani ba ba, that's means ka san da wani abu Aliyu! Zuwa ba tare da ka sani ba ya rusa yadda ka tsara abubuwa shiyasa ka saka matarka ta dauke ta kamin mu zo ta kaita gurin Turhan right? Saboda ka san ina son yata dole na kai kaina a gurinsa ko? Ka min alkawari Turhan ba zai taba sanina ta hanyar ka sai idan ni na bukata, ina alkawarin yake? Ka ci amanata ba zan sake yarda da kai ba Aliyu, kallon da nake ashe ba haka kake ba, ka dawo min da yata Aliyu"

Wani irin ihu take kamar zata tashi gidan sai da Aliyu ya ji wani tsammmmm yayi baya ya runtse ido ya bude saboda tsawar dake saka masa, ya juya da sauri ya fita a rikice. Motarsa ya koma ya koma ya shiga ya dauki hanyar gidansu Ammy. Zuciya a karye jiki a sanyaye kunyar yadda zai yi ido hudu da abokinsa ya rufe shi amman a haka ya daure ya shiga gidan saboda Emily ya san idan be dawo mata da Fatima ba ba zata taba yarda da shi ba, kuma ya san gaskiya idan ba shi ya dawo da Fatima ba Turhan ba zai bata yarinyar nan ba. Be raina kansa ya kara girmama laifin da Kameela ta yi ba sai da ya isa bakin kofar falon Ammy for the first time ya ji kunya da nauyi tura kofar dakin ya shiga, yayi unkurin fasawa ya fi a kirga kamin ya samu kuzarin tura kofar ya shiga da sallama.

A tsaye ya riski Turhan yana maida hannayensa duka biyu a baya ya daure fuska yana kallon kofar falon da alama yana jiran shigowar Aliyu ne. Aliyu be taba gani abokinsa a cikin irin wannan yanayin ba sai yau. Aliyu ya gagara furta komai sai kallon Turhan yake babu kowa a falon sai shi kadai.

"Fatima ka zo nema ko ka zo ka shirya wata karya ne? Ka ba ni mamaki Aliyu, daman ance acikin abokai da yan'uwa akwai makiyan mutum a yau na yarda, me na maka? Miye manufarka na boye Emily? Matar da ka san nemanta nake ido rufa? Matar da saboda ita mahaifiya ta gagara fahimtata har take ciwo? Abun bakin ciki kuma da kai nake shawarar nemanta? Har a airport na hadu da kai amman ka gagara cewa yata ce? A tsawon lokacin nan a tsawon wahalar nan ka san inda Emily take ka boye min? Da kai muka zo nan kana jin kalaman Ammy akaina amman ka gagara furta cewar ka san inda Emily take? Miye manufar ka? Wallahi kallon mutunen kirki nake maka aboki da ya juye ya zama kamar dan'uwa amman a yau wannan duk ya kau... Ka zama koren maciji a cikin korayen ciyayi, mutum mai fuska biyu! But thanks to your wife daman haka abun yake ka ci amanar wani kai ma aci taka, ta bayyana komai a lokacin da ya dace"

Har lokacin Aliyu ya rasa abun cewa tambayar ina Fatima take ma ya gagara yi, Ammy ce ta fito dakin dake kasa a falon, Aliyu ya kalleta cike da kunya da nauyi, ya ambaci sunanta wai ko ita zata fahimce shi.

" Ammy..."

"Aa Aliyu ban da yau, da ka dauke ni uwa da baka aikata haka ba, na tabbatar da Ummi ce ba zaka aikata mata abun da ka aikata ba, ka ba ni mamaki shiyasa hausawa suka ce halin mutum dabam kalamansa dabam, bana son wani abun bacin rai dan Allah ka tafi"

Ya juya ya fice daga falon tsabar kunya da bakinciki yana jin kamar kasa ta bude ya shige ciki ta rufe da shi, yana tafiya yana jin kamar ba kafafuwansa ba, haka dai ya shiga mota ya sak juyawa ya fice gidan sai kuma ya rasa ina zai tafi, ya san be isa ya koma gidansa ba tare da Fatima ba to yace ma Emily me? Haka kuma be isa ya dawo ya ce Turhan ya ba shi Fatima, gaba daya sai ya rasa ina zai saka kansa, gefe hanya ya faka ya bude motarsa ya fito yana sauraren kiran sallah da ake ko zai samu sallama. Shi ma dai yau ya zama marar mafaka be da wani gurin fakewa sai gurin mahaifiyarsa, wayarsa ya ciro ya kira Ummi tana dagawa ya ce.

"Ummi ki min addu'a dan Allah"

"Lafiya Aliyu"

"Ba lafiya ba, kawai ki min addu'a ko zan samu mafita"

"Ka daga min hankali wace irin addu'a zan maka? Me yake faruwa?"

A takaice ya labarta mata abun da zai iya na haduwarsu da Emily zuwa abun da ya faru yau.

"Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un, abu be yi dadi ba Aliyu ka yi sakaci na shiga tsakanin mutane biyu, gashi Allah ya baka mata da bata dace da kai ba ta jefaka a kunya, sannu a hankali idan baka rabu da yarinyar nan ba, nan gaba kadan ma sai ta yi kokarin kashe ka"

"Already ta gwada Ummi ta saka min guba a abinci saboda Emily, amman ban ci ba sanadin haka na maida ita gida Mama Barakat ta ba ni shawarar maida ta na dawo ne wannan abun duk ya faru, but i divorced her today"

"Guba kuma..... Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un..."

Ummi na rufe baki ta ji Aliyu ya amsa yana fadin Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un da karfi sai maimaitawa yake wayar ta fadi yana nishi da karfi sai karar abu take ji kamar ana dukansa.

"Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un.... Aliyu.... Aliyu.... Lafiya? Kana ina?"

Baya ina magana sai karar take ji kamin ta soma jiyo hayaniyar mutane sai kuma kiran ya yanke.

"Sun kashe min ɗa sun kashe min ɗa, ko dai Turhan ko ita yarinyar ko Kameela sun kashe min ɗa, Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un..."

Ta fada da karfi tana fitowa dakinta da gudu har tana zubewa kasa ta tashi tana kuka.

TURHAN POV.

Bayan Aliyu ya wuce ya ji ba zai iya natsuwa ba ya haura sama ya dauko keys din mota ya sauko keys din a hannunsa.

"Ina zaka je?"

"Gidan shi zan tafi ba mamaki Aisha tana can, ina bukatar ganinta kuma ba zan sake bari ya keba da ita ba"

Ya fice da sauri ya shiga motar da ya dauko key dinta mai gadin gidan ya bude masa ya fice, Ammy fitarsa da mintuna kadan Ammy ta kasa natsuwa da hakan ta dauki wayarta ta kira direban ta ya shirya mota ta saka hijabinta ta bi bayansa. @360 Turhan ya isa kofar gidan Aliyu, yayi horn da karfi babu daga kafa mai gadin ya fito a tsorace ya leka motar.

"Me gidan baya nan"

"Bude min Malam"

Turhan ya fada da karfi mai gadin ya kuma ciki yana fadin

"Allah yasa lafiya wannan lamari dake faruwa"

Ya bude masa gate din Turhan ya shiga habarta gidan ko fakin din kirki be yi ba ya fita motar ya doshi kofar falon Aliyu ya tura kofar ya shiga Emily na zaune kan kujera ya duba ko'ina a gaggauce ya nufi sama ba dan be ganta ba sai dan tunaninsa da idonsa ba su zayyana masa matar da ya gani zaune a falon a matsayi Emily ba, sai da yayi rabin stairs din idanuwansa suka dawo masa da kamanin jan gashin da ya gani a gurin mace da ya tarar a falon sai ya tsaya cak ba tare da ya juyo ba, yana kokarin kamanta Emily da wannan matar da ya gani a yanzu. Ya juyo ya kalli Emily da ko kadan bata kalli inda yake ba, sun yi kama ta gashi da hasken fata har ma a fuska amman wannan ta fi Aisha da yake nema kyau da tsari sau miliyan ma, to amman idan ba Aisha bace to wacece? Ya sauko yana kallonta har ya karasa inda take zaune ya tsaya gabanta zuciyarsa kamar zata fado, tsabar kwarjinin da ta cika shi da shi. Sai a lokacin Emily ta mike tsaye ta kalleshi. Cikin tsakanin mamaki da kokarin tantance Emilyn din ce ko mai kama da ita ya furta sunanta a zuciyarsa.

"Aisha.... Emily..."

Be sani ba ashe tsabar mamakin be iya rike kanshi ba, daga kasa ya kafara kallonta turawa suka ce from toe to head yana kaiwa saitin fuskarta ya ji sauka abu mai sanyi a tsadaddiyar fuskarsa. Touf... Ta watsa masa yawu a fuska. Ya runtse ido da karfi ya jimke hannunsa da mugun karfin numfashinsa na fita da karfi, babban wulakanci a gurin balarabe shi ne ka jefe shi da talkami ko ka tofar masa da yawu. Sai dai a yanzu be isa ya nuna komai ba a hankali ya bude idon, ya sake kallon idanuwanta da be taba ganin tsarinsu da kyau ba sai a yau, tassaa ta wanke masa fuska da mari sannan ta kauce gaba gabansa ta nufi kofar fita falon kamin ta karasa Ammy ta shigo falon da saurinta jikin na rawa na son arba da Emilyn da take ta nema tsawon lokaci.

__________________

ABOKIN RAYUWA.... ✍️ [7/6, 9:18 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy

🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*

*© Khadeeja Candy*

Page 4️⃣7️⃣

Ammy ta nufo ta cike da rawa jiki Emily kuma bata fasa dosar kofar ba har sai da ta ita da Ammy suka yi kicibus a falon, Ammy ta kai hannu zata taba Emily sai Emily ta matsa baya.

"Yata Aisha muna ta nemanki ina kika shiga? Ke ce haka? Ina Ibraheem?"

"Aisha ta dade da mutuwa..."

Emily ta fada, Turhan ya juyo da sauri daman zuciyarsa bata gama gamsuwa cewar wannan din Aishar da yake nema ba ce domin ta canja gaba daya.

"Aisha ta mutu tun a ranar da kika yi son zuciya kika aurawa mugun danki ita, wannan Emily ce ina yata?"

Ammy ta kalli Turhan idonta na cika da hawaye sannan ta kalli Emily tace.

"Aisha ki yi hakuri.. Wallahi..."

"Ba maganarku na zo ji a nan ba, ina yata take?"

"Tana nan lafiya, Aisha dan Allah ki saurare ni mu yi magana, na san kina cikin bakinciki amman yadda zuciyarki take raya ba haka ba ne"

"Where is my baby? Bani da wata alaka da ku, and bana cikin bakinciki ni baki gan ni ba? Na wuce yadda kuke tunani, ina yata take?"

"Tana gidana dan Allah Aisha ki saurare ni mu yi magana, tsawon shekara shida kenan muma nemanki, ba ni da lafiya amman da na ga sanadin ganinki sai na ji na warke, daman ciwon har da ke ne"

Emily ta tabe baki.

"A tsawon shekarun nan Ammy kike tunanin zan sake yarda da shirinki ne? Kin yi amfani da kyautatawarki kika cutar da ni yanzu kuma kina tunanin amfani da ciwonki zai saka na yarda ke sake cutar da ni ne?"

"Wallahi ban yi dan na cutar da ke ba! Duk wani abu da Turhan yayi miki ban san zai miki ba, ban san haka zai faru ba, ki fahimce ni mana wannan duk ba halinki ba ne waye hore miki kunne haka?"

Ammy na maganar cikin kuka domin gaba daya Aisha ta canja mata tun daga shigarta har kalamanta da kamaninta sun sauya.

"Ni da na zauna da kazakin mutum kamar wacan har jira nake wani ya hore min kunne"

"Kina cikin fushi ne kawai har yanzu, da zaki yi hakuri ki bi ni gida zamu karshe duk wannan"

"Har abada ni da gidanki, ba ni ba wata alaka da ke"

Turhan ya karaso gurin yana jin ransa na baci saboda kalaman da take furtawa ga Ammy.

"Aisha da ni kike da matsala ba da Ammy ba, wannan...."

Be karasa ba ta dauke shi mari, Ammy ta rufe baki Turhan kuma ya runtse ido ya bude ya kalleta idonsa har suna canja kala.

"Har yanzu haukarka na baka zaka iya kiran sunana? How dare you? How dare you zaka tsaya a gabana har ka ambaci sunana? A tunaninka har yanzu wacan yarinyar ce da ka maida baiwa a bakar masarautarku? Ka fadawa kowa kurma ce? Ka hana ta magana? Hadiman matarka suke dokanta? Matar da aka sadakar a matsayin baiwa ga wasu mutanen? Ai Abun kunya ne aji kana nemanta, ko da yake mutane irinka ba su da kunya"

"Aish..."

Yana sake bude baki ta sake dauke shi da mari. Sannan ta kalli Ammy ta ce

"Ina yata take?"

"Tana nan lafiya ki yi hakuri ko dan ita ki saurara ni"

"Baki da wannan matsayin Ammy, kin rusa wacan kallon da nake miki, saboda kin nade bakin maciji a farin kyale kika damka min, saboda na yarda da ke kuma ya tsare ni, ban mutu ba sai dai wani abu da ya alakance ki da zuri'arki ya mutu tun a wacan ranar, baki da wannan kimar a ido na yanzu, saboda haka ina Yata take?"

"Aish..."

Turhan na bude baki zai furta sunanta Emily ta sake juyowa ta dauke shi da wani mahaukacin mari sai da ya nisa

"Ahhhh"

Ya cije hakora ji yake kamar ya rama amman ya kasa.

"Huhmmm Aliyu yana ba ni mamaki, indai Har zai iya boye min inda kike da kuma alakata Fatima to zai iya komai"

Yayi furucin da yakinin shirya mata komai aka yi aka hure mata kunne domin sanin da yayi ma Emily ba zata iya tsayawa tana fada masa magana haka ba, amman gashi har da mari, kuma ya san ba kowa zai yi haka ba sai Aliyu mutumen da ya dauka a matsayin aboki ashe makiyinsa ne be sani ba.

"Kana nemana saboda ka maida ni masarautarku na cigaba da bautawa matarka? Idan akana akwai wata alaka ta nesa ko ta kusa tsakaninka da Fatima to hauka kake yi"

Ta nufi kofa zata fice Ammy ta riko jacket din Dr A-B dake hannun Emily tana rokonta.

"Ina zaki je? Aisha dan Allah ki saurare ni ko dan shekaruna?"

Emily ta tsaya kamar abun arziki ta juyo.

"Danki ya kamata ki fadawa wannan, shi ya kamata ya fi kowa sanin daraja da kimarki ya kyautata miki ya riƙe amanarki, shi be yi ba sai ni da ban hada komai da ke ba?"

Ammy ta girgiza kai.

"Wannan ba Aisha da na sani ba ce"

"Wacan Aishar da kika sani ai ita kika aurawa mutumen da ya tsoratata tun gabanin a daura masa aure da ita, mutumen da ya gargadeta kar ta yarda ta aure shi, ita kuma a kokarinta na maida alheri da alheri ta danna komai ta aureshi, wacan Aisha itace Aishar da ya tofawa yawu a fuska a ranar da aka daura aurensu, ita ce ya kira ranar da aka dauranta da shi a matsayin bakar rana a gurinsa, ita ce macen da ya maida baiwa ya masarautarsu, take bautawa matarsa, ita ce ya gabatar a matsayin kurma a masarautarsu kuma ya cilasta mata amsa haka, wannan kuma Emily ce ta sha banban da wacan"

Ta fisge rigar ta fice abunta, Ammy ta kafe idonta akan danta cikin wani kalar yanayi na bakinciki da takaici, matsawa yayi kusa da ita kamar zai mata bayani amman ya kasa cewa komai sai motsa baki yake.

"Da gaske ne abun data fada?"

Yayi shiru kamar ba zai amsa ba.

"Duk abun da ya faru Ammy kuskure ne"

Tasssss Ammy ta wanke shi da mari, hawaye na sauko mata.

"Allah ya wandaranka, wace irin zuciya ce a kirjinka? Ba ni da Martaba da zaka mutunta ni ashe? Ashe karyar biyayya kake min? Bayan idona ka aikata abun da zai zubar da kimata? Ka rusa duk wani mafarkina da buri da nake da shi, ban taba tambayar wace kalar zamantakewa kuka yi ba amman raina be taba kawo min irin wannan kazamar rayuwar ba, kalli wuyanta ka gani sarkar cross ce a jiki, ka kalli shigarta ta tashi daga musulunci ta koma kafirci, Allah ya biyaka na gode"

Gaba daya jikin Turhan yayi sanyi duk neman Emily da yake saboda Ammy ne, ba dan yana jin be kyauta mata ba, amman a yau ya dan ji wani iri.

"Zan gyara komai Ammy na miki alkawari, ko dan yar dake tsakaninmu, kuma na faranta miki"

Ammy bata ce masa komai ba ta juya ta fice daga falon ta fita ta shiga motar da aka kawo ta, direban ya juya da ita, Turhan na tsaye a entrance yana kallon motar har suka fice sannan ya juya ya kalli kofar falon yana jin kamar ya bankawa gidan wuta domin a yanzu ba shi da babban makiyi kamar Aliyu.

"Ina zata je?"

Wata zuciyar ta tambaye shi, sai ya sauka entrance din ya bude mota da sauri ya shiga yayi reverse ya fice yana ta kalle kalle zuciyarsa na raya masa wata kila ta tafi ta samu Aliyu wani gurin ne gashi be san inda zai ganshi ko ita ba. Haka ya bi titi yana tafe yana kalle kalle har Napep idan ya gani lekawa yake duk yake dare ne ba lallai ya ganta ba shi dai ya rike kamanin gashinta da hasken fatarta, kamaninta na baya da a yanzu sun hade masa har yanzu ganin yake kamar ba Aisha da yake nema ba ce ya gani. A hankali yake tuka motar yana bin gefen hanya da kallo idan ya ga napep sai ya mika kai ya leka, idan ya ga mota ma sai kallo yana son tantance motar da Aliyu ya zo da ita gidan domin be rike kamanin motar da kyau ba, yayi tafiya mai nisa har yana shirin juyawa ya koma gidan Ammy saboda wata zuciyar na raya masa wata kila Aliyu ya koma gidan ko kuma ita Emily, sai ya hango mai kama da ita an sauke ta a napep ta shiga wani shago da aka kawata shi da haske, da sauri ya faka can gefe yana kallon shagon.

EMILY POV.

Tana fita gidan ta samu Napep ta hau ba tare da ta fada masa inda zai kaita ba, kawai ta fada masa su yi ta tafiya, tana zaune a Napep din tana jin kamar ta yi kuka amman ta danne zuciyarta da idonta daga zubar da hawaye, tana jin a yanzu jaruma ya kamata ta zama. Ta ina zata samu yarta shi ne abun da yake damunta a yanzu, ta dayan gefen kuma tana jin tsanar Aliyu a ranta domin shi ne silar faruwar komai, meyasa ma ta yarda da shi tun farko? Gashi yanzu saboda abun da ya aikata har Turhan ya samu damar tsayuwa a gabanta da Ammy su yi magana da ita.

"Huhmmm Aliyu yana bani mamaki, indai Har zai iya boye min inda kike da kuma alakata Fatima to zai iya komai"

Furucin Turhan na dazun ya fado mata a rai, sai kuma ta tuna yadda yake kokarin fahimtar da ita ba shi ya shirya wannan ba, it could be true amman idan ba shi bane miyasa har yanzu be dawo gareta da Fatima ba? Meyasa be kirata ba? Idan ba haka ba meyasa ya zo da Fatima? Wane irin uzuri ne da ba zai fada mata ba?

"Ina zan kaiki Hajiya?"

Mai Napep din ya tambaya ganin ana ta tafiya bata ce komai ba.

"Ka sauke ni gurin da zan samu mai Pos ba ni da cash"

Readers Also Read