Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy - Chapter 4
Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 4: Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 4. Red hair dinta ma ya faku da kyau ta yi kyau ta…
4,421 words
Red hair dinta ma ya faku da kyau ta yi kyau ta fito tsab, kana ganinta ka ga kyakkyawar mace mai aji, da matukar daukar hankali. Id card dinta na aikin ta fara dauka ta saka sannan ta dauki jacket ta saka saboda yanayin garin akwai sanyin sai dai ba sosai ba. File din jiya ta dauka tare da jakarta ta wayarta ta fice daga dakin, sai da ta shiga dakin Londom ta duba shi ta sunbance shi sannan ta fito ta leka dakin Fatima, sai ta same ta zaune da alama farkawarta daga bachi kenan. Da murmushi Emily ta karasa kusa da ita ta aje kayan dake hannunta ta shafa kanta.
"Good Morning Princess"
Fatima ta kalleta ba tare da tace komai ba.
"Okay jiya na san mun yi fada kamin ki kwanta kin kwanta da fushina I'm sorry"
Ta bata fuska.
"I just hate Vito Mom, ke kuma kullum kina shigar masa baki ganin laifinsa"
"Princess V be mana komai na ganin laifi ba, yana kula da ku yana kula da ni, gidan nan da duk abun da yake ciki nasa ne, be taba mana komai ba"
"I just hate him, bana son ki aure shi Momy"
Ta fada cikin kuka, Emily ta juyo ta fuskance da kyau damuwar ganin hawayen yarta na bayyana a fuskarta.
"Ba aurensa zan yi ba, ni na gama aure a rayuwata, amman baki da dalilin tsanarsa, shi yake kula da mu, shi kadai ne mutumen da ya rike ni ba tare da kyama ba, shi kadai ne ya kaunace ni a yadda nake yake kokarin kyautata min, shi ya maida ni yadda nake a yanzu"
"Ya fada min aurenki zai yi ko da bana so, yace min na fara kaunarsa tun a yanzu saboda shi zai zama step father dina"
"No no... Princess ba zan auri kowa ba, ba zan aure shi ba, ba zai zama stepfather dinki ba, but ya kamata ki girmamashi"
"No... To mu bar masa gidansa Momy"
Emily ta shafa fuskarta.
"Shi ne kudirina, amman ba zan iya haka ba sai na tsaya da kafafuwana, shiyasa na dage nake son fara aikin nan, zan rika saving kudi idan na tara zan koma wani gurin za mu bar masa gidansa da komai nasa, na miki wannan alkawari Fatima"
Fatima na jin haka sai ta rumgume ta da sauri tana murna.
"Promise Mom"
"I promise"
Ta fada yana shafa bayan yarta, Fatima ta dago daga jikinta ta rike fuskarta.
"Momy a ina kika samu aiki"
"Wani babban kamfani ne dake hakar ma'adanai da bincike akan albarkatun kasa, babba guri mai girma kuma mai hawa har biyar"
"Ke a hawa na nawa kike?"
"Na hudu, ina aikin da wata mace mai mumman hali, sunanta Amal kin san musulmai ba su da kirki ko? Ita ma bata da kirki ko kadan"
Fatima ta wara ido kamar ba ita ce ta gama fushi dazun ba.
"But I'm Muslim Mom you know"
Emily ta ja kumatunta.
"You're different because you were raised by a Christian mother"
Ta yi dariya ta sauka daga kan gadon, Emily ta bita da kallo tana jin kaunarta sosai, haka take son yaranta fiye da kanta, tana son farincikinki yaranta fiye da nata, bana son su rasa komai domin ta san yadda ake ji idan ka rasa wani abu, domin ta tashi ita kadai ba tare da yan'uwa ko iyaye ba.
Ta sani ta rasa farinciki, sai dai ta daukarwa kanta alkawarin ba zata yarda yaranta su rasa farinciki ko su shiga makamanciyar kazantacciyar rayuwar da ta shiga ba. Tana zaune gurin har Fatima ta fito daga bandaki ta shimfida karamin sallayarta ta dauki hijab, kallonta kawai take cike da burgewa tana jin dadi tana jin farinciki a duk lokacin da ta ga yarta tana ibadar da ta zabarwa kanta, bata son tauye mata hakki ko kadan hakan ya saka ta barinta ta aiwatar da addinin da ta dorata akanshi da farko kamin ta yi kokarin canja mata ra'ayi hakan kuma ya gagara saboda abun da shiga zuciyar Fatima sosai. Even though ba ko da yaushe take sallah ba, amman duk inda zata shiga ko a tambaye zata fadi cewar ita musulma ce, hakan kuma ya kan bawa duk wanda ya san mahaifiyarta mamaki, domin mutanen da suka san Emily a yanzu sun santa a Christian, kamar yadda sarkar Cross din dake wuyanta take nunawa a kullum.
"Okay Princess zan tafi aiki, na san yanzu Chidimma zata shigo ta shirya miki zaki tafi makaranta, i love you"
Ta fada sannan ta mike tsaye ta dauki kayanta ta fice daga dakin. Ta yi tafiya sosai kamin ta samu abun hawa kasancewar safiya ce ba kasafai ake samun ababen hawa a unguwar da safe irin lokacin da ta fita ba, gashi bana da ra'ayin amfani da motar da V ya siya mata tana son nesanta kanta da wasu abubuwan ne tun a yanzu.
Karfe bakwai daidai mai texi din ya shiga da ita cikin kamfanin, sai da ta sallame shi sannan ta fita tana kallon yadda a yanzu ake bude wasu bangaren ma, masu shara da mopping na yi. Tsirararun mutane ne kawai suke shigowa a kamfanin. Kai tsaye ta shiga ciki ta hau Elevator zuwa 4 floor din da take, a nan din ma ta samu masu mopping suna gyara floor din. Da Keys din hannuna ta yi amfani ta bude kofar Office dinta ta shiga sai ta shiga ga mamakinta sai ta samu an goge ko'ina. Da mamaki ta aje file da jakar hannunta ta fito ta tambaye wani namijin dake mopping a gurin.
"Dan Allah ka ga wanda ya shiga office din nan?"
"Gaskiya bayan ni babu wanda ya shiga"
"Kai ka gyara office din?"
"Eh ni na gyara ni nake gyara ko'ina ai"
"Kana da key din dakunan kenan?"
"Eh ni nake kula da ni ni aka hannatawa komai"
"Okay sannu da kokari"
Ta koma ciki, har ta zauna sai ta tuna da Office din Amal a take ta yi hanzarin tashi ta fito ta nufi office din ta bude sai ta juyo ta kalleshi.
"Me yasa baka gyara nan ba?"
"Tace ke zaki rika gyara mata"
"Okay..."
Ta furta with little bit of confused, why her? Bayan ya fada mata shi yake gyara ko'ina, ko da yake Amal din ta fada mata da kanta tun a ranar farko.
"Idan ka gama ka ara min mopper zan gyara gurin"
A madadin ya bata sai yayi mata jagoranci zuwa gurin da ake aje moppers din ta dauko daya da tsintsiya ta gyara office din tsab sannan ta mayar ta aje. Komawa ta yi office dinta ta zauna bata san me zata yi ba dan haka ta bude data ta ta shiga social media sai misalin tara ma'aikatan kamfanin suka fara shigowa. Misalin 9:15am telephone dinta ta yi ringing, a gurinta abu ne sabo a kirata da telephone in her own office, sai da ta yi murmushi sannan ta amsa kiran
"Hello"
"Ki same ni a office"
"Oka..."
Kamin ta karasa wayarta furta okay din Amal ta aje telphone din. Emily ta mike tsaye ta fice daga office din zuwa office din Boss dinta. Tsayawa ta yi tana knocking domin bata manta gargadin da tayi mata ba a jiya.
"Yes"
Ta mata izinin shiga bayan ta bata lokaci tsaye a gurin.
"Good Morning Maa"
"Na fada miki sunana Amal ki daina kirana Maa kamar wata tsohuwar"
"I'm sorry"
"Waya gyara dakin nan yau?"
"Ni na gyara"
"Good, sauraka kasa ki samo min snacks zan yi breakfast da ki siyo min bubble tea"
Ta jafa mata Atm dinta, tana duba wasu takardu.
"Ina file din da na baki jiya"
Emily ta kalli Atm din dake kasa, me yasa ba zata iya bata da hannunta ba ko ta dora a tebur ta dauka? Me yasa take son wulakantata? Ko da yake ba abun mamaki ba ne ita din ai musulmace, ta duka ta dauki Atm din tana amsa mata.
"Yana office dina"
"Idan kin ga dama ki kawo nan"
Kallonta kawai Emily ta yi ta juya ta fice daga office din, nata office ta koma ta dauko file din ta sake knock ta tsaya har sai da ta yi mata izinin shiga sannan ta shiga ta aje mata ta fito. A nan kuma ta fara tunanin ina zata samo mata snacks da bubble tea a yanzu, ita ba sanin kamfanin ko unguwar ta yi sosai ba.
Haka dai ta nufi elevator ta danna botton din dake jiki ta bude mata, ta shiga sannan ta taba number 1, a take ta fara yin kasa har ta isa first floor ta fita, wata zuciyar na fada mata ta tambaye mutane wata zuciyar kuma na hana ta, ita wa ta sani ma balle ta tambaya. Haka ta mike ta fita daga roof din kamfanin ta mike doguwar hanyar har ta isa gate. Ta kalli dama ta kalli hagu kaminnta yanke shawarar nufar left side tana tafiya tana dubawa ko zata samu mai siyar da wani abu amman bata samu ba sai da ta bar unguwar gaba daya ta shiga wata karamar unguwa dake kusa da su, sannan ta fara ganin masu siyar da abubuwa wasu ma yanzu suke fitowa domin goma ta dan gota. Abubuwan da ta fada su ta siya mota ta biya da Atm din sannan ta sake juyowa tana takowa a kafa, tun tana tafiyar tana jurewa har ta fara gajiya ranta ya fara baci, tana daf da isa kamfanin ta ji an yi mata magana da shigar da Vito ne kadai yake mata haka.
"My Beautiful Babe"
Ta kalli gefen da titi yake sai a lokacin ta lura da motar dake binta, yadda fuskarsa take hade kai kace ba shi ne yayi mata furucin mai dadin sauraro ba, dan murmushi ta yi ta tsaya har ta bude motar ya fito, tana mamakin ganinsa. Ko da yake ba abun mamaki ba ne domin ya san kamfanin take aiki kuma kamfanin ba boyayyen kamfani ba ne.
"Waya aike ki siyen abu?"
Ta kalli robobin dake hannunta da bubble tea.
"Uhmm..."
Ta yi shiru kamar mai tunanin abun da zata fada.
"Ba ki sha Bubble tea na sani, kuma na shirya miki breakfast kamin ki fito, so don't lie to me"
"My Boss"
Ya gyara tsayuwarsa yana jin ba dadi.
"Are you a maid hare? A aike ki ki siyo abinci shi ne aikin nan Babe?"
"No ita kadai ce ta aike ni, saboda a karkashinta nake aiki, kuma ta zo bata karya ba"
Ya kalli kayan dake hannunta da kyau sannan ya sake kallon fuskarta.
"Ba ki rasa komai a gida ba, ban san miyasa kika zabi wannan rayuwar ba"
A kokarinta na kawar da zancen ta ce.
"Me ya kawo ka nan?"
Ya sauke numfashi a hankali ya matsa kusa da ita sosai.
"Na zo ne na yi miki bankwana zan tafi Lagos yanzu, akwai kayana da aka rike dole sai na tafi za a sake su"
"Drugs...?"
Ta tambaya kai tsaye, be amsa mata ba sai kawai ya kai middle finger dinsa yana shafa soft kuncinta na dama up and down, idanuwanta cikin nasa ita tana jira amsar tambayarta shi kuma kaunarta kawai ke kara zafafa daga idonta zuwa nasa idon then straight to his heart. Dauke yatsansa yayi ganin tana kokarin kawar da fuskarta ya juyo ba tare da yace da ita komai ba ya bude bakar motarsa mai bakin gilashi ya shiga ya ja ya barta tsaye a gurinta yana kallon sawunsa. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta juya ta karasa cikin kamfani, a nan ma sai da ranta ya kara baci saboda tafiya ce mai tsayi daga gate din zuwa cikin kamfanin, haka dai ta daure saboda tana son aikin, daman hausawa sun ce daukarwa ya fi bauta ciwo.
ALIYU POV.
Yana daura necktie dinsa ta aje masa littafi a gaban madubin da yake shiryawa ta zauna gefen gado tana kallonsa. Kallon littafin yayi sannan ya kalleta
"List din yaudara za a fara min? So kike duk sai kin karar da abun da na tara kin maida ni talaka ko?"
Ta saka dariya tana kai apple din dake hannunta a baki.
"Aa Wallahi kasan jiya ka yi min alkawari, to ni dai ban gamsu ba so nake ka rubuta, domin a doka ya fi ka'ida"
Ya zauna kusa da ita yana murmushi mai sauti.
"Rantsuwa fa na yi miki jiya baki yarda ba?"
"Na yarda amman dai kara ayi a rubuce ko da ka manta na rika tuna maka, ni fa a rayuwata babu abun da na tsana irin kishiya, ni bana sonta ko kadan, ko wata macen ka kalla a tv bakinciki nake ji, kuma mata a yanzu sun yi yawa da kansu ma suke kawowa mazan mutane hari, idan na mutu dai sai ka yi aure amman idan ina raye ban yarda ka yi aure gaskiya"
Ya girgiza kai, ya dauki littafin yayi rubutu a kai.
"Ni Aliyu Mudallab na yi alkawari ba zan yi ma Matata Aisha kishiya ba, har abada zata zauna ita kadai a gidana sai yayanta"
Yana rubutawa yana fadar alkawarin har ya gama yayi saka hannu, ba tare da tunanin komai ba, domin har ga Allah ba shi da ra'ayin kara aure.
"Hakan yayi miki?"
Ta daga mishi kai tana murmushi sonsa na karuwa a ranta. Bakinta ya sumbanta kadan sannan ya mike tsaye
"Sarkin kishi, anya zaki bar ni a aljanna na more hurul'aini kuwa?"
"Wallahi ba zan bari ba"
Ta fada da karfinta, kyalkyalewa yayi da dariya sosai ya dauki abubuwansa ya fice tana masa addu'a tare da rakiya har kofar falo. Sai da yayi addu'ar fita daga gida sannan ya fice ya shiga motarsa yana dago mata hannu da blowing mata kiss sannan ya fice. Karatun Qur'ane ya kunna a motar kamar yadda ya saba, domin baya sauraren waka idan ma yana son rage kadaice ne sai dai ya saurari karatun ko ya karanta ko ya rera kirar da kansa.
Kamar kullum baya shigowa sai 11am ko fiye da hakan ma, idan yayi sakammako shi ne zai shigo 10am, kasancewar CEO na kamfanin, sai dai kuma baya barin kamfanin sai 3pm ko 4 sometimes har 5pm ya kan kai idan aiki yayi yawa, ko wani Meeting. Ya faka motarsa a gurin da aka tanadar masa sannan ya bude motar ya fito, iPod dinsa ya saka a kunne ya cigaba da sauraren karatun Qur'ane a kunnensa na hagu, ta ko'ina ya wuce gaishe shi ake har nufi elevator, matar dake cikin yake kallon irin kallon nan da ya kasa kyabta ido ma balle ya dauki, kallonta yake da kyau yana tantancewa, tunaninsa kuma yana tafiya wani gefen.
Yana shiga ciki sai ya taba 5, a take Emily ta taba 4 ba tare da ta kalleshi ba.
"Ni na fara zuwa"
Be ce mata komai ba bayan karkatowa da yayi ya kalleta ya kalli ID din dake kirjinsa, ita kuma sai ta yi zaton kirjin nata yake kallo, hakan ya saka ta kokarin gyara rigarta da maballi sama yake bude ya bayyana wani bangare na kirjinta sai dai be fito da dukiyar fulaninta ba. A kokarinta na yin hakan Bubble tea din dake hannunta ya fadi ya zube. Bakinciki ya saka bata san lokacin da ta fara yi masa ihu ba.
"Kallo har na bala'i har na masifa, ka kura min ido har na zubar da abun da na yi wahalar tafiya can wata unguwa nesa na siyo"
Nan din ma dai be jin magana ta zame masa dole dan haka ya adana kalamansa ya kalli gurin da ya bace kawai ya dauke kansa, his mind is somewhere else shi dai jin yake kamar ya taba ganinta, and he won't lie tana da masifar kyau, ta ko'ina ta kai mace, shiyasa William ya rikice jiya yana ta masa santinta. Suna isa four floor ta Elevator ya bude sai ta fita suna hada ido ta watsa masa masa wani kallo na jin haushi wanda ya fi kama da harara. Ya dauke idonsa da sauri ta har Elevator ya rufe, number 5 ya taba, ya ciro wayarsa ya kira Turhan.
"Hello Aleeyou"
Turhan ya fada da dan sautin labarancinsa kadan.
"Turhan, yarinyar nan da kake nema fara ce sosai?"
"Eh fara ce, tana da jan gashi, da blue eyes and tana kiba"
Kibar da Turhan ya fada ya saka Aliyu kwankwanto, domin ita dai wannan da ya hadu da ita daga jiya zuwa yau siririya ce.
"Tana da masifa?"
"No bata da fada ko kadan, tana da tsoro idan ma aka mata fada sai dai ta yi kuka ba zata iya maida magana ba"
"Okay, sunanta Aisha ko?"
"Eh bata da wani suna bayan wannan?"
"Ba zata rasa ba, amman na manta sai na bincika Ammy ko zata fada min"
"Ta yi dogon boko ne?"
"No bana jin ma ta gama Secondary School, ba wai na san komai ne akanta ba, amman dai zan bincika, me ya faru?"
Aliyu ya amsa masa yana ficewa daga Elevator.
"No na tambaya ne kawai saboda na taya ka nema"
"Na gode sosai Aleeyou, yau zan tafi Lagos din In Shaa Allahu, ka taya ni addu'ar Allah yasa na dace, ga matsalar masarautarmu, ga matsalar Matata ga matsalar neman yarinyar nan"
"Karka damu komai zai wuce, ita haihuwa ai lokaci ne, ita kuma za a same ta In Sha Allahu"
"Ina fatan haka"
"Okay bye Allah bada sa'a"
Ya sauke wayar yayinda yake tura office din farko ya shiga.
"Good Morning Sir"
"Morning Nick. Please inform Michael to notify our new staff members that buying food during working hours within the company premises is not allowed. They can only do so either before work begins or after closing hours, as it seems they are not familiar with our rules. Also, remind them to sign in when they arrive and sign out when they leave"
"Okay Sir"
Ya amsa yana dan sirinawa alamar girmamawa, sai da Aliyu ya shiga office dinsa sannan Nick ya zauna ya fara cika umarnin boss dinsa da System kamar yadda aka saba, duk wani abu da za'ayi a cikin kamfanin sai dai a tura ta email, sai idan uzuri ne ko kuma wani abu ne da ya shafi mutum personally sannan ake amfani da Telphone din da aka tanadar a kowane Office.
_______
Allah yasa Aliyu ya cika alkawarin da ya dauka, domin maza sai Allah.
Anya idan Vito ya san kudurin Emily na guje duk wani abu nasa zai barta kuwa?
Kuna ganin Emily zata iya jure aiki a karkashin Amal kuwa?
Shin Turhan zai yi nasara idan ya tafi Lagos neman Aisha? [4/20, 9:58 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: *🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
SARAC STARS. C - Pen... ✍️
Page 6️⃣
Sai da ta sauke numfashi sannan ta tura kofar office din ta shiga, ta manta da dokar Amal na neman izini kamin shiga. A gaban teburinta ta dora mata abun da ta siyo sannan taja ta tsaya tana jiran Amal ta gama wayar da ta shigo ta same tana yi. Sai da Amal ta gama wayar sannan ta kalleta a fusace.
"Wai ke kam baki da tunani ne ko kuma dai rainin wayo ne yayi miki yawa? Zuwanki na farko na miki gargadin shigo min office ba tare da neman izini ba amman baki ji ba ko? Ke ba yarinya ba balle ace za'ayi ta maimaita magana"
Emily ta kalleta da kyau tana jin babu dadi domin matar dake zaune a gabanta tana mata fada bata wuce sa'arta ba, amman take kokarin wulakantata saboda kawai tana aiki a karkashinta.
"I'm sorry na manta ne, zan kiyaye next time"
"Better"
Cewar Amal tana daga bubble tea din da ya zube.
"Shayewa kika yi?"
"No zubewa yayi by mistake"
"To zan fada a cire min a cikin albashinki, yanzu kuma je ki siyo min wani"
"Okay"
Emily ta amsa mata sannan ta juya ta fice jiki a sanyaye, cikin rashin jindadi da kasala ta sauka kasa ta sake komawa gurin dazun ta siyo mata wani bubble tea din ta dawo ta hauro sama ta yi knocking ta jira har sai da ta yi mata izini sannan ta tura ta shiga. Saman teburinta ta dora mata tare da atm dinta sannan ta juyo ba tare da tace mata komai ba zata fice sai Amal ta kirata.
"Hey"
Emily ta juyo ba tare da tace komai ba, Amal ta nuna mata tulun takardun da suke zube kasa a gafen teburin.
"Ki dauki wannan ki je ki yi typing dinsu, a yadda kika gansu a papers idan kin gama ki turo min ta email dina"
"Okay"
In short sannan ta nufi tulun takardun ta dauka ta fice daga office din zuwa nata Office din, Widows din office din ta bude tana kallon titi da kasan building din, hutun minti goma ta yi sannan ta juyo ta zauna a kujerarta ta bude system din ta fara typing tana murmushi kamar ba ita ce ta gama bacin rai a dazun ba. Sai dai abun da baka saba ba, yana da wuyar aiwatarwa musamman a karon farko, bata jima tana yi ba ta fara gajiya, haka dai ta daure ta cigaba da typing har azahar.
Bata bar office dinta ba sai 4pm domin bata yarda ta fito ba sai da ta tabbatar ta gama komai, ko da ta fito kusan wasu sun dade ta tafiya gida, few mutane ne suka rage irinta sai kuma ma'aikatan dake gyara kamfanin. Bata samu Taxi ba dan haka ta hau okada ya kaita gida, bayan ta biya shi ta kwankwasa gate din mai gadin ya bude mata ta shiga ciki cike da gajiya, jakarta kawai ta jefar ta shiga kitchen, lunch da Chidimma ta aje mata ta dauka ta fito falo ta fara ci da sauri saboda yunwa.
"Anya zan iya aikin nan? Haka aikin yake ko kuma dai..."
Sai kuma ta yi shiru ba tare da ta karasa ba ta cigaba da cin abinci, a gurin da ta ci abincin a gurin ta kwanta ta fara bachin wahala da gajiya bata farka ba sai Magariba.
"Momy..."
Ta bude idonta daker domin bachin be isheta ba, ta kalli yarta.
"Fatima"
"Momy yau kin kwanta da wuri"
Ta tashi zaune tana murmushi sai a lokacin ta tuna da yaran domin gajiya ta saka ta manta da su.
"Ina kuka tafi?"
Chimdimma ta tafi da mu park daga can muka je gidansu. Emily ta kalli Chidimma dake tsaye.
"Baki fada min ba"
"Yes saboda Oga ya zo bayan kin fita yace na rika fita da su, saboda baki da lokacinsu yanzu kar ya zama suna kadaici a gida, musamman Londom da yake ba lafiyayyen ba"
"Okay amman daga yanzu, karki sake fita da yarana ba tare da kin fada min ba"
"I'm sorry Maa"
Emily ta mike tsaye ta nufi gurin da danta yake tsaye kusa da Chidimma ta risina tana shafa fuskarsa.
"My Baby how is your day"
Ya mata murmushi kawai ya cire hannunta a fuskarshi. Chidimma ta saki hannunsa
"Sai da safe ranki ya dade"
Emily ta fahimci Chidimma fushi ta yi dan haka ba ta dakatar da ita daga tafiya ba.
"Ba zaki karanta mana story book ba?"
Fadima ta tambaya. Sai mahaifiyarta ta amsa mata.
"Zan karanta muku, ina da labari mai dadi da zan baku, and zan girka muku dinner mai dadi"
Tana maganar tana rawa da kai tana murmushi, a take farinciki ya cika fuskarsu, yadda ta fada haka ta aiwatar, tana girka musu abinci tana fada musu yadda ta sha wahalar aiki yau.
"Ma'aikatar ana aiki da yawa ne Momy?"
Fatima ta tambaya tana cin abinc.
"Ina tunanin haka, amman akwai wahala wata zan saba zuwa gaba"
Ta busar da iskar bakinta, tana shafa kanta.
"Momy can i ask you something?"
"Yes My Love"
"Me yasa ake sunana ya kasance Fadima Aisha Emily, not Fadima Hamza like London"
A take Emily ta ji wani kunci da bacin rai ya tunkarota da kamar fada ta ce.
"Again? Ina tunanin mun gama wannan maganar tuntuni?"
"Momy kowa yana using sunan babanshi, amman ni sai dai na yi using sunanki? Why? Even London ana kiransa London Hamza, why not London Aisha Emily?"
Emily ta aje spoon din dake hannunta ta mike tsaye.
"Time to bed"
"I need to know Mom kullum yan makarantarmu sai sun min dariya, Yau ma da nafi gidansu Chidimma an tambaye ni sunana na ce Fadima Aisha Emily sun min dariya"
"Ba na sha fada miki ba ki da Baba ba?"
"London me yasa yake da Baba, Me yasa ake ce masa London Hamza?"
"How many time do i have to told you Babansa ya mutu, ke kuma ban haife ki da ubana ba, haka nan na haife ki"
"But-"
"But, if you ask me one more Question zan doke ki da daren nan"
Ta fada mata a tsawace.
"But kin taba cewa Babana musulmi ne, amman ban taba jin sunansa ba"
Da sauri Emily ta bar dinning din domin ta san idan ta kara minti daya a gurin zata doki Fatima ne, gidan ya rikice mata domin tun a yanzu London ya fara rikicewa yana kuka. Dakinta ta shiga ta zauna bakin gado ta rike kanta tana shafa goshinta a hankali idonta a rufe sai numfashi take maidawa da karfi. Ta kwashe minti talatin a haka sannan ta mike tsaye ta cire rigar jikinta ta shiga bathroom ta yi wanka ta fito ta saka fajamas sannan ta sake dawowa falon ta nufi London da har lokacin kuka yake ta rumgume shi.
"Ya isa haka ya isa haka gani a nan"
Jikinsa yayi zafi sosai alamar fever, rage tsayi ta yi ta dago shi daga jikinta ta kalleshi.
"London saurareni, kukan ya isa haka kaga jikinka ya fara zafi, Fatima London yayi wasa da ruwa?"
Fatima ta juyar da kai ta rumgume hannayenta ta turo baki gaba tana cigaba da kallon tv ta ba tare da ta amsa mata ba, ita ala dole fushi take.
"Fatima I'm talking to you...!"
Emily ta daka mata tsawa har sai da London din ya zabura ya kara fashewa da kuka.
"Yayi wasa da ruwa"
Ta amsa mata a dikile sannan ta mike tsaye ta haura sama tana wani halba kafa kamar wata babba. Emily ta rumgume London tana jin kamar ta fashe da kuka, domin babu abun da yake firgitata a yanzu kamar rashin danta, He's not just an autisms yana fama da sickle tana yawan tashin masa lokaci zuwa lokaci, abu kadan yana iya saka ciwon nasa tashi, kusan ta fi wahalar da shi fiye da Autisms domin yana a cikin jikinsa ya zama rayuwarsa da hallintarsa ce a haka, wannan kuma a cikin jininsa take.