Kenza eBookz

Abraham complete by nooreemaan - Chapter 8

Abraham complete by nooreemaan - Chapter 8

Abraham complete by nooreemaan Chapter 8: Abraham complete by nooreemaan Chapter 8. Shiru madam Gloria tayi, ta zauna tana sauke hucin bacin rai, amma ba…

3,331 words

Shiru madam Gloria tayi, ta zauna tana sauke hucin bacin rai, amma ba halin magana, domin ta San Abraham kaifi daya ne, sannan ta yi Controlling kanta ne domin kada tsanar da take wa Aysha ya fito b'aro-b'aro, saboda har ita kanta Ayshar bata so ta San cewa ta tsane ta, ta kuma tsara hakan ne domin plan din ta ya tafi daidai yanda ta tsara...

Indo kuwa runtse idanunta tayi tana jiran sauk'ar mari, jin shiru ne yasa ta Bud'e idanunta cikin mamakin rashin marin da madam Gloria bata mata ba, cikin sheshek'ar kuka ta dauko Abin shara da Abin kwashewa ta shiga tattare fasashen plates din, cikin rashin sani ta taka wani fasashen plate...

Kara ta saki, inda a tare ita da Abraham suka runtse idanun su, wanda shi kanshi bai San yayi hakan ba.....

Saboda d'auriya irin na Aysha, ta kuwa Mike ta karasa tattara wajen ba tare da ta damu da cire broken plate dake tafin kafar ta ba.

Cikin k'ok'arin shanye zafin da take ji ta koma kitchen din ta dauko wasu plates din, wanna karon Sam bata yarda sun hada ido ba, duk da yanda take jin idanun sa na yawo a kanta, a nutse ta fara serving dinsu, amma tayi kokari matuka wurin controlling kanta domin sosai hannun ta ke rawa....

Bayan ta gama, ta jaa kafar ta zuwa sama tana zub da hawayen da bata San koma menene ba, domin indai fada da zagin madam Gloria ne ta fara sabawa, har hakan bai fiye damun ta ba...

Kan mad'aid'aicin bed dinta ta zauna tana sauke nishi, kafar ta daya ta d'ora kan dayan da niyyar cire k'walban, amma ta kasa saboda zafin daya ziyarci k'wak'walwarta....

Kwanciya tayi a gadon ta cigaba kuka, har wani wahalallen bacci da bata shirya zuwan sa ba ya dauke ta....

Ta bangaren Abraham kuwa, hakan nan yaji ransa ba dadi a dalilin abinda ya faru, duk da dadin dandanon da abincin ke dashi akan bai sa yaci da yawa ba, ruwan black tea yayi sipping kana ya goge bakinsa da tissue, sannan ya mike...

"wait! Son don't tell me you re full?" ta fada cikin rashin jin dadi da kulawa kamar gaske.

"yes mum! Am going out"

ya amsa a takaice kana ya haura sama cikin abinda bai fi 7seconds ba... da kallo mai tattare da zallan tsana hadi da muradin cika mugun nufin ta a kanshi ta bishi, kana ta dawo da kallon ta ga plate dinta mai shake da chips with fried eggs, a hankali tace "shege mai taurin rai, dama kayi accident a hanya ka mutu idan ka fita, kaga ka sauk'ak'e min aiki, na rasa me yasa har yanzu na kasa cika burina akan ka, tabbas nayi kuskuren barin Dan zaki ya girma" ta fada cikin yaren igbo hadi da cizon yatsan ta mai dauke da artificial nails...

*ABRAHAM* Har ya murda handle da niyyar shiga part dinsa, sai kuma ya tsaya cak! Sak'amak'on brain din sa daya tariyo masa lokacin da fasashen plate din nan ya caki kafar ta da karan da ta saki, Lumshe ido yayi a hankali ya furta "is it still in her leg? "(ko har yanzu yana tafin kafar ta).

Tamkar wanda ake ja, haka ya nufi hanyar dakin ta, a hankali ya tura kofar ciki...

Kwance ya hangota, jin bata motsa ba yasa shi fahimtar bacci take, wanda hakan ya bashi kwarin guiwan zuwa gareta duk da bugawar da kirjin sa ke yi...

Tafin kafar ta da yayi jaa ya kurawa ido, a hankali ya dire guiwar sa kasa, kasancewar rub da ciki tayi ya bashi daman ganin kafar da kyau, a hankali yasa karfaffan hannun sa mai laushi ya kamo kafar ta, sannan ya a hankali ya fara zare fasashen plate din... motsa kafar tayi wanda yasa shi dakatawa, hadi da fatan kad'a ta farka har ya gama...

Sai daya bari baccin ta ya kara nisa kana ya cigaba, inda yayi nasaran cirewa, ajiyar zuciya amma boyayye ya saki, kana ya cilla fasashen plate din cikin wani karamin dust bin dake dakin, da haka ya Mike ya bar dakin zuwa nasa, inda cikin mintuna arba'in ya shirya cikin wani Turkish suit ya bar gida zuwa ginin company dinsa daya kammala, inda a cikin satin nan za a yi bikin bude shi....

*AYSHA* Awa biyu ta d'auka cikin baccin da bata jin dadin sa ba Sam, kana ta farka...

mikewa tayi zaune tana marairaice fuska saboda zogin da ta ji daga kafar ta, a hankali ta kamo kafar, yayin da kwalla ta cika idanun ta, sai dai rashin ganin alamun fasashen plate din ya bata mamaki kwarai, a hankali ta kai hannu ta shafi daidai wajen ciwon, taji wayam babu alamun plate din a tafin kafar ta, sosai hakan ya tsaya a ranta domin iya tunanin ta bata cire da kanta ba, toh waye? ganin kanta ya fara tsarawa sak'amak'on tunanin da ta fara yasa ta mike tana Jan kafar ta har zuwa toilet....

*Bayan kwana biyar*

Zuwa yanzu Aysha taji sauki sosai a kafarta, domin tana yawan dannawa da ruwan zafi,, kuma tun daga lokacin da Abin nan ya faru bata sake ganin Abraham ba, wanda hakan yayi mata dadi, domin idan ta ganshi rasa nutsuwar ta take yi, ko gyaran dakinsa sai ta tabbatar baya nan take shiga ta gyara masa....

*madam Gloria*

Zaune take kan gadon ta, tana k'ark'ad'a kafa hadi da sakin murmushin zallan nasara, Bud'e tafin hannun ta tayi, inda wani karamin roba mai dauke da guba, wanda wanna gobar ke da hadari sosai, domin daga India tayi order din sa, inda ta hanyar sirri tayi har ya iso gareta, domin hadarin da gubar ke da shi, saboda idan aka yi kuskuren kamata tata ta kare, hakan yasa tayi taka tsantsan k'warai wurin ganin cewa ba a samu matsala ba har poison din ya iso gareta...

Duba agogo tayi ta ga karfe 5:30pm inda a yanzu ta San cewa Aysha ta gama dinner, ko tana daf da gamawa, mikewa tayi ta fito zuwa kitchen, inda maganin na tamk'e cikin tafin hannun ta....

Share fisabillah

Comment for more typing...

Thank you all for reading my novel 🍇Abraham 🍓

#Noor🦋

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 0806626851 [10/9, 8:36 PM] 💖NoorEemaan💖: 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇 ABRAHAM 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇

*First edition*

*WATTPAD* @NoorEemaan

https://facebook.com/groups/943534712916776/ Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

Chapter 27-28

Tamk'ar barauniya haka ta fito cikin sanda, jin shiru babu motsin kowa a falon ya sanya ta sakin ajiyar zuciya, kana ta ci mur ta nufi kitchen kai tsaye, nan ma shiru babu kowa, hakan yasa cikin sauri ta shiga bud'e poison din, amma ta kasa, dogon tsaki ta saki, saboda ba karamin dauri aka masa ba, karshe dai wuka tasa ta yanke saman robar da k'yar, atishawa ta jera sau biyar, saboda karfin gubar da ta shak'a, gumi ta share, kana ta mayar da kallonta ga tukunyar dake ta tashin k'amshi mai dadin gaske...

Leka waje tayi ta ga babu alamun tahowar kowa, hakan yasa ta bud'e tukunyar, inda porridge yam din ke ta tafasa, murmushi ta saki, domin hakan yayi mata daidai, juye robar guban gabadaya cikin tukunyar mai dauk'e da porridge yam din tayi, inda dama ta cewa Indo ayi wa Abraham shi kadai, dama ka'idar gidan ne mai girki bata d'and'ana abincin da za ta yi wa masu gidan, idan ma ka yi tasting a bakin aikin ka.

Babban spoon ta saka ta jujjuya, rufe tukunyar tayi ta fita da sauri, inda taje toilet din dakinta ta yi flushing robar hadi da wanke hannun ta da hand-wash sosai saboda karfin gubar, fadawa tayi flat kan gadon ta, yayinda katon cikin ta da kamar ana kara masa girma kullum yayi tsalle, dariya zallan mugun ta ta saki tace "you re dead already Abraham hhhhhhhhh"

★★★

Aysha da ta fito daga toilet kuwa, cikin sauri ta sauko tuno abinda ta dora kad'a ya kone...

Shigar ta kitchen ya haddasa mata wata fad'uwar gaba da har yasa ta dafe kirjin ta, "Ya Rahman" ta furta saman labb'anta masu taushi da kyalli.

Idanunta ne ya kai kan saman murfin robar guban da madam Gloria ta yanke, wanda ta manta bata dauka ba, a hankali ta tsugunna hadi da dauko shi, while kirjinta ke cigaba da bugu kallon robar tayi ta ga anyi rubutun, amma ko harafi daya bazata iya pronouncing ba, cilli tayi dashi cikin dan kwand'on shara dake kitchen din, ganin wuka cikin sink ya bata mamaki, domin ita dai ta wanke komai ta mayar muhallin sa, ganin spoon again gefen sink ya kara bata mamaki....

"waya shigo kicin (kitchen) din nan?" ta fada cikin karyewar zuciya..

Bude tukunyar girkin tayi, kana ta mayar ta rufe tana sauke numfashi, ganin kuma ya dahu ne yasa ta yi turning off gas hadi da dauko had'add'en warmer ta juye ciki...

Wanke komai tayi ta kara kyar kitchen din, dama ta gama girkawa madam Gloria abinda take so, fito da komai tayi kan dinning table, sannan ta koma dakin ta saboda lokacin magriba ya kusa...

*6:55pm*

Cikin sassarfa ya shigo cikin falon, idaunsa har lumshewa suke, ga wata azababben yunwa da yake ji, domin tun safe ruwan Black tea ne kawai a cikin sa, a matuk'ar gajiye yake sosai, sak'amak'on gajiyar daya kwaso, domin bai taba zirga-zirga irin na yau ba...

Cikin kulawa madam Gloria ta tare shi hadi da bashi side hug, "welcome back my son, my son has suffered today, Undu nwamu nkwo (Sannu yarona kaji) " ta karasa da yaren igbo.

Murmushi saman labb'a kwai yayi, yayin da idaunsa na kara lumshewa, kamar wanda aka tilasta wa yin magana yace "mum am badly hungry"

Wani irin sanyayyar dadi ne ya ratsa zuciyar madam Gloria, kansa ta shafa tace "toh son bari na kira Aysha tayi serving dinka"

A hankali ya bud'e idanunsa kana ya lashe labb'ansa da suka dan bushe kadan yace "lemme fresh up first"

"OK son, zan sa ta kawo maka dakin ka"

Ta fada tana bin bayan shi da wani mugun kallo hadi da murmushin samun nasara, sai daya bacewa ganin ta sannan ta saki wata katuwar dariya amma kasa² har da buga cinyar ta, duk da bai kai ga cin abincin ba, amma wani dadi ne ke ratsa ta, domin ta hango alamun NASARA a yau, domin abu ne mai wuya Abraham ya nemi Abinci a k'aran kansa...

*ABRAHAM*

Yana shiga dakin sa ya shiga toilet hadi da cika ruwan dumi a bathtub ya fada ciki, ya dauki tsahon mintuna goma a ciki, yayin da yake jin gajiyar na warware wa yana barin jikinsa a hankali...

Madam Gloria kuwa sawa ta yi lubabatu Kiran mata Aysha, inda babu bata lokaci suka sauka tare da ita, a yatsine ta kalli Aysha tace "ki dauki Abunshin (Abinci) yarona ki kai masa part din sa"

Cikin ladabi Aysha ta amsa da "toh" duk da fad'uwar gaban da take fama dashi, wanda sai kara tsananta yake...

Kitchen ta shiga, ta d'auko wani k'yak'yawan tray, dinning area ta d'awo ta saka warmer din cikin tray hadi da plate da spoon, sai roban ruwa, sama ta hau dashi, madam Gloria dake binta da kallo ta saki dariya kasa² cikin farinciki.

Knocking tayi har sau uku shiru, hakan yasa bakinta d'auke da sallama d'aya zame mata sabo ta tura kanta ciki, Lumshe ido tayi, domin kamar kullum dakin na wani irin kamshin na musamman, ware idanunta tayi, daram! Kirjinta ya buga da k'arfi sak'amak'on hango faffad'an bayansa da tayi, wanda babu riga, domin tsaye yake da towel a gaban dressing mirror yana shafa lotion, duk da yaji shigowar mutum, sannan kirjin sa ya buga domin ta, amma ko juyowa bai yi ba....

Aysha kuwa kamar Wacce aka dasa, kasa dago kanta tayi, tun kallon farkon da ta yi masa, domin sosai ya cika mata ido, controlling kanta tayi sak'amak'on hannun ta dake rawa, gashi ta kasa ajiye tray din, kamar yanda ko motsi k'wak'wara bata yi.

ABRAHAM kuwa hankali kwance ya shirya abinshi duk da tana dakin amma ko a jikin shi...

Cikin dagon wandon fari kal, hadi da black singlet ya shirya, roll on mai suna *Old spices* ya Murza a hammatan sa hadi da taje kansa sama² ya dawo bakin gado ya zauna tsahon mintuna biyar ba tare da yace komai ba....

A hankali ya sauke ganinsa kan ta, inda baya ganin fusk'ar ta sak'amak'on kanta dak'e tsunkuye, dan cizan labb'ansa yayi ba tare da kuma ya sake kallon ta ba, yace

"Am hungry, serve me!"

Rud'u ta shiga saboda jin amon husky voice dinsa, da kuma turancin sa da bata fahimci ko kalma daya daga ciki ba. Amma sai tunanin ta ya bata cewa abinci yake nufin ta tabatar masa...

Dan haka tamk'ar mai tausayin taka saman tiles din ta nufi inda yake zaune, a hankali ta dire tray din kan Wani tum-tum dake gabansa, plate ta dauka ta fara serving din shi...

Sirarran hannun ta dake ta faman rawa ya shiga rarraba idanun sa a kansu, yana mamakin meke haddasa mata wanna rawan jikin...

Aysha kuwa abubuwa da dama sun dame ta, na farko kusancin su dake haddasa mata shiga wani yanayi na loosing control, na biyu kuma haka kawai kallon Abinci ke sata fad'uwar wanda bata taba Jin hakan ba, hakan nan bata yarda da abincin ba, duk da kyau, hadi da haduwar abincin...

Bayan ta zuba masa ta ajiye gabansa, gefe tayi ta shiga murza hannun ta, domin ta kasa barin dakin, a hankali ta Lumshe idanunta hawaye suka gangaro kuncin ta, hak'ik'a abinda take ji a zuciyar ta ba karami bane a yau, saboda bata taba faduwar gaba irin wanna ranar ba.

Share hawayen ta tayi, ta Bude idanunta inda ta sauke su kan doyar daya raba biyu da spoon, maimakon taga cikin doyar fari sai ta ganshi yellow shaar, ga wani kyalli da cikin doyar keyi kamar maiko-maiko...

kanta ne ya kara d'aurewa domin lok'acin da take fere doyar fari kal sosai yake, ba wanna ba, iya Sanin ta dai ko an dafa doya cikin shi baya wanna yellow'n ko da faten sa ne kuwa...

Take k'wak'walwarta ta kara hasko mata yanda ta ga kitchen dazu, so take ta furta wani Abu amma ta kasa ganin ya kai lomar farko bakinsa...

Wanda ya kara hadd'asa mata wata faduwar gaba mai tsanani, ganin yana kokarin kai loma ta biyu bakinsa yasa da gudu ta nufe shi, ta ture hannun shi, inda Abincin ya zube har kan farin wandonsa...

AYSHA duk da tsananin tsoron da take ji a dalilin abinda ta yi masa, amma bata da zabi, sannan bata damu da hukuncin da zai biyo baya ba matuk'ar ta samu ta hanasa cigaba da cin Abincin...

"ka... ka... ka... yi hakuri dan Allah da Annabi, wallahi hankalina bai kwanta da Abincin nan ba, duk da ni na dafa, kayi hakuri yanzu zan je in dafa maka wani Abu mai sauri kaji" ta karasa cikin yanayi na rud'ewa da zubar hawaye masu zafi...

*ABRAHAM*

Zuba mata ido yayi, yana kallon kananan labb'anta masu moving very fast, ba dan ya fahimci ko kalma daya daga maganganun ta ba, illa yana mamakin dalilin barar da lomar Abincin da yake kokarin kai bakinsa... Me hakan yake nufi?

Aysha kuwa cikin sassarfa ta nufi hanyar fita daga dakin, har ta dora hannun ta a handle ta ji ihun sa... "Arrrrrrrh!!!"

A razane ta juyo, inda ta gan shi har ya sauko kasa kan guiwar sa hannun sa biyu dafe da cikin sa, yayin da ya zuba mata idanun sa da suka yi wani irin jaa tashi daya hadi da tara ruwan hawaye cikin su...

(Not edited) 🤒

What's your opinion on this episode reader's???

Share✅ Comment✅

NoorEemaan🦋 07082281566

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 0806626851 [10/10, 10:54 AM] 💖NoorEemaan💖: 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇 ABRAHAM 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇

*First edition*

*WATTPAD* @NoorEemaan

https://facebook.com/groups/943534712916776/ Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

_kuyi hakuri Na san page din yayi kad'an sosai am sorry, dan nayi alkawari ne shiyasa na cika, at least da babu gwara ba dadi , ba haka na so ba wlh, amma banda zabi daya huce haka, domin babu lokaci, kuyi manage da wanna in sha Allah ranar lahadi zan Baku update, karku yi korafi please_🤒

Chapter 29-30

(Not Edited)

Sandarewa tayi a tsaye sak'amak'on abinda take gani, "mike shirin faruwa ne yau ya Allah " ta aiyana a ranta yayinda hawaye wani na bin wani a fuskar ta, jin ya kara sakin wani karan hadi da sulalewa kasa dafe da cikinsa da yake jin wasu azaba a cikin su.

Cikin firgicewa hadi da tsantsar tsoro daya bayyana a fuskar ta karara ta nufi wajen shi da gudu, cikin rud'ewa ta tallafi kansa da ke kansa tiles ta rike a tafin hannun ta, fashewa tayi da kuka tace "Dan Allah yallabai ka tashi, ka rufa min asiri, ni Dama ban yarda da wanna abincin ba, duk da ni na dafa, dan Allah ka tashi wayyo Inna ta!!!" ta karasa cikin amon sauti mai matuk'ar taɓa zuciya, Abraham kuwa wata mahaukaciyar yamutsa cikin sa ke yi, yayinda yake jin kamar ana saka wuka mai kaifi Ana dasa ko wani jijiya dake cikinsa, kasan maransa kuwa ji yake kamar ana diga masa narkakiyyar ruwan dalma a kai...

Still idanunsa na kan Aysha da yake bin ta da wani irin kallo dashi kan shi bai San ma'anar sa ba, ruwan hawaye ne suka taro a cikin kwarmin idanunsa, amma basu zubo ba, duk da sanyin air conditioner dake dakin, hakan bai hana jikinsa hadi da singlet din jikin sa sun jike da gumi daya karyo masa all of a sudden ba, saboda tashin hankali mara misaltuwa da yake ciki.

AYSHA

Kuka sosai take tana jijjiga kansa, fadi take ya rufe mata asiri ya tashi, ganin abin kara gaba yake yasa ta ajiye kansa a hankali ta fice da gudu zuwa downstairs....

Madam Gloria da ta yi pretending cewa tana kallo TV , amma azahiri Sam ba haka ne, ta kasa kunne ne taji kyakyawar labarin cewa Abraham is no more...

Jin takun sauk'owar Aysha yasa ta dago kanta da sauri, yayinda ta saki boyayyen murmushi, domin tsantsar tashin hankalin data hango a fusk'ar Aysha wanda ko tantama bata yi, alamun samun nasarar ta ne.

Gabanta Aysha ta zube, cikin shesheka take nuni da hanyar step din, kana ta fisgo maganar daya makale a makoshin ta... "zai mutu, ki taimaka min ki zo, yana kwance cikin mayuwancin hali"

"ke nutsu ki fadamin, me yana faruwa, waye zai mutu, me kika yi wa yarona, ki sani duk abinda ya samu yaron na bazan bar ki ba" madam Gloria ta fada hankali a tashe, kamar gaske.

Cak kukan Indo ya tsaya sak'amak'on jin abinda madam Gloria tace, wani sabon kukan ta kara sawa, kana cikin raunataciyyar murya tace "wallahi Allah na rantse ban yi masa komai ba"

Madam Gloria bata kara cewa komai ta nufi hanyar step da gudu, burinta ta kawai ta isa dakin, ba Wai dan ta damu da halin da yake ciki ba, a'a a k'age take ta je domin ganin halin da yake ciki, wanda take fatan ransa ya bar gangan jikinsa...

A tare ita da Aysha dake biye da ita suka sanya kansu dakin, sai dai shiru dakin, ba motsin komai, rarrabe ido madam Gloria tayi har ta hango shi kwance flat a can gefe idanunsa a Lumshe inda zuwa yanzu dishi-dishi yake gani.

Readers Also Read