Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 11
Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 11: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 11. Mamah ta dafe ƙirjinta, tana jin yadda…
3,364 words
Mamah ta dafe ƙirjinta, tana jin yadda zuciyarta ke raɗaɗi. "Aminatu, wallahi wannan zafin ya yi yawa. Ni fa matar farko ce! Na san komai game da shi. Na san yadda yake so in kwantar masa da hankali. Amma yanzu, kamar na zama tamkar kango ne babu kowa, babu kulawa."
Aminatu ta sake zama kusa da ita, tana riƙe hannunta. "Ki yi haƙuri, Mamah. Ki tuna cewa soyayya tana da wuya wani lokaci. Amma ina jin cewa Dadynmu zai dawo da kulawarsa da zarar abubuwa sun lafa."
Mamah ta kalli hasken birnin Dubai daga saman bene, tana jin sanyi na ratsa jikinta.
Ta duba wayarta, har yanzu babu wani kira ko saƙo daga shi. Ta rufe idanuwanta, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da sauri. Wata mace za ta maye gurbina a zuciyarsa?
Ta tashi tsaye cikin zafi, tana kallon Aminatu da idanu masu nuna kishi. "Aminatu, wallahi ina jin zan koma Nigeria. Ba zan iya ci gaba da zama a nan ba. Aminatu ta girgiza kai cikin ƙoƙarin lallashi.
Mamah ta koma ta zauna, tana lumshe idanuwa cikin gajiya. A zuciyarta, tana jin kishin wannan sabuwar matar yana ci gaba da yi mata zafi. Ya Allah, ka dawo min da mijina. Aminatu ta ɗan ja numfashi, tana kallon mahaifiyarta da tausayawa. Ko da yake kishi yana ci, amma dole ne Mamah ta yi haƙuri. Auren gidan sarauta ba zai taɓa kasancewa cikin sauƙi ba.
****
Babban falon gidan yana da faɗi da tsari mai ɗaukar hankali. An kawata shi da fitilun zinariya masu laushi, yayin da bango mai launin ruwan toka ya ƙara wa falon ɗaukaka. A gefen falon, akwai wata ƙatuwar kujera mai matasai na fata, inda mahaifiyar Khalil ke zaune cikin nutsuwa.
A ƙasa, Khalil ya tsugunna cikin ladabi, idanuwansa cike da hawaye da damuwa. Zuciyarsa na bugawa da ƙarfi kamar zai rasa numfashi.
Mahaifiyarsa ta kalle shi, tana gyara gyalen kanta. "Khalil, ba wai bana sonka da Ramlah ba ne. Na san kana ƙaunarta sosai. Amma mahaifinta... wallahi, baya sonka kwata-kwata."
Khalil ya dafe kansa da hannuwa biyu, hawaye suna kwarara daga idanunsa. "Mamanmu, dan Allah, ki taimake ni. Wallahi ina sonta sosai. Kinsan fa tun tana ƙarama nake sonta. Ko da bata gama makaranta ba, ki neman mun aurenta haka."
Maman Khalil ta sauke numfashi mai nauyi, tana kallon ɗanta cikin tausayawa. Ta ɗan sunkuyar da kai, tana magana cikin rauni. "Khalil, na fahimci yadda kake ji. Amma mahaifinta ya faɗa a fili cewa ko maza sun ƙare, ba zai ba ka Ramlah ba. Ina tsoron abinda zai iya faruwa idan aka ci gaba da matsawa."
Khalil ya goge hawayensa da bayan hannunsa, yana ƙoƙarin saita numfashinsa. "Mamanmu, wallahi zuciyata ba za ta iya jurewa ba. Bansan me yasa mahaifinta baya sona ba. Ina ji a zuciyata cewa ita ce cikar burina."
Maman ta dafe zuciyarta, tana jin yadda kukan ɗan nata ke tsaga mata zuciya. "Khalil, dan Allah, ka daina jawo min magana. Ka gane ni ba mai ƙarfi ba ce, kuma kasan halin Zainab matar uban Ramlah.
Khalil ya fashe da kuka mai sauti, yana kallon mahaifiyarsa da idanu masu bayyana raɗaɗi. "Mom, wallahi bazan iya ba! Nayi ƙoƙarin mantawa da ita, amma zuciyata taƙi yarda. Ko da mahaifinta baya sona, ki taimaka ki nema min ita."
Ta kai hannu ta share hawayen dake kwance a fuskar Khalil. "Dan Allah, ka gane halin da ake ciki. Kafin a kai ga matsala, gara ka hakura da wannan soyayya."
Khalil ya girgiza kai cikin murya mai cike da ƙarfi. "Mom, wallahi bazan iya daina sonta ba. Soyayyarta ta ratsa jikina. Na san cewa tana sona, kuma ban taɓa ganin wata mace da zata iya maye gurbinta ba."
Bayan Mamah ta tashi ta bar falon cikin raɗaɗi, Khalil ya zauna a ƙasa, yana jin kamar zuciyarsa zata fashe. Me yasa soyayya zata zama haka? Me yasa zan rasa farin cikina saboda banbanci na iyali?
Ya share hawayen da suka yi masa kwance, sannan ya mike tsaye cikin dauriya. "Dole ne in gwada nema daga Babah."
Ya nufi ɓangaren mahaifinsa cikin sauri, zuciyarsa na bugawa da fatan samun mafita. Da ya isa, sai ya samu mahaifinsa yana waya. Ya tsaya daga gefe, yana jiran ya gama.
Bayan an gama wayar, Khalil ya tsugunna cikin ladabi. "Baba, dan Allah, ina neman alfarma."
Babah ya kalle shi da nutsuwa. "Me kake nema, Khalil?"
Cikin rawar murya, Khalil ya ce, "Baba, dan Allah, ina neman aurar Ramlah."
Mahaifinsa ya sauke numfashi mai nauyi, yana kallon Khalil da idanu masu nuna damuwa. "Khalil, ka yi haƙuri. Mahaifinta ya riga ya faɗa cewa ko maza sun ƙare, ba zai baka ita ba."
Khalil ya lumshe idanu, hawaye suka taru a gefen idanunsa. "Amma Baba, me yasa? Me yasa baya sona?"
Babah ya gyara zamansa. "Khalil, matsalar ba kai ba ce. Matsalar ita ce Zainab marikiyar Ramlah. Kin san yadda take da tsauri da son mulki. Tana ganin cewa ba ka dace da yarinyar ba."
Ramlah tana shigar rayuwar TikTok, tana jin daɗin yin bidiyo da wallafawa. Duk da cewa tana jin daɗin sabon salon rayuwarta, har yanzu tana ƙoƙarin neman goyon bayan mahaifinta don biyan kuɗin makaranta.
*******
Karfe shida na safe, na kammala duk wani aikin gidan da aka saba. Na gyara dakina, na gyara gado, na share bene mai launin toka. A gefen gado, na ajiye system dina, na kunna don kallon Korean film.
Ina jin yadda labarin ya fara da ƙayataccen salo, amma hankalina ya fara tashi da tunanin TikTok. Ji ya kamata in duba yadda aka karɓi sabon post ɗina na jiya.
Bayan na duba lokaci, sai naga karfe bakwai tayi. Na kashe system ɗin, na miƙe tsaye, na nufi bandaki don yin wanka. Bayan na gama, na ɗaura gyale mai launin ruwan ja, na buɗe TikTok. Wallahi jiya na tabbatar cewa kaina a duhu yake, na faɗa a raina ina dariya. Ina buɗe feed ɗina, sai na fara ganin post-post na yan gayu. Wasu suna rawa, wasu suna tsokanar juna. Wani video na wata yarinya tana tafi da salon ban dariya sai na yi murmushi. Wasu kuma sai na danna "next" saboda basu birge ni ba. Haka TikTok yake?, na faɗa ina gyara gashina a gaban madubi. To nima fa ba zan bari a bar ni a baya ba! Na ɗauki wayata, na danna camera mode. Na zaɓi wata waka ta Hamisu Breaker wata da ta fi shahara a TikTok. Na kunna duk fitilun da ke dakina, don haske ya fito da kyau.
Na ajiye wayar a kan madubi, na fara rawa a hankali, ina jujjuya idanuwa, ina saitawa da murya. Kai! Na lura da yadda fuskata ta yi kyau sosai a cikin bidiyon.
Na tsaya na kalli bidiyon na, na ga yadda na yi kyau, sai na saki murmushi. Wai shi TikTok din nan yana sa mutum ya ji kamar tauraro. Na sa wasu hashtags kamar yadda Fatima ta koya min #YanGayu #Beautifu l#HamisuBreaker #TikTokTrend. Na danna Post, sannan na aje wayar a kan gado, zuciyata cike da farin ciki. Na fita daga dakin ina dariya, zuciyata na jin daɗin wannan sabon salon.
Gidanmu gida ne mai kayatarwa sosai. Abbah yana da kudi, amma ba irin masu saki nan ba. Kowane abu a lisafi yake yi. Gidansa yana da faɗi sosai, an gina shi da salo na zamani. Falo mai tsawo, kujeru masu launin toka da fari, da fitilun chandelier masu ƙyalli.Komai a gidan ya nuna cikar arziƙi, amma kuma akwai dokoki sosai. Abbah mutum ne mai tsauri a harkar kuɗi. Duk da kuwa muna da komai, sai an yi lissafi sosai kafin a kashe kudi. Na shiga falon, na ganshi yana zaune bisa kujera mai kauri yana karanta jarida. Na yi tsuguno, na gaishe shi da ladabi.
"Sannu da safiya, Abbah."
Yayi murmushi kaɗan, ya ɗaga kai. "Yau kin tashi lafiya?"
"Eh, Alhamdulillah."
Ban tsaya karɓar komai ba, duk da cewa ina so in yi masa magana kan WAEC da NECO, amma na bari malamin mu ya masa magana. Kar na matsa masa, ko kuma ya ce ba zai biya ba. Na shiga kicin na ɗauki ruwan zafi, sannan na koma dakina cikin nutsuwa. Ina kwance a kan gado, wayata ta yi ƙara notifikeshan TikTok. Na duba, sai naga comments suna tururuwa. Wasu na cewa
"Kai Baby Girl! Kina da kyau!"
"Salon ki yana birgewa!"
"Muna son ki sake yi."
Na saki murmushi mai cike da jin daɗi. Haba! Ai ba zan tsaya nan ba. Sai Natashi nakara dasawa ƙaina camera wannan karan wakar ado gwanja nabi ina dan ram gaji.
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI
Ranar Litinin ce, rana na zafi sosai. Makarantar ta cika da ɗalibai suna fita bayan kammala jarabawa. Ina tsaye a bakin ƙofa tare da ƙawayena, muna ta hira da dariya. Duk da nishaɗin da muke ciki Ina tsaye a bakin kofa tare da Fatima, ina nuna mata wayata cike da farin ciki. "Fatima, ki duba nan! Na samu followers dubu guda a TikTok!"
Fatima ta sanya hannu a baki cikin mamaki, tana murmushi. "Kai! Wallahi, kin yi ƙoƙari! Na faɗa miki cewa video ɗin nan zai tafi. Dubi views ɗinsa 200k! Wannan fa babbar nasara ce!"
Na yi dariya, na girgiza kai. "Gaskiya ban yi tsammani ba. Kawai na ɗora shi da zuciya ɗaya. Amma yanzu kuwa, zan ci gaba da dagewa. Idan na koma gida ma, zan sake yin wasu sabbin videos."
Fatima ta yi dariya tana bugun kafa. "Ai haka ake so! Idan kika dage, wallahi har miliyan za ki kai. Ki ci gaba da kirkira abun dariya da kuma salon ki na musamman!"
Na yi murmushi mai cike da jin daɗi. "Gaskiya zan dage. Wallahi, yanzu na fara gane cewa da gaske ana jin daɗin abubuwan da nake yi!”
A dai-dai wannan lokacin ne Fatima ta ce, "Kawata, akwai party da za mu yi!"
Na ɗan yi jim kaɗan, cikin mamaki nace, "A ina ne?"
"Isler Hotel," ta amsa tana murmushi. "Babban yaron garin nan ne zai yi celebrating na samun zabe. Zakije kuwa?"
Na ɗan ja baya, kamar zan ce a'a, sai kuma na tuna da maganar Mumy a kwanakin baya: "Idan ba ki shiga jama'a ba, tayaya za a sanki har ki zama 'yar gayu?"
Na ciji leɓe, zuciyata na bugawa. "Zanje, amma gaskiya ina tsoro wallahi."
Fatima ta yi dariya tana buga kafa. "Ai komai lafiya lau! Ni kaina zan je, kuma da yawa daga cikin ƙawayenmu za su halarta. Ki daina tsoro. Idan kina tare da ni, babu abin da zai faru!"
Na lura da yadda wasu daga cikin abokaina suke magana cikin sirri, suna kallona daga nesa.
Ina cikin wannan tunanin, sai na ga wata mota mai launin toka ta tsaya a gefen hanya. Na ɗan yi juyawa da mamaki, amma ban yi tsammanin komai ba har sai da na hango shi Khalil!
"Khalil?" na furta cikin ƙaramin murya. Me yake yi anan? Mahaifina ya sha faɗa masa cewa ba zai taɓa amincewa ya aure ni ba. Me yasa ya zo nan? Salon yajawomun wata matsalar?
Ban taɓa jin daɗin kasancewa da wani kamar Khalil ba. A duk lokacin da muka haɗu, yana sa ni jin inada daraja da kima yana ƙaunata nasani tun ina yarinya haka ko'ina yana biye dani hakan kuma yasanya kowa yasani acikin ahalina . Khalil mutum ne mai taushi da kulawa. Amma Abbah ya ƙi amincewa da shi saboda rashin aikinsa da wasu maganganun da ya ji daga mutane akan abarni Saka saka ina kulashi ko primary ban gama hakan yasanya yatsaidashi.
Tun daga lokacin da Abbah ya sa masa hani, Khalil ya daina zuwa wajena. Na san yana ƙaunata. Amma yanzu tsoro nakeji.
Lokacin da ya iso kusa da mu, ƙawayena suka ja baya. Na yi ƙoƙarin yin murmushi, amma fargaba ta fara mamaye zuciyata.
"Khalil, lafiya? Me ya kawo ka nan?" na tambaya cikin mamaki.
"Ramlah, ba wani abu bane. Na zo ne in ɗauke ki. An samu gaggawa a gida."
Na kalli ƙawayena, sannan na juya gare shi. "Gaggawa? Amma me ya faru?"
"Ba zan iya faɗa anan ba," ya ce cikin sanyin murya. "Don Allah, ki yarda mu tafi, zan faɗa miki komai a hanya."
Ban yi tunanin abin zai zama haka ba. Na shiga motar, zuciyata na bugawa. Khalil ya kashe ƙofar, sannan ya fara tuka motar cikin sauri.
"Khalil, me kake yi? Ina za mu?"
Ya ɗan yi shiru, sannan ya kalle ni ta madubi. "Ramlah, ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba. Na yanke shawara zan tafi da ke zan aure ki ko da ba su yarda ba."
Naji jikina ya yi sanyi. "Khalil, wannan ba daidai bane! Soyayya ba haka ake yi ba!"
"Ramlah, kin san irin yadda nake ji game da ke? Na gwammace na gudu da ke fiye da na rasa ki."
Na yi kokarin kiran wayata, amma Khalil ya lura. Ya ja wayar daga hannuna, yana girgiza kai.
"Ba zan bari ki kira gida ba. Zamu tafi wani wuri mai nisa. Zan aure ki da kaina."
Na fara kuka. "Khalil, don Allah ka tsaya. Abbah zai kashe ni idan ya gano wannan."
"Ki yi shiru, Ramlah. Ki kwantar da hankalinki. Ina sonki sosai. Ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba."
A wannan lokacin, na fara gane cewa soyayyar Khalil ta rikide zuwa wani abu mai haɗari. Yana kallona ta madubi, amma hankalinsa a rikice. Na yi ƙoƙarin kwantar masa da hankali, amma zuciyata cike da tsoro.
"Khalil, ka tsaya, don Allah. Wannan ba hanyar da za mu bi ba. Na san kana sona, amma ba haka ake tafiyar da soyayya ba."
Sai ya tsaya tare da daka birki a wani gefen hanya, yana numfashi da ƙarfi. "Na rasa mafita, Ramlah. Na rasa yadda zan ci gaba da rayuwa ba tare da ke ba." Ya kalli cikin idona, yana ɗan murya.
Haka Khalil ya yi ƙoƙarin shigar da ni ta ƙarfi cikin gidan da muka zo. Yayin da muka shiga, na ji zuciyata tana bugawa kamar ana dukan ganga. Wurin shiru ne, babu motsin rai ko tsuntsu, sai ƙarar zuciyata da ƙafafun Khalil suna dokawa ƙasa.
Da kyar na iya tsayawa a kan ƙafafuna, amma duk yadda nake roƙon sa da magiya, yana kallona cikin idanu da wani irin yanayi na zafin rai da kishi. Wani ɓacin rai ne ya bayyana a fuskarsa, kamar yadda wutar daji ke cinye koren ciyayi.
Ya ja hannuna da ƙarfi, ya tura ni cikin wani ƙaramin falo. Ƙofar ya kulle da sauri, sannan ya yi tsaye yana haki, yana kallona da idanuwansa da suka koma kamar na baƙin ƙogi cike da bacin rai da tsantsar ciwo.
"Mahaifinki bai isa ya hanani ke ba!" ya furta, muryarsa na rawa. "Zan tabbatar da cewa ba zai iya raba mu ba. Soyayyarki na cikin jinina, Ramlah! Shekara goma sha biyar ina jiran wannan lokaci. Yanzu za a ce na fasa? Wallahi Sai Na kusance ki Nayi miki ciki Ta yadda mahaifinki bai isa yarabamu ba kuma sai Ya auramun ke Wallahi."
Na tsaya kallonsa, hawaye na gangarowa bisa kumatuna. Na kasa gane yadda soyayyarsa ta koma kamar makami mai lahani. "Khalil, don Allah, ka tausaya mini," na furta cikin kuka mai rauni. "Ba haka ake tafiyar da soyayya ba. Ni marainiya ce! Ka yi hakuri, dan Allah!"
Amma Khalil bai saurare ni ba. Sai ya cigaba da matsowa kusa, yana magana cikin wani irin yanayi na rashin nutsuwa. Na ji wani irin tsoro yana taso daga zuciyata zuwa duk wani sashe na jikina. Na yi ƙoƙarin tserewa, amma yana rike da hannuna da ƙarfi, kamar wanda yake tsoron in tsere masa har abada.
"Matsalar ki ce ba ki gane ba, Ramlah," ya ce cikin muryar da ke haɗa kuka da fushi. "Na rasa mafita. Na rasa yadda zan ci gaba da rayuwa ba tare da ke ba.” Cikin bazata ya fizgo rigata yana rabani daita haka skirt din makaranta ma yana kokarin yagamin inaja ina kuka sosai Amma sai da yarabi da skirt dina sannan yashiga tuɓe kayan jikinsa Innalillahi wa inna ilaihirraji’un Nashiga uku Na shiga uku DanAllah khalil karka wulakantani Amma ya toshemun baki yana kokarin hayemun….
Nana hadiza
09030569336ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA GOMA SHA TAKWAS
Bayan sallar Magariba ne hankalin Momy ya fara tashi. Na san hakan saboda duk lokacin da aka fara kunna fitilar dare har ya kai ga shudewa, ni dai ban dawo gida ba. Duk yunkurin da Momy ta yi na kiran lambar Malam Idi ya ci tura lambar ba ta shiga ko ɗaya.
A lokacin da Abba ya dawo daga aiki, hankalin kowa ya yi mummunan tashi. Na san cewa Abba yana cikin gajiya daga aikin sa, amma lokacin da ya shigo falon, sai na ji muryarsa cikin damuwa yana tambayar Momy
"Lafiya? Me ya faru?"
Momy ta kalle shi cikin damuwa, tana girgiza kai.
"Wallahi har yanzu Auta ba ta dawo gida ba tun da safe da ta tafi makaranta. Na kira lambar Malam Idi sau da dama amma ba ya shiga."
Abba ya runtse idanu cikin damuwa, ya nufi inda yake ajiye wayarsa. Na san cewa yanzu Abba zai yi duk abin da zai iya don gano inda nake. Nan take ya umarci wani daga cikin mutane su je gidan Malam Idi don jin inda nake. Kafin lokaci ya ja, an dawo da amsa daga gidan Malam Idi cewa wani mutum ne ya zo ya ɗauke ni daga makaranta, yana tunanin ko Yaya Abbas ne. Wannan labari ya girgiza Abba sosai.
Abba ya dafa kansa cikin tashin hankali, yana magana a hankali kamar ba da gaske yake ba
"Wani ne ya ɗauke ta daga makaranta? Waye wannan?"
A daidai lokacin ne kuma Yaya Abbas ya shigo cikin gaggawa.
"Abba, me ya faru ne?" ya tambaya cikin damuwa.
Abba ya kalle shi cikin fusata, ya ce
"Wani ya ɗauki Auta daga makaranta. Ba wanda ya san inda take yanzu haka."
Momy kuwa ta rike zuciyarta tana kallon Abbas
"Abbas, nifa hankalina ya tashi. Kada dai wadancan kawayen banza nata su ja ta cikin abin da bai dace ba. Yau fa na shiga uku!"
Yaya Abbas ya girgiza kai, yana kokarin kwantar musu da hankali.
"Momy, Auta ba irin wannan bace. Ba ta da halin bin kawaye haka kawai."
Sai ga Billy ta fito daga daki cikin tsoro.
"Abba, na kira kawarta Fatima. Tace wai wani mai suna Khalil ne ya zo ya ɗauke ta."
Ran Abba ya baci sosai, har ya kai ga ɗaukar wayarsa cikin hanzari. Ya kira mahaifiyar Khalil a daren, yana yi mata fada kan dalilin da yasa danta zai ɗauki yarinya ba tare da sanin iyayenta ba.
Mahaifiyar Khalil ta nemi gafara cikin nadama, tana cewa babu inda zai kai ta. Ta kuma yi masa fada kan wannan rashin tunani. Sai dai wannan ba ya rage fushin Momy ba, wadda ta fara zazzaga zagi.
"Wallahi, dama na san Khalil ne ke zuganta! Daman shi ne ya sa ta fara fitsara da rashin kunya. Wannan dai sai an lallata tarbiyar yarinyarta saboda irin wannan hali!" Momy ta fada cikin bacin rai.
Abba ya rasa abin cewa saboda tashin hankali ya yi masa yawa. Ya yi shiru yana tunanin abin yi. Yaya Abbas kuwa ya cigaba da kokarin kiran lambar Khalil, amma har yanzu ba ya dauka.
Da suka ga zaman gida ba zai amfana ba, Abbas ya ce
"Abba, bari mu ja mota mu fita. Zai fi idan muka bincika da kanmu."
Abba ya amince, suka fita cikin hanzari. Har lokacin Momy tana cikin fargaba tana cewa
"Wallahi idan aka sake ganina tare da wannan yaron, zan hukunta ta da kaina!"
Ko da su Abba suka fita, babu inda ba su je ba amma babu ni babu labarina. Har wasu abokan Khalil din ne aka tambaya amma kowa sai yace ai ba su gan shi ba. Da kansa Abba ya je gidan su Khalil, ya samu mahaifinsa yana tambayar inda ɗansa yake. Mahaifin Khalil ya ce ba shi da labarin inda ɗansa yake, amma ya tabbatar wa Abba cewa za su yi bincike domin gano inda suke. Saboda tsananin damuwa da tashin hankali, Abba ya fara kuka. Yaya Abbas ya shiga bashi baki akan babu abin da zai same ni.
***
Su Momy dake gida kuwa, dariya ta sa bayan fitar Abba, tana barin falon cike da murna.