Kenza eBookz

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 7

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 7

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 7: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 7. "Karɓi wannan turaren. Gab da zaki shiga…

3,349 words

"Karɓi wannan turaren. Gab da zaki shiga gidan sarauta, ki gogashi a wuyanki da kunnuwanki. Wannan garin kuma ki watsa shi a kafar hagu. Wannan abu sirri ne, na tabbatar da cewa zai ja hankalin As'ad."

Ta tsayar da Haneefa ta kalli ta cikin ido

"Haneefa, komai rintsi, kada ki soma magana da kowa sai As'ad. Koda suna gaishe ki, ki yi kamar ba ki ji ba. Kin ji ni? Kada ki ɓatamun aiki!"

Haneefa ta gyara tsayuwarta, tana gyada kai

"Na ji mama. Zan yi yadda kika ce."

Maryama ta yi ɗan murmushi mai ɗauke da nasara

"Kin ga yan uwanki suna kokari, amma ke kadai na yarda da ke. Ki kula sosai, kada ki yi wani abu da zai bata mana suna. IAs'ad yana da rauni akan mace mai kyau da nutsuwa. Ki nuna masa cewa ke ce zaɓin da ya dace."

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA GOMA

Da Haneefa ta shiga babban falon gidan sarauta, ta yi sallama cikin wani irin salo na kissa, muryarta na rawa tamkar wadda aka koya mata. Ta tsaya a gaban As'ad, tana zuba masa ido da murmushi mai ɗauke da natsuwa. Amma abin mamaki, ko kallonta bai yi ba. Ya ci gaba da duban takardun da ke gabansa tamkar ba ta ma wanzu a cikin ɗakin.

Haneefa ta ji zuciyarta na bugawa da ƙarfi, fuskarta na ɗaukar wani irin yanayi na rashin jin daɗi. Ita kam, ba ta saba da irin wannan wulakancin ba. A daidai wannan lokacin ne ta sake ƙarfafa zuciyarta, ta gyara tsaiwarta, tana murza hannunta cikin rashin gaskiya.

"Ranka ya daɗe, barka da yamma," ta faɗa cikin sanyi, tana matsa maganarta da wata irin murya mai sanyi da salon lalama.

Sai a wannan lokacin ne As'ad ya ɗaga kai ya kalleta, idonsa na yin wata irin ƙyaƙyƙyawar gani. Ya lura da yadda ta yi shigar da ba ta dace ba kaya masu matuƙar ɗaukar hankali, nonuwanta suna bayyana sosai, ga kuma uban kwalliyar da ta yi tamkar mai shirin rawa. Bai ce komai ba sai kawai ya yi ɗan share murya, sannan ya ce cikin sanyin murya

"Barka."

Haneefa ta ji zuciyarta na tsinkewa saboda yadda ya yi magana cikin natsuwa da girmamawa, amma ba tare da nuna sha'awa ko kaɗan ba. Wata zuciya a cikin kanta ta ce, "Idan na auri wannan, lallai izzata za ta karu. A tare da shi, zan zama cikakkiyar sarauniya!"

Batare da ta samu ƙarfin yin wata magana ba, sai ta zauna kusa da shi, tana ƙoƙarin jan hankalinsa. Sai da aka ɗan yi shiru mai tsawo kafin As'ad ya dube ta a hankali ya ce

"Akwai damuwa ne?"

Firgigit! Haneefa ta yi kamar wadda aka tsayar da numfashinta. Cikin rawar murya ta ce

"A'a, ranka ya daɗe."

As'ad ya yi wani irin numfashi, sannan ya miƙe tsaye, yana kallon agogon bango. Ya juya ya kalleta ba tare da nuna wata damuwa ba, sannan ya ce

"Mu kwana lafiya."

Haneefa ta ji tamkar ta nutse. Yadda ya miƙe tsaye, tsayuwarsa mai cike da kima da mutunci, sai zuciyarta ta shiga karkarwa. Kafin ta ankara, ta furta da ƙasa da murya

"Woow!"

As'ad ya juyo ya dubi ta kaɗan, amma bai ce komai ba. Yana fita daga falon, ta ji zuciyarta na bugawa da sauri. Wata irin soyayya da sha'awa suka lullube ta. "Wayyo Allah! Wannan kuwa namiji ne. Wallahi, As'ad ba kamar sauran maza ba ne," ta furta cikin ranta.

---

Da Haneefa ta koma gida, tana cikin farin ciki mai cike da fargaba. Fulany Maryam na zaune tana jiran ta dawo. Da ganin yanayinta, ta gane cewa al’amura sun fara tafiya dai-dai.

"Mama! Wallahi As'ad ya haɗu, kai... ai a hoto baiyi kyau ba! Yana da kwarjini, yana da kyau! Wallahi wannan fa hadaddan mutum ne, kai!"

Fulany Maryam ta yi murmushi mai cike da tsokana, amma a zuciyarta tana sake nazarin yadda Haneefa ke magana tamkar wadda ta ji ƙauna.

"Ke kam, ki nutsu. As'ad mutum ne mai ra'ayi da natsuwa. Dole ne ki kula da yadda kike magana a gabansa. Kada ki nuna damuwarki ko kaɗan. Ki kwantar da hankalinki. Ranar daura aure na kusa, kuma As'ad ba zai iya tsallake umarnin sarki ba. Kina da lokaci ki tabbatar da cewa ya kalle ki da idanun sha'awa. Ki yi amfani da turaren da malam ya ba ki."

---

Da dare, Fulany Maryam ta ɗauki motarta, ta nufi gidan babban malaminta, wanda ake kira "Mai Iko." Ta shiga falonsa cikin girmamawa, tana sunkuyar da kanta. Malamin ya kalle ta cikin murmushi mai cike da ruɗu.

"Tunda na ganki na san cewa labari ne mai kyau kike ɗauke da shi."

Fulany ta gyara zaman gyalenta, tana murmushi. "Mai Iko, gobe za a daura auren!"

Mai Iko ya yi wata irin dariya mai ban tsoro. "Na gaya miki babu wanda zai iya tsallake wannan auren. As'ad yana a hannunki yanzu."

Sai dai Fulany ta nuna ɗan damuwa. "Amma Hajja tana tsaye kan lamarin. Bana son matsala idan har ta gano wani abu."

Malamin ya kwashe da dariya. "Hajja ba ta isa ba. Tsohuwa ce, bata da ƙarfin karya maganata. Ai ita ba ta isa ba! Wataƙila tana da wani ƙarfin addu'a, amma kin san me? Wannan turare ki yi amfani da shi gobe. Ki turara kayanki duka da shi, sannan ki shiga cikin gidan sarki. Zaki ga yadda As'ad zai zama naki. Amma kuma akwai wani abu da ya dame ni."

Fulany ta ɗaga gira cikin tsoro. "Wane abu kenan?"

Malamin ya lumshe idanu, yana nazari. "Ina gani kamar wata inuwa tana tsaye kusa da As'ad. Wataƙila ba matarsa ba ce, amma ba zan iya ganin komai ba."

Fulany tace. "Innalillahi! Wata kila matarsa ce! Na gaya maka tun da farko cewa ita ce ke kawo matsala a duk lokacin da aka ce za a yi wani abu."

Malamin ya yi murmushi ya yi wata dariya mai cike da mugunta. "Na haɗa aikinta ita tun tuni, amma ina ganin cewa wannan inuwar tana da alaƙa da wani abu mai girma. Ki yi duk yadda na faɗa miki, burinki zai cika."

Fulany ta gyada kai tana jin ƙarfin gwiwa. "Babu wata matsala mai iko. Duk abin da kake buƙata zan kawo."

Malam ya gyara zama, yana murmushi mai cike da mugunta. "Bukata ta dai a biya kamar yadda na faɗa miki.”Zan ƙara bincike, amma ki tabbata burinki zai cika."

Fulany ta yi murmushi mai cike da jin daɗi. "Ba zan yi wata-wata ba, Mai Iko. Ga wannan, ka ci gaba da aikin."

—----

A gida, Haneefa na gaban madubi tana tunanin As'ad. Ta rungumi kanta cikin shauƙi.

"Mama, wannan mutumin ai kamar jarumin fim ne! Wallahi, idan na aureshi, rayuwata ta gama kyau!"

Fulany Maryam ta kalli 'yarta, tana jin cewa ta kusa cika burinta. Amma tana da ɗan fargaba game da yadda Haneefa ta fara shiga ruɗani. Ta san cewa As'ad ba mutum bane mai rauni ga kyawawan mata, sai dai wanda ya samu matsayi a zuciyarsa.

---

Washegari da safe na tashi da uban aiki. Tun farkon tashina na fara gyaran gida, saboda Abba yace kosai yakeso, ita kuma ya Billy shawarma. Ai kuwa saboda tsabar iyayinta har da caramel ma, ba tea ba. Momy kuwa tace in hada mata teba. Na tsinci kaina cikin wani irin aikin wahala, amma duk da haka ban nuna komai a fuska ba, na ci gaba da gyaran gidan.

Wajen karfe tara na gama duk wani aiki. Na yi wanka, sannan na dauko system dina da wayata, na saka su caji. Tun jiya maganganun Fatima ke yawo a cikin zuciyata. Na rasa yaya zanyi da kaina. Kai! Ni Instagram din nan da TikTok din ma, na rasa yadda suke. Ai ko bantaba shiga ba. Na zauna ina tunanin yadda zan fita yau zuwa birthday din Fatima. Duk da cewa tsoro nake ji, amma irin yadda Fatima ta rika bani kwarin gwiwa yasa naji kamar zan iya zuwa.

Na tsaya na tsara yadda zan fada wa Abba. Na tabbatar idan nace birthday din kawata ne, ba zai bari ba. Sai kawai na tsara cewa zan fada masa cewa babbar kawata ce aka kwantar a asibiti, kuma mu da yan ajinmu na Islamiyya zamuje dubata. Nasan zai fi sauki idan haka na fada masa.

Ina cikin tunani sai naji muryar Momy tana cewa, "Ke Ramlah, meye haka? Ki dafa mun tuwo, ki kuma hada wannan abincin." Na tsinci kaina ina jin haushi amma na dake, nace, "Momy kiyi hakuri, nazata shi kikeso in dafa."

A nan take ta sake cewa, "Wai me yasa kika canza ne?" Cikin jin haushin kalamanta, amma ina danne zuciyata nace, "Wallahi Momy, na zata shi kikeso."

Nan fa naji takun Abba yana sakkowa. Ina tsaye cikin nutsuwa, sai naji Momy ta soma canza magana tana cewa, "To ai addu'a nake mata akan kokarin da take yi. Ka san idan na fada 'ke Ramlah,' nasan bata karya ba. Shine nazo yin mata fada."

Abba yayi murmushi, sannan ya ce, "Haba Zainab, duk aikin da yarinyar nan tayi, ki ci abin da ya samu. Kada ki matsa mata."

Momy kuwa sai ta saki marairaice fuska tana cewa, "Abban auta, addu'a fa nake mata akan wannan kokarin nata."

Na ji dadin kalaman Abba sosai. Bayan ya gama magana, sai na shiga gaisheshi cikin ladabi. Nan take na fada masa cewa mu da yan ajinmu na Islamiyya zamuje dubiya da yamma. Abba yace "Adawo lafiya."

Bayan haka ya zaro dubu biyar daga aljihunsa ya mikomin yace, "Ki siyo lemo, ki kai mata."

Na tsaya kaina ya dauki nauyi. Yau nice zan yi wa Abba karya? Amma kuma idan ban fita ba, Fatima zata ji haushi. Na karba cikin ladabi, na gode masa har ya fita, zuciyata kuwa na cike da damuwa.

Wata muguwar harara Momy ta watsa min, har naji mamaki. Kamar ba ita ce ta gama yabona ba a baya. Cikin wata irin murya mai cike da takaici, sai naji ta ce, "Ba zaki tashi ki je ki gyara saman ba? Ko ni zan gyara miki?"

Bance komai ba, na mike cikin jin nauyi na nufi dakin. Na gyara ko ina yadda nasaba, hatta wandonta da breziyarta na wanke musu kamar kullum. Ina gamawa, na duba agogo, naga karfe daya har ta wuce. Na sauko kasa, sai naji yaya Billy ta kira ni, "Auta, ga undies dina can ki wanke min, please. Na bar pad a dustbin, kinsan ban son kazanta."

Wata irin zuciya ce ta taso min. Kamar in kifa mata mari wallahi.

Ina tsaye cikin mamaki sai naji muryar Momy tana cewa, "Kiyi sauri kizo ki dora mana abincin rana."

Na cije baki, amma na kasa boye haushina, sai nace, "Wallahi Momy nagaji, sallah nake shirin yi."

Cikin tsawa ta ce, "Dan ubanki! Ni kike gayawa kingaji? Uban wanene zai yi mun aiki? Gaki agida, meye amfaninki? To wallahi baki isa ba! Fitsararriya mara kunya! Dalla, shige kije ki dora abinci. Sha sha sha!"

Baiwuya na fashe da kuka. Yaya Billy ta ce, "Haba Momy, is okay mana." Amma Momy bata kulata ba. Na shiga kicin din cikin kuka, na dora musu abincin rana, sannan na tsaya nayi sallah a can cikin kicin din.

Dakyar na gama aikin duk sai karfe hudu na rana. Ina kunna wayata sai ga kira daga Fatima yana shigowa. Na daga, ina sallama, ta ce, "Haba Auta, dan Allah kizo mana. Ina ta jiranki tun dazu."

Bacin rai ya gama mamaye zuciyata. Na ce mata, "Gani nan."

Nan take na fita na sayi kati a banki, sannan na yi download din Instagram da TikTok har da WhatsApp. Ban gama bude su ba sai ga sakonni daga Khalil sun fara shigowa. Khalil dai tun ina yarinya yake kaunata. Dan uwana ne, dan uwansu Abba da Babansa cikinsu daya. Yanzu kuwa ya gama karatunsa har yana aiki, amma Abba bai yarda da soyayyarsa a gareni ba.

Ban bude sakonninsa ba, sai na duba wasu group chats da aka kara ni. Na lura akwai wani group da sunansa "Bad Boys and Girls", sai nayi mamaki. Ban dade da shiga ba, naji wani irin tashin hankali saboda kalmomin batsa da suke ciki. A take na fita daga group din, sauran group din ma na fita gaba daya.

Cikin fargaba da mamaki naji wayata ta sake daukar kira daga Fatima. Zuciyata na dukan uku-uku, da alama yau akwai zance.

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA GOMA SHA DAYA

A yayin da kawata Fatima ke can tare da mutanenta, sai ga wani sako daga gare ta

"Kai Fareed, ta amsa mun zata zo!" Fatima ta fada tana kyalkyale da dariya.

Ta juyo da murmushi mai cike da tsokana

"Dan Allah, ina son ka cire mata wannan kunyar tata. Idan da hali ma, ka jefa mata wani abu cikin lemon ta, ku rage mata zafi. Kana ganinta, ka rungume ta kadai, mutumina."

Bayan haka, Teemarh ta kalle ni tana dariya, ta ce

"Kin biya ni wallahi! Kiduba nan, na sanya miki 500k. Wallahi narasa dadin da nake ji a raina. Thank you!"

Gaba daya zuciyata ta cika da farin ciki da dan karamin tsoro a lokaci guda. A yau ne kawata Fatima ta shirya babban taro a gidansu taron da ke cike da alkhawarin nishadi da hango sabbin fuska. Na san dai ba komai ba ne idan Fatima ta sa abu a gaba taron zai yi armashi sosai.

Ina tsaye a daki, na zura abayata sannan na nufi falo don sanar da Mumy zan fita. Mumy tana tsaye a gaban murhu tana hada kayan abinci. Na matsa kusa da ita cikin ladabi.

"Mumy, zan je gidan Fatima. Zan dawo nan da nan."

Ta juyo tana kallona da murmushi mai cike da kulawa

"Kada ki dade, kin san ke ce za ki dafa abincin dare."

Na ce

"Ba matsala, Mumy."

Yayin da nake kokarin fita, sai ga Yaya Billy ta fito daga dakin ta cikin wani riga da wando na zamani mai kama da jumpsuit, ta kalle ni da dariya.

"Auta, ki jira, zan kai ki."

Na saki murmushi nace

"Aa, Yaya. Malam Idi direba zai kai ni."

Ta daga kafada cikin rikon lamarin:

"To, ba damuwa."

Na fito daga gida, iska tana kada gashina cikin sanyin yamma. Na isa bakin kofa, na ga Malam Idi yana jiran fitowata a gefen motar. Na shiga cikin motar cikin natsuwa, na ce

"Dan Allah, ka jira ni bayan na shiga gidan su Fatima. Ba zan jima ba."

Ya gyada kai cikin girmamawa.

Ina shiga cikin gidan su Fatima, sai ga ita da wasu kawayenmu na makaranta sun fito, kowacce cikin shigar zamani mai kayatarwa. Fatima ta hango ni ta saki murmushi.

"Ke! Nace wa Malam Idi yatafi, ki kwantar da hankalinki, zan dawo dake da kaina."

Na dan waro ido cikin mamaki.

"Amma na riga na ce masa ya jira ni..."

Fatima ta yi dariya

"Ki kwantar da hankalinki.”

Da na shiga part din Fatima a gidansu, hankalina ya yi mugun tashi. Na tsaya a bakin kofa ina kallon yadda su Teemarh da sauran kawayen Fatima suka yi shigar zamani, kowacce sanye da mini skirt da wata armless ta makale a jikinsu. Gaba daya yan ajinmu sun cika wajen, kowacce cikin kwalliya mai jan ido. Na tsinci kaina ina jin kunya kamar na yi wani laifi.

A daidai wannan lokacin ne na ji Wafiya, yar ajinmu, tana maganganu da muryar raini

"Ke Teemarh, ya zaki gayyato mana wannan yar kauyen? Duba wata shiga da ta yi!"

Na ji maganar Wafiya ta soki zuciyata kamar mashi. Cikin kankanin lokaci, wasu daga cikin kawayen suka fara kallona da harara, wasu kuma na murmushi irin na mugunta. Teemarh ta matso kusa da ni tana roko

"Dan Allah, ki taimaka ki saka kayan nan. Wallahi, ko hotuna ba za a yi ba. Kuma fa iya matane!"

Duk yadda ta yi magiya, na tsaya kai tsaye, zuciyata cike da kunya da tsoro. Sai ga Wafiya ta kara magana tana kallon ni da wani irin kallo mai cike da wulakanci

"To ita tasanya me? Matar da ko nonuwa bata faraba, babu wani shape, ba komai!"

Na ji kalmarta ta yi min zafi kamar wuta, raina ya baci sosai. Amma na karbi kayan da Teemarh ta ba ni na shiga daki na saka. Lokacin da na fito, sai na ji kunyar duniya ta lullube ni, don haka na zura abaya a kai. Duk yadda suka yi kokarin cire min, na ki. Karshe na ce wa Fatima

"Sai dai kawai na koma gida."

Fatima ta saki fuska cikin damuwa

"Aa, kada ki koma. A haka kawai mu tafi."

---

Abba yana dawowa gida ya fara tambaya inda nake. Mumy ta amsa cikin tsoro

"Wallahi, ban san inda ta tafi ba. Ba ta sanar da ni ba. Malam Idi ne ya ce tun karfe biyar ya kai ta gidan kawarta. Nace masa ya jira ta dawo, amma tace zata dawo da kanta.

Abba ya kashe wayar cikin takaici. Ya dube ta yana fadin

"Zainab, ya zaki bar yarinya har karfe goma na dare bata dawo ba? Gashi babu waya”

Mumy ta fashe da kuka tana cewa

"Abba, yanzu na lura cewa ta fara canzawa. Wallahi tsoro nake ji yanzu."

Abba ya sa hannu ya shafa kansa, yana jin zuciyarsa tana tafasa. Lokacin da karfe 12 ta kusa yi, ga shi momy ta dinga zugashi da cewa

"Kana gani, yarinyar nan tana neman lalacewa. Gaba daya ta canza!"

*****

Wurin ya cika da hayaniya da nishadi. Kowanne bangare yana da mutane cikin kwalliya, manyan yaran gari sun taru sosai. Na ji tsoro ya lullube ni ganin babu mai shiga irin ta ni. Wani saurayi ya nuna ni yana dariya

"Teemarh, wannan fa me aikin gurin ce?"

Teemarh ta amsa cikin dariya:

"Aa, kawata ce."

Na tsinci kaina cikin kunya mai tsanani, zuciyata tana dukan uku-uku.

Kawai sai na ji wani ya rungume ni ta baya. Na waigo cikin tsananin mamaki, ashe Fareed ne! Cikin fusata na tureshi ina masifa

"Me haka? Me yasa kake min haka?"

Ya tsaya yana kallona kamar zai yi kuka.

"Dan Allah ki yi hakuri. Wallahi, ban nufi cutar ki ba."

Ya tsugunna yana mikon flower hannunsa yana dariya har da hawaye. Cikin wannan lokaci, MC ya fara yabonmu yana cewa

"Ah, yau an samu sabuwar soyayya a gurin!"

Na yi murmushi duk da kunyar da nake ji. Fareed ya karaso kusa da ni yana narkar da kalamai masu dadi. A haka muka zauna guri daya.

Bayan dan lokaci, aka kawo min snacks da drinks. Ina jin wani abu ya taso daga cikina kamar jiri. Nace masa ya dakata da dan jira. Sai na yi dabara na ce

"Zan je na sallami driver."

Fareed ya amsa cikin fara'a:

"To, ni zan raka ki."

Na samu nasarar fita daga cikin gida, amma sai Teemarh ta ce

"Wallahi, mun riga da mun sallami Malam Idi."

***

A lokacin ne na gane cewa dare ya yi sosai. Kamar an doke ni da tsoro, na cire takalmina na fara gudu. Na yarda cewa ni 'yar kauye ce, amma wannan kunya ta fi karfina. Har na fara ganin titi babu mota, na yi kokarin tsallaka, amma jiri ya kwashe ni har na sulale akasa. Na rasa yadda zan yi, kuka na ratsa zuciyata, zuciyata na bugawa kamar ana kokarin tsaga kirjina.

Baiwar Allah! Ban san yadda nake ba, amma dai na ji kamar numfashina yana neman daukewa. Na tsinci kaina a kwance a gefen titi, sanyi yana shigar jikina har cikin kasusuwa. Kamar mafarki nake yi—wani abu mai nauyi yana dannawa a kirjina, yana hana ni yin motsi ko ɗaya.

A nan ne na fara jin wani ƙara yana kusantowa, kamar na mota. Sai ga haske ya bayyana a fuskata. Na so in yi ƙoƙarin miƙewa, amma sai jiki na ya ƙi bani damar yin komai. Na ji horn yana ƙara ƙarfi, amma ko kaɗan ba zan iya motsawa ba.

Na ji muryar wani mutum yana masifa daga cikin mota

"Ke! Wacce irin mahaukaciya ce ke kwance a titi haka? Ba kya jin horn ne?"

Ina cikin kokarin bude ido na gane muryar, sai kawai na ji ya ƙaraso kusa da ni. Ya durƙusa yana girgizani, yana cewa

"Ramlah! Ramlah! Ya salam! Me ya same ki?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull