Kenza eBookz

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 9

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso - Chapter 9

Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 9: Ƙaddarar ramlah book 1 complete na nana diso Chapter 9. As’ad ya rintse idanuwa, yana jin tamkar…

3,344 words

As’ad ya rintse idanuwa, yana jin tamkar wani kulle ya ɗaure masa zuciya. Duk ƙoƙarinsa na tsayayya ya gagara.

Nikam nace As'ad har ankamu Ne????

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA GOMA SHA UKU

Adaren nan Abba gaba ɗaya bai kwanta ba. Bakaramun hankalinsa tashi yayi ba, domin tunanin abin da ya faru yana ta faman yi masa yawo a zuciya. Bai taɓa tsammanin za ta aikata irin wannan abu ba. A zahiri, bai iya ganewa ba ko da mafarki ne ko gaske. Ya daɗe yana tunani kafin ya miƙe ya watsa ruwa, sannan ya koma kan dadduma ya ɗora sallah, yana neman nutsuwa da natsuwa a cikin zuciyarsa.

Mumy ce ta taso daga ɗaki, tana lura da yanayin Abba. Ta san cewa lallai wannan lamari ya dame shi sosai. Ta zauna kusa da shi, cikin tausayi da natsuwa ta fara magana, "Dan Allah Abba, kayi haƙuri. Ai bata taɓa aikata haka ba, wannan ne na farko. Kasani, yaran yanzu, ba za ka iya musu ba. Kawaye ne ke jan su da waɗannan abubuwa. Ka yafe mata, dan Allah."

Abba bai ce komai ba, kawai sai ya cigaba da addu'o'insa cikin natsuwa. Bayan ya gama, ya kalli Mumy da kyau, yana jin nauyin maganar da take yi. Zuciyarsa na bugawa, yana ji kamar zuciyarsa ta tsinke saboda takaici da kuma tunanin yadda tarbiyyar 'yarsa ta fara ɓaci.

Mumy ta sake cewa, "Dan Allah, Abba, kayi haƙuri. Ni kaina na yi mamaki, amma ka ba ta dama ta gyara kuskurenta. Ka san yaran yanzu, sukan yi kuskure amma kuma suna buƙatar shiriya."

Abba ya ɗan numfasa, ya na jin baƙin cikin abinda ya faru, amma kuma yana jin maganar Mumy tana yi masa tasiri. Sai dai zuciyarsa tana ƙunci. Yana tunani, "Ina nayi kuskure ne wajen tarbiyyarta? Me yasa ta aikata haka?"

**

Washegarin ranar, da safe, jikina har yanzu yana ciwo, musamman ma ciwon kai da ya tashi tun da asuba. Na san na yi laifi, shi yasa tun ƙarfe huɗu ban sake yin bacci ba. Na shiga gyaran gida duk da cewa kwayar da Fareed ya zubamun a lemo bata gama sakina ba, ga gajiya da ciwon jiki. Duk da haka, na tattara ƙarfin guiwa na gyara ko'ina, na wanke bandakuna, sannan na ɗora abin kari. Ganin ƙarfe shida na safe ya kusa, sai na nufi ɗakin yaa Billy don tambayarta abin da zan dafa mata.

A lokacin ne na ji dariyarta, tana kyalkyala cikin jin daɗi. Cikin mamaki, na tsaya na saurari maganar da take yi. "Oga, wai wace kwaya ce yarinyar nan tasha? Ka san ko daga hannunta bata yi ba. Ni fa ban taɓa shan irinsu ba, yau na sha wata sabuwa. Gaba ɗaya ta kasa ɗaukata, baccin ma ban yi ba."

Na ji zuciyata na tsinkewa. Na furta cikin tsoro, "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un." Na dafa kirjina, ina tunani, "Kenan da gaske shaye-shaye take yi? Ko kuwa wani abu daban ne?" Amma ba wannan ne kawai ya fi tayar min da hankali ba, sai dai maganar da ta sake yi.

"Ai na gaya maka, wallahi sai na lalata rayuwar Ramlah. Soyayyar da mahaifina ya nuna kanta fiye da ni, sai ta zama masa ajalinsa. Ina so ka bani kwayar da zan dinga zuba mata cikin abin shanta. Lokaci kaɗan, shaye-shaye zai kama jikinta. Duk gidan nan, ni tafi yarda da ni. Nifa na fi kowa nuna mata kulawa. Kai dai kawai ka kawo. Ko Mumy bata isa ta nuna mata irin kaunar da nake nuna mata ba."

Gaba ɗaya jikina ya mutu, hawaye na zuba a fuskata. Na koma kitchen cikin sauri, na fashe da kuka. "Wannan wace irin ƙaddara ce? Yaya billy ce ke shirya wannan mugun nufin akaina? Na yi zaton itace mafi ƙauna a gare ni a gidan nan!"

Cikin wannan halin ne, Mumy ta shigo kitchen ɗin, ta ga ni ina goge hawaye. Ta ce cikin kulawa, "Yar albarka, har kin tashi? Na san ba halinki ba ne wannan. Kidaina damuwa da faɗan Abba, kinji? Ai inda kikaje ba wani abu ba ne. Haka yan gayu sukeyi. Kin san Abba bai waye ba. Ni da kin gaya min ai da sai na ce kije gidan Abbas ki kwana. Kema yakamata ki zama yar gayu ai."

Na rasa abin cewa, zuciyata na ƙara tsananin raɗaɗi. "Shin Mumy bata fahimci cewa da gaske Fatima tana nufin cutar da ni bane? Ko kuwa itama tana cikin wannan haɗin bakin?"

A cikin wannan tunanin, na san cewa ba zan iya dogara da kowa ba yanzu. Dole ne in nemi mafita kaina, kafin lamarin ya wuce gona da iri. "Amma ta yaya zan yi? Kuma wa zan nema ya taimakeni?"

Mumy ta gyara murya, tana dubana cikin yanayi na nuna kulawa.

"Kinga kawarki Fatima, tana son ki zama yar gayu. Bakya ganin yayarki ai? Macce sai da gayu. Mazan ma sun fi son yaran da idonsu suka buɗe."

Sai na ji wani irin karsashi ya shige ni, zuciyata tana raya cewa gaskiya Mumy ta faɗa. Tunda a makaranta ma haka suke cemin, wai ni marar wayewa ce. Na ji kamar idan na bi shawarar Fatima, zan zama kamar sauran 'yan mata. A hankali na ji kwarin gwiwa ya fara shigata.

Mumy kuwa, tana hawa sama sai ta faɗawa Abba, "Abban Ramlah, ni dai ina da shawara. Yarinyar nan kadaina bata kuɗin kashewa kwata-kwata. Ya zama na ƙanƙane mata, ta ji daɗin wahala, shi zai sa ta ƙara nutsuwa."

Abba ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan yace, "Ai tun da, daman ina tunanin haka."

Na je gaishe shi, bai amsa ba, duk da yadda na riƙa ba shi haƙuri. Na ji zuciyata ta tsinke, duk da haka sai da na fito muka tafi makaranta da Malam Idi.

A makaranta, na yi niyya ba zan kula Fatima ba kwata-kwata. Amma sai ga ta tazo tana bani haƙuri, abin mamaki kuwa sai na ji na yarda da ita. "Ai Mumy ta ce min Fatima masoyiyata ce, tana so in zama cikakkiyar yar gayu," na raya a zuciyata, duk da cewa na san halayyarta ba ta da kyau.

Yinin ranar, sai tiktok kawai take yi a wayarta. Lokacin da aka fita break, sai na fara jin cewa hakan ma yana da kyau, duk da farko ban kula ba. Sai da aka tashi sannan ta sake bani haƙuri, na kalleta cikin rashin gamsuwa nace

"Kinsan masifar da kika janyo min gida kuwa?"

Ta fashe da dariya, tana cewa, "Au, har yanzu ba a daina miki faɗa ba? Lallai!" Na tsaya ina kallonta da mamaki, sai ta ce

"Gobe idan na zo, zamuje gidan malami. A rufe bakin iyayenki baki, su daina ce miki komai akan duk abin da kike yi. Ki huta da wannan faɗan!"

Na ji kamar an tsikare ni, zuciyata ta tsinke da tsoro. Fatima ta shige mota ta bar makaranta, ni kuma na zauna a bakin hanya ina mamakin maganar da ta faɗa. "Gidan malami? Rufe bakin iyaye? Wannan wani irin shiri ne haka?"

*******

Kafin ya ce komai, Haneefa ta kai hannunta ta shafi sumar kansa da laushi. Wani irin raɗaɗi da nishadi suka haɗu suka mamaye shi. Jikinsa ya yi sanyi gaba ɗaya. Idanunsa suka fara lumshewa tamkar yana jin daɗin abin da take yi.

Ta sunkuya a kan kunnensa, tana saukar masa da numfashi mai dumi.

"As’ad... Na san ba ka saba da wannan ba."

Sai ya ji zuciyarsa na rauni, jikinsa na narkewa, tamkar wani abu yana tasiri cikin zuciyarsa.

Haneefa ta ɗora kanta a ƙirjinsa, tana wasa da wuyan rigarsa.

"Kada ka kore ni, ranka ya daɗe... Na jima ina mafarkin wannan daren."

Maimakon ya yi magana, sai kawai ya lumshe ido, numfashinsa na fita a hankali.

Haneefa ta lura cewa tasirin maganin ya fara aiki. Ta yi murmushi mai cike da nasara, sannan ta ɗaga fuskarsa a hankali.

"Ranka ya daɗe, ina son ka..." Ta furta a hankali, tana shafa gefen fuskarsa.

As’ad ya yi ƙoƙarin faɗar wani abu, amma muryarsa ta yi rauni sosai. "Haneefa... ki... ki barni..."

Sai ta ɗaura yatsunta a leɓensa. "Shiii... Kada ka ce komai. Ni zan kula da kai."

Ta dinga murza hannunta akan ƙirjinsa, tana shafawa cikin salo na bariki. Jikinsa ya fara rawar sanyi, idanunsa sun sauya daga tsayayyen mutum zuwa tamkar wani marar ikon tsayayya.

Ta ɗaura kansa a cinyarta, tana murza gashinsa, sannan ta rafka masa wata dariya mai kashe zuciya.

"Ka bar komai a hannuna, mijina."

Kafin ya ce komai, sai ta yi wani irin motsin birgewa, ta ɗora hannunta a gadon bayan wuyansa, tana murzawa cikin sanyi.

As’ad ya runtse ido, yana jin tamkar wani zararre. Kowane motsinta yana narkar da jikinsa.

Kowane motsin Haneefa na narkar da shi. Yana jin tamkar an daure masa tunani, duk wata tsayayyar zuciya ta gushe. Yana jin tamkar bawan da aka rufe a keji.

Ta yi murmushi mai cike da mugunta, sannan ta kai bakinta kusa da kunnensa.

"Zan kasance da kai duk daren nan. Ko da ace ka kore ni, ba zan tafi ba."

Ta kai hannunta ta ɗan murza gemunsa, sannan ta sunkuya tana raɗa a kunnensa.

"Kai ne jarumi na... Yau zan nuna maka banbancin matan gida da 'yan bariki."

Kafin ya ankara, sai ta dinga girgiza jikinta a hankali kamar mai raɗaɗin zumudi, tana kwantar da kanta a ƙirjinsa. Numfashinsa ya yi nauyi, yana jin tamkar zuciyarsa zata tarwatse.

As’ad ya kasa magana, yana jin zuciyarsa na kuna da sha’awa marar misaltuwa. Sai ya ji wani abu a cikin zuciyarsa na ƙoƙarin bijirewa, amma yana jin raunin da ya gagara tsayayya. A wannan lokacin, Haneefa ta rungume shi sosai, tana lallaɓa shi kamar jariri.

Bayan ɗan lokaci, ya yi ƙoƙarin janye jikinsa, amma ta sake manne masa. Sai kawai ya daina ƙoƙarin tsayayya, yana jin wani irin yanayi na murmurɗiyar zuciya.

"Ni naki ne... Haneefa..." Ya furta cikin rauni, tamkar wanda aka kwashewa tunani.

Haneefa ta yi murmushi mai cike da farin ciki, ta dora kanta a ƙirjinsa, tana jin cewa burinta na fara cika.

Nana hadiza

09030569336ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA GOMA SHA HUDU

Na dawo daga makaranta cikin gajiya, na shiga gida a hankali, na ajiye jakata kusa da ƙofar palo. Cikin falon, na hango Mumy tare da kawayenta biyu, Anty Faiza da Anty Maryam, suna ta hira da dariya. Na tsaya a bakin ƙofa, zuciyata cike da gajiya.

Na sunkuyar da kai, na tsugunna cikin ladabi. "Ina yini Mumy, ina yini Anty Faiza, ina yini Anty Maryam."

Mumy ta daga kai tana kallona da wani kallo na rashin jin daɗi. "Ke kuma da kika dawo, ba za ki cire takalminki ba? Sai ki shigo da datti?"

Na ɗan ja numfashi, na sunkuyar da kai cikin jin nauyi. "Yi haƙuri, Mumy."

Anty Faiza ta saki murmushi tana cewa, "Ba komai, Ramlah. Yarinya ce ai."

Mumy ta ja tsaki, ta ci gaba da hirarta. Na miƙe a hankali, na nufi dakina, zuciyata cike da damuwa. Me yasa Mumy ke yi min haka?

Ina shiga daki, sai na hango Yaya Billy kwance a kan gadona, tana latsa waya. Na tsaya daga bakin ƙofa ina kallonta cikin mamaki.

Ta ɗago kai, ta saki murmushi mai rauni. "Sannu da dawowa, Ramlah. Ya makaranta?"

Na dan ja numfashi, na yi murmushi na karya. "Alhamdulillah."

Ta gyara kwanciyarta tana dariya. "Gadonki ya fi nawa dadi, shi yasa na kwanta anan. Kin dawo daga makaranta kenan?"

Na gyada kai, zuciyata cike da al'ajabi. "Eh, na dawo."

Ta ɗan yi dariya. "Dazu na yi milkshake, na ajiye miki naki a cikin fridge."

Na ɗan tsuke fuska cikin wasa. "Ke kika yi milkshake? Yaya Billy, yau ke kika yi aiki kuwa?"

Ta kalle ni da idanuwa tana dariya. "Eh mana! Ai jiki na ciwo, amma na tashi nayi."

Na yi murmushi mai rauni, amma zuciyata tana cike da shakku. Me yasa Yaya Billy ke nuna kulawa haka yau? Na san dai a baya bata cika taimakawa ba.

Ina cikin wannan tunani, sai ga Mumy ta turo ƙofa ta shigo cikin hanzari. Ta daka Yaya Billy da harara. "Ke kuma Billy! Yanzu ba za ki taimaka ba? Ko sai ke da Ramlah ne ku zauna babu aikin yi?"

Yaya Billy ta tashi daga gadon cikin shagwaba. "Ai jiki na ciwo, Mumy."

Na yi saurin miƙewa cikin ladabi. "Mumy, zan taimaka."

Ta kalle ni da wani irin kallo mai cike da tsana. "Ke kuma da kika zo kika zauna, haihuwata kika yi da zan dafa miki abinci? Mara kunya! Kirji ba komai amma jin ki kike daidai da kowa?"

Na ji wani abu ya tsinke a zuciyata. Kafin na yi magana, sai kawai na ji mari ya sauka a kumatuna. Na ja da baya cikin tsoro, na yi ƙasa da kai, hawaye na neman kwacewa.

Mumy ta daka min tsawa. "Ni ce uwarki da za ki tsaya kina kallona haka? Ki shiga ki dafa mana tuwo! Asararriya mara tarbiyya!"

Na sunkuyar da kai cikin jin kunya da raɗaɗi, na kasa cewa komai. Yaya Billy ta kalle ni tana murmusawa da tausayawa, amma na san a zuciyata dadi takeji.

Na yi ƙoƙarin mayar da hankali kan littafina, amma duk lokacin da na taɓa kumatuna, zan ji ciwon marin da ta yi min. Hawaye suka cika idanuwana, zuciyata tana ƙoƙarin fashewa. Me yasa Mumy za ta mare ni haka? Shin na yi mata wani babban laifi ne da ban sani ba?

Na kalli milkshake ɗin da Yaya Billy ta kawo min, yana nan a gefen gado, amma zuciyata ta kasa karɓar cewa Yaya Billy ta yi wannan wahala don ni. Ko dai akwai wani abu a ciki?

Na ji tamkar dakina ya yi min zafi, don haka na fita farfajiyar gidan, na zauna a karkashin bishiya, ina duba littafana da wayata. Amma babu kati, babu kudi. Na zauna cikin damuwa, ina tunanin yadda zan yi.

Bayan na gama aikin kicin, na fito tsakar gida ina duba littafina, amma hankalina a tashe yake. Cikin wannan yanayi, sai na ji sallama daga bakin kofa.

"Assalamu alaikum."

Na dago kai cikin mamaki, sai naga Khalil tsaye yana murmushi. Ya naɗe hannuwansa bisa kirjinsa, yana kallona da wata fuska mai kulawa.

"Wa'alaikumus salam," na amsa cikin sanyi.

Ya zauna kusa da ni. "Ramlah, lafiya kuwa? Kamar kina cikin damuwa."

Na kauda kaina gefe. "Babu komai."

Ya girgiza kai, yana dubana da kulawa. "Me ke damunki? Makaranta ce ta wahalar da ke?"

Na saki murmushi mai rauni. "Ba komai, kawai na gaji ne."

Khalil ya kai hannu ya kama nawa, yana kallona da idanu masu cike da tausayawa. "Ba zan gaji da faranta miki rai ba. Kin sani."

Na sunkuyar da kai, ina jin wani irin sanyi a zuciyata. Khalil mutum ne mai kirki, amma ban taba sanar da shi matsalata ba.

Muryar Yaya Billy ta katse hirarmu. "Auta, ga nakinki cuppino."

Na juya, sai naga ta aje kofin a gabana tana murmushi. "Nagode, Yaya Billy."

Khalil ya kalle ni. "Wannan fa?"

"Cuppino ne, Yaya Billy ta yi."

Ya miƙa hannu zai ɗauka. "Ni zan sha."

Na yi saurin riƙe hannunsa. "A'a, Khalil. Bari na kawo maka wani."

Ya yi murmushi. "Kin san ina son komai daga hannunki."

Na kasa faɗa masa gaskiya. Na bar shi ya ɗauka, zuciyata tana tsalle kamar zata fado daga kirjina.

Ina tsaka da zama a bakin kujera, ina jin yadda zuciyata ke bugawa da sauri. Tun da Khalil ya tafi, ban samu natsuwa ba. Me zai faru idan cuppino din da Yaya Billy ta yi yana da matsala? Me yasa ta dage na sha, duk da ta san ban saba da irin wannan abin sha ba?

Kawai sai na ji nayi ya billy tace. "Auta, kin sha kuwa?"

Na yi saurin juyowa. "Eh, na sha Yaya Billy."

Ta kalle ni tana murmushi, sannan tace, "Kin ga, bacci nake ji wallahi." Ta sake dariya sosai, kamar yadda ba ta saba yi ba.

Na dan rike hannuna cikin damuwa. "Me ya sa kike dariya haka?"

Ta harare ni tana dariyar nan da ke cike da gulma. "Wai ni yar kauye ce ko? Ba na saba da irin wannan ba."

Na saki murmushi na karya, sannan na ce, "A'a, ba haka nake nufi ba."

Ta gyada kai.

Ina zaune ina daddanna wayata cikin sanyin jiki, sai na jiyo muryar Abba daga waje. Ya amsa sallama cikin gajiya. Na yi saurin gyara zama, na sunkuyar da kaina.

Yaya Billy ta mike cikin sauri tana gaishe shi. "Abba sannu da dawowa."

Abba ya amsa a hankali yana kallonta da kulawa. Amma ni kuwa ko motsi ban yi ba. Sai naji zuciyata ta kara tsananta bugawa.

Momy ta fito daga daki tana gyara mayafinta. "Abba, yau ka dawo da wuri."

Abba ya gyada kai, ya zauna a kujerar roba mai lankwasa. "Eh, aikin ya kare da wuri."

Na yi kasa da kai, ina kokarin guje wa idon Abba. Amma duk da haka, na san zai lura da ni.

Momy ta ja kujera ta zauna kusa da shi, tana kallona daga sama har kasa. "Abba, kayi haƙuri, amma gaskiya ne sai ka raba Auta da Khalil. Kamar yadda kayi a baya. Ba mu so ya rika hure mata kunne."

Abba ya ɗago kai yana kallon momy da mamaki. "Me ya faru kuma?"

Momy ta ja tsaki. "Ka san fa Khalil yana son Ramlah tun suna yara. Yanzu har ya fara zuwar mana gida, yana neman lalata tarbiyarta."

Na dago da sauri, idona cike da kwalla. "Momy, wallahi ba haka bane..."

"Yi shiru!" Abba ya katse ni da tsawa. "Kina musun abin da momynki ke fada? Na ce ki tsuke bakin ki!"

Na yi saurin rufe bakina, hawaye na sauka bisa kuncina.

Abba ya kalle ni cikin fushi. "Na kara ganin ki da wannan yaron, wallahi sai na ci ubanki. Bazaki sakamun ciwo ba!"

Na ji zuciyata na tsananta bugawa, hawaye na gangarowa kamar an bude famfo. Baki na na rawa, amma ba zan iya cewa komai ba.

Momy tace . " Hakan Yayi dai dai Abba, kai hakuri. Auta zata gyara halinta."

Abba ya girgiza kai. "Ai dama na ce, na kara ganinta da shi, saina karya lagonta. Ke Ramlah, tashi ki bani wuri!"

Na mike cikin sauri, na rasa inda zan sa kaina. Yaya Billy ta saki wani murmushi da bai kai fuska ba, tana cewa, "Auta, kin ji ko?"

Na fita daga falon da sauri, ina jin yadda zuciyata ke wani irin zogi. Na samu waje kusa da kofar daki na zauna, na jingina da bango, na ci gaba da kuka.

Na dafe kaina ina kuka a hankali, domin kada su ji. Duk lokacin da Abba ya nuna fushi, zuciyata tana karyewa. Ba don komai ba, sai don na san cewa ba zan iya kare kaina ba.

Me yasa ake kallon Khalil kamar wani mai lalata tarbiyar mutane? Khalil dai bai taba cewa mun komai ba sai na kirki. Shi ne kawai wanda yake kokarin faranta mun rai, amma ga shi yanzu, ana ganin laifi ne ma ya gaishe ni.

Na daga kaina, na kalli kofar falon. Sai na ji muryar Abba yana cewa, "Wallahi Yalwa, idan har kika bari wannan yaron ya ci gaba da zuwar mun gida, saina dauki mataki. Ni ba zan dauki wannan rainin hankali ba." Ashe abba yakira Maman khalil ce yana mata maganganun nan.Na ji momy tana cewa, "Yanzu haka, sai dai mu kara tsaurara mata, ko da yana nufin raba su gaba daya."

Yaya Billy ta kara cewa, "Ai kuwa hakan yafi."

Na tsinci kaina cikin kuka mai karfi, ban iya daurewa ba. Ji nake tamkar ana tsaga zuciyata da wuka. Muryar Yaya Billy tana dariya cikin radadi ya kara rikita ni.

Sai kawai na mike cikin rawar jiki, na koma cikin dakina, na fada bisa gadona ina ta kuka. Na rufe kaina da filo, ina jin yadda kalaman Abba da momy ke ci gaba da dokar zuciyata. Me yasa ake mun haka? Me yasa ba wanda yake fahimta ta yanzu kullum ciƙin laifi nake?

Bayan wani lokaci, na tashi daga gado. Na ji yunwa tana damuna, amma bana jin wani abu zai shiga cikina. Duk lokacin da aka yi mun fada haka, na kan rasa sha’awar cin abinci. Na tsuguna a bakin gado, na jingina da bango ina ta tunani.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull