Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 10

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 10

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 10: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 10. ........Shahidah ta kira Ammie ta…

4,401 words

........Shahidah ta kira Ammie ta sanar mata da komai game da abinda RK yazo ma Maanal da shi. A mamakin Shahidah sai ji tai Ammie na maimaita kalmar Alhamdullah. Kasa daurewa tai ta ce, “Ammie kin amince kenan kema tayi aikin?”. “Sosai kuwa Shahidah. Dan wannan wata mafita ce da masalaha UBANGIJI ya kawo mana. Ban sanar daku bane kawai amma tunda muka baro Abuja na dawo gidan nan a cikin cakwakiya ake da tashin hankali duk kuma akan batun auren Maanal da Yazeed ne. Namayi mamaki da kikace yau kusan kwana biyar bai leƙoku ba tunda yana Abujar shima.” “Wlhy kuwa bai zoba Ammie, nama zata ko yana Kaduna ko yayi tafiya ne wani waje. Amma naga yana ƙoƙarin kiranta a waya yaji lafiyarta. Wai Ammie miya faru ko ɗaura musu aure kukai? Ko har yanzu Mamma ɗin ce ke tijarar bata son?”. Ƴar dariya Ammien tayi da faɗin, “Kefa daɗina dake shirme Shahidah. Auren lafiya kuma yarinyata na a wannan halin na ciwo mai girma irin wannan hauka nake zan bari a mata aure bada amincewarta ba. Akan dai Hajiya Yaya ne da batun auren......” Tsaf Ammie ta zayyanema Shahidah yanda komai ya faru da kuma matsayar da ake akai yanzu. “Kai wannan mata ALLAH ya rabamu da masifarta Ammie. Ita dai ta sani mu ALLAH yasa haka shine mafi alkairi ma, dan wlhy garama ta auri Rafeeq ɗin amma haɗata kishi da wannan ƴar iskar yarinyar sangartacciya ai wani hatsarinne. Zasu iya haɗe kai su dinga cutar da ita watarana mu wayi gari zuciyar tata ta buga. Amma kinga Rafeeq ɗin nan wlhy Ammie yana da hankali da tarbiyya. Damma Maanal ɗin ce taƙi sakin jiki da shi kin dai san halinta”. “Karki damu a hankali ne. Kudai ku cigaba da tayata da addu'a. Watarana ai sai labari. Amma in sha ALLAHU batun Yazeed kam nima bana mata fatansa kuma suje can su ƙarata. Yanzu ki bani zuwa gobe zan yi magana da Daddyn naku, idan ya tirje sai shi mijin naki ya masa magana ko naje Zaria na haɗashi da abokin nasa.” “Shike nan ma Ammie wlhy dama haka kikayi”. “A'a bari dai na fara masa magana dan bana son butsutsunsa. Yaya jikin autar?”. “Alhamdullahi Ammie jikinta na ƙyau sosai. Dan naga har ta koma karance-karance novels ɗin nata na fama. Gata can ma tana shiri Abban Barru yace idan ya dawo zai kaita bookstore ta samo wasu”. “To Masha ALLAH, ALLAH ya ƙara lafiya. Nima zan shigo na sake ganinta in sha ALLAHU zuwa next week haka komai ya ƙara lafawa.” “ALLAH ya kaimu Ammie muna nan muna jiranki. Itama Amal tace next week zata dawo”. “To shike nan idan naga zai mana dai-dai sai kawai mu taho tare, amma ni ranar zan dawo gaskiya”. “Kai Ammie miyasa bazaki kwana ba?”. “Daga dubiya sai kawai na kama kwana. Tunda ina jinku kullum a waya ai Alhmdllh ya wadatar, ba kuma sai na zauna na kula da tsohon mijina ba da ƙananun ƴaƴana”. Dariya sosai Shahidah ta sanya. Daga haka sukai sallama....

___________★

Kamar yanda Ammie taima Shahidah alƙawari ta tunkari Daddy da batun aikin Maanal. Sai dai kuma kamar fa yanda tai tunani ya nuna ɓacin ransa. Ya kuma tujareta da masifa dan dama yana riƙe da takaicinsu ita da Hajiya Basariyya a rai. Kasa magana Ammie tai sai duƙar da kanta kawai tai tana saurarensa. Sai da yay mai isarsa yay shiru dan kansa sannan ta tashi ta kwanta dan dama itace da shi a yau ɗin. Wasu irin hawaye ne masu zafi suka dinga rige-rigen sakko mata. Sosai tausayin kanta dana iyalanta ke ƙara girma a zuciyarta. A rayuwarta tayi farin ciki ne da samun ƴancin kai na shekarun ƙuruciya kawai. Amma tun daga randa aka lulluɓa mata zanen aure zata iya cewa daga lokacin ƘADDARARTA ta fara. Daga lokacin ta fara tantance gatan iyaye da ɗacin rabuwa da su. Daga lokacin komai ya canja, sunanta na Asiya sarauniya ya canja zuwa Asiya baiwa. Eh dole tace bauta, duk da a zahiri baza'a kalli rayuwar tata ata mai bauta ba kasancewar wasu abubuwa sun mata ado a bayyane. Sai dai wanda yasan ainahinta ne kawai zai san minene mizanin bautar da take magana da ƴancin kai. Ansha gwagwarmaya na tsawon shekaru kafin ALLAH ya iyakance, iyakancewar bai zama sauƙi ba kai tsaye, wata sabuwar jarabawar aka sake shiga, ta yanda zaren ƙaddarar ne ya kawota a wannan matsayin da take a yanzu kuma. Bazatai butulci ma UBANGIJI ba, domin kuwa Alhamdullah, ta samu canje-canje masu yawan gaske a sabuwar rayuwarta, sai dai anan ɗin ma ta gamu da wata jarabawar rayuwa a cikin mugayen kishiyoyi da kansu kawai suka sani...... “Asia! Kuka kike yi?”. Furucin Daddy ya katse mata tunaninta. Da sauri ta saka hannu cikin dabara ta share hawayenta, sannan ta juyo garesa fuskarta da murmushi. “A'a Daddyn Hameed wane irin kuka kuma. Kawai dai na kwanta ne”. “Humm Asia kenan, nasan kuka kike, kina kuka saboda kina ganin kamar na tauye hakkin ki dana ƴaƴank.....” “Ya arrahaman”. Ta faɗa da sauri tana mai gaggawar ɗaura tafin hannunta a saman bakinsa. Zuuuu hawayen da take riƙewa suka shiga zirarowa. Kanta ta fara girgiza masa da sakin kukan gaba ɗaya. “Dan ALLAH kada kace haka Daddyn Hameed, ban taɓa raba ɗayan biyu a tsakanin su Maanal da sauran yaranka ba. Ni kaina inama mantawa bakai ka haifesu ba, saboda kana musu dukkan abinda uba kema ƴaƴa. Kana musu abinda mahaifinsu ya gagara musu. Taya zan kasance butulu waje rarrabe gaskiya da akasinta. Dan ALLAH ka gafarceni idan nayi kuskure, wlhy ban nema amincewarka ga Maanal tayi aiki dan baƙanta maka rai ba ko ƙasƙantar da dokar ka b.....” “Shiiiii!! Ya isa kukan haka to”. Daddy ya faɗa yana mai jawota jikinsa ya rungume murmushi shimfiɗe a fuskarsa. A hankali yake shafa bayanta cike da lallashi. Tsahon minti ɗaya kafin ya furta, “Nasani Asia. Na kuma yarda dake ɗari bisa ɗari. Domin nasha gwadaki akan yaran nan batare da kin sani ba ke kanki kuma kina cinye jarabawar. Babu abinda zance dake sai godiya. Domin tabbas a cikin matana kina gaba a wadda nake alfahari da ita. Bance miki suma sauran sun gaza ba ko basu da martabar da nake kallonsu da ita ba. A'a ku dukanku kowa da inda yake tausasa min da kuma inda yake tsaurara min, amma kina da manyan lambar yabo kashi-kashi a gareni da bazasu lissafu ba Asia. Hakama su Shahidah, ni kaina biyayyarsu a gareni da girmamawa yakan sani manta ma bani na haifesu ba, ina jin alfahari da su, ina kuma godema ALLAH daya bani su matsayin ƴaƴana a yanzu. Ba aiki bane bana son Maanal tayi, domin nima na fahimci hakan zai taimaka mata ya ɗauke mata kewa musamman da nima nasan harkar zane-zane hubby nata ne. Kawai dai ina jin haushinki ne da tunanin baki son haɗa jini dani, shiyyasa yau ba fanshe haushin ta nan, sai nake ganin kamar baki son wannan haɗin da nake sonyi ne Asia. Alhalin ni kuma na ƙwaɗaitu ƙwarai da gaske da son ganin jinina ya sake gauraya da naki kozan cigaba da samun nagartattun zuria daga tsatsonki a cikin zuri'ata. Hakan zai sake dunƙulemu ya curemu waje guda. Tun akan Amal naso nayi wannan haɗin, sai na fahimci hankalin Yazeed akan Maanal yake shiyyasa na ƙwallafa raina a kanta.” “Kayi haƙuri Daddyn Hameed sam ba haka bane kamar yanda kake tunani. Ka fahimceni dan ALLAH. Wlhy koda bana aurenka zan iya bama Yazeed auren Maanal. Domin ya taimakemu a gaɓar da muke matuƙar bukatar taimako. Zanma iya cewa ALLAH ya ƙaddara Manaal nada sauran kwana ne a duniya amma ya saka sanadin hakan a hannun Yazeed. Domin da ace kwannata ya ƙare tun a randa muka fara haɗuwa da sai dai wani zancen ake ba wannan ba. Dan haka ban taɓa jin bazan bama Yazeed Maanal ba. Kawai dai hankalina na matuƙar tashi kasancewar bakowane ɓangare bane ke buƙatar wannan haɗin, hakan kuma zai iya cutar da Yazeed ɗin kansa da ita kuma Maanal ɗin dake fama da rauni irin na ciwo mai haɗari. Amma yanzu masalahar da aka samu zai taimaka komai ya zama dai-dai itama ta samu sassauci haka shima Yazeed ɗin. Dan koba komai Hajiya Yaya mahaifiyace tana da tata darajar. Sannan Yazeed ya san komai daya shafi rayuwar Maanal, basai anyi sabon zama da zagaye-zagayen faɗa masa da fargabar zai amsheta ko zai canja ra'ayi” “Hakane Asia. Na kuma fahimceki yanzu ɗari bisa ɗari. Zan kuma cigaba da addu'ar zaɓin ALLAH akan al'amarin insha ALLAHU. Sannan abinda ya shafeta ki daina wani damun a kansa kanki ai ƙaddara ce, bata wuce kan kowa ba kuma, ALLAH kuma shine shaida bataje takai kanta ba domin yin hakan jarabawace, wanda ma suke aikatawa kai tsaye ko suke zuwa bariki su kama ɗakin kansu suke auruwa cikin salama da kwanciyar hankali yanzu a ƙasar nan balle ita. Saboda haka na amince Maanal tayi aikinta. ALLAH ya sanya albarka ya kuma sa hakane yafi alkairi.” Wani irin daɗi ne ya ratsa zuciyar Ammie. Ta ƙanƙame Daddy da ƙyau tana amsawa da amin. Shima murmushi ya saki mai faɗin gaske da karɓarta sosai ya rungume. A ransa kuwa yana sake ganin fara aikin Maanal ɗin wata masalaha ce. Dan zai fake da shi bayan anyi auren suyi zamansu acan, ita kuma wannan zaɓin uwar Yazeed ɗin anan cikin gidan yake son ta zauna tare da su saboda wasu dalilansa......

Tofa, mi kuke tunanin wai ya faru da Maanal ne?🥺. Sannan zamuga yanda wannan cakwakiya zata ƙare😂🏃.

__________★

Wani irin farin ciki ne ya mamaye Maanal lokacin da saƙon Daddy ya risketa akan amincewarsa tayi aiki. Su kansu su Shahidah sai da suka tsaya suna kallonta ganin yanda taketa murmushi yau kamar ba Maanal ba. Sai suma hakan ya sakasu a farin ciki. A karo na farko na tarihi Maanal taima RK text massage da albishir ɗin amincewar Daddy. Ai ba'a haɗa awa guda ba sai ga bawan ALLAH a gidan. Yau ko lallaɓatan da Shahidah keyi na taje ta samu RK ɗin ba'ai ba. Yana kiranta yace gashi a gidan sai gata babu jimawa ta fita. Tunda ta fito ya zuba mata ido, sai ya zam tana takune tamkar da bugawar zuciyarsa. ALLAH ya jarabcesa da son wannan halittar ƙwarai da gaske. Yana kuma fatan mallakarta in har hakan shine alkairi a garesu. Maanal ta tsani kallo, dan haka sai da ta masa tsogumi akan kallon ƙurillar da yake matan. Baice komai ba face basarwa yana sakin murmushi. Itama sai ta sharesa kawai ta shiga gaishesa. Ya amsa mata da kulawa, kafin ya ɗora da tambayar yanda abubuwa suka kasance. A taƙaice ta faɗa masa, bai damu ba dan ya gama karantar ta zuwa yanzu. Bata da son yin doguwar magana sai idan itace taso hakan da kanta. Shine ya dinga zuba mata zance da yanda abubuwa zasu kasance. Ya kuma tabbatar mata nan da kwana biyu zaizo ya amshi takardunta. Ya kuma buƙaci ta ɗan zazzana wasu samples na agogunan zaizo ya amsa gobe idan ALLAH ya kaimu dan zai sake nunama mai Companyn. Duk da dai ya nuna masa wanda ta zana a asibiti. Ta tabbatar masa babu damuwa zatayi ɗin, daga haka sukai sallama ya fice ita kuma ta shiga gida. Kamar ko yanda sukai alƙawari a wannan daren ta nutsu ta zana agoguna masu shegen ƙyau da ɗaukar hankali fin kala goma. Dan har gabannin asuba tana wannan aikin. Hakan ya saka mata makara. Tana yin sallar asubahi kuma ta sake kwanciya. Bata farka ba sai ɗaya saura. Ta samu RK yazo ya amshi zanen ma. Dan sun sanar masa tana barci yace kada a tasheta a barta tai barcinta, a bashi zanen kawai. Yana kuwa amsa bai jima ba ya wuce abinsa. Sai da ta tashi take jin yazo ɗin ya amsa. Har ta ɗauka waya kamar zata kirashi sai kuma dai ta fasa kawai. Tata tsumayen nasa kiran amma shima sai bai kira ɗin ba har dare. Sai da tana shirin kwanciya ne ma saƙonsa ya shigo. _“Ina Kaduna yanzu haka. Mun gana da Daddy da Ammie, na kuma amso takardunki suna hannuna. Amma sai da safe zan dawo Abuja in sha ALLAHU. Kiyi barci cikin aminci tare da mafarki mai nutsuwa gimbiyar mata”_. Baki kawai ta taɓe tare da jefa wayar saman gado ta cigaba da saka maɓallan rigar barcinta. Sai kuma ta tsaya cak kalamansa na dawo mata. Ya gana da Daddy da Ammie kamar yaya? Kai itafa shishshigin mutum nan ya fara bata tsoro. Kaji bala'i ko mi ya kaisa Kaduna?. Rashin mai bata amsa ya sakata jan ƙaramin tsaki ta haye gadon kawai ta kwanta. Addu'a tayi kamar yanda ta saba sannan ta kashe wutar ɗakin tana sauke ajiyar zuciya.........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖2️⃣1️⃣

.......Maanal bata sake jin labarin RK ba tun ranar. Ya dai kirata washe gari yace ya dawo Abuja. Daga haka bata sake jinsa ba. Gashi ita kuma ta ƙagu taji yaya ake ciki. Dan haka kawai sai ta ƙwallafa ranta a aikin saboda zaman waje ɗayan kuma ya isheta. Da yaran Shahidah sun wuce makaranta itama da mijinta duk aiki suke fita, sai ita sai mai aiki kawai. Bata da aiki sai karatun novels da kwanciya. Amma kasancewarta sarkin kamewa da dakiya sai bazaka taɓa fahimtar hakan ba kai tsaye. Sati ɗaya dayin hakan sai ga Ammie da Amal sunzo. Matuƙar farin ciki Maanal ta kasance a wannan ranar, gashi weekend ne duk masu gidan suna nan. Yini sukai dan Ammie tace bazata kwana ba. Babu irin shagwaɓar da Maanal bataima Ammie akan ta kwana ɗin ba amma tace sam ita bata sanarma Daddy zata kwana ba. Haka babu yanda zasuyi bayan magrib suka rakasu train station kasancewar jirgin ƙasan zasu bi. Dama a cikinsa suka zo....

Kwanakin su Ammie biyar da zuwa da daddare tana shirin kwanciya sai ga kiran RK. Ido kawai ta sakama wayar tana kallo harta tsinke sannan ta kauda kanta. Sake kira akayi nan ma kamar bazata ɗauka ba sai kuma dai mita tuna oho mata tai yunƙurin ɗaukar, sai kuma taga bashi ɗin bane Ya Yazeed ne. Fuska ta ɓata shima kamar bazata ɗaga ba ta dai daure ta ɗauka. Gaisheshi ta farayi da girmamawa kamar yanda ta saba. Shi kuma ya amsa mata cikin nutsatstsiyar muryarsa dake nuna alamar a kwance yake. Sun ɗan yi shiru sai kuma ya katse shirun da faɗin, “Ina muka kwana akan batunmu Maanal?”. Shiru tai kamar bazatace komai ba. Sai da ta mula dan kanta ta amsa masa da, “Yaya ni mikake son nace to. Ni duk abinda su Daddy suka yanke zanyi biyayya a kansa kawai”. “Saboda dama baki sona?”. “Ni dai Yaya bance ba. Amma ka tausaya mun mana. In dai kai namiji ka haƙura ka musu biyayya ni kuma sai naje nace ba haka ba.” “Humm shike nan, amma ke yanzu baki jin kishin na fara auren wata kafin ke?”. Karan farko ta saki murmushi mai faɗi, sai kuma ta zame ta kwanta. “Yaya ko naji kishi yaya zanyi. Ni dan ALLAH mubar ma maganar nan kawai ALLAH yasa haka shine yafi alkairi”. Murmushi taji ya saki da ga can, sai kuma ya ce, “Okay shike nan an barta. Tunda dai na gane ana kishina na gode”. Shiru ta masa batace komai ba. Shima daga haka yay mata sallama akan maybe gobe ma ya shigo Abujan, zai kuma leƙo ya fara ganinta kafin ya fara sabgoginsa. Daga haka sukai sallama. Kamar jira RK yake dama, Yazeed yana yankewa kiransa na shigowa shi kuma. Sai yanzu ma ta lura ya mata kira yafi goma ashe sanda take wayar. Kanta kawai ta ɗan girgiza. Sai da tana gab da zata tsinke sannan ta ɗaga. Muryarsa a cinkushe ya mata sallama. Amsawa tai itama ciki-cikin tai shiru. Tsahon minti ɗaya babu wanda ya sake magana. “Oh bama zaki gaisheni ba?”. RK ɗin ya faɗa daga can. Yitai kamar bazata tanka masa ba sai kuma ta ce, “Good evening”. “Humm good evening to baturiya. Fatan kin yini lafiya?”. “Lau”. Itama ta amsa masa a daƙile jin yana mata magana cikin wani ji da kai. “Humm! saboda kina waya da wannan tsohon tuzurun saurayin naki da baya dariya shine kika shareni.” Ita dariya ma zancen nasa ya bata. Amma sai bata dara ɗin ba ta ce, “Hummm ashe kaima tsohon tuzurun ne tunda ba girmarka yay ba”. “Oh zaki shigar masa faɗan ne kenan?”. Shiru ta masa taƙi tankawa. Shima sai ya saki zancen kawai. Amma ransa fal kishin Yazeed ɗin. “Baki da kirki ALLAH, kwana kusan goma baki jini ba amma baki neman ba. Wannan wace irin soyayya ce?”. “Kai dai ka sani. Rashin jinka kuma ai nasan lafiya ce ke ɓuya”. “Humm borin kunya, ALLAH dai ya shirya min ke. Duk da baki tambaya ba bara na faɗa miki. Auntyna ce bata da lafiya a randa na dawo Kaduna da yamma jikin ya tsananta, dole mukai gaggawar barin ƙasar da ita. Tashin hankali yasani manta wayar da number ɗinki ke ciki. Jiyan nan muke dawowa”. A hankali Maanal ta sauke numfashi da faɗin, “ALLAH sarki, ALLAH ya bata lafiya yasa kaffara ne. A wace anguwa take?”. “Amin ya rabbi nagode sosai. Zakije dubata ne kike tambayar anguwarsu?”. “Ina ruwanka to. Kai dai ka faɗa min mana”. Murmushi yayi daga can har tana iya jin fitar sautinsa. Sai kuma ya ce, “Okay ba damuwa zan tura miki address ɗin. Sai dai kuma yanzu ma na kiraki ne akan batun aikin can. Sun buƙaci ganinki, sai ki shirya gobe idan ALLAH ya kaimu kamar around eleven thirty haka zanzo na ɗaukeki”. Wani irin sanyi ne ya tsargama Maanal. Amma sai ta danne cikin dakewarta ta ce, “Miyyasa bazaka bani address ɗin ba kawai naje da kaina”. “Kina tsoron na saida ki ne?”. “Ai nasan nafi ƙarfin siyarwa”. “Hhhh haka dai kikace. Bari na barki ki kwanta lokacin barcinki na wucewa. Sai nazo”. Daga haka ya yanke kiran kafin tace komai. Murmushi ta saki itama, ta jima da fahimtar bayan naci RK ɗan rigima ne na bugawa a jarida. Sam daga ganinsa baya jin magana. Bazatace tana sonshi ba. Amma wasu abubuwa nashi sun ɗan fara birgeta kaɗan. Fasa kwanciyar tayi, ta tashi ta ɗauro alwala ta hau nafilfilin neman nasara da zaɓin alkairi akan wannan aiki. Duk da dai dama tunda aka tsira zancen taketa gayama ALLAH. Tayi raka'a biyun farko ta sallame ta ɗauki wayarta ta turama Ammie text. Tasanta bata wasa da ƙiyamullaili, kusan za'ace ma ita suka gado dan tun suna yara tai musu wannan horon na ibada. Kuma Alhamdullah su dukansu sun horu da wannan tarbiyyar tata. Dama itace mai ɗan raunin cikinsu lokacin tana a ganiyar rashin ji. Amma yanzu Alhamdullah kam komai ya sauya kamar yanda jiyanta ta zama tarihi mai ciwo da raɗaɗin tunawa agareta.....

*_WASHE GARI_*

Da safe ta sanarma Shahidah da mijinta komai. Sun tayata murna da fatan alkairi suma. Ta kumayi waya da Ammie da Daddy dan itace da shi jiya da yau. Hakama Amal. Bayan wucewar su Shahidah nasu ayyukan itama tai nata shirin. Kasancewar ta mai jinkirin shiri yasa ten nayi ta fara shirin nata. Sai ya zam kafin eleven ma tayi ta gama komai duk dama bawani shiri bane na'azo a gani. Amma tayi ƙyau sosai cikin Abaya ƙirar saudia baƙa. Daga ciki ta saka wandon jeans blue mai duhu da farar riga datai mata ƙyau. Ɗan kwalin abayar kawai tai rolling a kanta ta saka turare mara ƙarfi bayan na wuta da kayanta keyi dama jikinta gaba ɗaya da yuni gyara yasa ƙamshi ya kama. Sai ƴan tarkacenta data haɗa a hand bag ɗinta sannan ta fito. Kitchen ta shiga ta saka ruwa a ƙyaƙyƙyawar bottle water ɗinta ƴar zamani sai ta ɗan saka Linda ta daka mata snacks da basa rabo da shi a gidan kaɗan wai ko taji yunwa. Dan ta tsani sayen abincin waje a rayuwarta. Shiyyasa da wahala kaga Maanal ta fita anguwar data san zata yini babu wani abin ci a tare da ita. Tun Ammie na faɗa har ta saka mata ido ma. Falo ta dawo ta zauna kasancewar akwai sauran mintuna ashirin, sai kawai ta buɗe novel ɗinta ta cigaba da dubawa. Tanayi tana ɗan cin shawarma ɗinta guda ɗaya data ɗakko da drink a kofi. Batafi mintuna goma a wajen ba kira ya shigo wayarta. Ƙaramin tsaki taja a ranta tana addu'ar ALLAH yada ba Yazeed bane ba. Numfashi ta ɗan sauke ganin RK ne. Sai da ta kalla agogo sannan ta ɗaga. Yau dai bai roƙaba ta gaishesa. Sai shi kuma batare daya amsa ba yace ta fito gashi a waje. Sake kallon agogo tayi da mamaki ta ce, “Akwai fa sauran ten minutes”. “Oh kona koma sai ya cika na dawo?”. “Humm”. Ta faɗa kawai tana yanke wayar. Linda ta ƙwalama kira. Da sauri sai gata tana faɗin, “Yes Aunty kina bukatar wani abu ne?”. “No Linda zan wuce ne dai. Dan ALLAH ki kula sosai da gidan duk da dai nasan kina ƙoƙari dama. Ai baki manta ba dai Didi tace kima Uncle tuwon shinkafa ko?”. “Eh aunty ban manta ba har ma na ɗora”. “Yauwa to yayi, sai su Barrah kuma kisaka musu white rise kin san bazasu ci tuwon nan ba. Tunda akwai stew a fright kema kin huta kenan. Nima na wuce sai na dawo”. “To aunty, ALLAH yasa ayi nasara. Amma ke baza'a miki komai ba?”. “No Linda na huttashsheki kinji, bamma san ni sanda zan dawoba. Komai na dawo na samu a gidan zanci bye”. “Okay bye bye”.

Tunda ta fito ya wani zuba mata idanu ko ƙyaftawa bayayi kamar yanda ya saba. Bashi kaɗai ba kowa na faɗa a zuciya ko'a fili Maanal ƴar gayu ce gata kuma ƙyaƙyƙyawa. Ko bada kwalliya ta saka kaya ba zakaga sun mata ƙyau. Balle kuma ace tayi kwalliyar ai abin sai wanda ya gani. Gata dai ba fara ba, amma da wahala namiji ya kalleta bai sake mata kallo na biyu ba duk ustazancinsa da kamewa. Badan tafi sauran mata ƙyawu ko wani abu ba, a'a itama kamar kowacce mace take, kuma komai nata irin na kowacce mace ne. Sai dai yanayinta na kamewa da ɗaure fuska kan taka musu birki wajen yimata magana ko fuskantarta kai tsaye. Sam bata da sakewa da mutane, sannan bata da yawan fara'a ko magana sai a inda taso yi ko ga wanda taso yimawa.... Sai da ta tsaya a gabansa ta ɗan yamutse fuskarta da babu walwala sam. Dan bata son kallo sam, ko yaya ake kallonta takan tsargu taji a jikinta, shi kuma taka kallo ɗabi'arsa ce. Yanda take faman yamutse fuskar da sake ɗaureta ya sakashi sakin murmushi da warware hannunsa daya harɗe a ƙirjinsa. Sai kuma ya ɗan furzar da iska mai nauyi a bakinsa yana sake zuba mata idanun. “Wannan ɗaure fuskar fa? Ko duk laifin rashin cikar lokacin ne?”. Maimakon amsa masa zancen nasa sai kawai ta basar tace masa, “Ina kwana?”. “To lafiya ba ƙalau ba”. Kamar zata sharesa sai kuma ta ɗan kallesa. Fuska ya marairaice mata kamar wani ɗan yaro. Janye idanun nata tai kawai. Shima sai ya saki murmushi. Ƙofar motar ta buɗe mata yana faɗin, “Bismillah”. Komai batace da shi ba ta shiga. Shima ya zagaya nasa ɓangare ya shiga. Motar yayma key suka fice a gidan. Sai da sukai ɗan nisa a tafiya ya kalleta kaɗan ya maida hankalinsa ga titi. “Nace miki ina lafiya amma ba Lau ba, baki tambayeni mike damuna ba?”. Hankalinta na'akan novel ɗinta ta amsa masa da, “Ai banga alamar ciwo a tare da kai ba. Nasan neman maganarka ne”. “Oh oh, ni Rafeeq bin Kasheem. Ni har wani neman maganane da ni kuma?”. “Humm”. Kawai tace a taƙaice. Shima sai ya murmusa yana mai jinjina miskilancin yarinyar nan. Bai sake cemata komai ba sai zuwa can a bazata yaji tana ce da shi “Yaya jikin Aunty?”. Har cikin rai yaji daɗi, dan haka ya amsa mata fuskarsa ƙawace da murmushi. “Jikin Aunty babba Alhamdullah. Duk da dai yau ban leƙata ba sai zuwa anjima. Da ƙyar ma na kuɓuto kaina a asibiti dan na zo na kaikin nan.” “Ai sai da nace ka barni naje kawai”. “Bazan iya hakan ba ai. Shi abu mai daraja killacesa ake. Kaffa-kaffa da shi kuma akeyi. Fatana ma na samu na ɓarar da waccan gwamnatin data tare min ko'ina. Sai kuma nayi sakaci wasu ƴan bani na'iya su shigo neman hanyar min kutse?. Ko baki yarda ba”. “Kaima kasan mi kake nufi”. “Ki rantse kema baki sani ba?”. Shiru ta masa. Dan tama gaji da surutun. Yasa ko fahimtar labarin batayi ma. Sun iso katafaren comyanin *_MAWAAD_* daya tsaru da gini na zamani. Gashi babba sosai ta yanda hasashenta bai taɓa hasaso mata ba. Yanda aka tsara ƙaton harabar wajen da furanni koraye da jajaye harma da wasu kalolin abin ƙayatarwa, ga kwalta lafiyayya shimfiɗe. Hatta ababen hawa na ma'aikata an fakasu ne cikin tsari da birgewa. Bawani hauma-hauma ko hayaniya. Sai securitys dake kula da tsarin shiga da fitar kowa a wajen hatta cikin harabar. Dole ne wajen ya birgeka, dan duk iyayin mutum idan yazo *_MAWAAD COMPANY_* sai tsarinsa ya birgeka..........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖2️⃣2️⃣

Readers Also Read