Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 111
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 111: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 111. A lokacin da Nibras ke can tana…
4,471 words
A lokacin da Nibras ke can tana rabzar kukan takaici data saka kanta a ciki dan ita ta saka kanta kam anan Yaya Fawzan na komawa ɗakin cak ya ɗauka Najma zuwa bathroom. Tana zame-zame da ɓoye fuska da ce masa tafayi wanka da magrib baibi takanta ba yace shi zata taya yi ai yanzu. Ya mata haka ne kuma danta tabbatar yau babu ɗaga ƙafa. Yau asalin shiga ƙaulanin jin kunya ta tsinta kanta a ciki, dan haka ta rumtse idanunta gam har aka kammala. Yaya Fawzan kam ai wani cenema ta musamman ya samu ya baje ganinsa iya gani daga ƙafa har kai. Kafin dai ya daure ya haƙura su fito jikinsa duk ya gama saki. Kaida ka ganshi kasan yana cikin wani yanayi. Yanayin daya gagara barinsa ko shirin barci suyi da bathrobe a jikinsu haka ya direta a saman gadon. Da ƙyar yanzu kam Najma ta ɗan ɗaga ido ta kallesa. Muryarta na fita da ɗan rawa-rawa ta ce, “Yaya wannan rigunan sai mu samu mura”. “Karki damu ina da maganin mura mai ƙarfin gaske Love”. Ya faɗa cikin kunneta yana zama kusa da ita. Zata sake magana ya ce, “Shiii!!! Love babu ƙyau yawan magana a cikin dare fa”. Rasama mi Najma zatai tayi, duk ta ƙarasa daburcewa. Musamman daya kai hannu ya kashe wutar ɗakin gaba ɗaya ɗakin ya gauraye da duhu. Da ƙarfi ta runtse idanunta hawayen dake cike da su suka zubo. Dai-dai nan Yaya Fawzan ya kwantota jikinsa sai hawayen suka ɗigar masa. Idanunsa ya lumshe ya buɗe tare da kai hannunsa akan fuskarta. Jin tabbacin hawayen ne take ya sashi sakin murmushi. Murya a can cikin maƙoshi ya furta, “Love idan ke kina kuka tun yanzu idan na fara nawa ni kuma wazai lallasheni?”. “Kayi haƙuri”. Ta faɗa tana sake lafewa a jikinsa. Sai ya murmusa, tare da juyawa da su suna fuskantar juna. Kaɗan ya sumbaci lips ɗinta, cike da raɗa ya ce, “Love ki zame mun jaruma dan ALLAH, na miki alƙawarin zama sarkin yaƙinki kuma ganuwa mai baki kariya daga abokan hari. Na maidaki shalelena abar tattala tamkar ƙwai a cokali. Babu abinda nafi buri a yanzu fiye da ganinki da ciki. Ki daure kinji, komai mai sauƙi ne in dai aka ɗaukeshi da sauƙin. Baki so muje aljanna tare?”. A hankali ta ce, “Ina so”. “Yauwa Love ƴar albarka. Bari kiga na kaimu hanyar zuwa aljanna in sha ALLAHU. I love you so much”. Bai bari ta sake magana ba ya shiga sumbatar idanunta, hancinta har ya sakko kan lips ɗinta. A wani salon girma da nutsuwa ya cigaba da binta cikin soyayya da sallamawa. Ta shagala matuƙa da riritawarsa harta miƙa wuya batare data farga ba. Shi ko ya cigaba da rikice mata dan abu ne daya jima bai samu kamar haka cikin sauƙi da sallamawa ba. A hakan ma wai a tsorace take. Inaga nan gaba yarinyar nan zautar da shi zatai. To tun yanzu ma fa shi tun kan ai nisa ya fara zaucewar. A gaɓar daya shirya mallaka sai komai ya ƙarasa ƙwace masa. Ita tana kuka da neman agajin shi, shima bakinsa na buɗewa har bai san muryarsa ta ɗagu ba. Yana manta da wata Nibras kam a yau gaskiya. Dan da gaske ƙofar aljannar ya kwasu suka tafi ita da shi.... Kar kuga laifinshi, dan Alhaji Sheikh malam Fawzan ya shiga wani ajin karatu ne mai girman gaske. Daya gigita tanadinsa ya warware mamakinsa. Shi kam bazaice komai akan Nibras ba, dan itama ALLAH ya bata baiwa, shiyyasa ma ya iya juriyar haƙurin zama da ita da amsar hakkinsa a gare ta koda tsiya-tsiya. Amma Najma ma sai dai yayta godema UBANGIJI dare da rana. Dan ƴar ƙaramar yarinyar nan ta gama wanke masa hadda yau iya wanki. Yaji al'amarinsa yay matuƙar babbanta dana baya banbanci irin na gabas da yamma. Kodan wancan da ƙarfin ƙwanji yake samu ne? Wannan kuma an sallama masa sai ma roƙonsa ake da magiyar ya tausaya. Tsabar yanda ya ƙwace da yawa bai farga ta sume masa ba ma sai daga baya. A bayan ma a gaɓar da duniyar tai masa diff na ɗan lokaci shima kafin ya farko dai-dai.. Ai tuni ya nemo ruwa ya zuba mata, tana kawo numfashi ta sake fashe masa da kuka. Rungumeta yay shima hawayen na bi masa fuska, ya kasa magana, sai matseta da yay sosai a jikinsa yana shafa bayanta alamar lallashi.... (Mu fahimci wani abu mana a wannan gaɓar. Fawzan ya yarda itama Nibras ALLAH yay mata baiwa, sai dai rashin bashi haɗin kai cikin sauƙi yasa hakan na zuwa masa a raunane. Ga yanzu ya samu Najma da baiwar itama, a dalilin sallamawarta sai yake jinta ƙololuwa sama da Nibras ɗin ma. A yanzu fa a wata gaɓa ce ta Najma farkon shiga ce, inaga nan gaba ta miƙa wuya ta sallama cikin sauƙi da salama mi kuke tunani, balle ta haɗa masa da hidimar gidansa da sauran hakkoki dan mu gane ba kwanciyar aure bace kaɗai aure fa. Dole zata ƙarasa fita masa a rai ragin da yake mata sanda take ita kaɗai ya daina. Sai kuma ta koma gefe tana zaginsa da kiransa namiji ba ɗan goyo bane, ya ƙara aure ya wulaƙanta ni. Alhalin kafin auren nasa itace tai sakaci da damammakinta har a yanzu ya samu mai masa ita kuma ta rasashi. Kuma mu fahimci irin abun nan, in har mace ta wulaƙanta namiji son ranta sanda take ita kaɗai, da zarar ya ƙara aure da wahala bata rasashi gaba ɗaya ba koda tana a tare da shi. Duk da tabbas akwai masu butulci da zakiga macen na kokari a kansu amma basa gani kuma. To yake ƴar uwa dake nake anan. Koda kina zaune lafiya da mijinki, kina iyakar ƙoƙarin ki idan yazo miki da batun ƙara aure, maimakon ki ruɗa kanki kuyi fitina ke da shi, ko ki biyema ƴan uwa da ƙawaye ki fara leƙe-leƙen gidan malamai, ko ki ɗaura gaba da dangin miji kice sune suka sakashi, kai in ma sune suka saka shi yay miki kishiyar ajiye batinsu gefe kizo nan mu tattauna. Yazo da batun zai ƙara aure, ko kin fahimci yana neman aure, shawarar dazan baki nutsu ki tsaida hankalinki da zuciyarki waje ɗaya dan ALLAH. Ƙarfafa kanki matuƙar ƙarfafawa ki zama jarumar kanki ki shiya dai yinta ba shiga wutar jahannama bace, idan kinada zafin kishi ne sosai yawaita ambaton ALLAH__La'ilaha illa antassubahanaka inni kuntu minazzalumin__ko__Hasbunallahu wa ni'imal wakil. Zaki samu sassauci............✍️
Fatan alkairi tare da Barka da salla a gareku. ALLAH ya maimaita mana ya amshi ibadunmu ya dawo mana da mahajjatanmu gida lfy. Kwana biyu kun jini shiru, an binciki file ɗina ne 😀.
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣2️⃣5️⃣
______________
_____Ƴar uwa karki yarda koda a fuskarki a wannan gaɓar namiji yama fahimci kina kishi koda ace kafin ranar yasanki da zafin kishin, rikiɗe masa dan mace dama kamar hawainiya aka santa. Ki masa addu'a ki dake. Sai ki koma gefe cikin tunaninki karki nema shawarar kowa. Ko ki zauna da bironki da takarda ki rubuce dukkan abinda kika san kina masa ko kina tafiyarwa a gidan koma rayuwarki gaba ɗaya. Karki ɓoyema zuciyarki ko kwalwarki hakan ko mara ƙyau ne kikeyi rubuta shi. Sai ki zauna ki basu kwanaki kullum ki ɗauki hali ɗaya kiyi nazari a kansa, sannan ki koma gefe kiyi binciken illar halin da fa'idarsa daga shawarar wasu ko auna abinda ya shafi halin ko bincike a addinance da zamantakewa. Duk binciken da kika samo sai ki zauna ki banbance abinda yake tare da shi mai ƙyau ko mara ƙyau. Ki fahimci mi zaki rage a halin, ko mi zaki ƙara, idan baida fa'ida ajiyeshi gefe ɗakko wanda ya fisa nagarta ki canjeshi da shi. A haka ɗaya bayan ɗaya kima halayen naki ki ga ikon ALLAH. Wlhy sis.. koda ya ƙara auren sai ta shigo ta rasa tudun dafawa na samun lagonki ko shi mijin, dan duk inda ta kama ke kin riga kin wuce, kin kuma yi masa idan tayi sai dai ya kalla yaji a ransa wance tayi min wannan ai sai dai na ƙara dan jin daɗi. Idan kuma ke amarya ce da aka kawo, in ma ta biyu, in ma ta uku, in ma ta huɗu ajiye rawar kai gefe da shawarar ƙawayen banza, ta dangi yan a tayaki kishi a farkon zama kwantar da kanki ki nutsu ki ma fara fahimtar halayyar mijin a karan kansa, karki sake, nace kar ki kuskura ki yarda kwanciyar aure ko saka ƙananun kaya, ko dafa hanjin ligidi da alewar madara ne aure fa, yarinya wasan ɗan gaske ne aure fagen fama ne. Yaƙi ake na ka kashe ko a kasheka bada wuƙa ko mashi ba, a zuba capacity na ƙyawawan halayen tsira a duniya da lahira dan ibada ce ba hayya-hayya ta duniya ba. Ba halayen da namiji ya nuna miki a waje matarsa bata iya ba ko bata dasu dan su yazo gareki zakije kiyi ba. A'a amarsu haɗa harda wanda kikaga tanama mijin nata kema yi masa, idan da halin canja su zuwa sabon salo ta ɓangarenki, to ko hayya-hayya akeyi idan yace uwargidana ALLAH yay miki albarka zai juyi yace tare dake amaryata. Duk sanda kuma Ado gwanja yace SAMA MATA dake za'a miƙe wlhy, sannan muje lahira duk mu shige aljanna aure ai rahama ne. Raba kanki da ƴan faɗin namiji baɗan goyo bane, yo ko mage ne shi akan rashin daɗin goyo goyeshi koda tsiya-tsiya ki tamke da turmin zane kedai aljanna kike nema. Idan ta kama shi ɗan balaja'u ne burinsa ya ƙuntata miki ya azabtar dake idan kika sauke nashi haƙƙokin kika barsa da nashi nauyin sai aje ke kina a layin su Nana Asiya shi yana a nasu fir'auna a lahira. Amma duk runtsi kada ki yarda ki zama a jerin matan su Annabi Luɗu. Mazansu na aljanna su suna a ƙasan wuta. Yo hauka akeyi, sai kace ba ALLAH ya halicceni danna bauta masa ba dazan lalace wajen kai kaina wuta saboda halin sakaran namiji. Kama kanki yar uwa, idan ALLAH yay miki jarabawa da ɗan bala'i baya barci karki yarda ki halaka kanki da damuwa da tunani sabida halayensa, barshi yaji can da su kabarinki daban nashi daban nemi aljannarki ke dai sai ki bishi da addu'ar shiriya, idan ya gyaru ruwansa, idan ya cigaba da tarama kansa ya rage nashi. Wanda ya halicceki ya haliccesa ne ke hisabi bake ba. Amma mu kiyayi kammu da jefa kammu a bala'i saboda halin maza. Mune bin bokaye mune bin malaman tsubbu, mune cutar da kishiya mune aibantata, mune gallaza mata. Yo hauka ake na tarama kaina hakki saboda wata banza kishiya. Tirƙashi, kai wlhy nafi son aljanna fiye da komai, shiyyasa ba kowace rawa ce idan aka taka take zame min abin kallo ba. Zama haka ƴar uwa sai ki zauna lafiya. Amma kunga masu miji na ƙyautata muku iya ƙoƙarinsa ɗin nan kuna zuwa kuna biyema ƴan media ana zagin maza da ku ku fita idona wlhy, ku farka idan zaku farka idan ba hakaba kina comments da sunan zagin maza bayan ke ALLAH ya kama naki ya damƙa miki a hannu kina ganin comments ne kawai wlhy Mala'iku na amsawa da Amin. Kafin ki farga ya zame miki tantiri jinin gidan fir'auna irin su Baban Nazeerah ki kama nan ki saki can ki rasa gane yaya akayi bayan kece kika kirama kanki ruwa. Yanzu idan mata irin Saheeba ko Nibras na zagin maza muka tayasu bama tunanin ALLAH zai sakama mazan? Idan mata irin Maanal na yabon maza bama tunanin idan mun gwalesu munce ƙarya suke ko kuma basu san halin maza bane tunda yanzu sukai auren mun shiga hakkin mazan su kuma mun sare musu gwiwa daga gina ƙyaƙyƙyawar rayuwar data dace. Ko irin su Ammie idan sun zo sunce mana irin su Babu azzalumaine idan mukaga laifinsu ko rashin haƙurinsu bamu shiga hakkinsu ba. Idan irin su Abah sukace irin su Mamy, Sabuwa, Nazeerah, Hajiya Basariyya, Maman Yaseerah bala'i ne a rayuwarsu muka ga laifinsu bamu shiga hakkinsu ba. Ire-iren wannan misalan mu dinga aunasu mu fahimci ita rayuwa bangarori ne da ita, kowane irin ɓangare da nasu ƙalubale. Sai ki auna irin wanda kike ciki ki nemi ɗauki wajen UBANGIJI domin samun waraka daga garesa. Idan kika zama irin su Nibras, marasa alƙiblar rayuwa kina ji kina gani wata zatazo tai miki kwaf ɗaya ta barki wanwar a ƙasa wlhy sai dai ki ƙare da kuka. Ki nutsu ki fahimci rayuwa a yanda ƙaddararki take sai ki kamo can da can ki haɗa ki ƙulle ki samu zaman lafiya irin na Oum da Ammie, duniya taita tafiya miki cikin aminci kamar yanda ruwa ke zubowa bisa ƙasa tsirrai su fita abin sha'awa da ƙaunar kowa. Ki zama mai gayama kanki gaskiya ba ki dinga zaman jiran mai gaya miki ba irin Saheeba. Idan aka nuna miki ƙauna sallama ki barwa ALLAH komai irin Maanal, wlhy ko amanarki mijin yaci sai kin samu riba a gaba kamar ta Ammie. Kai bara ku tsaya anan naga mun saki labari da yawa ALLAH dai ya samu a aljannarsa. Sanda ƴan wuta ke wayyo-wayyo mu muna can muna shan madara da kaji, duk bayan awanni mu ziyarci gidan MANZON ALLAH. ALLAH yasa lokacin da UBANGIJI zai yi magana da ƴan aljanna muna kusa😭😭🙏).
Barka da juma'a masoya🥰🤏 ________★
KADUNA
Koda su Sabuwa suka iso gidan babu wanda ya kawo komai a ransa. Dan Daddy da Ammie ma daga gaisuwa basu sake bi takansu ba. Sai dai yanda Yaya Yazeed yaje yana gaishesu jikinsa har rawa yake ya zafesu a zuciya. Musamman ƴaƴan Hajiya Yaya dako kallon Sabuwar basu yi ba balle uban Nazeerah. Shi ko tsohon najadun sai bin yaran yake da kallo yana lasar baki. A ransa faɗi yake (Kaga yara kuwai-luwai sunci abinci sun ƙoshi ba mazan aure) a fili kam sai takalar Daddy yake da magana shi kuma yaƙi kulashi. Daga ƙarshe ma ya tashi ya shige sashen Ammie dan nashi ƴan sanda sunce a barshi a haka har a kammala bincike. Itama Ammie ganin haka sai kawai ta tashi tabi bayansa. Hajiya Basariyya taji haushi, amma batace komai ba dan yanzu bata kishi take ba ta ƴar dukiyarta data yara takeyi. Ganin haka sai Sabuwa da mijinta suma suka tafi sashen ƴarsu, batare da neman ina Hajiya Yaya take ba. Ziiiii Yazeed ya bisu shima. Suna shiga cikin falon Nazeerah ta masa tsawa, wai ya fita ya basu waje. Jikinsa har rawa yake ya shiga bata haƙuri ya fito, ƙasan zuciyarsa kuma na masa nauyi dan addu'ar da ake masa na tasiri a jikinsa matuƙa. Iyakace dai ALLAH bai kawo ba kawai. Wani ikon ALLAH korowar datai masan yana zaune anan compound Amrah tazo ta wuce sashen Ammie domin sanar musu Hajiya Yaya ta farka. Sai gasu sun fito sun nufi sashen harda su Hameed. Sai kawai shima ya miƙe ya bisu kamar yanda zuciyarsa ke raya masa. Mamaki ya kama kowa da ganin ya shigo ɗin, amma basuyi magana ba duk hankalinsu akan Hajiya Yaya da Basira ke bama ruwa tana sha. Ammie da Daddy na kusa da ita zaune. Murya a sanyaye ta kalli Ammie ta ce, “Ammien yara taimaka min naje bayi”. Babu musu Ammie tace to, haka ta taimaka mata ta miƙe ta rakata har bathroom. Sai ma ta haɗa mata ruwan wanka ta ce ta daure tayi zatafi jin ƙarfin jikinta. Godiya Hajiya Yaya tama Ammien hawaye na ciko mata ido. Yanzu idan Ammie na mata abun alkairi sai taita kallonta tana jinjina ƙyaƙyƙyawar zuciyarta. Wanda kafin yau gani take iya asirine kawai da munafunci da kissa. Koda Ammie ta fito saita ce duk yaran suje waje, itama tai nufin fitowa Daddy ya miƙe zai biyota ta juya ta riƙesa. Ƙasa-ƙasa tace, “Daddyn Hameed ina kuma zakaje? Kai ya kamata ma ka shiga ka taimaka mata bata da wani ƙarfi a jikinta wlhy ƙarfin hali ne kawai.” Zai yi magana ta ɓata fuska dan ta sanshi da gardamar tsiya idan bashi ne yay niyyar abu ba da kanshi. Rigimar Asiya daban take a gareshi, darunta na musamman ne babu hayaniya babu hauragiya. Amma idan ta sakaka a gaba dole kayi yanda take so ko kai baka so. Dole yay shiru ta fice ta ja musu ƙofar..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣2️⃣6️⃣
______________
.........Ganin Yazeed daya fito ya raɓe gefe abin tausayi kamar wani boyi-boyin gidan sai ƙwalla suka cika mata ido. Batare komai ba ta wuce zuwa sashenta, babu jimawa sai gata da goran ruwan addu'a da dama take ta neman hanyar fara bashi yana sha amma bata samu ba saboda koyaushe yana nane da matarsa. Ba kuma cin abincin kowa yake ba yanzu a gidan balle su samu su bashi ko yimasa girki da shi. Cike da kulawa da murmushi Ammie tai kiran sunansa. Ya ɗago yana kallonta, kujerun dining ta nuna masa tana faɗin, “Bismillah zomu zauna anan ko kafin ta fito”. A mamakin su bai mata musu ba, koda suka zauna sai ta buɗe ruwan ta miƙa masa. Nan ma amsa yay ya kai baki, zai sha kawai tace, “Kayi bismillah mana”. Sai yay shiru kamar wanda ya manta ma da bismillahr, hakan ya bata tabbacin an kaɗe masa hankali daga ibada ƙwarai da gaske. Dama tana lure baya zuwa massallaci sam yanzu. Sai su wuni su kwana ma uku suna sashensu shi da matarsa basu fito ba. Bismillahr ta maimaita masa, sai ko ya faɗa kamar yanda ta faɗa sannan ya sha ruwan. Kamar zai sha kaɗan ya ajiye sai gashi ya shanye tas ya ajiye goran. Ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi kamar yanda itama Ammien ta sauke tata a ɓoye. Sai cayay mata “Ammie ruwan nan da daɗi sosai”. Murmushi Ammie tayi, ta ce, “Sosai kuwa. Nima da naje bikin nan aka bani na shashi daɗin da naji yasa na sayo mana. Idan kana so ka dinga zuwa kana amsa kullum a sashena kaji ko”. Kai ya jinjina mata alamar to, dai-dai nan Daddy ya leƙo yace su shigo. Duk mikewa sukai, yaran suka shige cike da zaƙuwa. Ammie harta miƙe ganin Yazeed bai motsa ba ta juyo tana kallon sa. “Taso mana muje yayansu.” Shiru yay kamar zai ƙi, sai kuma ya miƙe ya bita, da sukaje bakin ƙofar sai ta bashi dama ya fara shiga sannan ta shiga. Hajiya Yaya zatai magana ganin Yazeed sai tai shiru, ta zuba masa ido tamkar yau ta fara ganinsa. Shi kuma ya tsaya cak kansa a ƙasa cike da rashin gaskiya. Duk da bawai abinda ya aikata yake iya tunawa ba, dan kaf abinda yay a daren jiyan tamkar an goge shi ne da ga brain nashi bai iya tuno komai. Kai hatta kai-kawon nan da ake na ƴan sanda da wani tambayoyi shi ba fahimtar komai yake ba fa. Ganin kallon da Hajiya Yayan kema Yazeed ɗin na neman yin yawa Ammie ta katse yanayin ta hanyar mata sannu, sannan tace Yazeed ɗin ya matso ya gaida Hajiyan shima. Kamar dai bazai zo ɗin ba sai kuma ya matso batare daya kalleta ba yace, “Sannu”. Daga haka yay shiru. Kai kawai Hajiya Yaya ta ɗauke batare da tace komai ba. Sai kuma zuwa can ta kalla yaran a sanyaye ta ce, “Kuje falo zanyi magana da Daddyn ku”. Fita duk sukayi, Yazeed shine farko ma, Ammie zata bisu Hajiya Yaya tace ta tsaya harda ita zatai maganar. Dole ta koma ta zauna. Sai da suka gama fita suka rufo musu ƙofar sannan ta dubi Ammie da Daddy. Idanunta na zubar da hawaye ta ce, “Ammien yara yaushe kuka dawo?”. Ammie bata ɓoye mata komai ba ta labarta mata kiran da yara sukama Daddy da zuwa ɗaukarsu da yay ita da Hajiya Basariyya dama ɓarnar da suka tarar a gidan mai ban mamaki daban tsoro. Zuwan ƴan sanda da hasashen yara na cewa Nazeerah ce. Murmushi Hajiya Yaya tayi mai ciwo, idanunta na zubda ƙwalla tace, “Ba Nazeerah bace Yazeed ne”. A firgice Daddy da Ammie suka kalleta. Daddy ya ce, “Yazeed!!”. “Tabbas shine, dan yazo nan da akwatin ɗakinka, nima shine ya ɗaureni saboda na masa magana. Bana raba ɗayan biyu shine ya shiga sashen Basariyya ma. Itama Asiya dan sun kulle ko'ina ne shiyyasa inaga ya rasa hanya. Amma tabbas shi za'a bincika yasan komai”. Idan akace hankalin Daddy bai tashi ba a wannan gaɓar ma ƙarya ne, sunma rasa taya zasu fassara al'amarin. Hajiya Yaya kam kuka take sosai, dan zuwa yanzu al'amarin Yazeed ɗin kam ya gama daga mata hankali matuƙa. Sai Ammie ce ta koma lallashinta. Daddy kam yayi shiru yana faman lissafi a zuciya da yake shi namiji ne, kai tsaye suke tunani ba kamar mu ba da za'aita haɗo gabas haɗo yamma.......
_________★
Washe gari AA ya tashi da shirin zuwa Kaduna ganin jikin na Maanal da suƙi sosai. Amma bai gaya mata kadunar zai je ba, yasan zata iya tayar masa darunta. Sai yay shirin kamar office, duk da ganin ya saka manyan kaya sai da tayi magana. Sai ya ce mata dan tana so ne ya saka. Da haka ya kashe bakin nata. Da yake ita yau ba office ɗin zataje ba yace ta bari sai zuwa gobe ta sake jin ƙarfin jikinta. Dan tun jiyan sai yamutse-yamutse take yi, idan ya tambayeta tace naman jiya take tunawa. Abinci ma taƙi ci sai fura da fresh milk. Duk kankambar girkinta yau ko kallon kitchen bata son yi, koda sukaje sashen Oum su Oum na kitchen ƙin shiga tayi. Shi AA ma hakan daɗi yay masa, dan inba hakan ba ALLAH bazata nutsu ba. Breakfast yayi shi kaɗai, dan yau babu babban Yaya babu Yaya Fawzan duk ana can ana tattalin amare. Maanal kuma tace bazataci ba, ko dining ɗin ma bata zo ba tana daga falo sai shi da Oum ne kawai data haɗa masa komai. Murya a ƙasa dan kar Maanal ta jiyo yace, “Oum Kaduna fa zanje.” Cikin jin daɗi Oum tace, “Kai Alhamdullah naji daɗin hakan kuwa. Ya kamata kam a bisu dan da dare munyi waya da ƙanwata al'amari babba ne gaskiya.” AA ya ce, “Nima dana kirata bayan sallar isha'i take mun bayani, abinda ya tsaya min a rai da tace tana zargin saka Yazeed ɗin akayi bayin kansa bane. Kuma nima gaskiya bana tunanin zai aikata. Tunda nayi huɗɗa dashi a watannin baya yana da nutsuwa da cikar kamala sosai. Kodan halallacin da yay a rayuwar su Ammie koda shi ya aikata zan masa uziri. Balle yanda Ammie ta musalta min jiya na kwana ina tunani da nazarce-nazarce. Shiyyasa zaije gara a tari abun da wuri dan duk inda mai saka aikin yake yana kusa da su gab. Ga Daddyn tace ya kasa ɗaukar kowanne mataki dan abin ta bigesa sosai”. “Ta ina kam zai iya ɗaukar wani mataki, ai yama yi jarumta, idan wani ne zubewa zai yi ALLAH sai dai kwanan asibiti. Baga abokiyar zamanta da sukazo nan ba Hajiya Basariyya jiya kaji sai da aka kwana kanta, da yake kuma bata da hankali wai Asiya ce tasa akai musu da yake bataji Yazeed ɗin bane da farko.” “Mtsoww! ALLAH Oum na tsani matar nan, shashasha an faɗa mata irintace mayyar kuɗi, Ammie ta damu da irin wannan abubuwan ne, kafin taga dukiya ita Ammien ta gani ai tunda mahaifinta ya bar mata azzalumin miji ya cinye”. Murmushi Oum tayi da faɗin, “Kasan idan mutum nada halin banza ɗauka yake kowa ma haka yake. Ni har ka tuna min ma da Habib ɗin, ya kamata ka sanya lokaci ka ɗauka Baby kuje Giro su san da auren nan naku”. Ɓata fuska yay sosai ya ce, “Oum miyasa?”. “Haka ya kamata Auta, ai ko ba komai shi uba ne, abinda yayma Ammien ku wannan tsakaninsu ne, tunda gashi ALLAH yay mata canjin alkairi, ku kuma yaƴane, dole ku sauke haƙƙinsa dake kanku. Anyi bikinku babu kowa daga ɓangaren su, bai kamata ba sam.” Shiru AA yay dan kawai bazai iyama Oum musu ba. Amma baya ƙaunar abinda zai sake haɗa hanyarsa da su Babu da shegiyar Gwaggon nan daya fi tsana fiye da kowa. Haka dai ya kammala suka miƙe, koda sukazo falon a mamakinsu barci Maanal ma takeyi. AA ya kalla Oum yana ɗan murmushi. “Da alama Babynki ta zama kasa Oum”. Dariyar itama Oum tayi, ta ce, “Ta zama kam. Dan barci baya mata wahala sam yanzu. Kaga ɗaga min ita zuwa ɗaki kwanciyar kujerar nan zata iya sakata ciwon jiki”. Amsawa yay da to yana ɗaukar Maanal ya kaita bedroom ɗin Oum ɗin, sai da ya sumbaci goshinta da lips ɗinta sannan ya raɗa mata bye-bye a cikin kunne ya lulluɓeta ya fito. Bai zauna ba yayma Oum sallama dan drivern sa ya shirya shine zai jashi. Har compound ɗin Oum ta masa rakiya, ya kalla sashen Babban Yaya dana Fawzan yay murmushi, ransa fal gulma. Yayi sallama da Mamy dan sai da suka fara zuwa suka gaisheta ita da Abah sannan sukaje sashen Oum, itama dai bai gaya mata Kaduna zai je ba, sallamar zuwa office kawai ya mata, duk da ma dai sama-sama yau ta amsa musu gaisuwa dan Maanal ma bata shiga ba a falo ta tsaya, da farko ma Haule catai barci take yi, sai dai shi ya wuce bedroom ɗin ya dubata dan yasan takai haka a kwance sai dai in babu lafiya, sai ko ya shiga ya sameta zaune tana waya, sai dai yana yin sallama ta katse. Ya fahimci ita tace ma Haule tace musu tana barci, dan haka ya gaisheta shi kaɗai ya fito yace ma Maanal ɗin tana barcin, Maanal kam sarai taji a jikinta itama idon Mamyn biyu, kawai dai ta ƙyalesa ne... Sai da motar ta fice sannan Oum ta koma ciki tana murmushi........✍️