Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 117
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 117: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 117. ..........A ɓangaren Oum…
4,452 words
..........A ɓangaren Oum maimakon kalaman Mamy su sakata a ɓacin rai da baƙin ciki a wannan yini sai UBANGIJI ya canja mata da saɓanin haka. Bawai bata juya su a zuciyarta bane ba. A'a tanata mata uziri akan akwai dai abinda ke faruwa da bata sani ba. Dama shekaran jiya sai da sukai rigima da Abah akan rashin girkin Mamy, bama ta ganin tana zuwa sashensa. Amma sai yaƙi ce mata komai. Daga ƙarshe ma ya gargaɗeta akan ta daina damunsa barci zai yi. Shiyyasa a yau da Mamyn taso mata da wannan batun sai ta sake yarda akwai wani abu dake faruwa da bata sani ba. Kuma ta fahimci Mamyn na cikin fushi ne shiyyasa zatai mata uziri daga nan zuwa wani lokaci sai ta sameta suyi magana ta hankali. Wannan kyakkyawan tunanin nata ne ya kawo ma zuciyarta masalaha. Kasancewar Najma da Ameerah a tare da ita kuma ya ɗauke mata hankali. Sai kuma ga Nuwaira da Saheeba da Nuratu. Duk da zuwan Saheeba da Nuratun ya bata mamaki sai ta ƙyautata musu zato. Ta kuma dinga jansu da hira da kulawa kamar yanda sukeyi da su Nuwaira. Duk da Najma da Nuwaira sun ƙi sakin jiki da su Saheeban. Ita ko Ameerah zuciyarta ta gama raya mata abinda taji a wajen Hajiya Turai su Saheeban ke son fara aiwatarwa shiyyasa suke son shiga jikin Oum ɗin. Dan haka tai matuƙat sakama dukkanin motsinsu ido, musamman a lokacin da suka shiga kitchen yin girkin rana. A lokacin zaman cin abinci da Babban Yaya da Yaya Fawzan suka shigo su kansu sunyi mamakin ganin Saheeba da Nuratu a sashen Oum ɗin kuma ana hirar arziƙi. Ganin babu Nibras Fawzan ya cije baki kawai. Kamar Oum tasan tunanin da yake yi ta ɗauka waya ta kira Nibras ɗin tace tazo sashenta. Babu jimawa kuwa sai gata. Duk ta rame daka ganta kasan bata da lafiya. Ga kumburin bakinta na bubbugewar da yayanta yay mata jiya har yanzu bai gama sauka ba. Komai Oum batace mata ba bayan amsa gaosuwarta, ta gaida Babban Yaya shima sannan ta zauna. Sauran kam yanda bataima kowa magana ba babu wanda ya kulata. Sai hakan baima Oum daɗi ba, tasa a ranta dole ne tai iya ƙoƙarin ta ba ganin ta haɗe kansu waje guda. Dan wataran sune gidan, idan babu haɗin kai a tsakanin taya zasu bama ƴaƴansu tarbiyya.. Sunci abincin a nutse, Yaya Fawzan na faɗin yayi kewar auta da Lilly. Babban Yaya ya ce, “Kayi kewarsu ko kayi kewar takura musu”. Dariya su Oum sukayi. Oum ta ce, “Ai wlhy kam kamar ka sani kuwa Fadeel, Fawzan ya saka min autoci a gaba matuƙa. Dan ma yanzu Auta yayi baki ramawa yake yi”. Babu wanda baiyi dariya ba, idan ka cire Saheeba dake na yaƙe, sai Nuratu da hankalinta ya rabu biyu. Tana jin daɗin hirar AA tana jin zafin sunan Maanal da ake sakkowa a ciki. A haka dai suka kammala, Nuratu da Saheeba da Nibras zasu tashi kamar yanda suka saba a barma ƴan aiki wahala Nuwaira tace, “Oya mu tattare kayan muje kitchen a wanke. Suma su Inte a rage musu aikin suna ƙoƙari”. Babu alamun damuwa a tare da Ameerah da Najma, dama su sunyi niyyar yin hakan. Amma Nuratu, Saheeba, Nibras abin ya musu ciyo, kamar su matan gida za'ace suyi wanke-wanke inama laifin girkin da sukayi. Oho Nuwaira ma batasan sunai ba. Fawzan da Babban Yaya kam daɗin abinda Nuwaira ɗin tayi aukaji sosai. Hakama Oum hakan ya mata daɗi. Sun gama wanke-wanken kenan akai kiran sallar la'asar. Dan haka kowa ya nufi sashensa domin yi. Su Saheeba na gab da shigewa sai ga Haule tazo kiransu wai inji Mamy. Ameerah dake gabansu sarai taji, amma sai tai wucewarta kamar bata jin ba. Su kuma kallon juna sukayi, kamar zasu magana sai suka ma suka fasa. Saheeba tace, “Ki gaya mata idan munyi salla zamu zo”. Har Haule ta amsa zata tafi sai kuma Nuratu taja hannun Saheeba suka bi bayan Haule. A falon sama suka sami Mamy, Haule na gaya mata saƙon su Saheeba ɗin sai kuma ga sakkanarsu. Itama sai da tayi mamakin bama Mamy ɗin kawai ba. Sai kawai ta haɗiye sauran bayanin da takema Mamyn ta fito ta bar musu falon. Yanda Mamy take zaune a kujera zaman ƙasaita haka suma suka zauna. Kit ɗin magani a gabanta da kofi alamar tasha shayi. Hakan na nufin bata da lafiya, sannan kayan data fita da sune a jikinta, hatta handbag ɗinta na kusa da ita ajiye ba'a kai ciki ba. Ganin basu da niyyar gasheta cike da takaici ta ce, “Lalacewar tawa takai har gaisuwa ku daina min kenan?”. Baki Saheeba ta taɓe, dan tafi jin matuƙar zafin Mamy fiye da Nuratu, a gadarance ta ce, “Mamy kin kiramu nan ne damu gaisheki ke nan?”. Tsuru Mamy tai tana kallon Saheeba. Ta jinjina kai tana mai cije lips. “Hummm Saheeba kenan, naga kwana biyun kanki na rawa a gidan nan.....” “Ashe ma sai yanzu kika lura”. Saheeba ta faɗa a gatsine. Yanzu ma kallonta Mamy tayi zuciyarta na sake yin nauyi. A ranta sake jinjinama Nana take yi, wato ta gama tsarama yaran komai. Shike nan zata nuna mata cewar ta isa da gidanta. Kallonta ta maida kan Nuratu. Cikin gargaɗi da sake kausasa harshe ta ce, “Ki shirya kayanki yau ɗin nan ki koma gidanku. Itama ƴar uwar taki tana hanyar biyo ki”. Maimakon Nuratun ta bata amsa sai Saheeban ta kwashe da dariya. Cike da iskanci da raini ta ce, “Ai ba gidanki bane Mamy, sannan ba wajenki take zaune ba. Nan ɗin gidan auren ƴar uwarta ne, zama daram babu fashi. Da kike cewa nima zan bita, sai dai mu bita tare ni dake. Dan kin san dai duk kanwar ja ce ai. Ta wani fannin ma gara ni, duk abinda nake yi kece kike sakani yi, sannan koba komai zan tsira da ƴaƴana. Kiji da damuwarki kinji. Idan kuma kikace zaki kafa mana karan zuƙa a gidan nan to wlhy tare dake zamu zagwanye. Sis... Tashi mu tafi”. Wata banzar dariya Nuratu tai tana miƙewa da faɗin, “Ai naga faɗan na surukai ne ni bai kamata na shiga ba sai idan na shigo daga ciki.” itama ta kalla Mamy ta watsar. Sai suka kwashe da dariya. Wani irin fisga numfashin Mamy keyi a ƙirjinta. Tsabar mamaki da kaɗawar zuciya ta gagara iya yin magana ma har su Saheeba suna neman ficewa, wani irin yunƙurowa zuciyarta tai ta miƙe ta finciko Saheeba baya. Ta ɗaga hannu zata wanka mata mari Nuratu ta cafke hannun ta murɗeshi har sai da Mamy tai ƙara. Dama kuma wanda ta taɓa jin ciwo ne har yanzu yana motsa mata musamman idan zata kunna ac sanyi ya shigesa. Nuratu ta yarfar da hannun Mamy har sai da ya bugu da kujera. Yayinda Saheeba tai wata dariya tana kallon Mamyn cikin ido. “Oh da marina zakiyi? A tunaninki wanda kikayi a waccan ranar gaban mijina ma zan barshi ne ya tafi a banza. To ki rubuta ki ajiye zan rama shi a gaban kuma ɗan naki. Sannan ki kiyayi cewa zaki kai hannunki jikina. Dan walhy watarana sai na ɓallashi ɓas fiye da yanda stairscase yay masa a randa kika kunnenki ya jiyo miki abinda yafi karfin kanki tsohuwar banza. Ni ba Maanal bace da zata iya miki kara da kawaici wlhy hadda zan goge miki tas kin san dai ni ɗin rainon SHARRINKI CE. kin san ko masu iya magana kance makwaikwayi yafi ma'iyi iyawa idan ya ƙware. Sai ki kiyaye gudun abin kunya ki sani a bakin duniya ace na mari yayar uwata, kishiyar uwar mijina dan ke kam ai ba uwar bace ba. Su kansu ƴaƴan bake suke ɗauka uwa ba matsayin kishiyar babarsu suke kallonsu. Dattijuwar arziƙi ƴar girma data gaji halin girma kenan Oum. Mtsowww!!! Ƴar wahala kawai.... Gaba ɗaya Mamy ma ta kasa fahimtar a sume take, ko an busar mata da jinin jiki ne ta yanda jikinta ya daina motsawa dan ta koma tamkar gunki a wannan gaɓar. Saheeba ta gama goge mata hadda tas da Nuratu..... (Nace hummm mutane na haka fa rayuwa take, shiyyasa duk tsanani kada ka sake ka raini zuciyar kowa da mugunta koda ɗan daka haifa ne. Idan ba haka ba bayan ya gama maka taka farautar wlhy kai zai dawo ya farauta. Kuma wadda zai maka sai tafi wadda kake sanya shi yanama mutane. Kuma babu yanda ka iya, dan ya sanka ciki da bai ɗin ka ta yanda garkuwar da zaka kare kanka ma sai ta maka wahalar nema balle samo takobin yaƙi da shi. Kun san shi ance sharri ɗan aike ne, duk inda ka aika shi, ko mai nisa da nisan shekaru sai ya dawo ya tabbatar maka yaje. Tsarkake zuciyarka ka zama mai barma UBANGIJI komai sai kasha mamaki. Koda harara karki cutar da kowa wlhy kina barci ALLAH zai tare miki faɗa da tarnaƙin kowacce irin guguwa. Kumuje zuwa muga yaya Mamy zata ƙare da nata karnukan farautar😂🤣)..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣4️⃣0️⃣
______________
........Tunda Hajiya Basariyya ta shigo falon taga baƙin da aka sakata zuwa gaisarwa tai wani kicin-kicin da fuska. Zama tai nesa da kowa, Daddy yay mata wani irin kallo ya ɗauke kansa. A maimakon gaishesu sai cema Daddyn tai gata. Idan kujerar dake falon ta motsa to Daddy ya amsata, yama watsar da ita tamkar bai ganta ba. Dan yanzu ya ƙudurtama ransa bazai sake ɗaukar iskancin kowacce ba ga ƴan uwansa. Dolene ya jajirce akan zuri'arsa kodan su san ƴan uwansa sunada daraja a duniyarsa. Arziƙin da ALLAH yay masa bashi ke nufin ya banbanta da su ba ko ya fisu. ALLAH sarki Baban Sageer mutum ne mai sauƙin kai. Sai kawai shi ya gaida Hajiya Basariyya, ya kuma jajanta mata. Hakama iyalinsa duk suka gaisheta. Gaba ɗayansu ta amsa musu ne a ciki. Abin ya sosama Sageer zuciya sosai, dan haka da farko yay kamar bazai gaida Hajiya Basariyya ba sai da mamansa ta hararesa. Aiko cikin dakewa da tsumewa yace mata ina yini daga zaunen da yake. Daddy yay ɗan murmushi, dan shi abinda Sageer ɗin yayi wlhy birgeshi yayi, koba komai ya nuna mata iyayensa masu daraja ne a garesa ai. Daga gaisuwar Sageer ɗin kuma sai kowa yay banza da ita aka cigaba da hira cikin nishaɗi harda Hajiya Yaya da Ammie. Sai kuma hakan ya zafeta, fuuu ta tashi ta fice batare data cema kowa komai ba. Suma ɗin babu wanda yabi takanta. Har lokacin sallah yayi mazan suka tafi massallaci matan sukayi anan. Koda suka dawo zaman cin abinci sukayi, ganin kowa yana nan banda yaran Hajiya Basariyya Daddy yace aje a kira masa su har Huznah”. Babu jimawa kuwa sai gasu har Huznah ɗin. Yanda suka shigo zai baka tabbacin gudowa sukayi uwarsu bata sani ba. Haka ɗinne kuwa, dan Hajiya Basariyya na bedroom suna tattaunawa da Maman Yaseerah ta waya akan al'amarin Huznah ɗin. Da yake tana shiga ta koro Huznah falo sai itama ta samu tabi ƴan uwanta. Tunda suka shigo idanun kowa akan Huznah ne. Musamman Sageer, dan kallo ɗaya zakai mata kasan tayi kuka. Ji yay duk abin ya damesa, ga kunyar iyaye dole ya dake. Gaban Daddy Huznah ta fara zuwa ta durƙusa tana gaisheshi. Maimakon amsawa sai yay shiru kawai yana kallon ta. Hajiya Yaya data fahimci ransa a ɓace yake sai tai magana. “Kinga Huznah tashi daga dirƙuson nan kinji, zauna da ƙyau wannan durƙuson baida amfani a gareki”. Kan Huznah a ƙasa tace to, sai kuma ta zame ta zauna sosai ta sake gaida Daddyn. Ajiyar zuciya kawai ya sauke ya amsa mata. Tare da tambayarta lafiyarta. Kanta har yanzu dai a ƙasa tana wasa da yatsunta tace, “Alhamdullah”. “Yanzu Huznah daban aika ai kiranku ba bazaki zo ki gaishe ni ba balle sauran iyayenki ko? Maimakon ki ƙara hankali kinyi aure sai ma ki ƙara neman lalacewa. Ni nasan wannan ba tarbiyyar Sageer bace ba, dan ke da shi duk tarbiyyarmu ce”. “Kayi haƙuri Daddy. Nayi kuskure”. Huznah tai maganar hawaye na rige-rigen zubo mata. Shiru Daddy yayi tsahon sakanni. Sai kuma ya ɗan furzar da iska kawai ya ce, “Tashi kije ki gaida iyayenki. ALLAH yay muku albarka”. “Amin Daddy nagode”. Ta faɗa tana miƙewa. Gaban Hajiya Yaya da Ammie taje duk ta gaishesu. Suma sauran ƙannenta suka gaida iyayen Sageer. Daga Ammie har Hajiya Yaya sun amsawa Huznah da kulawa sosai, suka sanya mata albarka, tare da addu'ar ALLAH ya sauketa lafiya. Ita dai kanta a ƙasa, damuwar mahaifiyarsu ce ke ci mata zuciya. A mamakin kowa sauran ƴan uwanta na ɗakin Hajiya Yaya duk sai suka nuna murnar ganinta, har manyan na tsokanarta. Suma su Waleed suka gaisheta. Sanyi sosai Huznah taji a ranta, zuciyarta cike da mamakin canjawar abubuwa da yawa na gidan. (Shin kodai ƙaddarar data faru ce ta sanya su komawa haka? Gafa yanda Hajiya Yaya ta canja kamar ba ita ba) abinda take ayyanawa a zuciyarta kenan... Sun fara cin abinci cike da raha babu jimawa sai ga Hajiya Basariyya ta faɗo musu rai a ɓace. Da wata irin tsawa ta shiga kiran sunayen yaranta. Kafin ta ɗora da faɗin, “Dan ubanku da iznin wa kuka zo nan?”. “Da izinin ubansu”. Daddy ya bata amsa kai tsaye. Kafin ma ta sake wata magana ya nuna mata ƙofa. “Ko ki fita anan, ko yanzu nan na baki mamaki irin wanda baki taɓa zato da tsammani ba”. Matuƙar ɓaci ran Hajiya Basariyya yayi, sai dai yanda Daddyn yayi da ganin yana neman kunyatata gaban kishiyoyi da ƙanensa da facaloli yasata juyawa ta fita tana ji a ranta yau duk sai taci uban yaranta. Koda ta koma sashenta kai-kawo ta dingayi kafin takai zaune cikin kujera tana faman girgiza ƙafa da kallon ƙofa. Sai dai shiru kake ji babu alamar yaran zasu dawo ma....
A nan kuwa babu wanda ya sake magana kowa ya maida hankalinsa ne ma a cin abinci. Sai dai banda Huznah da damuwa tai mata yawa. Kasa haƙuri Sageer yayi, dan hankalinsa duk yana akanta. Cikin sanyin murya ya ce, “Baƙya son abincin ne?”. Kasancewar bai ambaci suna ba kowa sai ya ɗago musamman yaran, sai dai ganin hankalinsa akan Huznah yake sai suma duk suka juya suna kallonta. Itama a karo na farko ta ɗan ɗago ta kallesa. Sai kuma ya girgiza masa kai muryarta na rawa ta ce, “A'a ina so”. “To kici”. Ya sake faɗa da kulawa. Kanta ta jinjina masa. Daddy da sauran iyayen da sukai kamar basu san mi akeyi ba kowa sai ɗan murmushi yake yi. Itama Huznah sai taji sanyi a cikin ranta. Karo na farko taji wani abu mai nauyi a ƙasan zuciyarta game da Sageer. Ana gama cin abinci ƴan Kano sukai haramar wucewa. Jin cewar anan zasu bar Huznah Daddy yace a'a. Sageer ya ɗauka matarsa su tafi. Amma sai Baban Sageer ya ce, “A'a baza ai hakaba Yaya. Kayi haƙuri bawai zanyi jayayya da kai bane ba. Yana da ƙyau a barta tai kwana biyu a gida ta gana da ƴan uwanta. Ai tayi ƙoƙari sosai. Bayan salla idan ALLAH ya kaimu sai yazo ya ɗauketa su tafi.” Ammie tasan halin Daddy sarai da dagiya, haka ma Hajiya Yaya sai suma suka haɗa baki suna lallashin Daddy ɗin. Dole ba dan yaso ba ya haƙura yay shiru. Shi ko man Sageer nata addu'a a ransa ALLAH yasa kada Daddy ya yarda. Sai dai addu'ar tasa bataci ba. Miƙewa yay ya fita tsakar gida, ya aiko Hameed da suka fita tare yay masa kiran Huznah ɗin. Batayi ko musu ba ta tashi ta fita. Tunda ta fito yake kallonta, harta iso inda yake tsaye a barandar sashen Yazeed. Sanin kowa yana ciki tana isowa gabansa kawai ya jawota ya rungume cikin jikinsa. Ya saki wata ajiyar zuciya mai ƙarfi, yayinda Huznah ke mutsu-mutsun kwace kanta duk da tana tsoronsa. Kamar ba Man Sageer ba cikin sanyin murya kamar ɗazun ya ce, “Please mana Sweetheart. Baƙya jin tausayina ne? Kin san fa zanyi kewarki sosai.” Yanda yake mata maganar da halin nauyin zuciya da take a ciki yasata jin zata iya haƙure masan. Sunfi mintuna biyu kafin ya saketa. Baya ta ɗan ja kaɗan daga kusa da shi. Yana binta da kallo shi kam. Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Mike damunki ne? Nasan dai ba haka muka baro gida ba dake. Kuma har muka shigo cikin gidan nan ma ba haka yanayinki yake ba. Ga fuskarki da sayin mari....” Karo na farko ta ɗago ta kallesa, ganin yanda ya tsareta da idanu sosai sai ta sake ɓata fuska ta ɗauke nata. Kansa kawai ya ɗan girgiza, dan tun ɗazun ya gama ji a ransa Mahaifiyarta ce ta mareta, ba kuma ya son yimata shishshigi akan mahaifiyar tata, wani gefen kuma baya son yin ko maganar Basariyya ma a gabanta dan wlhy zai iya danna mata zagi. Ya tsani matar ƙwarai-ƙwarai da gaske. Waya ya ciro a aljihunsa ya miƙa mata. “Ga wayarki, na canja miki layi, hakan na nufin bana buƙatar sake ganin number kowane namiji a ciki. Ga amanar cikina nan na baki Huznah, dan ALLAH, dan girman ALLAH duk tsanani kada ki bari a cutar min da shi. Ke dai kin san irin wahalar da kika sha kafin cikin nan ya zauna, na tabbata kuma ko baƙya sona kina son ganin gudan jininki kema a duniya. Huznah idan har kika bari wani ya baki shawarar salwantar da cikin nan ki sani tamkar kunyi kisan kai ne.....” A birkice ta ɗago tana kallon sa. Ya jinjina mata kansa. “Tabbas abinda na faɗa haka yake, dan duk abinda ke a cikinki zuwa yanzu an gama busa masa rai Huznah. Dan haka salwantar da shi na nufin kisan kai ne, kuma wlhy, wlhy na rantse miki da UBANGIJI NA bazan yafe ba, ba kuma zanyi ALLAH ya isa bane kawai, zan kaiki kowacce irin kotu domin haƙin ɗana ko ƴata. Shiyyasa ina mai sake baki shawara, ina kuma roƙonki da duk wani abinda kikaga yafi ƙarfinki ki sanar dani a waya. Na baki dama kiyi sati biyu in sha ALLAHU zan zo da kaina na ɗauke ki bayan salla da kwana huɗu. Zan saka miki kuɗi a account ɗin ki, bana son ki ɗaurama kowa lalurarki koda ta son cin wani abu ne da za'a a fita a sayo a waje na kwaɗayi. Ki kuma dinga ƙoƙarin barin wayarki a buɗe zan dinga kiranki akai-akai in sha ALLAHU.” Hawayen dake zubo mata ta share. Sai shima ya matsa ya sake rungumeta, sannan yasa handky ya share mata hawayenta tas ya sumbaci kumatunta da lips ɗinta. Lokacin da suka dawo inda su Daddy suke har su babansa sun shiga mota. Shima sallama yay ma su Ammie da su Daddyn ya shiga motar suka wuce idanunsa akan Huznah da itama ta kafeshi da kallo irin wanda bata taɓa masa ba a gidansa. Sai kallon ya tsaya masa a rai sosai har suka kama hanyar Kano yana zane a cikin idanunsa da zuciyarsa...........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣4️⃣1️⃣
______________
..........Maanal na zaune a falonta waya take da Didin ta Amaal da Shahidah ta video call a laptop. Bayan sun gama gaisawa cike da tsokana Amaal tace, “Kai Auta cikin nan fa ya miki ƙyau. Kinga wani fresh da kika ƙara. Wlhy skin ɗinki kamar wata ƴar Ethiopia.” Ta riga tasan halin Amaal idan ba faɗa sukai ba bata jin daɗi, dan haka tace, “Duk tsokanar ki yau dai bazan kulaki ba Didi. Cikin lafiya ana zaune ƙalau”. “Tab tsokana kuma. To miye abin tsokana anan. Bayan komai a bayyane yake kowa ma ya sani.” Cikin ɗan faɗuwar gaba Maanal ta ce, “Kai Didi dan ALLAH ki bari. Ni banda komai ALL......” “Karma ki rantse hajjaju. Wai kina nufin baki san da cikin bane ba? Bayan kowa ya gama sani kice ke baki sani ba kar ki rainama kanki wayo”. Fuskar Maanal na nuna ruɗani sosai ta kalla Shahidah dake murmushi. “Didi kinganta ko. Kice mata ta bari bana so. Kawai daga aure sai ciki sai kace wata mayya”. Wata shegiyar dariya ta suɓucema Amaal har da hawaye, Shahidah kanta dariyar ke son zuwa mata tana danneta da tsiya-tsiya. Ta ce, “Auta manta da ita, kin san dai halinta ai. Amma gaskiya ta faɗa miki kina da ciki. Ke kanki baki jin canji a jikinki, ko ciye-ciyen da kikeyi ai ya kamata kiyi tunanin hakan.” Ba ƙaramin waro idanu waje Maanal tayi ba, ta kalli cikinta ta kalli Yayun mata. Sai idanunta sukai rau-rau da hawaye. Haba kwana uku ke nan abin duniya ya isheta saboda rashin ganin period ɗinta. Sai ciwon da take ji mararta na mata har ma take tunanin zuwa asibiti a kan hakan. Sai kuma yau ta tashi dai alhmdllh shiyyasa ma ta manta da batun asibitin. Hawayen da suka zubo mata ne ya saka Shahidah faɗin, “To miye kuma abin kuka. Wannan ai abin farin ciki ne Maanal. Yau kece ɗauke da ciki, cikin ma na Ajwaad. Bake ba mu kammu a cikin farin ciki muke. Kullum hirarmu kenan da Ammie. ALLAH dai ya saukeki lafiya. Itama Amal ɗin dake miki dariyar ai cikin ne da ita”. Sai kawai dariya ta suɓucema Maanal itama, ta ce, “Oh Didi Amal keda kikace kin daina haihuwa? Yaya kuma akai haka?”. Harrarta Amaal tayi, tace, “Yanda akai ke da Ajwaad haka nima akayi anan”. Maanal tai mata gwalo tace, “Oho dai”. Kai kawai Shahidah ta gurgiza tana murmushi. Sai kuma ta katsesu da faɗin, “Badai wata matsala ko? Duk da nasan in har kema irin salon cikinmu kika ɗakko a yanzu baki da wata matsalar laulayi kam, sai nan gaba. Dan koni cikin Barrah inaga sai da ya kai wata biyu ma nasan da shi.” Haka kawai sai Maanal taji kunya ma, hannu tasa ta rufe fuska da faɗin, “Didi dan ALLAH abar maganar kawai.” Ƴar dariya Shahidah tayi, Amaal ta ce, “Almuna fun-fun, yanzu ne kuma kika fara jin kunyar mu, bayan nasan kina nan kina ji a ranki kamar ki tashi kita rawa dan farin ciki. Ɗan Besty fa a cikin ki. Inyeee lallai Besty baifa zo da wasa ba. Da yake abin na Besty da Besty ne zuwan farko kawai sai akai ehee”. Karan farko da Maanal taji bazata iya maidawa Amal tsokana ba, sai ma tasa hannu ta kife fuskar laptop. Harga ALLAH kunya ce taji ta kamata matuƙa. Cikinta ta kalla, tare da ɗaura hannunta a samansa ta wani lumshe idanunta. Sai ga hawaye na gangarowa a saman fuskarta. Muryarta na rawar kuka ta ce, “Ya ALLAH Alhamdullah, ashe dama zanga wannan ranar a rayuwata, ni Maanal ce ɗauke da ciki na ɗan mutum, kuma cikin ma na Ajwaad Aliyu Abubakar Darma. Besty na dai ba wani ba, kai jama'a......” Murmushi AA dake sakkowa daga sama yayi, sai kuma ya shiga takowa a nutse zuwa inda take. A gabanta ya zauna saman table ɗin bayan ya janye laptop ɗinta dake wajen, ya kai hannunsa shima ya ɗaura a saman nata. Da sauri ta buɗe idannunta tana kallonsa, suka zubama juna ido cike da wani irin rauni da soyayya. Cikin taushin muryar dake fita acan ƙasan maƙoshi ya furta, “Nima kina so nayi kukan ne?”. A hankali tai ƙasa da idanunta, tare da duƙar da kanta, shima sai ya ciri tissue ya miƙa mata. Batayi musu ba ta amsa ta share hawayen, har lokacin hannayensu na'a saman cikin. Ta ɗan zubama hannayen ido, sai kuma a hankali ta ce, “Miyasa ka ɓoye min? Baka son muyi murna tare? Baka son nima nasan na zama uwa? Baka son nasan ina tare da gudan jinin Besty na, my half......” “Kiyi haƙuri ban ɓoye miki ba, nafi kowa son mu kasance da farin cikin wannan ni'imar da UBANGIJI yay mana a tare Besty, na ajiye wannan sirrine domin yi miki surprise shiyyasa. Sai dai wani ya min shigar sauri. Amma Besty ko ƴar kunya babu ɗan fari ne fa”. Murmushi ta saki a karo na farko, sai kuma tasa hannu ta rufe fuskar tata da ƙoƙarin miƙewa zata gudu. Dariya ya sanya tare da riƙeta. Tana zame-zame bai saketa ba ya koma inda ta tashi ya zauna yana ɗorata a saman cinyar sa. Son cire hannun nata yake taƙi yarda, sai ma ta kife kanta a ƙirjinsa kawai. “Shike nan na bari, na kuma yarda ana kunyar ɗan fari. Wai ya kaga Besty a labor room”. “Yanda akaga kowa mana. Ko ka zata ni raguwa ce”. “Ni shaida ne Besty na ba raguwa bace ba”. Ya faɗa a cikin kunnenta. Murmushi tayi itama tana ɗagowa, da wani sassanyan kallo ta kashe masa ido ɗaya. Tare da faɗin, “Ashe dai ka gane”. Murmushi ya sake saki, ya kamo fuskar tata cike da shauƙi da soyayya ya manne lips ɗinsa akan nata, idanunsu cikin na juna ya fara sumbatar ta, sai kuma ta lumshe natan a hankali dan bata iya jurar kallon cikin idanunsa sam. Suna da wani sirri na musamman mai ruguza nata dukkan kuzari a duk lokacin da ya tsareta da kallo da su. Sunyi matuƙar shagala a falon har sun kai wani matakin da basu farga sun kai ba, sai da ƙurar ta lafa ya tasata da tsokana da dariya, itako tana masa shagwaɓa da faɗin ya gama da ita, dan abin kunya a falo. Cak ya ɗauketa sukai bedroom yana dariya cike da ƙeta. Dan bawai bata jin jikin bane ba a hannunsa, ba kuma tana iya dauriyar bane ba har yanzu, kawai dai Babynsa na taimaka masa ne wajen samunta yanda ya kamata batare data farga ba, sai daga baya kuma ta dasa masa rigimar tata, shiko baya gajiya da lallashi.....
__________★