Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 119
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 119: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 119. ............“Barka da zuwa…
4,435 words
............“Barka da zuwa Baa!”. “Barka dai Son. Fatan na sameka lafiya?”. Mabera ya faɗa yana bin ɗakin bacha ɗin sille da kallo. Shima Sille ɗakin yabi da kallo, sai kuma yay ƴar dariya da faɗin, “Normal ne Baa.” Mabera ya jinjina kansa, kafin ya kafe Sille da ido. “Yanzu Son bazaka bar cikin tsohon companyn nan ba ko? Na gaya maka zama a wajen nan akwai haɗari, sannan kowane jaki da doki zai maka kallon wani ƙasƙantacce ko karen ƴan siyasa ne. Amma ka kasa fahimta ta. Kaje ka kama hotel na shekara guda yafi min”. “Hummm Baa! bazaka gane bane. Shifa mugu shine yasan makarantar mugu. Idan naje hotel na zauna ya zan yi da waɗan nan karnukan farautar nawa ne? Idan na barsu su kaɗai anan ALLAH kowane banza ma zai kawo musu hari ne musamman waɗan nan masu baƙaƙen kayan. Kawai ka barni anan ina samun yanda nake so, kallifa ɗakin nan, minene marabarsa dana hotel ɗin. Ac yaji, solar taji, daga waje ne kawai zaka ɗauka bacha, amma a ciki ko ɗakin Kamila ai albarka”. “ALLAH ya shirya min kai Son, Kamila fa itace ta kamilo min kai duniya tun karana bai kai tsaiko ba.” “Hhhhhh!! Kai Baa, kuma fa kun tsula tsiya a ƙarninku dai-dai gwargwado. ALLAH dai yasa tuban da akai yanzu ya zama kaffara ce. Muma ALLAH ya maidamu danshin ku mu tuba a dai-dai muna cika 45, dan kasan shifa walakirin lahirar nan ba gajiya suke da ɗimar mutane ba. Kar muje ana hayya-hayya a aljanna mu muna ƙofar gate ana bamu horo, ai al'amarin baiyi daɗi ba wlhy. Koda yake koda rinto da wawa ai sai munje kusa da MANZON ALLAH”. “(S.AW). ALLAH to yasa. Amma gaskiya to, ba'ace komai ba dai Son, kasan nima dai nayi islamiyyar nan kiranyen sheɗanne kawai kasan shi mai rabon wahala yake ɗauka. Amma dai kai, anfayi al'amura, koma ace ana kan yi, amma dai gab muke ai da tuba ba komai. Yanzu yaya kuke ciki da Kamila?.” “Hhhhh sai da kai Baa! Langa-langa mugun ƙarfe, ƴan gwangwan na rainaka amma shine uwar cinikinsu. Rumfa makara ɗaki, ko baki kare ɗan kwarai ba ƙya kare shege, yo shima ai shegen da ubansa tunda ba'a ruwa ko a tuwo uwar ta shawosa ba ko taci. Kaga ƙwan jimina ba'a ganinka sai gidan masu kuɗi, coge takalmin mata gajeru na rubibinka dogayen ma sakawa suke dan su ƙara tsayi. Marfin tukunya mai rufe sirrin ƙazamar miya koda arniya ce ta rufu, kaga Junaid, baban Junaid mijin Sabuwa baban Nazifa da Sa'adatu. Ogan Kamila kota amsa ko jiki yay tsami”.. “Son baka da dama ALLAH yanzu mike tafiya a wajen Kamilar? Menene shiri ka kuma”. “A gareni komai normal ne, a gare ta kuwa tana can tana haukar nemana yanzu haka. Dan na toshe ko'ina. Sai dai ina samun imformetion ɗin komai a wajen Turai ”. “Turai? Son har yanzu kana tare da Turai ken nan?”. Kai Sille ya sauke ƙasa yana shafa keya. Ya ce, “Baa matar nan fa nada amfani sosai a garemu kaima ka sani. Kayi haƙuri ka yafe mata wancan kuskuren da tai....” “Amma kasan wacece Turai ai ko”. “Na sani Baa, kar kuma ka damu dan a tafin hannuna take wlhy, a yanzu haka komai daya shafi mijinta har mutuwarsa na sani, shiyasa ko ɗar bana ji a kanta dan har yanzu abinda naso ta sani kawai take sani. Kamar yanda kai treating ɗinta a baya nima haka nakeyi yanzu. Kasan mugu shine ya san makwantar mugu.” “Hakane. Shike nan ina jin ka.” “Yauwa normal ne Baa. Kamar dai yanda na gaya maka tsarin wasan a baya shine......” tsaff ya sake maimaita masa komai da suka tattauna a waya ranar. Mabera ya jinjina kai da sauke ajiyar zuciya. “Tsarinka duk yayi, sai dai dole ne mu canja dukkan wasan. Dan a yanzu mun zo wata gaɓa ne bata hawainiya ba gudun barewa zamuyi. Kamar yanda ka faɗa yaron nan Ajwaad shege ne. Kasan iya buge-buge na har yanzu mun gagara sanin ina ƙanwarka take da Yazeed. Ƴan sandan ma suna neman maidamu mahaukata. Yanzu haka zancen da nake maka Sabuwa na kwance a asibiti kwana biyar kenan. Daga ni har ita Chalawa ya hana a barmu mu shiga gidansa, ƴan sanda ma ke gadin gidan. Hakama yaransa makarantar boko da islamiyya jami'an tsaro na tare da su. Matansa ma idan zasu fita haka ne. Matarsa ce ta tsakkiya ce dai ma jiya kaɗan ya rage na cafketa a asibitin doctor Dev.. sai kuma na fasa dan na fahimci akwai abinda take ƙullawa. Kasan shegiya ce itama, kuma ta hasala ƙwarai da gaske akan kwasar kayanta musamman da Yazeed ɗin bai iya kwaso na amaryar ba sai take tunanin da sanya hannunta a ciki. Shiyyasa a yanzu haka na shirya yin aiki da ita, kuma nan da kwana biyu kacal nake so ta shigo tarko na.....” “Sai da kai Baa! Shiyyasa bana gajiya da maka kirari dan ka cancanta, ALLAH kuwa ubana yafi na kowa dan nawa kowace ɓaranɓarama ya haɗa. Ga ilimin bokon gana arabi amma yafi jahili jahilci. Ka tafka tsiya a ƙarƙashin ƙasa a zahirin rayuwa ko damo baya nuna maka haƙuri sai jinin Mabera tushen aiki...” Wata dariya Daddyn Nazeefa ya sanya mai ƙarfi, Sille na tayasa da iya iyawa, sai kuma suka cafke. Cike da so da ƙauna ya ce, “Son ALLAH yay maka albarka, in dai bakin iyaye nada tasiri akan ƴaƴa koda kuwa iyayen tantirai ne to kai dai bakai babu taɓewa. Dan kamar uban kamar ɗansa, idan kaji ana ainahin TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE to Mabera ne da ɗansa, wato Junaid ɗan Junaid ”. “Yess Baa! Sai da kai. Fitaaaa manaaaa!”. “Tuni na fice Son. Dan haka bayan wancan shirin nawa naka wasan na haɗaka ne ni da kai. Manta da wannan video ɗin bazai baka kuɗin da kake buƙata ba aiki zamuyi mai ɗungum a lokaci guda da zai mallaka mana Alhaji Usman Chalawa da da tsohon Ambassador kuma ɗan kasuwa Alhaji Aliyu Abubakar Darma, abokin ƙuruciya kenan, rayuwar jami'a ai ba wasa ba, wannan abotar tamkar ƴan uwan taka take. Lokaci yayi da zan maida murtani da ƙarfin ƙwanji, sannan da ƙarfin basira. Ta ƙarshe Kamila, itace zata fi kowa amsar sakamakon wannan wasan, dan gaba ɗaya ma wasanta ne, Aliyu Darma ya biya nashi tuni harda gyara, yanzu albarkacin ta zaici shima shi da ƴaƴansa” Wani irin cafkewa sukayi kamar ba uba da ɗa ba. Daga haka Mabera ya fara tsarama Sille bayani filla-filla.....
_________★
A can Sille da ubansa na ƙullawa, anan Kamila ma ƙullawar take yi. Dan shiri take yi sosai na wasan ƙarshe akan Oum, Abah, da yaranta uku zaratan mazaje. Plan b Nana da ƴaƴanta. Sille da mahaifinsa sune plan c ɗinta in har ta tabbata Junaid na a raye dolene ta maidashi gaba da inda ta aikashi a baya. Dan haka a yanzu shiri ne na gaske, dan ta shirya karɓa daga rasa Aliyu Darma amma kuma dole ne ta tsira da Fadeel, Fawzan, Ajwaad Aliyu Abubakar Darma. Dan bazata yarda tai 2-0 ba. Sai dai Fateema ta ɗauki wannan makin wlhy. Dan tabbas in dai tana raye dole ne Fateema ta rasa ALIYU DARMA, da ƴaƴan ALIYU DARMA. Ita zata mallaki ƴaƴan, Aliyu ya mutu, Fateema ta ƙarasa rayuwarta a ciwo. Dan bazata taɓa rayuwa a wannan duniyar Aliyu Darma na raye shima a wannan duniyar ba tare da wata ba ita ba. Dan haka kowa zai rasa, sai dai ita zata tashi da ƴaƴan Aliyu Darma kamar yanda ta faɗa. Tai wani makirin murmushi, fuskarta data gama lalacewa da rama na sake bayyana tayani muninta a fili.....
________★
“Mama magani ya iso yau da safe yaya tsarin yake ne?”. Saheeba ce mai maganar tana leƙe-leƙe gudun kar wani ya jita. Daga can Nana ta ce, “Duka kowa akwai tsarin da zaki bashi nashi batare da fahimtar kowa ba. Amma yanzu zaki fara da matar Ajwaad ne. Dan zubar da cikin jikinta zai saka hargitsi da tashin hankalin mutanen gidan ta yanda zakiyi amfani da ruɗewarsu ki ciyar da sauran nasu tsarin. Saheeba kada kiyi wasa. Ki nutsu dan ALLAH kiyi abinda ya dace. Kinga kayan nan kaf abinda na tara na kadara da wanda kema kika saya ne dana Nuratu harda aron kuɗi na sake yi a wajen Hajiya Turai duk na haɗa. Dai-dai da sarƙoƙin ki na gwal da jarin sana'arki duk suna a wannan kayayyakin, to ku lura ke da Nuratu, kuyi komai da lura dan abinda muka rasa ba komai bane kamar yanda malam ya faɗa. Muda babban kaya zasu shigo hannunmu a dare ɗaya. Kedai kiyi komai da lura musamman akan Kamila, kin san dai shegiyar kanta ce matar nan a ɓangaren gina sharri da tuggu da mugunta da makirci kanta naja matuƙa. A yanzu haka dukkan motsinku akan idonta ne. Kamar yanda suma sauran mutanen gidan na tabbatar duk da wannan kwantar da kan naku bawai sun yarda daku bane ɗari bisa ɗari”. “Hakane Mama muma mun san hakan, musamman shegiyar Maanal ɗin nan wlhy ƴar bala'i ce yarinyar, yanda kika san aljana haka take. Akwai wankakken ido da kwalwa mai kaifin haddace da gane abu. Yanda kika san tana ji a jikinta, shiyyasa ma nake tunanin kamar tana da aljanu”. “Aiko zamu sauke mata su”. “Nima haka nace Mama, sai batun Daddyn Naufal, Mama har yanzu duk da yace ya haƙura ko ɗakinsa naje baya ko taɓa ni, wlhy duk a matse nake da shi na rasa yanda zanyi. Amma shi ko'a jikinsa saboda ya samu wata sai da ya kwanta ya shari barcinsa hankali kwance.” “Karki damu wannan aikin nasa shima mai zafi ne, in dai kin jure kinyi yanda ya dace, yanda kikaga ubanku baya iya tsallake karan dana gitta haka shima zai koma miki.” “Kai da naji daɗi Mama aiko nagode sosai. Kunnenki ya zama a buɗe, hakama wayarki, dan a kwana a biyun nan kacal dole kiji karam kwacam ɗan Ajwaad yabi rariyar ruwan gidan DARMA”. “Dako na kwana ina saka miki albarka. Dan haka sai na jiki, amma nafi son komai ya kankama ranar salla zaifi bada amrmashi”. “Yanda kika ce haka za'ayi Mama”. Nana na yanke wayar Saheeba tai wata dariyar ƙeta da faɗin, “Lokacin yaƙin basasa a gidan Darma yayi, Maanal dake wasan zai fara a ranar babbar salla”.............✍️
🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🙆🏃🏃🏃🏃🏃🏃🏃🏃Yau ba magana nayi Nan. Lamarin Saheeba da Nana, Sille da Baa ɗinsa, Mamy ai shiru na ma shine zaifi alkairi kawai kuma kun sani😮💨.
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣4️⃣5️⃣
______________
...........“Wai saurin mi kake yi ne haka? Naga kamar ma farin ciki kake zaka fita ka barni a gida”. Murmushi AA yay yana mai saka maɓallin jikin gab da wuyan rigarsa. Ƙiri-ƙiri an maida shi mai saka manyan kaya na dole. Sai in office zaije ne kawai yake tsira. Fuskar Maanal dake ta ɓata fuska hannunta rike da lins ɗinsa ya shafa, cike da lallashi ya ce, “Haba Matar AA ina ni ina murna zan tafi nabar zuciyata anan. Kinfa ce kin haƙura. Kuma bazan daɗe ba awa biyar in sha ALLAHU na dawo gida”. “Hu'umm! Harma awa biyar? Ni ban yarda ba sai dai mu tafi tare”. “Kin fasa raka Oum anguwar kenan?”. “Ohhh to na haƙura. Amma gaskiya ban yarda awa biyar ba”. “Shike nan yanda kika ce haka za'ai, samun lins ɗin kinga ana jirana. Kuma na gaya miki mai jiran nawa yana da muhimmanci sosai”. Hannunsa ta kama ta sanya masa, sannan ta ɗauka turare ta fesa masa. Duƙe yakai a hankali ya sumbaci cikinta, tare da faɗin, “My Baby kaima kaima Abbie addu'a okay, mi kake so a saya maka?”. “A saya masa fura da kilishi”. Manaal ta faɗa. Murmushi AA daya ɗago yana kallonta ya saki, sai kuma ya tashi tsaye yana da faɗin, “Besty kiji tsoron ALLAH, wannan saƙon nashi ne ko naki”. “Nashi ne mana, bashi yake sakani ƙwaɗayin son ci ba”. “Haka ne kuma My Ever-Bloom”. Ya faɗa yana sumbatar lips ɗinta. Itama ɗiɗɗishe tayi ta sumbaceshi. Zai cafke tai saurin ja baya tana dariya da faɗin, “Kaida zaka fita”. Murmushi kawai yayi, ta kama hannunsa suka fita takalmansa a hannunta. Sai da suka sakko down stairs ya zauna ta jame slippers ɗin ƙafarsa na zaman gida ta saka masa takalman. A hankali ya furta, “ALLAH yay miki albarka”. “Tare da kai Autan Oum da Abah”. Murmushi yayi yana mai girgiza kansa. A yanzu kam shine ya kama hannunta suka fito har inda motarsa take. An gogeta sai ƙyalli take. In dai ba office ba ko tafiya kai nisa shike tuƙa kansa duk inda zaije. Shiyyasa da wahala ma weekend kaga drivern sa a gidan. In ma tafiyar da babu shiri ta kama sai dai yay kiranshi a waya. Har ya shiga mota ya zauna hannunsu na riƙe da juna. Manaal sai ɓata fuska take. AA dake kallonta ya ce, “Besty kinfa girma ki rage rigima. Ko haka Babyn zai zo kinayi yana yi? Hana zuciyar Ajwaad, ba nace zan dawo da wuri ba. Kuma fa fita zakuyi, kuma kiyi tuƙu a hankali kinji ko kuma driver dai zan kira?”. “A'a basai ka kira shi ba, ai harda su Ameerah zamu je sai cikinsu wani yayi driving ɗin”. “Hakan yayi.” Ɗan duƙowa tai ta cire masa gashi a wuyansa. Kafin ta saki hannunsa tana masa addu'ar dawowa lafiya. Murmushi ya mata yana amsawa ya gyara zamansa, ta rufe masa motar. Glass ya ɗan sauke yana kallonta. Tai murmushi da faɗin, “Ka yafi to”. “A'a ki fara tafiya dai ina kallonki”. Tai ƴar dariya. “Kana tsoron a sace ni ne?”. “Duk wanda yace zai yi hakan ai ƙaryarsa tasha ƙarya Zuciyar Ajwaad.” Murmushi ta sake yi, kafin tai wata magana kira ya shigo wayarta. Nene ce dan haka ta nuna masa wayar tana faɗin, “Hajiya Nene ce”. “Wannan hajiyar da kike kiranta da tsokana baɗi sai taje ta zama tazo ta rama. Ki gaida min da ita bye”. Manaal dake dariya ta ce, “Ya kaga Nene a makka, askarawa dai zasu sha fama”. Reverse yayi yana murmushi, kafin yazo ta sautin ta ya ɗaga mata hannu sannan ya wuce itama tana ɗaga masa. Ji suke kamar kada su rabu.... Kiran Nene ya katseta, dole ta yanke ta kirata, dan tana ɗagawa ma zatace mata idan ta cinye mata kuɗi sai ta biyata. Tana gefe tana wayar kusan mintina goma da fitar AA Sille ya shigo gidan, sam bata lura da shi ba, dan haka ta nufi sashen Oum tana ma Nenen tsiya. Shi kuma ya rufe fuskarsa da hula gadan-gadan ya nufi sashen Mamy ne kuma ta inda Maanal take tanan dole zai bi. Sai da suka zo gab da juna sannan kowanne ya farga. A irin bazatan nan Sille ya ɗan ɗago, itama Maanal ɗin haka ta ɗago zatace sorry suka haɗa ido. Da sauri ya janye nasa, ya raɓata ya wuce batare da yayi magana ba. Itama sai tai kasare tana binsa da kallo. Zuciyarta fal tunanin tabbas tasan wannan fuskar, amma a ina?. (Gidan Hajiya Turai) Brain ɗinta ta tuno mata. Kanta ta jinjina da faɗin, “Yes exactly”. “Miye wani yas ezatali. Kinga Manaluwa ki kiyayan”. Nene ta faɗa daga can. Maanal ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Oh Hajjaju Nene bafa dake nake ba. Ni dai bara na haɗaki da Oum ɗin.” “Ohh ai nazata da ni ɗin kike.” Kai kawai Maanal ta girgiza idonta akan sashen Mamy da mutum ya shiga, sai kuma can ƙasan zuciyarta ke ayyana mata maybe wajen Nuratu yazo. To amma har cikin gida dan rashin mutunci. Wannan mutumin mai ruwan kafirai, yaushe ma lalacewar gidan nan takai haka. Sai kuma ta juya tana kallon gate, Haule ta gani tana shigowa da leda a hannu, babu maigadi a wajen alamar ya shiga bayi ko cikin ɗaki. Kamar zatai magana sai kuma masifar Nene ta sake katseta. Dole ta saki batun ta shiga ciki kaima Oum wayar... A mamakin Maanal koda mata shigo Nutatu na nan a sashen Oum. Ameerah na gyarama Anum kanta Najma gefenta tana bata ribbons. Sai Nuratun kwance a kujera tana kallo....
________★
A sashen Mamy kawai ganin Sille tai a kanta kawai. Dan tana zaune a falon sama ne ita kaɗai kamar mayya tayi nisa a tunani sosai. Firgigit ta kallesa zuciyarta na harbawa. Sai kuma ta sake zabura tana kallon bayansa da sauri. Cikin ɓacin rai ta ce, “Amma baka da hankali ko? Kai wane irin daƙiƙi ne wai zaka dinga shigo min gida kai tsaye?”. Zama yay kamar bai jita ba, ya ɗauki kwalin jus data ajiye ya cire murfin yasa a baki yasha sosai. Sai kuma ya dire a inda ya ɗauka yana kallonta. “Kin san idan ni daƙiƙi ne a wajenki nayi gadon daƙi ƙancin. Gida kuma na Darma dai dan ke kam bana jin zaki amfanu ma da komai na cikinsa. Koda yake idan kin min yanda nake so maybe ki samu ɗin.” Tsaki mai ƙarfi Mamy tayi da galla masa harara, sai kuma fuuu tai yunƙurin barin masa falon. “Amma kin san ko bayi kika shiga kika tuɓe wlhy sai na biyoki, garama ki dawo muyi magana dan nima banda isashen lokaci”. Cak Mamy ta dakata zuciyarta na wani irin dokawa da ƙarfi saboda kalamansa, ita kam dai ta shiga uku da wannan mutumi. Ta tabbatar zai iya aikata abinda ya faɗan, dan haka ta dawo cike da borin kunya ta ce, “Yau kuma uwar mi kazo da shi”. Sai da Sille yay wata irin dariyar data saka Mamy daburcewa tana kallon ƙasa da faɗin, “Wai baka da hankali ne sai wani ya jika”. “To miye, ba sai kowa yaga babban ɗanki ba.” Mummunan kallo ta watsa masa ta ɗauke kanta. Shima sai ya taɓe baki tare da ɗage kafaɗa ya ce, “Kuɗi nake so”. “Ko kuma uban kuɗi ba”. Mamy ta faɗa a harziƙe. Hankali kwance Sille ya ce, “Dazan samu uban kuɗin ma ai da nayi murna. Dan haka ki bani kuɗi, in ba haka ba kuma zaki sha mamaki. Dama masu gadi sun sanar min Darma na gida”. Kallonsa kawai Mamy ta tsaya yi, zuciyarta na wani irin motsawa. Bata son abinda zai katse mata aikinta da kwanaki tara kacal suka rage mata, gara ta bashi ya tafi ya barta, ita da zata mallaki ninkin abinda yake nata sau ɗari miye na damuwa. Da Abah ya mutu fa dukiyar duk tata ita da ƴaƴanta. Fateema da timilin takaba kawai zata tashi, itama bata raba ɗayan biyu bayan kwanaki tabi bayan Aban tunda ji suke kamar ɗaya zai iya mutuwa idan babu ɗaya. Kinga tata dukiyar itama mallakin ƴayanta zasu zama daɗi kan daɗi kenan. Sai kawai ta saki wani makirin murmushi tare da ɗaukar wayarta. A take ta masa transfer na 50m. Shi kansa Sillen ɗagowa yay yana kallonta da mamaki. Ta ɗage masa gira tana murmushin. “Na baka wannan saboda bana son sake ganin fuskarka a gidana ko inda nake. Idan kuma ka sake zuwa duk abinda nai maka kaine kaja. Shashasha kawai, oya get out of here”. Kallonta sosai Sille keyi, sai kuma ya saki wani makirin murmushi, batare da yace komai ba ya miƙe tsam ya gyara hularsa, sauran lemon ya ɗauka ya shanye ya wurga kwalin gabanta sannan ya fice. Mamy ta raka bayansa da harara tana jan tsaki. A ranta faɗi take (Zanyi maganinka. Bari dai a gama binciko min inda uban naka yake. Duk ma gidan ubanda ya samoka yace maka nina haifeka sai ma baku mamaki kai da shi.” Daga haka tai hanyar bedroom. Tana shiga ta samu ɗayar wayarta na ring. Ƙarasawa tai ta ɗauka da sauri dan tasan wanene zai iya kiran nata. Ilai kuwa shine. Tasa a kunne tana kallon ƙofarta, sai kuma ta nufi closet ta shige bedroom sannan ta ce, “Ina jinka Amo. Yaya akayi?”. Daga can wanda ta kira Amo ya furta, “Hajjaju kayanki sun iso gasu a hannu na. Ya kamata zuwa anjima ki shigo ki amsa. Idan kuma zaki aiko ne tom ina dai jira”. “Woow thanks you Amo. Fitowata bazai yiwu ba weekend ne kowa yana gida, amma zan aiko Haule anjima kada ka damu. Sai dai a basu tsaro iya tsaro Please”. “Baki da matsala hajjaju, sai tazo”. Mamy ta jinjina kai tana yanke kiran gaba ɗaya fuskarta ta gama washewa da farin ciki. Ji take ma kamar ta aiwatar da aikin nata ne ma. A fili ta furta, “Aliyu Darma kenan, baka san wacece Kamila ba. Saboda da kaza ai baya hana a yanka ta. Dolene ka biya bashin soyayyar shekara talatin da wani abu, ka kuma biya bashin wulaƙanci da fifita wata a kaina duk da kasan na fita sonka”. Sai kuma ta ƙyalƙyale da dariya........✍️
Hummm mi kuke tunanin Mamy ta saka an kawo mata ne?🙆
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣4️⃣6️⃣
______________
.......AA kam kai tsaye gidan Daddy ta nufa, inda suka ɓoye Yazeed. Dan tun a washe garin da aka kamashi shi da Nazeefa aka taho da shi Abuja. Ita kuma tana can a kadunar wani gida, an ajiye tsohuwar dake kula da ita. Ba yau AA ya fara zuwa gidan ba, ba shi kaɗai ba hatta Abah da su Babban Yaya suna zuwa. Dan sosai aka dage akan Yazeed kuma alhamdullahi ana samun abinda ake so yanda ya kamata. Dan ya dawo hayyacinsa yanda ya kamata sai dai abinda ba'a rasa ba dan harkar sihiri wuya gareta. Daddy dake kallon AA da murmushi ya ce, “Son ka ƙaraso?”. Shima AA yana murmushin ya ce, “Eh Daddy, ina kwana”. “Lafiya Lau Alhamdullah. Ya ƙoƙarin ku? ALLAH ya saka da alkairi ya bada ladan zuminci. Ai naga mutuminka jiki ya ƙara sauki sosai gashi har muna hira kuma naga ana kula da ibada”. Murmushi AA yayi kawai, sai ya ɗan kalla Yazeed. Hannu Yazeed ya bashi suka gaisa. Ya tambayesa ya ciwon kan?”. Dan tunda aka dage da addu'oin sai ciwon kai ya gallabi Yazeed ɗin. Ya ce, “Alhamdullah ya iyalin”. A taƙaice AA yace, “Alhmdllh”. Dai-dai nan akai kiran wayarsa. Ya cirota a aljihu yana dubawa. Sai kuma ya kalla Daddy cike da girmamawa ya ce, “Inaga ya ƙaraso”. “Okay to bari nace maigadi ya shigo da shi”. Daddy ya faɗa yana ɗaukar waya yay kira. Babu jimawa kuwa sai ga baƙo da maigadi sun shigo... Wajen zama Daddy ya nuna masa, bayan an gaisa ya dubi AA cike da girmamawa ya ce, “Oga aimin afuwa huldup ne ya ɗan riƙeni a maraba, nayi zaton bazan kai haka ba a kaffi ɗin nan wlhy”. “Karka damu, yanzu ya ake ciki?”. Laptop ɗinsa ya zaro daga jakka yana faɗin, “Alhamdullah munyi nasarar samo yaron a jiya kamar yanda na sanar maka. Sai dai da ƙyar ma muka samu ya iya tuna sakashi akai yayi register ɗin shima kusan shekara biyar data wuce. Sauƙin da muka samu kuma anan cikin kasuwar su abin ya faru, wanda kuma yay masa register ɗin har yanzu yana a kasuwar. Yaso ƙin bamu haɗin kai shima sai da Faisal ya nuna masa I'd card ɗin aikinsa sannan ya tsorata. Sai mukai amfani da bayanan shi register ɗin yaron aka duba duk wanda ya sai layi a wannan ranar. Alhamdullahi mun samu kafin mutumin ya saka yaron wannan aikin shima yayi register a wajen kamar dai yanda yaron ya faɗa mana da farko. Yanzu dai ga hotonsa da sunan da yay register ɗin”. Yau maganar yana miƙama AA laptop ɗin cikin girmamawa. Amsa yay yana dubawa, cikin mamaki ya ɗago ya kalla Daddy, ganin shi yake kallo shima sai ya miƙa masa laptop ɗin. Amsa Daddy yay yana kallo shima cike da mamaki ya ce, “Mabera!”. “Daddy da gaske shine ɗin kenan?”. “Tabbas shine Ajwaad, duk da hoton yayi kusa kuma bai fita sosai ba wannan Mabera ne. Ga sunan ma, Junaid Abba Mabera. Kawai ya fara saka sunan uba ne a farko kafin nashi”. Kamar an bugama Yazeed guduma a kai ya dafe kan nasa saboda jin sunan Baban Nazeefa da aka kira, sai kuma ya shiga ambaton sunan ALLAH. Atare duk sukai kansa suna tambayar lafiya. Ina ya kasa magana, sai jujjuya kai yake, AA da kamar ya harbo jirginsa a nutse yaje kan dining ya ɗakko gorar ruwa na addu'oin Yazeed ɗin ya kawo, bashi yay yana faɗin, “Yazeed kasan Junaid Abba Mabera ɗin ne?”. Ƙara Yazeed ya sake saki. AA ya sake maimaita sunan yana ɗibar ruwan a hannunsa ya zubama Yazeed saman kai. Ai sai ya fasa ƙara gaba ɗaya. Ganin haka sai Faisal da Daddy suma suka cigaba da kiran sunan Mabera. Kawai sai Yazeed ɗin ya yanke jiki ya faɗi a sume. Daddy zai tada hankalinsa AA ya ce, “Daddy ka kwantar da hankalinka. In sha ALLAHU ina kyautata zaton lokacin nasara ne. Da alama an goge masa sunan a memory ɗinsa ne shiyyasa ya kasa tunawa gaba ɗaya, ƙila kuma jin sunan shine makarin sihirin shiyyasa”. “Tabbas oga haka ne, dan nima irin haka ta taɓa faruwa da Yayana kuma kamar dai na yallaɓai ɗin nan da kake gani.” Sosai su Daddy suka jinjina al'amarin, kafin aka zubama Yazeed ruwan addu'ar sai gashi ya farfaɗo. Cikin ikon ALLAH kuma yana buɗe baki sai ya fara da addu'a. Addu'ar Daddy ya tayasa suka ƙarasa, AA ya kamashi ya zauna da ƙyau. Sai ya dinga binsu da kallo. Zuwa can yace, “Daddy zan sha ruwa”. Ruwan AA ya miƙa masa, ya amsa yashanye tas yana sauke ajiyar numfashi. Sai kuma yabi gidan da kallo yana faɗin, “Daddy ina ne nan kuma? Miya faru?”. Ajiyar zuciya Daddy ya sauke, dan ya fahimci yanzu ne Yazeed ɗin yay asalin dawowa a hayyacinsa.......
________★