Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 121
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 121: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 121. Anan Kaduna kuwa abubuwa biyu…
4,207 words
Anan Kaduna kuwa abubuwa biyu ne zuwa uku ke shirin faruwa a lokaci ɗaya. Naƙudar da Nazeefa ta fara batare da sanin kowa ba. Sai shagalin girka abincin salla da akeyi tsakanin ɓangaren Ammie da Hajiya Yaya. Kafin kowa ya fito cikin shirin gayunsa kamar kowace sallar suka wuce massalaci. Ana idar da salla gida sukai yinƙurin nifowa. Banda Hajiya Basariyya da Huznah. Acewarta zasu je su fara gaida Yayanta ita da Huznah ɗin. Su kuma sauran yaran sai gobe. Babu wanda ya kawo komai a ransa har Huznah ɗin. Su Ammie suka wuce gida dan masu aikin raguna sun kira sun iso. Yaran kowa ka kalla yana cikin ɗumbin farin ciki mara misali. Su kansu yaran Hajiya Basariyya da alama tafiyar uwar tasu anguwa tai musu daɗi, dan suna isa gidan maimakon sashensu kai tsaye sashen Hajiya Yaya suka bi ƴan uwansu domin cin abinci....
_____★
Sosai gaban Huznah ya shiga faɗuwa, ganin maimakon gidan kawunsu da Ummin tasu ta faɗa sun nufi hayar wani gida daban. A ɗarare ta yarda suka shiga gidan. Matar gidan ƙabila ce, ta fito ta tarbesu cike da farin ciki. Aka saukesu a falo aka kawo musu ruwa da lemo. Babu abinda Huznah ta taɓa sai ma gabanta ne dake faman faɗuwa matuƙa. Bayan Hajiya Basariyya sun gaisa da matar sai take kallon Huznah, ta ce, “Itace wannan za'a zubar ma cikin?”. Hankali kwance Hajiya Basariyya dake murmushi ta ce, “Ƙwarai itace”. Huznah kam wani irin faɗiwa gabanta yayi, ta kalli mahaifiyarta ta kalli matar jikinta na rawa. Bama tasan bakinta ya suɓuce wajen faɗin, “Ummi zubar da ciki kuma?”. Hararrata Hajiya Basariyya tayi, a kausashe tace, “Ai kema kin san abinda zai biyo baya kenan, dan bazan taɓa haɗa jinin da ɗan Sani ba har abada.” “Amma Ummi ya kai wata biyar fa”. “Koma wata sha biyar ne dan ubansa sai yabi rariya. Oya Doctor zaki iya fara aikin ki dan banda isashen lokaci kin san yau muna bikin salla, yanzu ma nace zanje ziyara ne Na zaɓi wannan ranar ne saboda hankalin mutane bazai kai kanta ba musamman ma ubanta da ƴan sa idon matansa.” “Baki da damuwa Hajiya, komai zai tafi yanda ya kamata. Awa ɗaya ta ishemu dan allurar idan anyi zata ɗauki mintuna talatin ne ma shiyyasa. Idan kuma kin yarda da an mata zakije gida to, na tabbatar sanda zaku isa jinin bai fara zuba ba.” “A'a babu wata damuwa ayi mata anan, so nake ayi komai a gama dan idan mun tafi zan kaita wani waje ne ta zauna sai dare sannan ta koma gida ta gama dawowa hayyacinta”. “Haka ma dabara ce kam.” Kuka sosai Huznah keyi, maganganun Sageer na dawo mata ɗaya bayan ɗaya. Ta zamo a kujerar ta dur ƙusa a gaban Hajiya Basariyya tana kuka. “Ummi dan ALLAH na roƙeki kada ki zubar min da cikin nan. Wlhy ubansa bazai taɓa yafe mana ba dan yaji a jikinsa hakan zata iya faruwa. Ya kuma tabbatar min wlhy sai yabi kadin cikinsa. Koba haka ba ma wlhy Ummi nima ina son cikin, nasha wahala sosai a laulayi. A kwanakin nan ne kawai kike gani na da lafiya kamar haka. Dan ALLAH kiji ƙaina ko tausaya min babyna har ya fara motsi. Motsinsa da nake ji yasa nima na fara jin ƙaunarsa har bazan iya cutar da shi ba.....” Ba ƙaramin zama galala Hajiya Basariyya tayi yana kallon Huznah ɗin ba. Sai kuma ta shiga faɗin, “Eh lallai Huznah yanzu na sake yarda kin auri Sageer. Yanzu ni kike faɗawa haka, ni uwarki har ni kike sanarma Sageer zai bi kadin cikinsa, ke kuma kina son Babyn ki. To shike nan bari na ɓarar da shegen ciki in yaso ke da Sageer ɗin ku haɗu ku kaini kotun ALLAH ya isa. In ce dai shike nan”. “Ummi ba haka nake nufi ba dan ALLAH kiyi haƙuri, kiyi haƙuri koma miye kiyi min amma dan ALLAH banza zubda cikin nan na tuba”. “Aiko sai dai ki mutu, ciki babu fashi sai na ɓarar da shi dan ubanki. Kuma kika sake min magana sai na tsine miki!!!”. Wani irin komawa baya Huznah tayi jikinta na rawa kar-kar-kar........
_________★
Anan gidan Darma komai su Haule sun haɗa sun shirya kamar yanda aka saba. Dukkan abinda Mamy ta bama Haule ta shirya komai a inda Abah zai zauna. Haka ma Saheeba komai sai da ta tabbatar ta saka a gurbin daya dace. Kafin ta wuce sashensu dan bata buƙatar mutanen gidan suzo su sameta....
An idar da salla, kowa ka gani yana cikin farin ciki. Kamar yanda aka saba ahalin Darma sai da sukai hotuna sannan suka shiga motoci suka kama hanyar gida. Duk Mabera na kallonsu kuwa. Sai da suka wuce da kamar mintuna goma sannan shima ya shiga mota yabi bayansu. Sai faman zuba murmushi yake yi dan fuskar Kamila kawai yake hangowa a wannan gaɓar..........✍️
Kunga page ɗin nan kuyi hakuri da shi a hakansa. Wlhy aiki yamun yawa na kasa kaishi yanda nake so. Muhaɗe kawai ranar Monday idan ALLAH ya kaimu. Ina fatan zakuyi salla cikin aminci da ƙoshin lafiya. Karka a manya dani a addu'a awajen sallar idi, da kuma kai da ƙafafu ehe. Ayi salla lafiya. Ina sake bada hakuri da gajartar page ɗin nan na karshe ku bini bashi😘😘😘.
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣5️⃣0️⃣
______________
........Koda ahalin Darma suka iso gida matan ne kawai suka shige ciki. Amma su Abah duk nan waje suka tsaya suka gaggaisa da sauran mazan anguwa da Baba Imam dake musu yankan raguna. Sai da aka kammala yankawa masu gyara zasu fara sannan suka shiga ciki. Gaba ɗaya sun sami ahalin gidan a sashen Oum, abinda yaba Abah da AA mamaki harda Mamy. Kuma yau sai faran-faran take da kowa. Dan suna zaune ne ma suna hira da Oum su kuma su Maanal na hotuna. Saheeba ma ta fito tanata wani yamutse-yamutse ita adole wai mara lafiya. Zaman cin abinci akayi, gaba ɗaya hankalin Saheeba nakan Maanal. Mamy kuwa da kanta yau ta zubama Abah abinci, komai baice ba, bai kuma gwaleta ba dan tasan itama bazaiyi hakan ba kodan yara. Tana kammala zubawa kamar kowa yay bismillah ya fara cin abincinsa. A kusan tare Mamy da Saheeba suka sauke ajiyar zuciya, dan itama dai Maanal ta fara cin nata hankali kwance. Haka sauran ma. Ran Oum fes yau Mamy ta saki ranta family ya cika yanda take fata. Gashi anata hira da raha gwanin sha'awa. Suna gab da kammala cin abinci Bola ya shigo sashen Oum ɗin bayan ya nema izini, cikin girmamawa ya sanar ma Abah yana da baƙo. Dan shiru Abah yayi na mamaki dan yasan baiyi da kowa zaizo a yanzu ba, mafi yawanci ma a ranar babbar salla sai irin bayan azhar ɗin nan suke fara yin baƙi. Amma sai bai ce komai ba ya miƙe ya fita.
Tunda Abah ya fito idanunsa akan mutumin dake tsaye a jikin motarsa ya juya baya yana waya. A haka dai ya ƙaraso yana nazari da tunanin to wanene wannan haka?. Dai-dai yana ƙarasowa tamkar amma Mabera magana shima ya juyo, sukama juna kallon ido cikin ido. Abah ma sai ya rasa abin cewa, kallo Mabera kawai yake yi tamkar ya samu television. Yayinda Mabera ke dariya da kallon Abah ɗin shima, sai kuma ya tako a hankali kusa da Abah yana faɗin, “My Darma badai ka suma bane?”. Abah da mamaki ya kashe a tsaye ya ce, “Humm Mabera dole ne na suma ai, wai kai ɗin ne dai a gabana ko mafarkin dana saba yine dan ALLAH?”. Kai tsaye Mabera ya rungume Abah tare da masa raɗa a cikin kunne ya ce, “Idonka biyu My Darma, Maberanka ne dai tsaye a gabanka”. Rugumesa shima Abah yayi, kafin su saki juna yana kallonsa da ƙyau ya ce, “Mabera dama kana a duniyar nan a raye? Amma tsahon shekaru baka babu labarinka? Kasan irin neman da nai maka a rayuwar nan kuwa?”. “Humm Aminina kai dai kawai a rufe rufau. Wani ƙulli ne ya ƙulleni mai girman gaske, sannan aka sakani a ramin da duk ihuna babu mai iya jin kuka na”. Abah dake kallonsa ya ce, “Halan a wajen jaye-jayen ka ne?”. Dariya Mabera yayi kawai, Abah ya ce, “Ai na sani, nasan bazaka canja ba. Kaga na barka a waje muje ciki dai”. A yanzun ma dariya kawai Mabera yayi, a kaikaice kam sai sake bin gidan yake da kallo yana jinjina kai. A zuciyarsa yana ayyana, (Ta tabbata dai Darma yafi ƙarfina kamar yanda yasha gaya min. Duk da an haifeshi gidan kuɗi, nima an haifeni gidan kuɗin. Kuɗina da nashi muka fara dasa kasuwa na yaye komai amma hakan bai hanashi cigaba da zama a samana ba. Kenan kalmar daya gaya min ta har abada yafi ƙarfina, zai kuma cigaba da fin ƙarfina har ƙarshen numfashin mu ta tabbata).. Taɓawar da Abah yay masa ce ta dawo da shi hayyacinsa, Abah ya ce, “Bismillah shigo mana, nan fa gidanka ne”. Murmushin yaƙe Mabera yayi, ya shigo katafaran falon baƙin Abah na sashensa, wanda aka narkama uwar dukiya da kayan ƙawa. Kai daka gani kasan kazo gidan da nera ta zauna. Komai babu hayaniya, amma daka gani kasan an zuba kayan kuɗi. Zama sukayi Abah ya ɗauka kan waya ya fara neman Oum. Kusan mintuna goma da fitar Abah kenan, dan kowa ma ya tashi daga gaban abinci anata tattare kayan sai ga kiran Abah ɗin a wayar Oum. Tana ɗagawa yace a kawo ma baƙonsa abinci, sannan anjima kaɗan dukan su suzo sashensa a falon baƙi su gaisa da baƙon nashi. Abinci Oum ta saka aka shirya, su Haule suka tafi kaiwa sashen Abah. Koda Haule taga Mabera rikicewa tayi, har ta kusa faɗuwa ga kaya a hannu, ba ƙaramin bugawa zuciyarta ta shiga yi ba ganin mai kama da Sillenta, sai dai wannan kawai ya fishi manyantar shekaru. Bata taɓa sanin Sille nada mahaifi a raye ba balle ma ta kawo a ranta akwai alaƙa. Yanda taɗan rikice har sai da Abah yay mata magana. Yayinda Mabera da shi sarai ya santa ya wani ɗauke kai kawai gefe yay fuska. Haka suka fice Haule na waiwayensa har abin ya bama Abah mamaki. Kamar zai yi magana sai kuma yay shiru kawai. Babu wani kunya babu baƙunta Mabera ya buɗe ciki yaci abinci yay nak. Sai da ya kammala kafin ya kalla Abah ya ce, “Darma ya bayan rabuwa?”. “Kai ya kamata na tambaya bayan rabuwa Mabera. Daga kammala hidimar ƙasa shike nan kawai ka ɓace.” Murmushi sosai Baban Nazeefa yayi, sai kuma ya kalla Abah, “Ɓacewata ta farko kasan dalilinta Darma, kawai dai kana nan da halinka bazaka canja ba. Mutum ya maka laifi ka sharesa kamar baka san mima yayi ba”. Murmushi shima Aban yayi a kwaro na barkatai, ya kalla Mabera da ƙyau. “Abinda ya faru ai ya riga ya faru ya kuma wuce. Amma ban taɓa tunanin a dalilin hakan zaka gujeni ba Junaid. A tunani na ni da kai ai mun zama jini ɗaya. Kuma dama zo mu zauna ai zo mu saɓa ne. Kayi kuskure na kuma gaya maka kuskurenka a lokacin. Na kuma sameka har gida na nuna maka komai ya wuce ina buƙatar mu koma yanda muke. Saboda kaine aboki dana fara yi a duniya kuka amini bayan ƴar uwata Fateema dana tashi da ita. Bazan so kuɗi ya zama sanadin yankewar alaƙarmu ba. Amma abin mamaki na jika shiru bayan na dawo sake nemanka akace min ai bama asan inda kake ba, a dawowa ta biyu suma su Abbah na samu basa nan wai sun bar Kano. Na shiga mamaki da ruɗani sosai, na kuma cigaba da nemanka amma ko labarin wanda yasan inda kake bamma samu ba. Daga ƙarshe dole na haƙura duk da ina jin kewarka, yanda ka zauna a zuciyata yasa bana rabo da yin mafarkinka. Sannan a komai na ban san miyasa ba ban taɓa mantawa da kai ba”. “ALLAH sarki Darma lallai kai amini ne na ƙwarai kuma na gaskiya. Ni kaina kana a zuciyata, dan ban taɓa na manta da kai ba a dukkan al'amurana. Amma kafin na baka dukkan labarin bayan rabuwa bari na fara gaisawa da Fateema, dan nasan idan muka fara lokaci zai iya riƙemu da yawa”. Ɗan jimmm Abah yayi, sai Mabera yay murmushi. “Darma wannan ba Maberan da bane, in dai akan Fateema ne ka ɗauka a yanzu babu komai a wannan zuciyar sai alkairi wlhy. Kuma ko a baya kaima kasan da hakan, hasalima randa naci duka a wajenka kuskure aka samu da rashin fahimta” Sai da Abah ya sauke ajiyar numfashi, kafin ya kalla Mabera cikin ido sosai. “Nasan babu koman ai Mabera, kai koda akwai koman ma a yanzu babu abinda komai zatayi.” “Darma nawa, kana nan a yanda na sanka dai”. Ƴar dariya Abah yayi, ya ce, “Kai kuma kana nan da saka idonka ba”. Shima Mabera sai ya dara. Abah ya ɗauki waya yay kiran Oum yace dukansu suzo har yaran......
________★
Wani irin azababben mari Hajiya Basariyya ta ɗauke fuskar Huznah da shi. Cikin matuƙar kaushin harshe ta ce, “Na rantse miki da ALLAH idan kinga ba'ai miki wannan allurar ba mutuwa nayi. Amma babu fashi wannan shegen cikin sai na zubar da shi. Kuma aurenki da Sageer ya ƙare, idan bai sakeki ta arziƙi ba zai sakeki ta tsiya-tsiya. Madam yi aikin ki”. Doctor dake zaune tana kallon su ta gama haɗa allura ta taso kai tsaye ta iso inda Huznah take. Babu tausayinta ko na sisin kwabo a zuciyarta duk da yanda take kuka tace ta tashi suje ciki. Wani ɗaki dake anan cikin falon suka shiga. Daga gani ɗakin yara ne, Huznah ta ɗan bi ɗakin da kallo, sai kuma ta kalla Doctor tana share hawaye tace zatai fitsari. Karaf Hajiya Basariyya dake bayansu tace, “Baki isa ba, doctor yimata alluran inma fitsarin zatai”. Ai ko sai Huznah ta sake fashewa da kuka. Ko'a jikin Hajiya Basariyya balle Doctor dake aikin kuɗinta, haka ta danna mata allurai har biyu masu ƙarfi, sannan tace taje tai fitsarin. Kuka Huznah take yi na fitar hankali. Tana shiga bayi ta ciro ƙaramar wayarta da take ɓoyewa suna waya da Sageer dan Hajiya Basariyya ta kwace waccan shine Basira ta bata wannan ƙaramar sai take ɓoyewa shiyyasa Hajiya Basariyyan bata san da ita ba har yanzu. Shiru tai tana tunanin wa zata kira. Zuwa can kawai ta yanke shawarar kiran Sageer, sai dai harta yanke bai ɗaga ba, ta sake kira har sau uku ya zama huɗu amma ba'a ɗaga ba. Sauri-sauri ta tafa saƙo ta tura masa. Jin cikinta ya fara mata ciwo tai kiran number Daddy. Shima harta tsinke bai ɗaga ba, ga Hajiya Basariyya ta fara ƙwala mata kira da faɗin ubammi take a bayin da taƙi fitowa. Kuka ta sake fashewa da shi tace gata nan zata fito. Number Daddy ta sake kira, dai-dai nan Hajiya Basariyya ke buga ƙofar bayin tana kiran sunanta da zaginta, ta tabbatar mata kuma in dai ta ƙirga goma bata buɗeba ALLAH sai na lahira ya fita jin daɗi....
_______★
A lokacin da Huznah keta kiran Daddy a waya hankalinsu na nan a tashe da yanayin da Nazeera ke a ciki. Dan sun kammala cin abinci bayan gama yankan raguna Yazeed ya nufi sashen nasu. Kawai yaci karo da Nazeerar ta rarrafo cikin falo ga jini yanata zuba har takai numfashi take da ƙyar. Wani kalar faɗuwa gabansa yayi, babu shiri ya zaro waya a aljihu yay kiran Ammie. A rikice suka iso ita da Aunty Sakeena. Yaran Hajiya Yaya kam babu wacce ta motsa balle na Hajiya Basariyya. Hajiya Yayan ma tayi kamar ma bataji abinda Ammien ke faɗa ba.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣5️⃣1️⃣
______________
...........Tun Maanal bata hankaltu da irin kallon da Saheeba da Nuratu ke mata ba har ta fahimta. Sai dai duk sanda ta ɗago ta haɗa ido da su sai su ɗauke kai su basar. Mamaki ya kamata, zuciyarta ta fara wasiwasi, sai dai batace komai ba. Ashe ba ita kaɗai ba, hatta AA ya fahimta, dan duk motsin Maanal ɗin idanunsa na'a kanta shima. Wani irin ƙyau yau ɗin ta ƙara masa, ga cikin ya sata haske sosai jikinta ya ƙara wani ƙyau da zaunawa. Ga fatarta ko nesa da ita kake sai ka ga yanda take glowing. Wani sashin zuciyar AA na raya masa ƙyawun da Maanal ɗin ta ƙara ne ke ɗaukar hankalin su Saheeban suma, wani sashe kuma yaƙi aminta da hakan. Dan kallon yayi kama da irin na wanda ke jiran tsammani ne. Ana cikin haka Abah ya kira Oum, dan haka duk suka miƙe suka fito zuwa sashen Abah. Su Oum ne a gaba, har sunyi gab da shiga akai kiran Mamy a waya, sai ta ja gefe tana amsawa har duk suka shige. Cikin matsannacin mamaki AA ke kallon Mabera, shima kallon nasa yayi da murmushi a saman fuskarsa. Hakama Maanal kallon Mamaki take ma wannan mutumin mai kama dana ranar sak, sai dai wannan yafi wancan shekaru nesa ba kusa ba. Yayinda itama Oum ke mamaki da ganin Mabera yau a gidansu. Cikin kamun kanta da dattako takai zaune tana faɗin, “Gadanga yau babban baƙone haka damu a gidan?”. Abah yay murmushi da faɗin, “To kin dai ganshi nan nima har yanzu mamaki yaƙi sakina Fateema.” “Ai dole kam yaƙi sakinka, irin wannan bazata haka shekara aru-aru”. Yanzu kam ƴar dariya Mabera yayi, idanunsa akan su Babban Yaya cike da makirci ya ce, “Ai ni bata ku ma nake ba, shin duk yaranmu ne waɗan nan? Kenan Darma!”. Abah ya ɗan murmusa yana bin duk yaran da kallo. “Dukansu yara na ne, ga Fadeel nan shine babba, ga iyalinsa nan guda biyu, sai yara biyu gasu nan. Sai Fawzan, wannan sune nashi iyalin shima, ALLAH bai kawo haihuwar ba munata dai addu'a. Sai Auta Ajwaad, ga matarsa nan shima. Fateema dai ka santa, akwai ɗayar maman tasu”___ya juya yana kallon Oum yace, “Ina Kamila”. “Tana waya ne, yanzu zata shigo”. Cewar Oum kai tsaye. Kafin Abah ya sake cewa komai Mamy ta shigo falon da sallama. Sam bata lura da baƙon ba sai da ta iso tsakkiyar falon idanunta dana Mabera suka shiga cikin tsakiyar na juna, cak taja ta tsaya kamar wadda akaima tsawa. Illahirin jinin jikinta ya fara tsinkewa. Wani shegen murmushi Mabera yay ya ɗauke kansa daga gareta, ƙasa-ƙasa yace ma Abah, “My Darma kana nufin wai aure ka ƙara?”. Maimakon Abah ya bashi amsa sai yay murmushi kawai. Mamy kam da ƙyar ta iya jawo ƙafafunta gudun karta yanke jiki ta faɗi ta ƙarasa a kujera ta zauna. AA da gaba ɗaya yake a tsarge yabi Mamy da ido, ya sake maida kallonsa kan Mabera dan sarai yaga irin kallon da sukai ma juna shi da Mamyn, yanzu ma gani yay yana kallon Mamy ne a kaikaice, sai AA ya sake jin zuciyarsa na harbawa da sauri-sauri... Zuciyar Mamy kam duka take, duka mai azabar ƙarfi da tashin hankali. So take ta danne ta riƙe yanayinta amma hakan na neman gagara, dan koda Mabera ya gaisheta da kansa bata iya ta amsa ba, dan haka kowa sai ya kalleta a karo na biyu. Yanda take yasa kowa fahimtar hankalinta ma ba'a kansu yake ba. Sai Oum ta ɗan taɓata da faɗin, “Mamy lafiya kuwa?”. Firgigit tayi, sai kuma ta kalla Oum, ta sake juyawa ta kalli Abah da Mabera, wani ɗan iskan murmushi ya sakar mata girarsa a sama. Sai Mamy taji wani abu mai matuƙar nauyi yazo ya tsaya mata a cikin maƙoshi, wani irin tsoratata da hargitsata murmushi Mabera ke yi. Dai-dai nan kiran Sille ya shigo mata a waya, sai ta zabura gaba ɗaya ta diririce. Diriricewar da kowa ya zuba mata ido harta miƙe zumbur. Oum da yanayin Mamyn duk ya tsoratasu suma ta miƙe tana ƙoƙarin riƙota da yin magana. Amma mi wata irin hankaɗawa Mamyn tai mata. Har sai da Abah ya tashi da mugun sauri ya tare Oum a jikinsa. Dole su Maanal duk sukai ƙasa da kawuna. Su AA dukansu ukun suka miƙe suma sukai kan Oum. Mamy kam idanunta sun gama rufewa, tsabar yanda take cikin ruɗani irin na bazata, bama tasan ta ɗaga wayar Sille ba balle ture Oum. Cikin matsanancin rufewa idanu dana zuciya ta fara magana a matuƙar tsawace, “Kai tsinannen matsiyaci miyasa kake kirana, bana faɗa maka kada ka sake kirana a waya ba, kada ka sake kuma zuwa min gidana ba Junaid! Kake ko ubam mi? Mi ka taka har kake jin kanada karfin gwiwar saka rayuwata gaba wai?!!”. A yanzu kam babu wanda bai miƙe a falon yana kallon Mamy ba, hatta su Maanal da su Babban Yaya da suka zaunar da Oum Abah na bata ruwa duk Mamyn suke kallo zuciyar kowa na bugawa da sauri-sauri. Wata shegiyar dariya Sille ya saki daga can, tare da faɗin, “Ubana dake a gabanki duk zai iya baki amsoshin tambayoyinki ai Madam Kamila matar Darma. Idan kuma daga wajena kike buƙatar amsar ai ina ɗakin barcinki sai kizo na baki dalla-dalla”. “Sashena?”. Cewar Mamy a matuƙar rikice tana juyawa ta kalla Mabera. Kafaɗa ya ɗage mata da taɓe baki irin na i don't care. Abah daya gama kaiwa wuya ya daka musu tsawa, cikin matsanancin ɓacin ran yanda Mamy ta hankaɗe masa Oum, da fahimtar lallai akwai sanayya a tsakanin Mamy da Maberan ya ce, “Mabera miya kawoka gidana?”. Babu ko ɗigon damuwa a fuskar Mabera ya ce, “Bani ya kamata ka tambaya ba Darma. Matarka ya kamata ka tambaya ai.” yay maganar yana nuna Mamy da idanunta sukai matsanancin kaɗewa. Ji take kamar zata yanke jiki ta faɗi. Brain ɗinta kam wani irin harmutsawa take yi tana jin tamkar zata haukace. Ganin Abah yana takowa inda take ta shiga jan jikinta baya. Oum data fahimci yau ran ƴan maza sun motsa da sauri ta miƙe ta tare gaban Abah, zai yi magana kawai ta riƙeshi. Sai kawai Mamy ta fita da gudu, dan zuciyarta gaya mata kawai take taje ta tattare abubuwanta tabar gidan. A wannan gaɓar su Yaya Fawzan duk sunyi sumar tsaye ne, musamman ma AA da yake jin tamkar zuciyarsa na kumbura a cikin ƙirjinsa. Gaba ɗaya haɗa 1+1 yake amma sun kasa bashi abinda ya dace. A ɓangaren matan ma su Maanal a firgice suke, dan tuni sun miƙe tsaye jikin kowa na rawa. Cikin ƙarfin hali Oum tace su fita. Ai kafin ma ta gama rufe baki duk sunyo waje, dan kowa hanyar fitar dama yake nema... Saheeba da Nuratu duk sashen su Saheeban suka nufa kowanne na ƙoƙarin kiran waya. Hakama Najma RK take kira a waya dan ta fahimci al'amarin babba ne. Maanal kam da bango kawai ta jingina tai shiru tana kallon Najma, fuskar AA take mata kai-kawo a zuciya. Abubuwa uku data san sun sani akan Mabera da Sille na tisa mata kansu a zuciyar...
Saheeba na tsaka da gayama Nana abinda ke faruwa a gidansu cikinta yay wata irin ƙullewa. Da sauri ta duƙe a wajan tana mikama Nuratu wayar. Bata fahimci halin da take ciki ba ta amsa. Bayani ta cigaba da yima Nana. Sai yay dai-dai da fasa ƙarar Saheeba tana jan wani irin wahalallen mugun numfashi mai riƙe ƙirji. Da sauri Nuratu tayo kanta tana kiran sunanta. Saheeba da azaba ta isa ta ce, “Nuratu cikina, bani ruwa na sha na shiga uku. Da gudu Nuratu ta fita ya ɗibo mata ruwa ta kawo mata...
Mamy kuwa gaba ɗaya bata gane komai, a hargitse ta afka sashenta. Kai tsaye tai upstairs, a can ɗin ma bata tsaya ko'ina ba sai bedroom ɗinta. Ƙofar ta danna da ƙarfi, juyowar da zata yi kawai tai ido huɗu da Sille na sille Haule a saman gadonta, su duka tsirara haihuwar tsoffinsu. Sai kawai Mamy ta fasa ƙara tare da tafiya luuuu kawai ta baje a ƙasa sumammiya. Ko'a kwalar rigar Sille. Hankalinsa kwance ya cigaba da abinda yake yi, Haule ko duk da ta tsorata bata da damar nunawa dan tsoronsa take ji matuƙa. Dama tun da ya sata tazo ɗakin ya nuna ga abinda yake so a gareta ta saka masa kuka, aiko ya bata maruka ya kuma sakata cire kaya.....
_________★