Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 129
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 129: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 129. .........Wasu wahallun hawaye…
4,406 words
.........Wasu wahallun hawaye suka zubowa Mamy, da ƙyar yanzu kam ma take iya maganar. Ta jinina kai da faɗin, “Wlhy nima bani nace ayi asiri ba, dan tunda nake ban taɓa zuwa wajen malami ko boka ba. Gwaggo da Sailuba ne suka kawo maganin. Amma nice na fara zuwa musu da zancen son hana auren yarana da ƴayan Asiya, saboda nasan Gwaggo bata son Asiya dan tasha kawo min gulmarta akan alaƙarsu da Fateema. Ni kuma dama irin yanda Gwaggon kema Asiya namin daɗi, sai na yarda na haɗe kai da su musamman ma Sailuba, sai ya zama ma nice mai gayama Sailuba duk wani sirrin Asiya, takai duk wani asiri da Sailuba taima Asiya anan gidanmu ake shirya komai a bata taci ta hanyar Maanal batare da sun gane ba, shiyyasa bata gane abinda Sailuban ke mata sai wulaƙancin Baban su Maanal ɗin kawai da take fuskanta. Hatta batun bada zoɓon Gwaggo ce ta shirya komai, sai kuma aka samu matsala ita Maanal tasha zoɓon tare da Ajwaad, duk da ance a jikinta kawai zai yi tasiri abin mamaki sai yayi tasirin har a jikin Ajwaad ɗin ma. Dan lokacin da Ra'iz ya sanar mana Ajwaad yasha zoɓon tare da Maanal bamu damu ba, mukace ya koma wajensu, ya tafi ya haɗu da Maanal zata shiga ɗakin su Ajwaad tana riƙe ciki, shine ya dawo yana gaya mana, ya tabbatar mana Ajwaad na a ɗakin shima. Hankalina ya tashi nace yaje ya kira min Ajwaad ɗin, nan ma ya koma kiransa sai yaci karo da shi ya fito neman Fateema, da wannan damar Ra'iz ya shiga wajen Maanal, ni kuma na tare Ajwaad na tambayesa mike faruwa? Yana faman riƙe ciki shima ya gaya min halin da Maanal ke ciki shine nai masa wayo nace yaje ɗakina ya ɗakko min magani na bata, ya bar Fateema tana cikin taro kada ya tada mata hankali. Yana shiga bedroom ɗina na kulleshi ta baya, ashe nabar wajen ina sauri ban cire key ɗin ba wani kuma yazo ya buɗe shi, wannan shine dalilin komawarsa ɗakinsu ya samu Ra'iz akan Maanal. Daga nan bamu san miya faru ba kawai al'amarin ya juye kan Ajwaad cewar yayma Maanal fyaɗe. Hankalina ba ƙaramin tashi yayi ba, ga Ra'iz mun nema a gidan mun rasa tako ina. Gida kuma ya rikice akan abinda ya faru. Cikin ɓacin rai muna ɗaki inama Gwaggo da Sailuba masifa akan yaya akai haka, bayan sunce maganin Maanal ɗin kawai zaici gashi ya haɗa da Ajwaad, maimakon yaron da muka kawo fyaɗe ya koma kan Ajwaad. Suna cikin min rantse-rantse kawai juyawar da zan yi naga Ajwaad a bayanmu, kuma tabbas yaji komai da muke faɗa. Ƙoƙarin juyawa yake zai fita na damƙoshi, wannan ya bama su Gwaggo damar fita a ɗakin, kuka Ajwaad kemin akan miyasa zanyi hakan? Miyasa zan aikata, takaici ya sakani buge masa baki. Cikin ɓacin rai nace masa nayi ɗin, kuma idan ya sanarma wani ina da alaƙa ko hannu a cikin abinda ya faru ɗin wlhy sai na kashe Fateema da Maanal ɗin, shi kuma sai na tsine masa. Ko tuhumarsa akayi ya faɗi cewar Ra'iz ne ya aikata komai, shi yazo ceton Manaal ɗin ne, kuma daga ranar na haramta masa huɗɗa da Maanal na har abada. Idan kuma ya sake yarda ko zama waje ɗaya sukayi ALLAH ya isa ban yafe masa ba, ko mutuwa nayi idan ya aure Maanal nan ma ban yafe masa ba. Kai yana ma ƙara haɗa alaƙa da zuri'ar Asiya da Habibu koda ta magana ce ALLAH sai na kashe Maanal da Fateema har lahira. Ina gama yimasa wannan barazanar na fito na baroshi a ɗakin, na samu gida ya ƙara rikicewa Fateema ta faɗi, ita kuma Maanal ɗin an wuce da ita gidansu ana kuma neman Ajwaad dan maza sun shigo. Ban san ya akai ba, ban san miya faru ba kawai an tsare Ajwaad da tambaya bayan likita ya tabbatar da amma yarinyar fyaɗe yaron nan ya amsa cewar wai shine yay fyaɗen. Raina ya ɓaci, sai dai ta wani ɓangaren naji sanyi da akace za'a aura masa ita yace baya so, ta haka na fahimci kurarin danai masa akan kashe Maanal da Fateema yayi tasiri kenan. Oho ko'a hakama naci riba ai, tunda aure dai ya fasu, duk da amsar zancen fyaɗen nan da yaron nan yayi har yanzu yana min ciwo a rai, muka zo kuma muka shiga tashin hankalin ciwon daya tsinta kansa a ciki dan ni na Fateema bai wani dameni ba....” “Toke dama kin damu da damuwar wani ne inba taki ba Kamila”. Mabera ya faɗa yana murmushin takaici, sai kuma ya kalla ƙofa da jami'an tsaro keta faman ɓaɓatu amma sunƙi tankawa. Baki ya taɓe ya dawo da kallonsa kan Abah dake ta kallon Kamila ko ƙyaftawa babu. Ƴar dariya yayi da faɗin, “My Darma indai wannan matar ce kaɗan daga abinda zata iya kaji, dan mun yanke maku abubuwa da yawa a kanta ma saboda bamu da time sosai , dan lokacin fara aiki ya kusa cika. Bana son mu wuce 2 a jejin nan. Gashi har 12 ta wuce yanzu. Amma a gurguje zan ƙarasa muku abinda ya rage kodan kasan halin da kake ciki a yanzu kai kanka game da ƙullinta” Sille dake ƴar dariya ya ce, “Gara dai ka faɗa masa kam Baa! Ko dan wannan tsageran ɗan nasa da yayta ɓoye ainahin halin uwarsu da abinda ta dinga aikatawa saboda bata kariya yasan ita ɗin kara da kiyashi ce ɗaukar mara sani, ɓoye hallayarta bazai amfane shi da komai ba. Dan bana son mu rabu basu san komai akan wannan azzalumar matar ba”. Ya ƙare maganar yana shurin ƙafar Mamy har sai da ta saki marainiyar ƙara. Ko'a kwalar rigarsa. Cikin rashin damuwa Mabera ya cigaba da faɗin, “Bayan Ra'iz yabar gidan a wahale ya koma wajen Junaid, ransa ya ɓaci da bayanin da yay masa akan abinda ya faru yace sai ya ɗauki fansa. Nine na hanashi, na kuma sanar masa ai lokaci baiyi ba da saura dan wanan wasan ya ɓaci kuma, dan bai kamata Kamila ta faɗi ba a wannan gaɓar da sauƙi tunda al'amarin ya juye haka. Dan haka na tattara su suka koma Lagos. Sun koma da sati ɗaya Turai ma ta koma nima haka, itace ta bamu labarin dukkan cakwakiyar data ƙarasa faruwa har barinku ƙasar. Anyi haka da kusan wata guda na tafi saudia yin wani aiki, watana kusan uku na dawo, na tarar da wani tashin hankali na asalin halin da Turai ta jefa ƴaƴana a ciki, wato maida Junaid tamkar mijin aurenta. Hankalina ya tashi matuƙa, dan abune da ban taɓa kawoma raina ba. Naci mata mutunci matuƙa, na bayyanawa mijinta ainahin wacece ita, na kuma ce sai mun shiga kotu da ita tunda ta lalata min yara. Da ƙyar mijinta ya lallasheni ya bani maƙudan kuɗaɗe, ya tabbatar min idan wannan maganar ta fito shine zai faɗi a ƙasa, dan dama danginsa basa son aurensu shine ya dage. Kuɗin daya bani ne ya kashe wannan rikici, na canjama yarana anguwa dan hayar gida guda na kama musu, wannan shine sanadin rabuwarmu da Turai, su kuma suka baro Lagos suka dawo Abuja da zama, sai dai ko shekara basuyi ba mijinta ya rasu. A lokacin nima ina tsakanin Kaduna da Abujar amma ko gaisuwa ban mata ba, kai inda take ma ban taɓa nema ba. A wannan gaɓar ne kuma Ajwaad yazo Nigeria, bamu san ta yanda akai ya gano inda Ra'iz yake ba, kawai sai kirana akai wai nazo Lagos ga Ra'iz a hannun jami'an tsaro an kaishi asibiti wani ya masa dukan mutuwa, ya ragargaza masa ƙafafu ya illatashi a gabansa. Hankali tashe naje, zuwa lokacin an kaishi asibiti, hankalina ya tashi da ganin halin da yaron yake ciki, wlhy saika ɗauka haɗarin mota yayi ba duka bane, dukan ma wai na yaro kusan sa'arsa, dan Ra'iz da Ajwaad sa'anni ne ai. Junaid ya shirya ɗaukar fansa a lokacin amma nine na hanashi, muka maida hankali a kan jiyyar Ra'iz, dan bincike ma ya tabbatar min Ajwaad ya sake barin ƙasar dama yazo neman su yarinyar da akaima fyaɗen ne. Sai dai baima sameta ba, Darma yazo ya sake maida shi ƙasar da suken. A ƙarshe dai bayan gama jiyyar Ra'iz ya zama gurgu, sannan an tabbatar mana shi da mace sai dai kallo dan Ajwaad ya masa babbar illa a mazantakarsa. Wannan al'amari ya min ciwo, ya yima Junaid ma. A tsakanin kuma kuka dawo Nigeria cikin Abuja, sai dai bamu samu labari ba sai daga baya sakamakon mu duka munyi nisan kiwo, wannan shine sanadin dawowar Junaid cikin Abuja shima, muka kuma cigaba da bibiyar al'amarinku. Kwatsam kuma sai na ganku a Kaduna bikin ɗan Chalawa, sai dai ban yarda ku kun ganni ba, na taƙaice muku labari dai nine na fallasa batun yima Maanal fyaɗe da ɗanka yayi a wajen bikin nan dan kawai na ƙuntata Kamila da itama bata ganni ba. Daga nan kuma Junaid ɗan Junaid ya bayyana mata ainahin kansa. Abu na ƙarshe da nake son ka sani shine Kamila ta tanadi guba domin kasheka kaima, sai dai ban sani ba ko ta baka gubar ko bata baka ba.....” A wani irin hankali tashe su AA da kowa ma suke kallon Mamy, Babban Yaya ya ce, “Guba?”..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣6️⃣7️⃣
______________
........Kafin Mabera daya buɗe baki zai bashi amsa ya furta wani abu jami'an tsaro da suka gama kaiwa wuya suka bugo ƙofar gidan, suka fara shigowa. Da wani irin Sauri Mabera yay tsalle ya dire gaban Abah ya ɗora masa bindiga a kai. Haka Sille ma tuni ya damƙi wuyan Mamy ya ɗora mata bindigar, yaransu ma suka zagaye su Maanal. Cikin ƙaraji Mabera yacema jami'an tsaron, “Wlhy kuna motsawa duk sai mun kashe su. Dan haka sai ku zaɓa rayuwarsu ko fitarku waje.” A fusace cikin jami'an wani ya ce, “Kai ɗin banza daka isa ka bamu umarni, ka miƙa wuya kawai dan ta ƙare maka.” “Ta dai ƙare mana, dan sai dai ayi mutuwar kasko”. Cewar Sille yana hura hanci. Jami'an tsaron nan da suka fusata na motsawa kawai Sille ya harbi Anum dake jikin Nana. Yarinyar tai wani irin wahallen fasa ƙara, jami'an tsaron suka yunƙuro, Nana ta zabura, hakama su Oum. Sai kawai wani harbin akan Nana itama. Itama ihun ta fasa ta zube ƙasa Anum tai gefe alamar da wahala idan yarinyar nada rai. Gaba ɗaya hankalin kowa ya gama tashi a wajen. Sille ya wani share bakin bindigarsa a jikin Mamy yana faɗin, “Da kun ɗauka wasa muke, wlhy idan baku fita ba haka zan dinga musu tsinci ɗai-ɗai”. Hankalin IG yay matuƙar tashi, dan shugaban ƙasa ya jaddada masa kada su bari ko mutum ɗaya daga ahalin Darma yaji koda rauni, cikin bada umarni yayma yaransa magana suka fara fita da baya-baya har suka gama ficewa gaba ɗaya a gidan. Kallon Mabera Sille yayi, ya ce, “Baa! Ka shirya zamu bar gidan nan yanzun?”. “Son tayaya!? Ta kuma ina kana ganin sun zagaye gidan”. “Ta wannan ƙofar dai ba wata ba, kuma duk ku shirya kowa ya kama mutum ɗaya a cikinsu”. “Son!”. Da sauri Sille ya ɗaga masa hannu, sai kuma ya daki idon Mamy ya jefar da ita a wajen, ƙarasawa yay inda Mabera yake yana masa raɗa a kunne. Yayinda ihun Mamy ya cikama kowa kunne a wajen dan Sille fasa mata idonta ɗaya yayi, abun zattashin hankali da tausayi. Gaba ɗaya hankalin su Oum ya sake tashi, su Nuratu kuka sukeyi sosai, hakama su Maanal a wannan gaɓar sun kasa jurewa. A karo na farko AA da tunda aka harbi Anum ya duƙar da kai yay shiru ya ɗago ya kalli Maanal. Da salon maganarsu ta lips da suka iya tun suna yara yay mata nuni da lips ɗinsa bayan ya mata alamar share hawayenta, lips ɗin nasa ta ƙurama ido kuwa tana share hawayen nata, yana faɗar abinda yake son gaya mata ta gane. Kai ya jinjina masa tana ƙara share hawayen da suka gagara tsayawa. Shi kuma ya juya yana kallon Babban Yaya, AA ya jinjina masa kai yana miƙa masa hannunsa ɗaya, ya kama, ya juya sashen da Yaya Fawzan yake shima ya jinjina masa kai ya bashi hannu ɗayan suka riƙe juna kam. Cikin amincin ALLAH suka haɗa ƙarfin daya rage musu waje guda suka matse hannayen juna. A gefensu Maanal ce ta kai baki kusa da kunnen Ameerah dake gefenta ta raɗa mata wani abu. Ameerah ta jinjina kanta tana share nata hawayen. Hannuwa suka cika da ƙasa cikin dabara, cikin bushewar zuciya Maanal tace, “Kai tsinannen Sille ubanka Junaid Mabera”. A wani mugun fusace Sille da a duniya babu abinda ya tsana irin ka zagar masa uba ya juyo. Kawai suka ambula masa ƙasa akan fuska harma da idanun wasu a yaransu musamman na kusa da su. A bazata sai cikin idanunsa daya zazzaro dan fusatar zagin da sukai masa. Wani irin ihu Sille ya saki dan abin yazo masa a bazata, hakama yaransa da ƙasar ta shigarma idanu duk sun saki bindigu a ƙasa. Bindigar hannunsa ta shima faɗi. Yay taga-taga zai faɗi hakan dai-dai da miƙewar su AA tsaye kawai suka saka ƙafafu suka taɗesa ƙasa suka take, yanda kuka san ragon layya ko sa mai gardama haka akai masa... (🤣🤣kuyi haƙuri wlhy dai gurin nan dariya ya bani 😆😂🤌). A gigice Mabera dake ɗan nesa da su bindigarsa akan Abah yayo baya saboda ihun Sille, hakama su Oum da su Nuratu duk miƙewa sukai suna kallon su Maanal da su AA ɗin, dan tuni Ameerah ta jefa ma su AA bindigar Sille data faɗi. Mabera na isowa Babban Yaya na ɗora bindigar akan kunnen Sille. Yaransu suma suka ɗana kunamin bindigunsu akan su Maanal. A kausashe AA yace ma Mabera, “Kuna motsawa zamu tarwatsa kansa wlhy. ALADEN banza. Kai ka isa kace zaka sake barin nan da mu ne. Wawa matsoraci, ai da ka isa ɗan iska da bakai mana wannan allurar ba kaga a maimakon Ragunan layyar mu idan bamu maidaka RAGON LAYYAR ba tun a gidanmu.” “Amma kun san zan iya kashe ubanku ko? Yarana zasu iya kashe kaf iyalanku”. Mabera ya faɗa a fusace yana sake danna bindigar hannunsa akan Abah. Cikin bushewar zuciya Ameerah ta ce, “Mun sallama rayukanmu indai a kansu ne.” Manaal tace, “Tabbas Ameerah idan sun isa su kashe mu ɗin?”. Najma ta ce, “Wannan haka yake ku kashemu mi kuke jira ne karnuka”. A fusace shima Yaya Fawzan ya amsa masa da, “Ai sai dai ayi MAJA kuwa, dan muma za mu kashe wannan TSINANNEN da kai kanka!!”. Babban Yaya ya wani ja kunamar bindigar cike da ƙwarewa ya sake ɗanata dan ya iya harbi sarai, kai su dukansu ma babu wanda bai kowa ba a zamansu turai. Cikin ihu da hargagi na firgita, Mabera ya ce, “Stoppp!!!”. Yana ɗagama yaransu dake shirin harbi hannu “Oh kace kai ɗan iska ne”. Cewar AA dake kallon yaran Maberan da ke zagaye da su da bindigu suna ja da baya. Sai da ya gama ƙirgesu tas da ido sannan ya maida idonsa akan Mabera. “Idan kana son rayuwar wannan JAKIN ɗan naka waɗan nan ƴan iskan su ajiye bindugunsu. Kaima kuma ka saki mana Abah”. “Anƙi ayi hakan.....” “Please Baa! Su ajiye su ajiya idona wlhy bana ganin komai. Ka sakar musu ubansu su sakeni Baa!”. “Baka da hankali Son, kasan wanene Darma kuwa? Ko kana tunanin ƴaƴansa ba jininsa ne ke yawo a jikinsu ba duk da waccan tsinanniyar ce ta haifesu”. Yay maganar yana kallon Mamy da azabar ciwon ido ta sakata nutsuwa waje guda. Ya cigaba da faɗin, “Bakaga shegiyar yarinyar nan data ambula maka ƙasa a ido rainonta kawai sukayi ba amma idanunta a bushe suke like soyayyar gyaɗar ƙauye”. Baki Maanal ta murguɗa masa, taja tsaki. “Zanyi maganinki”. Mabera ya faɗa cikin zafin zuciya. Tsabar iskanci kawai Maanal tai masa gwalo. Aiko gwalon nan ya ƙona masa zuciya. Sai dai kafin yay magana a fusace Sille da azaba ta isheshi ya ce, “Kai dan uwarku kowa ya ajiye bindigarsa”. Da gudu kuwa yaran suka fara ajiye bindugun, to dama tun asali su ɗin rainonsa ne, suna girmama Baban nasane kawai saboda shi, amma Sillen ne asali ogansu, duk da a cikinsu akwai rainon Maberan shima kaɗan. AA daya fahimci Sillen ne lagonsu saiya saka yatsa cike da iya mugunta ya danne jijiyar wuyan Sille da ƙarfi har sai da yay ƙarar ihu. Ya ce, “Ce musu su shiga cikin ɗakunan nan....” “Ai ko rufe baki AA bai gama yi ba Sille ya fara musu magiya da faɗin, “Kubi umarninsa ku shige”. “Son kana da hankali kuwa?”. “Baa! Bazaka gane ba, jijiyar numfashina fa ya riƙe”. Sille ya faɗa da ƙyar. Wato AA yasan takan mugunta, sai ya sake dannawa. Sille ya sake sakin uban ihu har sai da Mabera ya runtse idanu. Ji yake zuciyarsa na tafasa kamar ya sakarma Aba kunamar bindigar hannunsa a cikin kai. Sai dai baya son rasa ɗansa. Dan shine rayuwarsa, shine komansa, ya ɓata shekarun ƙuruciyarsa kaf a rainonsa ne, sai yanzu a gaɓar da zasu ɗauki fansa ya yarda ya salwantar da rayuwarsa da kansa. Kai ina Junaid ɗan Junaid ne fa, wlhy yaron dabanne a garesa da rayuwarsa, saboda shi ya haƙura ya rasa iyayensa, bazai iya haƙurin rasashi ba akan ganganci. Haka yana ji yana gani yaran suka shige cikin ɗakunan kaf ɗinsu. Suka tada Sille tsaye akan ƙafafunsa, suma su Maanal duk suka miƙe, AA yace “Kufita waje.” Gaba ɗaya Oum ta tattarsu sukai hanyar fita waje, da yake ƙofar a buɗe take Jami'an tsaron na hangosu, sai dai a tunaninsu su Sille na bayansu ne sai duk suka ɗana bindigu sukai shirin kota kwana. Sai da su Maanal suka gama fita sannan su AA suka koma kan Mabera da har yanzu yake rike da Abah. Da farko yaso turjewa. Yaya Fawzan na ɗaga hannu zai daki cikin Sille da sauri Mabera ya ce, “Wai kuna mantawa ubanku na hannuna ne kuma?”. Abah dake murmushi ya ce, “In dai nine karku fasa yi masa duk abinda kukai niyya, na sallama rayuwata kuyi komai da yazo muku. Shi ma idan ya isa ya sallama rayuwar ɗan nasa”. “Amma Darma kasan abinda zan iya ko?”. “Sanin abinda zaka iya ɗinne ya sani basu dama”. Abah ya faɗa cikin halin ko'in kula, dan ya fahimci akan Sille babu abinda Mabera zai iya yi. Shi kansa AA ya fahimci hakan akan Maberan, shiyyasa yay masa talala da shi. Ba ƙaramin a tashin hankali Mabera yake ba, haka ya saka Aba a gaba suka nufi hanyar ƙofa bisa umarnin su Yaya Fawzan. Su AA da Babban Yaya biye da shi sun tasa Sille da idanu ke cike da ƙasa a gaba suma. Yaya Fawzan ya shiga tattare duk bindigun yaran su Mabera waje guda ya zuba a rigarsa ya ɗaure. Abin dariya abin tausai, yaran su Sille dake leƙe ta windows ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Waɗan da sukai kiddinapping kuwa ganin yanda wasan ya juye a wani irin farin ciki suke mara misali, tuni sun shiga fitowa daga ɗakin da aka rufesu Yaya Fawzan ya buɗe musu.........✍️
To jama'a bari mu tsaya nan nima na ɗan huta zuwa Monday idan ALLAH ya kaimu, in sha ALLAHU mun dai kusa mu tsarge. Ko yaya Abah zai kuɓuta a hannun Mabera kuma?, yaya batun gubar da akace Aba yaci. Anum, Nana, Mamy a wane hali suke ciki. Saheeba, ɓangaren su Huznah duk yaya ake ciki? In sha ALLAHU duk zamu tsarge komai a sati mai zuwa da izinin UBANGIJI. ALLAH ji nake kamar na rufe ido littafin ya ƙare😭🤌.
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣6️⃣8️⃣
______________
........Fitowarsu ta kasance abu biyu a lokaci guda. Farin ciki da tashin hankali. Dan anyi-anyi Mabera ya saki Abah yaƙi. Ya dage akan sai an sakar masa ɗansa sannan. Su kuma su Babban Yaya sunce bazasu saki Sille ba sai Mabera ya saki Abah. Wannan taƙaddama ita ce taja zaren sabon wasa na tsawon lokaci. Suma jami'an tsaron basa son su AA su saki Sille, saboda Sille da ubansa masu laifi ne da aka daɗe ana nema amma ba'a sansu ba saboda fuska biyunsu. Kuma suna son kuɓutar da Abah. A cikin wannan halin aka gama tattaro yaransu dake cikin gida, aka kuma shiga binciken jejin tako ina, su Mamy dake cikin wani hali da su Nana da wanda suka daɗe a wajen anyi garkuwa da su Ambulances na isowa aka shiga ɗibarsu aka juya. Dan tabbas suna buƙatar taimakon likitoci da gaggawa. Anyi-anyi a ɗiba su Oum sunƙi, sai da Baba yayi magana. Su baba Sardauna da su RK suna cikin matsannacin tashin hankali. Duk da dai Alhamdullah ga wasu sun kuɓuta. Amma irin wannan zakaga komai baka son ka rasa. Makamai sosai aka dinga tonowa a ramuka, da mashina da abinci buhuna-buhuna. Da kuɗaɗe suma a jaka ƙatuwa cikin wata mota. Jami'an tsaron sun fahimci al'amarin babbane gaskiya. Yayinda wasu a cikinsu suka fara amsa kira ta bayan fage daga wasu ɓoyayyun mutane akan komi za'ayi kada su yarda Mabera da ɗansa suyi magana. Hakan na nufin yin maganar tasu zai zama suma tasu zata fito. A yanzu ko basu shirya hakan ba ma kansu. Ganin komai zai iya faruwa musamman yanda su Babban Yaya suke a fusace, shi kuma IG baya son su ɗauki doka a hannunsu sai ya umarce su da su bashi Sille. Da farko sunƙi, sai da Baba Sardauna yay musu magana, wannan tarbiyyar su ce ƙin tsallake maganar na gaba da su, shi ma IG ɗin dan basu san ainahinsa bane ba, dan tabbas wannan ƙarfin nasu Mabera ba nasu bane kaɗai akwai masu dafa musu baya daga sama. In ba haka ba ta ina zasu shigo da irin waɗan nan muggan makaman har su raini yara matasa ƙanana kamar waɗan nan dake ƙarƙashin su. Al'amarin fa na aduba ne. Wani mugun hankaɗawa AA yay ma Sille gaban IG, sai da ya zube ƙasa aka ɗagashi saboda idanunsa basa ganin komai an cikasu da ƙasa. Amsar Sille a hannun su AA akace su shiga mota abar jejin da su Aban ma za'a taho da shi. “Ina wannan gamgan ne ƙafarmu ƙafarsa”. Cewar AA a fusace a kuma dake. Babban Yaya da Yaya Fawzan suka ce, “Wannan magana haka take Auta.” RK ma ya matso yace, “Wannan shine batu na gaskiya ranka ya daɗe. Yanda suka baka ɗanshi, shima ya baka Yaya kawai. Idan ba haka ba sai dai ai mutuwar kasko, mu duk mun sallama zamu mutu saboda shi ɗaya”. Ba ƙaramin ɗaukar zafi kan IG yayi ba. Dan yau yaga ainahin taurin kai da garada da yake shan ji anacewa zuri'ar Darma nada shi. Gaba ɗaya babu wani tsoro ko shakka a idanun yaran nan. A tsayensu suke zaratan mazaje, da ace yaran nan jami'an tsaro ne a ƙasar nan lallai kowa sai yaci ƙaniyarsa a hannunsu. Dan ba ƙananun jarumai za'ayi ba. Karo na farko aka fara lallashin Mabera, dan ya turje akan idan fa har ya saki Abah to an sakar masa ɗansa ne, in ko ba haka ba to fa sai dai ayi mutuwar kaskon shima ya shirya ya kuma yarda.....
_________★
Anan cikin jeji anata tirƙa-tirƙa anan cikin gari hankalin mutane a tashe yake sosai musamman duk wani mai alaƙa da zuri'ar Darma. Ga dai wasu an fiddo amma rashin fitowar tasu gaba ɗaya yay matuƙar tadawa mutane hankali. Anata cigaba da tayasu da addu'a. Kai tsaye cikin Abuja aka wuce da su Maanal cikin asibitin KK HOSPITAL. Dan danan aka shiga basu taimakon gaggawa musamman ma Mamy, Nana, Anum da wanda akai kidnapping. Shahidah da mijinta da Amal da mijinta itama da tun ɗazun suka iso Abuja tuni sun iso asibitin. Haka suka haɗa Ameerah, Najma, Maanal duk suka rungume suna kuka. Sannan suka koma kan Oum. Su ma su Hajiya Majdiya da tawagar ƴan Kano sun iso Asibitin, dan haka kusan family ɗin Darma duk suna Abuja. Kai wanda ma basa ƙasar tuni labari ya isar musu dan wannan shine labari mafi shahara a yau ɗin tako wane bangare.....
_______★
A Kaduna kam kowa yayi mamakin ganin Ammie batai kuka ba, ta dai nutsu waje guda tai shiru kawai. A haka su Nene suka iso asibitin hankalinsu tashe suma da jin abinda ya faru. Daddy da Yazeed ma al'amarin ya tsaya musu a rai sosai. Abin tashin hankali dai-dai lokacin da ake sanar da kuɓutar da su Maanal Nazeerah da ake shirin farama cs sai ga haihuwa gadan-gadan. Dole aka dakata aka shiga taimaka mata, da ƙyar ta haihu ashe yaron babu rai ne. Yaro na gama fitowa kuma ta hau jijjiga. Ya suhanallah al'amarin akwai tashin hankali da tausayi musamman ga Sabuwa da abun ya zame mata goma da ashirin. Ga karaya a hannu, ga gocewar ƙashi a ƙafa. Ga halin da miji ke ciki gana ɗiya. Wani irin hawa da jininta yayi sai gata a ƙasa zube...
Huznah an samu nasarar tsayar da jininta ita, an mata allurar barci. Sai dai doctor baice komai game da cikin na nan ko baya nan ba. Yadai ce su kwantar da hankalinsu. A wannan halin Sageer da mahaifinsa suka iso, yanda kowa baiga Huznah ɗin ba suma basu ganta ba. Haka suka zauna cikin jimami biyu suma. Na al'amarin dake faruwa a ƙasar da wanda ya shafe su na Huznah....
_______★