Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 132
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 132: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 132. Koda su Daddy suka koma gida…
4,447 words
Koda su Daddy suka koma gida ƙiri da muzu yaƙi maida hankali akan batun Hajiya Basariyya. Ammie ce da shi yau ɗin, ta tasashi da naci da magiya amma yay mata shiru. Da yaga zata takura masa sai yace taje sashenta bai buƙatar taya kwanan. Ƙin tafiya tai, ta koma gefe ta ɓata fuska, shima yana gama shan tea ɗin daya saka ta kawo masa yaje bayi yayi brush yazo ya haye gado ya kwanta. Haushi ya sake kama Ammie. Cikin rawar murya zatai masa kuka ta ce, “Amma Daddyn Hamee.....” “Asia! ALLAH ranki zai ɓaci. Nace ki ƙyakeni! Ki ƙyaleni mana. Ko dolene sai na shiga abinda bai shafeni ba. Matar nan bata da wani haƙƙi a kaina yanzu ko dole sai kin tilasta min ne”. Sosai gaban Ammie ya faɗi, ta ce, “Wane irin magana ce wannan Daddyn Hameed. Taya zakace matarka bata da hakki a kanka?”. Harara Daddy ya zuba mata, cike da takaici yace, “Tunda so kike kiji bara na gaya miki na saketa, saki uku kuma. Karki sake min maganarta, idan ba haka ba kuma wlhy zaki bar ɗakin nan shirme kawai!”. Ba ƙaramin suman zaune Ammie tayi ba, sai kawai hawaye suka shiga rige-rigen zubo mata. Tabbas mutuwar aure kota maƙiyinka ce bata da daɗi wlhy. Tamkar wadda ƙwai ya fashewa a ciki haka ta miƙe ta fita tabar masa ɗakin. Karan farko da taji kamar ta kama Daddy da duka. Wane irin yanke ɗanyen hukunci ne haka. Koba komai Basariyya ai uwar ƴayansa ce, ƴaƴan ma mata da suke zaune tare da su babu aure. A tunaninsa hakan masalaha ce ko shuka sabuwar cakwakiya a gidansa. Dan duk yanda yake tunanin zasu iya riƙema Basariyya ƴaƴa wlhy bazai yiyu ba tinda yaran dai rainonta ne, komai mugun halin mahaifiyarsu kuma bazasu so su sama da son da suke mata ba...
Washe gari itama Hajiya Yaya ta sameshi da zancen Hajiya Basariyya saboda ganin yanda damuwa ta fara bayyana a fuskokin ƴaƴanta. Ta saka Yazeed yaje ya bincika station har ya gano inda Hajiya Basariyya take. Koda yay ƙoƙarin yin belin ta sukace bazasu bada ita ba. Dan ana zargin ta ne da yunƙurin kashe rai. Hankalin Yazeed a tashe yazo ya sanar ma Hajiya Yaya, itama ta kira Ammie. Sosai al'amarin ya girgizasu. Yazeed yace shifa yana zargin Sageer ne yasa aka kama Hajiya Basariyya kuma da haɗin kan Daddy. Nan ma zancen sai ya ƙara basu mamaki, Hajiya Yaya tace bara ta samu Daddy ɗin to taji ta bakinsa. Shine tazo itama ta samu kalar tujarar da yayma Ammie a daren jiya. Haka ta fita ta barshi. Jin abinda yace shima Yazeed yace bari to ya sameshi shi. Yana shigowa Daddy ya dakatar da shi. Dan a harzuƙe ya ce masa, “Dakata anan, idan kaima iyayen naka ne suka turoka akan batun Basariyya ALLAH tak kace da ni sai ranka yafi nasu ɓaci. Dan haka ka rufama kanka asiri ka koma inda ka fito tun muna mutunta juna”. Jiki a sanyaye Yazeed ya fita, koda ya koma inda su Hajiya Yaya suke duk abinda ya faru ya sanar musu. Hajiya Yaya ta dafe kai da faɗin, “Matsalata da Alhaji kenan Ammien yara, shi idan yay fushi babu mai iya tankwarashi. Ya kamata ya duba kodan yaran nan ai”. Kafin Ammie tace wani abu Yazeed ya ce,.........✍️174
.......“Mammah abunne fa da ciwo, itama tayi ganganci wlhy, kuma taso zuciyarta, yanzu da yarinyar nan ta rasa ranta fa. Ko taje ta haɗu da wata matsalar. Doctor ɗin fa yace allurar da sukai mata muguwar allura ce wlhy, kuma da ba'ai saurin kawota asibiti ba komai zai iya faruwa da ita. A yanzu haka suna tunanin ta ɗan taɓa mata brain ma, shi kansa cikin duk da bai zube ba sunce da wahala ya zaman ba'a taɓa lafiyarsa ba. Shiyyasa ma sai a yau zasu sallami Huznahr. Wanne irin son zuciya ne wannan ace har ɗanka daka haifa a cikinka baka bari ba. Idan tace bata son haɗa zuri'a da Sageer sai ta tuna shi jinin Sageer ɗin a jikin ƴarta yake, kuma cikin nan ya fara girma, ai gara ta bari idan yazo duniya sai ta kashe shi kinga tasan dai jinin Sageer ɗin ta cutar”. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un su Ammie suke maimaitawa kawai, amma sun kasa ma iya cewa komai dan su kansu al'amarin Hajiya Basariyya ya gama kaisu maƙurar mamaki a wannan gaɓar.....
_______★
Alhamdullahi anan Abuja an sallami Oum itama yau da safe, dan ta matsa ma RK bata son zaman gadon asibitin. Gefe farin cikin da kowa ke son gani a fuskar ta musamman su Yaya Fawzan da komai suke mata inba abinda ya shafi shiga bayi ba ya sake bata nutsuwa. Baiwar ALLAH ana sallamarta Mamy ta fara cewa a kaita ta gani bayan Abah da ta leƙa ta glass dan shi kam ba'a barin shiga inda yake har yau ɗin nan. Shiru su AA sukayi cirko-cirko kowa yaƙi magana kuma yaƙi motsawa. Oum ta zuba musu ido kawai, sai kuma ta koma tana kallon RK cike da tuhuma. Shima dai fuskarsa ta canja amma bai ce komai ba saboda su Babban Yaya. “Magana fa nake da ku, nace a rakani inda ƴar uwata take kunyi shiru kamar gunkinaye.” Wayancewa Babban Yaya yayi ya zaro waya zai kai kunne wai ana kiranshi. Yana ɗaga ƙafa zai bar wajen a dake Oum ta ce, “Fadeel!”. Cak ya tsaya yana matse idanu, sai kuma ya juyo a hankali ya kalla Oum ɗin. Ganin yanda tai kicin-kicin da fuska ya duƙar da kai ƙasa yay shiru. Sam babu wasa a tattare da ita ta ce, “Mi kuke nufi? Bakuma san ɗakin da aka kwantar da ita ba kenan ko mi?”. Rai a ɓace Yaya Fawzan ya buɗe baki zai yi magana. Bubb Oum ta buge bakin nasa kaɗan, sannan ta shiga nunasu da faɗin, “Duk wanda ya sake magana a cikin ku sai na fallama fuskarsa mari. Yau she har zukatanku sukai irin wannan bushewar akan bijirema abinda yake hakki a kanku ya kuma dace kuyi. Ni zakuma haka ƴar uwata na kwance cikin matsannacin hali ku kasa zuwa ku dubata? Shike nan nagode, nagode sosai Fadeel tunda ka zama babban banza. Rafeeq wuce ka raka ni”. Ba ƙaramin tashi hankalinsu AA yay da ganin ɓacin ran Oum ba. Cikin sauri duk suka bita suna bata haƙuri. Amma ko kallon su batayi ba. Su Baba Sardauna sai murmushi suke zukatansu na ƙara jin ƙaunar gudan jinin nasu. Ai duk ahalin Darma basa maida sharri da sharri sai alkairi. Wannan mutuntawarsu ce. Har ɗakin da Mamy take kwance su Babban Yaya suka shiga a karo na farko, Aunty ce tare da ita, dan tun jiya da akai addu'ar uku ta dawo asibitin. Suma su Baban Nuratu sun wuce Kano dan ba wani karɓar gaisuwan ake anan Abujar ba. Amma Nuratu na tare da Saheeba ita ke jiyyarta. Farin ciki da kunya suka kama Aunty duk a lokaci ɗaya. Sai faman duƙar fa kai take tana ma Oum ya jiki. Sai da Oum ta ce, “Haba Aunty miye amfanin hakan, karfa ki manta kefa yayace a garemu”. Sosai Aunty ta sauke ajiyar zuciya, sai kuma ta shiga share hawayen dake kwarar mata. Itama Oum a karo na farko hawayen take yi data kalla Mamy. Tana kwance idonta biyu sai dai babu ido ɗaya sai ɗaya. Wanda Sille ya ya daka ya tsiyaye tas ya kuma zazzago waje sai da aka mata aiki aka maida shi, shine aka rufe shi da uban bandage. Hakan kuma sai ya saka fuskar kumbura gaba ɗaya ɗayan idon shama ya shige ciki sai kaɗan-kaɗan take iya ganin mutane da shi. Hakama hancinta ya kusa shanyewa a kumburin fuskar, lips ɗinta sun zama ƙatin-ƙatin babu ƙyawun gani. Ga ƙafa a naɗe itama da uban bandage. A kwanaki biyar kacal ta sake wani irin mugun rama a jiki ta tashin hankali da baƙi, sai ƙaton kai da ƙatuwar fuska da ƙafa itama data kumbura. Da rabin idon nata take kallon su Oum da su Babban Yaya. Ga ƴar sanda mace dake gadinta har yanzu da handcuffs a hannunta. Sharrr hawaye suke rige-rigen sakkowa ta idon ɗaya suna zirara mata a cikin kunne. Tunda aka baro jejin nan da ita sai yau ne take ganin ƴaƴan data ɓata tsahon shekarunta na ƙuruciya akan fafutukar mallakarsu da mahaifinsu. Gasu dai zagaye da Fateema maƙiyayyarta suna take mata baya like sarauniya da fadawanta. Yanda ko kallonta babu wanda yayi a cikinsu ya sake tabbatar mata tursasa musu akai zuwa dubata yanzun ma.... Gaishetan da Oum keyi yay mata wani irin duka a zuciya da ƙoƙarin riƙe mata numfashi. Ita kanta bata san irin tsanar da taima matar nan ba. Musamman a yanzu da suke wata gaɓa mai tabbatar mata da taci wannan wasan. Fateema taci wannan game ɗin kota yarda koma karta yarda. Duk gwagwarmaya da faɗi tashinta sun tashi a banza. A banzan da bata da sauran ƙarfi ko damar canjawa ko aiwatar da koda ƙaramin abune daga tarin plans ɗinta. Babban tashin hankalinta jin Abah bai mutu ba, Mabera ya kuɓuta daga hannun jami'an tsaro. Mutuwar Nana ta girgiza ta a ƙasan zuciya, amma ta wani fannin sai take jin hakan ai nasararta ce. Koba komai a yanzu Nana da ƴaƴanta sun fahimci ita tafi ƙarfin uwarsu. Yanda Oum keta faman gaida Mamyn ita kuma ta tafi duniyar tunani bama jinta take ba balle ta amsa ya ɓatama AA rai. A fusace ya ce, “Please Oum kizo muje gida kema kina fama da kanki amma kin damu da wadda burinta ta ganki a ƙasa ke da ubanmu. Haba Oum wace irin zuciyace wannan haka kike da ita? Wlhy ko ƙaunar tunawa da wannan matar bana son yi balle ganinta a cikin idanuna. Bana son ganin fushinki ne kawai yasa na tako ɗakin nan amma da har abada bazata sake gani na ba. Sai dai bazaki taɓa bani umarni na tsallake ba koda na faɗawa cikin wuta ne dan ke mahaifiyace da har abada babu mu babu tsallake umarninki. Amma wadda kika tursasa mana zuwa mu gani ta sani, bamu zo nan dan ita ba sai domin ke, sannan ta rubuta ta ajiye, idan har wani abu ya samu mahaifinmu itama ta shirya amsar irin wannan sakamakon dai-dai da shi dan babu yafiya ko ragi kuma a tsakaninmu. Yaya let's go ”. Babu ko wanda ya musa masa tsakanin Yaya Fawzan da Babban Yaya suka kama hannun juna suka fice. Gefe Mamy da zuciyarta ke wani irin kumbura a cikin ƙirji ta maida kanta, sai hawaye masu zafin gaske suka ƙara ƙarfin gudu. Har su Oum najin yanda take jan ajiyar zuciya. Sumar tsaye Oum tayi ƙwarai da gaske. Ga wani irin jiri-jiri na neman ɗibarta sai da RK da Aunty suka riƙeta. Sai kawai itama Mamy ta fasa wata irin gigitacciyar ƙarar kuka har gadon na jijjiga. Kafin kace mi tari ya sarƙeta sai aman jini. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, Oum tai wata irin zabura ta rungume Mamy a jikinta tana kuka. Da sauri RK ya danna buttom ɗin dake bama alerm damar isarma da doctors saƙon ana buƙatarsu. Aiko sai gasu suna rige-rigen shigowa. Da ƙyar aka fita da Oum a ɗakin suka duƙufa kan Mamy.......
________★
A lokacin da nan ake duk wannan taƙaddama da kunji-kunji anan Giro baƙuncin mutanen Sen... Bukar su Gwaggo suka samu a safiyar yau. Domin kuwa tunda Rabilu ya fahimci al'amura fa na neman susucewa ubangidan nashi yan kwanakin nan sai ya tasashi da zuga da tunzurawa akan batun su Gwaggo, duk da kuwa Sen.. Bukar ɗin yafi ƙarfin ninkin baninkin ɗin abinda ya bama su Gwaggo akan Maanal sau dubu. Amma haka Rabilu ya dinga bin hanyoyi iri-iri da dagiya da naci badan komai ba sai dan in an amshi kuɗaɗen ya tsira dasu. Duk da dai a farko Sen... Bukar bai maida hankali ba sai ma kwaɓar Rabilu da yayi na cewar shi fa yabar wannan batun dan bashi bane a gabansa. Amma Rabilu sai yaƙi sakama ransa salama. Kwatsam ana haka kuma sai ga wannan al'amarin ya faru, Sen... Bukar baya ma Nigeria ba'a nan yay salla ba, sai kwana biyu da fitowar zuri'ar Darma ya dawo. Sai kawai suka shirya shi da abokansa da yan kanzaginsu na siyasa irin su Rabilun suka tafi asibiti duba Abah harda ƴan jarida dan su nunama duniya sunzo. Sai dai mi AA da kansa ya hana a barsu su shigo. To asibitin dai tamkar nasu ne, tunda mallakin kawunsu ne Rafeeq Kasheem Kura. Maimakon sun zo su nunama duniya zasu duba Aliyu Darma sai aka kuma nunama duniya su sunzo duba shi an hana su shiga. Yan jarida suka juya zance da faɗin lallai akwai lauje cikin naɗi, akwai kuma ayar tambaya a wannan al'amari. Domin kuwa anga manya-manyan jiga-jigan gwamnati ciki harda shugaban ƙasa da kansa yazo ya duba tsohon Ambassador'n Nigeria na Amerika Aliyu Abubakar Darma ba'a hanasu ba dan miyasa za'a hana su su Sen... Bukar ɗin da tawagarsu?...........✍️
Magana ta ALLAH AA baka ƙyautama Kawuna ba😏🤌🥱.175
........Kowa dai yasan Aliyu Darma ba ɗan siyasa bane, amma kasancewar ƴan manyan gida masu faɗa aji ta harkar kasuwanci a ƙasar dama wajenta yasa suna tare da manyan ƙasar tun daga kan shugaban ƙasa, gwamnoni, ƴan majalisu har zuwa ministoci da Sarakunan gargajiya. Dan yanda manyan keta kara kaina da kai-kawo hatta da manyan malamai ma ya ishi kowa shaida hakan. Rasuwa ce ta ƙaramar yarinya a gidan na Darma amma sai zuwa manyan suke gaisuwa mai haɗe da jajen abinda ya faru da waɗan nan ahali. To fa wannan abu ya girgiza duniyar su Sen.. Bukar ya kuma zafesu matuƙa. Dan haka suka kafa dandalin meeting ɗin rama abinda AA Darma ya aikata musu. Sai dai tako ina sun buga babu mafita. Har sun haƙura akan sai nan gaba idan ƙura ta lafa sai kawai maganar ƴan Giro tazo ma Sen.. Bukar a zuciya. A take ya bama abokan nasa labari tas, shine fa suka samo mafita suka maida akalar shirinsu akan su Gwaggo. A safiyar yau Sen... Bukar ya tura tawagarsa suyo musu ɗaukar amarya zuwa Abuja. Su Rabilu sun iso kuwa da sanyin safiya dai-dai lokacin da mutanen gari basu kai ga tafiya gona ba. Ta ko ina an taru group-group ana karin safe da raɗe-raɗen sunan haihuwa da aka samu a ƙauyen har guda uku. Yara dake cin uban gudu suna ihu ne suka fara fargar da manya gari halin da ake ciki. Dan kuwa sojoji ne har kusan su hamsin sukaima ƙauyen Giro dirar mikiya. A take kuma suka dinga kama mutane ana zubawa a motoci. Hankalin mata ya tashi matuƙa gaya, ga tsoro sunata afkawa ɗakuna suna kulle kansu ga tashin hankalin anata kame musu maza da yara matasan gari. Dan kuwa dai basa ɗaukar mata da kannanun yara sam. Da al'amarin yakai kukan kure har cikin gida suke shiga saboda wulaƙanci da tozarci ana zaƙulo mazan da suka samu ɓuya da matasa. Ta wannan hanyar ne suka ɗauki Babu dake fama da kansa dan zuwa yanzu jiyya yake mai tsananin gaske. Suka kuma haɗa da Gwaggo da Sailu dake kuka da ihu da kururuwar a taimakesu amma basu sami wannan taimako ba kam. Haka aka jefa su a mota aka wuce da su cikin babban birni, ashe al'amari babbane, ba nan za'a tsaya da su Gwaggo ba su. Dan sauran mutane an zubesu anan amma Gwaggo, Babu, Sailu an wuce da su birnin tarayya Abuja. Dan danan kuma aka saki Update wai an samu criminals da suka shiga garin Giro, dan haka jami'an tsaro sun zaƙulosu kaf yanzu haka suna a hannun hukuma. Kafin kace mi labari ya fara yawo a media tamkar wutar jeji.......
__________★
Azaba tayi matuƙar isar Mabera da Sille a cikin rami. Shima kansa Maberan ganinsa neman gushewa yake saboda azabar ciwon kai. Da ƙyar ya iya kama Sille suka fito ta cikin motar, babu zato jami'an tsaron dake ata kusa da motar sai gani sukai tana motsi. Dan da nan sukai shirin kota kwana duk da a farko sun tsorata da tunanin ko wani makamin ne mai fashewa. Sai da kukan Sille dake kiran a taimakesu ya ratsa kunnuwansu sannan suka shiga matsawa bindigu a ɗane. Cak suka tsaya suna kallon mutanen da suke wahalar nema tsahon kwanaki amma babu ko alamarsu. Dan nan suka zagaye motar, sai kuma aka fiddosu. Nan fa aka fahimci daga inda suke. Motar aka janye sai ko ga rami. Ai babu ɓata lokaci jami'an suka shiga binciken irin ramukan sai gasu da yawan gaske harda ƙaton ramin da suke tara gawarwakin mutane idan sun kashe. Babu ɓata lokaci sukai kiran IG. Kafin wani dogon lokaci jejin ya cika da jami'an tsaro da ƴan jarida masu ƙarfin hali. An tattare su Sille akayo gari da su domin kaisu asibiti, gari kuma ya ɗauki labari kamar wutar jeji. Ƴan jarida tuni sun fara sakin Update a media tako ina. Matuƙar tashin hankali mara misali iyayen gidan su Sille sun shiga. Burinsu kawai samun jami'an tsaron da suka kamasu su basu kuɗaɗe masu nauyi dan gama musu da su kawai kafin ma aje asibiti dasu. Sai dai ina hakan ya gagara sakamakon maganar ta girma da yawa balle shugaban ƙasa da kansa ya saka baki, ya kuma ɗora alhakin controlling ɗin case ɗin ga IG da kansa ba saƙo ba ko haɗa wani kwamiti.. General hospital na Abuja aka wuce da su kai tsaye. Aka zagaye jami'an tsaro da ɗakin da aka shiga dasu a tare. Sai da ya zam hatta likitocin da zasu dubasu zai da Jami'an suka tantance suka kuma bincike sannan suke shiga ɗakin. Dan danan aka rufu a kansu su duka biyun dan duk suna a cikin mawuyacin hali mai firgitarwa...
________★
Su AA na hanyar tafiya gida daga asibiti da suka bari a fusace suka sami labarin. Dan Uncle Najeeb ne yay kiran Babban Yaya yace sunga abinda ke faruwa kuwa a media yanzu-yanzun nan?”. Babban Yaya yace masa a'a. Ya ce ku duba maza. Koda ya yanke wayar Yaya Fawzan yay parking a gefen titi kowa sai ya fiddo wayarsa. A tare suka saki murmushi da sauke ajiyar zukata. Babban Yaya yace ma Fawzan. “Juya mota maza mu koma asibiti Fawzan”. Babu musu Yaya Fawzan yayi hakan. Lokacin da suke dawowa suma su Oum labari ya iso musu ta hanyar gani a television. Ga kuma Mamy dasu RK suka rufu a kanta sai hankalin Oum ya rabu biyu. Koda su Babban Yaya suka shigo kallo ɗaya tai musu ta ɗauke kanta. Suko ai ita suka nufa suka rungume a tare. Dan wlhy ba ƙaramin farin ciki sukaji da zancen kama matsiyacin mutumin nan da akai ba. Sai dai suna cikin wannan murnar kuma sai ga wani sabon labari akan abinda ya faru a ƙauyen Giro. Lallai babbar magana kenan....
________★
Maanal na tsaka da bibiyar labarin kama Mabera da ɗansa taci karo da badaƙalar Giro kuma. Ai babu shiri ta tashi zaune daga kwancen da take cikin kujera a falo dan bata jima da baro sashen Oum ba su duka su suna tare da su Umma saboda ƴan anguwa dake zuwa yin gaisuwar rasuwar Anum da jajen abinda ya faru. Tunda babu Oum sai su Umma baƙi dole su suke zama. Da farko dai komawa Maanal tayi kamar wadda ta suma a tsaye sai ga kiran Shahidah ya dawo da ita. Ƙasa ɗaga wayar tayi harta tsinke aka sake kira sannan. Shahidah dake kuka ta ce, “Manaal kinga abinda ke faruwa kuwa?”. Sharr hawaye suka shiga rige-rigen sakkoma Maanal. Wato shifa tushenka dai tushene komi akai maka na bakantawa a cikinsa tuwo sunansa tuwo, sannan jini sunansa jini. Murya na rawa Maanal tace, “Na gani Didi, amma wlhy ni naji a raina wannan zancen ba gaskiya bane. Kaf asalimu babu ɗan ta'adda akwai abinda yake ba dai-dai ba dai”. “Tabbas maganarki nakan hanya, amma duba videon dana tura miki ta WhatsApp sannan”. Kafin ma Shahidah ta rufe baki Maanal ta katse kiran, WhatsApp ɗin ta shiga dama data ɗinta a buɗe take. Videon ma har ya buɗe. Koda ta shiga nutsuwa tai tana kallon yanda ake ɗibar mutane kamar an samu wasu dabbobi. Da farko bata fahimci komai ba face ganin yanda ake tozarta musu ahali dan taga waɗanda ta sani sosai a ciki harda ƴan gidansu duk da wahala tasasu canjawa daga yanda ta sansu a shekaru tara baya. Shahidah tai kiranta tace, “Mi kika gani?”. “Banga komai ba Didi sai cin mutunci da tozarta ahalinmu”. “Ba shine saƙon da nake son isar miki ba Maanal. In ce dai baki manta da yaron tsohon mutumin nan da yace hana sonki ba har ya ɗakko su Gwaggo ya kawo Kaduna shekara ɗaya data wuce?”. “Tabbas zan iya mantawa da shi Didi, dan bawani kallon tsaff nai masa ba a lokacin hatta shi kansa tsohon banzar. Amma kimin bayaninsa mana?”. “Ba bayaninsa keda amfani ba, tabbatar da shi ɗin ne ko bashi bane mai amfani. Ki ƙoƙarta dai bari na amsa kiran Amaal ina zuwa”. Ƙitt Shahidah ta yanke kiran, dai-dai Maanal na kaiwa zaune jagwab sai ga AA ya shigo. Kai tsaye inda take yayo yana faɗin, “Are you okay?”. Kanta ta jinjina masa kawai, sai kuma ta miƙa masa wayarta tana faɗin, “Besty zaka iya gane yaron mutumin nan Sen... Bukar dan ALLAH? Ba ɗansa na cikinsa ba, wanda muka taɓa haɗuwa da shi a ƙofar Mawaad harda su AS randa kuka fara ɗaukata a mota?”. AA dake kallonta ya ce, “Sosai ma kuwa, duk da ba yaron da kowa ya sanshi da shi bane sai ta hanyar neman matan banza da yake masa ni na sanshi dan a kanki ma har kamashi sasa anyi yay kusan sati biyu a police station sai shi Bukar ɗin ne ya fitar da shi”. Sosai Maanal ta sauke ajiyar zuciya, tare da faɗin duba videon ka gani dan ALLAH ”. Komai bai sake cewa ba ya amshi wayar ya buɗe videon, nutsuwa yay ya kallesa daga farko har ƙarshe duk da kuwa da tsawon mintuna biyar ne. AA ya jinjina kai tare da dawo da videon baya yana nuna mata fuskar Rabilu daya tsayar dai-dai shi, abin mamaki yana sanye da kayan sojoji shima. “Tabbas wannan shine, hakan na nufin wannan abun shirine ke nan? Amma taya akai Bukar yay amfani da jami'an tsaron soji haka?”. “Ta hanyar makirci mana in har ta tabbata shi ɗin ne da hannunsa a ciki. Zai je ya shirya musu abinda basu sani ba, kuma su basu da laifi, a halin da ƙasar nan ke ciki musamman ta yankin namu ko yaya wani magana zai fito akan bara gurbi jami'an tsaron mu zasuyi kowane irin yunƙurine su, kuma basu da laifi dan aikinsu ne yin hakan a garesu kuma shine dai-dai”..........✍️
Na haƙura AA aci uban kawuna a wannan gaɓar🥱🏃🏃🏃
176
..........“Lallai maganarki na kan gaskiya kam, kuma bana raba ɗayan biyu shine ya shirya komai, wato abinda akai musu a asibiti shekaran jiya shine zasu juyashi akan bayin ALLAH da basu ji ba basu gani ba. To lallai banga ta zama ba. Dole ina buƙatar ganawa da shugaban ƙasa yanzun nan”. “Amma Besty kai kasan hakan bamai sauƙi bane. Haka nan ɓakatatan rana tsaka kaje kace zakaga shugaban ƙasa duk da kusancin da kake da shi a tsakaninku”. “Na sani Besty, amma wannan maganar bata waya bace ba. Dan haka bani wayata a ɗaki, cikin bed side drawer ”. Miƙewa tai da sauri, dan wayar itace yake da ajiyayyun numbers na manyan mutanensa, baya kuma fita da ita ko ina daga office sai gida. Taɗan fara haye stairscase da ɗan gudu yace, “Please bar gudun nan tafi a hankali”. Juyowa tai ta kallesa, sai kuma ta koma yin tafiyar batare da tace komai ba. Babu jimawa ta dawo masa da wayar, yana tsaka da rubuta massage da zai turama shugaban ƙasa sai ga su Babban Yaya da Fawzan har ma da su Baba Sardauna. Hijjab Maanal ta ɗauka ta saka, sannan ta nufi ƙofa ta buɗe suka shigo. Cike da girmamawa ta gaishesu bayan sun zauna. Jaje sukai mata na abinda ke faruwa, kanta a ƙasa tana share hawaye Baba Sardauna yace, “Ba abin kuka bane kinji yarinyata ƴar albarka. Addu'a zamuyi kuma ALLAH na tare da masu gaskiya komai zai warware, in har basu da laifin komai za'a sake su.” “Ai bama su da shi, shiri ne kawai wannan abun Baba”. AA ya faɗa dai-dai yana gama turama shugaban ƙasa text. Da mamaki duk suke kallonsa. Ya ɗauki wayar Maanal ya latso musu hoton Rabilu.” Babban Yaya ne kawai ya gane Rabilu, ya kalla AA yana faɗin, “Ajwaad wannan ba yana cikin tawagar yaran su Bukar Kaugama ba kuwa?”. “Tabbas yana ciki Yaya, dan yaronsa ne ma na kusa sosai. Idan ka kula bai san ana ɗaukar wannan video ɗin ba.” “Lallai bai sani ba kam, to miya haɗa shi da kayan soji kuma?”. “Wannan shine Abin tambayar kuma abin nazari, amma idan zamu kalli al'amarin ta wata fuskar zata iya yiwuwa yaje musu matsayin wanda keda information ɗin ne, ko kuma su sojojin bana gaskiya bane ba...” Baba da yay shiru yana nazari ya ce, “Bazasu tura sojojin daba na gaskiya suyi wannan ɗanyen aikin ba, akwai dai abinda yake ba daidai ba dole. Amma ina zuwa bara nai kiran mataimakin gwamnan nasu.” Dai-dai nan Maanal dake hawaye ta dawo ɗauke da basket data zubo gorinan ruwa. Sai kuma gasu Umma sun shigo harda Oum data baro asibiti da Ammie da suka iso ita da Hajiya Yaya. Karo na farko kuma da Hajiya Yaya tazo gidan Darma. Duk da halin da ake ciki kallon ko ina take tana faman jinjina kai....
Da gudu Maanal tazo ta shige jikin Oum, Oum ma ta rungumeta tana lallashinta saboda Baba Sardauna na waya da mataimakin gwamna, yana masa kuma bayani dalla-dalla ta yanda suma suke samun bayani a yanzu-yanzun. Dan ta ɓangaren su shugabanni basu san komai ba suma sai yanzu da videos ɗin ke yawo, wanda aka samu wasu yara ne ƴammata suka ɗorashi a social media. Ya kuma tabbatar ma Baba a yanzu haka sun buƙaci ganin shugaban soji na jihar ma baki ɗaya. Sannan an sake tura jami'an tsaro garin Giro ɗin ma domin bama mata da yara da aka bari a garin tsaro. Baba Sardauna na gama sallama da mataimakin gwamna ya ajiye wayar yana jinjina kai da faɗin, “Lallai wannan ƙulli ya ƙullu. Dan haka bamuga ta zama ba dolene mu wuce Giro a yanzun nan. Sannan duk inda wannan yaron Kaugama yake a kamashi kafin suyi wani siddanarun makircin”. Dukansu sun gamsu da bayanin Baba Sardauna ɗin. Babu ɓata lokaci Babban Yaya ya miƙe yana faɗin, “Wannan aiki nane game da kama shi yaron Kaugaman, bara na nemi abokina Deen”......
_________★