Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 134
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 134: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 134. .........Sabuwa kam kuka take…
3,970 words
.........Sabuwa kam kuka take tana ƙarawa. Dan ganin wannan kaya ya dawo mata ne da mutuwar ƴarta sabuwa fil a zuciya. Da yake tana a gidansu ne bata koma nata gida ba har yanzu. Sai mahaifiyarsu ta bada shawarar akai kayan can tunda itama dai can zata koma da zama. Mizai faru, kawai sunje kai kaya suka samu gida a kulle an tile mata komai na gidan a compound. Mamakin ALLAH ya kama Sabuwa. Babu shiri ta shiga maƙotamsu tana tambaya. Bayan sun sake mata gaisuwa basu ɓoye mata komai ba sukace ai Hajiya Zahedah ce da mijinta da wannan aikin. Hatta motocin gidan gudan huɗu, tata ɗaya, sai ta Nazeerah dana Mabera biyu duk su suka kwashe. Ama taƙaice mata zance gida dai sun saida shi. Sai dai kuma a yau wani sabon rikici ya sake tashi akan ai mijinta ma ya riga ya saida gida kafin ya tafi shima, yanzu haka ita Hajiya Zahedah da mijin nata ma suna police station. Sunan station ɗin kawai ta amsa itama, tace motar kayan Nazeerah ta koma da su can gidan babanta. Masu mota haushi ya fara kamasu. Amma da yake ta ƙara musu kuɗi sai suka juya suka koma. Ita kuma ta nufi police station ɗin da akace mata ana rikici tsakanin su Bakori da wanda suka sai gida a hannun Mabera. Tako tadda rikicin, dan har ana fara bama hammata iska sai da jami'an tsaron station ɗin suka shiga ciki. Zuwan Sabuwar kuma rikicin ya sake sama. Gata tana fama da ɗaurarren hannunta mai karaya. Ƙafarma cike da ƙarfin hali take takata. Faɗa ya sake tashi tsakanin Hajiya Zahedah da Sabuwa. Bakin Hajiya Zahedah ya suɓuce ta ce, “Wai shin Sabuwa mi kike taƙama da shi? Kin haihu da Mabera kawai? Shiyyasa kike ganin kina da wata isar banza da wofi akan dukiyarsa. To ai kin yi ta banza dama wofi, dan nima nawa ƴaƴan ai jininsa ne sunma fi naki ƴaƴan gadon tunda su maza ne!!”. Wani irin shiru station ɗin ya ɗauka na sakanni like shirun nan da yara ke faɗin mutuwa ta ratsa, da ba'ai shiru ba data ɗauka😆😂. Kowa yayi wani irin galala yana kallon Hajiya Zahedah har shi mijin nata Bakori. Sai da Sabuwa ta karya alkadarin shirun da faɗin, “Ƴaƴanki ƴaƴan mijina ne kuma Zahedah?”. Shiru Hajiya Zahedah tayi dan ta fahimci kam dai tayi ɓarin baki a wannan gaɓar, sai kuma ta ɗan kalla mijinta kaɗan, ganin ita yake kallo shima da sauri ta kauda kanta. Sai kuma ta maida ga Sabuwa zata fara borin kunya mijin nata ya daka mata tsawa yana wani irin miƙewa. Da sauri ta koma jikin bango ta maƙale, cikin matuƙar tsawa ya ce, “Zahedah! Maimaita abinda kika faɗa! Ƴaƴan nawa ne kike kira da ƴaƴan Mabera?!”. Cikin rawar jiki data baki ga hawaye Hajiya Zahedah ta shiga rantsuwa ita ba haka take nufi ba. Ita wlhy kawai dan tana son su amshi gidan ne kamar yanda yace suyi... Ganin tana ƙoƙarin tona masa asirin shirin da sukayi akan ƙwace gidan Sabuwar ya sashi sharara mata maruka sai da ƴan sanda suka riƙeshi. Ai ko ya dinga babbotai bazai yarda ba wlhy sai sunje yau ɗin nan an musu gwaji shi da yaran kaf. Da ƙyar ƴan sanda suka tausashi yay shiru. Daga nan aka kwashesu zuwa asibiti. Suma yaran akaje aka ɗibosu da yarinyar Sabuwa ɗaya data rage......
________★
Tunda su Saheeba suka shigo gidan ta saka maigadi ya rakasu inda kabarin Anum yake. Durƙushewa tai tana kuka mai ban tausayi. Shike nan ta rasa ƴar Anum ɗinta. Ƙyaƙyƙyawar yarinya mai tsannanin kama da mahaifinta. Anum na sonta fiye da Naufal. Duk da dai shima har yanzu yaro ne. Amma yanda Anum ke ƙulafucinta shi sam bayayi, gaba ɗaya rayuwarsa ma yafi sonta a sashen Oum. Nuratu data riƙota tace, “Aunty ya zamuyi, shike nan mun rasa Mama mun rasa Anum a lokaci guda. Na rasa Yaya AA kema kin rasa cikin da akasha wahala kafin samunsa kin rasa mahaifarki har abada. Shike nan Aunty mun rasa komai”. Suka sake fashewa da kuka. Sun jima sunayin abinsu babu mai lallashi dan babu wanda ma yasan suna a wajen kowa hankalinsa nacan akan Nuwaira maijego. Daga ƙarshe dai da ƙyar Nuratu ta saka Saheeba suka taso suka dawo sashensu. Babu kowa a sashen dan Ameerah ma tana can sashen Oum. Su Babban Yaya kuwa suna sashen baƙi tare da su Uncle Najeeb. To haka dama ita rayuwa take, ana bikin duniya wasu ke na kiyama. Lokacin da kai kake kuwa wani a lokacin yake samun farin ciki, sanda kake farin ciki wani a lokacin yake kuka. Shiyyasa kuma masu iya magana sukace IDAN ZAKA GINA RAMIN MUGUNTA, KA GINA SHI GAJERE DAN MAYBE FA KAI NE ZAKA AFKA BATARE DAKA SANI BA. Ga dai Saheeba komai ya suɓuce ya ƙare a gaɓar da ba'a shirya ba ko hasasowa balle tsarawa. Kullum cikin shiryama rayuwar wasu MUGUNTA ake da son taɗe su. Ba'a shiryama zuciya da rayuwa alkairi sam tamkar suke da yau da gobensu. (Ƴan uwa sai mu hankalta. Mu kuma sani duk yanda ka kai da muguntarka baka isa canja ƙaddarar kowa ba. Haka taka a karan kanka. Kana can kana shirya ma wani bala'i kai bala'in na tunkaro rayuwarka baka sani ba. A maimakon damuwa da damuwar wani ko burin tarwatsa shi yafi ƙyautuwa mu maida hankali wajen addu'ar neman kariya da wadatuwa da ƙyaƙyƙyawar zuciya. Mu saka gaskiya a dukkan al'amuran mu wlhy sai kuga anata bugawa haggu da dama amma an kasa cimmaka. ALLAH zai tsare ka ya kuma baka kariya tako wane ɓangare) A wannan gaɓar ma Nuratu ta fi Saheeba ƙarfin hali, dan ita ta taimaka mata tai wanka ta fita samo mata abinci. Sai ta samu Ameerah a kitchen, bata kulata ba itama Ameerah sai tai kamar bata gantan ba ta cigaba da aikinta. Dama cikin haushin Babban Yaya ya tasota tana hirarta wai ta masa kunun gyaɗa. Indomie Nuratun ta shiga store ta ɗakko, ta buɗe fridge ta ɗauki ƙwai. Ameerah dai nata faman motsa kununta kamar bata san da ita ba. Sai kawai Nuratun ta dinga jin kamar ta ɗaga tukunyar kunun ta kife a fuskar Ameerah ɗin.. Da sauri wani sashi na zuciyarta ya gargaɗeta. (K Nuratu ki dawo hankalinki, yanzu abinda duk ya faru da ku bai zame miki iznah ba kenan. In dai ba so kike babban Yaya ya saki ƴar uwarki ku tattara ku koma Kanon da baƙya so ba toki kama kanki) Ajiyar zuciya ta saki a ɓoye. Sai kuma ta ajiye kayan ta fita akan sai Ameeran ta gama ta dawo. Ameerah da duk take sane da ita tai murmushi da faɗin, “Ashe gyaɗa dai taji matsa. Ai na zata zaki kawo min wani wargi ne na baki mamaki.” haka ya kammala aikinta harta kwashe tabar kitchen ɗin Nuratu bata dawo ba. Sai da tai wanka ta fito falo Babban Yaya ma ya shigo dan tare sukai wankan sannan taji motsin Nuratun a kitchen. Batai magana ba sai shi Babban Yayan, batare data kalli ko hanyar kitchen ɗin ba ta bashi amsa da, “Nuratu ce”. Kawai tai shiru. Bata sake magana ba ta cigaba da bashi kunun. Mizai faru Nuratu na fitowa zata gitta da indomie ɗin nan ƙamshinta ta daki hancin Ameerah. Da sauri ta miƙe tana toshe hanci. Gudu-gudu sauri-sauri tabar falon. Shi babban Yaya ma sai abin ya girmeshi. Ya bita da kallon mamaki kawai yana kallon kununsa da bata ƙarasa zubawa ba. Itama Nuratu sai tai kasade tana bin hanyar da Ameerah tabi da kallo. Tsohon lokaci zuciyarta na bugun ɗari-ɗari kafin taja ƙafafu da ƙyar zuwa sama. A yanda ta shigo ɗin ya saka Saheeba kallonta da jajayen idannunta da har yanzu hawaye sun gagara tsayawa a cikinsu. “Lafiya kuwa?”. “Da dai sauƙi kam Aunty, anya yarinyar nan ba cikine da ita ba?”. Mugun faɗuwa gaban Saheeba yayi, ta ce, “Wace yarinya?”. “Ameerah mana!”. Ai tsabar yanda maganar ta daki Saheeba bata san ta zubo ƙasa ba daga gadon. Lips ɗinta na rawa ta ce, “Mimm mi mikika gani?”. Tsaff Nuratu ta kwashe labari ta bata. Gaba ɗaya Saheeba sai taji kamar kanta zai fashe dan tashin hankali. Dole ta zube a kwance jin ɗakin kansa na juya mata.....
★★ Anan falo kam jin shiru Ameerah bata dawo ba Babban Yaya ya tashi ya bita. Yana buɗe ɗakinta ya shiga dai-dai ita kuma ta fito daga bathroom tana goge fuska da ƙaramin towel. Kallonta ya tsaya yanayi, sai kuma a hankali ya ce, “Miya faru?”. Fuska ta yamutsa, kamar zatai kuka tace, “Ba komai fa. Kawai warin indomie ɗin can da Nuratu ta gitta da ita ne ta nema ɗaga min hankali”. Kallonta kawai yake yi, shi dai indomie ɗin can baiji tana wani wari ba. Hasali ma ƙamshi yaji. To lafiya kuwa Ameeransa take. Tunaninsa ya katse saboda matsowar da tai ta kama hannunsa tana faɗin, “Muje kasha kunun kada ya huce”. Riƙota yay ya saka a jikin shi. Cike da kulawa ya ce, “Amai kikayi?”. Kanta ta jinjina tana sake narke masa. Ya ɗan furzar da ajiyar zuciya da faɗin, “Bar batun kunu muje na kaiki asibiti”. “No! Yaya nifa babu abinda ke damuna. Ƙamshin indomie ɗin ce kawai bana so.” Ganin yay shiru yana kallonta ta marairaice masa fuska da faɗin, “ALLAH da gaske nake ni lafiyata ƙalau”. “Shike nan naji, basai kin min kuka ba muje”. Yay maganar yana kama hannunta suka fita. Wajen dining ɗin suka koma ta zuba masa kunun ta miƙa masa. “ALLAH yay miki albarka”. Ya faɗa a hankali yana kallonta. Zama tayi itama a kujerar kusa da shi ta saka kanta a kafaɗarsa ta amsa da “Amin mijina”.........✍️
Ehem-ehem 🤣. Nace nayi shiru ko nayi magana🤯😂.180
........Ta tabbata dai Sille ya makance, dan kuwa likitoci sun tabbatar da jinkirin kwanakin da aka samu batare da kawoshi asibitin ba ƙasa cike da idanun sun lalace. Kuka sosai Mabera ya dinga yi, dan shi an masa maganin nasa ciwon kan. Yanda yake darzar kuka haka Sille ma ke kuka. Gasu duk an maƙale hannayensu da Handcuffs babu damar zuwa wajen juna duk da suna a ɗaki ɗaya. Gashi yau da safe ganin da Mabera yayi a labarai cewar Aliyu Darma na cigaba da samun lafiya har ma ya fara magana yay matuƙar tsaya masa a zuciya da ruhi. Har ya gama ƙulla ta yanda zai haɗa baki da cikin ma'aikatan aje ai masa aiki akan Abah ɗin da Kamila. Dan haka yanzu da Nutse ya shigo domin saka musu ƙarin ruwa cikin raɗa yacema Nurse ɗin, “Abokina idan bazaka damu ba muyi magana mana”. Nurse dake ƙoƙarin haɗa allurai a cikin ruwan da zai saka musu ya ce, “Ina jinka Alhaji”. “Idan na saka ka wani aiki na baka miliyan hamsin zakayi”. Shiru Nurse ɗin yay yana kallon Mabera, sai kuma a sace ya kalla alluran daya saka a ruwan nan. Tuna alluran minene ya sakashi sakin murmushi, sai kuma ya kalla ƙofar shigowa. Kafin ya sake dawo da dubansa kan Mabera. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Ina jinka, mi kake so ai maka?”. “Idan babu damuwa ka bani takarda da alƙalami zan rubuta maka. Sai dai ka sani idan kaci amanata wlhy yarana bazasu barka ba”. “Baka da matsala Alhaji in dai nine. Ai kaga dai kullum nike zuwa ina treating ɗinku, sai doctor. To kuwa kasan bazanci amanarka ba dan bazanyi wahalar kamawa ba”. “Hakane kuma tabbas”. Cewar Mabera cikin gamsuwa. Takarda da biro Nurse ɗin nan ya bashi, tsaff Mabera ya rubuta masa komai sannan ya amshi aron wayarsa. Wasu numbers yasa yay kira, babu jimawa kuwa aka ɗaga. Sai ga muryar matashi namiji. Mabera ya ce, “Ra'iz Baa! Ne”. Cikin matuƙar rikicewa daga can Ra'iz yace, “Baa! Akace an kama ku, an kashe min ku!?”. “Ƙarya ne Ra'iz kwantar da hankalinka daina kuka. Muna nan da rammu cikin ƙoshin lafiya kuma. Yanzu abinda nake so da kai ka tsaya ka saurareni da ƙyau.” “To Baa! Ina jinka, amma dan ALLAH ina Broth?”. “Yana a tare da ni kada ka damu zan haɗaka da shi. Idan mun gama. Akwai wani mutumi dazan haɗaka da shi, shine mai wannan layin dana kiraka. Ka bashi 50m yau ɗin nan. Ka haɗashi da Dr Ozaya zai bashi wani saƙona dake a hannunsa. Akwai wani aiki ne da zai mana. Sannan ka gayama su Ɗan-hau aikin dana basu su aiwatar kawai daga nan zuwa gobe. Kai kuma ka tattara komai namu dake hannunka yanzu zan kira Lawwali gobe yazo ku wuce Niger, zamu haɗu da kai a sabuwar ƙasarmu”. Cikin jin kwanciyar hankali Ra'iz yace, “Shike nan an gama Baa! Ina Broth ɗin?”. Wayar Mabera ta bama Nurse ɗin nan yace ya bama Sille. Koda ya bashi sai ya dawo ya sakama Maberan nashi ƙarin ruwan, shi kuma Sille suna magana da Ra'iz. Yana kammalawa ya koma kan Sille shima ya saka masa, daga nan ya amshi wayarsa ya fice yana sanar masa sai kuma anjima ya dawo cire musu ruwan.. Yana fita Mabera yay murmushi, ransa fal farin ciki. Ya tabbatar in har su Ɗan-hau sukai wannan aikin a gobe shi da Sille zasu bar asibitin nan. Hakama zai shafe babin Kamila tunda ita tace mai taurin rai ce......
________★
Maanal na kwance jikin AA ya gama hutawarsa hannunsa akan cikinta daya fara tasawa dan har ana ganin tudunsa. Ganin yanda ya fara sauke numfashi a hankali yasa a shagwaɓe faɗin, “Wai barci zakayi ma?”. Kansa kawai ya jinjina mata. Itako ta sake shigewa jikinsa tana tura baki. “Ammafa in ta gaskiya za'ayi ba haka mukai da kai ba Besty. Dan ALLAH ka tashi muyi wanka sai muje shan furan. Daga can basai muga idan su Ammie sun iso ba?”. Cikin Muryar son yin barci yana sake riƙota jikinsa ya ce, “Besty zamuje, Please ki barni na ɗanyi barci kaɗan”. “Ni gaskiya a'a ai ba haka mukayi da kai ba”. Shiru ya mata, zata sake magana yasa tafin hannunsa ya rufe mata bakin, dole tai shiru. Duk mutsu-mutsun ta kuma bai barta ba. Tun tana masa ƙananun duka har itama barcin yaci ƙarfinta. Dama yasan shi take ji, rigima ce kawai da fitinarta. Shi yanzu yanda garin nan ke ɗaure da hadari ina zai ɗauketa suje. Su Ammie kuwa tun ɗazun sun iso, baya son yaje ne tace zatai aiki shiyyasa yace mata basu iso ba sai an jima. Barci kuwa suka sha sosai, dan kwanakin nan gaba ɗaya basa samun isashen barci. Raba dare suke a nafilfili da addu'oi. Da safe kuma ba dama gida cike da mutane ga zuwa asibiti. Balle kwana biyun nan lamarin mutanen Giro shima yana cin lokaci su sosai. Lokacin da suke farkawa yana kallonta kawai yaji dariya tazo masa. Dan tai wani irin zubawa agogon ɗakin idanu ne hawaye share-share a fuska. Ya tabbatar idan yay dariyar nan matsala za'a samu. Dan haka ya ɗauka ƙasa yay kneeling ya kama kunnuwansa duk biyu. Pillow Maanal ta ɗauka ta fara kai masa ƙananun duka. Shi ko ya shiga kare kansa yana dariya. Da ƙyar ya kamata ita da pillow ɗin ya rungume gaba ɗaya. “I'm sorry Sweetheart, na tuba na tuba...” “Ba dariya kake min ba, shine ka tuba. Ni ka sakan babu ruwana da kai, kuma ALLAH saina haɗaka da Abana”. “Nace fa kiyi haƙuri, ki rufa min asiri da haɗani da Abah ɗin nan, haka kawai ya sake amshe min ke sai bayan wata biyu ya bani. Wlhy bazan iya jurewaba wannan karon, sai dai Oum ta haɗamu duka ta riƙe kawai dan nima sashen nata zan koma”. “Basai na koma Kano ba”. Ta faɗa tana dariya cike da ƙeta. Fuska ya ɗan ɓata. “Oh dariya ma kike min?”. Jikinta ta janye a nasa tana masa gwalo, ya bita zai kama ta zille. Haka ya tashi ya bita suka shige bayi. Sun jima a ciki kafin su fito, kowanne da rigar wanka alamar shi sukayi. Da taimakon juna suka gyara jikinsu. Sukai shirin barci. Tea kawai suka sha suka sake komawa gado suka kwanta bayan sunyi shafa'i da wutri dan yau zasu ɗan yi barci. Yana rungume da ita suna hirarsu ƙasa-ƙasa akan haihuwarta barci yay awon gaba da su kusan lokaci ɗaya. Basu sake sanin kansu ba sai asubahi.....
_______★
Anyi gwajin yaran Hajiya Zahedah duka, dana Salima ƴar Sabuwa. Hakama Bakori mijinta. Haka sukai zaman jiran result ana ƴar hararar juna. Sai dai babu damar yin magana dan akwai jami'an tsaro a tare da su. Mizai faru kawai an tura su wajen likitar da zata musu bayanin result ɗin Hajiya Zahedah taci karo da abinda ya hargitsa mata lissafi. Domin kuwa dai likitar nan ba kowa bace face ƴar aikinta data kamasu ita da Mabera a shekarun baya har Mabera yay mata fyaɗe. Kar-kar jikin Hajiya Zahedah ya shiga rawa. Itako likita tayi ma kamar bata santa ba, haka suka zauna duk tana a ɗarare. Shi kansa Bakori da ita kanta Sabuwa kallon sani sukema likitar, amma yanda ta kame babu alamar wasa a tare da ita ya saka suka nutsu. Waya ta ɗauka tayi kira, babu jimawa wata matashiya kamarta tare da dattijuwa suka shigo. Dattijuwar ta kalla cike da girmamawa tana tashi a kujerarta ta bata, ta ce, “Mama bismillah,” Wadda ta kira da Mama ɗin tace, “Miya faru Jameelah?”. “Babu komai Mama, result ɗin ne dai ke ya kamata ki faɗa saboda wani dalili. Ban buɗeba gashi nan suma suna gani, sannan ban san su waye ba sai yanzu da aka tura min su. Dan haka ki fara dubawa su san sakamakon kafin nai muku bayani”. Baki Hajiya Zahedah ta buɗe zatai magana security ɗin dake tare da su ya daka mata tsawa. Dole kuwa taja bakinta tai shiru. Zama Mama tayi, ta buɗe duka result ɗin tana dubawa, sannan ta miƙama ɗayar da suka shigo tare tace tai musu bayani. Aiko dalla-dalla waccan tai musu, daga ƙarshe ta tabbatar ma da Bakori yara manya mata guda biyu na farko sune ƴayansa. Amma sauran guda ukun duk ba nashi bane ba. Suna da alaƙar jini da Salma ƴar Sabuwa. Cike da borin kunya Hajiya Zahedah ta tashi zata fara hauka mijinta ya kwasheta da mari. Zai ƙara na biyu aka rirriƙeshi. Dr Jameelah tai murmushi mai ƙayatarwa, cike da nutsuwarta da kamewa tace, “Hajiya Zahedah kenan. A ganina ai lokacin wani kai-kawo da pretending ai ya ƙare kuma. In ce shima tsinannen kwarton naki yana hannun hukuma ne. To miya rage, kema ki miƙa wuya kawai zaifi miki sauƙi ai.” “To ke ina ruwanki? Ke wacece?”. “Ke kin san ni wacece, domin tun shigowarki ofishin nan kin shaida hakan. Alhaji nasan kaima dole kana min kallon sani, to kwantar da hankalinka yanzu zaka sha labari. Ina fatan baka manta da Jame ba mai aikinku shekaru kusan goma da suka shige zuwa sha biyu. Yarinya ƙarama da aka kawo muku daga ƙauyen soba daka hana na dinga taɓa maka duk wani abinda ya shafi abincinka”. Shiru Alhaji Bakori yana nazari, zuwa can ya ce, “Tabbas anyi haka baiwar ALLAH. Daga baya kuma na nemeki na rasa lokacin kin fara tasawa da canjawa tunda a ƙalla kin kai shekara biyar a tare damu”...........✍️181
.......“To Alhamdullah tunda har ka tuna. Na ɓace ne a duniyarku sakamakon wannan matar taka da kwartonta Mabera. Dan kuwa tun farkon zuwana gidanku duk da banda wani isasshen wayon sanin mi suke aikatawa na fahimci komai. Saboda da zaran ka fita aiki yara sun wuce makaranta shi kuma zai shigo gidan. Haka zasu kwashe a wanni a ɗakinta ko naka. Da yake da haɗin bakin maigadinka yake shiga hatta da daddare idan kai tafiya zuwa yake gidan ya kwana. Da farko rashin wayo yasa nai tunanin ko ana auren maza biyu ne, sai kuma koma tunanin shi ɗin ɗan uwanta ne ko naka. Sai a hankali a hankali na gane cin amanarka fa akeyi. Ina son faɗa maka ina jin tsoro, har takai abun nasu ya isheni ranar na fito na kamasu a falo babu kunya babu tsoron ALLAH nace sai na tona musu asiri. Shine ya kamani yay min fyaɗe a gabanta suka ɗaukeni suka kai garinmu da gargaɗin idan na sake dawowa cikin Kaduna sai sun kasheni. Da yake UBANGIJI ba azzalumin sarki bane sai ya haɗani da Mama, sunje garinmu wani aikin asibiti mamana ta kaini asibiti saboda halin da nake ciki da suka gane kaina bayan sunyi maganin aljanu, sunyi na mayu dan ban faɗama kowa ba sai suka ce bari su gwada na asibiti. Anan ne Mama ta gane fyaɗe akai min. Ta tsareni da tambayoyi, naso ɓoye mata itama amma ta nuna min taimakona zatayi. Hakan shine sanadin komawata yanda nake a yanzu. Dan kuwa ta ɗakkoni daga ƙauyenmu tazo tai min magani, bayan na warke sarai ta sakani a makaranta har ALLAH ya kaini ga kaiwa wannan matsayin na likita. Yanzu haka inada aurena harda yaro ɗaya gani da cikin na biyu, ina auren babban likita da ayanzu haka shine akan case ɗin Mabera dan shi ne ma ke kula da shi” Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un Bakori kawai ke faɗa, bai ma san sanda ya damƙo Zahedah ya shaƙe ba yana kuka da dukanta yana tsine mata albarka ita da Mabera. Da ƙyar aka amshi Zahedah a hannunsa, har ma ta suma dan wuya. Kafin kace mi ƴan jarida sun iso asibitin. Dan yanzu komai ƙanƙantar abu akan Mabera ba'a wasa da shi musamman ga ƴan jarida da ƴan sa kai masu ɗauka a wayoyi. Abu kamar wutar jeji dandanan gari ya ɗauka, abubuwa suka fara yawo a media da gidajen tv. Kowa sai sake yin ALLAH wadarai yake da al'amarin Mabera. A karo na farko kuma bbc suka buƙaci yin hira da Bakori. Bai ko musa ba ya bada haɗin kai....
Idan kunji ana zazzaga to ita Bakori yay ma Mabera a wannan rana. Dan kuwa wasu manyan sirrikan Mabera da babu wanda ya sani sai UBANGIJI sai shi dake abokinsa, shima kuma bawai ya fito ya sanar masa bane kawai dan bakorin na bibiyarsa ne ya sani yau ya buɗema duniya su. Ciki kuwa harda kashe mahaifiyarsa da Maberan ne ashe yasa akayi, da ƴan uwansa biyu maza suma daya kashe a shekarun baya. Ya kuma tabbatar da Mabera na tare da manyan ƴan siyasa ne ta ƙarƙashin ƙasa shiyyasa yake aikata duk abubuwan nan batare da an taɓa ko kamashi ba. Hatta kidnapping daya kafa sansanin yi duk da shi yana gida kwance shike bada information ɗin da yaran ke bi su kama mutum su amshi kuɗin a kawo masa ya basu abinda ya gadama ya raba sauran da iyayen gidansa. Anyi-anyi Bakori ya faɗi su waye iyayen gidan nashi yace shi baza'a ji mutuwar sarki a bakinsa ba. Su jami'an tsaron da suka kamashi su bincike sa mana ai ya musu sharar fage tunda ya fito musu da ainahin wanene Mabera batare da shan wahalar bincike ba. Daga ƙarshe yace akwai babban yaron Mabera dake zaune a Niger sunansa Lawwali shike masa safarar kaya daga Niger zuwa Libya, Sudan, har zuwa Nigeria. Sai yaronsa ƙarami da baida ƙafafu yana a Lagos shima shegen kansa ne dan babban dila ne na ƙwaya....
_______★
Wannan saƙon hira ya isa har kunnen Mabera a television ɗin dake a ɗakin jiyyarsa, rawa jikinsa ya fara yi kar-kar, dan kuwa Bakori ya gama kwance masa komai daya rage. Ashe dama shegen mutumin nan da yake kallo sakarai yana amfani da shi ne ashe komai ya sani game da shi amma ya dinga kwantar masa da kai uwa wani gara. Ai ko wlhy sai ya kashe shi. Hankalinsa ya tashi matuƙa, addu'a kawai yake Nurse ɗin nan ya shigo cire musu ruwan daya saka musu ya amshi wayarsa yay kiran Ra'iz yace ya gudu. Sai dai ina ita ƙarshe sunanta ƙarshen ne kawai. Babu abinda ke canja ƙaddarar ƙarshe wlhy. Dan ko munƙi ko mumso dole-dole wataran sai an iskema wannan ƙarshen...
★★★