Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 142

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 142

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 142: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 142. A nan Saudia kam Maanal da…

3,695 words

A nan Saudia kam Maanal da twin's na samun dukkan kulawar data dace ta ɓangaren lafiya da na family, dole Oum da su Ameerah suka wuce Dubai a washe garin cs ɗin, dan lissafin ya canja, dukkan sayayyar da akai a baya ta yaro ɗaya ce. Yanzu kam dole a ƙara tunda ALLAH yay musu ƙyautar biyu. Anan kuma su Yaya Fawzan sunata haɗa abinda ya dace suma sun tura komai Nigeria, sai Abah da AA ne ke tare da Maanal da Babies duk da bama wani barinsu ake koda yaushe suna ganinsu ba sau ɗaya ne a rana. An bama Maanal isashen lokacin hutu ita da yaranta. Aiko tana shan barci sosai bana wasa ba, dan yunwa kawai ke tashinta hakama yaran da ake ba nn da ƙyar tana mita da shagwaɓar zafi-zafi. Wani lokacin dole Doctors ɗin ke neman taimakon AA idan za'a basu abincinsu. Sai ya zauna yana lallashinta da bata baki take haƙuri su sha yanda ya kamata. Gashi kuma Alhamdullah suna wadatuwa da abincinsu. Duk da ma AA ɗin tausayin Maanal yasa kai tsaye ya nema shawarar likitar akan haɗa musu da madara tace hakan yayi. Dan haka yaje ya kwaso irin wadda ta dace ana haɗa musu da ita. Da rana kawai suke shan nn, da dare kuma madara dan ta samu tayi barci ta huta itama. Aiko tsarin yayi, da alama hakan kuma zai tafiyar da tarbiyyar yaran akan cin abincin dare dake jikin mahaifiyarsu. Maanal nada jiki mai ƙyau, a kwana shida kacal abubuwa suka fara daidaita mata sai dai abinda ba'a rasa ba dan cs ba'a rabashi da tsarabe-tsarabe a jikin wanda akaimawa. Kawai dai wanda basu gane bane suke ɗauka cs yafi haihuwa sauƙi. A kwana na tara suka bata sallama, a kuma ranar su Oum suka dawo saudia, dukan sayayyarsu sun turata gida Nigeria. Babu zama suka fara shirin wucewa suma washe gari dan dangi sun ƙosa su koma. Suma dai a ƙage suke da komawa ƙasar haihuwarsu haka nan musamman Abah da Oum dake neman watanni bakwai. Alhamdullahi a yau da Maanal ke cika kwanaki goma ciff da ciro mata kyawawan yaranta jinin Darma da kallo ɗaya zaka shaida haka babu tambaya suka iso gida Nigeria. A mamakinsu sun sami zuri'ar Darma dana Chalawa cike da airport sun zo tarbarsu. Babies na hannun Babban Yaya da Yaya Fawzan, AA angon ƙarni na riƙe da Bestynsa. Yayi ƙyau cikin ƙananan kayansa na fama, itako tana sanye da Abaya ƙirar Egypt kalar oxblood datai mata masifar ƙyau, dan jegon ya sakata zama wata shar da ita. Kumburin nan da tayi duk ya saɓe sai wani uban haske da glowing fatanta keyi like wata laɓuɓuwa can. Bata wankan jego ba wani shan kunu da su miye-miye namu na gargajiya tsabar kulawar data samu a asibitin ce da abincin da suka tsara mata tana ci ne da nutsuwa waje ɗaya, ga isashen barci babu wata hayaniyar ƴan barka ta sakata komawa hakan. Ƙanshi kam da Oum ke dafata da shi ya zauna ɗaram kamar ba maijego ba ya subahannallah........✍️

199

........Suna ƙarasa fitowa inda mutane suke akai musu caaa. Tsabar iya shege irin na oga AA yaƙi sakin Maanal, duk ma wanda zai zo rungumeta sai da ya rungumeta a hakan. Har gwada cire hannunta tayi a nashi saboda kunya amma bawan ALLAH yaƙi bata dama ya katantane. A haka kuma ya jata har gaban su Ammie da su Umma suka gaishesu. Kunya kamar ta nutse shiko ko'a kwalar rigarsa. Yo tunda bai barta ba a gaban Abah da Oum ai dole kowa ma ya shafama kansa lafiya. Kowa ya shiga mota, RK ya ɗauki maijego da angon ƙarni a mota ta musamman da aka tanada domin su. Ashe a can ma gida danƙare yake da mutane ƴan suna domin tarbarsu. Dan yau har ƴan Giro an kaisu can gidan ne. Duk da magrib na neman rufawa sai da Maanal taga garin ya canja mata. Gaskiya Nigeria muna buƙatar canjin shugabanni adalai, masu zuciya da son inganta rayuwarmu da zuciya ɗaya. ALLAH yayi mana dukkan arziƙin da zamu gina ƙasarmu ta kamo waɗan can ƙasashen koma ta fisu amma son zuciya ya hana manyanmu hakan. Mutum ɗaya sai ya handame kuɗaɗen da zasu wadatu mutanen jiha guda. Amma dan mugunta da son zuciya ya tafi wata ƙasa ya zube musu su su ƙaru. Ƙasarshi da al'ummar sa kuwa ko oho. Idan ka shiga ƙasashen duniya kaga fariyayyar da manyan ƙasarmu keyi da dukiyiyinmu su da ƴaƴansu dolene kaji ka tsanesu ka raina tunaninsu. Amma ba komai ai ALLAH baya barci... Kissing ɗin kumatunta da AA yayi ne ya dawo da ita hayyacinta, ta kallesa suka sakarma juna murmushi. Cike da raɗa ya ce, “Mi Bestyna ke tunani ne? Bayan gani a kusa da ita”. A hankali ta sake lafewa a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya, bata ɓoye ba ta sanar masa komai. Shima lips ɗinsa kawai ya cije a hankali. Dan irin wannan ciwon da raɗaɗin halayyar mayan ƙasarmu ya jima da zama gyambo a zuciyarsa. A haka suka iso gida, tun a gate suka fahimci lallai an shirya musu tarba ta musamman, dan gate ɗin kansa yasha decorating, ga wani ƙaton Symbol da aka rubuta sunansa dana Maanal ɗin da hasken wuta, ƙasa kuma na ƴan biyu abin masha ALLAH. Sai suka sauke ajiyar zuciya a tare da har ta saka RK da Uncle Modibbo dake gaba yin ƴar dariya. Maigadi ya wangale gate suka shige, wani irin ƙyau gidan yay musu ga ko'ina cike da dangi. A farkon shigowa RK ya tsaya, basu fito a motar ba aka kawo musu yaran sannan kowa ya amshi ɗaya. Suka ɗan zuba musu ido sai kuma suka ɗago suna kallon juna. Murmushi sukayi AA na wani kashe mata ido ɗaya. Sai abin ma ya bata kunya ta kauda kanta gefe tana cije lips da murmushi. A dai-dai lokacin aka basu damar fitowa. A tare suka fito a nutse, yaran na jikinsu AA ya zagayo inda take tsaye ɗauke da Hussain, shi kuma Hassan ne a hannunsa. Koda yazo sai ya maida yaran a hannunsa ɗaya ya rungumota da hannu ɗaya itama jikinta na'a rabin jikinsa. Ai ƴan Giro sai suka saki baki da hanci suna kallonsu, tab ɗin yo wannan rashin ta ido har ina?. Oho basu san sunayi ba, suko Darma Family ko'a jikinsu. A nutse Maanal suka shiga takawa gaban kowa daki-daki suna gaisuwa ana kallon yaran a haka. Dan Hajiya Shuwa ta kawo shawarar, Abah da kansa ya bada goyon bayan kafa wannan dokar sakamakon zuwa yanzu Mamy ta busar masa da zuciya baya jin yarda da kowa kai tsaye. Duk wanda sukaje gabansa zaima yara addu'a yay musu congratulations na samun ƙaruwa. Har ƴan Giro da Maanal taji masifar daɗin ganinsu. Hakama ƴan uwanta duk suna nan har ƴaƴan Daddy, Huznah ce kawai babu amma har Yaya Yazeed yazo. Koda suka iso gaban Nibras da Saheeba da Nuratu dake a waje ɗaya da ƙyar suka haɗiye abu daya tsaya musu, shakkar AA ta sakasu gaishe da Maanal, duk da dai ita kafin ma suyi magana ta gaishe da Nibras da Saheeba, Nibras da Nuratu sun ƙure AA da kallo kamar zasu cinyeshi, shi kuma yayi kicin-kicin da fuska kamar ba shine ke ɗan sakin murmushi kaɗan ma mutane ba. Manaal da duk ta lura da su ta girgiza kai kawai. Sun ma yaran addu'a da ƙyar, Maanal ta amsa AA kam ko uffan bai ce ba. Daga haka suka wuce sashen Mamy Aunty biye da su dan ita bata fito ba bata jin daɗi. AA baiyi niyyar zuwan ba Maanal ta ɓata fuska da jan hannusa dole ya haƙura suka shiga. Shegiya Uwangale makiran duniya, tana zaune a ƙasa ta kama ƙafar Mamy dake zaune a wheelchiar tana daddana mata. Nan ko da zaginta take tana jin motsin taɓa ƙofa ta kama ƙafar. A kallon farko da Maanal taima Mamy zai da zuciyarta ta motsa. Shi kansa AA ɗin sai da yaji tsigar jikinsa ta tashi. Uwa uwace duk lalacewarta. Amma haka ya daure ya dake bai nuna a fuskarsa ba, dan sun gama haƙƙaƙewa a ransu hakan da suke mata suna nuna kamar basu damu da ita ba maybe ya canja mata zuciyarta mai cike da tsatsa. Itama kallonsu take, kallon dake bayyana abubuwa da yawan gaske a cikin idannunta. Amma haka Maanal ta dake ta je har gabanta ta duƙa tare da ɗaura mata Hussain dake cikin ƙyawawan kaya farare ƙal masu haɗe da showal, ga wani ƙamshi mai sanyin daɗi da sakarma zuciya nutsuwa na fita a jikin yaron. Sun huce abinsu sun ƙara ɗan girma fiye da sanda aka haifesu ƙananu da su fit-fit. Wani irin harbawa zuciyar Mamy tayi tamkar zata fasa ƙirjinta ta fito. Kawai sai taji ma jikinta na neman fara rawa dai-dai shima AA ɗin na ranƙwafowa ya ajiye mata Hassan kamar yanda yaga Maanal tayi. Sai kawai Mamy ta zubama yaran ido, a karo na farko wasu hawaye masu azabar zafi da gudun tsiya suka shiga rige-rigen cika mata idanu dan sai taga kamar twin's ɗinta data haifa bayan haihuwar AA suka rasu, sai kuma gasu da gudu sun zubo suka ɗiga akan yaran. Abin kamar wani almara Hussain ya wani ɗaɗe da kuka kai kace ruwan dalma aka zuba a kanshi. Gaba ɗaya sai Mamy ta rikice. Cike da suɓucewar harshe tana kallon su AA da sauri tace, “Wlhy ba abinda nai musu” sai kawai ta fashe da kuka. A hankali AA ya maida kansa ya duƙar, Maanal kuma ta sake matsawa ta kama hannun Mamy data ɗaga sama kamar wadda tai surrender ta riƙe cikin nata. Cike da lallashi da tausasawa ta ce, “Mamy Please calm down. Mu ma mun san babu abinda zaki musu, haka Hussain yake da rigima sosai. Dan ALLAH ki daina kuka”. Wani shegen murmushin ƙeta Uwangale ta saki, Maanal da ko kallon Uwangalen batai ba tunda ma suka shigo ta cigaba da faɗin, “Mamy ina yini? Ya ƙarfin jiki?”. Zafi sosai Mamy ke ji a ranta, zafi irin wanda kamar ta shaƙe Maanal da waɗan nan yaran da suka mamayeta suka zo duniya a gaɓar da rayuwarta ta gama rugurgujewa. Maanal dai da ta tsana, taƙi alaƙarta da ɗanta mafi soyuwa a ranta yau itace ta haifa yara har biyu da shi. Hakan na nufin bata fita da komai a gidan Darma ba a yanzu. Miyasa ƙaddara zatai mata haka, miyyasa? Saboda mine.... A zuciya take duk wancan tunane-tunanen. A zahiri kam muryarta na rawar tahowar sabon kuka batare data amsa Maanal ba ta zubama AA ido tare da kiran sunansa. Shiru yayi yaƙi ɗagowa tamkar bai ji ba, tsahon minti ɗaya sannan ya ɗago babu wasa akan fuskarsa ya kalli Uwangale. A daƙile a kuma dakensa ya furta, “Excuse us”. Wani irin dukan zuciyar Uwangale razananniyar muryar AA tayi, sai jikinta ya hau ɓari, gashi bataji mi yace ba dan irina ce ba turancin take ji ba. Manaal data fahimci Uwangale bata gane miyace ba a hankali ta riƙe hannun AA ɗin dake yunƙurin sake magana a fusace fiye da farko, sai ta kalla Uwangalen da ɗan murmushi a fuskarta tace, “Kije waje idan mun gama gaisawa sai ki dawo”. Cike da tsantsar ladabin daya bama Mamy mamaki Uwangale harda duƙawa tace, “To to Hajiya, sannunku da zuwa sannunku, ALLAH dai ya raya mana ƴan biyu ya ƙara miki lafiya hajjaju uwar ɗakina. Hamshaƙiya balarabiya jinin girma da ƙyawun sura. Ai Alhaji ya more ƙwarai da gaske, dan ya samu hurulanin sa ta duniya kam”. Ita Maanal ma abin na Uwangale dariya yaso bata, mata kamar zararriya ko haɗiyar yawu batayi wajen magana. Sai da ta fita harta rufe ƙofar sannan AA ya dubi Mamy a karo na farko, babu wasa a muryarsa ya ce, “Maanal ƙara gaisheta”. Ajiyar zuciya Maanal ta ɗan sauke, cike da girmamawa ta sake gaishe da Mamy. Yanzu kam dolenta ai ta amsa, tare da tambayarta ya yaran?. Maanal tai murmushi kawai batace komai ba saboda kunya, ina ita ina amsawa uwar miji lafiyar yara. Ai kodai yayane Mamyn dai mahaifiya ce ko sunƙi ko sun so, baƙin halinta tsakaninta da UBANGIJIN ta ne da ƴaƴanta da mijinta su minene nasu. Sai lokacin AA ya gaishe da Mamyn shima, ta amsa tana share hawayen da shi yasan bana nadama bane ba ko damuwa. Na tsantsar takaici ne da mugun halin daya gama sallamawa da wahala mahaifiyarsu ta canja wlhy, sai dai wani ikon ALLAH kawai dan zuciyar Mamy ta riga ta kangare ta bushe UBANGIJI ne kaɗai ke iyawa da su. Wadda tai yunƙurin kashe musu uba mi kuma ya rage. Bata tambayesa yaran ba, dan haka a dake yace,........✍️200

........“Mamy ga jikokin ki nan, ki saka musu albarka tunda ALLAH ya rubuta zasu zo duniya su sameki a raye damu kammu”. Harga ALLAH AA baiyi maganarsa da wata manufa ta raini ko izgili ko cin fuska ba. Amma sai Mamy ta fassara ta da wani abu daban har zuciyarta na kumfa a cikin ƙirjinta. Da ƙyar ta iya dannewa a taƙaice tace, “ALLAH ya raya”. Komai AA baice ba, dan dama iya abinda yay tunanin ji kenan ya miƙe abinsa tare da kama hannun Maanal da mamakin duniya akan Mamy ke neman halakata. Wlhy tayi zato da tsammanin zuwa yanzu zuciyar Mamy tayi matuƙar laushi da rissina. Kai anya matarnar nan mutumce kuwa? Irin waɗan nan matan ne fa ake kira da ainahin rainon shaiɗan fa. Ace duk wannan abubuwan daka aikata suka fito fili ma duniya bama ƴaƴanka da zuri'arka kawai ba amma sam babu alamar sauyi ko nadama. Hu'um wasu dai kam tun a duniya kake shaidasu a cikin ƴan wuta wlhy.... Tunanin Maanal ya katse saboda ɗora mata Hassan da AA yayi a hannu, shi kuma ya ɗauki Hussain da har yanzu ke kuka. Tissue dake a Centre table na falon ya cira guda ɗaya ya goge hawayen Mamy dake a fuskar yaron har yanzu. A mamakinsu kamar wanda aka cirema wani bala'i sai yay shiru ya koma sauke ajiyar zuciya. AA ya rungumesa a jikinsa kamar yana magana da wani babba ya ce, “Oh Oh! Sweetheart, don't cry. We love you so much me and Mah-mah, alright? ALLAH yayi muku albarka, ya tsarkake ku manyan gobe”. Ya sumbaci yaron ya matsa ya sumbaci Hassan shima itama Maanal ɗin ya sumbaceta sannan ya kama hannunta suka fice. Gaba ɗaya sai Maanal taji babu daɗi, amma babu damar yin magana haka suka fice.....

_________★

A lokacin da nan Abuja suke cikin farin ciki da murnar samun ƙaruwa a Kaduna sabuwa ce ke cikin kuka da nadamar kufcewar komai. Dan kuwa al'amarin rikicin gida sai da ya kaisu zuwa kotu ita da wanda suka saya a hannun Mabera da kuma su Bakori suma da suka sayar. Bayan kaiwa da komawa na kusan watanni uku kenan a yau aka yanke hukunci bisa hujjoji masu ƙarfi. Gida dai da gaske ya suɓuce tunda mai shi ne ya sayar da hannunsa ya kuma basu takardun sa ga kuma saka hannunsa a jiki. Su Bakori da Hajiya Zahedah da suka amshi kuɗin mutane sukaci suma dole sukai amansu. Dan suna ji suna gani haka aka ɗaga gidansu aka sayar aka biya waɗan can. Wannan abu yay matuƙar fusata Bakori dama ga tsanar Hajiya Zahedah da yayi ya tattara nata kadarar kaf shima ya amshe yace a matsayin gidansa. Ya kuma ɗauki yaransa biyu da aka tabbatar sune nashi yabar garin Kaduna. Suko yara abinka da maza takaicin wulaƙanta rayuwarsu da uwarsu tayi ta haifesu ta hanyar zina da aurenta yasasu sakata a gaba da zagi da rashin mutunci, suma suka tattara yanasu-yanasu suka barta kuma sunce na har abada wlhy. To dama biyu sun riga sun zama ƴan samari, tunda har sun fara University. Ƙaramin ne ke ss2 Secondary. Sun tabbatar mata gara su shiga duniya da zama da ita. Tana kuka da roƙonsu ko kallonta basuyi ba sukai gaba. Bayan taci kuka har bata iya gani da ƙyau ta tattara ta koma Bakori, ƴan uwa sukace ina bazasu zauna da ita ba sai dai tayi gaba wlhy, magiya ban haƙuri babu wanda batayi ba amma suka ƙi saurarenta. Haka ta baro garin tana kuka itama ta shiga duniyar dan kuwa a Kaduna dai duk inda ta shiga hantararta akeyi da ƙyamarta ana nunata matsayin mai karuwanci da abokin mijinta. Dole ta yanki tikitin wucewa Legas a motar ƴan kawo shanu dan ko kuɗin mota bata da, can kuma shine mafakar duk wani shege....

★★★

Sabuwa kam samun takardar sakinta uku daga Mabera ya sata kuka matuƙa har idanunta na komawa dishi-dishi bata gani. Kayansu da aka kwaso kusa ta bincike tsaff babu komai nata mai daraja na kayan kuɗi a ciki Mabera ya tattare. Da kayan gidan kawai ya barta sai sutura. Ga mutuwar Nazeerah har yanzu ta gagara sakin mata zuciya. Ga ƙafarta data goce ɗin nan al'amari kamar wasa yana neman zama gaskiya gareta. Dole sai Baba da Daddy keta cacar kuɗin asibiti anama kafar hoto da gwaje-gwajen amma an gagara ganin komai sai uban kumburi take yi. Sarai Hajiya Yaya tasan komai dake faruwa da ƴar uwar tata amma ko a waya bata taɓa kira taji yaya take ba. Sai ma a wajen Daddy ne take jin komai. Kai tunda suka dawo Abuja ma saboda Sabuwa dake a gidansu taƙi leƙa Kaduna ita da ƴayanta. Tana dai kiran iyayenta ta gaishesu tana kuma waya da sauran ƴan uwanta. Dan a sunan nan ma na Maanal har shirin zuwa suke yimata kara dan dama dai sukam basu da wata matsala da Ammie. Wata innarsu ce ta bada shawarar a juya yin na gargajiya ma ƙafar, dan al'amarin dai kam kamar akwai mutanen ɓoye a ciki. Da farko baba ya ƙi dan shi baya son irin waɗan nan abubuwan da ƙyar aka lallashesa. Koda aka gwada zuwa wajen wani malamin magungunan musulunci a kallo ɗaya ya fahimci akwai jinnu a jikin Sabuwa, haka ya shiga mata addu'a da hayaƙin magani sai ko gasu sun bayyana kansu. Basu kuma wani ja al'amarin da nisa ba suka tabbatar da sune suka kadata a waccan ranar, kuma har abada bazasu barta ba sai sun illata mata ƙafafu duka. Dan kuwa abinda tai ne ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya. Tayi ma Hajiya Yaya asiri ne su kuma suka kasa iya komai akan Hajiya Yayan saboda yawan ibada da addu'oi shiyyasa suka dawo kanta, dan su idan aka sakasu aiki basa komawa da shi sai sun tabbatar. Iya ƙoƙari mutum nan yayi aljanun nan subar sabuwa sun tubure akan babu gudu babu ja da baya. Ran mahaifiyarsu ya ɓaci tace a barta da su, ai tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan daka. Koda aka gayama Hajiya Yaya mamaki ta dingayi harda hawaye. Wannan wace irin rayuwa muke ciki haka? Wane irin zamani ne wane irin ƙarni ne ace ɗan uwanka ciki ɗaya, uba ɗaya na shirya makirci da muguntar halaka ka akan son duniya da kayan cikinta. A ganinta bata cancanci haka ga Sabuwa ba, dan kuwa kaf ƴan uwanta babu wanda taima gata da yarda da shi hatta gayama sirrinta irin Sabuwa. Amma ta saka mata da irin waɗan nan abubuwan masu ban mamaki. Irin su Sabuwa suke hana zuminci ƙarko, suke hana yarda da juna ko'a cikin ƴan uwa. Suke saka ma zukata jin ko ƴan uwanka ba kowa ke sonka dan ALLAH ba. Kuma duk da haka akwai na kirki na ƙwarai masu ƙyawawan zuciya a cikin zumincin. Kaicon mu da shagala a wannan duniya, kaicon mu da mantawa da rayuwa mai ƙarewa ce, akwai wata can gabammu mai zuwa. Alkairinka ko sharrinka kuma sune kawai zasu zaɓa maka makoma......

________★

Komai yayima Hajiya Basariyya zafi da ɗaci. Dan a yanzu ta tabbatar da micece rayuwa. Wata irin rayuwa akeyi a gidan Alhaji Balala da wanda ya taɓa sanin minene ainahin rayuwar ƙauye ƙarami irin nasu kawai ne zai fahimci abinda take nufi. Komai a birkice yake a wannan rayuwar. Babu maganar bin dokar ALLAH ko wayewar zamani mai inganci dake tafiya da ilimi. A ɓangaren addini daga Alhaji Balala har matansa babu abinda suka sani balle aje ga ƴaƴa. Ita har mamaki take ma da yaje aikin hajji saudia ɗin wane irin aiki yayi na ibada shi kam. To wlhy ko fatiha Alhaji Balala bai iya karantawa dai-dai. Matansa kam alwala wannan cikakkiya basu iya ba. Balle ai maganar wankan tsarki ma to. Bata taɓa sanin akwai kishin jaraba da bala'i ba sai a wannan gida. Ka rasa mi suke ma kishin. Kwana biyu kacal tayi da lafiya a gidan aka sakar mata jini. Ba ƙaramin tashin hankali ta tsinta kanta a ciki ba. Tun tana ɗaukar al'amarin wasa harta fahimci fa ba wasan bane ba. Dan can taji kishiyoyi sun haɗa kai a tsakar gida suna dariya da arerewa sakamakon Alhaji Balala ya zo ya haike mata kamar wata kasƙantacciyar dabba ta ce masa ga halin da take ciki. Sai kawai ya balbaleta da tujara wai miyasa bazata gaya masa al'adarta zata zo ba, ai shi da yasan haka ne da bai yarda ta tare ba sai ta gama. Amma dan mugun hali tayi shiru ga kwanakin angwancinsa biyu zasu wuce a banza tunda bazawara kwana huɗu ne. Itafa dan mamaki ma kasa motsi tayi ta zuba masa ido kawai. Dan wlhy al'amarin fa ya girmi kanta yafi ƙarfinta. Gaba ɗaya ya sillace ta susuce kamar ba Hajiya Basariyya dai da kuka sani ba. Bata da aiki sai zaman kuka da tunanin yanzu haka rayuwa zata ƙare mata. Magana wannan bata iya maidawa ta zafi yanzu. Duk wannan tujara ta Alhaji Balala matansa na laɓe suna jinsu. To shine fa yana fita suka samu na sanyata a gaba kamar wasu ƙananun yara. Tun bata fahimci da ita ake ba harta gane. Sai kawai ta ɗaukesu mahaukata, amma kuka ya gagara tsaya mata da dana sani da nadama. Ta dinga tuno rayuwar kishi ta gidansu tsakanin ita da Hajiya Yaya da Asiya. “Kai jama'a na cuci kaina wlhy na cuci kaina. ALLAH na tuba ka yafe min ya ALLAH, ALLAH ka sake bani damar gyara kurakuraina. Ya ALLAH ka cireni a cikin wannan gafalalliyar rayuwar na tuba”. Kuka yaci ƙarfinta sosai har tana shiɗewa..........✍️

Hummmmm Hajiya Basariyya kowa ya tuba dan wuya.....🤕201

Readers Also Read